Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 13 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 13 Complete

Novels Elite English


_ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_
سجن القدر💋✊🔥~Takun Ƙarshe🔥~
قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘
Daga alƙalamin Boss Bature💋✊
__________________________✍️

 Cikin muryar kuka taci gaba da cewa"Idan ba ku son ganin mu ba sai   kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamakin ta su ke yi yarinya ƙarama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita, ba karamin jan hankalin su Captain yasir tayi ba, sun kafe ta da idanun su kamar za su haɗiye ta.


    Fashewa da kuka Jemimah tayi muryarta da gunjun kuka ta ke fadin


 "wallahi babu inda zamu je, don baku san wahalar da mu ka sha ba mu ka yi gayu hada gyaran gashi saboda mu nuna maku, shi ne ma zaku kore mu, to wlh ba zamu tafi ba... " a faɗa ce ta faɗa tana nuna su da yatsan hannun ta, Hankulan su gaba ɗaya ya koma kanta, ƴar ƙarama da ita sai masifa, idanun ta sun yi jawur da su, ta harzuƙa, dama ya lafiyar giwa, tsana da tsangwama da zuluncin da akayi masu arayuwarsu ya ɗan ta6a lafiyar kwalwarsu, silar maganganun da ake fadi ayanzu ne ya fara motsa haukan kansu, da sauri Unaisah ta janyo jamimah ta ƙanƙameta a jikin ta cike da fargaban kada ta ja masu jaraba.


 Dafe goshi Azeeza tayi da hannun ta dake kerma kerma cikin wani irin yanayi na jin tsoro da fargaba ta soma magana muryarta da shessheƙar ku ka 


"Inna... lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ni dai mu koma gida, ku mai dani gida, ba su san mu, ba su son ganin mu, za su iya cutar da mu....' ba ta ƙare maganar ba, Sajeed yai hanzarin janyota tare da rufe mata fuskarta jikin laps dinsa.


Sautin shessheƙar kukan su ya cika hall din, mazan cikin su ne kadai ba su karaya ba, sai dai hankulansu ba a kwance ya ke ba, Mom Turai sarkin tausayi zuciyarta ta karaya ita da Hajjaty har sun fara sharar kwalla saboda tausayi ne da su, ga kaunar yaran da ta ɗar su a zuciyoyin su, da ace suna da damar da zasu ja su a jiki su rungume su da kuwa sunyi hakan.

 

   A hankali unaisah ta ɗaura idanunta akan chief owais, mutumin da bata jima da sanin fuskarsa ba, duk da babu kwanciyar hankali atattare da ita sai da taji ya kwanta mata arai saboda jajircewarsa akan su.


   Kamar yarda take kallon shi haka shi ma yake kallon ta, har cikin zuciyarsa bai ji dadin zubar hawayen su ba.


 "ba laifin ka ba ne, abun da akayi mana, sai dai inaso ka sani bakowane zai fahimce mu ba ko ya kaunace mu kamar yadda ku kayi mana, zamu tafi kawai....." ta ƙarasa maganar ƙananun la66anta na kerma ta ruƙo hannun batool da na jemimah har zasu juya muryar Sir mubarak ta dakatar da su.


"Duk da bansan su wanene ku ba, ni dai kun kwanta min araina, kun sace min zuciyata, don haka ban gaji da ganin ku ba, ina yi maku maraba da shigowa family din mu...." a ruɗe su  hajiya saratu suke kallon Sir mubarak, wanda fuskarsa take ɗauke da murmushi yayin da yake kallon su.


Pravin dake ta faman mazurai, jin maganar sir mubarak yasa shi jin bakin ciki da takaici tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, kwata kwata babu kwanciyar hankali a tare da shi, duk ya rasa sukuninsa kamar wanda yayi ma sarki ƙarya, burin shi a kore su daga hall din.


Sheikh Imam dai lamarin nasu ba karamin mamaki yake ba shi ba, kallon su kawai ya ke yi, Sam baiji dadin halin da su ka jefa yaran ba.


"Meye ribar ku idan kun 6ata ran wadannan bayin Allahn? Farin ciki ku ka yi ko bakin ciki da kuka sanya su zubar da hawayen su? Idan ya'yan ku ne a irin halin da ku ka jefa su za ku ji dadi ne? Daga ni har ku bamu da tabbaci akan abunda muke zargin su da shi, don haka yakamata mu kyautata masu zato, sannan shiekh imam yayi mana bayani, babu wanda baisan wanene sheikh imam ba, kuma mun yarda da maluntarka sa, bai kamata mu musa ma maganar shi ba, bayan haka owais jinin mune bazai ta6a kawo abun da zai cutar da ahlinsa ba, idan ma saboda kuna fargaban kada su cutar da ku ne to ku sha kuruminku owais shi ya ke da alhakin da duk wani abu da zai faru" 


 cike da ƙwarin gwiwa Mai girma sharafuddeen yayi maganar babu wasa akan fuskar shi, tuni wasu sun fara shan jinin jikin su.


Matsawa Chief owais yayi kusa da baba obie wanda tun ɗazu bai tanka ba, ruƙo hannunsa yayi acikin nashi, a hankali Ya ɗago suka haɗa ido da juna


   In a calm voice ya furta"banji kace komai ba baba, umarninka kadai nake jira, In har ka nuna bakason su zauna zan koma da su, Idan kuma ka amince babu wanda ya isa yasa subar wajen nan, sai dai mutun ya tafi" ran shi yakai maƙura awurin 6aci 


Lumshe idanu baba obie ya yi yana nazari, na ɗan lokaci yana yanke shawara da zuciyarsa kowa ya ƙagara yaji ta bakinsa domin kuwa shi kaɗai ne zai zartar da hukunci kuma dole ayi biyayya......


Komai dake faruwa akan idanun zahra, tsoro duk ya cika ta ganin rikicin dake shirin 6allewa, tun ɗazu ta 6oye kan ta a bayan su hindu dake a tsaitsaye,  jikin ta sai kerma ya ke yi saboda batason tashin hankali arayuwarta...


Pravin Allah Allah ya ke baba obie yaki amincewa da zaman su a hall din ji yake tamkar ya shiga zuciyarshi don ya  samu damar tunzura shi akan kada ya bar su, jikin shi sai tsuma ya ke yi.Chief owais dake kallon shi amsar shi kawai yake jira, cike da fargaban kada Ya kunyata shi a bainar jama'a duk da yasan abune mai wuya baba obie yayi mashi hakan saboda baya son 6acin ransa.


Gyaran murya yayi hankali gaba ɗaya ya dawo kan shi, kafin ya soma magana yana duban kowan nan su


"Bana son abun da zai cutar da ahlina, sannan bana son duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a zuri'a na...." tunkafin ya kare maganar, munafuki pravin ya soma sakin shu'umin murmushin farin ciki don yasan karshen zancen zai ce ne a kore su.

