Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 12 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 12 Complete

Novels Elite English

 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_

12

سجن القدر💋✊🔥

~Takun Ƙarshe🔥~

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

Gently ya dira ƙafarsa kan Polished marble floor din wurin A matuƙar ruɗe suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da ƙarfi ƙarfi.

Lokacin daya ƙarasa shigowa ciki, Gaba ɗaya Suke bin shi da kallo mai cike da tsantsar ruɗani, idanun kowa akan zazzafar surar jikin shi, kasancewar ya sanya face mask hakan ya 6oye ainihin suffar fuskarsa, wato wata hadaddiyar Emirati thobe ce a jikin shi yar ubansu launin Black gold, yadda kasan a jikin shi aka ɗinka ta saboda yadda ta bi shape nasa, ta baiyanar da surar shi mai matuƙar jan hankali, Musamman sick packs din kirjinsa ya fito 6aro 6aro, da murɗaɗɗan damtsensa, abun ka ga dogon namiji komai nashi is exraordinary, farar fatarsa kuwa har wani salƙi take tana walwali, yadda kasan namijin hurul aini tsabar kyau da daukar ido, wrist din hannun sa na asanye da agogo ƙirar Rolex sai ƙyalli take, face mask din dake lullu6e da fuskarshi dai dai ƙasan idanunsa ya rufe kyawawan sexy eyes dinsa waɗanda ke a kewaye da lallausan long eye lashes dark brown sun ƙara ƙawata kyawun idanunsa, yalwatacciyar sumar kanshi kuwa tasha gyara har ƙyalli take, gaba ɗaya gashin an tattare shi an ɗaure yasauka har kan gadon bayan sa, Wani irin sanyayyan ƙamshin turare ne ke fita daga jikin shi mai narkar da zuciya,


Hankali fa gaba ɗaya ya tashi da ganin ɗan tahalikin nan, tun kafin ma ya buɗe fuskarshi sun gama girgiza da kyawun shi, kowannansu sake sake yake a zuciyarsa wanene wannan? Daga ina Yake?


Zuciyoyinsu ba su gama kiɗima ba, sai da su ka yi tozali da kyakkyawar matashiyar dake shigowa hall ɗin ta bayan shi, wohoho zo ka ga yadda idanu suka koma kanta, from head to toe suke kallon ta, ta ɗauki wankan Embroidery Open front baya, launin black anyi mata adon gold stone works da zanan Red flowers, rigar tayi masifar yi mata kyau, ta yi rolling mayafi akanta, itama fuskarta asanye da face mask take, ƙafafuwanta kuwa Highhills ne jigunanu, Tsabar ruɗani Ya hana kowa na hall din furta magana sai dai su bi da idanu kamar kurame, ko da shigowarta daga gefen shi ta tsaya, Jim kadan suka cigaba da shugowa kowan nan su da face mask, matan cikin shiga ta abaya mazan kuma Emirati thobe ne a jikin su, sai da suka cika su goma sha ɗaya cuff tukunna suka dakata suna kallon kallo atsakanin su da mutanan hall din, ga dukkan alamu bakin su ya mutu, saboda babu alamun zasu furta magana, lamarin ya ruɗar da su, mamakin su ina aka samu wadannan matasan yan matan da samari? Daga gani dai ba yan nahiyar su bane saboda komai nasu is exraordinary, dai dai da yanayin tsayuwarsu abun kallo ne kamar a shirin drama.


A ƙalla an shafe tsawon Mintuna ana jifar juna da kallon ƙurulla, daƙyar Hajiya saratu ta samu ƙwarin giwar buɗe baki ta furta"Su wanene ku"? Ta jefa masu tambayar tana mai zare idanu


"Bayin Allah daga ina ku ke? Wanene Ya gayyace ku dinner din nan? Meyasa ku ka rufe fuskokin ku da face masks? Hajiya Madina ce tayi maganar a ƙagare da son jin amsarsu


Gaba ɗaya mutanan hall din suka matso gab da su, kamar sunga sabbin halittu daga wata duniyar


"To ko dai mutanan boye ne? Wai ba zakuyi mana magana ba, kuntsaya kuna kallon mu kun bar mu a cikin duhu"! Da tsiwa hajiya laurat ta faɗa tana tada jijiyoyin wuya.


