Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 19

Kurkukun Kaddara Book 2 Episode 19

 


BossLadiesWriters

           KURKUKUN ƘADDARA

Middle step

  

              The Prisoners E19🔥💫

Daga alƙalamin Boss Bature


In a smoky voice ya furta"I'll call you later." da mutumin da su ke yin video call ɗin da shi ya ke magana. Tun kafin ta ɗago da kanta cikin shessheƙar kuka ta ke faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Am sorry daddy, nayi kuskure bani da hankali, dan Allah ka yi haƙuri wlh bazan ƙara ba" lumshe idonshi ya ɗan yi kafin gently ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, Hannun shi tallabe da laptop ɗinsa, ko kaɗan bai ji zafin ruwan da ya hau saman jikinsa ba.


 Zeenatu ba ta dai na yi mashi magiya akan ya yi hakuri ba, hankalin ta duk yabi ya tashi saboda mugun tsoran daddyn nata ta ke ji.


  "Daddy na tuba bazan ƙara ba, Ka yafe min nagane kuskure na" tsoro Ya hana ta ɗago su haɗa ido. 


  Miƙewa yai daga saman sofa ɗin ya juya ya nufi cikin Katafaren room ɗin nasa, After some minutes sai gashi Ya dawo babu laptop din a hannunsa, Ya canza jallabiyar jikinsa, ɗaura idanuwansa yai akan bayan zeenatu, dogayen yatsun hannunta sai kerma suke Yi.


   Agaban Sofa table ɗin Ya dakata da yin tafiya, da kakkausar murya yace"Ke! Miƙe tsaye tun kafin ran ki ya 6aci" Jikinta na kerma ta ɗago da kanta hawaye sun wanke fuskarta sharkaf, abunka ga farar fata face ɗin ta yi jawur, Blue eye balls dinta sun ciza launin su idon nata ya rune, small pink lips ɗinta tsabar ƙarantarsu tamkar na jariri.


  Cikin rashin natsuwa ta zube saman gwiwowinta, Idanuwanta na kallon tiles ɗin ɗakin

  "Dad...am sorry bazan ƙara ba, nasan bana jin magana bani da natsuwa amma ka yafe min, kada ka hukun......"


Gigitacciyar tsawar da ya daka mata ce tasa ta yin saurin toshe kunnuwanta da tafin hands dinta


 A razane take faɗin "Na shiga uku daddy, nace maka bazan ƙara ba, Nagane kuskure na"


    Muryarshi a kausashe Ya furta sunanta"Zeenatu? Sau nawa ina gargaɗin ki akan ki daina faɗo min ɗaki ba tare kin nemi izni na ba? Waya baki iznin shigowa ciki"?


  Wahalallan yawu ta haɗiya, idanuwanta sunyi luhu luhu sai faman wurwurga eye balls ta ke Yi kamar ƙwayar zata faɗo ƙasa.


  "Am sorry dad..." katse ta ya yi"Kin Iya tsallan kwaɗi?" tun da ya fara magana bata bari ta ɗago sun haɗa ido ba sai Yanzu da ta ji yace Tsallan kwaɗi


  A hargitse ta zare mashi manyan idanuwanta

     A matukar ruɗe take girgiza mashi kai"daddy bazan Iya ba, Ni bansan yarda akeyi ba, ai nace ka yi haƙuri bazan ƙara ba"


  Gyaɗa kai Yai"Tashi ki fuce ki bani wuri shashasha, daga yau karki kuskura ki ƙara faɗo min ɗaki"


Zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, duk sai ta ji ba daɗi, ba ƙaramin kewar daddyn nata tayi ba, maimakon Ya nuna farin Cikin ganinta saima korar ta da yayi.


  Ganin yarda ta tsare shi da ido taƙi motsawa ne Yasa shi daka mata tsawa"nace ki tashi ki fuce min daga ɗaki tun kafin In yi ball dake" fuskarshi a haɗe Yai maganar ba annuri.


A gurguje Zeenatu ta miƙe ta juya tana tafiya Jikinta na kakarwa har Ta kai bakin ƙofar fita ɗakin, ta ji ba za ta iya jure fushin daddynta ba, tasan duk akan kuskuren da ta yi mashi ne.


  Yana atsaye ya goya hannayenshi saman faffaɗan kirjinshi Ya natsu Yana kallon Bayanta, Har ta kusa fucewa daga ɗakin A lokacin Ya juya zai shige ciki ba zato ba tsammani ya ji an rungumeshi ta baya, ƙanƙameshi ta yi tana faɗin"wlh daddy ba in da zan je, ai na faɗa maka kuskure ne bada sani na na 6arar maka da coffee, yakamata ka yi haƙuri ka yafe min, Ni banason kana fushi dani saboda kai mahaifina ne, kuma inason ka sosai bazan Iya jurar fushin ka ba" 


 Har cikin zuciyar shi ba ƙaramin sanyi ya ji ba, kalaman zeenatu sunyi matuƙar kashe mashi jiki, Ba tun yau ba duk idan ta 6ata mashi rai ko ya kore ta daga ɗakinsa ba ta tafiya shiyasa yai mata hakan don ta ga ne kuskuren ta yasan dole ta dawo ta bashi haƙuri.


  Da hannu ɗaya ya ruƙo hijabin jikinta Ya janyota zuwa gabanshi, Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, A hankali ya ke ɗan bubbuga bayanta da hannayenshi cikin sigar lallashi, hakan da yai mata ba ƙaramin kwantar mata da hankali yai ba, harta fara samun natsuwa.


  Tsawon mintuna kafin ya raba Jikinshi daga nata, fuskarta jawur idanuwanta har sun ɗan kumbura.


  "Kin 6ata min riga da hawaye" tana faman zazzare ido ta furta"am sorry"


 "Is okey, kinsan banason ganin hawayenki, meyasa kike min kuka"?


  "Daddy ai kai ne ka sani yin kuka, Ina baka haƙuri kaƙi ka saurareni"


  "Zeenatu ɗago ki kalli Cikin idona" daƙar ta Iya ɗagowa ta sanya idonta cikin nashi gabanta Ba ƙaramin faɗuwa yai ba saboda ƙwarjinin da yai mata.


  "Bansan meyasa ki ke jin tsorona ba, Nifa daddynki ne, saboda kawai kin 6arar min da coffee shine duk kika ɗaga hankalin ki? Ni shine abunda Ya 6ata min" fuskarshi a ɗaure tamau yai mata maganar.


  Muryarta na ɗan rawa ta furta"dad..dy ai kai ne baka dariya ko murmushi ba ka yi min kullum fuskarka a ɗaure, kuma baka son ina zuwa kusa da kai, nasan saboda rashin natsuwata ne amma in sha Allah daddy zan daina, ina yin addu'a ma har tsakar dare Akan Allah ya yaye min..." Yatsan Hannun shi ya daura saman lips ɗinta


  "Ya isa haka, Karki kuskura na ƙara ji kin ce bana son kina zuwa kusa dani, kinji ko? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh


 Mayar da ita Yai saman chest ɗinsa, Yaci gaba da shafa bayanta Yana ƙara lallashinta.


  A haka Hajiya sarah ta riskesu, a bakin ƙofar shiga room ɗin nashi taci burki, farar mace alkebbar mata doguwar riga ce a jikinta fitted gown ta lace, Kusan rabin ƙirjinta awaje Yake, Tubarkallah na shanunta atsaitsaye su ke, tamkar bata ta6a haihuwa ba, light make up ne akan fuskarta, Ƙafafuwanta na sanye cikin High hills, sun ƙara mata tsayinta. Babu mayafi akanta zallar sumar kantace tasha ado tsabar haɗuwarta tamkar budurwa.


  "May I come in"? Muryarta har cikin kunnuwansu, Alhaji musa ne ya bata Iznin shigowa ciki, ɗagowa zeenatu ta yi daga kan chest ɗinsa, Muryarta na ɗan rawa ta furta"daddy zan tafi" 


 "Da iznin wa"? Ya jefa mata tambaya, shiru ta yi tana ƴan kame kame, Sam ba ta son mommynta ta shigo ɗakin daddynta idan tana aciki.