   

"Bawai don bana son yaran bane, ɗa na kowa ne, sai don ina son mu ƙare dinner din nan lafiya, zaman su acikin mu, ba lallai ya zama alkhairi ba, tun da wasu sun nuna basu buƙatar ganin su,......" da tsantsar mamaki chief owais ya ke kallon fuskar baba obie, hajiya saratu da su laura har sun fara sakin fuskokin su sai kace akan su za su zauna....


Chief bai tsaya jin karashen zancen ba, saboda zuciyarshi ta karaya, a raunace Ya sakin hannun baba obie, ya juya ya kalli prime minister wanda tuni ruwan hawaye sun kwanta luff a idanunsa...


Cikin sanyin murya ya furta"am sorry uncle, banyi tsammanin abun zai kai haka ba, dana san ba za a kar6e su ba da banyi gigin zuwa da su dinner din nan ba, dama nayine saboda farin cikin ka" ya faɗa yayin da yake mayar da idanunsa kan baba obie


  "zan tafi tare da su....'


 yana ƙarasa maganar cikin takun sauri Ya nufi su unaisah, wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskar pravin da su hajiya saratu.


"Owais"!! Har Ya kusa kaiwa bakin kofar muryar Baba obie ta katse shi, Cak ya tsaya da tafiya, dama da biyu yayi hakan don yasan baba obie bazai iya jurar 6acin ranshi ba.


"Meyasa ba zaka tsaya kaji karashen maganata ba"? A hankali Ya juyo yana duban fuskarshi, Nan take murnar pravin ta koma ciki.


Matsawo yayi kusa da shi, fuskarshi dauke da murmushi yace"kamar yarda kayi saboda farin cikin Uncle dinka, Ni kuma saboda farin cikin ka, na amince su shigo ayi shagalin dinner din nan tare dasu, sannan bana so na sake jin wani ya fadi abun da zai 6ata ransu, Umarni ne wannan!!


Yana ƙarasa maganar shi, Chief owais  ya nufeshi, gaba ɗaya yayi huggin dinshi.


rai a6ace hajiya saratu ta nufi hanyar fita daga hall din.


  "Karki kuskura ki fita! Dawo ki zauna" muryar Sir mubarak Ce ta katse ta, tana faman haɗe rai ta dawo ta tsaya hannunta dafe da ƙugu.

   

Damƙo hannun hajjaty pravin yayi, yana faman fitar da huci Yace mata ta biyo shi subar hall din, sam ya manta da hajiya saratu dake kallon shi, ga alama ya fita hayyacinsa, jikinshi duk yayi zufa sai kace babu a.c a hall din


 Muryar hajjaty da tsantsar tashin hankali ta furta"pravin meke damun ka ne? Agaban mutane kake ruƙe hannu na? ina zaka kaini ne? bayan ba agama dinner din ba, dan Allah ka kyale ni" ta fada tana kokarin cire hannunta daga mugun ruƙon da yayi mata.


  Da karfi hajiya saratu ta furta sunansa"pravin!!" ko kallo bata ishe shi ba, ƙoƙari kawai ya ke yi yaja hajjaty don su bar hall din, ita kuma ta dage akan bazata bi shi ba, gaba daya hankulan mutane ya dawo kan su.


  "Nashiga uku pravin, dan Allah ka kyaleni, nace maka bazan bika ba....." gigitacciyar tsawa hajiya saratu ta daka mashi da kakkausar murya mai haɗe da zafin kishi ta furta"ka fara haukane? Agabana kake ruƙe hannun ta? Anya kuwa kana acikin hayyacin ka"


 Ɗagowa ya yi da idanunsa waɗanda suka kaɗa jawur ya dubi hajiya saratu da masifa ya furta"Bai shafe ki ba!" har sai da taji gabanta ya fadi, Su hajiya laura sun saki baki da hanci suna kallon ikon Allah, hatta su Hajiya malikat da su sir mubatak mamakinne ya kamasu yadda ya rufe ido yana jan hajjaty da tsiya yake son fitar da ita daga hall din.


Alhazawan canada suna ta kallon ikon Allah abu kamar a drama, anbarsu a duhu sun kasa gane meke faruwa...


Tsawar da Sir mubarak Ya daka mashi ne yasa shi saurin shiga taitayinsa, A fadace yace"wannan wani irin shashanci ne? Baka da hankali ne? Ina ruwanka da ita? Tun da ta nuna batason tafiya ka ƙyale ta mana!"


Kallon hajjaty pravin yayi idanunshi jawur yana huci ya furta"idan har baki bini mun koma gida ba ranki zaiyi mugun 6aci, wlh kada ki bari na riga ki fita daga hall din nan" yana fadar hakan Ya juya tamkar mayunwacin zaki Ya nufi kofar fita hall din cike da sa ran hajjaty zata bi bayan shi, sai dai har ya fuce babu alamun zata bishi, kamar an ruƙe ƙafafuwanta, hakanan taji ba ta son tabi shi, taji kunyar abun da yayi mata, agaban jama'a, tasan dole adasa masu ayar tambaya, ita kanta a ruɗe take batasan dalilin dayasa pravin ya rikice mata ba, Hajiya saratu yau taga abunda yafi karfinta, tamkar a mafarki take ganin komai, akan idonta pravin ya ruƙe hannun hajjaty bainar jama'a batare da ya ji tsoronta ba, lallai zai fuskanci horo mai tsanani daga gare ta, har ta ita kanta hajjatyn yaja mata bala'e domin kuwa bazata ƙyale ta ba, ransu twins su yayi mugun 6aci musamman zayn shi da yafi zuciya......


Bayan hatsaniyar ta lafa, senate lateef ya dubi su unaisah "tun da mahaifinmu ya yanke hukunci akan ku zauna, ba mu da ja, ya zamar mana wajibi mu tarbe ku, amma kafin nan ku sauke facemask dake akan fuskokin ku" ya fada yana nuna faces din su.


Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su.


"Kamar ka shiga zuciyata, nima abun da nakeso nace kenan, gaskiya ba zamu bari ku shiga da wannan face mask din ba, yakamata mu ga fuskokin ku," tun da aka fara rikicin nan sai yanzu his excellency abdul razak ya sanya baki,


  His excellency deen yace"to nima dai abuɗe min inga fuskokin nan, ko hankalina ya kwanta" ya fada da ɗan murmushin kan fuskarsa.


A hankali Batool ta ɗaura yatsun hannunta da ke kerma ta ruƙo face mask din ta yaye shi daga kan fuskarta, Har saida gabansu ya fadi da ganin kyawun fuskarta, wato wani guntun murmushi da tayi ta sunnar da kanta kasa ba karamin tafiya yayi da imanin su ba, wasu tuni sun fara danasanin sanya su kuka da su ka yi.


Bayan batool ta cire nata, Sajeed Ya zame face mask din fuskarshi, tsabar kiɗima da ganin fuskarshi yasa hajiya laura ɗan zaro idanunta ga dukkan alamu akwai wani abu da ya ruɗe ta da shi, kyawun sajeed ba ƙaramin tafiya yai da imanin su ba.


