HAMRA'UL YAZEEDA
STORY AND WRITTEN
BY
NUSAIBA_ ALKAMAWA✍️
(Aunty nuseee)
PART Three
HAMRAT
_______Ajjiye alƙalamin nata tayi, ta dakata dayin rubutun,kallon tsadadden agogon dake hannunta tayi, taga lokacin tashinta ma yayi .
Litttafin, ta adana ama adenshi, sannan tamiƙe tafita waje duk inda ta gifta gaisuwa ake kaimata cike da girmamawar shugabar tasu.
" ita kuwa cike da izza take Amsa musu, darect parking space ta nufa, tashiga motar ta, tanufi titi sanɓel bata dire a ko ina ba sai awani tamkameman shago.
Shiga tayi sainaga ma ashe chemist ne, gaisawa sukai da mutumin cikin mutumci da girmama juna dan sunsan juna farin sani kuwa.
"faɗa masa irin maganin da zai bata tayi.
"yaɗanyi jum kamar bazai bayar ba sai kuma yadauko yabata domin yasan halinta, yarinyar kirki ce baza taje tayi abinda ba shikkenan ba, karɓa tayi taimasa godiya tafice fuskarta dauke da murmushi wanda nakasa gane ma'anarsa .
*******
Gida ta nufa gateman ya bude mata wangalelen gate ɗin," tashiga tai parking ɗin motar a parking space tashiga cikin parlour taji gidan shuru addu'a tayi aranta Allah yasa me gidan ya mutu, anya kuwa? Amman tayaya xangane ya mutun,?"atine ce ta faɗo mata aranta bangaren masu aiki tanufa tatarar da atine kuwa tanata aikace _aikace cikin girmamawa atine ta rusuna ta gaisheta Amman hamrat bata amsa ba SBD girman matar dan zata iya haifar ta ma kuma tahana mama atine gaishe da ita Amman taƙi ji.
"Mama atine yajikin dadyn tafada cike da jin wani ɗaci azuciyarta, na kalmar da tace wai Dady. ta,daure ta faɗa ne kawai dan ta bigi cikin tane .
"Hajiya karama ai suna asibitin ɗazu ma naje nakai musu abinci jikin nashima da sauki dan asthma tashice ma ta motsa masa .
"Hmmmn me Wannan dattijon yake nufi danine nasan yanxu yasan gaskiya Amman yaboye, me hakan yake nufi kodai akwai wani babban abu dayake shirin aikatawa ne lalle saina ƙara tashi tsaye kuwa," tafada ajuciyarta Amman afili tace" ohk, kawai tajuya tashige dakinta.
*******
*AUNTY*
* Zaune take akan wata hadaddiyar kujera mai numfashi ta ɗora kafa kan ɗaya tana wani taunar chewing gum,wayarta ta dauka kirar iphone 13 ta latsa ta wajan kira ta shiga tadanna kira ,aikuwa ringing din farko aka daga kiran.
"hello ameerah?Aunty ya akayine kodai ta samune dan nasan kiranki to samuwa ce ,takarasa fada cikin jin daɗi.
",cike da yauƙi Aunty tace wai dan Allah ameerah yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne ?
"Adayan ɓangaren amerah tace Aunty me kuma aka ce miki nayine indai maganar binne wane tuni na binne ai,"hmmn ruwanki,inma baki binne ba , Ni ba Wannan ne yasa na kira ki ba ,nakira kine akan maganar Wannan malamin dana saka yayi min aiki Akan maganar wannan jaririyar kinsan fa haryanxu uwar tana tuna yarinyar tata kuma kinsan dai halin Alhaji zai iya shiga shima cikin damuwar wanda bana fata yakara shigar ta ban karasa cikar burina akan saba,don haka nakeso kije asake wani aikin,ina jin wancen aikin baiyi ba shiyasa nakeso asake wani.
"Wata iriyar mahaukaciyar dariya ameerah ta bushe dashi, wanda da kajita kasan na muguntane,don ita abinne tun yana bata mamaki harya dawo yadaina bata mamakin.
Dan gaskiya yayarta ta bata da imani ko kadan duk rashin imaninta Amman Aunty ta danneta ta shanye,"baki da matsala Aunty na takaina Amman bayan haka inaso kituro min da kudi inyaso sainaje ko jibi ne.
"cikin washe baki Aunty tace" ohk baki da Matsala kema ai kinsan kuɗi ba matsala ta bane ba ,xakiji alert,kit takashe wayar.
