Kurkukun Ƙaddara Book 2 Episode 6

Kurkukun Ƙaddara Book 2 Episode 6

 _~*BossLadiesWriters*~_           _*KURKUKUN ƘADDARA*_


          


  _The Prisoners E6🔥💫_


    

         *Daga alƙalamin Boss Bature*~Middle step~ 
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._


*JUSTICE DEMOCRATIC PARTY*


(JDP HQ)


Manyan mutanene dattawa da matasa zazzaune a babban ɗakin taro na jam'iyyar Justice democratic party ɗaya daga cikin jam'iyun da su ka shara a ƙasar Nigeria, zungureran table ne wanda ke kewaye da kujeru, daga saman teburin akwai microphones na kowani member da zai yi magana, An tanadi kayan sha jere saman table, ɗakin taron yai tsit babu mai magana a cikin su, fitinannan ƙamshin turaren jikinsu ya gauraya da sanyin A.c na comference room ɗin da su ke a ciki.


 Tsabar 6acin rai ne da fusata akan fuskokin su ga dukkan alamu suna fuskantar tashin hankali a jam'iyarsu, musamman party leader ɗin su Alhaji bukar mai guduma fuskarshi a murtuke ta ke babu annuri, baƙin shi ya nunku har shining ya ke yi, Ya dunƙule tafin hannayensa da ya ɗaura su saman table din, Kowannan su ya ɗauki wankar tsadaddiya shadda daga gani naira ta zauna masu, kuma gogaggun ƴan siyasa ne waɗanda su ka jima a harkar suna gwagwarmaya, tsawon mintuna goma shabiyar, kafin shugaban jam'iyar mai guduma ya sassauta fusatar fuskarshi idanuwanshi jawur ya ɗago yana kallon mambobin su, tun daga jerin waɗanda ke a 6angaren damansa, Alhaji ubaid wadata Alhaji musa wadata former president, Alhaji badamasi da sauran ƴa'ƴan jam'iya, A hankali ya ɗauke idanuwan shi daga ta 6angaren dama ya mayar dasu kan mambobin dake zaune 6angaren hagunsa, Jinjina kansa ya ɗanyi yayin da ya ke fitar da huci ya soma magana tamkar mayunwacin zaki"Me ke shirin faruwane da jam'iyar mu? Zamu zauna ne mu zuba ido kamar mazurai muna kallon su? Mun ɗaura shugaban ƙasa dudu 4 yrs ya faɗi aza6e, mun kuma tsayar da sabon ɗan takararmu ubaid wadata an kayar dashi aza6e, Ga dukkan alamu durƙushewar jam'iyarmu ce tazo, tayaya jam'iyar da bata fi shekara biyar da kafuwa ba zata  nemi ruguza tarihin tamu party din? A zafafe ya kai ƙarshen maganar yana kallon kowan nan su, babu wanda yai yunƙurin tanka mashi saboda sunsan halin shi idan ranshi ya 6aci, wani irin bauɗaɗɗan mutunne,


Jinjina kan shi yai yayin da ya ke fitar da huci duk irin sanyin A.c da ke shawagi a ɗakin hakan bai hanashi fitar da gumi ba.


"Babu irin tarihin da jam'iyar mu bata kafa fa, Ina ce shi kanshi dattijon arziƙin rainon jamiyar jdp ce, daga baya ne ya sauya ra'ayin shi akan wata manufa tashi ta daban wadda ba mu da masaniya akanta ya kafa tashi jam'iyar mai taken Progressive action party (PAP) Yan zu ga shi cikin ƙanƙanin lokaci sun ƙwace ƙarfin ikon da mu ke da shi a ƙasar nan, tsabar haɗama gaba ɗaya ƴa'ƴan shi ke juya ƙasar nan idan har bamu ta6uka wani abu ba zamu tashi a tutar babu ne"! Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu Ya daki table din gaban shi, kowa yasha jinin jikin shi, damuwace ƙarara akan fuskokin su.


