Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 14

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 14

 


BossLadiesWriters

           KURKUKUN ƘADDARA


  The Prisoners E14🔥💫

         Daga alƙalamin Boss Bature

Middle step 

A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔.


Universal Hospital


Ba sai na tsaya misalta kyawun asibitin ba, tun da akace america zance Ya ƙare just imagining ɗinsa zakuyi, lokacin da motocin suka ƙaraso entry way na shiga asibitin ɗuff suka ɗaukar jiniyar bayan shigarsu A parking space motocin suka dakata da yin tafiyar, Cikin ƙanƙanin lokaci Emts Suka kammala jigilar shigar dasu cikin asibitin duk wani motsinsu akan idon sojojin Bayan kammala Shigar da su asibitin, Likitoci da nurses suka duƙufa domin duba lafiyar jikinsu, tuni sun canza masu kayan jikinsu daga Uniform ɗinsu Jajaye zuwa Patient's uniform launin Light blue, hatta waɗanda suka 6aci da ta6o sun wanke su tass tamkar basu ta6a faɗawa cikin ca6ali ba.


gaba ɗayan su a Amenity ward aka kwantar dasu, sashe na musamman da ake kwantar da sarakuna da hamshakan masu kuɗi, duk mutun ɗaya ɗaki ɗaya, tsabar haɗuwar ɗakunan tamkar bana jinya ba, anzuba ababen more rayuwa, kama daga haɗaɗɗen gado, ga A'c hada tv da frigde komai na jin daɗi, tuntuni sun farfarɗo daga suman sai dai gaba ɗayansu they were in a state of unconsciousness sakamakon firgici da tsoron da ya rikitar da su, razana suke yi haɗi da yin sambatu hakan yasa likitoci su ka yi masu allurar kashe ƙwarin jiki don su samu damar duba lafiyar jikin su, the first thing da doctors su ka fara yi masu is general checkup wanda ya haɗa da sauraran bugun zuciyar su duba hunhunsu, fatarsu da idanuwansu daga bisani suka fara yi masu gwaje-gwaje da su ka shafi blood test, chest X-ray, da sauran gwaje gwajen hotunan wasu 6angarori na ga6o6in su, domin duba raunukan da suka ji da cututtukan da ke damunsu, Cikin ƙwarewa likitocin su ke  gudanar da binciken nasu, ɗaya daga cikin abunda suka gano wanda ya ɗaure masu kai, duka yaran akwai depression atattare da su (ciwon baƙin ciki da damuwa) Mutun ɗaya ne ke fama da Ciwon Zuciya (stress-induced cardiomyopathy, agaggauce su ka fara bashi taimakon gaggawa, Ga ƙarancin Jini da ya ke fama da shi, tuni sun fara yi mashi Blood transfusion.


 A ƙalla likitoci sun shafe tsawon awanni akansu, wani abu da yai mugun ɗaurewa Likitocin kai Ƙoshin Lafiyar Danish da kyawun surar shi! Tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun mai rai da lafiya irin shi ba, gashi yaƙi farfaɗowa sun rasa gane wani kalar bacci ne ya ke yi, kuma sam babu wata lalura da ke gare shi, bacci ne kawai yake ta shara abin shi, Duk sun ƙagara da su ji bayani daga Gare su, Amma sun bari sai Yaran sun ji sauƙi tukunna su ji daga bakinsu menene ya haddasa masu depression? Da ƙananun shekarun su, mutun ɗaya da Sojojin su ke tsammanin Jin bayanai daga gare shi, Tun acikin jirgi da suka yi mashi allurar bacci bai ƙara farfaɗowa ba, Yanzu haka Yana akwance saman gado sai sharar baccinsa Ya ke yi.


Till Wuraren ƙarfe 12 Na rana, Gabriel ya soma mutsun mutsun farkawa daga bacci, Dama jiran shi suke Yi ya tashi, Kasancewar akwai na'urorin cctv a kowace kusurwa na medical rooms ɗin ta hanyar su likitocin su ka san da tashin sa.