"Saura ku, Ku cure naku mu gani" Zaki  ne ya fada yana nuna sauran


Sajeed ne ya taimaka wurin Cire ma Azeeza nata, Duk tabi ta ƙanƙame shi, fuskarta tayi sharkaf da hawaye har wani zazza6i ya lullu6e ta, ganin fuskar Azeeza ya yi matuƙar razana Sir mubarak har sai da ya kalli fuskar Mom turai, ba shi ba, hatta Dr jazz da su Ibad kusan a lokaci ɗaya suka jefa wa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar mamaki da al'ajabi.


Jamimah dake a maƙale jikin angel, babu alamun zata motsa, ruƙo hannunta Angel tayi tare da cire mata mask dinta, fuskar ta 6aci da hawaye hada majina hakan yasa basu samu damar ganinta da kyau ba.


Kusan atare Javed da Haris suka tu6e nasu face mask din, Kallon kallon aka komayi atsakanin Iyalan obinna kowa da abun da ya ɗaure ma shi kan shi.


"Parveen ku cure naku" cikin sanyin murya Unaisah tayi masu magana


Batare da 6ata lokaci ba, Parveen ta cire nata mask din, wani irin bugu zuciyar hajiya saratu tayi, haƙiƙa ta razana da ganin kamannin ta dana yarinyar, har sun 6aci kamar tayi kakin ta, banbancin su launin fata, ba ita ba harta sauran matasan family din da iyayan mamakine tsantsa akan fuskokin su...


Lokacin da Naufal ya cire mask din fuskar shi, wata irin firgita hajjaty tayi, har sai da ta dafe saitin zuciyarta da ke yi mata wani irin mahaukacin bugu, tagaza yarda da abun da idanuwanta suke gane mata, gani take tamkar mafarki ne ba gaske ba, domin kuwa ita dai tasan wanda ya mutu baya dawowa, harta su Hajiya Muhibbat sai da suka saci kallon fuskar hajjaty da ta naufal saboda wani abu daya ja hankalin su....


Gaba ɗaya sun rikice Sun ruɗe, sun gaza gasgata abunda idanunsu ke nuna masu


Tamkar an kulle masu baku nan su, Sun kasa magana, Lamarin ne yafi karfin tunanin mai tunani, mamakin su tayaya akai yaran suke bala'en kama da ƴan family din su?


 _Ba zata juri bugun da zuciyarta ke yi mata ba, da azalzalarta akan son ganin fuskar yaron da hateem ya kwallafa rai akanshi, tabbas tana son ganin shi, kowa na gurin burin shi Danish ya cire mask din fuskar shi, sunyi matuƙar ƙagara da son ganin sa, walking gently gimbiya mujeedat ta tako ta tsaya gab da inda danish yake atsaya kamar mai wani nazari abu akanshi, idanunshi na kallon kasa sam bayason hada ido da kowa_


 Sanya hannu tayi ta cire mask din dake akan fuskar shi............


Kiris ya raga zuciyar gimbiya mujeeda ta daina bugawa saboda razanar da tayi, gaba ɗaya hankulan su ya dawo kan shi, Wani irin mugun bugu zukatan su suka soma yi, yadda kasan ana dakan sakwara, Gaba ɗaya suka zazzare idanunsu gami da buɗe bakunansu saboda tsabar kiɗima kamar sun ga wani mugun abu, wato Sun gigita sun razana da ganin wanan abin al'ajabi da yai matuƙar Ɗaga hankulan su, Afirgice Chief Of Staff Na canada Ya dubi fuskar Security Advisor da wani irin ruɗani akan fuskokin su, at same time su ka yi saurin kallon Prime minister Hateem, Baba obie kuwa kusan suman tsaye yayi da ganin wannan Kama ta ban al'jabi, Senate lafeef da su His excellency sai faman jinjina kan su suke yi sam sun gaza magana kamar kurame, sai yanzu suka gane dalilin dayasa hateem ya firgice ma su da kaunar yaron ashe shi yasan abun da ya gani, Kai kowama dake a wurin ya rasa lissafin kwalwarsa saboda ganin fuskar Danish, Wai shin Ina Nazli? Ay tun da tayi tozali da danish tsabar firgici da ruɗani yasa har batasan sa'adda ta saki wayar hannunta ba, gaba ɗaya ta kife kan flloor, Jikinta ya kama kerma kerma tana faman zazzare eyes din ta akan fuskar shi yadda kasan twin brother din ta. 


 saboda ruɗu tunani su ka yi ko dai Nazli ce ta koma inda danish yake atsaye hakanne yasa sukayi Saurin kai idonsu inda take atsaye don suga idan tana nan, Ganinta yasa suka ƙara rikicewa.


  Security adivisor ya kasa samun nutsuwa saboda al'ajabin da ya kama shi, Muryar shi na rawa rawa yana tangyadi cikin harshen turan ci yace" dama prime minister yana da wani ɗane da ba mu san da shi ba, ko kuwa ƙaninsa ne? Ko dai giyar dana sha ce takai mun karo? Pls ku yi min bayani yadda zan fahimta.


   Senate lateef ne ya bashi amsa da cewa"ba su haɗa alaƙar komai ba, kama ce kawai" babu alamun za su gasgata maganar shi.


"Abun da ɗaure kai, amma ya ya akai su ke bala'in kama har haka? Kamar an yi photo copy din fuskar Hateem, ko ma ince Nazli" his exellency Deen ne yayi maganar, Yazrin sam takasa samun nutsuwa Sai kallon shi take yi ko ƙyaftawa babu, wato danish ya girgiza su da kyawun shi, Hankulan su Faryat ya tashi haikam tsabar yadda su ke kallon shi kamar za su haɗiye shi, yadda kasan irin kura taga naman nan.


Haƙiƙa sun rudu da prisoners, babu wanda bai yi mamakin sanyin kyan su ba, da al'ajabin kamanceceniyar su da ƴan uwan su yadda kasan ya'yan cikin wasu daga cikin su tsabar yadda kamannin su ya bayyana da juna...


Ganin kallon nasu ba mai ƙarewa ba ne  gashi sunbar yara atsaitsaye, da sauri Ziyad ya ce


"Lokaci yana tafiya, yakamata acigaba da shagali"


kafin Ya ƙare maganar sautin waƙa mai ratsa zuciya ya karaɗe cikin hall din, Ɗaya bayan ɗaya Suka juya suna nufar wurin zaman su kowa da abun da yake saƙawa a cikin zuciyar shi.


Hateem kamar jira yake yi a samu maslaha, jiki na rawa ya nufi danish ya ruƙo hannun shi acikin nashi, burin shi su haɗa ido don su kalli juna dakyau amma yaƙi bashi damar hakan, murmushi ne dauke akan fuskar sharafudeen sai faman kallon su ya ke yi, yaji dadin ganin hateem a irin wannan yanayin.


