_ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_
سجن القد💋🔥💞
~Takun Ƙarshe🔥~
Dedicated to Aunty Kubra💋💞
قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘
An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘
Daga alƙalamin Boss Bature💋✊
__________________________✍️
A hankali ta buɗe idanunta wadanda suka kumbura suntum da su sakamakon kukan da tasha jiya, ƙurawa ceilling din dakin idanu tayi na ɗan wani lokaci zuciyarta cike fal da tunanin meya faru da ita a jiya? tamkar tayi loosing memory ɗinta, da sauri ta sanya hannu ta shafa kayan jikinta, lokaci ɗaya ta yunkura ta miƙe zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, ko'ina na bedroom dinsu ta soma bi da kallo kafin ta sauke idanunta akan batool da ke kwance gefenta tana bacci, tayi mamakin ganin kayan bacci a jikinta, ƴar gown ce da bata wuce gwiwarta ba, launin purple colour, ta rude sai faman shasshafa jikinta take yi burin ta ta tunano ya akai aka canza mata kayan jikinta! kamar ma hada wanka akayi mata, hannu tasa ta ɗan bugi kanta a kokarinta nata farkar da kwakwalwarta ko taci gaba da yin aiki yadda ya dace.
Buɗe ƙofar ɗakinsu akayi da sauri taja bargo ta lullu6e kanta, tunkafin ma taga wanene.
Atare suka shigo dakin, boss tare da Ummi da ke abiye da shi cikin shiga ta kimono robe, ta yafa gyale a kafadarta, hannun kowannan su ruƙe da ɗan ƙaramin tray na kayan abincin.
"Barka da safiya daughter" wani irin wurgi tayi da bargon gefe ɗaya ya faɗa kan Batool, ta ɗago tana faman zare mashi idanunta.
Sunyi mamakin ganin yadda ta zabura, ummi tace"ko dai har yanzu jikin ne"? Ko kallo unaisah batai mata ba idanunta na akan taj, wanda ke sanye da facemask, A hankali take tariyo abun da ya faru jiya, lokaci daya ta rushe masu da matsanancin kuka wanda yayi silar farkawar batool.
Hankalinsu atashe su ka soma ambaton sunanta, tare da tambayarta meke damunta! Ko ciwonta ya motsa.
Sauko tayi daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja kofa ta rufe tana cigaba da yin kukan
Kallon juna ummi da taj sukayi a lokaci ɗaya, fuskokin su dauke da matsanancin damuwa, atare suka daura trays din hannun su kan table suka nufi bakin kofar toilet
Batool dake zaune kan gadon sai faman mutsustsuke idanu takeyi tana ambaton sunan unaisah...
Magiya suka dinga yi mata akan ta buɗe ƙofar
"Dan Allah unaisah Ki fada mana meke damunki? Ko cikin ki ke maki ciwo? Idan akwai inda ke maki radadi ki fadamin Yanzun nan zanje na karbo maki magani, wallahi mun damu dake jiya ko runtsawa bamuyi ba, har sai da muka ga kinyi bacci" cikin sigar lallashi ummi takeyi mata magana.
"My daughter ki yi shiru ki saurare ni, nasan meke damunki, ni nasan dama dole kiji haushi, inaso ki kwantar da hankalin ki, saboda mun riga da mun gano wacece tayi maki aika aikarnan kuma in sha Allah zamu hukuntata, idan ma kinaso zamu kawo maki ita, ki rama abunda tayi maki"
Maimakon unaisah ta sassauta kukanta, jin lallashinta da suke yi mata sai ma takara sautin kukan nata tamkar zata fasa kunnuwansu, da gudun gaske sajeed Ya fado dakin Yana haki daga shi sai gajeran wando bai jima da shigowa ba naufal Ya shigo shima yana tambayar meye faru da angel dinsu?