   Ƙarasowa Ciki Hajiya saratu tayi, kaitsaye ta nufi Alhaji musa, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi take duban su shi da zeenatu.


  "Masha Allah, Uba da ƴarsa kunyi kyau fatan ban takura maku ba" 


 Zeenatu ce tai saurin cewa"Mommy, na shigo gaida daddy ne dama, yanzu zan tafi" kallon da Alhaji musa Yai mata ne yasa ta yin saurin canza magana"A'a ba yanzu zan tafi ba, sai daddy ya bani iznin tafiya"


Ta yi maganar tare da samun wuri saman sofa ta zauna, Jikinta nata yin kerma acan cikin zuciyarta addu'o'i take karantowa.


  Matsawa Hajiya sarah Ta yi dab da shi, duk da shakkarshi da ta ke ji hakan bai hanata nunawa mijin nata soyayya, tarairayarshi ta ke yi kamar sabon jinjiri ta haka ta ke iya samun damar Iya sarrafa shi.


 Hannayenta ta ɗaura saman waist dinsa, Daddaɗan ƙamshin turarenta tuni ya fara Kashe mashi jiki.


  "Baby, jiya ka hana kowa yazo kusa da kai, kuma ina buƙatar ka, Na kwana da son kasancewa atare da kai" cikin harshen turanci ta ke yi mashi magana, gogan naka babu fara'a akan face ɗinsa ya ƙame a tsaye kamar soja.


  "Zeenatu, ta shi ki je ɗakin Yayanki shureim, Tani ta faɗa mini tun safe ba ki ci abinci ba, nayi mata magana ta shirya mashi abincin aɗakinsa, Za ki Iya zuwa can kuci atare da shi" 


Kamar Jira ta ke yi mommyn ta yi mata magana, da sauri ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin Har Allah Allah take aranta, saboda bata son ganin Iyayen ta suna yin romancing din junansu agabanta Kunya take ji kuma hakan Yana jefata wani hali.


   Baya fitar Zeenatu ta dawo da dubanta akan fuskar shi.


   Muryarshi a kausashe Ya furta "Baki da kunya? Baki ga me kika ruƙe min ba ne" 


 Kashe mashi ido ɗaya tayi muryarta da kwarkwasa ta furta"kaine ka koyamin rashin Kunyar," hakan da tayi mashi ba ƙaramin jefa shi yanayi tayi ba, dama Shi mutunne da baya wasa da duk wani abu da jikinshi ke buƙata.


  "Yanzu ina da aikin da zanyi, Da anjima zan neme ki" marairaice mashi fuska tayi"A'a baby, yanzu nake buƙatarka ni, kusan 3 days  baka atare dani, bazan iya jurewa ba."


  Yamutsa fuskarshi Yai, Kafin Yai yunƙurin ƙara furta wata kalma, tayi saurin zame wuyan rigar jikinta, Ba ƙaramin shammatarshi tayi ba, gaba ɗaya ya rasa sukuni, Baisan ya akai ba ya tsinci kanshi asaman gado sun tsunduma suna Korar shaiɗanu, Suturar jikinsu A saman floor na tsince su bansan ina zan kaisu ba, Laundry ko toilet? (🤣 wato duk izzar namiji sai in bai haɗu da mace ba)


Tuni Dr shureim Ya kammala shiryawa,     Ya canza suturar jikinshi, still Arab dress ne, kayanshi na gado, Yana daga zaune gefen gadon shi, Hannun shi ruƙe da Wayarshi Yana kallon hoton abar ƙaunarsa da ya buɗo a gallery.


  Ba zato ba tsammani Yaji Muryar matashin saurayi Yana Kwaɗa sallama daga bakin ƙofar ɗakinsa, slowly ya ɗago da ido yaɗan Juya yana kallon Saurayin dake sanye cikin black suit, dogo kuma faffaɗa, Hannun shi ruƙe da Ƙatuwar shopping back mai ɗauke da sunan Obinna tech


  A sukwane Dr shureim ya ɗaura wayarsa saman mattress Ya yunƙura ya miƙe Still idonshi akan mutumin.


  "Dr shureim Barka da warhaka"

 Muryarshi babu natsuwa ya furta"yawwa barka dai" duk yasha jinin jikinshi saboda mutumin babu fara'a akan fuskarshi kamar wanda aka ɗaurawa aure da mutuwa.


 "Saƙo ne daga Uncle ɗinka" nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tunawa da saƙon da uncle musa Yace za'a kawo mashi.


  A hanzarce ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, Ya miƙa hannu biyu ya kar6i kayan daga hannun mutumin haɗi da yi mashi godiya.


  Fuskar shurem ɗauke da murmushi ya nufo cikin ɗakin, A saman gado Ya ɗaura shopping back ɗin, Bayan yayi bismilla, Ya buɗe ta tare da zura hannu Ya zaro kayan dake aciki, har saida gabanshi Ya ɗan faɗi.


  Apple laptop ce, tare da Apple watch, abu na ƙarshe da ya gani Unexpected Danƙareran Key ɗin Mota, Zubewa yai saman gwiwowinsa agaban Kayan Yana duban su, A tsanake Ya ke ƙare masu kallo, haƙiƙa Yayi farin Cikin Kyautar nan da uncle musa yai mashi ya ji daɗi sosai, ɗaga Hannayenshi sama Yai, Ya soma jera addu'o'i Yana yiwa kawunsa bisa irin farin cikin daya Sanya shi ayau, Ya faranta mashi sosai.


  Bai gama shan mamakin Kayan ba, Muryar mutumin da ya kawo Kayan ta katse mashi addu'o'in da ya ke yi.


  "Dr shureim Zan iya shigowa Ci ki?

 Da sauri Ya miƙe tsaye Yana kallon shi.


   Manyan Akwatuna ne guda Biyu a hannun shi ya ruƙe handle ɗinsu Yana Jansu irin masu tayoyin nan.


  "Bismillah" yai mashi nuni daya shigo Ciki, Bayan ya shiga Cikin ɗakin agaban  tafkekiyar Glass wardrobe ɗin ɗakin mai faɗi Ta mamaye bangon da take a jikinsa, Anan mutumin Ya dakata da yin tafiya ya buɗe akwatunan, Farin Ciki Ya hana dr. shureim Rufe bakinsa.


  Arab dress ne kala kala Na maza, Kalar waɗanda Yafi so, A ƙalla sunkai kala Hamsin sababbi fitigil dasu shaƙe cikin akwatin, Hada Arab turban ɗin da Yake naɗawa akanshi.


  Atare da mutumin suka soma jera kayan acikin wardrobe ɗinsa, Bayan sun kammala jera kayan, Man ɗin Ya buɗe ɗayan akwatin Wa'iya zubilla Uncle musa Ya gwangwaje ɗan nasa da Haɗaɗɗun leather shoes da tsadaddun turarurruka Na Larabawa, Da suran Kayayyakin amfani na gyaran Jiki, a gaban mirror suka jera Kayan, Bayan mutumin Ya kammala, Dr. shureim yai mashi godiya suka Yi sallama da shi.


  Yana atsaye idonshi akan sabbin Kayanshi sai binsu ya ke yi da kallo, daɗi kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.

  

 Muryar Tani ce Ta janyo hankalin shi ga dubanta.


 A yayin da ta ke shigowa ɗakin nashi


 "Dr shureim barka da rana, Fatan Ka wuni Lafiya? Ya kwanan gidan uncle ɗin naka"


  Hannunta biyu ruƙe da Faffaɗan wooden tray, daga saman shi jerin lunch ɗinsa ne.


  Da fara'a akan face dinsa Ya soma Amsa mata gaisuwar"Alhamdulillah, Fatan kema Kina Lafiya ya aiki"?


   "Lafiyalou, ai Munji daɗin zuwanka gidan nan, Ko ba komai zaka ɗebe ma Zeenatu kewa, Baiwar Allah jiya tayi murnar zuwanka, Tana matuƙar son yayanta" Fuskarta awashe Ta yi maganar, adai dai takai gaban table ta ɗaura mashi tray ɗin.