Da zolaya yace irin wannan kallo haka? Ka da fa ka lashe mana yaro" ƴar dariya hateem yayi,


Chief owais da ke kallon su ba karamin kwanciyar hankali ya samu ba ganin ya faranta ran uncle din sa


"Uncle ka tafi da shi, zaman shi anan bazai yiwu ba, saboda baya son hayaniya, kuma baya son ana kallon sa, From now until nightfall, I entrust him to your care" wani irin farin ciki ne ya ƙara lullu6e prime minister, kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, cikin sanyin murya yake fadin"nagode owais, wlh ka gama min komai, bazan ta6a manta alkhairin ka a gare ni ba, Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" addu'o'i ya dinga zuba mashi, bai manta da sheikh imam ba wanda ke atsaye tun dazu murmushine akan fuskar shi.


"shukran jazeelan Ya sheikh, Allah ne kadai zai iya biyan ka, saboda babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani da su wurin yi maka godiya" ya faɗa yana ruƙo hannun sheikh imam gaba ɗaya wani irin annurin farin ciki ne akan fuskokin su.


Unaisah da ke ta sauraron su aranta Allah Allah take Danish ya amince da buƙatar chief yabi prime minister don tasan halin shi da kafiya ba kowa ke iya tankwara shi ba.


Kafin ta ƙare zancen zucin nata ba, da mamaki taga danish yabi prime minister hannun su ruƙe cikin na juna suka nufi hanyar fita daga hall din ko irin ya waigo ya kalle su baiyi ba, ajiyar zuciya ta sauke, sarai ta fahimci masu satar kallon ta.


 gimbiya mujeedat sai bin su da kallo take yi, tarasa ma wani irin tunani zatayi game da bawon Allan nan mai tsantsar kama da Nazli, kasa jurewa tayi da sauri ta bi bayan su, ita ma Yazrin ta bi su, Nazli ce kaɗai ba tayi yunkurin bin su ba, kwata kwata babu annuri akan fuskarta, Ita bakomai ne damuwarta ba face abu biyu, na farko yaron da ke kama da ita! arayuwarta ta tsani ace wani yana kama da ita, saboda izzarta, tafi so mai nata ya kasance ita kadai ke da shi, bayan wannan sai Unaisah! Hankalin ta bai kwanta da ita ba, saboda wani kallo da taga sun jefa wa juna a tsakanin ta da chief owais nan take taji bata son ganin yarinyar, Nazli tana da zafin kishi, izzarta ce ke hanata bayyanawa.


    Fuskarta babu annuri ta kai hannu ta dauki wayarta dake kan floor, da wani irin takun qasaita ta juya tabar wurin su.


 Mom turai da ke ta kallon su tun ɗazu take son tunkararsu ganin babu dama ne yasa ta yi shiru tana kallon badaƙalar da ake yi, yanzu kuwa da ta samu dama, Da sauri ta nufi wurin Azeeza saboda sun bata tausayi da suna kuka, hanky ta zaro daga purse dinta, ta zuƙunna agaban ta tare da sanya shi kan fuskarta ta shiga share mata hawaye 


Cikin kulawa tace "Stop crying kin ji ko? everything is over now, we are welcoming you to our family" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyinsu har sun fara ɗan sakin jikin su.


  A hankali Sir mubarak Ya nufi Jemimah dake a maƙale da Angel ta cukuikuiye mata rigarta zukunna yayi agabanta, ya ruƙo hannayenta a cikin nashi yana rarrashinta ganin har yanzu tana shesshekar kuka. 


  "Sorry baby girl, share hawayen ki...."


 muryarta na rawa ta furta"wlh baku son mu, shiyasa ku ke korar mu, ni dai gida zan koma Allah" a fadace ta faɗa tana faman zabga masu harara, ƴan kumatunta sunyi jawur da su.


Ba zato ba tsammani Taji Sir mubarak Ya dauketa dungurum Ya daurata kan kirjin shi, wuƙi wuƙi tayi da idanunta.


"Sai mu ga da wasu kafafun zaki koma gida, ay tun da ki ka shigo wurin nan sai mun ci abinci dake, idan kuma mutun yace zaiyi min rigima zan sanya bindiga ne in har be mashi tsakiyar kan shi"


 Ya fada Yana daura yatsan shi akanta, Murmushi kowan nan su ya dan saki.


  "Bismillah ku shiga daga ciki mu zauna, ko baku gaji da tsayuwa bane"


Zaki ne yayi maganar Yana nuna masu cikin hall din, su kansu so suke su zauna kafafuwansu har sun fara ruƙewa kawai suna fargaban shiga ne.


Ganin hakan yasa zaki matsawa ya ruƙo hannun Sajeed Dana Naufal Ya shiga da su cikin hall din, Da sauri Dr Jazz Ya matsa Cikin su ya ruƙo hannun javed dana haris yayi ciki da su.


Bayan mom turai ta gama sharewa azeeza hawayenta, ruƙo hannun ta tayi suka nufi table din su.


babu wanda yayi tsammanin Hajiya malikat zata tanka, don tunda aka fara rikicin bata sanya baki ba, sai yanzu data matso kusa da su ta ɗan saki fuskarta tana fadin"naga kowa dan uwansa yake dauka nima bari na dauki nawa" ta fada tare da ruƙo hannun Unaisah, ta haɗa dana batool dake a gefenta"mu shiga ciki Ƴan mata,"  wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da sauri suka bi bayan ta, chief owais dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa sai kallon su ya ke yi, hankalin ya kwanta babu sauran damuwa.

    

   "Toh, ni ma dai bari na dauki nawa ƴan matan" hajiya madina ce tayi maganar da fara'a akan fuskarta ta ruko hannun Parveen da na hannah, ta nufi wurin zaman su da su, gaba daya sun koma ciki, hatta su Hajiya saratu kowa Ya koma mazaunin su wasu suna daga tsaye har yanzu hankalin wasun su bai kwanta da yaran ba, Abunne ya daure masu kai sun gaza samun sukuni a fakaice su ke satar kallon su.


 Tuni Daddy sharafudden yayiwa sheikh Imam mazauni a wurin su, umarni aka bawa servers din dake awurin akan su kawo masu abin da zasu ci, nan fa suka fara aikin jera masu abinci kala kala da abin sha shaƙe da table...

 

Wata irin nauyayyar zuciya jemimah take ta faman saukewa, mom turai da sir mubarak sun tasa su agaba sai faman tarairayarsu su ke yi, kamar ƴa'ƴan cikin su.


"Me ku ke son ci"? Cikin kulawa tayi masu maganar.


 Jemimah ce tai kokarin bude baki tace"komai ma muna ci" murmushi mom turai tayi, ba karamin burgeta su ke yi ba, 

   

    "Ko kin lura yaran nan suna kama da ke? Kamar ƙannan Jazz saboda sunyi kama da shi kan shi" murmushi tayi tana kallon Sir mubarak da yayi maganar.


  "Nima nayi mamakin kamannin mu" ta fada idanunta akan fuskar Jemimah da azeeza, wadan da tuni suka fara cin abincin da aka kawo masu.


