*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 24
*_Asalamu alaikum warahmatullah,barkanmu da warhaka_*
*_Har yanzu dai ina nan ina ci gaba da sauke muku kabakin kaya masu tsananin kyau quality da kuma saukin kudi kamar a kyauta a HUGUMA CLOSET_*
*_SARI KIKEYI KI SIYAR KEMA?,KO NA SANYAWARKU NE A JIKI?_*
*_TO TABBAS BA GROUP DIN DA YAFI DACEWA DAKE SAISHI👍_*
*_ki siya kayanki cikin farashi me sauqi,kaya masu quality kuma unique one,suzo su sameki fiye da yadda kike zato hankalinki kwance cikin aminci_*
*GANI ANCE YA KORI JI*😊
Iftee na riqe hannun wasila suka fito daga sashen ruqayyan. Tayi kyau sosai cikin doguwar rigar wani material wadda take zuwa hade da mayafinta,yaron cikin jikinta ya qara mata kyan fuska da na fata gaba daya. Fes da ita qamshin sassanyan turarenta kawai takeyi.
Hira Suke ita da wasilan,wasilan na qorafin kan case dinta da faisal
"Nidai bansan lokacin da idanunki zasu bude ba wasila,bansan sanda zaki gane abinda ke gabanki ba,ai alamun qarfi yana ga me qiba,hakanan duk juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,ya kamata ki bude idanunki da kyau wasila" baki tadan tabe,har yanzu tana jin ciwon abinda faisal yayi mata
"Shi kuma isma'il gaba daya yama daina kirana"
"To zaizauna ne kina wulaqantashi son ranki?, bazaiyiwu ba ai,Allah ya hada kowa da rabonsa,tunda dai ya baki dukkan dama"
"A yadda ma naji wai yakai kudin aure" ta fada tana jin dacin abun har cikin ranta
"Ato,kinga ya sawwaqa miki wahala ko?" Maimakon wasilan ta amsa sai sautin dariyarta da ya isa kunnen ruqayya dake qoqarin zura key ta bude motarta. Daga kai tayi tana duban wasilan
"Ke kuma lafiyarki?,muna magana me ciwo da kuma muhimmanci kina kuma dariya?"
"Qanwarki za'a tambaya lafiyarta daya?,don muhammadur rasulillahi da gaske haka zata je makarantar 'ya'yan nata?" Duk yadda ruqayya taso ta dauke kai kada ta kalli zainab amma saita kasa,yadda wasila ke sheqa dariya abinta ta tabbatar ba qaramin abu bane.
"Subhanallahi" ta fadi tana dauke kanta da sauri kada zainab ta fahimci suna maganarta ne. Wata irin hautsinanniyar shiga tayi kamar wadda ke shirin fara aikatau din abincin biki. Sai data tausa kanta da kyau sannan ya hadiye dariyarta,ta jefi wasila da harara
"Gulma ajali,to ina ruwanki?"
"Ki barni Allah yau daya na bata shawara kada taje a haka ta zubdawa 'ya'yanta aji" caraf ruqayya ta kamo hannun wasila,domin kuwa tasan halinta sarai,'yar takife ce,tsaf zata iya tarar zainab din,tayi imani kuma abun bazai qare da kyau ba,wasilar 'yar rigima ce ta gaske,zainab kuma ba haquri ta tabbatar ba zata dagawa wasila qafa ba.
"Ba ruwanki don Allah, shige mu tafi" ta fada tana turata gaba. Duk da haka bata fasa tiqa dariyarta ba har zuwa sanda zainab din tazo giftasu. Suna Hada ido da ruqayya ta saki wani mugun tsaki sannan ta barke da waqa tanayin gaba
"Kanbalasti,don girman Allah ki barni na yagawa jakarnan dawa,wai ita a nan haka macace?" Wasila daketa dariyarta kamar ba gobe ta fada.
"Nace miki dai ba ruwanki bakinta ne tayita yi"
"Su kishi manya,ni da gwaigwai" wasilan ta sake fadi tana kallon qafafun zainab data rabasu tana niyyar shigewa mota
"Nikam wannan matar ko primary ta gama kuwa?"