Slowly ya buɗe idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin, Tamkar a mafarki Ya ke kallon shi, tsantsar mamaki ne da al'ajabi akan fuskarshi, Tambayar kanshi ya soma yi cikin ruɗanin zuciya, Ina ne nan? Wanene ya kawo ni? Anya ba mafarki nake Yi ba"? da wata irin kasala Gabriel ya miƙe zaune Yana faman wurwurga ƙwayar idanuwansa akan haɗaɗɗen room ɗin da ya ke a ciki, Lamarin ya ɗaure mashi kai, Daddafe kanshi yai da hannayenshi biyu tamkar zai fasa ƙara, abunda ya ƙara rikitar da shi Uniform ɗin da aka canza mashi, daga jajaye zuwa light blue Riga da wando, Ƙasa ƙasa da murya yake ambaton sunayen ƴan uwan shi


 "Azeeza! Angel! Danish! Batul! Naufal! Javed! Par....." bai ƙarasa maganar ba sakamakon Jin motsin buɗe ƙofa, A firgice ya zazzare idanuwanshi akan masu shigowa.


Uku daga Cikinsu asanye suke da scrub suit, Kayan Likitoci, biyun da ke  biye da su cikin kakin Sojoji masu ruƙe da muƙaman Major da Captain wakilai ne da aka turo daga can headquater, likitocin uku dake atare dasu Turawa sun haɗa da md (medical director) Dr. mark Johnson, bayan shi sai Hospital Ceo Dr. laura Davis babbar macace fara jawur, na ƙarshen su health records technician ne Dr. Danial Brown hannun shi ruƙe da Apple ipad.


 A gaban gadon shi su ka tsaya suna dubanshi 


  Cikin harshen turanci suke Yin magana

  "Fatan ka farka Lafiya? Ya jikin naka"? Dr Brown ne yai mashi maganar, cikin kulawa,.Muryarshi adabarbarce ya furta"Ina ƴan uwana suke"? Tambayar farko da ya fara jefa masu."Did you forget that we found you in the forest? (Kamanta a daji muka tsince ku"?) Major ne Yai mashi maganar, Gabriel was silent as he tried to remember what had happened. They could see that he was confused and would need time to sort out his memories.


 Nuna mashi screen ɗin Ipad dr bown yai, hotunansu Angel ne a jere da suka ɗauka yayi saving ɗinsu akan wayar, ƙura ido gabriel yai akan screen ɗin, a tsanake ya ke ƙare masu kallo, nan take ya zaro ido wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi, hada murmushin sa.


  "Do you remember everything now"? Major ne yai maganar, Jinjina mashi kai yai alamar eh, janye wayar dr.bown yai tare da kallon abokan aikin nasa da sojojin


  "He needs some food and a cold drink" Jinjina kai su ka Yi, A waya Md Ya kira nurse Ya isar da saƙon abunda za'a kawo masu, cikin ƙanƙanin Lokaci Nurse ta shigo hannunta biyu ruƙe da round tray saman shi plate ne shaƙe da abinci sai bottles biyu na ruwa dana lemu mai sanyi, A saman table ɗin gaban gadon gabriel ta sauke tray ɗin kafin ta juya ta fuce, Zama suka yi saman sofa ɗin dake a ɗakin suna jiran shi Ya kammala ci.


  Kafin ya fara cin abinci sai da ya fara ɗagowa ya kalle su"Ni zan ci"? murmushi suka sakar mashi Jin tambayar da yai masu


 Md yace"'It's all yours. Eat until you are satisfied. We need to talk to you when you're done."


A kan idonsu Gabriel Ke cin abincin sai da ya ci ya ƙoshi Ya kora da ruwan sanyi, tukunna ya dawo da duban shi gare su.


  "Zamu iya farawa yanzu" ɗaga masu kai yai alamar eh


  Major ne Ya fara yi mashi magana

  "Zaka Iya fadamin alaƙar dake a tsakaninka da sauran yaran? Jinjina kai Gabriel yai"Eh, Ƴan uwana ne"


  "Menene sunayenku da shekarunku"?

 Duk wata kalma da Gabriel ya furta a rubuce dr. Brown ya ke shigar da bayanan cikin ipad ɗin hannunsa.


   "Muna zargin Ɗan ta'addan da muka je kamawa A dajine yai garkuwa da ku don gujewa farmakin da zamu kai mashi Shin dagaske ne"? Ras Gaban Gabriel Ya faɗi, tuni yanayin fuskarshi ya canza baisan amsar da zai basu ba, jin shiru yasa Major ambaton sunanshi"Gabriel amsar ka mu ke jira, muna so mu tabbatar da hasashen mu ne"


 idanuwanshi sunyi wuƙi wuƙi akan fuskokinsu, duk sun ƙagara da son jin amsar da zai basu, abunda yasa ya shiga ruɗani kokwantone yake yi Akan ya faɗa masu gaskiya ko kuwa ya 6oyeta gudun kada su ƙara jefa rayuwarsu cikin hatsari, Yana tsoron abunda harshenshi zai furta, Tunawa da Angel yasa shi saurin cewa


  "I have forgotten everything, but my sister Angel knows everything." ya faɗi hakanne don su ƙyale shi, don kuma su tuntu6eta don yasan tafi shi wayau ita kaɗai tasan yadda za ta yi ta fidda su.