"Anya kuwa waɗannan ba mutanan 6oye bane? Nifa wlh hankali na bai kwanta da su ba, akan me zaku faɗowa mutane ɗakin taro babu sallama? mun tambaye ku su wanene ku kun yi shiru ba ku tanka mana ba, ko dai turo ku akayi ne don ku tarwatsa mana taron mu"! A faɗa ce Hajiya saratu ta kuma yin magana, Hankalin fa kowa Ya tashi wasu sun harzuƙa, su kan su tsabar fargaba ne ya hana su buɗe baki suyi masu sallama, duk sun sha jinin jikin su.


  Baba obie da Manyan mutanan canada sunyi kasaƙai Suna Kallon su tamkar a shirin drama, sam babu alamun sun tsorata da ganinsu saboda sun san akwai jami'an dake tsaron gurin dole akwai wanda ya gayyace su, sai dai zallar mamakin dake shimfiɗe a kan fuskokin su.


 Ƴan matasan family din maza da matansu sunyi cirko curko suna kallon su, cike da son sanin su wanene wadannan bakuwar fuskan da suka faɗo masu a hall!!!


Mc da ke atsaye ya ruƙe mic sai mazurai yake yana fadin"ga dukkan alamu mun samu baƙi daga jinsin aljanu, suma sunzo taya mu jimamin tafiyar prime minister Hateem, wannan abun mamaki ne da al'ajabi, lallai prime minister ba karamin mai farin jini ba ne......." sai sambatu mc yake yi yana dubansu babu alamun wasa akan fuskarshi, bilhakki dagaske yake koro jawabi, su sir mubarak kuwa jira kawai suke suga iya gudun ruwan wadannan bayin Allahn da suka faɗo masu bagatantan babu sanarwa.


Sannu A hankali sautin takalman prime minister ya karaɗe tsakar filin, babu fargaba ko kaɗan Ya nufi inda suke har ya ƙarasa gaban matashin nan daya fara shigowa kafin yaci burki yana bin shi da kallo tun daga sama har ƙasa, hakanan ranshi ya dinga bashi cewar yaron daya jima yana kwaɗayin sanyawa a idanun shi ne, zuciyarshi ce  ta soma azalzalar shi da son tabbatar da abun da yake hasashe, a hankali Ya juyo baya ya dubi chief owais dake a can gefe ɗaya ya goya hannayensa bisa ga kirjinsa tamkar baisan meke wakana ba

   Haɗa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...? *WAIWAYE A DON TAFIYA*


Abun da ya faru, lokacin da Chief ya dawo gidan bai samu kowa a falon ba,, har su naufal da suka zauna sun koma daku nan su, direct Ya nufi bedroom dinsa bayan shigar shi, tsayawa yayi agaban mirror zuciyarsa a cike fal da tunanin ta wace hanya zai iya taimaka ma Uncle dinsa! Saboda yaji tsantsar tausayinsa ganin irin halin da ya shiga na kaunar yaron, bai da burin daya wuce danish ya farka ko dan Ya faranta Ma daddy hateem kafin yabar nigeria....


Yayin da ya ke wannan tunanin Yana safa da marwa a tsakar ɗakin sa Ya shafe kusan Mintuna ashirin, Batare daya samu mafita ba, Yanke shawarar kiran layin ɗaya cikin drs dinsu yayi don azo aduba lafiyarshi wata'kil adace, duk da shiekh Imam Ya ce basai sun kira likita ba saboda rashin lafiyar tasa bata asibiti bace, kawai a lokaci Ya ƙosane daya farkan shiyasa ya yi deciding kiran likita.


