Kurman Baƙi Page 28 by Huguma

Kurman Baƙi Page 28 by Huguma

 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫


*HUGUMA*


PAGE 28

________________________________


*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥



*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

_____________________________



            "mu'amala dasu bata qarawa bawa komai face cire masa imani da yaqini da ubangijinsa,ta fidda maka dukka wani hasken tauhidi,ta cire maka wani ginshiqi cikin ginshiqin imani wato yadda da qaddara me kyau da mara kyau,wasila.....ki kiyaye dokokin Allah sai Allah ya kiyaye duk wani abu da kikeso,kiyi kishin Allah sai Allah yayi kishinki,ki gwada wasila da iklasi da tsarkake niyya,wallahi wallahi wallahi Allah bazai baki kunya ba bazai bani kunya ba" sai ruqayya ta zare hannunta a hankali daga cikin na wasila tana kallon tsakiyar idanun wasilan wadda sannu a hankali maganganun ruqayya taji suna samun wani matsugunni me kyau a ranta,irin matsugunnin da basu taba samu daga gareta ba.

  

              Washegari da safe da hannunta ta tarkata duk wasu abubuwa da tasan tana ta'ammali dasu ta qona,irinsu jan farce nail polish,ribbon din attachment,shi kansa gashin da ake mata kitso dashi,ta cire sarqa qafa uban barimomin kunnenta,magungunanta da duk wasu takardu na rubuce rubuce da malamanta suka bata sukace tayi amfani dasu, supplement dinta na qarin qiba da haske dukka ta tattarasu ta qonesu. Bata cewa ruqayya komai ba,saidai ruqayyan taji dadin hakan ta kuma tabbatar da cewa lallai komai yana da lokacinsa,yau dare daya wasila taji nasiharta?.


                Ko bayan sun gama buda baki a ranar saita kalli ruqayya


"Me dame kike ganin ya kamata na riqe a yanzu?" Sosai ruqayya taji dadin tambayar,ta saki murmushi


"Muna lokaci na amsa addu'a,ki riqe istigfari ba kuma iya a baki kawai ba,duk sanda kikayi istigfari din kiji har zuciyarki kina yine saboda neman yafiyar ubangiji akan zunubanki,kuma kina yine saboda samun kusanci da Allah,ki yawaita ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astgis,Allahumma rahmatika arju,fala takilni ila nafsy darfata ainin,wa'aslihi li sha'ani kullahu la'ilaha illa anta,sai uwa uba kuma shakundum salatin annabi muhammad  S A W ko shi kika riqe da istigfari sun isheki komai basai kinje gurin kowa ba,amma akwai babban abu muhimmi guda daya wanda da yawan mutane basu sanshi ba....."


"Menene shi ruky?" Wasila tayi tambayar tana kallon fuskar ruqayya


"Husnul kulq wato kyakkyawar mu'amala"


"Kaman yaya?"


"Ma sha Allah" ruqayya ta fada tana gyara zamanta


"Ubangiji yana masifar kishin bayinsa,duk yadda kikai ga ibada da kusanta kanki da Allah muddin baki da mu'amala me kyau tsakaninki da mutane bayin Allah to za'a iya cewa ibadarki ta tashi a banza" idanu wasila ta fidda


"Kaman yaya?"


"Yauwa,zan baki wata kissa,watarana annabi S A W yana zaune da sahabbansa,sai akazo wucewa da gawar wata mata,sai sahabbai suke fadin irin halayen matar,macace me azumi ga ibada ga sadaka ga kuma tsaiwar dare,amma maqotanta basu tsira daga cutarwarta ba,sai annabi yace wajabat,wato tabbata akanta,da sahabbai suka tambayi ma'aiki akan hakan sai ya shaida musu ta tabe,yar wuta ce,kinga azuminta da ibadarta basu amfaneta da komai ba tunda bata da mu'amala,sau da dama mutumin da yake da mu'amala me kyau da mutane yana iya samun rahamar Allah bayan ya mutu koda kuwa shi din me yawan zunubi ne,sai yaci albarkacin kyautata zamantakewa da bayin Allah" sosai jikin wasila ya sake sanyaya,tayi shuru tana nazari,matan yayyenta duk da tana kyautata musu amma suna yawan kuka da halinta,kamar ruqayyan tasan me take tunani ta sake cewa


"Abinda ka raina sai kaga ranar gobe babban abune a wajen Allah,ki zauna da kowa lafiya da kyakkyawar zuciya"


"In sha Allah" ta amsa mata a sanyaye.


