Kurkukun Kaddara Book 2 Page 36

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 36

Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*

Idan muka koma 6angaren Hajiya saratu data garƙame kanta acikin toilet, tsoro da fargaba sun hana ta sukuni, ta haɗa uban gumi zufa ta ko'ina take tsastsafo mata, ga wani takurarran bacci daya addabi idanuwanta, ta rasa ya za ta yi, ta kasa tsaye takasa zaune, sai zarya take yi acikin toilet, jin shiru tsit babu sautin komai daga waje hakan yasa tayi tsammanin ko dai jami'an sun kashe macijin ne, cikin sanɗa take yin tafiya tana tunkarar toilet door, ta ruƙo handle din ƙofar ta buɗeta, shigowa ɗaki tayi ta nufi wayarta dake ajiye saman bedside drawer takai hannu ta ɗauke ta tana ƴa waige waige duk tabi ta ruɗe.
  Layin pravin ta danna ma kira, kusan sau uku bai ɗaga ba, hankalinta ashe take fadin"pravin ka ɗaga kirana mana" Sake kiran layin tayi, a lokacin da kiran ya shigo mashi yana a kwance saman shimfiɗeɗɗan gadon hajjaty, sleeping dress ne ajikinta, shi kuma shorts ne babu riga, ya rungumeta a kirjinshi, sun manne ma juna, duvet din daya lullu6a masu iya saitin kafaɗunsu ya tsaya.


Bacci ya ƙaura ce ma idanuwan hajjaty, tun da tayi tozali da narkekan macijin nan, lallashinta yake yi duk don ya samu ta kwantar da hankalinta.


   "Pravin wayarka fa tana ringing yakamata ka duba me kiranka"


 "Nasan wa ke kira na, bai wuci hajiya saratu bace, ta gama ci min mutunci shine yanzu take kirana saboda ta tsorata da ganin maciji, wallahi ba zan je ba, nafi so taji a jikin ta" 


 Muryar hajjaty ƙasa ƙasa tamkar me yi mashi raɗa ta furta"please, matarka  ce, yakamata kana darajata"


  "Ni ma ai batasan darajata ba, saratu bata girmamani, tayi min gori ta gaya min maganganun da suka ƙona min rai, sauƙin ma ba ita ka ɗai bace Ina dake"


  Lumshe mashi ido hajjaty tayi, 

Yaci gaba da cewa"kina ƙaunata tsakani da Allah, baki ta6a guduna ba, kin rabu da kowa naki kin biyoni Nigeria, a zaman da mukayi dake ni baki ta6a yi min laifi ba..." ƙayataccen murmushi tasakar mashi.


"Ina fata kai ma ba zaka ta6a guduna ba, Kuma ba zaka ta6a yi min laifi ba, pravin bani da kowa a halin yanzu Allah ne gatana sai kuma kai, dan Allah ka ruƙe min amana kada ka aikata abun da zaiyi silar rabuwar mu, ka ji tsoron Allah a dukkan lamuranka na rayuwa, idan kana tunawa da mutuwa zaka ƙara jin tsoron Allah, bana so wata rana muyi abun da zamu yi danasani arayuwarmu..."


Bai bari ta ƙare maganar ba yai hanzarin katse ta"my woman, bansan yaushe kika fara yin wa'azi ba, idan ban manta ba, Ni ne na koya maki alwala ko" 


 Dariya ta saki jin abunda pravin yace, kafin ta ƙara cewa wani abu ya rigata fadin"muyi bacci please dare yana ƙara nutsawa" da shagwa6a hajjaty tace"ni dai ka tafi ɗakin matar ka, ita yakamata ace kana atare da ita bani ba"


 "Bana so in bar ki ne saboda na lura haryanzu jikin ki bai daina kerma ba"


"Amma itama saratun ai tsoron take ji, tana buƙatarka agefenta, pls ka tafi wajenta, Ni nafiso kana kamanta adalci a tsakanin..." bai bari ta ƙare maganar ba, yai saurin haɗe bakinsu, ya zura hannayenshi biyu cikin rigar baccin jikinta, sarrafata ya soma yi cikin ƙanƙanin lokaci ya fara caza mata kai, yayi mata hakanne don ya mantar da ita zancen tafiyar da take yi mashi, kuma yaci galaba akanta, bai rabu da ita ba har saida yaji ta fara yin bacci tukunna ya ƙanƙameta.


   Phone dinsa sai ringing take yi, tana daga can gefe daya saman mattress din, a hankali ya raba jikinsa daga nata.


    Ya laluba hannu ya damƙo wayar, murmushin mugunta ya saki kafin ya ɗaga kiran.


 Ko sallama babu hajiya saratu tace"pravin ina ka shiga? Ina ta kira baka picking! Ba zaka dawo daki ka kwanta ba ne"?


 Tun daga kan muryarta ya fahimci babu natsuwa atare da ita

  "Me zan dawo nayi maki? Ni da bani da amfani awajenki"?

 Muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace'kaga ni ba wannan na tambayeka ba, ina son ganinka ka, pravin, hankalina ba akwance yake ba, nasan kaga abunda ya faru ɗazu"


 Tuntsirewa yayi da dariyar mugunta, ran hajiya saratu ya 6aci matuƙar masifa ta soma zazzaga mashi sai da tayi mai isarta tukunna ya katse ta da cewa"saratu kenan, kefa da kanki kikace nine ɗan kwali ke ce hula, hakan na nufin kece namiji ko? To meyasa kike neman mace donta baki kariya? A tunanina ni yakamata inji tsoro bake ba, shi namiji da jarumta aka san shi bada ragwantaka ba"!


