Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 15 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 15 Complete

Novels Elite English

_*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

                     سجن القد💋🔥💞    

                  ~Takun Ƙarshe🔥~

            Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

_Gaba ɗaya sun shiga yanayi, sai dai fa duk da haka babu fara'a akan fuskokin su kamar basa son kasancewa da juna, bayan motar ta isa gidan, bata bari chief ya kubce mata ba, don ta fahimci hankalinsa na akan dinner hall kuma tasan bai wuci saboda yarinyar nan ba, jan shi tayi da ƙaryar ciwo da kisisina har ta samu yabita Part din ta don taji dadin ruƙe sa kamar yadda faryat ta tsara mata.........👀_(Back to Dinner Hall)Bayan tafiyar Nazli da Yan Mintuna, sai ga kiran ta ya shigo layin faryat, A lokacin harta koma wurin su Zulaihat bayan ta gama shirya makircin, A hanzarce tabar wajensu ta samu wurin da bakowa tayi picking ta kara wayar a kunnanta.


Muryar Nazli tamkar tame jin bacci tace"faryat, nakira ne nayi maki godiya,  yanzu haka muna a gida tare da chief"


 "Naji dadin jin hakan sisters, babu godiya tsakanina dake nayi ne saboda farin cikin ki" 


"Ina yarinyar nan take"? 


Rass taji gabanta Ya faɗi jin abun da Nazli tace, ita sam ta manta da zancen ƴar mutane da tasa aka kulle a restroom.

 

"Naji kin yi shiru baki ce komai ba"?


"Sister kulle ta nayi a restroom yanzu zanje na buɗe ta""Okay, I don't want any problems tun da buƙata ta biya, kawai ki ƙyale ta tafi, i  know her relatives will start looking for her as soon as they notice she is not there."


"Okey, bari naje na buɗe ta" sallama su ka yi da juna, tsaye tayi tana bin Hall din da kallo, can Ta hango matar da suka hada baki da ita, Cikin sauri ta nufe ta.


  "Ke! Ina son Magana dake ki biyo ni yanzu"  da sauri matar tabi bayanta suka ke6e a wani wuri.


"Yarinyar dana sa kika kulle a restroom, ita nakeso kije ki buɗe ta yanzu" 


 Hannu matar tasa tana laluban aljihun uniform din jikinta, can ta rabka salati tana fadin"Inna lillahi! Nashiga Uku..." idanu azare faryat tace"what"?


  Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Sister, I think I lost the key, ba tare da sani na ba"


 Waro idanu faryat tayi cike da masifa tace"amma Baki da hankali! So kike kija min bala'e, kin manta yadda mu ka yi dake ne? Sai da nace maki da zarar kinga kirana kije ki bude mata kofa, shi ne zaki ce wai key ya bata"? ta fada tana zare mata idanu taci gaba da cewa "to wallahi baki isa ba! Kisan yadda za'ay ki nemo shi da gaggawa ki buɗe ta" ta fada tana faman cije le6en ta, da yatsan hannu ta nuna ta"Don't you dare mention my name if anyone finds out what we've done, Idan ba haka ba hmmm kinsan sauran" rai a6ace ta faɗa tare da juyawa har ta fara tafiya ta dan dakata tunawa da CCTV dake a hall din, Hankali A tashe ta ta kuma juyowa ta kalli matar dake a tsaye ido ya raina fata, jikin ta sai kerma yake daga gani tana acikin matsanancin tashin hankali.