    Murmushin gefen fuska Yasaki tare da faɗin"Allah sarki, Tun Jiya bata ƙara dawowa ɗakina ba, Idan ba damuwa ki kira min ita idan kin fita, nasan saboda Kunyar abunda Ya faru Jiya ne Yasa ta kasa zuwa gaishe ni da safe"


   "Wlh kamar ka sani, abunda ya hanata zuwa kenan, ai zeenatu akwai kunya, Yarinyar kuma tana da mutunci ga kamun kai, Ga ilmi, ita dai taji daɗin rayuwarta, Gaskiya ba ƙaramin mai sa'a bane zai mallaki Zeenatu" tun da Tani ta fara Yi mashi sambatun Kyawawan halayar zeenatu Ya natsu Yana sauraranta haɗi da kallonta, Ya fahimci so ta ke Yi, Ta yi mata gyaran hanya awurin shi. Dama tun Jiya da yazo matar take ta yi mashi sambatu akan zeenatu.


   "Idan badamuwa, inason Ganinta" washe baki Tani ta yi"Toh, yanzun nan zaka ganta," Da sauri Ta juya ta fuce daga ɗakin.


    Tattara Kayan saman gadonshi yai, acikin Shopping bag ɗin Ya tura su.


  Ajiyar zuciya ya sauke Ya koma gefen gadon shi ya zauna yana jiran ƙarasowar Zeenatu.


  Akan Hanya Tani taci karo da zeenatu tana tafiya kamar munafuka, sam babu natsuwa atattare da ita, sai ƴan waige waige take Yi, har sai da suka bangaji juna da Tani tukunna ta zabura ta kalleta suka haɗa ido


  "Ina kika shiga ne?"


 "Ɗakin daddy" ta bata amsa

 "Hawayen menene akan fuskarki! Waya ta6amin ke" zumbura mata Baki Ta yi ba tare da ta bata amsa ba.


  Ruƙo hannunta Tani tayi"Muje ɗaki ki gyara fuskarki, dr shureim ne yace in kira mashi ke" waro ido waje tayi jin ance Yaya shureim ke kiranta.


  Jiki na rawa Tabi Tani suka nufi falo abakin stairs suka hau elevator takai su Second floor, Bayan sun fito da sauri suka nufi ɗakin zeenatu, sai da Tani ta jira tayo wanka tukunna ta taimaka mata wurin canza Kayan jikinta, Pakistan ta sanya riga launin blush pink har gwiwa, Tare da burgujejan wando Fari anyi mashi adon stones, Tani ta ɗaura mata Mayafi akanta, Babu makeup Iya kyawun fuskarta ne.


  Flat shoes Ta zura a ƙafarta, Atare da Tani suka baro ɗakin Bayan sun sauko down, sai da Tani taja mata kunne akan ta natsu kada Tayi mashi hauka, ta amsa mata da toh.


  A hankali take Yin tafiya tana nufar sashen room ɗinsa, a bakin ƙofar ɗakinshi ta la6e tana leƙensa Yana zaune idonshi akan screen ɗin wayarshi, Ya natsu Yana kallo ko motsi bai yi, Kunyace ta kama ta, muryarta 

Ƙasa ƙasa take ambaton sunanshi"yayana rabin raina" shiru dr a

Shureim bai amsa mata ba


  "Hubbyna" still shiru, da alama bai ji sautin muryarta ba.


 Tunani ta soma yi ko menene ya ke kallon acikin wayarshi wanda yai silar ɗauke hankalinshi! Ras taji gabanta Ya faɗi sakamakon amsar da zuciyarta ta bata na cewa wata'ƙil hoton girl friend dinshi yake kallo.


  Cikin sanɗa ta ke yin tafiya cikin ɗakin nashi duk don ta gano abunda Yake kallo, daga 6angare hannun dama na gadonshi ta zagaya tana yi mashi dogon wuya, ƙamshin turarenta ne Ya tona mata asiri, lumshe idonshi yai yana tunanin a ina aka samu fragrance me daɗin shaƙa a ɗakinsa, ɗagowar da zai yi keda wuya idonshi ya sauka akan zeenatu dake leƙan wayarshi, da sauri ya danna power button hasken phone ɗin ya ɗauke screen yai duhu.


  Duƙar da kanta ƙasa ta yi, yanayin fuskarta ya canza"yaya shureim ɗina, ka wuni lafiya? Am sorry Jiya ban dawo mun gaisa ba" A hankali Ya miƙe ya zagayo ta Inda take atsaye dab da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo.


   Baisan ya akai ya tsinci kanshi da kallon wankan pakistan ɗin da ta ɗauka ajikin ta, ta yi bala'en yi mashi kyau, Yarinyar kamar Fure haka take da ɗaukar ido.


 Tabbas Idan yaci gaba da kallonta zai shagala ne


 Acikin zuciyarsa Ya ambaci


"A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim"


 A fili kuma Yace"Zeenatu, kada ki damu bakomai, ay nayi maki uziri kece kika takura kanki"


Muryarta da shagwa6a tace "Mommy ne tace inzo muci abinci atare, tun Jiya dana bar ɗakinka banci komai ba" Ya rasa gane wani irin yanayi yake ji atare dashi, tana yin magana blue eye balls ɗinta na jujjuyawa, Yatsun hannunta sai kerma sukeyi saboda rashi natsuwarta.


   Abu mafi jan hankali a jikinta ƙirjinta kamar zasu tsonewa mutun ido

  "Ki jirani awaje"! Abunda Ya furta mata kenan

 "Yaya shureim ba abinci zamuci atare ba"? 

  "Eh, amma ba'a cikin ɗakina ba, kinsan babu kyau mace da namiji su ke6e a ɗaki ko"? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh 


  "Bari na ɗauko mana kayan abincin sai mu koma dining room" tuna abunda ya faru Jiyane yasa shi yin saurin cewa"No! Ni zan ɗauka," amsa mashi tayi toh" Ya zagaya other side ya ɗauko tray din Kayan abincin da hannu biyu ya ruƙo shi, yana agaba tana bayanshi, a Haka suka ƙarasa cikin Haɗaɗɗen ɗakin Cin abincin gidan, Dining tables har kala Uku, Kowanne a kewaye da chairs, a saman table Ya ɗaura masu tray ɗin, suka zaune suna fuskantar juna, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya yai ba, A inda suke Masu aiki Na iya hangensu daga main palour.


   Sai faman sakar mashi murmushi take Yi


  "Yaya shureim, zamu dinga fita yawo atare ko? Kaga kullum ina agida daddy baya barina zuwa yawo, tun da na kammala secondry school kullum Ina agida" ta ƙarasa maganar tare dakai hannu ta ɗauki serving spoon ta buɗe warmer ta Fried rice ta zuba masu a plate Biyu, ta sanya masu spoons aciki.


  Suna ci suna Yin fira ga lemunsu me sanyi a glass.


  "Kada Ki damu, Munyi magana da daddynki, Yace yanason ina taimaka maki da wasu abubuwan"


  Washe baki Tayi"yaya shureim zamu fara fita shan ice cream da zuwa cinema? And shopping ko"? Ɗaga mata gira yai alamar eh, cizon pink lips dinta tayi"Yaya shureim Amma ka ta6a yin soyayya"?  Ƙiris ya rage ya shake saboda surutun zeenatu, girgiza mata kai yai"ban ta6a ba ke fa"? 

  "Maza dayawa suna haukan sona, Ni kuma nafison auran miskilin namiji, mai ilmin addini dana zamani kuma Yana amfani da su, sannan me Koyi da sunnar Annabi Muhammad SAW"


 Tunda ta fara lissafa kalar namijin da takeso, dr shureim ya dakata da cin abincinsa, Ya natsu yana kallon pink lips ɗinta, taƙi tsayar da idonta wuri ɗaya Sai faman ƙeƙƙeftasu takeyi kamar babie.