 Takaicin duniya ya ishi hajiya saratu, cikin lalama tace"pravin dan Allah ka dawo ɗaki, idan saboda abun da na fada maka ne ya 6ata maka rai, zan baka haƙuri"


 "Bana buƙatar haƙurin ki saratu, lokacin daya dace ki lallasheni ki tarairayeni ki bani hakuri bakiyi ba till now da buƙatar kan ki ce ko? An gaya maki ni shashashane bansan ciwon kaina ba"?


  Shiru bata tanka mashi ba, kuma tana sauraronshi.


  "Ko gobe kada kiyi tunanin zan dawo gida, ni yanzu haka ma gani akwance tare da wadda tafi ki iya tarairayar miji....."tsawar da ta daka mashi ce ta sanya shi yin shiru, tamkar zata fasa mashi screen din wayarshi"ya isa haka!  Ya isa! Kada ka ƙara maimaita min maganar da kayi idan ba so kake ranka ya 6aci ba......" bata ƙare maganar ba, yai rejecting kiran, Ya jefar da wayar saman mattress, Ya janyo hajjaty a jikinshi, ya daura hannunshi saman sumar kanta, har cikin ranshi yana ƙara jin ƙaunarta, bai da tamkarta a duniyar nan, saboda kyautata mashin da take Yi, yana matuƙar ƙaunarta, kiss ya manna mata saman forehead nata, kafin ya cusa kanshi gefen wuyanta, ƙamshin turarenta ya daki hancinsa ahaka bacci yai awon gaba da shi.


Jefar da wayar hannunta tayi saman gado, ranta ya 6aci matuƙa pravin ya ƙona mata rai, kishine da ita, gani take kamar dagaske ne abun da ya faɗa mata yana can shida wata suna sheƙe ayarsu, kokwanton maganarshi take Yi, ta riga ta yarda da pravin tasan bazai Iya cin amanarta ba, wata'kil ya faɗa mata hakanne don ya huce raɗaɗin abunda tayi mashi.


   Damuwace ƙarara akan fuskar hajiya saratu, adaddafe ta nufi gado ta haye ta kwanta idanuwanta suna fuskantar ceilling, babu alamun zata runtsa adaren Yau.*Hajiya Turai💔*Safa da marwa take Yi acikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da wayarta, night gown ce a jikinta.


  Fuskarta tayi jawur tamkar wadda tasha kuka, musamman kumatuntu, green eyes dinta kuwa sun ciza launinsu, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, since wuraren ƙarfe goma take kiran layin dr.jazz babu alamun zai ɗaga, gashi har dare ya nutsa bai dawo gida ba, ta kira layin Sir mubarak kusan sau talatin shima Bai daga ba tamkar ta fasa ihu haka take ji.


     "Mom" kamar daga sama taji an ambaci sunanta, tsabar ruɗi sai taji kamar muryar jazz ne.


 A firgice ta juyo don ganin wanene, Yana daga tsaye bakin ƙofar ɗaki, cikin shiga ta kayan bacci ya zura hannayenshi cikin aljihun wandonshi, matashin saurayi ne kamanninshi sak dana Sir mubarak.


   "Ibad kai ma baka yi bacci ba"? Muryarshi da kalasa ya furta" How can I sleep, Mom? Jazz hasn't come home yet. na jaraba kiran layukan wayarsu duk akashe, bansani ba shi jazz ko aikin kwana yake yi a asibiti, nazo ne naji ko sun faɗa maki meya hana su dawowa gida"?


  Ta lura da yanayin shi tsantsar damuwace akan face dinsa, batayi mamaki ba saboda ƙaunar da suke yi ma Jazz, sun dauke shi tamkar shaƙiƙinsu


 "Ibad, I don't know why they haven't come home yet, I've been trying their phones since 10 o'clock, and nobody is picking up. I'm really worried, inajin fargabar ace wani abun ne ya faru da su" tuni idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla.


   Ruƙo hannunta Ibad yai"haba mommy, kada ki zubda hawayenki please, ki kwantar da hankalin ki, Everything is going to be okay. They'll come home safely."


girgiza mashi kai tai"basu ta6a yi min haka ba ibad, daga jazz din har daddyn naku, kullum ne idan zasu kai dare awaje, sai sun kira awaya sun faɗa min, amma yau shiru babu wanda ya tuntu6eni" muryarta na rawa ta furta maganar, tausayinta duk ya kama ibad, jinta yake yi tamkar mahaifiyarsu data rasu.


  Gyaran muryar da akayi masu ne Ya janyo hankulansu ga duban shi, tafiya yake yi yana tunkarosu tamkar baisan da su ba, Hannun shi ruƙe da apple laptop dinshi, daga shi sai short a jikinshi, Ƙirar jikinshi da komai kalar na daddynsu ne, sai dai shi yafi ibad da daddynsu hasken fata nashi chocolate colour ne mai kyan gaske, sumar kanshi tasha gyara luf ta kwanta saman bayanshi, Yana da kirar karfi kamar ɗan wrestling, wani irin daddaɗan kamshin turarene ke fita sako da lungu na jikinshi, komai nashi da aji yake yin shi, mutunne shi maiji da kanshi, baida wasa a aikinshi, yana ruƙe da muƙamin CEO na babban Companynsu dake a ƙasar canada.


