Kurkukun Ƙaddara Book 2 Episode 5

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Episode 5

 

Boss Bature

_~*BossLadiesWriters*~

    KURKUKUN ƘADDARA

  _The Prisoners E5🔥

         *Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~ 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._*ANEELERH*Kwance ta ke asaman katafaren gadon ta da ke acikin haɗaɗɗen bedroom ɗinta da ke a sabon gidan su na Abuja mallakin Uncle ɗan Iya ɗaya daga Cikin ƙannan Abie ɗinta mazaunin garin Abuja, Attajirin mai kuɗi ne mai yiwa ƴan siyasa hidima, Tun bayan da Abie ya samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi aka yi mashi transfer zuwa ministry of finance da ke anan Abuja, a ƙalla yau watan su bakwai da barin jihar jos, ba ƙaramin canjin rayuwa su ka samu ba a gidan ɗan Iya, mutunne mai son jama'a ga iya mu'amala da kyautatawa mutane, kusan halin shi ɗaya da matar shi Aishatu wadda ake da Aunty Ummi.


"Aunty Aneelerh! Auntyna! Where are u? i'm back" can cikin bacci ta dinga jin ana ƙwala mata kira, Sautin muryar matashiyar budurwa.


Nauyin bacci ya hana ta buɗe idanuwanta sai ma ƙara ƙudundune kanta da ta ke yi acikin lallausar bargonta, faɗowa cikin ɗakin ta yi Tabarakallahu Zankaɗeɗiyar budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuɗi,  Ta yi rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ƙaramar wayayyi bace a jin farko, Takalman ƙafarta high hills ne launi ɗaya da Mayafinta white colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. Ƙamshin turaren Jikin ta mai matuƙar sanyaya zuciya, wayar da ke a ruƙe a hannunta ƙirar i phone 15 pro ce.


Agogon bangon da ke a ɗakin ta kalla ƙarfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ƙwayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta ɗanyi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tace"Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje" da zolaya ta yi maganar  a yayin da take ƙarasa shigewa Cikin bedroom ɗin,  Cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, ɗaukar shi ta yi saboda mugunta ta ƙure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke ƙara nannaɗe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunƙurin buɗe ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove ɗin saman drawer, ta ruƙe qugu tana binta da kallo.


Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buɗe ido ta soma surfa masifa tana faɗin"junaid bana hana ka ƙara min sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na damƙi hannun ka sai ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai......" Bata ƙarasa maganar ba ta soma Jin sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan fuskarta.


Gwalo ta yi mata tare da ɗaga mata gira tace"Ba junaid bane yayar shi ce mai irin halin shi, " Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar ƙwayar idon zata faɗo kasa.


Zahra tana dariya tace"Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya dake ni, kai da ka zo baƙunta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci....." bata samu damar ƙarasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi ƙofa cikin rashin sa'a ƙafarta ta jirkice ta fasa ƙara zata kife ƙasa da sauri Aneelerh ta janyota zuwa jikinta, sosai ta ƙanƙameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita sosai.


"Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai ƙwatarki yau sai Allah" Kokoyi su ka soma Yi kamar ƙananun yara, Zahra sai ƙwalawa Umminta kira ta ke yi tana faɗin tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata ƴarta, Aneeleh na dariya tace"Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya" ta ambaci hakan tare da ƙwalawa Maminta kira.


Sun shaƙe junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman tiles, gashin kanta baƙi wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaɗarta.


"Aunty Aneelerh Am sorry wlh na miƙa wuya, zan maki biyayya na tufa bazan ƙara ba" Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta ƙyale ta.


Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ƙasa suka zauna saman floor suna kallon juna.


"Ɗauko mun ruwa mai sanyi in sha" harara zahra ta ɗan jefa mata"Baki da hannu ne"? Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa"bugun da nayi maki bai ishe ki ba" Jin haka yasa zahra yin saurin miƙewa hannunta ɗaya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh tayi fuskarta ɗauke da murmushi fucewa tayi daga Cikin ɗakin, after some minutes ta dawo hannunta ɗauke da glass ɗin ruwa me sanyi, ta miƙa ma Aneelerh hannu tasa ta kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya ƙare, Janye shi tayi daga bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.


"Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo roƙona in faɗa maki ƙiyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin nan da ki ka ƙwallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh, Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi ƙofar fita daga ɗakin tana faɗin"Heart beat of Obinna" Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa"Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne" bayan fitar zahra miƙewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet Muryar zahra ta katse ta"Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty Aneelerh, " Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta ɗauke da murmushi.


Harara ta jefa mata"ƴar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna" Zahra tace"idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki" ta6e mata baki Aneelerh ta yi a yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja ƙofa ta datse.


Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta buɗe ƙofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara ƙyal, ganin yadda zahra ta tsare ta da ido yasa ta murguɗa mata baki "Tubarkallah" Dariya Zahra ta sa ki kafin ta tsagaita da yin dariyar tace"Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa" girgiza kai Aneelerh ta ɗanyi"Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan sanya sutura, Ki jira Ni a palour " maƙe mata kafaɗa zarah tayi"Nifa ba ƙaramar yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace wani gardin ƙato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da....." Kafin ta ƙarasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin ɗakin tana dariya.


Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ƙarasa ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha riga da zane ba ƙaramin kyau su ka yi ba.


"Gani nan tafe" kamar daga sama suka ji miryarta.


Atare suka ɗago suna kallonta, mami tace"yaushe kika dawo gidan"? 


"Ban jima da shigowa ba, Na shiga ɗakin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana bacci," Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun ɗaya.


"Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration ɗin, Kin ci abinci kuwa"? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta ɗauke da murmushi tace"mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan akace maki ta Hamshaƙan attajiran masu kuɗine komai dagaske ake yin shi basu ƙaramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce...." tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace"Ae Obie estate Aljannar Duniya ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace ƙasa kike, tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai ƙaramin Imani na rayuwa acikin tuni zai daina Sallah....." Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su, daga uwar har ɗiyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.


"Aunty duk yadda zan kwatanta maki Haɗuwar Kayan alatun dake acikin Estate ɗinsu Ba zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman Kanta, Ranar dana ta6a zura ƙafa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faɗi, nace Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi" Dariya sosai Mami ta ke yi tana kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta ɗaura da cewa"Ni wlh Naso Daddy ya sama mun Ko aikatau  ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk wanda Ya haɗa alaƙa Da ɗan familyn Obinna kakar shi ta yanke saƙa, Shi da talauci sun raba Jaha...." in serious matter za'a ta ke magana, Ummi taci gaba da cewa"Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama ɗan bangar siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu dangawali arziƙi" ta ƙarasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin abunda Ummi tace"haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar Family ɗin gaba ɗaya, Taya zaki haɗa ni da yaron da har yau ba'asan waye ubanshi ba acikin family ɗin" da mamaki akan fuskar Mami tace"kamar ya ba'asan Ubanshi ba"? Zahra tace"ɗaya daga Cikin ma'aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma farar fata ce,  ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna...." tana magana tana turo baki.


Ummi tace"Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa'an kwando bane, Babban Goro sai magogin ƙarfe, Wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, In banda haɗama irin ta zahra taya zaki nace wa mutumin da yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace ƙwara Dr Jazz ɗin shine dai dai da ke," ɗaure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faɗi, ta haɗe rai sosai, Muryarta a ƙule tace"Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging ɗina, meyasa ta ke yi min haka ne"? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da ƙwalla.


Fuskar mami ɗauke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake"kwantar da hankalin ki zahra, Ai duk kyan takalmi ƙafa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya ƙaddara cewa shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min muƙamin shi duk mun izzar shi da kyanshi wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai kuɗi ko talaka Zahra kuma ta haɗa komai da duk wani ɗa namiji zaiso zama da ita a matsayin matarshi,..." Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna batasan sa'adda ta sauko daga saman sofa ɗin da ta ke zaune ba, ta dawo ƙasa saman carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan ba ƙaramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana yabanta.


"Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta ƙwallafa rai akan abunda ita kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta runƙa tuna matsayinta, Mahaifinta fa ɗan bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata Mallakin Hamshaƙin mutun kamar *OWAIS   SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada Ɗiyar Chancellor na ƙasar Germany  bayan ita akwai Ƴar sarkin saudi arab, Ga ɗiyar shugaban ƙasar America....." Lamarin ya ɗaure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta kai ƙarshen maganar tukunna tace"Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul ainin, Farin Jini sai kace ɗan gwal yo wannan koda lu'u lu'u aka ƙera fatar Jikin shi sai haka,"  Dariya su ka saki gaba ɗayan su.


"Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata ƙofa da za'a Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza" Ummi ce ta kora mata jawabi, Al'ajabi Ya kama Mami"Na ƙosa Inji tarihin Family ɗinsu, Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan fuskokin Ya'yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba"


 Gyara zama Ummi ta yi"Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family ɗinsu laƙabi da shi saboda wadatar Arziƙin da Allah yayi masu, Suna ɗaya daga cikin Most richest family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana faɗi Kakan su ne tsohon ɗan siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ruƙe muƙamai da dama tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaɗai ne ya rage, ƴa'ƴan shi bakwai kaf ɗinsu suna ruƙe da manyan muƙamai, su ke ruƙe da ƙasar nan, Manyan ƴa'ƴan shi ƴan Uku ne sune first born ɗin shi" numsafawa Ummi tayi kafin ta soma zayyana mata sunayen su kamar haka.


"SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar Lagos, waɗannan sune yan ukun shi, bayan su akwai  ƙannan su maza HIS EXCELLENCY DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA Shugaban ƙasar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat ƴar Sarkin Dubai....." Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan alamu al'ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta


"Bayan Hateem sai mai bi mashi SHARAFUDEEN OBINNA Current president na ƙasar Nigeria, Adalin shugaba hawan shi mulki da wata biyar kacal ba a ƙara jin ɗuriyar Ƴan ta'adda ba" Fuskarta ɗauke da murmushi ta yi maganar"Kada ki ji Ina yabon shi ya cancanta ne, matan shi biyu Uwar gidan shi ɗiyar Sarkin Yarbawan Jihar lagos ce, Ta biyun kuma ƴar gidan Alhaji wada ce, Ƙanwar former Gomna na Jiharku Jos" Murmusawa mami ta yi fuskarta da alamun mamaki tace"Wai Alhaji Ubaid ki ke nufi surukin tajudden? Dama ƙanwarshi ke auran Sharafuddeen"? Dariya ummi tayi"haba dai kada ki ce min ba ki da masaniya," watsa hannu mami tayi"taya za'ae in sani? Ni da ba shisshige masu na ke yi ba, In banda ma abun ki ae bani da alaƙa dasu da ya wuce ƙawancen Benazir da Aneelerh, Makaranta ce ta haɗa kuma Yanzu sun rabu, amma duk da haka Na yi mamaki,"


Ummi tace"Auran su shekara goma sha ɗaya kenan A lissafi na, kada ki yi tunanin ina sanya masu ido ne, Kinsan in mutun nada Arziƙi da ɗaukaka a kyauta ake bin diddigin shi...." ta ƙarasa maganar tana dariya Mamin ma dariyar ta ke yi.


"Nasan zakiyi mamaki Idan na faɗa maki cewa Duk irin wadatar Arziƙin dake gare su da ɗaukakarsu Basu da yawa family ɗinsu, Jikokin Obinna Goma sha Biyar" A ɗan ruɗe mami tace"kai! Wai dagaske"? Jinjina kai mami tayi"ƙwarai kuwa, Saratu Obinna ce kaɗai ta ke da ƴa'ƴa Uku, twins zaid da zain sai autarsu Faryat Obinna, Na manta ma ban faɗa maki ita a jerin ƴa'ƴan shi ba, Saratu obinna Itace Autarsu, tana ruƙe da muƙamin Minister of health Mijinta Pravin Obinna ɗan ƙasar india ne silar zuwanta karatun likitanci india Allah ya haɗa ta dashi....." Ummi bata ƙarasa maganar ba, Zahra tai saurin cewa"Cin Arziƙi ya kawo shi, tsabar son banza mami ya canza sunan ubanshi ya maidashi na Obinna, Sai ki rasa gane ɗa ne ko suruki a gidan" tun da suka fara magana sai Yanzu ta tsoma masu baki hannunta ruƙe da wayarta da alama chatting ta ke yi.