A firgice ta farka daga gajeran baccin da yayi awon gaba da ita tun bayan kammala sallar azhar, Hannun ta dafe da saitin zuciyarta dake yi mata wani irin bugu tamkar ana dakan sakwara, wani irin faɗuwar gaba ta soma ji, Hankalin ta sam ba'a kwance yake ba, tarasa gane dalilin jin bugun da zuciyarta take yi mata da rana tsaka, kuma ita ba mafarki tayi ba, saukkowa tayi daga kan gadon su, batool dake a kwance babu alamun zata farka, Cikin sauri ta fito daga room dinsu zuciyarta na azalzalarta da taje ta ƙara duba danish dinsu don tana ji aranta wani abu ne ke faruwa da daya daga cikin su shiyasa taji wannan faduwar gaban, kuma bakowa ne ya fara fado mata aranta ba face shi din dama da tunanin shi ta wuni.


Gudu gudu sauri sauri ta nufi second floor, ko da ta shiga falon babu kowa.


Tana ƙarasawa bakin ƙofar ta sanya hannu biyu ta dafe ta da karfi har sai da ta buɗe kafin ta faɗa a fujajen shigarta keda wuya, idanun ta su kayi mata tozali da abun da Ya figitar da ita, da wani irin faduwar gaba take kallon shimfidar shi.


   Wata irin zuface take tsastsafo mashi tun daga cikin sumar kanshi take gangarowa har izuwa saman fatar wuyan shi, kyakkyawar fuskarshi ta jiƙe sharkaf da gumi, hatta jallabiyar jikin shi ta manne ma fatarshi saboda ruwan zufar daya jiƙe ta, muryart na kerma ta soma kokarin ambaton sunan shi.


 "Dad...da..nish" bata ƙare maganar ba, ganin yadda yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suka fara kerma tamkar na wanda sanyi ya kama.


  Kasa samun nutsuwa tayi, har batasan sa'adda ta haura saman gadon nashi da rarrafe ta ƙarasa saitin inda kanshi ya ke, ta zuba mashi ido tana kallon shi da tsananin firgi ci.

  

Cikin lokaci ƙanƙani, Ilahirin Jikinsa Ya jiƙe sharkaf da gumin zufa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai.


Tsabar Yadda Jikinsa ke kakarwa Har gadon kerma yake yi ita kanta jikinta ya kama kakarwa, tun zuciyarshi na bugawa a hankali har ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje, sautin numfashinsa mai haɗe da gurnani ya gauraye bedroom dinsa, da karfi Yake Jan shi tamkar babu wadatacciyar iskar da zai shaƙa.

Ko wani sashe na jikin shi tuni ya soma motsawa, Unaisah dake kallon shi idanunta azazzare duk tabi ta rude ta firgice Lokaci ɗaya tsoro Ya cika ta, Zabura tayi da niyar ta watsa aguje gudun kada Ya cutar da ita don ta fahimci kamar baya hayyacin sa ...


 Sai dai kafin tayi wani yunkuri juyawa yayi wani kwakkwaran juyi tamkar mayunwacin zaki haka Ya damƙo sumar kan nan nata daya sha gyara gaba ɗaya ya dawo da ita jikin sa, Yana huci ya matseta kamar zai tsinkata biyu, Ji tayi tamkar an daureta da igiyoyin kaca, hucin zafin jikinsa har anata jikin take jin shi, Zuciyarta ce ta bata shawarar ta hankaɗe shi ta gudu, kafin yai yunƙurin cutar da ita, Cikin ƙarfin Hali ta daddage ta fusge kanta daga ruƙon da yayi mata, gaba ɗaya ta kundumo saman tiles kanta ya daku, Harta zabura zata mike da niyar ta watsa a guje taji ya damƙi ƙafarta ɗaya, ta ƙarfi ya janyota kamar ɗiyar roba ya dawo da ita saman gadon, runtse idanunta tayi da sauri tana ambaton La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.