Gyaran murya Alhaji Ubaid wadata yai kafin atsanake ya soma magana cikin dattako


"Allah ya huci zuciyar mai girma jagoran mu, Ni anawa ganin yakamata  mu fito da dabarun da za mu bi don ganin mun dawo da ƙarfin ikon da mu ke da shi ada, idan ma ta kama mu bi tsarin da su ka ɗauko wanda yasa jama'a suke rububin tasu jam'iyar, Idan har muna so mu farfaɗo da tamu jam'iyar" bayan Alhaji ubaid yai magana sauran Ƴan jam'iyar kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, Idan ka cire mutun ɗaya wanda tun da ya zauna meeting ɗin idanuwanshi su ke a lumshe daga gani yana da jiji da kai da izza, ɗakin taron ya rikice da zafafan zantuttukan su kowa yana faɗin ta cikinsa, rai amatuƙar amace Ya sanya hannu ya daki table ɗin gabanshi wanda silar hakan ya janyo hankulansu ga dubanshi, Ƙaraminsu babbansu slowly ya buɗe idanuwanshi akan faces ɗin su, sun kasa kunne suna jiran jin me zaice hatta shugaban jam'iyar tasu ya natsu yana jiran jin bayani daga gare shi.


Cikin harshen turanshi Ya soma magana da kakkausar murya"Let's take a step back and focus on what we need to do right now. We need to come up with a strategy for the next election, We need to come up with a plan to fight back. We need to show the people that we are the party that can make a difference in their lives. We need to show them that we are the party that cares about their needs. We need to show them that we are the party that will fight for them, And We need to let them know that we are the party that is on their side." tun da Alhaji musa wadata ya soma magana ƴa'ƴan jam'iyar su ke jinjina kansu ga dukkan alamu ya ɗauko magana mai ma'ana a ƙarshe ya daki table din gabanshi ya furta"Sharafudden obinna ba zai haura 4 years a mulki ba! Alƙawarine na ɗaukar wa kaina, duk yadda za'ae sai mun kayar dashi a za6e na gaba, dole jam'iyar mu ce asama babu wani mahaluƙi da ya isa ya durƙusar da jam'iyar mu, abokan hammaya ba za su ta6a cin galaba akan mu ba," yana kai ƙarshen maganar azafafe ya yunƙura ya miƙe yana gyara malunmalun ɗin jikin shi, Ko sallama baiyi masu ba, Ya haura ƙafa yabar cikin ɗakin taron, yayin da su ke bin bayanshi da ido, har saida ya 6ace ma ganinsu tukunna suka dawo da dubansu kan maiguduma. tattaunarwar tasu ta ɗauki tsawon awa ɗaya kafin suka rufe taron da addu'a da kuma fatan nasara ga jam'iyarsu, Ɗaya bayan ɗaya suke fitowa harabar headquater  inda jerin danƙara danƙaran motocinsu suke a killace. Bayan sun ƙara gaisawa da juna kowa Ya nufi motarshi, Musa wadata Yana kishingiɗe a back seat na danƙareriyar motarshi tsadaddar gaske, Ya lumshe idanuwanshi sanyin A.c ta ko'ina, gefen shi P.A dinsa ne, security ɗin da ke jigilar tuƙa su yana zaune a driver seat yana jiran jin umarninsa.


Ƙwanƙwasa glass ɗin motar da akayi ne yasa shi ware manyan idanuwanshi, muryar Alhaji ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi"Ina son magana da kai" Iya abunda ya furta mashi kenan, Muryarshi da izza ya amsa mashi da toh, daga haka yaba drivern nashi iznin ya tada motar su nufi gida" A jere motocin su su ka nufi gate ɗin fita daga cikin headquater ɗin su...


*JOS CITY*


Zaune ya ke saman darduma cikin shigar larabawa farare ƙal, kyakkyawan balarabe daga ganin fuskarshi ba ƙaramin mutun bane ya ɗan fara manyanta, Arab turban ɗin da ke nannaɗe akanshi, ya ƙara mashi kyau ga wani kwantaccen saje baƙi wulik mai matuƙar jan hankali, lallausar sumar kanshi ta sauko har saman wuyanshi dark black.


Daddaɗan ƙamshin turararen jikin shi mai matuƙar sanyaya zuciyar mai shaƙar shi, idanuwan shi suna a lumshe yayin da ya ke yin qira'ar Alqur'ani mai girma, Yatsun hannunshi na dama na a asargafe da cazbaha, Qur'anin da ya ke karantawa yana agabanshi saman wooden qur'anic stand dogayen eye lashes ɗinsa a jiƙe su ke sharkaf da hawaye ga dukkan alamu ayar da ya ke karantawa ce ta sanya shi tsuma.