Kafafuwanshi suna asanye da slippers, magana ya somayi tamkar baisan furtata


  "Mom, yanzu major ya kira ni awaya, ya fadamin suna atare da jazz wani aiki ne mai muhimmanci ya tsayar da su, so they couldn't come home tonight. But they'll be back early tomorrow"


  Ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta taji dadin jin hakan, Murmushi Ibad ya saki yana fadin"mun samu nutsuwa yanzu, Mom ki koma daki ki kwanta,    ƙarfe 3 fa ta buga, gobe nasan zakiyi ramuwar bacci, murmushi tasakar mashi"bari na koma ciki, mu kwana lafiya My Sons," ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakinta, saman gado ta haye idanuwanta suna fuskantar ceilling, bakomai take jimawa ba face kwanan da za ta yi ba tare da mijinta ba, sun saba faranta ma junansu kafin su runtsa yau kuma babu shi atare da ita, ga kuma ɗanta da take jin kewarshi,

 Pillow ta janyo ta rungume a ƙirjinta.     "Babban yaya nan fa ba kasar canada bace, taya zaka dinga yi mana yawo da short a tsakar falo? Kai ala dole ga bature ko? Ko kunyar mommy baka ji," Ibad ne ya fada da zolaya. Ko kallo bai ishe shi ba, saman Sofa mai mazaunin mutun uku ya kishingiɗa kanshi saman sofa hand, Ya daura laptop dinsa saman flat stomach dinsa.


  In a husky voice ya furta"ibad! Ina buƙatar abun sha" 


  Ruƙe qugu Ibad yai sam baya gajiya da zolayar yayan nashi duk da tazarar shekarun dake atsakaninsu, domin kuwa Zaki ba ƙaramin mutun bane


"nan fa ba canada bace, Nigeria ce daddy Ya hana ana aikena idan dare yayi" yamutsa fuska Zaki Yai Ibad ya fara hayaƙa shi.


  Calmly ya furta"Don't make me repeat myself" kama kunne ibad yai"sorry big bro, na tuna kada ka hanani silallan kashewa" ya fada tare da nufar frigde Ya bude ya dauko mashi coke mai sanyi, ya dawo Ya daura mashi saman sofa table din gabanshi.  "Babban yaya gashi na kawo, Ni zan cire maka murfin?" banza yai mashi tamkar baiji me yace ba.


 Bottle opener yaje ya dauko ya zuƙunna agaban table din Ya soma kiciniyar bude murfin, sai nishi yake yi, sam bai saba da wahala ba, ibad mugun sangartacce ne yayanshi ya 6ata shi da hutu, dogon tsoki zaki Yaja, ya yunkura ya miƙe Ya ajiye laptop din gefe ɗaya, ya kai hannu ya kar6e coke din da bottle opener din, sau ɗaya ya murɗa murfin ya cire.


  Washe baki Ibad Yai"babban yaya ba za ka yi bacci ba? kana buƙatar hutu fa, kai kullum aiki baka gajiya"!


 Banza yai dashi baice komai ba, a tsanake yake kur6ar coke din me sanyi, Ibad ya ƙura mashi ido yana kallon bakinsa har haɗiyar yawu yake yi.


 Janye coke din yai daga bakinshi, Ya galla mashi harara"meyasa kake kallona kana haɗiyar yawu kamar wani maye? Idan so kake kasha bakasan inda zaka dauko bane"


 Kwa6e mashi fuska ibad yai"Ai ni nafi so kasha ka rage min"


  Sakin baki yai galala yana dubanshi"oh dole sai na baka ragowa na zaka sha" ɗaga mashi gira yai alamar eh.


  Babu musu Ya miƙa mashi, don ya san rigimar ibad idan har ba bashi ragowar yai ba to kuwa zasu kwana azaune"


  Yana sha yana kallon fuskar Zaki, aiku sarkin ɗumi.


  "Big bro, where's my sister pretty ? You told me she came back to Nigeria. When can we see her? Should we go to their house, or will she come to ours? (Babban yaya Ina sister pretty dina? Ba ka ce min ta dawo Nigeria ba, to yaushe zamu haɗu da ita? mu zamuje gidansu ko ita zata zo gidanmu?)


  Dafe kanshi yai da hannu ɗaya"Ibad, I don't like making noise, Please go to your room, lie down on your bed, and  sleep."


    "Shikenan zanje na kwanta amma kafin nan inaso ka fadamin gaskiya, dagaske babu soyayya atsakaninku"?


 Ji yake tamkar ya dauki laptop din gefenshi Ya kwalama ibad saman kanshi, Ya takura mashi.


  "Ka yi shiru bakace min komai ba"!


  Miƙewa zaki yai ya dauki laptop dinsa Ya nufi sashen bedroom dinsu, da sauri Ibad Yabi bayanshi, har yakusa shiga dakin ya ɗan dakata da yin tafiyar, in a cool voice ya soma magana


  "Ibad, she is married and even has a daughter, And she loves her husband. But there is no love between me and her. taimakon da nayi mata dan Allah nayi shi"


  Da mamaki Ibad yace"babban yaya kana nufin duk tsawon shekarun data dauka a canada a gidanka, da auranta? To ya akai ta gudu tabar mijinta da ƴarta? kuma take rayuwa agidanmu harma kuke rungume juna ai ina ganinku idan kuna shan soyayya...." kafin ya ƙare maganar, afusace zaki ya waiwayo da niyar ya kwaɗa mashi laptop din hannunshi da gudu Ibad Yabar wajen yana dariya.