                Tun daga ranar komai na wasilan ya canza,hatta da magana me yawa ta rage duk da ita din gwanar surutu ce,ko yaushe zaka sameta da counter a hannu,koda ta sha'afa an fara doguwar hira zata koma istigfar dinta da salatinta. Sannu a hankali sai ta dinga jin wata nutsuwa tana saukar mata irin nutsuwar da tunda take yawan bin gifan malamai suke bata wurdodi bata taba jin makamanciyarta ba,dukka damuwarta akan zaid sai taji tana gushewa,tsananin tunanin zaid da takeji kaman zai zautar da ita sai ya fara raguwa a ranta,tana iya wuni ba tare data tunashi bama. Har a ranta kuma takejin zata iya daukar kowacce qaddarar rayuwa da zata sameta,samun zaid ko rasashi,taci gaba da addu'ar samun nagartaccen miji kadai wanda zai zamewa rayuwarta alkhairi.


*_ZAINAB_*


           Ko sau daya bata taba kaiwa hankalinta ga yadda dinkinta ya dinga zarewa zaren yana ficewa ba tun baikai ace ta warke ba,ranar da taga zaren farko ta yanke abinta tana murnar


"Dinkinnan yayi mugun saurin warkewa,ga zare nan ya fice da kansa?, gaskiya ina da sa'a" tsananin qazanta ya hanata jin tashi tashin da wajen ya farayi. Abun tun safina bata fara jinsa ba har ta fara yi mata complain,sannu a hankali itama ta fara ji saidai kadan kadan,sai kawai ta bagarar ta azawa ranta qaranta amfani da ruwan dumin da akace tayi amfani dashi da takeyi ne ya jawo haka. Wannan ya sanya kullum sau daya a rana zata cika baho da ruwan dumi ta shiga ta fito,a hankali ta soma jin qaiqayi,qaiqayin da yasa ta sake imanin dinkinta warkewa yakeyi fes,abin yayi mata dadi saboda yazo ne dai dai sanda ya rage saura kwanaki biyar saleem ya dawo.


             

******Zuwa lokacin ta fara jin sauqin laulayinta sosai,tana iya wasu abubuwa da yawa da kanta,hakanan azuminta taba bakin qoqari taga takai,sam bata sanyawa kanta irin son jiki na matan yanzu ba,wadanda daga ciki su da azumi sunyi hannun riga,idan ya sake zagayowa kuma suce shayarwa,wata shekarar kuma an samu wani cikin,sai ka wayi gari da yawa yawan mata suna wasa da ibadar azumi,wanda babbar masifa ce muke jefa kawunanmu,muna kuma kwashewa yaran albarka don ta silarsu muke fakewa da qinyin azumin.


                Tsaf wasila ta tayata sukayi kwalemar sashenta,don kada su jigata duka sai ansha ruwa sukeyi. Gwanar tattali ce ita,kuma uwa uba tana Sana'a,gashi cikin watan da ciniki yake yawaita,don haka cikin ribarta da abinda ta tattala din tayi siye siye,kusan tafi rinjiyar da komai ga gyaran dakin saleem din,burinta ya dawo ya samu komai ya banbanta da sanda ya tafin. Tun daga bedsheet blanket dinsa zuwa qananun underwears na ciki da curtains na dakinsa. Kwanaki biyu ya rage ya dawo ta kirayi me qunshinta ta ta zuba mata jan lalle ita da iftee,aka yiwa wasila itama a mazaunin qunshin sallarta,bayan ansha ruwa taje akayi mata wankin kai,take gashinta ya qara tsaho da sheqi ta hadeshi cikin ribbon gwanin sha'awa.


*_ZAINAB_*


             Kusan tunda lissafin kwanakin dawowar saleem ya fara matsowa nata dokin ya ninka na kowa saidai ana iya cewa dokin banxa tunda nata tunanin yasha banban da na kowacce mace me hankali. Gaba daya tafi karkata tunaninta wajen neman magungunan mata da zata sake tsuma kanta da kanta a cewarta,dai dai da gyaran sashen ba abinda ta iya tsinanawa banda dakin saleem din data gyara a daddafe,tana gamawa ta sharbe a wajen,bata sake motsawa ba har sai da safina ta tasheta bayan ansha ruwa.


           Da dan hanzarinta taso miqewa,saidai hakan ya gagara kwata kwata saboda wani mugun riqewa da qugunta yayi. 


"Wayyo na shiga uku" ta fada tana dafe qugunta hadi da ware idanu.