Sam bai ji takun tafiyar mutun acikin ɗakin shi ba, tafi ƙarfin mintuna talatin da shigowa, idanuwanta akanshi ganin bai da niyar tsagaita karatun ƙur'anin nashi ne yasa ta ambaci sunan shi


*"DR SHUREIM*"Nasan kana jin takun tafiyata don haka idan ka kai ƙarshen Aya ina son magana da kai"! tamkar ta yi magana da bango ko kallo bata ishe shi ba, sai ma ƙara sautin muryashi da ya yi" dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi ta kai hannu ta rufe qur'anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta ƙwace cazbagar dake nannaɗe a hannun shi ta ɗaura ta saman qur'anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin karatun duk don kada ya saurari maganarta.


Tana huci ta ɗago tana kallon shi still bai buɗe idanuwanshi ba, kuma bai dakata da yin karatun ƙur'anin ba domin kuwa haddace akanshi


"Ka da ka bari raina ya 6aci wlh  zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me na yi ma ka daka ɗaura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda tafi ni ne a duniyar nan"? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaɗa kai tayi"ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba, tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka Shureim"? Cikin jin ƙunar rai ta yi maganar, A hankali ya buɗe idanuwanshi farare ƙyal da su ya ɗaura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban ɗansu, Ya ya ne awurin Benazir mahaifiyar Angel.


Daddaɗar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta"ba ki min laifin komai ba, har yanzu kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana buƙatar kusancin ki da ni" Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna"Nasan dalilin dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ruƙe abu aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata ƙara faru wa ba" fuskarshi a ɗaure ta ke babu walwala" tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai ƙara magana ba.


Ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, zuciyarta na ƙuna tace"na lura sam faɗuwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana ƙaunar mu a matsayin mu na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu" murmushin takaici dr shureim ya saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen haƙoran sa su ka bayyana masu kyau da tsari.


"Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya" fuskarta a ɗaure tayi maganar, Yunƙurawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana"Saboda ku ba iyaye bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba, Gaba ɗaya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faɗi a za6e? Aini abun farin cikine agare ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin ciwon ƴa'ƴa Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa dana tsinci kaina aciki......." daƙyar ya ƙarasa maganar cikin jin ƙunar rai, a bun ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi adisashe yace"kun manta cewa ƴa ƴa amana ne agare ku? Ranar gobe ƙiyama Allah zai tambaye ku game da amanar da ya ba ku, Rashin nasara yanzu ku ka fara gani, in sha Allah ba zaku ta6a samun abunda ku ke so ba, har tsayuwar dare zanyi maku akan kada Allah ya cika maku burinku na mallakar kujerar....." bai ƙarasa maganar ba sakamakon zazzafan marin da Layla ta sakar mashi, da sauri ya dafe kuncinsa da tafin hannun shi na dama, Idanuwanshi sun rune zuwa ja.


Tana hu ci ta nuna shi da yatsa"don uban ka ka tattara kayan ka kabar gidan nan tunkafin ranka ya 6aci, shashasha kawai wanda baisan ciwon kanshi ba," Cikin sanyin murya yace"zan tafi koda ace baki kore ni ba Mommy, dama ita gaskiya ɗaci gare ta, kuma in sha Allah zanje na nemo ƴar uwata benazir aduk inda take, idan ku bakusan ciwon kanta ba ni na sani...." tunkan ya kai ƙarshen maganar layla ta nufi ƙofar fita ɗaki kamar zata tashi sama tsabar 6acin rai.


Zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa idanuwansa jawur hawaye na cigaba da gangarowa saman kuncinsa, haƙiƙa mahaifiyarshi ta fama mashi mikin dake acikin zuciyarshi, matsawa yai gaban gadon shi ya miƙa hannu ya ɗauki wayarshi yana duban hoton da ke a kan wallpaper na wayarshi, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su sosai akan hoton da yake kallo, baya gajiya da kallon fuskarta A hankali ya furta


_ke ce silar tarwatsewar farin cikina kuma kece silar shiriyata! Ki yafe min nayi kuskuren da bazan ta6a gyara shi ba, ina son ki sosai ina jin ki har cikin raina, nasan haƙƙin ki ne ya ke bibiyar rayuwata_


kifa kansa yai saman mattress sosai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro.


Bayan fitar Layla kaitsaye ta nufi falon gidan, ranta ya 6aci sosai, kalaman Dr shureim sun sosa mata zuciyarta, yau kusan shekara uku da dawowarsu Nigeria tun bayan barin su Dubai, Layla taji takaicin faɗuwar Alhaji ubaid saboda tafi kowa ƙwallafa rai akan hawan shi mulkin shugaban ƙasa don ta ji daɗin yin sharholiyarta a matsayin first lady, sai dai Allah bai basu nasara ba, bugu ɗaya aka ƙundumo shi ƙasa, tun farko sai da ya ji fargabar tsayawa takarar jin wanda za su kara da shi, don kuwa yasan muddin Sharafudden Ya nemi takarar shugaban ƙasa zaiyi wuya ya iya kada shi, sanin farin jinin da Allah ya yi mashi, Mutun ne na jama'a mai kyautatawa al'umma.