   Dogayen yatsun hannayensa dake kerma ya ɗaura saman wuyanta, ya shaƙeta sosai tamkar zai tsinka wuyan, radadin azabane ya ziyarce ta, ta kware baki ta fasa wata irin ƙara mai sautin gaske, sai faman kiciniyar kwace kanta take yi amma ta kasa saboda ƙarfin dake gare shi tamkar zaki a haka ma don bai da koshin lafiya da tuni yajima da kashe ta cikin rashin sani. Radadin da tajine yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske


Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga room din ta, don taje ta fara shiryasu ganin lokacin dinner din Ya kusa Cika


Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci ɗaya taji gabanta yai mugun faɗuwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba


  A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah"


 Kofar tamkar an datse ta da key taki buɗewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_


 Ta faɗa jiki na tsuma ta zura hannu ɗaya ta dauko wayarta  daga cikin aljihun skirt dinta.


  Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin buɗe kofar ta datse..."


Muryarshi a ruɗe Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta ƙare maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun kaɗa jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta.


Kamar an jeho shi Ya faɗo  falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ƙofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba.


Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya duƙar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai ƴan kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa  meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Haƙiƙa sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin ƴan kwanakin nan.


 Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun aljani gashi ya damki yarinya a hannun shi


Cikin shessheƙar kuka Ummi take rokonshi akan Ya saketa, kada ya kashe masu ita.....'


Karfin Hali taj yayi da sauri Ya nufi gefen gadon inda su ke a zaune Ya miƙa hannayenshi biyu da niyar ya kawar da ita, Damƙar hannunsa Danish yayi tare da dagowa yana faman lumshe idanun shi tamkar na wanda yasha giya, muryar shi da kasala Ya furta"ina bukatar ruwan da zan yayyafa mata" kusan atare ummi da Taj suka sauke ajiyar zuciya, saboda sunyi tsammanin baya ahayyacinsa ne.


    juyawa ummi tayi da sauri ta fita daga dakin sai gata ta dawo hannunta ruƙe da robar ruwan da ta ɗauko a fridge ta miƙa ma taj, shi kuma Ya kar6a ya Miƙa ma danish, a hankali Ya sanya hannu ya kar6a bayan ya cire murfin ya tarfa hannunsa dake ɗan kerma Ya ɗebi ruwan ya watsa mata akan fuskarta, lokaci ɗaya ta zabura zata fara buge buge da sauri boss Ya damƙi hannunta, tare da dago da ita ya zaunar.


  Wani jiri jiri take gani a idanunta, hannu tasa ta dafe makoshinta tana fadin ruwa ruwa zan sha.


   Kwafa mata ruwan yayi abaki ta rurruke robar duka ta shanye shi, ta dago da luhu luhu idanunta wadanda suka kada jawur da su Sam ta manta a ina take zaune, gani take kamar amafarki lamarin Ya afku, Kwata kwata bata lura da danish ba, wanda ke a gefenta kuma shi ya bata ruwan da ta sha.


  "Unaisah, are you okey? Ina fata bai ta6a lafiyar jikin ki ba"! Cikin kulawa ummi keyi mata magana


Kallon ummi tayi murya na ɗan rawa ta furta"nayi mafarki danish Ya farka, Har Ya shaƙe min wuyana" ta faɗa tana shafa wuyanta


 "Ba mafarki ki ka yi ba, dagaske ne Ya faru, danish Ya farka sai dai baya a hayyacinsa ne lokacin daya shaƙe ki"  boss ne ya bata amsa, da wani irin Hanzari ta dubi danish da ke gefen ta,  idanunsa suna a lumshe numfashin sa na fita a hankali.


Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kukan farin ciki, ta kamo yatsun hannayensa acikin nata, Muryarta cikin shessheƙar kuka take fadin"My man...kana lafiya? jinjina mata kai ya danyi alamar eh.


   "Alhamdulillah Ya Allah, Alhamdulillah..." sakin hannunsa tayi ta sauko daga kan gadon ta zube saman gwiwowinta tare dakai goshi kasa tayi sujjada tana mai nuna godiyarta ga Allah.