"Bansani ba nidai" ruqayya ta fada tana tayar da motarta tare da qoqarin danne dariyar da wasila ke qoqarin sakata yi qarfi da yaji.
Ta daidaita motar suna shirin fita dab da motar zainab din wasila ta sauke glass
"Mata suna muka tara,a cikinmu wace zara tauraruwa acan a sama......" Daga haka ta fuske ta maida dubanta wani sashen na daban.
Sarai zainab taji maganganun wasilan,kuma ta tabbatar da ita take,ba tun yau ba tasan halinta,wannan ya sanya sam basa shiri da ita,muddin tazo gidan ba kasafai ta fiya tafiya salamun qaulin wani abun bai hadasu ba.
Mita ruqayya ta shiga yiwa wasila bayan sun fita a gidan
"Ke kike jin tsoronta,ni so nayi ma ta kulani na wanke qazama,yo koni da nake ba wanda ya ajjiyeni tsigau nake ta yaya zan zauna a haka bare ina da miji?"
"Amma kinfi kowa sanin halina,ta yaya zanji tsoronta?,tashin hankali ne kawai ni banaso,zaman lafiya kuma yafi komai dadi"
"A wajen wanda yake sonshi ba" ba wani jin dadin jikinta sosai takeji ba,don haka taja bakinta ta kulle ta qyale wasila,saboda tasan ko meye zata fada ba lallai ta yarda ta dauka ba.
Sanda suka isa makarantar harabar gidan ta fara cika da mutane. Tsaida motar ruqayya tayi tana cewa
"Banajin qwarin jikina sosai,ba jimawa zamuyi ba zamu koma gida gaskiya"
"Ba damuwa,nima din yau zanyi baqo" dan dubanta ruqayya tayi
"Really?,Allah yasa shine mijin" dan tabe baki kadan wasila tayi
"Toh.....gashinan dai,yaa bashir ne ya hadamu" ta fadi tana bude murfin motar. Da kallo ruqayya ta bita,itakam wani lokaci al'amarin wasila kamar wata me almutsutsai,duk wanda yazo yakai mijin aure a idon kowa amma banda a idanun wasilan,ko meye yake damunta oho?.
Tunda yaran suka hangi ruqayyan suka fara murnar ganin ummansu,haneefa na zaune daga gefansu tana raba ido. Duk da ba wanu shekaru bane da ita ba can amma shigar zainab ta sanyaya mata jiki. Kowa cikin yaran yanata nuna ummansa da azamarsa da karsashinsa amma banda haneefa da ta sake noqewa,kwata kwata shigar ummantata batayi mata ba.
Cikin lokaci qalilan aka fara gudanar da taro gadan Gadan,har zuwa sanda aka fara raba kyaututtuka. 'yan biyu makaranta wato alhassan da alhussain sun samu kyaututuka kala daban daban har kusan kashi hudu. Zainab na daga gefe amma tana bibiye da komai,kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yadda komai yake gudana. Ta kasa kunne ta jirayi jin an kira koda Khalil da ta saka buri me yawa a kansa,har wani lokaci takan kirashi da doctor,amma har akayi aka gama shuru maqatau kakeji
"Shegun yara,an koya musu shegen sanabe da iyayin masifa da iya mallaka" zainab dake zaune akan kujera ta fada tan binsu alhassan da harara.
Da daya da daya yawancin yaran suke gabatar da abokansu ga iyayensu,tun zainab bata ankara ba har idanunta sukakai ga su haneefa.