"Hajiya.."muryar mai aikin gidan su ce a dabarbarce ta ambaci sunanta ganin yadda ta bi ta da matsiyacin kallo"lafiya"? 


Cikin harshen larabci ta ce "Mun yi baƙi ko da ya ke sun wuce baƙi" 


"Saboda ƙannan uwata ne"? Ta jefa mata tambayar, Sunnar da kai ƙasa zainab ta ɗan yi"Hajiya Aisha ce matar governor tare da...." bata kai ga ƙarasa maganar ba, layla ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu"ni ban  gayyaci uban kowa ba a gidana, Matsiyatan banza gulmace ta kawo su wato an zo aga yadda na ƙare to ta Allah ba ta su ba ƴan kutmar uba, jajen ne har yanzu bai ƙara ba abu an kusa rabin shekara da faruwarshi saboda baƙin hali sunƙi su manta.." tun da ta fara sambatu zainab ta yi kasaƙe tana kallon fuskarta ba ki asake, ta fahimci zallar baƙin ciki ne Azuciyar uwar gidan ta ta, rashin nasarar su ya tsaya mata a zuciya nema ta ke ta zauce, dama ya lafiyar gwiwa mutun mai ƙarancin imani.


Tsawa layla ta daka mata, firgigit! zainab ta ɗan zabura"Ki je ki sanar da su cewa bana nan" muryarta na ɗan rawa tace"Ae an riga an faɗa masu cewa kina a cikin gidan, yanzu haka anyi masu iso suna acikin main palour..." daƙyar zainab ta ƙarasa maganar tana mai haɗiyar yawu ganin irin kallon da layla ta ke jefa mata tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa, guntun tsoki taja"masu aikin gidana sun fara raina ni saboda rashin nasarar mu dole na yi wani abu akai, su kuma waɗancan taron magulmatan zanje gare su, bari na fara zuwa ɗaki in zuba gwalagwalai na don kar su raina ni" acikin zuciyarta ta yi maganar tare da juyawa ta nufi sashen da ɗakinta Ya ke. 


Binta da ido zainab ta yi haɗi da ɗan girgiza kanta"Allah ya shirye ki layla" har zata Juya idon ta ya sauka akan Dr shureim da ke shirin fitowa daga ɗakin shi hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, tsananin tausayin shi ne ya kamata ganin yadda ya canza, ta lura da damuwar da ke akan fuskarshi, a hankali yake tafiya yana tunkaro inda take ga dukkan alamu bai lura da ita ba har sai da ɗan yi mashi gyaran murya, tukunna ya ɗaura fararen idanuwanshi akanta, Sam babu walwala akan fuskarshi, darajar da ta ke da shi a idon shi yasa shi nufarta, ya ɗauki zainab taimkar auntynsa, Babbar macace mai hankali da natsuwa.


Yana ƙarasa gabanta ya duƙar da idon shi ƙasa ba tare da ya gaishe da ita ba


"Ko ba ka faɗamin ba dr shureim naga damuwa akan fuskarka, na ɗauke ka tamkar ɗan ciki na, dan Allah shureim ka da ka bari damuwa ta canza ka, inaso ka sani komai ya faru muƙaddari ne daga Allah, rubutacciyar ƙaddara ce wadda ba wanda ya isa ya canza ta" cikin kwantar da murya ta ke lallashinsa, sai faman karkaɗa car key ɗin hannunsa yake yi, tun da ta fara yi mashi nasiha bai tanka mata ba sai da ta kai aya tukunna ya soma magana a tsanake "Aunty zainab na aikata babban zunubin da har abada ni nasan Allah ba zai ta6a yafe min ba, Ni kaina nayi danasin mara amfani...." duk yadda yaso ya jure ya kasa kamar ƙaramin yaro cikin muryar kuka yaci gaba da cewa"Ina sonta aunty zainab sune silar komai, bazan ta6a yafe masu ba na tsane su, Mu kuma tamu jarabtar ta iyaye ce, basu damu da mu ba, buƙatar su itace agabansu, Yan zu haka da nake maki magana Mommy ce ta kore ni saboda na faɗa mata gaskiya, ki yi haƙuri Aunty zainab kada ki ce za ki dakatar dani ƙwara na tafi, zama atare dasu bai da amfani, zanje na nemo ƴar uwata Benazir In ruƙe ta a hannuna waɗannan mutanan ina zargin sune silar tarwatsewar rayuwarta kamar yadda su ka yi silar tarwatsewar tawa rayuwar......" yana magana hawaye na cigaba da wanke fuskarsa, ita kanta zainab ɗin tuni idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, ruƙo hannunshi tai a cikin nata, da sauri ya ɗaura kanshi saman kafaɗarta"Shureim Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wanda ya cuci wani Allah zai saka mashi, ko a tsakanin ƴa'ƴa da iyayen su akwai hisabi, Na yi maka alƙawarin zan taimaka maka akan komai, ashirye ni ke dana zama uwa agareka, Ae ɗa na kowa ne idan su basu so to ni inaso, dama ban ta6a haihuwa ba" jin abinda tace ne yasa shi ɗago da fuskarshi yana kallon ta, murmushi ya ƙaƙaro akan fuskarshi, haƙiƙa kalamanta sun sanyaya masa zuciyar shi.