Shigowa suka dinga yi, daga me hamma sai mai miƙa daga gani basu jima da farkawa daga bacci ba, dama da tunaninta suka kwanta bacci jiya shiyasa suka farka da ita aransu, atare Jemimah da Azeeza suka shigo kowannan su kayan bacci ne a jikin shi, ba su jima da shigowa ba, Parveen ta shigo hannun ta ruƙe da brush, sumar kan nan a haukace gyaran gashin da akayi masu duk ya tarwatse kowa fa hankalinsa Ya tashi matuƙa, Jemimah sai kuka takeyi masu hada tsallanta tana fadin dama tasani mutanan nan sai da suka cutar mata da Angel dinta, wallahi bazata ƙyale su ba dole ta rama mata...
Gaba ɗayan su sunyi curko curko abakin kofar toilet din
"Please ku kwantar da hankulan ku, ku bari muyi kokarin shawo kanta sai muji meke damunta" ummi ta fada tana duban su kafin ta mayar da dubanta ga boss man.
"nifa ina tunanin watakil ko tayi zaton kai ne kayi mata wanka a daren jiya shiyasa take kuka"
Dafe kanshi yai da hannu ɗaya saboda shi ma ya yarda da maganar ummi, cikin muryar lallashi Yace"Unaisah, bani ne nayi maki wanka ba, Aunty umminku ce, bayan na dawo dake jiya na kawo ki gida da taimakonta kika tsarkake jikinki har kikayi wanka.. " kafin Ya kare maganar, cikin muryar kuka tace"ni ba wannan bane damuwana ba, daddy meyasa za ka yi min haka?
Hankali atashe taj ya ɗan zaro idanu Ya dubi ummi babu alamun ya fahimci abunda Unaisah take nufi sai ma cewa yayi"kinyi mafarki ne da daddynki"? A tsiwace tace"ba mafarki nayi dashi ba, a zahiri na ganshi jiya, saboda me zaka dinga 6oye min kanka daddy, ko ka daina sona ne" ta faɗa tana haki
Dariya ce ta kubcewa ummi ganin yadda taj ya daura hannayensu biyu saman kanshi alamar Ya shiga Uku gaba daya yabi ya ruɗe Sai lokacin Ya tuna da abun da Ya faru Jiya, da kanshi Ya cire facemask dinsa Ya jefar da shi saboda baya ahayyacinsa ashe idonta biyu taga fuskarshi
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka Yace"am really sorry my Angel, nayi laifi ay min afwa, nasan ban kyauta maki ba, amma dan Allah ki fahimce ni, ki nutsu ki saurari me zan fada maki.." kafin ya kare maganar ta katse shi da cewa"ni bazan saurari komai ba daddy, kawai ka daina sona ne ba ka damu dani ba, kuma ba ka yi kewata ba shiyasa kake 6oye min fuskarka..." ta fada tana jan majina kafin taci gaba da cewa"Daddy, what did I do to deserve this punishment from you? Daddy kasan kuwa irin kalubalan rayuwar dana fuskan ta? Daddy duk halin da na shiga ban ta6a mantawa dakai ba, bana kwana batare da na sanya ka acikin addu'ata ba, kullum zullumina ya rayuwar daddyna ta ƙare? Meya faru da shi bayan Ya jefa ni cikin ruwa, Ya rayu ko ya mutu.... "
Ba ta kare maganar ba saboda kukan daya ciyota, ta kuma fashewa da wani kuka tamkar ana zare ranta, abunne Ya tsaya mata aranta ya 6ata mata rai duk irin kewansa da tayi amma shine ya boye mata kansa.
Gaba ɗaya hankulansu Sajeed Ya koma kan fuskar tajuddeen, kalaman Angel ne suka fahimtar da su wanene shi
Muryar na rawa Azeeza tace"dama kai ne daddyn Angel wanda kullum take bamu labarin shi"?
Da sauri Parveen tace"idan bazan manta ba, duk in muka zauna fira unaisah saita bamu labarinka, itace tafara sanya mana kwaɗayin ganin ka, da zumudin son muje gidan su don muyi rayuwar ƴan ci, har fada mana takeyi daddyn ta zai kar6emu kamar ya'yansa..... Kasa karasa maganar tayi nan take ta fashe da kuka.