  Guntun tsoki Zaki Yaja, Ya faɗa katafaren room dinsa, saman gadonshi ya kwanta, haɗi da daura laptop dinshi on his broad chest, hoton fuskarta dake akan wallpaper din laptop nasa ya ƙurawa ido yana kallonta, bazai Iya misalta ƙaunarta da yake ji ba, yana sonta baya jin zai iya son wata ƴa mace aduniyarnan kamar yadda yaso baiwar Allahn nan, sun rayu na tsawon shekaru tamkar ma'aurata rana ɗaya Allah ya ƙaddara rabuwarsu, yana fatan sake haɗuwa da ita, da tunaninta bacci yai awon gaba da shi.*ANEELERH❤*
Kiran sallar asubar farko, ringing din wayarta ya daki kunnanta, firgigit ta farka daga bacci tana faman sauke ajiyar zuciya, yayin da la66anta ke ambaton sunan baby junaid, mafarkin da tayi da shi ya ɗaga mata hankali, a ruɗe ta mike zaune, rigar baccin jikinta duk ta yamutse, haka zalika sumar kanta a hautsine take.


    Daukar wayar tayi dake ajiye gefenta, ta duba me kiranta, missed calls ta gani sun kai biyar na hajiya adama, aranta ta ayyana Allah yasa ba mafarkin da tayi bane ya zama gaske.


  Bin kiran tayi nan take kiran ya shiga, bugu uku kafin hajiya adama ta ɗaga.


  "Assalamu alaikum, daughter in-law, fatan dai ban katse maki baccin ki ba" da buɗar bakin Aneelerh sai cewa tayi"mommy ina junaid"

 Sautin dariyar hajiya adama ne ya fargar da ita, da sauri ta dafe baki tamkar tana agabanta tace"au...namanta ban gaishe ki ba, ina kwana mommy"


   "Lafiya lou Aneelerh, lallai yau na shaida kin ƙosa kiga ɗanki, tun da gashi har kin fara ambaton sunan shi tunkafin ki gaishe ni" 


  Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace"ba haka bane mommy, daga bacci na tashi bansan Na ambaci sunanshi ba"


  Hajiya adama tace"oh am sorry na tada ki daga bacci tun da asubahi, agafarce ni, jikana ne ya takura min akan in kira mashi ke awaya, yaban mamaki da sunanki Ya farka yanata kuka yana fadin wurin mommy zaije shine nace bari na kiraki kuyi magana wata'ƙil hankalinshi zai kwanta, kafin mu shigo gidan zuwa anjima in sha Allah"


   Hankalin Aneelerh yaɗan tashi jin abun da mommy adama tace, aranta ta ayyana kodai shima yayi kalar mafarkin da tayi da shi ne?


  "Aneelerh kinyi shiru, ga shi ku gaisawa" muryarta adabarbace tace"toh mommy" 


   Sautin kukan baby junaid ne ya cika mata kunnanta, murmushi tasaki tana fadin"My baby boy, ba hello ba hi sai kuka? So kake hankalina Ya tashi ko"?


   Cikin shessheƙar kuka yace"mom..my wallahi kizo ki ɗoke ni, idan ba haka ba bazaki sake gani na ba, mutuwa ma zanyi" rass taji gabanta ya fadi,


  "Junaid kadaina ambaton mun mutuwa, banaso, idan wani abu ke damunka ka faɗamin mana!" aɗan tsawace ta furta mashi maganar, tunawa da hajiya adama yasa ta sassauta muryarta,

  "My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, Yau in sha Allah mommy adama zata dawo min da kai"


 Tsagaitawa yai da yin kukan, Muryarshi da shagwa6a yace"Ai ni tsoro nake ji, bana son zama agidansu...." bai ƙare maganar ba tayi sauri furta"shiru! Agaban mommy adaman kake fadin haka"?


  "A'a mommy, ba agabanta bane, ai ta fita daga dakin"


 Ajiyar zuciya ta sauke"yanzu fada min me ke baka tsoro? Ko wanine yake bugunka"?


  "A'a mommy, idan ina bacci, sai ina ganin wani mutun sanye da baƙaƙen kaya hannun shi ruƙe da ɗan kwano, kalar wannan abun na ɗakin mami, wanda ake zuba fura a cikin shi, hannun shi zaƙo zaƙo da akaifu kalar na Ana mai girka mana abinci, wai yake ce min inzo mu tafi" zaro ido waje aneelerh tayi"Junaid ka natsu kayi min bayani, a mafarki kake ganin shi ko kuwa a zarihi? Kai kaɗai ka ke kwana aɗaki idan dare yayi"


  "Ni ba mafarki nake yi ba, dagaske nake ganin shi, kuma a ɗakinsu nake kwana" aneelerh duk tabi ta ruɗe.


  "Junaid kaji tsoron Allah, ka faɗamin gaskiya, nasanka da ƙarya, Idan baka fada ba, to bazan baka zoben Angel ba"


  "Kin siyane"? Ƙumshe dariya tayi don tundaga kan yadda ya tambayeta ranta ya bata cewar ƙarya ya shirga mata.


 "Na siya mana, ai jiya naba mahboob kuɗi Ya siya maka zoben mai kyan gaske"


  Tuntsirewa yayi da dariya yana fadin"to mommy wasa nake yi maki, wallahi dama awani cartoon ne da muke kallo a tv, anan naga mutumin" fashewa tayi da dariya sosai har fararen haƙoranta suka bayyana"yanzu naji magana ɗan rainin wayau, duk kabi ka tasar min da hankalina, Yau har mafarkin ka nayi saboda nayi kewarka babyn mommy, ina sonka Yarona"


  Yace"nima inasonki mommyn baby" dariya tasaki, idan yana yi mata magana kamar wani babban mutun daya mallaki hankalin shi, sai idan yayi wata kwa6ar ne zaka gane ƙaramin yaro ne.