   Numfasawa Kowan nan su yai, sun fahimci har yanzu babu kwanciyar hankali atattare da shi


   "Gabriel, please calm down and explain to us what happened. We're medical professionals, and we have the right to examine your health and help you get better. And those soldiers you see are the ones who saved your life in the forest. If you cooperate with us, we'll help you and reunite you with your family." cikin kwantar da murya dr laura ta yi mashi magana.


wahalalln Yawu gabriel ya haɗiya muryarshi na rawa ya furta"Angel tasan komai, duk wani bayani da kuke son ji daga bakina ita zata faɗa maku," 


    "Can you identify your sister from these photos? Wacece Angel a cikinsu"? Dr.brown ne yai maganar tare da nuna mashi hotunansu ta cikin  ipad's gallery din hannunsa


  Ƙura ido gabriel yai akan fuskarta ya ɗaura yatsan shi"Itace"  


  Dr. mark ne ya soma yin magana


"muna son jin bayani dangane da abunda ke damunku"? Ya yi mashi tambayar ne saboda abun da ya ɗaure masu kai, na farko Depression dake damunsu da ƙananun shekarun su, na biyu dangane da matashin saurayin nan da ya tsone masu ido wato Danish  da ya ƙi farkawa daga bacci.


  "Babu" amsar daya basu kenan

Captaim yace"ka natsu kayi mana bayani, ba cutar dakai zamuyi ba, idan har baka bamu amsa ba zamu maida ku inda muka ɗauko ku ne" jin haka yasa Gabriel zazzare mashi ido, da sauri ya girgiza kai yana faɗin"Ni ai bansan komai ba Angel ce ta sani," kansu ya ɗaure jin yanata ambaton sunan Angel


  "We should wait until your sister wakes up and see if she can provide any information that might help us." acewar dr. brown


Gaba ɗaya sunyi amanna da hakan, Miƙewa Sojojin sukayi tare da likitocin Bayan sunce mashi ya koma ya kwanta suka fuce daga ɗakin, A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya suna tattaunawa a tsakaninsu, Hankalinsu yaƙi kwanciya da yaran, sun fara kokwanton Anya kuwa Jinsin su ne? Ko dai sun yi kuskure wurin ɗauko su a matsayin ɗan'ta'addan ƙasar su ne yai garkuwa da su, Kyawun yaran yafi komai tafiya da hankalin su, sun rasa da wani jinsi zasu danganta su, Saboda Kyawun prisoners Ya banbanta dana sauran mutane su ɗin na dabanne.


Bayan kammala tattaunawar su, Sojojin sun bar asibitin da niyar idan sauran Yaran suka farfaɗo daga bacci Ayi hanzarin kiransu da gaggawa don suna buƙatar ganawa da su.


Nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel ya sauke tun bayan fitarsu yake ta sakin murmushi baƙin shi yaƙi rufuwa, tuni hawayen farin ciki sun wanke fuskarshi bakomai yake tunawa ba fa ce twin sister ɗinsa da sauran ƴan uwansu da suka rasa rayukan su a kurkuku, Ya ji raɗaɗin Rasa su da su ka yi da yanzu duk atare zasu ji daɗin rayuwarsu, don yana ji aranshi ƙarshen wahalar su ce tazo, babban burin shi a yanzu sauran ƴan uwansu su farfaɗo, Yasan zasuyi farin ciki Mara misaltuwa, fatan shi Allah yasa Idan Angel ta farfaɗo Ta yi ƙoƙari wurin yin magana da sojojin cikin hikma yadda zata yi masu hanyar komawa gidan daddynta ko dan saboda azeezarshi da ta ƙwallafa rai da son zuwa can.


Yayin da ya ke yin tunanin, hawaye basu daina yin sintiri akan fuskarsa ba, a saman pillow ya ɗaura kansa, ga sanyin A.c dake ratsa jikinsa.