 Murmushi taj ya soma saki yana kallon danish, Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e shi mara misaltuwa Yaji dadin farfadowar nan tashi, Har ya fara tunanin haduwar shi da Prime minister.


 Har yanzu Danish babu fara'a akan fuskar shi, jefi jefi Ya ke kallon su da lumsassun idanunsa, ganin lokaci na shirin kure masu yasa ummi ruko hannun unaisah tace su tafi su fara shiryawa, kamar karta baro dakin tana tafiya tana waiwayon danish gani ta ke kamar in ta fita zai koma yar gidan jiya, har sai da boss yace mata zai kira chief yanzu awaya tare da sheikh imam tukunna ta ɗan samu kwarin gwiwar barin dakin.....


   Batare da 6ata lokaci ba, Taj Ya kira chief awaya ya sanar da shi dangane da farfaɗowar danish, A lokacin chief Har Ya kira likitan da zai duba shi,  yayi murnar jin zancen tashin danish, kafin ma karasowar su dakin sai da ya Kira Shiekh Imam suka jira Ya zo falon Kafin suka sauko shi da likitan dayazo duba dashi a tare suka nufi dakin shigar su keda wuya Chief owais ya nufi danish, tamkar dan uwansa na jini Ya miƙa mashi hannu ya taimaka mashi ya sauko daga kan gadon gaba ɗaya yayi hugging dinsa a jikin shi, ya ɗaura hannayensa abayansa yana dan bubbuga shi, har rada yai mashi a kunna ya furta"nayi farin ciki da samun lafiyar ka, Ina fata babu abun da ke yi maka ciwo ayanzu..." ya fada tare da dafe kafadun danish ya dago da shi.


  Babu wanda baiyi farin ciki acikin su ba, Musamman sheikh imam Ya ambaci kalmar alhamdulillah tafi sau a kirga, ya ɗaga hannayensa sama ya dinga zubawa Allah kirari Haɗi da nuna godiyarsa ga nasarar da suka samu, Bayan ya gama ya janyo danish din duk da bai sakar masu fuska ba wannan bai shafe su ba, dama su burinsu ya farfado kuma Alhamdulillah kwalliya tabiya kudin sabulu, Rungume shi shiekh imam yayi tamkar zai mayar dashi cikin sa, ya dinga shafa sumar sa yana karanto addu'o'i yana shafe mashi ko'ina na jikinsa.


Ko da likitan ya duba danish baiga komai ba  sai ma wani abun ban mamaki daya gano wato Lafiyar dake gare shi, har ta wuce wadda hankali zai dauka, babu ko ciwon kai a tare da shi.


Bayan tafiyar likitan shawarwari suka tsaya sunayi atsakanin su, kafin daga bisani chief ya raka shi bathroom don yayi wanka, Kafin ya fito aka shirya mashi lafiyayyan abinci a daki aka shigo mashi da shi, atare da chief suka ci abinci, gwanin ban sha'awa kamar wasu yan uwan juna sai daya tabbatar danish Ya cika cikinsa tukunna ya samu kwarin gwiwar sanar da shi dangane da uncle dinsa dake son ganinsa, ya nemi alfarmar yana so su tafi atare, shiru danish yayi mashi dama yaƙi furta masu magana tun da ya farka kamar wani kurma sai dai yabi su da ido.


  Tarairayarsa suka dinga yi suna lalla6a shi, duk don ya amince, amma ɗan tahalikin nan yai shiru, dabara ce ta fadowa taj da sauri yace mashi a tare da su unaisah zamu tafi da sauran ƴan uwan ka, kuma duk sun amince zasu je.


 Jin ya ambaci zasu tafi da su unaisah ne yasa shi saurin amince masu ta hanyar jinjina masu kai, domin kuwa bazai bari su tafin masa da yan uwansa ba, Murmushi sukayi gaba dayansu ganin sunyi nasara akanshi... Nan fa suka fara shirya shi, kamar wani yarima.