_________Suna gama wayar , Aunty tatashi domin itace yau da girki domin Daddyn yara bayacin abincin ƴan aiki.
",taku take ɗai_ɗai cike da izza haɗe da mulki ta shiga cikin kitchen din ,haɗa idanu sukayi da mutumin nata Waheed saurin dauke idanunta tayi daga gareshi domin wani ƙwarjini da yake mata ,ta nufi wajan gas Amman duk atakure take .
******
Shikuwa gogon tunda yahaɗa idanu da ita sauɗaya yadauke bai kara kallon kurar taba , **Waheed** Shine babba agidan daga shi sai Abdallah ,sai kuma Safwan, sai sabeer kwata_kwata jininsu sam bai hadu da aunty ba ita kuma haka ta tsane shi iya tsana bata kaunar ganinsa sbd duk shine yake ɓata mata shirinta akan mahaifiyar su,waheed ne kadai yake taka mata birki agidan domin baya daukan raini shiyasama basa shiri da sabeer ɗan gidan Aunty,dan Sabeer yana da matukar rashin kunya shiyasa baya sakar musu fuska.
_______Baxa ka taɓa ganin dariyar Waheed ba saiyana gaban mommy ko daddy suka daine kawai suke ganin fara'arsa domin mugun miskiline.
"Bude freezer Waheed yayi yadauko kifi yaxuba acikin girkinsa cikin mintina ƙalilan ya kammala dafa indomie nasa yajuyeta a plate yafita.
"Yana fita,aunty tayi ƙwafa "tace mara kunyar ƴaro kawai banxa kawai,kayi magana ya xageka na kusa yin maganinka komai yazo karshe idan na kawar da kai ,duk kabi kahanani aiwatar da Abinda ke cikin xuciyana shekara da shekaru hmmn dani kake bayani,tafaɗa tana kiciniyar ɗora girkinta,har ta kammala.
Tana tashi tabar kicin din ta tafi Dakinta tayi sallah tana idarwa ta koma kicin din ta tarar da momy tana xuba shinkafa A ruwan da ta Dora.
" tsawa ta Dakawa momy "ke Nafisa bana hanaki taɓamin tukun yaba idan ina girki kinxo ne ki sake barbaɗawa alhaji irin abinda kika zubamai ne lokacin da kika ganshi kika kwacemin shi ko kuwa yaya ?"to bara na gayamiki wani Abu da baki sani ba wlhi tallahi bazan taɓa barinki ki zauna lpy ba tunda haka kika zabarwa kanki kuma bara na fadamiki alhaji nawane ni kadai babu wata mace da ta isa ta rabani da shi keeee banza bara kiji duk munafurcinki saida kiyi ki gama amma alhaji be isa ya juyamin bay...... bata karasaba tayi shiru safwan ne yashigo a fusace "keee zainab dawa kike? zaro idanu aunty tayi bakinta yana rawa tace" da baba ladi nake nabarmata girki amma ta tafi ta barmin se kamawa yakeyi duk jikin aunty tsuma yakeyi Don tasan halin safwan yanxu saiya iya wanka mata mari babu ruwansa kuma alhaji goyamasa baya zaiyi.
" Daddyn yara ne ya Dawo daga masallaci kowa ya hadu a Daining za'ayi Dinner ,Aunty kawai akejira cikin takun ƙasaita ta shigo hannunta rike da basket zata fara jera abinci, mommy tace Aunty ba rana tayaki mana murmushi tayi na yaƙe Wanda yafi kuka ciwo tace toh.
Mommy kuwa fita tayi cikin rashin jin dadin furucin auntyn yara.
", , mommy ta tashi ta fara zubawa kowa nasa sannan kowa ya fara cin abincinsa "Daddy yace wai ina babana ne ?Aunty tayi ƙwafa tace rabu dashi kasan babannan naka ba,a iya masa kanwar tawa ya nemi yayiwa rashin kunya shine naci mutuncinsa taya zan goyi bayan rashin gaskiya shiyasa yayi fushi sabida na tsawatar masa shiyasa yayi zuciya tafaɗa cike da kissa.
______Allah ya shirya kawai Daddy yace sannan yafara magana da Mommy ," Momyn yara yakamata kusani cewa babana yarone yana da karancin shekaru daga shifa se me sunan mama, Aunty takara cewa waye yaron haba dadyn yara yaron da in a kauye ne yanxu yaci ace yana da yara biyu kuma kana cewa dagashi sai mai sunan mama to ka manta tazarar da take tsakaninsu ne shekara biyar fa yabawa mai sunan mama ayanxu haka inda muna tare da ita da tuni ta shiga shekara 18 years ko ita yanxu ai baza,ace mata yarinya ba bare kuma shi,ta karasa fada cike da kissa.