  "Yaya shureim kai fa watakalar mata ka ke son Aure" baisan sa'adda Ya furta"ra'yinmu ɗaya" zare mashi ido tayi


  "What"? Girgiza mashi kai tayi"amma yaya shurem idan ra'ayinmu ɗaya kenan bakason mace me surutu? Mara natsuwa mai rawar kai haka"? Murmushi ya sakar mata har dimples dinsa suka lotsa.

    "Nidai nace Ra'ayinmu ɗaya" ya sake nanata mata maganarsa, murmushin gefen fuska tasakar masa"indai dagaske Ra'ayinmu ɗaya da kai, Toni inason Namiji mai surutu mara natsuwa mai rawar kai, kaga kenan Kaima kana son mace irin haka" 


dariya ce ta kubce mashi, Harya shaƙe da abinci Da sauri ta miƙa mashi lemu Ya kar6a Yana kur6a, Gwanin ban sha'awa haka suka cigaba da cin abinci tana Janshi da surutu.  


DAULAR OBIE ESTATE


A ɗakin Hajjaty, Kwance suke asaman gadon sun mannewa juna, Babu sutura a jikinsu zufa duk ta wanke jikinsu tamkar A.cn ɗakin Bata aiki, tsawon awanni da suka gama sharholiyarsu baccine Ya ɗauke su, Faɗaɗan tafukan hannayenshi ya cikasu da boobs ɗinta, ƙafarshi ɗaya tana a tsakankanin cinyoyinta sosai Ya shigeta, Ahaka bacci yai awon gaban dasu.


    Sautin ringing ɗin wayarshi ne Yai silar farkawarshi, Idanuwanshi sunyi jawur dasu, kasala duk Ta baibaye shi, daƙyar Ya Iya zame jikinsa daga nata, wani irin mayataccen kallo yake binta dashi, ji yake kamar ya ƙara second round don Baya gajiya da ita, matsawa yai saitin face dinta, ya kama lips dinta yai sucking dinsu, kafin A hankali Ya zame tongue ɗin ya mayar saman nipples dinta sosai yai sucking dinsu kamar zai karar dasu.


  wayarshi sai ringing ta ke Yi yaƙi mayar da hankali kanta.


 Jin Zafin abun da Yake yi mata ne Yai silar farkawarta, idanuwanta sunYi mata nauyi muryarta a disashe ta furta sunansa"Pravin pls ya isa haka, Yakamata Ka tafi, marece har Yayi, Nasan Hajiya saratu zata neme ka,"


ɗagowa yai da idonshi Ya kalli face dinta

  "Kin gaji dani ne"? Girgiza mashi kai tayi"kaima ka sani bani gajiya da kai pravin, da ace zan gaji da kai da tuni na rabu da kai" daƙyar take yin magana idanuwanta na lumshewa har yanzu mayen shi ta ke Yi.


   "Pls ka tafi pravin na roƙe ka"

   Da kasalalliyar muryarshi yake yi mata magana"zanyi kewarki nasan idan Owais ya dawo gidan nan ba ƙaramin takura zan yi ba, amma duk da hakan zanyi ƙoƙari ina satar hanya ba tare da kowa ya sani ba zan dinga zuwa ɗakin ki kina rage min zafi' harara hajjaty ta ɗan jefa masa"matarka fa? har mamaki nakeyi irin yarda kake liƙe min bayan matarka tafi ni komai"


 Ta6e lips dinsa yai'kada ki ce haka, arziƙi kawai zata nuna maki bayan haka bana tunanin akwai wani abu da zata Iya finki dashi, sai dai ma ki fita.


  "Amma kafi sonta akaina? Saboda Ta haifa maka ƴa'ƴa"


   "Waya faɗa maki? Kema ai na samu ƙaruwa dake, sai dai Allah bai nufa zai yi tsawaicin kwana ba, Ya rasu amma zamu sake haifar wasu idan kina so"


     Tamkar ya fama mata raunin dake acikin zuciyarta, kifa kanta tayi saman pillow, Hannu ɗaya ya ɗaura saman sumar kanta yaci gaba da shafa lallausan gashin kanta.


  "Its ok, kada Ki yi min kuka kinsan banaso My honey, "


  Cikin shessheƙar Kuka take faɗin"Pravin na gaji da irin rayuwar nan, bana jin daɗin kasancewata a matsayin ƴar aiki agidan nan saboda matarka saratu, ta tsane ni bata sona, har Gori ta ke Yi min tana kirana da sunan karuwa, wai ina shisshigema babansu wai ni pravin...' sautin kukanta ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yai ba


 Lallashinta ya soma Yi"am sorry nasan ba daɗi but ki yi haƙuri, in sha Allah zan nema maki mafita, idan bakya son zama gidan zan siya maki wani ki koma ki zauna can Hakan Yayi maki"?


 Ya yi tambayar yana leƙen fuskarta


  Ba tare da ta ɗago da kanta daga saman pillow ba tace"A'a, ai ni bana son inyi nesa da kai, Idan ka siya min gida na koma zaka Yi min wuyar gani, amma idan anan ne zan dinga ganinka akai akai, koda ba za mu yi magana ba idan ka gifta ina jin sanyi araina.


  Lumshe ido yai, muryarta na ƙara jefa shi cikin Yanayi na jin shauƙinta.


  "Shiyasa nake ƙara sonki My heart beat, kin fiye min kowace mace a duniya divya, kinyi haƙuri dani da daɗi da ba daɗi kin zauna dani, Inason ki sosai, kema kin sani, saratu bata fiye min ke ba, zan Iya rabuwa da ita amma ke bazan Iya rabuwa dake ba saboda ke Jinina Ce kuma amanace ke agare ni.


  Kalaman pravin sun sanyaya mata zuciyarta sosai, bata ta6a kokwanto akan abunda yake faɗa mata ba.

  Idanuwanta jawur take duban fuskarshi


   "I love u so much, My life partner," murmushi ya sakar mata.


  "Idan akwai abunda kike buƙata Ki sanar dani zanyi maki shi"


  Girgiza mashi kai tayi"a'a ai ni ka gama min komai pravin, ka haɗani da mutanen kirki waɗanda har yau ina alfaharin kasancewa ta acikin su, sun ɗauki nauyin komai na rayuwata ci na shana da suturar sanyawata, kaine sila pravin, bayan Albashi da nake samu awurinsu kaima kana turamin kuɗi duk ƙarshen wata masu yawan gaske, bansan ina zan kaisu ba, Tun da bani da buƙatarsu da ace Yaronmu yana araye kaga sai mu dinga siya mashi abubuwan wasan Yara, da sutura masu kyau ....."da rawar murya takai ƙarshen maganar, sosai ta sanya mashi kuka. 

  Cikin shessheƙar Kuka tace"Pravin bazan 6oye maka ba, Inason na haihu ko dan na samu madadin shi"

   "Ki kwantar da hankalinki, Zanyi shawara akan hakan" jinjina mashi kai Tayi

   Yunƙurawa yai tare da miƙewa Ya sanya hannu Biyu ya cuccu6eta duk girman jikinta baya jin nauyin ɗaukarta, Saukowa yai daga saman gadon Ya nufi toilet da ita, wayarshi da ya bari acikin aljihun short dinsa dake yashe ƙasa sai ringing take Yi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa.


****************❤


A ƙalla ta shafe sama da mintuna 30 tana zarya A cikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da I phone dinta, Yayin da idanuwanta ke kallon Haɗaɗɗiyar agogan bangon ɗakinta Ƙarfe 6 na marece, Lamarin Ya ɗaure mata kai, damuwa ce ƙarara akan fuskarta, Tun ɗazu da ta kammala Yin waya da Gimbiya mujeedat, Hankalinta ya dawo kan Mijinta, Ganin time ɗin dawowarshi daga aiki har Ya zarce babu shi babu alamar shi, saboda damuwar rashinsa ta manta da zancen Kiran Zahra, Hatta P.A dinsa Ta kira awaya ta tambaye shi ina pravin? Yace mata ai shi tun wuraren ƙarfe sha Biyu na safe rabon shi da pravin, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, hakan na nufin ko aiki baiyi a office ba, to ina Ya shiga? Tun ɗazu take kiran layin shi ba'a picking, abun duniya ya isheta, saboda ta damu da pravin tayi kewarshi sosai, bata tunanin ko abincin zata Iya ci idan bai dawo ba.