Cikin karyayyar murya Batool tace"ashe kai ne daddyn Angel, Ni burin da nake dashi idan Allah yasa na haɗuwa dakai shine inyi maka godiya saboda Angel ta faɗa min kaine ka ilmantar da ita, ka tsaya mata tsayin daka har ta samu ilmin addinin da take da shi, uwa uba kaine silar da Angel tazo duniya...." tana magana hawaye na wanke fuskarta.
"Wallahi ba mu ta6a sanin wanene mahaliccin mu ba, sai a sanadin zuwan Angel GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, , In da mu ka yi rayuwar kulle, cikin duhun jahil ci, harta toilet atare muke shiga da ƴan uwanmu maza Angel itace ta tsawatar mana ta fada mana cewa babu kyau mu daina haramunne wani yaga tsiraicin wani......" kuka ne ya kubce ma batool, ummi dake sauraransu a matuƙar ruɗe take ɗan zare idanunta akan fuskokinsu, gaba ɗaya sun jefa ta a cikin ruɗani lamarin yayi muƙar girgiza ta, tayi matukar razana.
Bata gama shan mamaki ba cikin sanyin murya haris Yace"Allah ne kadai zai iya biyanka daddy, zuwan Angel cikin rayuwarmu tamkar baiyanar haske ne a cikin duhu, wallahi baki bazai iya furta irin wahalar da unaisah tayi akanmu ba, duk da kasancewar ta ƙarama a cikin mu amma tana da kaifin basira kuma tana da hankali, Angel ta zama jigo na rayuwarmu, ta share mana hawayenmu a lokacin da muke kukan radadin kuncin rayuwar da muke aciki, Angel uwace agare mu, saboda ta kwatar mana ƴancin mu da aka tauye mana......" zu6ewa haris yayi kan gwiwowinsa hawaye naci gaba da sintiri kan fuskarsa, Gaba ɗaya sun gama kashe ma tajuddeen jikinsa, yayi sanyi laƙwas zuciyarsa ta karaya, wasu irin zafafan hawayene masu ɗumi suka soma wanko fuskarshi yayin da yake kallonsu ɗaya bayan daya, yana mai jin tsantsar tausayin su da kaunarsu azuciyarshi, Angel ta gama masa komai a duniyar nan baisan ma ina zai tsoma kanshi ba tsabar yadda Yake jin mahaukacin sonta na kara nunkuwa acikin zuciyarshi, ba zai iya misalta irin alfarin da ya ke da ita, burin kowani ubane ya sami ƴa kamar Angel wadda zata kare masa martabarsa da kimarsa a idon duniya, wadda zata daukaka darajarsa ta kuma yi silar shigar shi aljanna, hannu ɗaya ya daura akanshi Yana cigaba da kallon su jikin shi har kerna kerma ya ke yi.
Duk wannan abun dake faru a kunnan chief owais da Big guy wadanda basu jima da zuwa bakin kofar dakin ba, sunzo zo ne don su duba jikin Unaisah sai kuma suka ji abunda ba suyi tsammani ba wannan dalilin ne yasa suka dakata suna sauraron su
Cikin shessheƙar kuka Naufal Yace"daddy duk yadda zamuyi maka bayani ba lallai ka fahimce mu, amma wallahi muna kaunarka muna son ka daddyn Angel" wasu hawayen nan suka kuma wanke fuskar taj, idanunshi sunyi jawur da su gaba ɗaya ya rasa bakin magana sai dai kallonsu da yake tayi gwanin ban tausayi
"Unaisah itace take ƙarfafa mana gwiwa, itace komai namu, itace muke gani muji dadi, unaisah ko mun 6ata mata rai bata yin fushi damu ba, sai ma taja mu ajikinta saboda tasan bayin kan mu bane, rayuwa mu ke a cikin duhun jahilci, ....."
gaba ɗaya suka dubi batool da ta dauko maganar hawaye na sintiri kan kuncinta, dakatawa tayi da yin maganar na ɗan wani lokaci kafin taja numfashi taci gaba cewa"ɗaya daga cikin abun da unaisah tayi wanda har a bada bazai ta6a gogewa acikin zuciyata ba, shine musuluntar da yar uwar mu unaiza da tayi, unaisah bata bari unaizah ta mutu a matsayin arniya ba, sai da ta taimaka mata ta kar6i shahada duk don saboda ta tsira a lahira..." muryarta na rawa tayi maganar, kusan atare suka rushe da kuka tunawa da yar uwarsu unaizah, maganar batool ta fama masu raunin dake acikin zuciyoyin su.