"Mommy tasa baki wadda tunda su Daddy suka fara magana batace komai ba ta fara magana wannan haka yake alhaji gaskiya take faɗa .
"Mommy ta fara wani tunani wato indai ta fahimci Aunty sai aibata dan lelen dan nata take yi,yaron da kin taboshi katabo masifa da bala'i yau tana nunawa Daddyn yara cewa babu komai a tsakaninsu hmmn lalle ta sarawa makircin Auntyn yara .
*******
Mommy ta kawar da tunanin ta tamaida kallo gurin Daddyn yara tace dadyn yara?
Daddy yace na,am mommyn yara?
"Mommy tace dama inaso muyi wata magana ne dakai idan ka bani dama,daddy yace to ina jinki .
" Dama akan maganar Waheed ne yaron nan fa fir yaki yayi aure to mezai hana muda kanmu mu zaɓa masa matar da zai aura?
Da sauri Waheed yaɗago kanshi,wanda tun da suke maganar bai ko kalle su ba sbd acewar sa bata shafe saba,sai Yanzu da yaji ana hada sunanshi da aure ,kafe dady yayi da idanu sbd yaji irin amsar da Daddyn xaibawa Momyn .
"Gyaran murya dady yayi yace "nima wllh zancen nan yana raina kawai kinriga nine a fili,gaskiya kam Yakamata yayi aure duba da shekarunsa idan baixaɓo ba aimu Sai mu xaɓa masa dama ina masa sha'awar ƴar abokina minister,"hakan yayi kuwa dady
yanxu momy wai auren Dole zakuyimin?" suka tsinkayi Muryar Waheed "Daddy ne yace eh ƙwarai ma kuwa idan baka xabi matar da zaka aura ba nanda wata uku kuma.....
" karar buga cokali sukaji Aunty ce ta ajiye cokalin da karfi tayi ficewarta abinta , momy ta tashi zata bita "Daddy yace ta dawo ta zauna suka cigaba da tautaunawarsu, Waheed yana shirin mikewa Daddy yace Waheed?
Waheed yace na,am Daddy nabaka nan da wata Uku kazabi matar da zaka aura nayi maka hakane danna baka Damarka ta karshe, Waheed yace to Daddy yatashi yabar gurin rai babu daɗi, momy da Daddy tare suka miƙe ta rakashi mota,domin haka al'adar gidan take duk sanda Daddy xaifita to su biyun saisun rakashi to yanzu kuma aunty tashige dakinta shiyasa mommy ta rakashi, ta juyo abinda tayi Daki.
" shi kuwa Waheed yana fita daga falon darect part dinsa ya nufa yana shiga ya tarar da safwan yana waya a babban falonsu tsaki kawai yayi ya wuce Bedroom dinsa Toilet ya nufa ya watsa ruwa ya fito ya fara shiryawa yana gama Shafa mai ya dakko shadda light blue yasa da takalminsa sau ciki shima kalar hular ya Dakko cumb ya taje sumarsa wacce take a kwance ya wuce ya Dauki wayarsa yayi gaba yana fitawo falo, parlourn ya ƙaure da kamshi ya yadanna kira awayarsa...
HAMRAT
Tana shiga cike da gajiya ta faɗa bed Saida ta huta sannan taje tayi wanka tashirya tazauna tana tunani kala_kala
______Ba tunani yadace kiyi ba aunty hamrat samo mana mafita yadace kiyi awannan lokacin hamrat ta tsinkayo muryar yazeeda tana mata gizo radau kuwa a kunnenta.
"Kiyahkuri ƙanwata ruhinki bazai tafi abanxa ba saina bi muku hakkinku akullum addu'ar dana keyi Allah yacikamin burina YAZEEDA labarinki saiya karade duniya sakon da mukeso mu isar sai yaje inda mukeso yaje ɗin burinki da kikeso ya cika saina cika miki shi sunan da kikeso kiyi sai duniya tasan dake ,kawai kiddara nice yazeeda kece HAMRAT takai karshe maganar hawaye na silala afuskarta
Ni kuwa writer tsoro yagagareni cigaba muku da typing dan karkashin gado nashige ganin hamrat na magana da fatalwa zance ko aljana ko kuma zarewa tayi ne oho.
*Story and*
*Written by Aunty nusee*
Plx Comment and share