Cuta Ta Ɗau Cuta Page 41 by Bilyn Abdul

Cuta Ta Ɗau Cuta Page 41 by Bilyn Abdul

Novels to read

 *_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na arba'in da ɗaya_

.......“Minene sunansa?”.

     A matuƙar rikice Mami ta ɗago ta kalli Daddy da yay maganar. Sai dai a mamakinta hankalinsa nakan tv ne da ake labarai ma. Juyawa tai ta kalli inda Ammie take. Itama dai ba ita take kallo ba shayi ma take ƙoƙarin zubama Daddy ɗin. Sashin su Muhammad ta juya, sai taga wayam alamar sun tashi gaba ɗayansu daga falon....

    “Nace minene sunansa?”.

  Daddy ya sake maimaitawa a karo na biyu yana mai katse Mimi dake dube-dube. Kuka ta fashe da shi tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Daddy kayi haƙuri natuba. Wlhy bazan sake kulashi ba. Na maka alƙawari”.

         “Fateema! Nace minene sunansa?”.

    Kaɗan ya rage kam a yanzu zuciyar Mimi ta ɓaro jin ainahin sunanta a bakin mahaifin nata. Abu mai wahalar gaske kaji ya faɗa kuwa. Ƙaruwa rawar jikinta ta ƙara. Cikin matuƙar rawar harshe ta ce, “D...d...daddy Ya...zee...d!”.

      “Waye babansa?”.

   “Abdul-kareem Waziri. Ministarn Abuja”.

     “Tun yaushe kuke tare?”.

Kuka ta fashe da shi har sai da Daddy ya daka mata tsawa.

    “Nace tun yaushe kuke tare?!”.

“Ka k....kayi haƙuri Daddy wata huɗu kenan. A wajen dinner ɗin bikin Uncle Awwal”.

         “Fateema aure kike so?”.

    “Daddy wlhy wlhy kaji na rantse maka a'a. Shima na faɗa masa ya daina zuwa ni karatu zanyi. Amma yaƙi yarda Daddy. Shine yake bini har school. Ko nace bazanje ba sai yayta roƙana kamar zai yi kuka. Wataran ma har kukan yake min. Amma wlhy Daddy ba aure nake so ba. Kuma wlhy na maka alkawarin bazan sake binsa ba”.

        “Bani Number sa”.

   “Daddy Dan ALLAH na roƙe ka...”

Tsawa ya sake daka mata mai firgitarwa da har sai da ta sakata zabura tana sake fashewa da kuka. Cikin ɓacin rai da bata taɓa sanin Daddyn nasu ma da shi ba dan shi mutum ne mai saukin kai sosai. Yakan zauna yay hira yay wasa da dariya da su. Wani lokacin ma Ammie ta fisa zafi. Wayarta gaba ɗaya ya amshe ma. Sannan yace ta tashi ta bashi waje. Haka ta tashi tana kuka da magiyar roƙon suyi haƙuri su yafe mata shi da Ammie bazata sake ba. Amma babu wanda ya saurareta ya korata.

         Koda tabar falon da ga shi har Khadijah babu wanda yace da ɗan uwansa komai. Dan wayar tata ma gefe ya ajiye ta ya cigaba da kallon labaransa. Sai goma dai-dai suka tashi suka haye sama bayan sun leƙa ɗakunan yaran nasu har Mimi ɗin. Sun sameta a saman sallaya tana karatun Alqur'ani. Babu wanda yay mata magana a cikinsu suka maida mata ƙofar suka rufe. Sama suka haye. Sai bayan sunyi shirin barci Khadijah na daga jikin mirror tana saka turare shi kuma yana a bakin gadon zaune ya ɗauki wayar Mimi. Bincike ya farayi lungu da saƙo na wayar dan babu password, hakan dokace da ga Ammie. Sai da ya gama bincike wayar tsaf yana ɗan sauke ajiyar zuciya ganin babu wani abin tada hankali sai text messages na soyayya mafi yawa ma yaron ne ya tura mata. Sai wasu ta WhatsApp da hotunanta data tura masa shima ya tura mata nashi. Dukansu kuma da hijjab ma tayi su. Shima kuma cikin kamala yake. Iskar samun nutsuwa ya furzar. Kafin a hankali ya ɗago ya kalli Khadijah dake kallonsa. Hannu ya miƙa mata alamar tazo gareshi. Babu musu ta nufesa. Jikinsa ya jawota suka faɗa saman gadon. Da ga haka yaja musu bargo yana sumbatar kumatunta da faɗin, “Ki ɗan yi murmushi mana Baɗɗo am”.

    Murmushin ta ɗanyi da sake shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shima sai ya sauke tasa ajiyar zuciyar yana sake rungumeta da ƙyau...