     "Mommy ina mamina? da abie, da uncle mai ƙaton hanci, da mahboob mai son kuɗi, da zahrah mai dogon wuya" 


  Tsabar yadda take yin dariya hada dafe ciki,

  "Junaid baka da mutunci, Uncle dinne mai ƙaton hanci"!

 Kaitsaye yace mata"eh mana, baida kyau Allah, mummuna ne uncle dan Iya, ni naji dadi ma bashine daddynki ba, da wallahi bazanyi kyau ba" 


  Mamaki ne ya kama Aneeleerh, jin yadda yake kushe mata kawunta.


 "Junaid dan Allah ka yi shiru kada wani yaji ka, Ni zan ajiye wayar, ka koma bacci zuwa anjima Mommy adama zatayi maka wanka ta shiryaka sannan zata dawo mun dakai gida, fadamin me kake so in tanadar maka"?


Da shagwa6a yace"fura nakesho, asanya kwakwa da yoghurt aciki" bakomai ya tuna mata ba face Angel, tana son furar da aka sanya kwakwa da youghurt, kusan kullun idan tazo gidansu sai ta sanya Aneelerh ta haɗa mata ita, musamman saboda Angel take ajiye damarmar fura cikin robabi ta sanya mata su a frigde don su yi sanyi.


  Tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, Muryarta na rawa ta furta"zan ajiye maka my baby boy, ka kwanta ka huta zuwa anjima zamuga juna" daƙyar ta samu baby junaid Ya ƙyaleta, badan ta gaji dashi ba, ta ajiye wayar on pillow, ta sauko daga saman gadon, A hankali take bin bedroom dinta da kallo, har idonta ya sauka akan hotonsu da ta liƙa shi a bango, wanda sukayi tare da aminnanta, su uku abunsu, kowacce ta ca6a uban adon lace, fuskokinsu ɗauke da murmushi.

  

Ta natsu tana kallon hotunansu, sam ba ta ji takun tafiyar mutun ba, har ta ƙaraso gefenta ta tsaya, Ƙamshin turaren zahra ne yaja hankalinta ga dubanta, tayi mamakin ganinta a ɗakinta, tun ranar da abunnan ya faru na hajiya falmata ko magana bata ƙara haɗa su ba, amma yau sai gashi ta tako ta shigo room dinta, dogon hijabi ne a jikinta daga ƙasa har sama launin maroon hannayenta biyu ta fiddo dasu ta cikin hannun abayar, hada cazbaha ta ruƙe tana ja kamar wata matan limam.


"Aunty Aneelerh Ina kwana, kin tashi lafiya"?


  Daƙyar ta iya amsa mata da lafiyalou, ina fata kema haka"

Daga mata kai tayi alamar eh, idanuwanta sam basa akan Aneelerh suna akan hoton da take kallo, wani irin kunyarta take ji, tunawa da rashin mutuncin da tayi mata akan ta bata shawarar ta ba Hajiya falmata haɗin kai, tayi danasani tun jiya da Mahboob Ya fayyace mata komai.


"Nayi mamakin ganinki a ɗakina zahra, ai nayi tunanin mun rabu kenan har abada"


  Girgiza kai zahra tayi"Idan kinga mun rabu to mutuwace ta raba"


  Aneelerh sam batasan Mahboob ya fada ma zahra ba, bayan ta gargade shi akan karya gaya mata, shi kuma bayason suna gaba atsakaninsu, don ya fahimci zahra ta fusata sosai, Idan har bai fada mata gaskiya ba to kuwa zata cigaba da zabga ma Aneeleeh rashin mutunci abisa rashin sani shiyasa ya yanke shawarar ƙwara ya faɗa mata, don ta yi takatsantsan kada ta wuce gona da iri azo aji kunya.


"Kiyi haƙuri da abunda Ya faru atsakanin mu, nasan na 6ata maki rai, tuntuni nake taso in nemi yafiyarki, sai dai baki bani damar yin hakan ba" Aneelerh ce tayi maganar tana duban zahra.


  Cikin sanyin murya zahra tace"ni yakamata nabaki hakuri auntyna bake ba, saboda ni ce mai laifi, ban kyauta maki ba, duk irin shaƙuwarmu da kyautatamin da kike yi amma nagaza fahimtarki, har takai takawo ina zarginki, maimakon na kyautata maki zato, wallahi naji kunya, daren Jiya daƙyar na runtsa tsabar takaici, Ƴan kwanakin da muka samu sa6ani atsakaninmu aunty Aneelerh naji jiki ba kaɗanba, na ƙuntata, na gane mahimmancinki agareni, Ina da abubuwa dayawa da suka faru wadanda nakeso in samu abokin firar da zangayama wa ya tayani farin ciki sai dai kash babu, ke kaɗai ce nake jin dadin tattaunawa dake akan duk wani abu daya shafi rayuwata saboda nasan zaki ƙarfafa min gwiwa ki kuma bani shawarar da zata amfane ni...." zafafan hawayene suka wanke fuskar Zahra, tuni idanuwanta sun kaɗa jawur da su.


 "Meyasa banyi dogon nazari ba akan shawarar da kika bani"? 