Guntun tsoki taja A fili ta furta"ya Salam, Ya Allah ga bawanka nan, Ka tsare min shi a duk Inda Yake, " ta ambaci hakan tare da jefa wayarta saman Gado, da sauri ta nufi tafkeken closet na kayansu ta buɗe ta ɗauki Mayafi ta Yafa a kafaɗa, tsabar sauri takalman da ta zura a ƙafarta daban daban, adai dai baƙin ƙofar fita daga ɗakin Suka yi kicibus da Twins Bakunansu ɗauke da sallama, Wankan suit ne a jikinsu, sun bi shape ɗinsu, Masha Allah, wrist watch dinsu mai Kyan gaske, Wani irin daddaɗan ƙamshi ke fita daga Jikinsu.


  Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba ganin mommyn nasu fuskarta babu walwala.


  Har suna haɗa baki wurin furta"Mom Lafiya? Meke damunki ne" girgiza kai Tayi"inafa lafiya, daddynku tun ƙarfe  shabiyu yabar office, har yanzu bai dawo ba, Na kira Layin shi wayar tana ringing ba'a ɗayawa.


  Atare suka kalli juna, babu alamun damuwa akan fuskokinsu.

  Kwantar mata da hankali suka soma Yi"mommy ki kwantar da hankalinki, daddy fa ba wani ƙaramin yaro bane da zaki tashi hankali akanshi, Yasan inda Yaje kuma zai dawo ne in sha Allah"


  Fuskarta babu walwala take dubansu"pls ku bani Hanya in wuce inaso Naje na faɗa ma baba" har suna haɗa baki wurin furta sunan baba


  "Haba Mommy, Akan wani dalili zaki je ki faɗa mashi? So kike ki tashi hankalin shi, Gaskiya a'a ki koma ki zauna, zamuje mu nemo daddy duk In da ya shiga"


  Ruƙo Hannunta Zayn yai, Suka koma Cikin ɗakin, Gefen gado ya zaunar da ita,


  "Zayn pls, Ku duba daddynku, Ni damuwata kada ace wani abunne ya same shi dama jiya ya faɗamin baya jin daɗin jikinshi" muryarta tamkar zata fashe da kuka ta yi masu maganar.


  Zaid Yace"in sha Allah ba abunda ya  same shi mommy, yanzu zamuje mu nemo shi" ya ambaci hakan Tare da ruƙo hannun ɗan uwansa suka fuce daga ɗakin.


Ransu ya 6aci matuƙa, daga gaban ƙofar ɗakin suka tsaya suna kallon juna

  "Mutumin nan ɗan rainin wayau ne, wlh Zaid zan tona mashi asiri awurin mommy, Ta ya ya zai bar mahaifiyarmu cikin damuwa, Yana can Yana sharholiyar shi, dama zuba mashi ido nakeyi ina tara shi...." duk yadda zaid yaso ya dakatar da Zayn Akan Yai shiru yaƙi rufe baki saida Yakai ƙarshen Aya


 "Ka daina ɗaga murya bro, Ni bawai ina goyan bayan abunda yake yi ba ne, just ka yi tunani mana, muddin ka tona ma daddy asiri wlh mu zaka ja ma bala'e, Kana ganin irin gorin da ake yi mana a family, akan mahaifinmu yana zama gidan surukansu Yanzu idan ka faɗama Mommy cewa daddy Yana bin matan banza me kake tunanin zai Biyo baya"?


Sassauta fushin fuskarshi Yai"Hakane Zaid amma abun Yana ƙona min rai, why ya ke son ja mana baƙin jini? Dame mommy ta rage shi da har yagaza kama mutuncin kansa, wai shi so yake dole saiya 6ata mana suna" tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla


 Ya ci gaba da cewa"Shine silar komai dake faruwa arayuwarmu, Zaid Ina kishin mahaifiyata sosai, Ina jin takaici da ƙululun baƙin Cikin mutumin nan,   wlh duk ranar da mommy taji labarin abunda Yake aikatawa tabbas zuciyarta zata Iya bugawa saboda tana da kishi kuma Tana son daddy, ni har kokwanto nakeyi anya daddy yana son mommy kuwa? Ko dai Abunda mutane suke hasashe akanshi gaskiya ne? ya aureta saboda dukiyar family dinmu' yana magana hawaye naci gaba da taruwa acikin idanuwanshi.


  Dafa kafaɗarshi Zaid Yai"duk abunda ka ke ji zayn nima inajin shi, Amma Ya zamuyi? Mu tamu ƙaddarar ahaka tazo mana, Muyi haƙuri wata rana sai labari Sannan Yakamata muna tayashi da addu'a akan Allah ya shirye shi, saboda shi mahaifinmu ne duk inda za'aje adawo mu jininsa ne kuma ba zamu so mutuncinsa ya zube a idon jama'a ba.


  Lallashin junansu su ka yi, Hannunsu ruƙe cikin na juna suka Nufi Babban falon gidan, masu aikine keta kai komo.


Suna dab da zasu fuce daga falon, Kwatsam Pravin Ya faɗo Sai faman zumbula sauri Yake Yi, Jikinshi sanye da Suit dinsa light brown, ƙiris Ya rage su ban gaji juna da shi, duk da faɗin ƙofar kasancewar Kowan nan su Hankalinshi ba a kwance yake ba

  Har zasu gifta shi, suka ci wani uban burki agabanshi, Tun daga Kan Yarda suke jefa mashi kallo yasa shi kame kanshi.


   "Har kun dawo daga aikin"? Tambayar daya jefa masu kenan.


   Zayn tamkar ya shaƙe baban nasu haka Yake ji, takaici Ya hana su yi magana.


   "Lafiya? Baku ji ina magana ba"? 

  Saida suka taushi zuciyoyinsu tukunna suka Iya yi mashi magana,


Zaid yace"Sannu da dawowa daddy, Ya office din? Naga yau ka yi marece ko duk Aikin ne ya ruƙe ka"? 


  Basarwa Yai tare da cewa"Eh, " daga haka bai ƙara tanka masu ba, Sai bi da yai ta gefen su Ya wuce, kamar sakarkaru haka suka Bi bayanshi da kallo, Sam baisan cewa sun san abunda yake aikatawa ba.


  Kusan atare suka girgiza kawunan su.


  "Zayn tunda Ya dawo mu koma ɗaki, dama Ni agajiye nake wlh, inaso na ɗan kwanta In huta"

Juyawa sukayi Atare suka nufi part dinsu.


Hajiya saratu na zaune gefe gadonta, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta Hannu biyu ta zabga uban tagumi, gabanta sai faɗuwa yake yi gani take yi kamar wani abunne Ya faru da mijinta, Kasa samun natsuwa tayi zumbur ta miƙe kamar an zungureta da sanda, safa da marwa taci gaba da yi acikin ɗakin tana ƙarewa agogon bango kallo.


Ba zato ba tsammani muryar Pravin ta ratsa kunnuwanta"Assalamu alaikum" tunkafin Ta juyo ta kalleshi ta soma sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar farin ciki da sauri ta nufeshi, hannu biyu ya rungumeta a ƙirjinsa.


  Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, yayin da take ƙara shaƙar ƙamashin turaren jikinsa.


  "Am sorry My wife, nasan ban kyauta maki ba...."tunkan Ya ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dago da fuskarta, babu annuri ko misƙala zarratin tuni yasha jinin jikinshi.


  Da kakkausar Murya ta furta"PRAVIN DAGA INA KAKE"!? Rass Yaji gabanshi Ya faɗi

  "Na kira p.A dinka Awaya ya sanar dani cewa tun ƙarfe 12 kabar office, Inason Jin ya akai kabar office ina kuma kaje"? Rai a6ace take Yi mashi magana, Hannunta ruƙe da qugunta.

   Ya tsareta da Ido batare daya furta kalma ba, hakan ba ƙaramin Ƙona mata rai ba, Tsawa ta daka mashi kamar mahaukaciya Ta cakumi Gaban rigarshi.