        *_WASHE GARI_* kamar yanda suka saba duk suka fita aiki. Yaran kuma makaranta har Mimi. Sai dai yau Daddy da kansa ya kai su makarantar. Ya kuma hana Mimi fita. Suna zaune a mota ita da shi sai ga kira ya shigo a wayarta dake hannunsa. Miƙa mata yay babu alamar wasa a fuskarsa yace “Ki amsa masa kamar yanda kika saba”. Kanta ta jinjina tana share hawaye. Ganin yanda mahaifin nata ya tsareta da ido dole ta amsa ɗin. Suna gamawa ya amshe wayar yace mata taje inda yake. Kuma koda wasa ta sanar masa tare suke sai ya mata dukan mutuwa. Tana hawaye ta amsa masa. Tsawa ya mata akan ta share hawayen. Haka ta gogesu tsaff ta gyara yanayinta sannan ta fita bisa umarninsa.

         Tana shiga motar suka bar wajen . Bayansu yabi har garden ɗin da Ammie ta dinga bibiyarsu. Sai da suka fita a motar suka sami wajen zama Mimi dai duk a ɗarare sannan ya fita zuwa inda suke. Koda Yazeed yay tozali da Alhaji Abaan gabansa rikicewa yay. Dan kuwa mahaifin Mimi ba ɓoyayyen mutum bane. Sannan duk wanda ya kalleta ya kallesa yasan shine mahaifinta. Jikin Yazeed na rawa ya kai har ƙasa yana gaida Abaan. Amsa masa yay tare da masa nunin ya tashi. Batare da yace komai ba yace su biyosa. Ganin babu alamar wasa a tattare da shi Yazeed ya bisa babu musu. Ita dama Mimi yasan bata isa yin musun ba. A motarsa ya ɗebesu su duka aka bar ta Yazeed anan. Mami na baya Yazeed na gaba kusa da Daddy.

      Hankalin Yazeed ya tashi ganin gidansu suka zo. Bai sake ruɗewa ba sai da aka buɗe musu gate yaga motocin mahaifinsa na nan alamar bai fita ba. Ita dai Mimi bata san nan ne gidan su Yazeed ba. Sai da akai musu iso ciki suna shiga tai tozali da mahaifin Yazeed ɗin. Duk sai itama taji ta sake rikicewa.


     Tarba ta girmamawa Alhaji Abaan ya samu a wajen Ministar. Domin kuwa akwai sanayya batun yanzu ba, sannan akwai huɗɗar kasuwanci. Tun kuma a daren jiya ya nema ganinsa ta hanyar tura masa saƙo ta waya. Hakan yasa batare da wani kace nace ba suka haɗu a gida kai tsaye kamar yanda Ministar ɗin ya bashi dama yau da safe ta hanyar kiransa. Dan Alhaji Abaan ko shugaban ƙasa ya buƙaci gani duk da a ƙurarren lokaci ne hakan bazai gagaresa ba. Dan ya wuce duk yanda mai hasashe zai iya hangowa yanzu a ƙasar nan. To ada can baya ma da suke matasa akayi dasu balle yanzu da gwamnatin ma sune suka kafata da dukiyarsu da iliminsu.

    Bayan gaisuwa da ɗan barkwanci tsakanin dattijan guda biyu Alhaji Abaan ya nuna Mimi da Yazeed dake zaune ƙasa kawunansu a ƙasa tamkar masu neman gafara. Yazeed ya nuna da faɗin, “Nasan kasan wannan. Wannan kuma first born ɗina ce Fatima”.

     Fuska cike da murmushi Ministar dake kallon Mimi ya ce, “Masha ALLAH dota yaki nan. Wato girman dai ɗan mutum babu wahala. Yanzu Alhaji Abaan yarinyar da muka sha shagalin sunan ta ce ta girma haka oh ALLAH”.

   Murmushi kawai Daddy yay batare da yace komai ba. Yayinda Mimi ta taso a ɗarare har gaban ministar ta sake zaman gurfane. Daka ganta kasan hankalinta baya tare da ita. Gaishesa ta sake yi cike da girmamawa. Ya amsa mata da kulawa yana jera mata tambayoyi. Har suka kammala Daddy baice komai ba. Sai da sukai shiru sannan Daddy yayma Yazeed nuni da shima ya matso. Tasowa shima Yazeed ɗin yayi a ɗarare ya gurfana kusa da Mimi kansa a ƙasa kamar yanda take. Daddy ya maida dubansa ga ministar da yayma ɗan nasa kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Batare da ɓata lokaci ba Daddy ya shiga yima Ministar bayanin abinda ya faru a jiya game da fitar Mimi gida. Har bayanin da Ammie tai masa zuwa abinda ya faru yau. Sannan ya miƙama ministar wayar Mimi dake hannunsa. Shima duk sakwanin da suka shiga tsakaninsu ne ya dudduba. Bayan ya kammala ya ɗago ransa a ɓace yana kallon Yazeed. Magana yaso yi amma Daddy ya dakatar da shi.

        “Kasan miyyasa na kawosu gabanka?”.