6angaren Su Hajiya saratu kuwa, sun kasa sun tsare sai jifar Parvin take yi da wani kallo mai wuyar fassaruwa, dama su biyune hajiya madina takai su tebur din su, ita da hannah wadda jikin ta keta kerma

   "Baki da lafiya ne"? Hajiya laurane ta jefa mata tambayar fuskarta a yamutse, girgiza kai Hanna tayi, ta6e baki tayi"to meye kike ta kermar jiki! Tun da kun riga da kun samu wurin zama, ay sai ku saki jiki kuma ku kwashi arziki" ta fada tana hura hanci.


  "Please ni ban kawo su nan da agaya masu magana ba!" Hajiya madina ce ta fada tana mai nuna 6acin aranta, kafin ta mayar da dubanta ga su parveen


   "Ku ci abinci mana" da sakin fuska tayi masu magana, parvenn kamar jira takeyi aikuwa ta dauki glass of juice ta fara sha, tana shanyewa ta soma cin fruit salat, bayan ta gama ta koma tana cin spring rolls, ɗan zaro idanu hajiya saratu tayi tana kallon ikon Allah, yadda kasan irin kwancen yunwar nan, 

 Hajiya laurat tace"ba banza ba naga tayi kama dake ashe itama din acici ce" ta fada da zolaya tana yar dariya, parveen dai ko kallo basu ishe ta ba, ta dage damtse komai ci take, har kwara hannah a hankali take dan cakura tana ci

   "Wai ni ka ɗai ce nake mamakin kamannin yaran nan da family din nan"? Hajiya madina ce tayi maganar,

  Hajiya saratu tace"hmmm, ay ni abun ya gama ɗaure min kai, har yanzu zuciyata ta gaza samun nutsuwa, na ruɗe musamman dana ga yaron nan mai kama da hateem" lumshe ido Hajiya laurat tayi tunawa da surar shi don ba karamin tafiya yayi da imaninta ba.


  Hajiya muhibbat tace"na girgiza da ganin shi, lokacin da mujeeda ta cire masa mask din fuskarshi araina sai da nace wannan kyau haka kamar ɗan sarkin aljanu? Dariya su kayi gaba dayan su


  "Ay tun da nayi mashi kallo ɗaya na kau da ido, saboda wannan kyan nashi kadai ya isa yasa mace fadawa ga halaka" acewar Hajiya laurat


      "Ina kananun Yaran nan ƴan mata masu kama da tagwaye, wlh yadda kukasan Hajja turai tayi kakin su, Ƙaramar fuskarta da komai kalar nasu ne, sai kuma wani mai kama da hajjaty kamar anyi photo copy din fuskarta acewar Hajiya mudeena.


   "Nima na lura da su, amma fa ni duk ba wannan ba, Yarinyar nan ta burge ni, kwarin gwiwarta ya tafi da imani na....".hajiya muhibbat ce ta yi maganar   tana kallon can cikin hall din inda su unaisah su ke

      

  Duk wannan suratan da su ke yi, akan kunnan su Parveen sai dai sam basa ganewa hankalin ta na kan abinci ci, hajiya saratu sai faman satar kallon ta ta ke yi afakaice, tun parven bata lura ba har dai ta gano ta, da zarar ta ɗago suke haɗa ido da juna.


_________________________💞


Gyaran murya Zaki yayi masu, a tare su ka dago suna kallon shi,


"Kunyi shiru baku faɗa mana sunayen ku ba"


  Murmushi sajeed ya ɗanyi 


   "Ni sunana sajeed, shi kuma ɗan uwana Sunansa Naufal"


  "Masha Allah, It's a pleasure to meet you both, I hope you will feel at ease with us, sannan ku dauka tamkar ƴan uwan ku ne mu" jinjina mashi kai su ka yi alamar eh.


  "Okey, Yanzu ina so ku bani mamaki, ku cinye wannan abincin da nasa aka kawo maku" dariya su ka yi gaba ɗayan su, har cikin ransu sunji dadin tarbar da zaki yayi masu.


       Nan fa suka saki jiki suka soma cin abinci.


 Ɗagowa zaki yayi tare da kallon Su captain, yayi mamakin ganin yadda suke dogon wuya suna leƙen table din su unaisah.


  Da zolaya yace"kun dai ji kunya wlh, ina ajin naku yake"?


 dariya ziyad yayi yana fadin"wlh yarinyar ce ta tafi da imanina, ni ka gane bawai sonta nake ba, wannan ay tafi karfin ɗan jarida, kawai dai kamar nasan fuskarta, sai dai narasa gane a ina nasanta, abun ya shige min akaina...." 


  Daƙyar captain Yaseer Ya janye idonsa daga kan fuskar Unaisah.


 "Nifa ina ji zan canza sheƙa ne, wlh ko da dukiyata zata ƙare ne akan neman waccan yarinyar saina jaraba sa'ata..." justice na murmushi yace"karka soma wlh, domin kuwa iskace zata wahalar da mai karan kara, ay ni tun daga kan kallon dana ga chief yanayi mata raina ya bani cewar da akwai wata aƙasa"


  Kwa6e fuska captain yayi"kana nufin yana sonta"? Dage mashi gira Justice yai.


 Yatsina fuska yayi"again, bayan ya kwace nazli, ga kuma wata, mata biyu kenan zai aura!" 


     "Ni duk ba wannan ba ma, ganin yaron nan mai suffar lu'u lu'u yaɗan girgiza ni, wai ku bakuyi mamaki ba? Ziyad ne ya fada.


  "Ay mamakinne yasa ka ji munyi shiru da zancen shi, domin kuwa kwakwalwa zata iya daina aiki" dariya su ka yi jin abun da Justice yake fadi.


  "Gaskiya nayi mamaki ace wai yaron nan a daji aka tsince shi, ay hankalima bazai dauka ba, kai daga ganin zubin halittarsa ɗan wani ne, shiyasa nifa gaba ɗaya na ruɗe da lamarinsu, kaina a duhu yake, kamanninsa sun 6aci da Uncle Hateem kamar yayi kakinsa kuma gaskiya ina kishi da shi Allah" captain ne ya fada.


  Sajeed dake sauraran su murmushi ne dauke akan fuskarshi, Naufal Kuwa gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa saboda kallon da hajjaty take mashi, Da zarar Ya ɗago da idanun shi karaf suke sauka acikin nata, saboda shi ta baro wurin da take ta dawo kusa da table din dake fuskantar nasu ta zauna tana ta kallon shi, ko kyaftawa babu.


        Cikin muryar raɗa yace da sajeed "waccan matar sai kallo na take yi kamar zata haɗiye ni, taƙi bari naci abinci cikin kwanciyar hankali, bansan me na tsare mata ba, ni fa duk na tsorata" da sauri sajeed ya saci kallon inda naufal ke nuna masa ganin hajjaty yasa shi yi ma naufal rada"ka kwantar da hankalin ka, saboda kana kama da ita ne shiyasa take kallon ka"  ya fada yana ƴar dariya, shi dai naufal hankalin shi yaƙi kwanciya, kamar anyi mashi dole ya kalle ta.