 Zuciyar aneelerh ba ƙaramar karaya tayi ba"zarah! Mahboob Ya fada maki ne"?


 Jinjina kai tayi"ƙwarai kuwa ya fadamin komai, har gargaɗi na yayi akan kada na nuna na sani, saboda kince mashi kada ya gaya min, shi kuma a ganinshi bai kamata ki zubda mutuncinki a idanuwana ba, saboda ku rufa ma hajiya falmata asiri awurina, don in cigaba da ganin darajarta, hakan kuma bazai ta6a yiwuwa ba, saboda shi mutunci madarane idan ya zube baya kwasuwa, sai dai naji dadi da ke  kika yi silar shiriyarta, ke din ta dabance Auntyna"


  Rungume Aneelerh tayi, atare suka fashe da kukan farin ciki, yau sun shirya da juna, babu wanda baiji jiki ba acikinsu.


  Bubbuga bayanta Aneelerh tayi da hannunta Cikin shessheƙar kuka take fadin"komai ya wuce zahra, abunda ya faru laifina ne dana baki shawarar banza duk da ko a lokacin bawai zan zuba maki ido bane don ina jarabaki ne nayi hakan, wallahi duk wani motsinki atafin hannuna, tun bayan dana baki shawarar, fargabana kada ki amince da shawarata ki kama hanya ki tafi kai mata kanki, shiyasa na sanya maki ido, akarshe na yanke shawarar zuwa gidanta don in gargadeta akan ta fita sabgarki, Cikin Ikon Allah sai gashi na 6uge da yi mata nasiha, ashe nice silar shiriyarta, naci ribar jarabawar da nayi maki zahra, Naji dadi kuma nayi farin cikin samun ƴar uwa mai tawakkali irinki, zan iya cewa duk namijin daya mallaki mace irinki yayi nasara sai dai fatan ya cika da imani"


  Dariyar farin ciki zahra tasaki, tare da dago dakanta daga jikin Aneelerh

  "Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya saboda babu su auntyna, Ina fatan nima Allah yabani abunda zan kyautata maki da shi, sannan mahboob Ya faɗamin cewa kin bashi kyautar kuɗi duk da yaƙi gayamin nawa ne kinsan halinshi May be Yana gudun kada Ince ya bani kasona, baisan cewa Nima na samu alheriba, abunda nake ta so in faɗa maki kenan"


 Waro ido Aneelerh tayi da alamun farin ciki akan fuskarta tace"masha Allah, kice kun samu abun arziƙi" Jinjina kai Zahra tayi"zakisha mamaki auntyna, naga yanzu kika farka daga bacci, da anjima idan muka kammala yin breakfast zan fada maki komai"


Murmushi Aneelerh tasaki"Yau zansha kanun labarai, Yanzu bari na shiga toilet in yi wanka" 


 "Auntyna wai yaushe za'a dawo mana da baby junaid dinmu, nifa nayi missing dinshi, Allah na kusa zuwa in dauko shi, Jiya har mami na tambaya game da zancen dawowarshi"


 Aneelerh tace"kada ki damu, Babyn mu yau zai dawo gida, Hajiya adama zata kawo shi, Nima yau da shi na tashi araina"


 "Allah ya kawo su lafiya, shima na tanadar mashi kyautarshi ta musamman da zan bashi" Aneelerh taji dadin maganar zahra.


  "Kada na cika ki da surutu, nayi kewarki ne auntyna, bari nabarki kiyi wankan in kin fito mun tattauna, amma kafin nan niko inaso in tambayeki wani abu in ba takura" dariya aneeleh tayi kafin tace"okey ina jinki fadamin menene"


 Da ido tayi mata nuni da hoton dake amanne jikin bango.


  "Wacece wancan black beauty din mai diri? Ita kadai ke bansani ba cikin ƙawayenki, nadai san Benazir mahaifiyar kyakkyawar yarinyar nan Angel"


 Jim Aneelerh ta ɗanyi kafin ta furta"Aishatu bintu sheikh Iman Malik, shine sunanta, kamar yadda na fada maki aminnan juna ne mu"


  Cike da son jin ƙarin bayani Zahra tace"to amma ta rasu ne ita? Naga ko waya ba ku yi, Ita dai benazir nasan abunda ya faru da ita" a kagare ta jefa mata tambayar.


 Cikin sanyin murya Aneelerh tace"ƙaddarace ta afka mata wadda tayi silar tarwatsewar farin cikin rayuwarta, baiwar Allah, nan da kike ganinta mahaddaciyar alƙur'anice, tun tana ƴar shekara goma sha wani abu ta haddace shi, Tana da kaifin basira mace ce mai kamun kai, tana da aji, idan nace zan baki labarin rayuwar Aisha wallahi saikinyi sha'awar yin koyi da ita, saboda kyawawan ɗabi'unta da halayanta, Ni kaina ban ta6a tsammanin zamu rabu da itaba....." tun da ta fara magana zahra ta kafe ta ido tana sauraronta, idanuwan Aneelerh sun kaɗa jawur, sam bata son tuna baya, hakan zai fama mata ciwon dake acikin zuciyarta.


