Kurajen fuska ko pimples a turance Wasu irin nau'in kuraje ne da suke fitowa a fuska musamman idan mutum yana ta’ammali da mayuka iri-iri ba tare da kula da man daya dace da fatar fuskar ba.
Matsalar kurajen fuska so da yawa tafi shafar Mata musamman matasa inda za’a ga wasu matan har nikab suke sanyawa a fuskokin Su saboda kar aga ta’adin da kurajen suka Yi musu a fuska.
Maza ma sukan fuskanci irin wannan matsalar ta kuraje a fuska sosai amma ba'a cika ɓata fukar maza ba kamar yadda yakeyi ma mata.
Kadan daga cikin Abubuwan dake janyo kurajen fuska sun hada da:-
(1) Yawan cin Abu Mai maiko.
(2) Amfani da mayukan da Basu dace da fatar fuska ba
(3) Kwayoyin cuta
(4) Shiga rana sosai.
Mutane da dama kan kashe maƙudan kuɗaɗe don sayan maganin da zai magance musu kurajen amma yawanci ba’a samun biyan bukata.
Ana iya magance kurahen fuska ta wadannan hanyoyin :
(1) Bawon lemon zaki:
Ana shafa bawon lemon zaki a inda abin ya shafa Sai a barshi ya kwana da safe Sai a wanke da ruwan dumi.
(2) Zuma:
Ana samun zuma Mai kyau a goga da auduga a fuska, a barshi zuwa Yan mintuna Sai a wanke. Za’a iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen Su fita.
(3) Ruwan lemon tsami:-
Ruwan lemon tsami wata sahihiyar hanya ce mai matukar amfani wajen maganin kurajen fuska.
Lemon tsami yana taka rawar gani sosai wajen kashe kananan kwayoyin cuta a fuska da kuma fitar da maikon fuska. Yadda za’ayi amfani da lemon tsami shi ne a samu lemon tsami a matse ruwansa sai a samu auduga mai tsafta a dinga goge fuska dashi kafin a kwanta bacci, da safe sai a wanke fuskar da ruwan dumin. Za’a iya maimaitawa sau biyu ko uku a rana har kurajen su fita.
(4) Ganyen darbejiya / Man darbejiya:
Ana kwaba ganyen darbejiya da man darbejiya a shafa a fuska zuwa mintuna biyar sai a wanke da ruwan dumi ko a dinga shafa man darbejiya da auduga a fuskar har zuwa lokacin da kurajen zasu baje. Kurajen fuska dai sun dade suna batawa mutane fuskokin su har ta kai wasu ma sun gaji da nemawa kansu magani, mata ma kan yi duk yadda zasuyi su rufe fuskokin su don kar a ga kurajen,wasu ma kanyi amfani da hodar foundation akai akai don boye kurajen dake fuskar su.
Wannan hanyoyi da na lissafa da karin wasu zasu taimaka sosai wajen cire kurajen fuska cikin sauki ba sai mutum ya kashe makudan kudade ba wajen neman magani ba.