"Aunty zaina are u serious zaki taimaka min"? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, farin cikine ya bayyana akan fuskarshi'Aunty zainab akwai wani aiki da nake so mu yi atare bana so kowa Ya sani...." bai kai ƙarshen maganar ba, Takun tafiyar Mahaifiyarshi Ya dakatar dashi, muryar zainab na rawa tace mashi


"Ka tafi kawai zan kira ka awaya anjima sai mu yi magana" amsa mata yai da toh, Da sauri Ya fuce ita kuma ta nufi hanyar kitchen.


Cikin takun izza ta ke tafiya, har ta canza kayan jikinta zuwa tsadadden leshi wuyanta da hannyenta Zinari ne, ta buga uban ɗaurin kallabin nan ture kaga tsiya, Takalman ƙafarta high hills ne, ta wanke jikinta da turare, tana tafiya tana hura hanci


Tana dab da zata shiga palourn gidan muryoyin manyan matan da suka kawo mata ziyara ta karaɗe kunnuwanta, da sauri ta la6e tana sauraron abunda su ke tattaunawa


"Ae ban ta6a ganin mutum mai haɗamar tsiya irin Alhaji ubaid ba, nifa  tun lokacin da ya sauka mulki yana fama da ciwon ƙafa raina ya bani cewar wani munafuncin suka ƙulla ashe kujerar shugaban ƙasa yake so, yanzu gashi ba wan ba ƙanin duka sun rasa" 6a66akewa su ka yi da dariya


"Ni dama tun da naji Sharafudeen Ya tsaya takarar shugaban ƙasa raina ya bani cewar shi zaiyi nasara, sai gashi ta tabbata, wa zai Iya ja dasu? Ganganci ne ya kai Alhaji ubaid, Ko da ya ke matar shi ce mai haɗamar a yadda na fahimta" hajiyar da ta yi maganar ta ƙarasa tana dariya, wata ta ɗaura da cewa"ai ko sharafudeen bai tsaya takara ba kinsan Allah ba wanda zai za6i ubaid, Mutanan da basu son darajar ƴa'ƴan su ba taya zasu Iya ruƙe ƙasa irin nigeria mai cike da taron Talakawa? Ƴar ta fa benazir tana ƙasar ture, ayadda naji labari karuwanci take yi kuma ana zargin uwarce ta turata, Allah na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai ƙarfi naji ..."Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi matuƙar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu ba, haƙiƙa ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da yin firar, ɗaya bayan ɗaya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya ke.......


*UNCLE ABDALLAH*


A ƙalla yau wata ɗaya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ƙara ƙiba abunta.


Ta natsu tana kallon portrait artist ɗin dake zuƙunne agaban Drawing board Yana gudanar da aikinsa, daga ƙasa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da hajiya adama ta miƙa mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a shekarunta na yanzu don su samu sauƙin gane ta


"Ranki shi daɗe, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu"? Me zanan ne yai mata tambayar.


"I think 15 to 16 years," amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan shi,


 "Mijina ya faɗa min cewa kai ƙwararre ne a 6angaren zana mutane, so please don't disappoint me" murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta mata"In sha Allah" 


"Assalamu Alaikum"! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi, Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri ɗayane.


Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara'a ya ɗago ya kalli Hajiya adama"mu shiga ciki ina son magana da ke" amsa mashi tai da toh, Yai gaba ta miƙe tabi bayanshi, A cikin bedroom ɗinsu su ka tsaya suna fuskantar Juna


"Tun ɗazu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na ƙwallafa raina akan son ganinshi, "


"Duk yadda kika kaiga ƙagara da son ganinshi ba ki kaini ba,"


"Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani ɗa da zamu dinga kallo muna jin daɗi" fuskarta amarairaice tayi mashi maganar, girgiza mata kai Uncle Abdallah yai"idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta"? Ɗaure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci"Abdallah baka son farin cikina, Ni zan koma palour wurin mai zanan can" Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi, Har takusa kaiwa bakin ƙofa muryarshi ta katse mata hanzarinta"ba zan ta6a manta irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin bana son farin cikin ki"? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta


"A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama, na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da ɗanta ba, haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai" idanuwanta ne suka cuko tab da ƙwallar farin ciki.


Fasa fita ta yi daga Cikin ɗakin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta saman ƙirjinshi, Hannun shi Ya ɗaura saman bayanta yana cigaba da gayamata daɗaɗan kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta ɗago dakai Tana kallon shi


"Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea, Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matuƙar ƙaunarta, kuma zatayi mamakin ganinta a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun ƙware a iya zane" tana magana Hannunta ruƙe da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta


"Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu ɗari akayi maki shi fa"


 murmushi ta ɗan saki"saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na ɗauke shi," yace"mai zai hana ki bata sabon zanan da za'ayi ke sai ki ruƙe na koriyan? Girgiza kai ta yi alamar "a'a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da tsada, Farin cikinta kawai nakeso,"  yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata aƙasar korea, ba ta kawo komai aranta ba saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba.


"Hajiya an kammala" daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su ƙarasa shiga Ciki idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel jikin allon zanan nashi, Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana tajudden Hasken fatarne kaɗai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta.


"Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over" hajiya adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin zanan, Suffar Angel sak sai dai an ƙara mata girmanta, takai dai dai age ɗinta na yanzu 15 to 16 years, 


Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke yabon aikinsa


"Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru nayi maka alƙawarin zan ninka maka kuɗinka" fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar tana kallon mai zanan, washe baki yai yana faɗin"In sha Allah ranki ya daɗe ƴar ki zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina roƙon Allah yasa zanene ya zama silar ganinta" atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan saida suka haɗa mashi sha tara na arziƙi.


*EVIL FOREST*


*the Prisoners💔*


Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah kaɗai yasan awanni da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya duhun dajin ya ɗan washe, A hankali ta soma mutsun mutsun buɗe idanuwanta a yayin da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai daƙyar ta ke iya buɗe shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, kaɗan ta ke iya buɗe shi tana kallon Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun ƙaddara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take ƙoƙarin ƙwalawa ƴan uwanta kira ɗaya bayan ɗaya, duk tabi ta furgice.


"Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne"? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da ƙarfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya ɗan ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya ƙirjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta"My Angel" jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, ƙoƙari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, kaɗan ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi"Da..Nish" fatanta Allah yasa ba mafarki bane.


Dogayen yatsun hannun shi ya ɗaura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta ɗaura nata hannun saman nashi dake akan face ɗinta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, Ɗago da ita yai zuwa saman ƙirjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ƙanƙameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri,


"I can't explain how much I miss you. I'm sorry for what happened, it's all my fault. I'm sorry, Angel."


Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shessheƙar kuka ta soma yi mashi magana"ba laifinka bane Danish, ka daina faɗin hakan, ni abunda yafi damuna rashin ƴan uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu alƙawarin da na ɗaukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran ƴan uwan mu da mu ka rasa" daƙyar ta ƙarasa maganar, zafin jikin su duk ya ɗumamasu, Yanayin weather ɗin dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa.


Ɗaura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaɗai yasan raɗaɗin da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi ta ɗaura eye balls ɗinta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke ƙarewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, ' 


"Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai ƙara ta6a zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu," shiru bai tanka mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta


"Danish! Am talking to u, bana jin daɗin jikina, maganar ma daƙyar nake iya furtata" Still bai motsa la66ansa ba' ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido Ya ƙi tanka mata," Gyaɗa kai tai"shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je na rufe su" tana ƙoƙarin miƙewa sexy voice ɗin shi ta ratsa kunnuwanta"Kin ta6a ganin an binne mutun da ranshi"!! ras taji gabanta ya faɗi a matuƙar ruɗe ta zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi........ 
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426, 
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post