Motsin buɗe ƙofa ya ji da sauri ya ɗan yunƙura ya miƙe zaune yana kallon mai shigowa ciki, Matashiyar Nurse ɗin da ta kawo masa abinci ce ɗazu, Fuskarta  ɗauke da murmushi agaban gadon ta tsaya tare da goya hannayenta saman ƙirjinta

  

Fuskarta da murmushi ta soma magana


"Hello, I'm Sister Rebecca, May I know your name?" 

  Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta suna shi "Gabriel" jinjina kai nurse rebecca tayi a wayance tace "It's wonderful to meet you, Gabriel. How is your body? I hope you're feeling better now,"  

Rashin sabo ya hana ya saki jiki da ita,  cikin rashin natsuwa yake amsa mata. 


Ganin yadda take sakar masa fuska yasa shima sakin tashi fuskar


 "Is there any part of your body that's hurting?" cikin kulawa ta yi mashi tambayar.

Girgiza mata kai yai"A'a lafiyata ƙalau"


"Okay, is there anything you need?" again ta ƙara tambayar shi.


Ƙasa ƙasa da murya ya furta "No, thank you."


  "Okey, ko akwai wani abu da kake buƙata"? Shiru ya ɗanyi yana faman wurwurga eye balls dinsa ɗakin Ya ke bi da kallo 

  Ganin kamar tv yake kallo yasa tace" "Would you like to watch some TV?"


 Numfasawa yai tare da mayar da idon shi akanta


  "I wanna see my brothers, I want to know how they're doing."


"Please, don't worry, Your relatives are in good health and we expect them to wake up soon." da sauri ya tari numfashin ta

"Can you help me go to their room to see them?" A ƙagare yai mata maganar


  "Don't worry I'll take you to see them but first you need to rest. You've traveled for hours, and you must be tired. I'll turn on the TV so you can relax, and if you need anything, you can use the phone to call me." ta yi maganar tana nuna mashi wayar dake ajiye saman table na gefen gadonshi


  "Ga kuma ƙofar shiga toilet idan kana buƙata" duk abunda ta yi mashi bayani saita nuna mashi da hannu


  Bayan ta kammala, Taje gaban plasma tv dake manne jikin bango ta kunna mashi tashar da ake wasan ƙwallon, don tasan mafi akasin maza sunfi sha'awar kallon wasan ƙwallo,


A ƙirji ya rungume pillow yana kallon tv ɗin, fuskar nan ɗauke da annuri banza ta samu an samu ƴanci, Yadda nurse ɗin ke tarairayarshi kamar wani ƙaramin yaro da bai wuci shekara goma ba.

 Kafin barinta ɗakin saida ta ɗauki Kayan abincin da ta kawo mashi ta fuce da su robar lemun da bai sha ba kaɗai ta bar mashi, Hannu ya miƙa ya ɗauke ta, Yana sha Yana kallo Hankalin shi kwance gwanin ban sha'awa


The prisoners Middle step❤


Wuraren ƙarfe goma sha Biyu agogon birnin san antonio ta buga, adai dai wannan lokacin sambatun muryar Angel ya cika ɗakin da aka kwantar da ita, tana akwance saman haɗaɗɗen gadon, patient's gown ce a jikinta launin ligh blue, drip ɗin da aka sanya mata tuni ya jima da ƙarewa, zazza6in jikinta ya sauka temperature ɗinta ya dai dai ta.

   Muryarta na kakarwa take ambaton sunan danish, Shi ya tsaya mata arai shiyasa take sambatun ambaton sunansa, duk da sanyin A.c na ɗakin hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, zucyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi

  "Danish ɗina kura ta cinye min shi, wayyo Allah Danish ɗina na shigo uku munbar Danish Gabriel kura Zata kashe min shi....." tuntana sambtun a hankali har takaiga ƙware murya da wata irin firgita Ta ware Gray eyes dinta ta zazzare su akan haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakin, Sam bata acikin Hayyacinta, bakomai take gani acikin idanuwanta ba face Fuskar Kurar da ta biyo su A daji tana gurnani, gizo take yi mata, A gigice ta zabura har batasan ta fisge iv line ɗin dake hannunta ba, durowa daga saman gadon tayi Hannayenta bibbiyu daddafe da kanta, Tsantsar tashin hankali ne akan fuskarta, duk tabi ta furgice, doguwar sumar kanta har saitin gwiwarta gaba ɗaya ta hautsine gashin kan tamkar na mahaukaciya, Sam bata acikin hayyacinta batasan A ina take ba? Daji kawai take gani a idonta


  Sosai ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, idanuwanta sun makance,,


Da gudun gaske Likitoci suka faɗo ɗakin da take a ciki, Dama jiran farkawarta suke yi, wasu daga cikin Ƴan uwanta sun farka acan inda aka kwantar dasu, Sun rasa gane kan Yaran tsabar tsoro da firgici Jikin su sai kerma ya ke yi sunga mutanan da basu saba gani ba, duk wanda yai yunƙurin tunkararsu ƙara suke fasawa tamkar ana zare ran su, Kalma ɗaya su ke iya ambato abakunansu Sunan Angel wannan yasa Likitocin su ka ƙara da ta farka, don sun fahimci ita kaɗaice zata Iya sarrafa su.