zu6ewa su ka yi gaba dayansu saman gwiwowinsu agaban tajuddeen, suna kuka yana kuka babu mai lallashin wani a cikin su, ummi da batasan kan zancen nasu ba tuni itama ta fara matsar ƙwalla cikin rauni na murya tace dan Allah ku fahimtar dani ku yi min bayani tun kafin zuciyata ta buga, saboda hankalina ya tashi na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarku......."
Lumshe ido chief owais yayi, zuciyarshi ta karaya, wankan suit ne ajikin shi, bai jima da dawowa daga Airport ba wurin rakiyar prime minister.
A hankali Ya dubi Big guy dake a tsaye gefen sa, hawaye ya gani sun cika mashi idanunshi,
Shi kanshi dauriya ce kawai, amma kalaman su sun ta6a ta6a zuciyarsa.
Cikin sanyin murya ya furta"ka kira salsabeel a waya ka faɗa masa inji ni ya shirya sauran yaran, su zo nan gida su sameni, inaso suga yan uwansu"
cikin girmamawa big guy yace"okey, sir." ya faɗa tare da zaro wayarshi ya danna ma salsabeel kira wayar na fara ringing, yayi picking,
"barka da safiya yalla6ai"
"Yawwa barka, Ina fata dai ban katse maka baccinka ba" muryarshi da yar dariya yace"ay bana yin baccin safe saboda khadeeja kasan halinta kamar mai fama da cutar yunwa, tun da safe take tashina, don in shiga kitchen in dafa mata indomie"
"Allah sarki, ka cigaba da haƙuri da ita, Yanzu dai gani tare da chief, yace yana son ganin ka da sauran yaran yanzun nan ku same mu agidansa"
Muryar salsaleen da dan rudani yace"yallabai badai wani abune ya faru ba? Naji kace nazo da yara da sassafen nan"
"Ba wani abu kazo kawai, " amsa mashi yayi da toh, kafin su ka yi sallama Ya maida wayar cikin aljihu...
Angel dake atsugunne bakin kofar toilet din, jikinta ya gama yin sanyi tamkar wadda aka zarewa laka, duk abunda su batool ke fadi akan kunnanta tuni tayi shiru ta dakata da yin kukan, ita kanta bata ta6a tsammanin sun ruƙe kyautatawar da take yi masu ba acikin zuciyoyin su, shiyasa ake son bawa ya kasance yana aikata abun alkhairi arayuwarsa saboda duniya tayi alfahari dashi, al'umma su yi koyi dashi ko bayan ba ranshi, unaisah dai ta bada gudummuwa ta bangarori da dama harta ta bangaren addinin musulunci ta musuluntar kuma ta fadakar Allah ne kaɗai zai iya biyan ta.
Cikin shessher kuka suka soma yi mata magana, muryoyinsu duk sun disashe
"Yar uwarmu rabin ranmu, amadadin abban mu, muna baki hakuri dan Allah ki taimaki daddynmu, Kiyi hakuri ki fito yana son ganinki, daddy ya gane kuskurenshi kuma ashirye yake daya baki hakurin laifin da yayi maki.... " magiya suka dinya yi mata duk don su samu ta buɗe masu kofa
"Unaisah kin manta irin kyautatawar da daddynmu yayi maki tun kina karamarki, lokacin da mommynki ta gudu tabar ki a cikin kwamin wanka, ya daukeki yaci gaba da baki kulawa duk da kasancewar bakyajin magana ahaka yaci gaba da rainonki saboda irin son da ya ke yi maki shi bai tafi yabar ki ba, unaisah da bakin ki ki bamu labarin nan ko kin manta ne......" gaba ɗaya kowan nan su ya ƙosa ta fito saboda ta rungumi daddynta.