Zugar yuyar qawayenta ne ta jasu zuwa wajen ruqayya dake zaune tana magana da abokansu alhassan,duk da cewa kusan fiye da rabinsu ta sansu dama,don bata wasa da zabarwa 'ya'yanta abokai,hatta kuwa da iftee da take qanqanuwa a cikinsu (mu kula da kyau iyaye,mu kula,mu sanya idanu,tabbas abokai na daya daga cikin mutanen dake taka muhimmiyar rawa ga rayuwar yaranmu,kada kace ba komai don abokin yarona baya zuwa makaranta tunda yarona yana zuwa,kada kace ba wani abu bane don abokin yarona ya kwana ko ya yini da yunwa tunda dai nawa dan yaci abinci hakan bazaiyi affecting dinsa ba,kada kace ba komai don abokin yarona yana zagi ko gidansu ba tarbiyya ai basa haduwa ko yaushe bazaiyi affecting nasa ba,a'ah......sam wallahi,kiyi iya bakin qoqarinki tuquru,yadda kikasan danki bai rasa komai ba kuma yana kan turba ki tabbatar abokan 'ya'yanki ma haka,daga yaranki suka fara samawa rayuwarsu abokai to aikin tarbiyyar dake wuyanki ya linku, tarbiyyar ta zame miki double muddin kinason kiga daidai,kiyi naki kiyi na abokan yaranki,duk yaran da iyayensa zasuyi fushi donkin hukunta dansu ko kin masa gyara ko tsawatarwa ko tabbas ki nesanta yaranki da wannan yaron,Allah ya dafa mana yayi riqo da hannayenmu wajen basu kyakkyawar tarbiyya ameen summa ameen).
Washe baki sosai haneefa keyi tana cewa
"Ga mommy na nima,ku gaisheta" da murmushi ruqayya ke bin qawayen haneefan da kallo,saidai babu wanda yakai ga furta komai suka tsinci bankowar zainab tsakiyarsu.
"Mommyn uwarki mommyn ubanki?,ina tasan ciwonki don******ubanki,annamimiya kema an koya miki annamimanci ne koko yaya aka soma?,ko sihirin ya fara biyomin ta kanku?" Zainab ke fada a tsawace tana kallon fuskar haneefa data ruqayya.
Har wasila zatayi magana ruqayya ta damqi hannunta,ta jata suka miqe tsam tace dasu alhassan
"Ku wuce muje hakanan,taro ya tashi alhamdulillah,'yan yara sai watarana,ku dage kuyi karatu ku yaqi jahilci kunji?,domin shi jahilci babban ciwo ne da yafi na hauka". Daga wannan bata qara ba tayi gaba bayan ta sanya su alhassan a gaba.
Daga inda motarta take take tsaye tana qoqarin bude musu amma tana iya jiyo ashariyar da zainab din ta lailaya sannan ta fara tunkaro inda suke
"Don annabi kada ki tashi motarman,ki bari na nunawa matarnan qaramar qwaruwa ce ita tunda ke ta shanyeki"
"Ba zamu raba hauka a nan wajen ba,indai mukayi haka damu da ita din dukka daya muke kenan,ki barta idan ta haifu ta sameni cikin gida" daga haka ta tayar da motar tun zainab bata qaraso ba,wanda hakan ya sake qona ran zainab din taja burki a wajen tana huci,saidai kuma zuciyarta na gaya mata tsoro ruqayyan taji ta gudu
"Aiko baki tsira ba,yau sai na fanshe haushinki billahillazi,sai nayi sanadiyyar wannan matsiyacin cikin da ake feleqe a kansa" tana gama fadin haka cikin zuciyarta ta durfafi motarta,haneefa dake binta a baya idonta da ruwan hawayen takaici saboda yadda taga qawayenta da wasu mutane da sukayi saura a wajen na kallonta tabi bayanta
"Kinga fa umma sai kallonki akeyi" ta fada tana kyabe baki cikin tabara. Tana waiwayowa batayi wata wata ba ta tsinketa da mari hadi da ingizata cikin motar
"Kece sila da kika raina uwarki sai uwar wasu,sai nayi maganinki wallahi zakisan da waye kike magana" itadai yarinyar bata amsa ba sai kuka da take gurzawa cikin motar kamar wadda aka tsinkewa rai.