Sassauta murya tayi "Kiyi kokari ki gano key din, ki je ki bude yar mutane, kinga akwai CCTV duk wani abu dake faru suna gani, kuma wallahi muddin baki bude ta ba har suka gano kece kika kulle ta, Na lahira sai yafi ki jin dadi" ta karasa tana sakin shu'umin murmushi ta kuma cewa"ni nasan yadda zan fidda kai na, ke ce a ruwa, dama kwadayin abun duniyane yasa kika amince min muka shirya komai, na riga dana biya ki kudinki, shawara ta rage wa mai shiga rijiya, ni kinga tafiya ta" cike da shakiyanci faryat ta juya ta nufi hanyar fita daga hall din don zaifi mata kwanciyar hankali akan ta tsaya ganin rikicin da za'ay na rashin ganin Yar Mutane


  Kafin ta fuce ta kira layin Jazz tace mashi ya same ta a bedroom dinta tana son ganin shi, tayi hakanne saboda ta samu damar ke6ewa dashi kafin gobe Subar Nigeria.


Hankalin matar ba karamin tashi yayi ba, wata irin zuface ta soma wanko mata, har ta fara danasanin kudin da ta kar6a a hannun faryat, gaba daya tabi ta firgice sai faman lalube lalube take yi tana neman key din, Sako da lungu bata gan shi ba, ga shi lokacin ana gab da za'a rufe taron dinner din tasan dole a nemi yarinyar, a karshe da taga ba ta da wata manufa, sai ta yanke shawarar guduwa daga hall din.....


___________________________________✍️


  "Ai ga irinta nan, Ni dama nasan za'a rina, yadda yake rawar kai akan yaron nan kamar ɗan cikinsa, hakan na nufin yafi kowa mahimmanci awurinsa shiyasa yaja su suka tafi wata uwa duniyar, Allah kadai yasan ina suka je..."  senate lateef ne ya fada Yana huci yayin da suke atsaitsaye curko curko 

  

"Ni abunda nake ma fargaba, kada yaron nan ya cutar dashi, don ni wallah hankalina bai kwanta da shi ba, saboda ina zargin ba cikakken mutun bane" His excellency Deen yayi maganar 


Abdul Razak Yace"Laifin Owais ne, Ya cika daukar kasada, akan me zai hada shi da yaro, hada karfin halin cewa ya tafi da shi salon Yajaza mana bala'e"


Kwa6e fuska Senate lateef yayi"ay tin farko ubansane ya daure masa wurin zama da duk hakan bata faru ba, Ina kallonsa dazu Ya hakikance akan cewa owais ba zai kawo abunda zai cutar da ahlinsa ba, Idan ma muna jin fargaban wani abu zai faro owais ne  ke da alhakinsa, don haka bai kamata muna tada jijiyoyin wuyanmu akan sa ba, Mu zuba ido mu gani" 


  "Wannan duk ba abun tada hankali bane, In sha Allah zai dawo cikin koshin lafiya, yakamata muna kyautata masu zato, ku kanku fa dazu ku ka gama tsegumin kamannin Yaron da hateem har kuna fadin baku ga laifinsa ba daya kusa zaucewa akan kaunarsa, shine kuma yanzu kuke korafi don kun ji shi shiru" ya fada yana ɗan jifar su da hararar zolaya.


 Dakuwa Senate lafeet yai masa"ungo nan, dani kake wannan maganar, ni banma ga wani kamanninsu ba, na dai fadi ne kawai" dariya suka sanya gaba dayansu.


  Sir mubarak yace"kaifa ɗan iskan mai raine, Lokaci ɗaya sai ka burkicewa mutane ka hakikance kan abu daga baya kuma ka dawo ka canza magana, daɗina da ɗan siyasa kenan, Haka halin ku yake, Shiyasa dazu na zuba maku ido kunata jaraba saboda an shigo da yara hall alhalin nan kuwa duk kun ƙyasa da ganinsu, musamman shi yaron da kuke magana akai"

 Harara suka watsa masa atare, Senate yace"ba ka girmamani mubarak"


"Da dai ba lokaci ɗaya muka zo duniya ba," acewar Sir Mubarak.


  "Bari na fada maku gaskiya, wallahi da ace Hateem ya ta6a haihuwar Namiji tsab zan iya dafe alkur'ani ince dansa ne yaron nan sai dai kaffara ta hauni" his excellency abdul razak ne yai maganar.