Lokacin da su sajeed suka ji labarin Farkawar danish, Aguje suka watsa da gudu suka nufi bedroom dinshi,  Tsabar farin ciki maimakon suyi dariya saima suka fashe da kuka suka dinga rungumar shi,  Dadi kamar zai kashe su, Shi kanshi yayi farin ciki da ganin su duk da yaki tanka masu sunyi sunyi dashi akan ya bude baki yayi masu magana amna yakiya sai dai fa kallo ko irin sakin fuskarnan babu

Hakan bai wani dame su ba, tun da ya farka falillahil hamdu, duk wannan mai saukin ne, dama sun riga da sun san halin kayan su, bayan sun gama murnar samun lafiyan dan uwan nasu, Ummi ta tattarasu suka koma dakunansu, kowan na su yayi wanka, Suka soma shiryawa cikin kayan su cike da zumudi, bayan haka dangane da abun da ya faru a hall na kashe Hasken lantarki aikin chief owais ne shine ya tsara komai, tare da interior designers da sukayi decoration na hall din saboda yana son yaga reaction din family nasa, bayan ya gama tsara komai, Shi yafara halartar dinner din, ya riga su Unaisah tafiya kamar yadda ya tsara saboda yana son ya fara yi masu hanyar shiga batare da an samu matsala ba, tun da wurine mai tsaron gaske, su boss da big guy ne da wasu daga cikin jami'an isod sukayi jigilar daukar su Unaisah a cikin motocin su, suka kawo su bakin hall din, bayan tafiyar su tuni Ummi ta shirya saboda ta samu amincewar chief akan fitar da za ta yi, taje ne ya nema mata alfarma, Jami'in isod ne yayi driving dinta zuwa gidan da tace zata je na kawarta.


(Wannan shine abunda ya faru kafin zuwansu dinner hall din)


(CIGABAN LABARI)


   Haɗa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...?

 Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh, wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarshi dauke da wani irin annurin farin ciki mara misaltuwa da tafukansa ya tallabo fuskarshi yana bin shi da kallo mai nuni da tsantsar ƙaunarsa, kasa jurewa yayi baisan sa'adda Ya janyoshi zuwa ga faffadan kirjinsa  yai huggin insa tightly kamar zai mayar da shi cikin cikinsa, hannayensa biyu dukansu ya tallabe bayan danish dasu, yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da bugu mai tsanani, wani irin yanayi mara misaltuwa....


  Hakan ba karamin ɗaga hankulan mutanan dake a hall din yayi ba, gaba ɗaya sun ƙara rudewa da ganin rungumarshi da prime minister yayi.


  Muryar Hajiya saratu tamkar zata fashe da kuka ta furta"wai ba zakuyi mana bayanin su wanene ba? Kun barmu atsaitsaye cirko cirkon kamar sakarkaru" ta fada tana kallon chief owais don ta fahimci yasan da zamansu tun da taji Pm hateem ya tambaye shi shine....

  "Owais su wanene wadannan Yaran! "? Baba obie ne ya furta maganar

 

Sai lokacin chief Owais ya soma takowa yana tunkaro wurin da su ke atsaitsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya soma magana genlty


   "A gafarce ni, nayi laifi ban sanar da zuwan su ba....' ya faɗa awayance yana bin kowan nan su da kallo.


   "Idan ba zaku manta ba, na ta6a baku labarin Yaran da Sojin america suka tsinta a evil forest, suka damƙa case dinsu ga hukumar mu ta Isod, ga wadanda basu san da zaman su ba, to ga su nan, sune yaran da nake ruƙo a hannuna, na gayyace su ne don su gana da dangina saboda sun zama tamkar ƴan uwa agare ni"


     Lokacin da ya ƙarasa maganar, hajiya saratu ta zabga salati tana huci ta furta"wlh baka isa ba Owais! Ka haukace ne? da Zaka kwaso mana tsintattun Yaran da ba'asan asalin su ba, ka kawo mana acikin dangi? Anya kuwa kana a hayyacin ka? Rai amatuƙar 6ace tayi maganar, Hankalin su Unaisah ba karamin tashi yayi ba, Masu tsoro acikin su har sun fara Ja da baya jiki na kerma...