Ba zato ba tsammani, suka ga taj Ya dafe saitin zuciyarshi yana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Muryarshi da wani irin sauti na tashin hankali, gaba ɗaya suka zabura da sauri suka rufe shi suna ambaton daddy meke damunka? Baka da lafiya ne...."
Jin wannan maganar yasa unaisah yin saurin miƙewa, yatsun hannunta na kerma ta soma kiciniyar buɗe kofar, a fujajen ta fado dakin, ganinta yasa suka bata hanya, ta faɗa jikin tajuddeen ta ƙanƙame shi tana kuka take fadin daddy dan Allah kayi hakuri nasan nice na bata maka rai, ka tashi ka ji daddyna abun alfahari na, la66anta na kerma takeyin maganar, hawayen fuskarta tuni sun wanke fuskarshi, sumbatar goshin shi tayi, tare da manna masa wani kiss din kan kuncinsa ...." sai da taj ya bari ta gama firgita, tukunna ya buɗe idanunsa fuskarshi dauke da murmushi, fashe mashi tayi da kuka da sauri ya janyota jikinsa suka rungume juna tamkar zasu koma mutun ɗaya tsabar yadda suka matse junan su lallashinta yaci gaba dayi yana fadin"am sorry my angel, ki yafe ni, nasan bankyauta maki ba, wlh kina araina, kamar yadda kike fadin kin yi kewata nima haka nayi kewarki, angel rashinki ba karamin gi6i yayi min ba rayuwata sai da nakusa zaucewa saboda haukan rashin ki a kusa da ni, Angel bana iya bacci batare da nayi mafarkin ki ba, duk dare na Allah sai na tashi nayi salla saboda inyi maki addu'a Allah ya kare min ke duk da bani da tabbacin kina araye ko kin mutu......" dakatawa yai da yin maganar, idanunsa acikin na Angel dinsa, sai da ya fara tattara nutsuwarsa kafin cikin sanyin murya ya fara basu labarin abun da Ya faru dashi bayan ya jefa Angel cikin ruwa.
_______________________________✍️
Abun da ya faru lokacin da wadannan migayun dattawan su ka ƙyasta lighter bayan sun zazzaga mashi fetur a jikin shi, idan ba zaku manta ba, ba su kaiga jefa mashi lighter din ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna suka cinna wutar, sannan ba su tsaya sunga wutar ta kone sa ba, suka shiga cikin motocinsu tare da fusgarsu suka bar dajin a guje, bayan tafiyarsu hucin wutar Ya daki fatar jikinsa wani irin radadin azaba ne ya ziyarci sassan jikinsa, nan take ya farfaɗo daga suman da yayi ko da yaga wutar dake ci, cikin matsanancin tashin hankali ya yi wani irin kwakkwaran juyi da dukkan karfinsa gaba ɗaya ya rubza cikin Kogon ruwan daya jefa Angel, tsulundun Ya rubza cikinsa ya nutse can kasan ruwan kuma nan take ya sake sumewa.
Suna acikin ruwa ɗaya da Unaisah sai dai akwai tazara tsakaninshi da unaisah, wanda silar hakan yasa har danejo ta ceto rayuwar unaisah ba tare da tasan cewa akwai mutun acikin ruwan ba saboda ruwa daya ja shi... A kalla taj ya kwashe tsawon kwana uku acikin ruwan ba tare da ya samu taimako ba.
Ana haka cikin ikon Allah, Wasu fulanin daji dake kiwo daga can wata ruga dake a cikin dajin, su biyu matasa suka koro shanayensu zuwa wurin da ruwan nan yake, Anan suka yaɗa zango, to ɗaya daga cikin su mai suna habu mayen ruwa ne duk in suka zo bakin ruwan sai ya shiga yin wanka, babu irin gargadin da ɗan uwansa garbati baiyi mashi ba akan yadaina shiga ruwa saboda hatsarin dake gare shi amma yai kunnan uwar shegu da shi saboda taurin kansa da kafiyarshi, Abun ne yabi jikin shi tun suna kanana Yake shiga ruwa yin wanka har izuwa girmansa, shi kuma garbati mugun tsoron ruwane da shi, ko kusa da ruwa baison zuwa jikin shi kerma yakeyi saboda Labaran da yake ji daga wurin mutane dangane da mugayen halittun ruwa dake cinye mutun shiyasa yake jin shakkar kusan ta kanshi da ruwa, aranar da suka je bakin ruwan, habu na kokarin cire kayan shi don yashiga yayi wanka, garbati yayi saurin damƙar rigarsa suka soma kokawa a tsakaninsu, cikin harshen fulatanci suke magana garbati yace wlh bazaka shiga ruwan nan ba, ka manta da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi?
Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hankaɗe garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci.
Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma ɗaura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu
Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa.
Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka daɗe suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa
Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri ɗaya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin ɗan mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya ɗaga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba ɗaya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka ɗaure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi ƴan dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi....
Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan ƴarsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba,
A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time ɗin kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya ƙafe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa.
Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya ƙi komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya haɗa mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai buƙata......
Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba ɗaya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba ɗaya hankalinshi baya akanta....
Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta.
Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta.....
Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba.
Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta.
Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar hausar ke fita irin ta ƴan koyo.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa
Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta ɗebe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira kaɗan kaɗan saboda rashin sabo, da kuma ƙarancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba.
Tun daga ranar daya haɗu da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, roƙansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ƙara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta ƙwalla rai akanta ne?
Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da buɗar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu na neman wuce gona da iri.
Cikin kwantar da murya yace masu su yi hakuri, su daina bugunta indai saboda shi ne yanzu zai tafi yabar masu rigarsu" sam basu fahimci me yake cewa ba, sai ma wani irin kallon tsana da suke jifar shi da shi, har ya juya zai tafi danejo ta ruƙo hannunsa, a fusace gidado ya ruƙo hannunta, suka riketa don kada tabi shi.
Sautin kukanta ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, shi kanshi baya son rabuwa da ita, ba don yaso ba sai don ba yadda zaiyi ne...
Har yayi nisa da tafiya, ya ɗan dakata zuciyarshi na raya mashi ya juya ya kalle ta, watakil bazai sake haɗuwa da ita ba, har zuwa lokacin da zai bar dajin,
Juyawar da zaiyi keda wuya, kwatsam idanunsa suka sauka akan rigar Angel dake shanye kan ɗaya daga cikin bukkokin su, daga gani wanke ta akayi aka shanya don ta bushe, da farko bai tantance abunda idanunsa ke nuna masa ba, sai da ya ɗan kara ƙura idanunsa tukunna Ya shaida itace rigar baccin da ke a jikin Angel aranar da ya gudo da ita, sune kayan jikin ta, was wasi yafara yi a cikin zuciyarsa tayaya akai rigar unaisah tazo dajin a hannun fulani? Ko dai suma suna da irin rigunan gayu ne"? Farat ɗaya zuciyarshi ta bashi amsa da cewa me zai kawo irin wannan suturar a hannun mutanan da ke rayuwa a daji? Sai dai idan tsintar ta su kayi...' muryarshi na rawa ya furta"idan har dagaske ne abunda nake hasashe tabbas Wani ya ceto rayuwar Angel ɗina bayan na jefata a cikin ruwa tun da gashi har rigarta ta bayyana...
Ba zato ba tsammani, suka ga mutumin da suka kora ya watso da gudu ya dawo wurin rigarsu, har sun har zuƙa zasu fara dukanshi da sandunan su sai kuma suka fasa ganin Ya damƙo rigar da danejo ta shanya kan bukka, ruƙe rigar yayi a hannunshi zuciyarshi na bugawa da matsanancin karfi ya soma ambaton sunan Angel Angel, Lokaci ɗaya su bawuro da su hasiya suka kalli juna da mamaki jin yana ambaton sunan yarinyar da danejo ta tsinto a cikin ruwa, tambayar shi suka soma yi wanene shi? Ya akai yasan yarinyar?