  "Nace ka faɗamin Ina kaje pravin? Saboda ka maidani shashasha ban da amfani awurinka shine zaka kama Hanya kabar office tun ƙarfe sha Biyu baka kirani awaya ka sanar dani ba, Kasa duk nabi na tashin hankalina akanka, ni na ɗaukama wani abunne ya same ka sai gashi ka dawomun lafiyarka qalou"


  Ƴan hanjin cikinsa tuni sun soma kaɗawa, Abunka ga shu'umin namijin wanda yasan takan mace, runtse idonshi yai tare da kai hannu ya dafe gefen cikinsa.


  Nan take Hankalinta yai matuƙar tashi la66anta na rawa take faɗin"pr...pravin? Lafiya? Meke damunka" 

   Da wata irin kasalalliyar murya ya furta"My stomach, bana jin daɗi ai tun Jiya na faɗa maki,"  ya ƙarasa maganar yana faman cizon la66ansa, lokaci ɗaya fushin fuskarta ya sassauto, tsananin tausayin shine Ya kamata, ganin yana tangal tangal kamar zai faɗi yasa tayi saurin talla6e waist ɗinsa, da taimakon ta suka ƙarasa gaban Gado Ya hau Ya kanta Yana fuskantar ceilling, daga gefen gadon ta zauna daga gefenshi tana kallon shi



  "Pravin am sorry nayi maka faɗa bansan baka da lafiya ba, kaine kaƙi Yi min magana, why pravin kasan baka da lafiya meyasa baka kira awaya ka sanar dani ba? Cikin kulawa take yi mashi magana, har ta manta da zancen tambayarshi Ina yaje.


  Wahalallan Yawu ya haɗiya, Cikin mawuyacin Hali Ya furta"wayar bata a hannuna ne a mota nabarta, Ina Cikin Yin draving zan dawo gida, Ciwon ciki Ya takura min, draving dinma na gagara Yi, shine na wuce gidan abokina dake anan kusa, to acan bacci ya kwashe ni, 


  "Pravin why baka je asibitin Gida ba? ai da komai yazo maka da sauki, yanzu ka tashi ka shirya In kaika asibiti da kaina inyaso sai in dubaka acan"


  Tana Ƙoƙarin miƙewa yai saurin fusgo hannunta, gaba ɗaya ta faɗa saman jikinsa, Ƙanƙame ta yai da hannayenshi biyu 


  Yana faman cizon le6e ya furta"rashin lafiyata bata asibiti bace, My wife kece kike damuna saboda rashin bani haƙƙina da bakya yi akai akai, shiyasa nake fama da ciwon cikin nan, ko da yaushe Aikinki ne agabanki, idan dare yai nayi maki magana kina danna laptop sai kice min In jira ki kammala daga nan har bacci ya ɗauke ni baki gama ba......"


Pravin Ya kashe mata Jiki da kalamansa, ta yarda da abunda ya faɗa mata saboda tasan bata kyauta mashi ta 6angaren nan mafi yawan time idan Ya matsa mata tana Yin aiki bata kula shi saita kammala.


   "Am sorry dear, indai nice zan gyara, kayi haƙuri nayi kuskure but bazan ƙara Ba, tun da abun Yana affecting dinka". Lumshe ido Yai, har cikin zuciyarshi ba ƙaramin daɗi Yaji ba, ganin yai nasara akanta.


    "Yanzu ka faɗamin me kakeso? Za ka yi wanka in taimaka? Ko zaka fara Cin abinci ne"


  Yana faman sakin nishi Ya furta"nafi buƙatar wankan, amma idan kin amince muyi atare"

  Murmushi tasakar mashi"is Okey, shine kaɗai abunda kakeso"? Ɗaga mata Gira yai alamar eh, A hankali ta ɗaura yatsun hannayenta saman coat din jikinsa Ta cire mashi ita, kafin ta zame mashi belt din wandonsa, yunƙura yai tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon Ya ƙarasa zame wandon ya rage daga shi sai short da singlet dinsa, Yaja hannunta suka nufi toilet, da gudu nabi bayansu sai dai kafin in ƙarasa Pravin Ya kulle ƙofa.


   EX-PRISONERS❤


Idan muka koma 6angaren Prisoners, sai dai muce Alhamdulillah, tun bayan da Dr laura davis ta tattauna da Sojoji bata ƙara Ji daga gare su ba, An dai samu damar Kammala Yi masu injections ɗinsu kuma kullum sai sunsha magani na safe daban na rana daban na dare daban, injection ɗin duk mutun ɗaya uku suke Yi mashi arana, Likitoci sun ci kwakwa Wurin ma Matan allura, Musamman Azeeza da Jamimah, mugun tsoron Allura su ke ji, idan za'ayi masu sai an kira Angel ta ruƙesu, tukunna ake samun sauƙin yi masu allurar, Mazan dai da sauki basu tsoron Allura tamkar basu son ana tsira masu ita a jikinsu ba, cikin kwanaki huɗu da su ka Yi a Texas Rayuwarsu ta fara canzawa, saboda kyakkyawar kulawar da suke samu tarairayarsu ake Yi kamar new born babies, abinci sau uku ake basu, Breakfast, lunch and dinner, Lafiyayyan abinci mai gina jiki, sau ɗaya ake sanyasu yin wanka, su canza Kayan Jikin su, Su Angel an dage da yin sallah da addu'a, har tsakar dare tana tashi yin night prayers, yawanci addu'o'inta akan Danish ne, ta roƙi Allah da ya kare mata shi, idan farkawarshi Alkhairi ce Allah Yasa ya tashi cikin amince, idan kuma farkawarshi ba Alkhairi bace Allah yasa yaita sharar baccina har zuwa su koma Nigeria zaifi masu sauƙin su Yi control dinshi, duk da yanzu ta fara fargaban kada su zo Nigeria A nemi Ruwan zam zam arasa tabbas ba ƙaramar matsala za'a samu ba, damuwarta yanzu akan Sojojin ce shiru basu dawo ba, Kuma bata Ji daga bakin dr laura Ya ake ciki ba, Shin za'a maidasu ƙasarsu ne ko kuwa a'a, Ta dai zubawa sarautar Allah Ido 👀


Sam ta kasa runtsawa, tun wuraren ƙarfe tara na dare ta farka, saboda mugun bugun da ƙirjinta ke yi mata, tabbas tana ji aranta wani abun ne ke shirin faruwa.

  Miƙewa Tayi zaune saman gadonta, ta jingina Bayanta Jikin pillow, idanuwanta suna a lumshe, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinta Yake yi wata irin kasala take Ji da matsanancin faɗuwae gaba.

   "Masoyiya Angel, Lafiya kika farka daga bacci? Na lura kamar wani abu ke damunki"

  Muryar Nurse Jessica ce ta fargar da ita, har saida ta ɗan zabura don bata yi tsammanin jin Muryar mutun a kusa da ita ba.

      Slowly ta wurga eye balls ɗinta akan fuskar nurse ɗin, tana daga zaune saman chair ta kusa da gadonta, hannunta ruƙe da wayarta, fara ce sol, uniform ɗin jikinta light blue ne kalar nasu, ta ɗaure jar sumar kanta da ribbom.

   Nauyayyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa"sister, nagode da kulawarki agareni, nakasa runtsawane saboda inason ganin yan uwana ko zaki Iya taimaka min"?