"B kowanne lokaci bane ba kuma ko yaushe ne idan kishiya tayi miki abu kike tanka mata ba,ba kishiya ba hatta dashi mijin da kike zaman domin shi,yawaita tankawa kishiya akan ko meye tayi miki yana sanyawa ta rainaki,ta gane lagonki,ta kuma fahimci abinda bakiso da abinda yafi qona miki rai,wanda wadannan kuma sune makaminta da zata yita yaqarki dasu tana hanaki sukuni. Sa'insa ko tankiya yawan maimaitasu ba abinda yake haifarwa face jawo raini da zubewa girman babba. Duk mace idan taso tana iya siyawa kanta kwarjini da martaba a idanun kishiya,ita zainab da kike gani,har yanzu batasan mene yake mugun bata raina ba,har yanzu babbankiya takeyi saboda naqi bata wannan damar,har yanzu duk sanda zatayi iskancinta bata isa ta shigo sashe na ba iyakarta farfajiya,kuma har yanzu bata isa ta saka hannu a kaina ba,har kwanan gobe kuma akwai fadan da bata iya tsaiwa mu yishi,har yau har gobe kuma akwai abinda yake hurumina ne cikin gidan,ita ko shi ba wanda ya isa ya taka,idan na zartar saidai kawai su gani a qasa,koshi bazaice komai ba bazaice kuma don me ba,itama tun tana damuwa har ya zamar mata jiki. Ko zage zagen da takeyi yanzu ai sai dana bada baya bawai cikin idanuna ba. Idan kinso kina iya saiwa kanki wannan martabar,wanda tun farkon kawo kishiya zaki siyeta,ki girmanki da mutuncinki,kada ta sameki kina haukan kishi,ki nutsu ta sameki me cikakkiyar nutsuwa,ki yawaita addu'a da roqar Allah ya haskaka fuskarki a idanunsu ita da mijin,sannan kiyi fatan Allah ya baki mijin da yasan darajarki,don gwargwadon yadda ta shigo taga miji yana qimantaki gwargwadon yadda zata fahimci muhimmancinki,koda baya baki martaba shi da ita ajesu a gefe ki kama kanki,ki ki aikata musu a aikace ba ta hanyar magana ba cewa kefa kinsan kima da mutuncin kanki,ko baya qaunar Allah dole yayi biyayya koda bai shirya ba,musamman idan ke din ma'abociyar addu'a ce,me tsarkakkiyar zuciya,wadda baki zaluntar kowa kina qoqarin fita haqqin kowa" shuru wasila tayi jikinta ya sake,zuciyarta kuma na juya kalaman ruqayya. Tabbas tun suna qananuntasan ta fita hikima,ba komai bala'i da masufa yake baka shi ba.
Hirarsu ta duniya sukaci gaba da yi wadda cikinta a yau wasila taji tana qaruwa. A nutse take musu tuqi har suka isa gida. Taso ta saka motarta ciki amma saita lura da motar zainab wadda aka yiwa wani banzan parking,so babu hanyar da zata shiga din,don haka ta tsaida motar ta fito tana cewa wasila
"Bari naga me ya faru,idan ta matsar da motar ki shigo min da ita ciki,fitsari nakeji sosai"
"Yauwa nima yau na dan dana kafin Allah ya kawo mana me siya mana muma" wasila ta fada cikin zumudi tana komawa seat din da ruqayya ta tashi a kai.
Tana shiga farfajiyar gidan ta tambayi yaron gidan nasu ya aka ajjiye mota a haka?. Cikin dan rusunawa yace
"Ummansu haneefa ce,nima nayi mata magana da nufin ta gyara ko bata lura bane ta zageni tace yau a haka taga daman ajjiyeta" dan jim ruqayya tayi tana gyada kai,sai ta koma da baya ta yiwa wasila magana
"Ki ajjiyeta nan qofar gida ku fito ku qaraso ciki"
"Me yasa?"
"Haka dai nace" ta amsawa wasila tana dawowa ciki idanunta akan motar zainab har ta wuce sashenta.
*_ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTANKU NA SHEKARAR 2024_*
*_ZAZAFAR SOYAYYA ME SANYAYA ZUCIYA CAKWAKIYA GWAGWARMAYAR RAYUWA DA TATABURZA_*
*_ZAZZAFAR MUHAWARA CIKIN KEBANTATTUN COMMENTS GROUPS NAMU,MUHAWARA ME SANYA NISHADI DA QULLA ZUMUNTA (ZAFAFA FAMILIES)_*
*ZABABBUN LITATTAFAN NAMU SUNE KAMAR HAKA*
*AMEENATU* Mamuhghee
*KWANKWASON JIMINA* Miss xoxo
*TSUTSAR NAMA* Billynabdul
*GUDUN K'ADDARA* Huguma
_TURK'ASHI!,KADA WANNAN DAMAR TA WUCEKU_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING ZAFAFA BIYAR*❤🔥❤🔥❤🔥