  Deen yace"yadda kasan irin an tsaga kara, Har hancinsu da idanunsu, kai komai fa, ni fa da za'a bi ta shawarata zance ne muje asibiti ayi masu gwajin DNA" wani kallon harara Senate lateef yayi masa da zolaya yace"lallai siyasa tafara haukata ka, in ba haka ba kawai daga ganin yaro tsintacce daga daji sai ka ƙababa ma Hateem!" watsa hannu yayi"ni abunda ke raina na faɗa"


Shiru suka danyi na wani lokaci kafin  senate yayi yar dariya yana fadin Yau wani zaici ubansa a hannun shalelen baba obie" gaba ɗaya suka sanya dariya cikin raha don sun gane me Yake nufi

  Sir mubarak Yace"na tauyasa mashi, don wallahi nasan bazata ƙyale shi ba, sai ya yabawa aya zakinsa Hmm Allah dai ya kyauta.

  Senat yace"yayi banban kuskure na ruke hannun wata mace agabanta, Ni abun da bangane ba, meyasa yayi hakan ne? Ni fa nafara zargin mutumin nan, wallahi babu gaskiya acikin lamarinsa in ba haka ba akan me zai ja hannun baligar mace bazawara a bainar jama'a da sunan zai fitar da ita ta tsiya daga hall har yana ikirarin kada ta kuskura tabari ya riga ta fita......"


  His excellency Deen Yace"idan ma akwai wani 6oyayyan sirri atsakaninsa da ita, a sannu zamu gano koma menene ay mu ba'a shiga family dinmu da fuska biyu a zauna lafiya.... Fira suka cigaba da yi atsakaninsu,


Abu kamar wasa har Bayan Magrib ana gab da za'a rufe taron babu prime minister babu Unaisah, Ga mutane sunataso suyi mashi bankwana saboda ba lallai gobe su haɗu da shi, asubar fari zasu bar nigeria, babu wanda bai jaraba kiran layin hateem acikin su ba, sai dai wayar tayi tayin ringing, ba'a picking, Shima owais sun kira layinsa wayar bata shiga, ransu yayi mugun 6aci, sauƙin su ɗaya zuwan gimbiya mujeedat itace ta sanar da su inda Hateem yake, ba tare da 6ata lokaci ba, suka yanke shawarar zuwa can su same shi, kusan gaba daya mutanan hall din suka nufi gidan prime minister don suyi mashi bankwana tun da shi yaki dawowa dakin taron, yana can tare da sanyin idaniyarsa., 


Idan muka koma bangaren zahra da batool lamarin Ya fara Tsoratar da su ganin Har mutane sun fara watse wa babu alamun Unaisah zata fito daga toilet, kwatsam wayar zahra tafara ringing, da sauri  ta ɗaga ganin sunan hajiya saratu.


"Meet me outside the hall right now, Zarah!" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, bayan ta katse kiran, Ta kalli batool jikinta yayi sanyi lakwas sam bata so ta tafi tabar Hall din ba tare da an gano unaisah ba.


  "Ki yi hakuri sister batool, tafiya zanyi ba don naso ba, matar da ta gayyace ni dinner din nan itace take kirana, shawarar da zan baki, Ki sanar da sauran yan uwanki da kuma jami'an dake tsaron hall din su taimaka maki ku gano yar uwarku" ta fada tare da ruko hannayen batool a cikin nata kafin taci gaba da cewa"kada ki manta idan kun gano unaisah ki sanar da ita cewa na tafi da kewarta" batool ta amsa mata da toh, kamar kar su rabu da juna su ka yi sallama.