  Smiling gently nurse jessica tace"Na lura kina son ƴan uwan nan naki, cos tun ranar dana fara kula da ke, sau uku kike zuwa room ɗinsu Kina duba su, faɗamin ko dai akwai damuwane? Ko tsoro kike ji kada mu sace maki su"? Da zolaya nurce jessica tayi mata maganar

  Cikin jin kunya Angel takama ƴan kame kame tana faɗin"am.... Ba haka bane just inason su sosai, mun shaƙu da juna, shiyasa bana samun natsuwa idan ban gansu akai akai ba"


   Nurse jessice tace"Kuna burgeni sosai, inaso Inga ƴan uwan masu son junansu, masu haɗin kai, ta hakanne ake cin ribar zaman duniya, idan har kana da ɗan uwa mai share maka hawayenka, mai nuna maka ƙauna wanda baya gajiya dakai tabbas ka gode ma Allah, zai yi wuya ka rasa madafa a duniyar nan, babu wanda zai yi gigin cutar dakai muddin kuna da haɗin kai a tsakaninku, amma idan Ya kasance kuna ƴan uwa baku da haɗin kai, danasani zai biyo baya cos dayawa rashin kulawa keja har damuwa tayi ma ɗan uwanka Illa, ya akaita abunda zakuyi danasani gaba dayanku" 


  Angel ta natsu Tana sauraron Kalaman Nurse Jessica, Haƙika kalamanta sun ta6a mata zuciya, sai taji ta ƙara ƙaunar ƴan uwanta, ta ɗanyi mamakin yarda nurse ɗin take sakar mata fuska suke Yin fira, saboda ta ta6a Jin ana faɗin turawa sun tsani baƙar fata suna nuna masu wariyar launin fata, sai dai tayi tunanin ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, sannan kuma su basu da banbanci dasu, hasken fata, launin ido da kuma sumar kai, shiyasa suka zama ɗaya.


"Ki tashi muje in raka Ki ɗakunan ƴan uwan naki, Nima Inason ganin su, musamman twins ɗin nan" murmushine Ya bayyana akan fuskar Angel jin abunda nurse ɗin tace, tuntuni ta faɗa mata, ba twins bane Jamimah da azeeza ɗaya ta girma ɗaya amma taƙi yarda, ba ita kaɗai ba hatta sauran nurses ɗin da likitocin kallon twins suke Yi masu acewarsu Basu da banbanci, Komai nasu kala ɗaya.


  da zumuɗi Angel ta sauko daga saman gadon, light blue uniform ɗinta ne a jikinta, sai da ta fara zuwa gaban closet ɗin ɗakin ta buɗe ta ɗauko Hijabin da aka bata Nayin sallah ta zura a jikinta.


  Hannunsu ruƙe cikin na juna ita da nurse ɗin suka fito daga ɗakin, hasken electric bulbs Ya haskaka Asibitin tamar da rana, a tsanake suke Yin tafiya suna tattaunawa a tsakaninsu, ɗakin Gabriel suka Fara shiga, tayi mamakin ganinshi idon shi biyu Shida nurse rebecca, ta kunna masu kallo sun natsu abunsu.


  Jin motsin shigowar Mutun yasa suka kai eyes dinsu ga ƙofar, murmushi ne ya bayyana akan faces dinsu


  Mayar masu da martanin murmushin nasu Angel tayi"ɗan uwana, Baka Yi bacci ba? Fadamin meya hana ka Yin bacci"!

  Kafin Ya bata amsa nurse rebecca tace"Ni na hana shi, Ko bakisan mun fara soyayya bane, Gabriel baka faɗa mata ba"? Gaba daya suka sanya dariya, jessica tace"har kinyi kamu kenan" ɗaga mata gira tayi"yap, taya zan bari damar nan ta wuce ni"? Firarsu ba ƙaramin nishaɗi take sanyasu ba, Angel tuni ta haye saman gadon gabriel, Ruƙo hannunshi tayi acikin nata,

  "My sister, meya hana Ki yin bacci"? Ƙasa ƙasa da murya ta furta"Danish, Hankalina Yaƙi kwanciya da rashin farkawarshi, Yaufa kusan One week kenan a lissafina, Gabriel bansan ya zanyi ba, Ni nafi so Mu koma nigeria...."katse mata maganar yai da cewa"ai kin faɗamin dr laura tace zata taimaka mana mu koma can ko?


  Ɗaga mashi kai Tayi"eh, amma har yau shiru, banji daga gareta ba, Kuma kaga sojojin basu ƙara dawowa ba"


  Ganin kamar duk ta damu yasa shi kwantar mata da hankali"Wani jinkirin alkhairi ne Angel, wata'ƙil ki ga gobe anzo mana da kyakkyawan labari, don haka Mu ƙara haƙuri kada mu damu kanmu komai zai tafi dai dai My lovely sister" Yai magabar Tare da jan kumatunta da hannunshi, Hakan ba ƙaramin dariya Ya bata ba.


  "Masoyiya Angel, zamu Iya tafiya "? Muryar nurse Jessica ce ta katse masu tattaunawar tasu.


  Peck tayi mashi saman cheek dinsa"ka kwanta ka huta," ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadonshi ta nufi nurse jessice taja hannunta suke fuce bayan sunyi masu sallama.


  Room ɗin Batul suka shiga, A kwance suka same ta saman gado, ta ƙudundune da bargo, da alama tayi zurfi abaccinta, Basu shiga ɗakin ba suka wuce ɗakin Jemimah, Itama baccin take Yi, ta wawware ƙafafuwanta ta saki baki da hanci, nurse din dake kula da ita, Tana acikin ɗakin har gaisawa sukayi da ita kafin suka nufi ɗakin Azeeza, Kamar yarda suka samu jemimah haka suka sameta a kwance bacci yai daɗi, murmushi Angel tasaki kafin suka ƙara gaba zuwa ɗakin Parveen, Hallau dai mai hali Baya ta6a canzawa, bata Yi mamakin ganinta a zaune gefen gado ta tasa abinci saici take Yi, An kunna mata tv tana kallon mbc channel Suna Yin cartoon tom and jerry, Sai tiƙar dariya take Yi kamar zata kifa kanta saman table din gaban gadon, babu alamun bacci a idonta, sam bata ji motsin shigowarsu ba, plate ɗaya ne agabanta shaƙe da chicken wings, gefen plate ɗin kuma Apple juice ne, Duniya Ta yi mata daɗi, Gyaran muryar da Angel Tayi mata ne yai silar Jawo Hankalinta ga dubansu, bakinta cunkushe da nama ta furta "Angel"


 Nurse ɗin da suka zo atare da ita sai murmushi take saki, Da alama parveen ta burgeta, ba tun Yau ba, duk in tazo dubata sai ta sameta tana Cin abinci, da wuya ka same ta bakinta babu abun taunawa.


   Farin Cikine Ya bayyana akan fuskarta, Da sauri ta ƙarasa suka rungume juna ita da Angel.


  Shafa sumar kanta Tayi"Parveen kowa Yai bacci banda ke, kina nan kinata cin abinci Ko gajiya bakya yi, so kike ki karya masu jari ko"? Da zolaya tayi maganar, bayan ta raba jikinta daga na Angel, Just 4days Har kumatu ta ƙara.

   "Ai nurse ɗinne Yace min duk in ina buƙatar wani abu Inyi mashi magana..." zaro ido Angel Tayi hada ruƙe ha6a tace"Eyehh! Wato saboda yace maki haka shine kuma ko da wani lokaci sai kince mashi zaki ci abinci, Angaya maki nan Restaurant ne? You're a patient bai kamata aga kina cunkushe cunkushen abinci, kamar me fama da cutar Yunwa" sam Sun manta da nurse din da ke abayansu, Da turancin Angel Keyin maganar, hakan Yasa ta fahimtaci abunda suke tattaunawa, sai faman sakin murmushi take Yi tana binsu da kallo.


   "Angel ai su ba ruwansu, komai mutun yake so suna yi mashi, baki ga yarda nurse din Ya ke ji dani ba, Shine ma Ya kunna mun abun nan ba ƙaramin Daɗi naji ba" ta yi magana tana nuna mata plasma tv


    Watsa Hannu Angel Tayi"Okey, Koma Ki cigaba da cin abincinki, pls Ki samu ki kwanta ki huta, ki kula mun da kanki" murmushi parveen ta sakar mata


  "Thank u sis, Allah yabar mana Angel ɗinmu" Nurse jessica ta tsaresu da ido, gwanin ban sha'awa take kallon su

  Sallama sukayi Ma parveen bayan sun fito daga ɗakin suka nufi ɗakin Hannah, Yarinya ƴar madara, hankalinta kwance take sharar baccinta, Rabin jikinta duvet ne.