  "Aunty Aneelerh kinyi shiru? tun da kika ambaci kyawawan halayanta naji na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarta"


 Girgiza kai Aneelerh tayi"Am sorry zahra, bana son tunawa, " bubbuga ƙafa zahra tayi tamkar zata fashe mata da kuka tace"please Aunty Aneelerh, wallahi tana burgeni duk da ban ta6a ganinta ba"


Murmushin yaƙe Aneelerh tasaki tana duban hoton yayin da hawaye ke bin fuskarta"Ni kaina bani da masaniyar tana araye kota mutu, tunkafin muyi aure tabar gidan iyayenta, Silar wani mummunan abu daya faru, wanda ni nayi imanin bata da laifi, tuggune da makirci aka shirya mata....." dakatawa Aneelerh tayi dayin maganar tana kallon zahra, tsabar son jin gulma har ta jefar da cazbar hannunta batare da saninta ba.


 "Aunty Aneelerh kinyi shiru! Meya faru da ita? Wanda yaja har tabar gidan iyayenta? Wani irin tuggune aka kitsa mata"?


 Tuntsurewa Aneeleeh tayi da dariya, juyawa tayi da sauri ta nufi toilet door tana fadin"Zahra ƙwara ki fidda rai da son jin labarin Aishatu Bintu sheikh imam malik, dan zan baki shi ba yanzu ba sai kin ƙara hankali" ta kare maganar ta shige toilet taja kofa ta datse.


  Ta tafi Tabar Zahra da cizon yatsa, idanuwanta akan hoton fuskar Aisha, aranta ta ayyana ai wallahi saina ji labarinki baiwar Allah, Ai ni dama tun da naga hotonki na shaida kinbar tarihi arayuwarki, Oh ni ƴar ubansu,  gata kyakkyawa, mace har mace, ga diri kamar nicki minaj, ko tana ina ahalin yanzu"? Sambatu zahra tadingayi tana kallon hoton aisha, sai daga bisani ta duƙa kasa ta dauko cazbaharta, ta futo daga ɗakin ta nufi nata dakin don ta kimtsa kafin lokacin yin break fast.


   

*Daular Alhaji Musa🏙*

  


A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data sanya launin milk, gaba ɗaya ta tattara natsuwarta akan addu'ar da take Yi, ta ɗaga hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu'o'i, yayin da hawaye suka cika idanuwanta, bakomai take roƙo ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da ƴarta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matuƙar ƙagara da son ganinsu.


Ƙamshin turaren dr.shureim ne Ya dakatar da ita daga yin addu'ar da take yi, da sauri ta shafa saman fuskarta, A hankali ta fuskance shi, yana daga zaune gefen gadonta, bai jima da shigowa ɗakin ba, fuskarshi dauke da annurin farin ciki, Daren jiya da tunanin ƴar uwarshi ya kwana, ya damu da ita.


"Yayana nakaina, Ina kwana ka tashi lafiya"?


"Lafiyalou rabin raina, ina fata kin yi kwanan farin ciki agidan Uncle" shiru tadanyi tunawa da abunda ya faru duk da ta dauki hakan amatsayin mafarki, jinjina mashi kai tayi"Alhamdulillah, jiya naji dadin bacci, hada munshari, balle ni da nake atare da Zeenatu, yarinyar akwai shiga rai"


Murmushin gefen fuska dr shureim yasakar mata"hala tacika ki da surutu"?

 Girgiza kai benazir tayi"a'a, ai yarinyar kunya gareta, tana jin nauyin yi min magana yadda kasan bafullatana"


Dariya dr. Shureim yai kafin ya tsagaita yace"hakane tana da kunya, amma fa ta iya zuba kamar aku, sai kun saba da ita zata saki jiki dake"


Dr shureim yasaki baki yana maganar zeenatu, baisan cewa tana la6e cikin toilet tana sauraronsu, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, kalmar akun daya furta ta ta6a zuciyarta.


Murmushi benazir tasaki, abunda baisani ba tun jiya tasan da surutun zeenatu, kafin su kwanta bacci, sunyi firar dare, ta saki jiki da ita tamkar abokiyarta.


"Yaya shureim, Ni yanzu damuwata Mijina da ƴata, mami ta fadamin cewa basa ƙasar, amma sun kusa dawowa, ni namanta ma ban tambayeta sunan ƙasar da suka tafi ba" ta fada tana dubanshi"yaya shureim ko kana da number wayar taj"? Ras yaji gabanshi ya fadi, saboda shi baisan komai dangane da mijin benazir ba.


 Shiru yai mata batare da ya iya furta mata kalma ba, don baisan amsar da zai bata ba


  "Au namanta, kaima bakasan mijina ba ko? Lokacin dana aure shi......" bata ƙarasa maganarba cak ta ɗago suna kallon juna.


  Cikin sanyin murya yace"ai ba laifi kikayi ba, lokaci bana acikin hayyacina, ban kaiga farfaɗowa daga radadin abunda ya same ni ba, Benazir bansan mijinki ba, bana zumunci dashi, saboda ni kaina bana cikin natsuwata, kuma hada ƙarin ni ba azaune nake ba, idan baki manta ba, da abun duniya ya isheni, tattarawa nayi na koma egypt wurin ammim mu da zama" daƙyar yake furta maganar, launin idonshi harya fara canzawa

 Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa"nasan ban kyauta maki ba, amma kiyi hakuri, daga ni har ke ƙaddarar rayuwace ta afka mana,"Wallahi bazan Iya misalta maki ƙunci da radadin da naji ba, lokacin da labarin tafiyarki ya same ni, idan bazan manta ba, aunty zainab ce ta sanar dani komai dangane da guduwarki da jinjirar da kika bari, bayan haka bansan komai game da rayuwarsu ba nima ban jima da dawowa gida ba......."