Bayan tafiyar zahra, batool tabi yan uwan su daya bayan daya ta sanar da su zancen bacewar Unaisah, nan fa hankalin su yai mugun tashi, su sajeed suka bazama nemanta, tsantsar tashin hankaline da damuwa akan fuskokinsu, babban abunda suke ma zullumi kada ace wani mugun abunne ya faru da ita, dama sun lura bakowa ke son su ba, tsaf za'a iya cutar masu da yar uwarsu, bacci tuni yayi awon gaba da jamimah, Sai dai haris ya goyata abayan shi, itama Azeeza daukarta Naufal yayi abayanshi sbd lalurarta, Parveen da su Hanna idanu sunyi jawur ga bacci suna ji ga kuma tashin hankalin rashin yar uwarsu, babu wanda Ya lura da halin da su ke a ciki saboda babu mutane sai jefi jefi wasu suna bakin hall wasu kuma sun tafi gidan Hateem kusan su kadai ne suka rage a hall din sai servers din dake tattara kayan abincin da aka yi amfani da su, da kuma interior designers din da suka fara kwashe kayan decoration din dakin taron.


A lokacin da ba su yi tsammani ba, Sai ga Boss tare da biy guy sun shigo hall din cikin takun sauri, sun zo ne domin tafiya da su ganin lokacin yayi, su parveen na ganin su suka fashe da kuka da gudunsu suka nufe su tare da fadawa jikin boss da big guy suna kuka suka fada masu basu ga unaisah ba, ta 6ace sun nemeta sun rasa.


Da tsantsar tashin hankali Taj Ya furta"wai wata unaisah ne ta 6ace? Ko kuna nufin Angel dina"? Adabarbarce Yai maganar Yana dubansu,

 Sajeed Yace"ita muke nufi, tun dazu muke nemanta bamu ganta ba, mun duba ko'ina"

Kallon juna boss da big guy su ka yi a lokaci daya, 

  wani irin bugun fargabane Ya darsu a zuciyar taj, Jin Angel dinsa ta bata babu ita,

Muryarshi na rawa yace"bata fada maku inda taje bane"?

Hada baki sukayi wurin cewa Eh 

Dafa kafadarsa Big guy yai ganin Yana neman rikicewa.


 "In sha Allah babu abunda zai same ta, zamu nemo ta, sauƙin ma akwai cctv a dakin taron zamu ga inda ta shiga ne"

Mayar da dubansa yayi kansu batool"sajeed, Ka tafi da su bakin hall din, akwai Jami'an mu dake jiran ku zasu tafi da ku gida" 


Muryar batool da shesshekar Kuka tace"ni dai bazan iya tafiya, in ba tare da unaisah ba, zan jira har agano ta ...." kafin ta rufe baki Sajeed Yace"nima bazan tafi ba, kamar yadda muka zo tare da yar uwarmu atare da ita zamu koma"

!

"kwara kubarmu anan wlh ko mun koma gida, hankalin mu bazai kwanta ba, ko runtsawa bazamu iya yi ba, in har unaisah dinmu bata dawo ba...." Haris ne ya fada idanunsu sun ciko tab da kwalla, gaba ɗaya sun turje akan ba zasu tafi ba....


 Cikin rauni na murya taj Yace"Ya isa haka! Ku daina zubar da hawayen ku, ku samu wuri ku zauna Yanzu zamu nemo ta," da sauri suka samu kujeru duk suka zauna suna jiran tsammani


Ba su fara zuwa dakin cctv din ba, big guy ne ya bada shawarar su fara bincika restrooms din dake a hall din kafin su fara zuwa can, da sauri suka nufi hanyar da suke, daya bayan daya suka dinga dudduba cikin su ba su ga kowa ba, cikin rashin sani suka tsallake kofar wanda take a ciki ba tare da sun ankare ba, tsabar kidima yasa taj sulalewa jikin bango Ya zukunna, idanunsa sun kada jawur dasu, fuskarshi duk ta yamutse idan harfa ba ganin unaisa sukayi ba to kuwa bazai ta6a dawowa dai dai ba


"Ni nafi tunanin ko dai tabi family din chief xuwa can gidan prime minister" big guy ne Ya fada Yana duban fuskar taj, wanda tuni ya hada gumi duk da sanyin A.c din dake a wurin babban tashin hankalin shi kada Ya rasa yarsa tilo da yake da ita, tabbas zuciyarsa zata iya bugawa.