"To ke ina ruwanki zahra? Na rasa meya tsone maki ido da mutumin nan, ya fa riga daya zama ɗan gida, yafi ƙarfin a kira shi da suruki sai da ɗa" Ta6e baki zahra tai"Haba Ummi haka ake surukuntaka, mutun ya tare a gidan surukai don kawai yana auran yar shi, nifa Pravin sam baya burgeni mutun kamar ɗan ta'adda" mami sai kallonta take yi, ta fahinci bata ƙaunar mutumin.


Ummi na ƙoƙarin buɗe baki don ta yi magana Muryar Baby Junaid ta katse masu firar tasu.


Mommy! I'm back! I really missed u, Na maki tsaraba" Gaba ɗaya suka ɗago suna kallon shi, shigowar shi kenan Cikin Falon Jikin shi sanye da suit Na yara Black colour, Madarar kyau, Ya ƙara girma ayanzu yana acikin shekara ta biyar a duniya. hannun shi na aruƙe da Farar leda ta shopping, ba shi kaɗai ya shigo palourn ba, Yana atare da Mahboob Ƙanin Zahra, Kamar su sak kamar tagwaye shi da ita, Crazy Jeans ne a jikin shi, daga sama Ya sanya farar t shirt, Sumar kanshi kwance luf tasha gyara, Miƙewa zahra tayi da gudu ta nufi baby junaid tana ware mashi hannu don yazo ta rungume shi, tunkan ta ƙaraso ya girgiza mata kai Yana faɗin"Na mommy ne wlh, Wayo kike so ki min dan In ɗan maki tsarabata" Dariya suka saki, Zahra tace"matsalata dakai kenan, Komai Mommy mommy, idan da kara nima ai uwarka ce, Zonan dallah" ta ambaci hakan tare da janyo shi zuwa jikinta.


Ummi tana murmushi tace"Kada ka yarda Junaid, Aunty zahra wayau zata maka don ka ɗan mata tsarabarka, " ɗaure fuska zahra tayi"Ummi kada kisa ya raina ni fa" Ummi tace"ƙarya nayi ne? Yaro yayiwa babarsa tsaraba ke kuma Uwar wayau kina son cinye mashi abu" gatsina mata hanci zahra tayi tare da Wuce Bedroom ɗin Aneeleh ɗauke da Junaid a hannunta, Ya ɗaure mata fuska duk don kada tace zata Ci mashi tsarabar shi.


"Sannu da dawowa," Mami ce tayi maganar tana kallon mahboob dake zaune saman Sofa, Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya ce"Yawwa mami fatan na same ku lafiya," Suka amsa mashi da lafiyalou


"Har an kammala registration ɗin"? Ummi ce ta yi mashi maganar, ɗaga mata kai yai alamar eh Saura zuwa school Ya rage mashi On monday zai fara zuwa, Uniform ɗinshi suna acikin mota nabarsu, wlh nagaji Ummi yunwa nake ji kamar in ci ƴan hancin Cikina" yai maganar Yana yamutsa fuska,


Ummi tace"nayi zaton Kun biya restaurant Cin abinci" ɗan zaro ido yai kafin yace"Tab, Ga abinci agidanmu sai in kwasa in tafi restaurant cin abinci saboda almubazzaranci, " dariya mami ta saki, Mahboob Ya iya tattalin kuɗin shi, Ya tsani almuzarranci arayuwarshi. Yasan ciwon kuɗin shi.


"Tsokanar ka na ke yi don nasan halinka, Da shegen maƙo, Fatana Allah yasa ba ka bar mana yaro da yunwa ba"  ta6e la66ansa yai"Tun da muka baro school ɗin ya fara yi min kukan yunwa, don dole na tsaya a wata plaza na siya mashi snack, shine fa daya ci ya rage saura nace ya bani inci yace mommyn shi zai ma tsaraba, ni da na sayi abu da kuɗina amma ya hanani ci, Sauƙin ma wurin jatumarshi zanje ta biyani ƴan canji na,"  tuntsirewa Mami tayi da dariya, ita kanta Ummin murmushi ne akan fuskarta, Lamarin mahboob sai addu'a, Babu mutunci indai akan kuɗine