Bayan sun ƙara gaba ɗakin Naufal su ka shiga da ɗakin Javed, Kowan nan su bacci Yake Yi, daga ɗakin Javed suka nufi ɗakin Haris, Bawan Allah ba laifi Jiki Yai kyau, yana samun kulawa fiye da sauran ƴan uwanshi saboda lalurar shi.


  Sunyi tunanin bacci yake yi ganin shi kwance ya rufe idanuwanshi, Har sun Juya zasu fuce muryar shi ta katse masu hanzarinsu


  "Angel!" Atare suka Juyo suna kallonshi, Ya buɗe idanuwanshi da suke a lumshe, farin Cikine Ya lullu6e Angel, da sauri ta nufi gadon shi daga gefe ta haye, taimaka mashi tayi ya mike zaune, ta rungume shi a chest ɗinta, hannunta asaman bayanshi tana shafashi


  "Haris ɗina Ya jiki naka da sauƙi ko"? Muryar shi, ƙasa ƙasa Ya masa mata"da sauƙi Angel, bana jin ciwo a jikina sai dai har yanzu ina yin  mafarki akan Deejana, ina ganinta a prison suna azabtarmin da ita, tana kuka tana roƙona akan in taimaki rayuwarta' cikin rauni na murya yai maganar


   "Ka kwantar da hankalinka haris, Mafarki ba gaskiya bane, sau dayawa mafarki Shaidanne yake assasa shi, wani daga Allah ne wani mafarkin kuma ya danganta daga Yarda ka ƙwallafa abu aranka, shiyasa nace ka dage da yin addu'a, in sha Allah haris in dai Deeja tana araye zaku haɗu ne,"


Nurse ɗin ta zuba masu ido tana kallon su, bata san me suke tattaunawa ba a tsakaninsu, saboda sunyi amfani da harshen hausa.


   Still Haris bai ɗago kanshi daga saman chest ɗinta ba ji yake kamar deejanshi ce


   "Wlh Angel inason deejana, Kuma inayi mata addu'a, Ko yanzu da kika sameni na rufe idanuwana, addu'a nakeyi mata, Ni bazan ta6a gajiya dayima deeja addu'a ba, Har nunfashina na ƙarshe"


  Tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, (Ƙaunar dake a tsakanin haris da Deeja, daga Allah ne, irin son da ake kira true love, Inason ka kana so na badan wani abu ba❤ Allah Ya bamu masu sonmu tsakani da Allah🙏)


Shafa sumar kanshi Angel Ta yi da hannunta, Jin shessheƙar kukan shi Ba ƙaramin Karya mata zuciya yai ba


  "Haris pls don't cry, kasan bana son jin kukan ka, ko ba danni ba, nurse da ke kula dakai bazata Ji daɗi ba, Suna iyakar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun sanyaka farin ciki duk don ka rabu da ciwon zuciyar dake damunka" a hankali ya ɗago da kanshi Idanuwanshi sun ɗan kumbura.


   "Angel, nadaina bazan ƙara ba" tafin hannunta ta ɗaura saman fuskarshi tana share mashi hawayenshi


   "Zan tafi Yanzu nurse tana Jirana, Amma kafin nan kayi min murmushi mana" daƙyar ya ƙaƙaro murmushi kan fuskarshi, Hakanan taji gabanta Ya faɗi ƙura ido tayi akan face dinshi kamar tana son gano wani abu sai dai ta kasa gane menene shi.


  Ganin yadda take kallonshi yasa yace mata Lafiya Angel'? Girgiza mashi kai Tayi bakomai, ka kula mun dakanka, Sai Allah Yakaimu" daga haka ta sauko daga sama gadon, suka fice daga ɗakin shi ita da nurse jessica.

Last room da suka Nufa ɗakin Garkuwa, tunkafin su ƙarasa take Jin faɗuwar gabanta na ƙaruwa, ji take yi kamar idan ta shiga ɗakin wani abu zai faru, Da bismillah abakinta ta kutsa kai dakin nurse jessica tabi Bayanta, kamar matacce haka suka same shi kamar kullum Sai sharar baccin shi Ya ke yi, Lamarin Danish ba ƙaramin ɗaurewa likitoci kai Yai ba, tsawon kwanaki mutun Yana yin bacci yaƙi tashi? Tun abun na damunsu har sun haƙura sun zubawa sarautar Allah ido.


  Saman chair nurse ta zauna idonta akan face din Danish


   A hankali Angel ta zauna gefenshi Tana ƙare mashi kallo, Ji take yi tamkar ta fasa ihu acikin kunnuwanshi wata'ƙil idan Yaji zai farka, sai da tasan ko Tayi abanza, Allah shine shaidarta, ta matsu a ƙagare take da son farkawarshi kamar ta yi hauka

 Sam ta manta da nurse dake a ɗakin, ta natsu tana kallon shi kamar zata Haɗiye shi, A hankali Ta ɗaura small pink lips ɗinta farar fatar cheek dinsa ta manna ma kiss.


  Murmushin gefen fuska nurse jessy ta dan saki, abun ba ƙaramin ƙayatar da ita yai ba, kamar ta samu tv haka take kallonsu.


  A hankali Angel ta kwantar da kanta saman faffaɗan chest dinshi ta kasa kunne tana sauraran heart beat dinsa


   Muryarta cikin raɗa take Yin magana"My man pls wake up, nayi kewarka kamar zan zauce, dan Allah ka taimaki rayuwana ka farka danish, a matse nake duk na takura da rashinka, pls idan kana Jina Ka amsa min" hauka ta soma yi mashi asaman jikinsa tabi duk ta hayeshi, shessheƙar kuka tadinga yi mashi duk don ya farka sam babu hawaye akan face dinta, ɗagowa tayi da kanta, gray eyes dinta akan fine face nasa, eyes lashes dinsa ta ƙurawa ido masu kyau da tsari.


  Bakomai take tunawa ba face Farkon haɗuwarsu a prison, a karo na farko da Ta yi tozali dashi saida gabanta Ya faɗi saboda zazzafan Kyanshi, Murmushi tasaki tunawa da maganar farko data fara haɗasu lokacin da tana zazzaga masu masifa akan afaɗa mata ubanwa ya kawota prison

 Muryarshi ta ratsa kunnanta, tamkar ana busa sarewa

   "Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!" a lokacin takai maƙura A zafafe Ta juyo ta kalle shi tsabar mamaki tamkar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, duk da bugun da zuciyarta tayi mata na ganin kyanshi hakan bai hanata zazzaga mashi masifa ba.


   "Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!"


  Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, Rayuwa kenan, Idan mutun ya kasance ƙaddararka baka isa ka canza shi ba, bata ta6a tunanin zasu sasanta tsakaninsu ba, saboda rashin jituwarsu sai gashi a yanzu sun shaƙu da junansu ita da sauran ƴan uwanta prisoners.


    Nurse Jessica Har tafara Gajiya da zama bacci na shirin kwasarta a saman kujera, sam batason ta katse Angel donta fahimci ba ƙaramin so take Yiwa ɗan uwan nata ba, duba da yadda ta haye saman jikinshi tana sambatu hada murmushi da dariya.


      Soft lips ɗinsa ta ƙurawa ido tamkar anyi mixing din launinsu da pink


  "Masoyiya Angel Yakamata mu koma ɗaki ko"? Muryar Nurse jessica ce ta fargar da ita, Amsa mata Tayi da toh Kafin ta miƙe ta ɗan dukar da kanta saitin fuskarshi sumar kanta ta yi mashi rumfa, A hankali ta ɗaura small mouth ɗinta saman Forehead dinsa Da Niyar ta manna mashi peck ba zato ba tsammani taji ya damƙi waist dinsa ruƙo bana wasa ba, Agigice Take kallon face dinsa wani abun mamaki bai farka daga baccin ba, tashin hankalin da ba'a sama shi data, Nan take Jikinta Ya hau Yin kakarwa ido Ya raina fata, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata ta cikin hudar gashin jikinta.......


  



Boss Bature✍ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin




First bank




3196407426, 




Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post