Ganin bai da alamun motsawa ne Yasa Big guy dafa kafadarsa Cikin kwantar da murya yace"dan Allah ka yi hakuri ka daure ka ta shi, mu shiga cctv room din zaifi sauki muga ina ta shiga"


Zuciyarshi a hautsine Ya cire facemask dinsa tare da jefar da shi gefe daya.


  Cikin sanyin murya ta wanda Ya karaya yace"Wallahi tun ina agidan su salsabeel nake jin faduwar gaba, shiyasa nakasa samun nutsuwa na kamo hanya nazo hall din nan ashe abun da zan taras kenan" ya fada tare da kallon big guy"ka tafi ka duba, don bana jin zan iya matsawa daga wurin nan, jiri nake gani a idanuwana"


Dan murmushin gefen fuska Big guy yayi mashi dazolaya yace"duk son nan da kake yi mata ahaka zaka damka ma wani kato ita yaci gaba da kula da ita"

 Kallon harara Boss Ya jefa mashi"kaga pls kada ka daura min wani hawan jinin, ka tafi kawai, Ina jiranka"


 Yar dariya yayi kafin ya juya ya bar wurin


Dafe kansa yai da tafin hannunsa, wani irin ciwon kaine Ya farmasa, Yana cikin wannan Halin, kamar ance ya dago ya kalli Floor din wurin nan take eye balls dinsa suka sauka akan Stone din rigar unaisah, da alama daga jikin rigarta Ya fadi kasa, mika hannu yayi tare da daukar shi Ya kura ido Yana kokarin tariyo a ina ya ta6a ganinsa, sai da ya zurfafa tunaninsa kafin lokaci daya ya zabura ya mike yana bin kofofin toilet din dakallo saboda ya tuna itace ta sanya abaya me adon gold stones.


  Kofar da suka tsallake basu duba ta ba, ita Ya nemo, ganin ta adatse ya kara tabbatar mashi da tana a ciki.


   Muryarshi har rawa takeyi wurin ambaton sunanta"Unaisah!Unaisah!My Angel" shiru ba'a amsa mashi ba, nan fa hankalin shi ya kara tashi, Ga shi Ya duba babu key jikin kofar, Karfi yasa wurin bangaje ta da kafadunshi sai dai ko gizau kofar batayi ba, Ja baya yayi kafin Ya nufeta da iya karfin shi na karshe yayi mata wani irin bahagon bugu, nan take kofar ta saki, shi kanshi bai yi tsammanin Yana da karfin da zai Iya bude ta, batare da key ba Allah ne ya taimake sa.


Karasa ture kofar Yayi, a fujajen ya fada cikin toilet din yana faman zubda gumi, shigar shi ke da wuya idanunsa suka sauka kan Unaisah dake kwance saman floor, baiwar Allah ita kaɗai tasan radadin azabar da ta fuskanta, taci bakar wahala ta jigata sosai, zufa ta gama wanke jikinta, Takalmanta ware da ware sun yi gefe guda, Ga mayafinta a kasa, hannunta daya dafe a saitin cikin ta, da wani irin rauni da murya ya furta"My Angel" A sukwane da sanyin gwiwa Ya zube gabanta saman gwiwowinsa, duk irin dauriyarsa baisan sa'adda hawaye masu dumi suka soma sintiri kan kuncinsa ba, yatsun hannayensa na kerma ya daura su kan kafadunta tare da janyota ya dawo da ita kan kirjinsa, ya rungume abunsa tare da runtse idanunsa yaci gaba da shesshekar kuka Yana ambaton sunan ta....