"Kai yanzu saboda rashin ta ido, Sai ka je wurin Aneelerh ka ce ta biya kuɗin daka siyama yaronta snacks? Ɗanka ne fa" Hura hanci yai tare da cewa"Kusan fa dubu ɗaya na kashe mashi, haba ummi, kinsan fa yadda nake wahalar neman kuɗi, Daddy fa ko sisi baya bani sai in yaga dama kema kuma haka" Baki asake Mami ke kallon shi Ummi tace"indai mahboob ne kaɗan kika gani, ae baida mutunci indai akan kuɗin shi ne, Mara Kunya tashi ka bamu wuri, kuɗinka kuma Ka zo da anjima ka kar6a ni zan biya ka," har ya yunƙura zai miƙewa, Idon shi ya sauka akan Ana mai aikinsu Aneelerh, Fitowa tayi daga Kitchen hannunta ruƙe da tray an jera kayan breakfast ɗinsu, hankalinta kwance take tafiya jikinta na sanye da Skirt pensil baƙi yabi shape din Jikinta, Daga sama ta sanya Riga launin green, Ƙura mata ido yai yana kallonta, Idon su mami akanshi ganin yadda yake binta da ido.


Tsawa Ummi ta daka mashi a firgice ya waiwayo yana kallonta, fuskarta a ɗaure tace"Uban me kake kallo"? Yamutsa fuska yai"Kayan abincin dake a hannunta nake kallo ba wani abu ba," yai maganar tare da wuce ya nufi dining table ɗin, da Ana take jera masu kayan breakfast, Kujera yaja ya zauna Yana faɗin"Ya ki ke"? Murmushi ta sakar mashi"lafiyalou, na gan ka ɗazu da safe zaku fita da baby junaid" 6ata fuska yai"shine baki min magana ba mun gaisa"? 


Hankalinsu mami gaba ɗaya akanshi, Ummi tace"Oh Ni ƴar ubansu, Yaro ya zama mayen mata, In banda haɗama irinta Mahboob ina zai kai Ana"? Mami tace"tashen balaga ne kawai, nan da wani lokaci zai dawo hayyacin shi," dariya suka saki, Kafin suka miƙe zuwa Dining ɗin domin suyi breakfast..


Lokacin da Zahra ta shigo ɗakin Aneelerh ɗauke da baby junaid, A zaune ta same ta gefen gado hannunta ruƙe da hoton su, wanda su ka yi aranar birthday ɗin Angel, tun da ta fito daga wanka, ta shirya kanta Cikin riga da skirt, kanta na ɗaure da mayafi, jin motsin shigowar Zahra yasa tayi saurin ɗaura hoton hannunta saman drawer, idanuwanta acike suke tab da ƙwalla.


"Aunty Aneelerh Ga Baby Junaid ɗinmu Ya dawo" cikin sanyin murya zahra tayi maganar don ta fahimci yanayin da Aneelerh take aciki, taƙi ɗagowa su haɗa ido, saboda ba ta san zahra taga hawayenta.


Sauke Junaid ta yi ƙasa, da gudu ya nufi Aneelerh ya haye saman Jikinta hannun shi ruƙe da ledar tsarabarta"Mommy ba ki yi missing ɗina ba"? a hankali ta ɗago ta kalle shi, wani irin farin ciki ya ratsa zuciyarta, duk halin da zata shiga idan tayi tozali da fuskarshi sai ta ji sanyi aranta, Ɗaukarshi tayi tare da ɗaura shi saman laps ɗinta sosai ta rungume abunta"Momy ga tsaraba ki ci" Zahra na atsaye tana kallon fuskar Aneelerh, tsananin tausayinta ta ke ji.


"Thank U my baby Boy, Nayi kewarka kamar zan zauce, Ya school ɗin? Surutu ya soma yi mata yana zayyana mata kyawun makarantarsu, yana magana ya buɗe ledar tsabar ya curo guntun donut daya ajiye mata abaki Ya tura mata, taunar shi ta soma yi tana murmushi, daga gefen su Zahra ta zauna still idonta akan fuskar Aneelerh, Sai kakkauce mata take yi duk don kada su haɗa ido


"Mommy uniform ɗina suna acikin motar bro, hada sandals ɗina, kuma ya ce in faɗa maki ba zai ƙara kaini school ba saboda fetur tsada yake yi, wai sai dai ke kina kai ni" dariya Aneelerh tasaki jin abunda yace"kwantar da hankalin ka, nima ai ina da mota, kuma zan fara zuwa aiki, Kamar yadda nake ɗawainiyar kai Angel makaranta lokacin da tana araye, inje in ɗauko ta kaima haka zan dinga yi maka...." zahra ce ta katse ta da cewa"nima ina da mota, kuma ashirye nake da in dinga ɗawainiyar kaishi," sai da tayi wannan maganar Aneelerh ta ɗago tare da kallonta, Hawayen da take 6oye mata ne suke soma gangarowa saman kuncinta.