     Kai ministar ya girgiza masa rai a jagule. Daddy yay ɗan murmushi. Sannan ya cigaba da faɗin, “Saboda mu fiskancesu tare. Da farko naso hukunta yaron dake tare da itan ne koda ɗan waye. Sai dai jin yaronka ne yasa naji bazan taɓa iya hakan ba. Sam ba soyayyar tasu ko alaƙarsu ta ɓatamin rai ba. Hanyar da suka ɗora kansu wajen gina soyayyar ne ya zafeni ya kuma tayar min da hankali. Domin hanyace mara ɓillewa. Wlhy wlhy ko ɗan maigadin gidana Fatima ta kawo gabana tace min Daddy ina son wannan da aure shima yana sona bazanji komai ba sai farin ciki, zan kuma goya musu baya na bama alaƙarsu ƙarfi ta yanda basuyi zato ba. Amma soyayya a bayan fage da ɗaukar salon cutar da iyaye koda ɗan wanene bazan ɗauka ba. Dibesu, dukansu basu haura shekaru ashirin ba a duniya amma sun san su yaudari iyaye ta hanyar barin makarantun da muka turasu su tafi lambun soyayya. A da fa iya makaranta ake bari zuwa garden, amma yanzu ta fara kaiwa matsayin barin gida babu izini zuwa gidan cin abinci. Daga haka mi kuma muke tunani zai biyo baya....” ya dafe kansa cikin takaici. Batare da ya jira cewar ministar ba ya cigaba da faɗin, “Wannan ta riga ta faru, ba kuma na fatan ta cigaba da faruwa. Dan haka nazo da su gabanka. Idan ka shirya yima Yazeed aure ka turo min magabatansa na bashi auren Fatima. Ba kuma nason komai ya wuce nan da wata biyu. Taje tai karatun a gidansa idan tana da ra'ayin hakan, idan kuma bata buƙata duk ya rage nata. Ni dai Alhmdllh nasan na sauke nauyinta da ke kaina matsayin mahaifi. Hakama mahaifiyarta na iya ƙoƙarin ta a kanta. Sai dai na sharɗantama Yazeed kar ya sake tareta a waje da sunan soyayya, kada ya sake zuwa ɗaukarta makaranta da sunan soyayya. Kada ya sake kiranta ta fita a gida saboda sunan soyayya. Na bashi dama yazo gida a duk ranaku uku na cikin mako, suyi hira a falona daga nan har zuwa randa zan bashi ita a matsayin mata. Yazeed wannan alfarmar kawai nake buƙata a gareka dan ALLAH dan ALLAH ka taimakeni”. Ya ƙare maganar yana kallon Yazeed dake hawaye kansa a ƙasa. Hakama Mimi kuka take kamar ranta zai fita dan maganganun Daddy sun matuƙar gigita mata zuciya da sata a ɗimuwa. 

      Shi kansa Ministarn kallon ɗan nasa yake cike da matukar mamaki da al'ajabi. Dan da wani ne yazo ya sanar masa Yazeed ɗin zai aikata haka wlhy bazai yarda ba. Saboda kaf a cikin yaransa babu wanda ya kamo ƙafar Yazeed hankali, nutsuwa da biyayya. Yaro ne nagartacce da ƙyawawan halaye. Sannan gashi shiru-shiru kamar idan ka saka masa yatsa bazai iya taunawa ba. Cikin tsananin ɓacin rai ya rufe Yazeed da faɗa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai da yay masa biji-biji Yazeed ɗin na hawaye sosai sannan Daddy ya riƙo hannunsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Ya isa haka tom”. 

      Kansa ya girgiza tare da maida dubansa ga Daddy. “Nagode sosai da wannan halaccin da kaimin Alhaji Abaan. Wlhy wlhy kaji na rantse daga ni har mahaifiyarsa bamu san hakan na faruwa ba. Dan kullum ya shirya ya fita a saninmu makaranta ya nufa kawai. Yanayin rayuwa da taɓarɓarewar abubuwa yasa mahaifiyarsu bata yarda su ƙetare ƙasar nan domin yin karatu ba, musamman ma su mazan, matan kuma idan mazajensu sun amince su tafi dasu dan da sun kammala sakandare muke aurar dasu. To ashe shi shaiɗani yana can yana hurema yarinya ƙarama dake aji biyar na makaranta kunne saboda zalunci. Kai idan akaima ƙanwarka haka zakaji daɗi? Duka nawa kake ma Yazeed. Just twenty years fa, amma kake.....”

     Sake riƙo masa hannu Daddy yay yana murmushi. “Oh calm down ya isa haka. Ai kuskuren ba nashi bane shi kaɗai harda ita Fatiman. Amma in sha ALLAHU ni zan magance matsalar in dai kun shirya masa aure. Dan ita dai in sha ALLAHU bazata sake min wata biyu a gida ba koba Yazeed ba zan aurar da ita ne na riga na yanke hukunci”.

      Sake rikicewa Mimi tai da kuka.........✍️ 

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post