"Am.. sorry my Angel laifina ne da ban zauna a dakin taron ba, da duk hakan bai faru ba....." 


 Baisan meke damunta ba da yai silar shigarta wannan Mawuyacin halin, baisan Ya akai aka kulle ta a restroom ba.


Yana acikin wannan Yanayin big guy ya shigo da saurin shi, Yana ganin taj rungume da unaisah Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.


    Daga bakin kofar ya tsaya don baisan me zai taras ba.


 Cikin sanyin murya yace"idonta biyu"?

Muryar taj kasa kasa Yace"bansani ba, kamar ta sumane anan, amma daga gani taci bakar wahala"

Big guy yace"mun gano wacece Ta kulle ta a restroom din, Kuma in sha Allah zamu bincikota sai ta dandani kudarta wallahi" Yana fuci Ya faɗa


Babu alamun taj Ya fahimci me yake cewa hankaklinsa na akan Angel dinsa yace da shi"please Ka koma wajen yan uwanta kada su ji mu shiru, yanzu zan fito da ita" amsa mashi yayi da okey, a hanzarce Ya fice.


   Har ya yunƙura zai mike Yaji alamun lemar wani abu a hannun shi, da sauri Ya dago da tafin hannunsa Yana kallon jinin daya ta6o, sai lokacin Ya fara jin karninsa a hancinsa, Idanunsa azazzare yake kallon jinin Hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta dinga harbawa da karfi da karfi tamkar zata fasa kirjinshi,duk a zaton shi wani mugun abun akayi mata, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana mashi kodai raping dinta wani yayi ko kuma Wuka aka caka mata.


  Zuciyarshi na tashi, Yai hanzarin Sanya hannu Ya dage rigar jikinta, santala santalan cinyoyinta tsakankaninsu duk jinin ne daya gangaro mata.


 Sai da ya bincika ta sosai, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin ba abunda Yake zargi bane, A hanzarce ya fara wanke mata inda jinin Ya 6ata, kafin Ya lullu6a mata mayafinta ya daure mata qugunta da shi, asaman kafadarsa ya rungumo unaisah, yayin da ɗayan hannunsa ke a ruke da rigarta, tuni tajima da farkawa tun lokacin daya fara wanke mata jinin da ruwa sai dai bata iya komai, Jikinta ya sake ga wata irin kasala data mamayeta.


  Fitowa yayi da ita sabe a kafadarsa, tunkafin Ya karasa inda su Batool suke, da gudun gaske suka nufoshi, lokaci daya su ka ja burki idanunsa azazzare da tashin hankali suke kallon Taj

 

 Muryoyin su na kerma suke tambayar shi meya faru da unaisah? Bata da lafiya ne? Ko bacci take Yi ne"?


Kokarin danne damuwarsa yayi kafin yace masu"Babu abunda ya sameta, lafiyarta kalou, Ku zo mu tafi gida" 

Da sauri Ya wuce gaba suka bi bayan shi, masu aikin dake zarya suna kwashe kayan da akayi amfani da su na hall din sai satar kallon taj suke Yi ganin shi dauke da yarinya kamar ba rai.


Fitowa yayi daga Hall din su Batool suna abiye da shi, Jami'an dake tsaron dakin taron suna ganin shi suka fara tambayarshi meye faru da ita? 

Baibi takansu Ba, Ya nufi mota, da sauri jami'insu Ya bude mashi Ya shiga back seat tare da Unaisah, suma su batool suka shiga cikin sauran motocin da aka kawo su, kusan atare su ka bar garden din, da matsakaicin gudu suka nufi hanyar komawa gida

Mutsu mutsun bude idanunta ta somayi wadanda suka kada jawur da su, da kyar ta dan ware su kadan ta kalli fuskar taj dake a rungume da ita, hannayensa duka biyu akan bayanta kamar wani yace zai ƙwace mashi ita.