A matuƙar firgice Senate Lateef Yace"kana nufin ƴan uwan yaron nan da ya rikiɗa ya koma maciji"? Wannan maganar da senate lateef Ya furtane Yaja hankulan mutanan Hall din, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, Muryoyinsu a kidime suke maimaita kalmar maciji ga wadanda basu san da zancen faruwar lamarin ba, nan take Pravin yayi wuf ya kwashe komai daya faru ya sanar da su, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un shine abunda suke furtawa a bakunansu....


Prime minister sam baya gane me su ke cewa saboda idanunsa sun makance, Ya kurmance baya ji baya gani tunda ya rungumi danish a jikin shi bai ƙara ɗago da kanshi ba, Kamar daga sama yaji an damƙi damtsen hannunsa da ƙarfi aka raba shi daga jikin danish wanda bakowa ne yayi hakan ba face Senate Lateef, ya janye shi gefe guda, Yana faman zazzaga masifa"wlh bazamu lamunta ba! Don Na fahimci bakasan ciwon kan ka ba, taya zaka kwaso mana mugun abu ka kawo mana a cikin dangi? Wannan wata iriyar masiface? So kake ka tarwatsa mana farin cikin mu? Ko kuwa so kake ka ƙarar mana da dangin  mu ne!? Wai ma wanene ya baka shawarar ka kawo su wurin nan....."?


 Tunkafin Senate lafeef ya kare maganar, sautin shessheƙar kukansu Ya soma karaɗe hall din, sun girgiza da jin munanan kalamin da ake fada akansu, bayin Allah da farin cikin su da zumudi su ka zo ganin dangin chief owais sunyi tsammanin suma zasu sosu kamar yarda shima yake son su ashe ba haka bane......'


  "Wallahi sai dai ka za6a, ko dai ka tattara su ku koma can gidanka, ko kuma mu mu fita mubar maka hall din ka ƙare dinner din tare da su, don wlh baka isa ka jazamana masifa ba, wannan ay annobace ka kwaso mana" acewar hajiya saratu ta faɗa tana watsa hannayen ta.


  Chief owais dake sauraronsu ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo daman yasan za'a rina ba lallai su wanye lafiya ba, sai gashi ta tabbata, kowa da abun da yake tofawa, mutane ƙalilan ne basu tanka ba.


   Hankalin Hateem yafi na kowa tashi, ganin za'a raba shi da muradin ranshi, Ga samu ga rashi, Ji yake tamkar Ya fasa ihu, ƙiri ƙiri su Senate lateef sun rurruƙe hannayenshi gudun kada Ya ƙara tunkarar Danish.


    Security advisor din Hateem ne ya tambayi meke faruwa ne? Muryarsa a bubbuɗe yasha ya bugu baya gane komai sama sama yake jin kan shi, Kasancewar basa jin yaren hausa basu san takan zancen ba, da sauri pravin uban Ƴan zigi Ya buɗe baki da niyar Ya sanar dasu, wata irin tsawa mai kama da saukar aradu chief owais Ya sakar mashi, wadda tay matuƙar gigitasu  a hanzar ce yaja baki ya yi shiru.


Dalilin dayasa ya yi mashi hakan gudun kada ya sanar da su, don muddin sukaji da zancen Yaron daya rikida ya koma maciji to kuwa nan take zasu sa a dakatar da taron bayan haka zasu sanya jami'ansu su kori su unaisah don ba zasuyi ganganci da rayuwar hateem ba...