 Hakanan take jin shi a zuciyarta, komai nashi sak kalar na yaron ta, bazata ta6a mantawa da suffar shi ba, abinne ya daga hankalinta, ya kuma tada mata tsohon Ciwon dake kwance a cikin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face yaronta da ta rasa tun farkon zuwan su nigeria wannan wani labari ne wanda sai nan gaba kaɗan zamu ji shi...🥺


Dr jazz sai Rawar kai yake yi da su Haris, kamar kannansa, Ya tasa su agaba shi da ibad sai fira suke jan su da shi.


    "A cikin ku wanene Haris"? yai tambayar yana duban su, da yake yana fuskantar su, da sauri Javed Ya nuna haris," ɗan zaro idanu Dr jazz yayi"masha Allah, kaine haris kenan"? Jinjina mashi kai haris yayi alamar eh, da biyu ya tambaye shi saboda yasha jin labarin shi awurin deeja, tana yawon yin sambatun sunan shi idan haukan ta ya motsa.


  Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi yana fadin"kun burgeni, ina kaunarku, ganin ku kawai da nayi kun kwanta min arai na" murmushi kowan nan su ya saki.


  "Wlh nima Na kamu da kaunarsu, dan Allah ku dawo gidan mu da zama, dama ni bani da abokai a nigeria" ibad ne yayi maganar da yar shagwa6ar shi.


   "Kun ƙi sakin jiki damu, ko dan baku san mu bane" kallon juna haris da javed su ka yi, sufa basu saba mu'amala cikin mutane ba.  "Okey, yanzu bismillah mu fara cin abinci"


  Atare suka soma cin abincinsu, jefi jefi Dr jazz yake satar kallon Haris Aranshi ya ayyana duk ranar da khadeeja ta yi tozali da shi ba karamin hauka zatayi ba.


  "Yaya jazz, wadancan twins din sunyi kama da mommy da kai," ya faɗa yana nuna su azeeza.


 Murmushi jazz yasaki shi kanshi ya kamu da kaunsarsu, tun dazu yake ta faman satar kallon su, ji yake tamkar kannansa na jini.


 "Please Ya jazz mu yi wa daddy magana, akai mana su gidan mu, ni wlh bana so suna kuka, kaga mom saratu da waccen tsigai din ko ina ruwansu da rayuwarsu, ni fa shiyasa bana son zuwa nigeria saboda su, ko gajiya da masifa basayi, ina ruwan su da ƙaddarar rayuwarsu? Su ne suka tsara ma kan su ne? Ni fa kaganni ya jazz ba ruwana da shiga sabgar wani ko in wulakanta sa, wai don basu da asali, sai kace an gaya masu daga sama suka fado, mutun dai ay sai an haife sa yake xuwa duniya ba daga sama aka wurgo saba, balle ace da rashin asali aka haife su," Rai a6ace ibad yakeyin maganar da zallar shagwaba.

 

Su haris sun saki baki suna kallon shi, komai nashi burge su ya ke yi, ganin suna kallon shi ne yasa shi dakatawa da maganar yana yar dariya yace"na cika ku da surutu ko"? Girgiza mashi kai su ka yi alamar a'a.


Hankalin Zahra Yaƙi kanciya, bakomai ne yajawo hakan ba face Unaisah, ko kwanto takeyi kamar tasan ta, sai dai takasa gane a ina tasan fuskarta, sai yanzu ta samu damar kare mata kallo daga inda take azaune, duk wani motsin unaisah akan idon zahra, ta kwallafa rai akan son yin magana da ita dama kawai take jira....


Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin nauyin haɗa ido da chief ba, tun da suka zauna ta sunnar da kanta tana wasa da yatsun hannayenta, ƙamshin turarensa gaba ɗaya ya cika mata hanci, duk wannan abun da take yi chief owais na lura da ita, da yake suna fuskantar juna da shi, wayarsa ce ruƙe a hannunsa da yake daddanawa cikin nutsuwa.


    Ga jerin kayan abinci da aka shaƙe masu table da shi amma takasa ci, ga yunwa tana ji.


    Gyaran muryar da Hajiya Malikat tayi masu ne yasa suka dago a tare suka kalle ta, tana daga zaune gefen chief

    

    "Nasa an kawo maku abinci kun ƙi ci, meyasa?"cikin kulawa tayi ma su maganar.


  Murmushi suka dan saki suna faman noƙe kai.


   "Ko dai Kunyar Chief ku ke ji" kamar ta shiga zuciyar su, murmushi tayi ma su


   "Ku ci mana, hankalin shi ba akanku Yake ba" 


  Batool ce ta fara cin abincin ganin zata sanya hannu yasa hajiya malikat cewa"ki ɗauki tsokali" muryarta na dan rawa tace"ban iya ci da shi ba"


  "Okey, nagane ki sanya hannun" 

Hannu tasa ta soma ci, unaisah kuma ta ɗauki glass na lemu tana ɗan kur6an shi sama sama take satar kallon fuskar chief owais da zarar taga zai ɗago da idanunsa take yin saurin kau da nata gefe ɗaya, bakomai ne yaja hankalin ta gare shi ba, face kamanninsu da Danish, kusan komai nasu iri ɗaya banbancin su kaɗan.


Mai girma sharafudeen ne ya nufo wurin su, fuskarshi da fara'a Ya samu wuri ya zauna yana dubansu, da sauri suka gaishe shi cikin girmamawa ya amsa masu.


  Duban owais yayi"baka cika min alkawari na ba" ya faɗa yana ɗan haɗe fuskarshi.

     Dagowa chief yayi tare da kallon daddyn nasa, da alama bai fahimci me yake nufi ba

    "Maganar da mu kayi dakai ɗazu da safe"

  Sai yanzu ya fahinci inda zancen daddyn nasa ya dosa.


     A hankali ya ɗaura idanunsa kan Unaisah dake kur6ar lemu.


    Murmushi hajiya malikat tayi 

 

"tubarakallah Masha Allah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina da lafiyana, gani ga second in-law ɗina, yarinya mai hankali da nutsuwa, ni dai surukan nawa duk kyawawa ne, ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa...." amsa mata yai da ameen.


Ga dukkan alamu unaisah bata fahimci takan zancen ba, ta dai ji ana zancen suruka, Ruƙo hannunta daddy Sharafuddeen yai a cikin na shi fuskar shi dauke da murmushi yace"I'm so happy to meet you, my daughter-in-law, I don't even know how to describe the joy I feel just from seeing you today"


murmushi tasakar masa har dimple din ta lotsa, duk da batasan wanene shi ba, ranta yana bata cewar Mahaifin Chief ne saboda kamannin su da ga gani.


   Muryarta cike da jin nauyin shi ta furta"nima naji daɗin haɗuwa da kai,"


"Shekarunki nawa ne"? ya jefa mata tambayar.


 "Sha shida amma na kusa shiga ta sha 17"

  A wayance Daddy sharafuddeen yace"Wonderful, Now, what about your studies?

 

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta amsa mashi tambayar da yayi mata ba.


 "Sorry kada daddy ya takura maki da tambaya ko"? Murmushi ta ɗanyi masa.