Idanunta na faman lumshewa dakyar dakyar take kallon fuskarshi ba tare da sanin shi ba, acikin zuciyarta ta dinga ambaton sunan shi daddyna daddyna dama kaine kake boye min fuskarka..." siraran hawayene suka wanke fuskarta, ganin yana kokarin juyowa yasa tai saurin lumshe idanunta, saukar hannun shi taji asaman kanta, A hankali Yake dan shafa mata shi, wata irin ni'ima taji ta saukar mata, jikin ta yayi sanyi ba kamar dazu da zazzabi Ya lullu6eta ba, bakomai take tunawa ba face lokacin da ya jefata cikin ruwa...


Taj sam baisan cewa babu face mask a fuskarshi ba, gashi har unaisah taga fuskarshi, don ma babu kwarin jiki ai da ta tuhumesa nakin bayyanar mata da kanshi da baiyi ba, dama tuntuni ranta yana bata cewar daddynta ne duk da bata ta6a ganinsa ba, amma kulawar dayake bata fiye da ta sauran yan uwanta da yadda yake janta a jikin shi da kuma muryarshi su suka kara sanya ta hasashen ko shine.


Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, tuni Kowa ya koma masaukinsa bayan da suka hallara a  gidan prime minister inda suka karasa shagalin nasu acan, a 6angaren chief owais tun bayan da suka shiga Part din Nazli, ba tare da sanin shi ba, ta kashe mashi wayar shi don kada a kira shi, bayan haka ta hada baki da daya daga cikin hadiman gidan ta sanya mashi maganin bacci a coffee, duk don kada ya tafi yabarta, Sai wuraren karfe sha daya na dare tukunna chief Ya farka, a lokacin nazli har tafara bacci, bai bi ta kanta ba, da sauri ya fito daga part din ta ya sauko down, Kafin Ya kunna wayar shi, Layin prime minister Ya fara dannama kira don Yaji idan Yasa an mayar da danish gidansa.


 Bayan yai picking Hateem Ya fada masa suna atare da shi a bedroom dinsa, bai tsaya bata lokaci ba Ya nufi part din prime minister, dakyar ya raba shi da danish, kamar karsu rabu, na rana daya kawai sun shaku da juna har kyautar zobe ya ba shi mai tsadar gaske saboda ya dinga tunawa dashi, kuma yayi mashi alkawarin kullum xai dinga kiransa suna gaisawa, bayan chief Ya tafi da shi har kwalla saida Ya zubda daboda kewar rabuwa da danish.......


Asubar Fari, Motoci suka dinga tururuwa wurin fita daga Estate din,da wata irin jiniya mai kuwar gaske tamkar zasu tashi sama, kaitsaye suka nufi shantalelen titin da zai sada su da Airport, gaba daya family din obinna ne dashi kanshi obinnan suka yi masu prime minister rakiya, Kamar karsu rabu da juna, musamman mahaifinsa da yan uwansa, duk irin juriyarsu saida suka share kwallar rabuwa da shi, Hajiya saratu tasha kuka kamar karamar Yarinya, shi kanshi hateem din saida Ya zubda kwallar rabuwa da yan uwanshi, Ji yake kamar idan ya tafi ba lallai Ya kara dawowa ba, hakika kowa yayi jimamin tafiyar prime minister da Iyalansa, ko bayan da suka baro Airport din suna akan hanyar komawa estate nasu lokacin da suka jiyo karar jirgin su


Haka suka dinga leken jirgin ta windows din motocinsu, har Sai da ya bace ma ganinsu tukunna suka hakura kowa Ya sanyawa zuciyarsa salama, kusan duk aranar Su his excellency deeen suka bar abuja, harta su Justice kowa Ya koma inda Yake da zama wasu Nan cikin Nigeria wasu kasar suka bari, Zaki ne kadai bai tafi ba, yanzu estate din Ya rairaye ma zauna cikinsa ne kadai suka rage.
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*
 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post