"Lafiya?" Safina ta fada tana kallonta,don ita kanta zuwa yanzu ta fara gajiyawa da abubuwa da yawa na Zainab,Allah Allah take mijinta ya dawo ta tarkata ta barsu


"Mugun ciwo marata takeyi" ta fada tana yarfar da hannu


"Sannu,ki daure ki tashi saikisha ruwa kisha magani" ta fada tana kallonta. Ta jimaa haka kafin ya saketa,ta miqe tana dafawa da qyar ta isa bandaki.


               Saman tiles ta tsugunna zatayi fitsari duk da yadda safina ke masifa idan ta wanke toilet din duk wanda ya mata fitsari a qasa. Maimakon ruwan fitsari sai ga jini yana fita da wani butaci butaci


"Kaddai period ne yazo?" Ta tambayi kanta da kanta bayan ta gama fisarin. Cikin ranta ta gamsu shi dinne,saidai kuma yadda taji jini yana bin jikinta sai abun yadan bata mamaki


"Koma meye kafin nan da ranar da zai dawo na gama period din nan,duk da ba haka naso ba amma ba matsala" ta fada a ranta tana duba tsummokaran da take period dasu,don kudin always dinta na watan shima ta sakashi a layin kudin magani.


             Tana sakawa ba dadewa ya jiqe,sanda ta fiddo tsumman yawan jinin da wari warin da yakeyi yasa ita kanta ta yamutsa fuska,a ranta tana tunanin maganin da ta shane da asuba bayan ta gama sahur. Wasu tsumman ta ninka sukayi tudu sosai sannan ta samu yadan zauna a jikinta.


              Bata wani jima dashi ba shima taji ta fara leaking,sosai hankalinta ya fara tashi da ganin yadda take bleeding. Daga daren zuwa safiya ita kanta tasan ta zubda jini sosai,cikin zuciyarta kawai taji taqi yarda ko gamsuwa da zubar jinin, zuciyarta ta shiga raya mata akwai wata a qasa,don haka ta jawo wayarta ta kirayi raliya abokiyar shawara.


               Sun jima suna waya da raliyan,kuma dukka maganganun data gaya mata sun zauna sosai a rai da zuciyarta,ta gamsu da maganar raliya,lallai ba makawa asiri ne,jifanta akayi,kuma ba kowa bace da wannan aikin sai ruqayya,da alama ta lura da shirin da taketa yi da gyaran HQ dinta don sake samun fada a wajen saleem,lallai kam wannan karon ba zata bari ba,koda bata taba bin malamai ba a wannan karon saita taba ruqayya don ta nuna mata ba tsoronta takeji ba,ba kuma wai finta sanin hanyar gidan malamai tayi ba,sai ta sanya an zubda cikin da take taqama da shi,sannan kuma ta sanya a saka mata warin jaba ta yadda ko dosota saleem bazaiyi marmarin yi ba,idan yaso ita da itan dukka su rasa ayi mutuwar kasko.


                 Tana saman kujera tana faman kada qafa hadi da lissafin dokin rano safina ta shigo falon. Kallon safinan tayi sama sama ta sake maida hankalinta ga lissafinta,itama safinan bata bi ta kanta ba ta samu waje ta zauna tana cewa


"Ba wani gyara ne da za'a yi umman haneefa?" Dan maida kanta kadan tayi ga safina


"Gyaran me?,wani abu ya lalace ne a gidan nan?" Kai ta mirgina cikin takaici amma ta danne don har ga Allah tanason ta gyara din


"A'ah,ba babansu haneefa saura kwana biyu ya dawo ba?,banga kin canza komai ba"


"Me kuma zan canza?,dakinsa ne na shareshi yana kulle babu me shiga" haushi ya sake kamata,ko ita da take budurwa ai tasan abinda idan mace tayi zai dadadawa miji matafiyi


"Haba ke kuma anty Zainab don Allah,share daki wani abune?,dakinma da daga shara ko goge goge bakiyi masa ba?,bakiga momynsu alhassan ba?,bakiga har qunshi akazo akayi musu ba?,ta wanke kanta ta gyare sashen har curtains naga ta canza......"


"To baqar munafuka" zainab ta fada tana gyara zamanta hadi da ajjiye wayar hannunta a gefe


"Da alama idan nayi baccin rana satar jiki kikeyi ki shiga wajenta ko?"


"Kinsan inda zan shiga idanunki biyu ma shiga zanyi.....ita tsafta ai bata boyuwa hakama akasinta,ko kai makaho ne kazo gidan nan ka zauna zakasan matar tana da tsafta,don ko ta sashenta kazo giftawa zakaji qamshin sashenta daban yake,kwalliyarta daban haka sutturar da yaranta suke sawa ma atsaftace take"


*_Mu hadu anjima in sha Allah new page_*😊



*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥



*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post