"Haba Aunty Aneeleeh i know it's hard to let go of the past, but worrying about it won't change anything wlh bamu jin daɗi idan muna ganinki cikin damuwa" zahra na rufe baki Baby junaid yace"sai da na mata faɗa ta daina kuka, ta ƙi jin maganana, mommy bata jin magana zanje na faɗa wa mami kina kuka" yai maganar yana ƙoƙarin sauka daga saman jikinta da sauri ta ƙanƙame shi"na daina babyna, tun da baka so, ba sai ka faɗa ma mami ba kaji ko" amsa mata yai da toh amma idan ki ka ƙara saina faɗa mata" murmushi Aneelerh ta saki idonta akan zahra dake kallonta.


"Idan ina kallon hotunansu ina tuna irin rayuwar farin cikin da mu ka yi, Shiyasa ni ke zubda hawaye na, Allah na gani bazan Iya mantawa dasu acikin rayuwata ba, waɗannan mutanan uku masu mahimmanci sun kafa tarihi acikin zuciyata, nayi imanin har in koma ga mahaliccina bazan ta6a samun wanda zai maye min gurbinsu ba, Nafi damuwa da Angel wlh ina son yarinyar nan naji takaicin rashinta naso ace sun rayu tare da ɗan uwanta junaid, Angel abun tausayice ta rayu ba tare da mahaifiyarta ba, Na rasa wata irin zuciya ce a ƙirjin benazir......" sosai Aneelerh ta fashe da kuka, Jikin zahra duk yai sanyi, zagayo da hannunta tayi saman bayan Aneelerh ta kwanto da kanta saman kafaɗarta"I feel ur pain Aunty Aneelerh, da inada halin da zan iya yaye maki damuwarki da nayi sai dai babu, abu ɗayane nayi maki alƙawari zan tayaki addu'a, ni a tunanina bai kamata ace anyi shiru da maganar nan ba, idan har ba a yaɗa labarinsu taya za'asan in suna araye? Yakamata atada zancen labarin 6acewarsu a social media, inaso labarin ya zama sabo tamkar a yau ya faru in dai har mu ka yi hakan in sha Allah indai suna araye zasu bayyana ne......." tunda zahra ta soma magana Aneelerh ta natsu tana sauraronta, ga dukkan alamu ta gamsu da zancenta


Da sauri ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar zahra muryarta adisashe tace"Zahra kina ganin idan muka yi hakan za'a dace" fuskar zahra ɗauke da murmushi tace ƙwarai kuwa in sha Allah zamuyi nasara, Kibar komai a hannuna Idan Daddy ya dawo zamu yi magana dashi, tunda kinga shi mutunne na jama'a zai tsara mana yadda za'a watsa labarin 6acewarsu, so nake duniya ta ɗauka," lumshe ido Aneelerh tayi har cikin ranta take jin ƙwarin gwiwa.


"Samu Ƴar uwa kamarki zaiyi wuya Zahra, shiyasa nakeson ki ina matuƙar ƙaunarki, ke ta dabance kina da kaifin basira, Ni ban ta6a tunanin tada zancen 6acewarsu tajuddeen ba sai da ki ka bani shawara, Allah ya Biya maki buƙatunki na alkhairi"


"Ameen auntyna, ko dan saboda farin Cikin ki zanyi ƙoƙari inga an watsa labaransu tare da hotunansu, "farin ciki ya cika Aneelerh, sosai ta rungume zahra, Baby Junaid yayi lamo saman ƙirjinta, sai faman lumshe ido ya ke yi bacci ne ke shirin ɗaukarshi


"Excuse ma'am" muryar Ana ce ta katse su, atare suka ɗago suna kallonta, tana daga tsaye bakin ƙofar ɗakin, a mutunce suka gaisa kafin ta sanar dasu cewa Breakfast yana jiransu a dining' amsa mata su ka yi da toh, kusan atare suka miƙe, Aneeleh na ɗauke da babyn junaid" 
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426, 
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post