Cikin sanyin murya prime minister yayi ma mutanansa bayani da yaren da zasu gane ya kwantar masu da hankalin su, da cewa family issue ne kuma in sha Allah zasu shawo kan matsalar yanzu, iya abun da ya fada masu kenan, dama kuma ba ahayyacin su suke ba, shiyasa abin yazo masa da sauki da tuni sunsa an tada taron gaba ɗaya.


Da kakkausar murya chief owais Ya soma magana babu annuri akan fuskarshi.


   "ni ne silar dana kawo su wurin taron nan, bawani ya bani iznin in gayyace su ba, kuma basu suka nuna suna son zuwa ba, face don ni nake so su zo...." bai ƙare maganar ba, Hajiya saratu tayi yunkurin dakatar dashi aikuwa a fusace Ya ɗaga mata hannu alamar tayi shiru, Waro idanu waje tayi ba ita ba hatta sauran mutanan hall din sunyi mamakin rashin kunyar da owais yayi.


  "Suma ya'yane kamar kowa! Yaro kuma da bashi da lafiya, Bayin kanshi bane, Aljanu ne suka shafe shi, kuma ya samu lafiya bayan da shiekh Imam ya dau kwanaki Yana duba shi.....' bai ƙare maganar ba, muryar sheikh imam ta karaɗa kunnuwansu a yayin da yake shuowa dakin taron.


 "Tabbas maganar owais gaskiya ne, Yaran nan ba masu cutarwa bane, mutanene kamar kowa, kuma abin a tausayamawa ne....." a tsanake cikin hikma sheikh imam ya fayyace masu komai dangane da halin da danish yake a ciki, wasu sun fahimta yayin da wasu sam kamar kurame basa gane komai.


Gaba ɗaya hall din Ya rikice da maganganunsu, wasu suna hura wutar akore su daga hall din yayin da wasu sukayi shiru basu tanka ba irin su mai girma sharafudden, sun natsu suna bin duk wani mai magana da kallo, ga dukkan alamu akwai abun da suke jira shiyasa suka yi shiru.


 Cikin sanyin murya prime minister yace"dan Allah kowa yakwantar da hankalin shi, Idan har saboda ni aka shirya dinner din nan, to ina rokon alfarmar ku bar su na yau kawai su zauna, in sha Allah ba abinda zai faru" idanunshi akan danish ya ƙare maganar, wanda tun shigowarshi hall din idanunsa suke alumshe tamkar ma baisan sunayi ba, su batool daine suka ruɗe jikinsu sai kerma yakeyi bayin Allah sun firgita.


"Meye amfanin kawo su wurin nan? Inace an shirya dinner din nan ne saboda mu ƴan family ba bare ba! Don haka afitar mana da su idan ana son zaman lafiya, idan ba haka ba mu zamu tattara yanamu yanamu mubar masu hall din" rai a6ace hajiya laurat tayi maganar tana faman haɗe rai.


Runtse ido chief owais ya yi, har cikin ranshi baiji dadin irin tarbar da akayi ma yaran ba, zuciyarshi ta raunana duk sai yaji dama bai sa anzo da su ba.


_Cikin sanyin murya mai ratsa zuciya Unaisah ta soma magana"dan Allah ku yi hakuri idan mun 6ata maku rai, wlh ba mu zo da niyar mu cutar da kowa ba, hasalima ba da son ranmu mu zo ba, face don chief ya nuna yana son mu ziyarci danginsa, ba ku san mu ba, muma bamu san ku ba, bai kamata kuna munana mana zato ba, akan

abun da baku da tabbas akanshi_


tun da ta fara magana hankula suka dawo kanta, Idanu zuru zuru  cike da mamakin karfin halin ta.


 _A hankali ta sanya hannu ta cire facemask din fuskarta tare da jefar da shi gefe ɗaya, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Hankalin maza ya tashi da ganin kyakkyawar fuskar unaisah wadda take a jike sharkaf da hawaye_

 

_Cikin murya kuka taci gaba da cewa"Idan bakusan ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamaki sukeyi yarinya karama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita_


    

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*


 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post