  "Inaso ne nasan me yakamata mu fara yi don tallafa ma rayuwar ki, ko ba haka ba" cike da rashin fahimtar kalamansa take duben shi, Hajiya malikat dake kallon ta murmushi ne dauke akan fuskarta, yarinyar ta kwanta mata aranta.


       Chief owais ya nutsu yana sauraron su.


    "Aure ko karatu wanne kika fi so a yanzu" waro mashi gray eyes dinta tayi da sauri ta sanya tafin hannu ta rufe fuskarta alamar taji kunya, hakan da tayi ba karamin dariya ya basu ba, hatta chief saida yayi murmushin gefen fuska.


Hankalin batool gaba ɗaya baya akansu tun da ta samu abinci take ta aikin ci.


"Kinyi shiru baki ban amsa ba" ya ƙara tambayarta, ƙasa ƙasa da murya chief ya furta"dad..." dakatar da shi daddy sharafudeen yayi"no kada ka shiga tsakanina da surukata, baby Angel ke nake sauraro," tayi mamakin jin ya ambaci nickname dinta, ba tare data buɗe fuskarta ba tace"Aure zanyi kafin na cigaba da karatu"


  Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa da zolaya yace"ta kwana gidan sauƙi, yanzu faɗa min kina da saurayin da zaki aura ne ko babu" 


 da sauri hajiya malika tace"haba dan Allah, kabarta mana, miji ay ta riga da ta samu ko ba haka unaisa"? Ɗaga mata kai tay alamarh.


Duk wannan abun dake faruwa a tsakanin daddy sharafudeen da Unaisah akan idanun Nazli wadda tuni tagama cika ta batse ranta yayi mugun 6aci tamkar ta ɗaura hannu bisa kai tayi ihu, wani irin kishine Ya ziyarce ta ganin yadda chief owais yayi zaman shi a wurin yarinyar, tun zuwan su hall din bai tako yazo inda take ba, kamar ma baisan da zamanta ba.....

Bazata juri kallon su ba, miƙewa tayi da niyar tabar hall din kamar daga sama muryar Faryat ta katse mata hanzarinta.


 "sister Nazli, Ina zaki je ne bayan ba'a kammala taron ba"!


  Ba tare da ta kalli faryat ba tace"bazan juri zama ba, sai nake ga kamar ba don mu aka shirya dinner din nan ba, because everyone's attention is focused on them. Daddy Ya tafi da wani wanda bamusan wanene shi ba and the chief is only paying attention to that girl." ta faɗa tana nuna saitin inda unaisah ta ke da hannun ta.


 Ruƙo hannunta faryat tayi a cikin nata" Sister, ba ke ya kamata ki bar hall din ba! They are the ones who should leaves"


 Girgiza kai Nazli tayi"no ni bana son hatsaniya, barina shi yafi min kwanciyar hankali"


Ta faɗa tana kokarin kaucewa rukon da faryat tayi mata.


 Sai dai taki bata damar tafiya

 "Nasan menene ya 6ata maki rai sister, ba ke kaɗai ba, mu ma ran mu ya 6aci da zuwansu saboda babu alkhairi atattare dasu, gaba ɗaya hankali Ya koma kansu, Amma ni na maki alkawarin zan kawar da yarinyar can daga hall din nan, indai hakan zai kwantar maki da hankalin ki, amma bai kamata ki tafi ba, ba zamu ji dadi ba" shiru Nazli tayi na ɗan wani lokaci kafin ta ɗan sauke ajiyar zuciya.


 "What are you going to do to her I hope you won't hurt her."?


 Shu'umin murmushi faryat tasaki, 


"Don't worry sister, I won't hurt her. I'll just keep her out of sight until the dinner is over."


"Bana so a samu matsala faryat!"


'kawai kibar komai a hannu na, abun da nake so dake da zarar kinga babu yarinyar kiyi kokarin jan hankalin Yaya owais" 


 A hankali Ta furta Okey, fasa fita tayi da sauri ta juya ta koma wurin zaman ta.


Faryat kuwa ba karamin dadi taji ba, dama ta tsani ganin unaisah, tun farkon shigowarsu taji bata yi mata ba, da sauri ta koma wurin su Yusra tana jiran ta samu damar da zata aiwatar da mummunan kudurin ta........


Bayan kammala cin abinci, Mc Ya Kira su ɗaya bayan ɗaya suke hawa saman step suna taka rawa, sautin kiɗa Ya karaɗe ko'ina na hall din, Ta ko'ina hasken camera ne ke Ƙyalli, sai daukar hotuna sukeyi, abun ba karamin burge prisoners yayi ba, Ay tuni Sajeed Ya miƙe dama ta samu tun da ya shiga filin Ya fara taka rawa hankalin kowa ya dawo kan shi, harta su baba obie da suke atsaitsaye hankalin su na akan shi, abun a jininsa yake da zarar yaji kiɗa bai iya jurewa kamar ana kada mashi mazari, In har baiyi rawa ba hankali sa bazai kwanta ba, wakar da aka sanya tana ƙarewa wakar calm down ta shiga, aiko jiki har rawa yake yi su Parveen suka shiga fili suka dinga tikar rawa, gaba ɗaya suka ja hankulan mutanan hall din, sunyi matuƙar burgesu in ka cire su Yusra dake jin haushin su badan komai ba, sai dai saboda sun hana su rawar gaban hantsi, Hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba, ganin yadda suke rawa da alama sun manta a ina su ke ne, daga ita sai batul ne ba su shiga filin ba, Manyan mutanan dake a wurin ne suka soma yi masu liƙin kuɗi, tamkar ana yayyafa masu ruwan sama.


Hajiya turai da Hajjaty suma suka shiga filin suna tayasu yin rawar, kusan gaba ɗaya suka shiga cikin su, cikin raha da nishaɗi suka taka rawarsu.


  Jemimah ta dage duk wanda ya lika mata kuɗi sai ta kwashe su ta tura a aljihun rigarta, ta tarasu dayawa har a hammata take saƙe wasu, tayi zaton abun wasan yara ne.


 Mutanan dake harin Unaisah dama jira suke ta miƙe, a lokacin chief Owais  Yabar wurin su, Ya tafi amsa kiran da akayi mashi awaya.


   Miƙewa ta yi tana tafiya a hankali yayin da idanunta ke akan dance floor din, da alama itama so takeyi tayi rawar ta ɗan gagije jikinta.


    "Baiwar Allah sannu" jin muryar mutun abayanta yasa tayi saurin dubanta, zahara ce fuskarta dauke da murmushi, Mayar mata da martanin murmushin unaisah tayi.


 "Yawwa"


 "Tun ɗazu nakeson yi maki magana ban samu damar yi ba, saboda mutanan da kike atare da su...." da ɗan mamaki take kallon bakuwar fuskar da tayi mata magana.


  Miƙa mata hannu zahra tayi don su gaisa, A hankali unaisah ta ɗaura hannunta a cikin nata.


  "Sunana zahra ke fa"?