Sam bata ji motsin shigowarsu ba, Sai dai ta ji muryoyinsu akanta, Nan fa hankalin Ta ya ƙara tashi, A firgice ta waiwayo tana binsu da kallo tun daga ƙasa har sama, Waro idanuwanta waje tayi tamkar ƙwayar zata faɗo kasa, jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu, tsantsar tashin hankaline akan fuskarta da ruɗani, sai lokacin ta soma tunanin wai ma A ina take ne? Ya akai ta tsinci kanta a wurin nan? Wanene Ya kawota? ina ƴan uwanta suke? Su wanene waɗannan masu fararen Kayan kamar likitoci ne"? Wahalallan Yawu ta haɗiya, zufa duk ta wanke fuskarta da jikinta, yadda kasan wadda ta yi tozali da aljanu, ganin komai take yi tamkar a mafarki


   Cikin kwantar da murya su ke yi mata magana don sun fahimci arikice take babu natsuwa atattare da ita

  "Ki kwantar da hankalin ki, Dukanmu nan da kike gani likitoci ne, mune masu kula da lafiyarki, Sannan anan inda kike Asibitine....." Ras taji gabanta ya faɗi Cikin sarƙewar murya ta soma motsa small lips ɗinta

   "Ban...ban..gane ba wanene ya kawo ni nan? Su wanene ku kuma Ina ƴan uwana su ke"? Kallon tuhuma take binsu da shi gani take yi kamar mugaye ne. 

  "Ƴan uwanki suna nan Cikin ƙoshin Lafiya, idan kika natsu zamu Nuna maki su, wata'ƙil hankalinki ya kwanta" maƙe mashi kafaɗa tayi"wlh bazan yarda daku ba, so kuke ku cutar dani, Ni ku faɗamun Ina danish ɗina yake da sauran ƴan uwana....." cikin disasshiyar murya tayi maganar hawayen nabin fuskarta, ganin suna matsowa kusa da ita aiko da sauri ta dinga ja da baya tana girgiza masu kai, haɗi da zazzare masu ido don karsu ta6ata

  

Hakan yasa suka dakata da yin tafiyar, turo ƙofar da akayi ne yasa gaba ɗayansu suka juya don ganin wanene

   

   Nurse rebecca ce Ta shigo ɗakin hannunta ruƙe dana Gabriel, Wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi ganin Angel, Ita ko ta runtse ido, Masifa kawai take Ji, da ƙarfi Ya ambaci sunanta"ANGEL!!" Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnanta, Kamar an tsunkuleta Ta buɗe ido Tana faman zazzaresu Akan fuskokinsu, da gudu gabriel Ya ƙarasa gabanta, Gaba ɗaya ya rungumeta Yana dariya, A ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirgita, ƙanƙame shi tayi tamkar zasu koma mutun ɗaya.

   Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirkon suna kallonsu, murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, tamkar sun samu tv.

  Raba Jikinta Tayi daga na Gabriel Muryarta na rawa take faɗin"Gabriel wanene ya kawo mu nan? Pls ka faɗamin Aruɗe nake bangane komai ba, Ina danish dina da sauran Ƴan uwana? 


  Ruƙo Hannayenta yai acikin nashi"Angel mun tsira! Mun ku6uta daga kurkukun ƙaddara da Evil forest......." a tsanake Gabriel Ya kwashe komai Ya sanar da ita, Cikin harshen hausa, hakan yasa Doctors din basuji me yake faɗa mata ba.

  Maimakon tayi dariya Sai gani suka yi ta rushe da matsanancin kuka, abunda da ya ɗaure masu kai, tana kuka tana dariya a lokaci ɗaya, slowly ta zube saman gwiwowinta, tare da ɗaura goshinta saman tiles, Sujjada tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan ranar da suka daɗe suna Jiranta!


  


Boss Bature✍ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin
First bank
3196407426, 
Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post