Bai ƙare maganar ba ta tari numfashinshi da cewa"kana nufin baka ta6a haduwa da ƴata Angel ba? Amma ni ayadda mommy ta fadamin taj yana kawota gidan mu, suna daukar dawainiyar kula da ita kuma suna nuna mata hotona harma tana tambayarsu Yaushe zan dawo"


 Zaro ido dr.shureim yai alamar mamaki da jin ƙaryar da mommynsu ta shirgawa benazir, duk da ba a ƙasar yake zaune ba, yasan komai dake faruwa a gidansu, ta hanyar aunty zainab dake fada mashi akai akai, shi dai a iya saninshi Hajiya layla bata zumunci da tajuddeen, hatta auran benazir da Alhaji ubaid ya bashi bada son rantaba, saboda ita ta tsani bare, balle shi da yakasance mai rufin asiri ba attajirin mai kuɗi ba, har fada saida sukayi da Alhaji ubaid saboda yabama ɗan jarida auran ƴarsu.


Ganin yanayin fuskarshi ya canzane yasa jikin benazir yin sanyi,


"Yayana kayi shiru baka ce min komai ba! Mommy ba gaskiya ta fadamin ba ko"? Adabarbarce ya girgiza mata kai yana kokarin tattara natsuwarshi yace"bahaka bane, ai ni bana a ƙasarne, bani da masaniya akan komai, lokacin dana dawo Nigeria shi taj din da yarinyar sun riga sun bar ƙasar, nima awurin Aunty zainab naji labarin"


Ajiyar zuciya benazir ta sauke, fatanshi Allah yasa kada ta kuma tambayarshi wani abun da zai kasa amsa mata.


 "Mommy ta fadamin cewa yarinyar kamanninta sak dana tajuddeen amma hasken fatarta nawane ta dauko, yarinyar kyakkyawace idan zan iya tunawa, kafin na gudu nabarta dana haifeta saida na kalleta har naga launin idanuwanta ruwan tokane kalar na amminmu, kuma tana da curly hair kalar nawa, ni dai fatana Allah yasa bata dauko halina ba, banason ace bata jin magana.


  Dariyace ta kubce ma dr shureim, sambatun benazir ba ƙaramin kayatar dashi suke Yi ba.


Zeenatu dake a la6e tana sauraronsu, takasa fitowa daga toilet din, zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin wacece yarinyar auntynta benazir? Ya akai bata ta6a ganinta ba? Kamar dai ta ta6a jin labarin jinjirar da benazir ta bari awajen mommynta sarah.


Lokaci ɗaya dr shurem yadaina yin dariyar, hawayen dake taruwa cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman kuncinsa.


  Da sauri ya kifa kanshi on his laps,

Hankalin benazir ba ƙaramin tashi yai ba, Jiki na rawa ta mike daga kan dardumar ta koma gefenshi ta zauna haɗi da daura hannunta ɗaya saman bayanshi"yaya shureim meke faruwa? Meyasa ka zubar hawaye? Yanzu fa kake yin dariya? Kona fadi wani abune daya 6ata maka rai? Shiru bai ɗago ba, duk tabi ta ruɗe, zeenatu dake yi masu la6e jikinta yai sanyi jin dr shureim dinta yana zubar da hawaye, muryar benazir taci gaba da jiyowa tana fadin"dan Allah kayi min magana yayana nakaina, kasan bana son ganinka acikin damuwa" bazata iya jurar halin da dr shureim dinta ya shigaba, Har ta miƙa hannu zata buɗe kofar toilet din, sai kuma tafasa ta dan buɗe kadan ta yadda zata iya leƙen su


Ɗagowa yai da kanshi, hawaye sun wanke fuskarshi, benazir dake kallon shi itama hawayen ke fita a idonta

 Zura hannunshi yai cikin aljihun jallabiyar jikinshi ya zaro wayarshi, batare dayace komai ba, Ya miƙa mata wayar, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskarta Yarinyar dake akan wallpaper dinshi.


  Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ya sanya tafin hannunshi ɗaya ya toshe mata bakinta, haɗi da girgiza mata kai, alamar tayi shiru, daƙyar ta haɗiye kukanta, yayin da suke kallon juna, sai yanzu tagane dalilin zubar hawayenshi.


A hankali ya zame tafin hannunshi daga saman bakinta, hakan ya bata damar yin magana Cikin rauni na murya ta furta"munyi babban rashi yaya shureim, babu rabon suyi rayuwa tare da ƴata Angel, yarinyar tana kama damu, kamar ni na haifeta, mutuwa tayi mana yankan ƙauna, Allah ya jiƙanta" daƙyar ta ƙare maganar a hankali ta mayar da rinannun idanuwanta kan hoton jinjirar yarinyar dake a nannanɗe cikin towel fari ƙal, an sanya mata kayan sanyi, farace sol kamar ka ta6a jini ya ɗigo, dara daran idanuwanta sun buɗe sosai.


   "Bani da abun kallo daya wuce hotonta, da ita nake kwana da ita nake tashi, na mutu akan ƙaunarta, bazan ta6a daina sonta ba, kuma bana tunanin koda ace nayi aure zan samu madadinta a duniyar nan........   ⁉️❗

   


  Mu haɗu jibi Alhamis kenan, idan Allah yakaimu darai da lafiya, game bukatar cigaba da karanta prisoners 500 ne zaku zaku tura ta bank acct dina, ga ta inda za'a tuntu6eni 08103884440
3196407426


Bature Hafsat Muhammad

First bank 

Idan kin tura zaki bada hoton receipt amatsayin shaida🤗

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post