"Unaisah"


"Banyi tunanin zakiyi saukin kai har haka ba," 


Murmushi unaisah tayi mata.


"meyasa kikace haka"?

"Raina ne ya bani haka" girgiza kai unaisah tayi

 "Kin burge ni, idan badamuwa inaso muyi hoto a tare"

  Bata kawo komai aranta ba, ta amince ma zahra.

  Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin curo wayarta daga cikin yar purse dinta, ta dinga daukar su hoto da unaisah, A kalla zahara ta dauki hoto sama ashirin, Tsabar iyayi na zahra harda rungumeta sukayi hoto amanne da juna kamar kanwarta....


    "Kinga yanzu na samu wanda zan dinga kallo awayana," ta faɗa bayan sun gama


 "Ko zan iya samun layin wayarki? Ina so mu dinga gaisawa.


 "Ban haddace number dina ba, kuma wayar bata a hannuna"


 Shafa gefen fuskarta zahra tayi"ba damuwa, ay ina zuwa estate din nan zamu dinga haduwa...."  wayar zahra ce ta soma ringing da ɗan sauri tace ma unaisah yanzu zan dawo ana kirana" amsa mata tayi da toh, har zahra tabar wajen Unaisah bata daina bin bayanta da kallo ba, hakanan taji ta burgeta, aranta ta ayyana wato duk yadda wani yaƙi ka, to wani zai so ka ne.

 

 Murmushi tayi, tare da juyawa da niyar tabar wurin cikin rashin sa'a ta bange ɗaya daga cikin servers din dake safa da marwa wurin raba abinci, Gaba ɗaya tray din lemun da matar ta ɗauko ya 6are a jikin abaya dinta, glass cups din suka rikito kan floor, hankalin ba karamin tashi yayi ba ganin ta 6ata mata wankanta don ma Allah yasa rigar baka ce 


    Muryar matar na rawa ta soma bata hakuri.


   Shiru unaisah tayi tamkar bazata tanka mata ba tace"bakomai, ay ba laifin ki bane, Ni ce na bangaje ki, bansan da mutun abayana ba"


  A ruɗe matar tace"akwai rest room ki zo muje ki wanke rigarki please, idan ba haka ba za'a hukunta ni ne idan wani yaga ruwan lemun nan a jikin rigar ki"


Girgiza kai unasah tayi"a'a bani buƙatar zuwa, Ki tafi kawai, ay rigar baka ce babu wanda zai gani"


  Magiya matar tadinga yi mata akan tazo su tafi ta wanke mata rigarta, ganin tasa naci ne yasa ta amince mata, da sauri matar ta zukunna ta kwashe glasses din ta mayar a tray, kafin ta juya Tayi gaba unaisah tabi bayanta, babu wanda ya lura da abun da ya faru saboda sautin kiɗan daya karaɗe hall din hankalin kowa na akan dance floor,.


Wani corridor suka shiga a inda jerin rest rooms din suke ta nuna mata ɗaya daga cikin su, ki shiga zan jira ki anan" amsa mata tayi da toh.


   Unaisah kamar kada ta shiga haka take ji saboda hankalin ta bai kwanta da matar ba, buɗe kofar tayi shigarta ke da wuya taji alamun an datse ƙofar, sai dai ranta bai kawo mata komai ba, agaban sink ta tsaya ta kunna tap ruwa ya shiga karanyowa ta soma wanke inda lemun ya 6ata, bayan ta gama ta tsaya tana kallon fuskarta ta cikin mirror bakomai take tunawa ba face fuskar chief Owais hakika Yaja hankalin ta, musamman a lokacin da aka so aci mutunci su ya kare masu martaban su, 

 Murmushi tasaki har dimple din ta ya lotsa, can kuma ta juya akalar tunanin nata ga garkuwarsu, tasan duk inda yake ayanzu yana cikin koshin lafiya don ta fahimci prime minister ba karamin kaunarsa yake yi ba, tabbas zataso taga yadda zai tarairaye shi.....


  _Sam ta manta a rest room take, tunawa da yan uwanta yasa tayi saurin juyawa zata fuce sai dai me? Tana jan ƙofar taji kamar ta damƙi dutse, bata kawo komai aranta ba, ta soma knocking tana fadin"pls kibuɗe min kofar na kasa" shiru taji mata bata amsa mata ba, kusan sau uku tana neman taimakonta amma shiru, bata amsa mata ba, gaba ɗaya taji ta takura hankalin ta ya fara tashi, bubbuga ƙofar tadinga yi tana cigaba da fadin pls bakowa ne akusa ku buɗe mun kofa, tun tana sa ran za a buɗe mata har ta fara fidda rai, zuciyartace ta soma raya mata gaya can za'a cutar da yan uwanta aikuwa da karfi ta soma bubbuga ƙofar kamar zata balle ta, har kafa take sanyawa tana harba jikin ta, babu alamun zata buɗe, tana nishi ta ja da baya ta watso da gudu ta bangaji kofar duk don ta samu ta buɗe amma duk abanza, Lokaci ɗaya tafara burkicewa dama brain ɗin su da rauni acikin ta, gaba ɗaga rayuwar kullan da su ka yi a gidan kurkukun ƙaddara ta fara dawo mata a cikin kanta, sautin dariya dariya ta soma ji da shessheƙar kuka yaran da muryoyin wadannan tsaffin da suka ta6a bata naman mutun ta ƙarfi suka sanyata dole ta ci, runtse idanuwanta tayi tare da sanya tafukan hannayenta ta daddafe kanta dake wani irin mahaukacin sarah mata, wani irin tsoro da firgici ne ya soma ziyartarta, rushewa tayi da kuka tana bugun kofar muryarta da shessheƙar kuka take fadin"Wayyo Allahna ku buɗe mun kofa! na shiga uku, zan mutu kaina, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in Boss ka buɗe min kofa zasu kashe ni, Danish kana ina kazo ka taimake ni, nasan bazaka bari a cutar dani ba, nashiga ukuna sajeed naufal Batool wai baku jina nane so kuka na mutu....  cikin fitar hayyaci take yin sambatun tuni mayafin dake akanta ya zame ƙasa, duk tabi ta yamutsa gyaran gashi  da akayi mata tamkar mahaukaciya haka ta koma, jikinta duk ya raunata saboda bugun kofar da take yi tana faman ciccije la66anta, ga ƙarancin iskar dake a wurin ta fara affecting dinta, gwanin ban tausayi baiwar Allah, jan numfashi ta cigaba dayi tana ganin jiri jiri a idanunta kamar daga sama taji zubar wani abu a tsakankanin cinyoyinta da wani irin matsanancin ciwon mara na fitar hayyaci nan take wata juwa ta kwashe ta gaba ɗaya ta kife kan floor sumar kanta ta tarwatse har ta saman fuskarta, hannayenta daddafe da cikinta dake ta murɗamata yanayi mata zogin azaba, muryar ta adisashe take ambaton Allah.............._

   *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*


*Mu haɗu jibi Alhamis Idan Allah yakaimu da rai da lafiya*


 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post