Hawaye na zuba daga idanunsa ya dago rigar yana nuna masu yace" wannan rigar ta ƴata ce Angel, da hannuna na jefa ta cikin ruwa, dan Allah ku fada min a ina kuka samu rigar? Ko dai kune kuka ceto rayuwarta....." kukane yaci karfinsa, gaba daya ya rikice masu, su kansu so suke son san me yake cewa don suji ko shine mutumin nan da yarinyar take nema don bazasu ta6a mantawa ba da irin kukan data dinga yi masu tana kaisu bakin ruwa donsu nemo mata daddynta tun basu fahimtar me take cewa har suka gane cewa wani nata ne take nema..
Danejo ce kaɗai ta fahimci me Yake cewa, nan take ta fashe da kuka Cikin harshen fulatanci ta sanar ma sauran ƴan uwanta abun da taj Ya ke faɗi nan suka gane cewa shine mahaifin Angel, yarinyar data tsaya masu aransu, har yau har gobe basu cireta aransu ba, hakika sunyi farin ciki mara misaltuwa da ganinsa.
Tsabar farin ciki yasa danejo ta watsa da gudu ta fada kan kirjinsa ta rungume shi tana kuka, ta soma tambayarshi ina Angel? Ko ya ganta"? Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, a ruɗe ya tambaye ta me take nufi? Ba su suka taimake ta ba" cikin sanyin murya danejo ta labarta mashi komai daya faru tun daga lokacin da ta tsintota a cikin ruwa har zuwa time da ta gudu daga rigar su.
Wani irin jiri yaji yana shirin kwasarshi saboda kuncin dayaji, bakomai ne ya jawo mashi jinkirin da yayi ba nazuwa daukarta face loosing memory din da yayi.
Zubewa yai kan gwiwowinsa zuciyarsa a hautsine tamkar zata buga, gaba ɗaya suka kewaye shi, suna kallon shi gwanin ban tausayi, ganin yadda ya ke matsar kwalla.
Saboda son da suke ma Angel yasa suka yi mashi kyakkyawar tarba, a kalla ya shafe wata a rigar su, kafin Yaji bazai iya cigaba da zama a dajin ba, kwara ya koma gida watakil idan yaje can ya sameta ta koma wurinsu Aneelerh.
Ranar da taj ya shirya tafiya, zai bar rigar, ya yi masu bankwana kamar karsu rabu, yace masu zai fara zuwa wurin mutanan da suka taimake shi kafin ya wuce garin su, guzurin tafiya suka hada masa, kowa ya kawo abunda yake dashi, suka bashi sannan sukace mashi idan Allah yasa yaga yarsa angel ya fada mata sunyi kewarta, zuciyarshi cike fal da kewarsu ya kamo hanya zai bar rigarsu, harfa yayi nisa yajiyo takun gudunta sai faman kwala mashi kira takeyi, a hanzarce ya juya yana kallonta, danejo ce hannunta ruƙe da kullin kayanta, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, ganin ta biyo shi.
Karasowa tayi tana haki tace"dan Allah ka tafi dani inason ganin Angel"
Girgiza mata kai yayi"kiyi hakuri bazan iya tafiya dake ba, meyasa kika yarda dani har haka? ki yi hakuri ki koma wurin ƴan uwanki" fashewa tayi da kuka.
Ana cikin haka, yajiyo sautin takalman yan uwanta kusan gaba dayansu ne suka biyota.
Fuskokinsu babu walwala, ruƙo hannunta kakansu yayi tare da mika ma taj, da mamaki yake kallonshi don bai fahimci me yake nufi ba, har saida yayi mashi da kurmanci Ya nuna mashi cewa ya tafi da ita, sun bar mashi ita, saboda tace in har basu bari tabi shi ba, to zata kashe kanta ne, shiyasa suka yanke shawarar kwara su bar mashi ita, don ko sun barta ba lallai su iya shawo kanta ba.
Babu yadda taj baiyi da su ba akan subar yarsu, hankalinsu sai yafi kwanciya idan tana akusa da su amma suka sanya kafiya akan dole ya tafi da ita, ganin ya turje ne yasa suka fada mashi cewa marainiyace, tun kafin ta mallaki hankalin ta iyayenta suka rasu, bata ta6a neman wani abu daga gare su tarasa ba, don haka sun bashi amanarta, yaji tsoron Allah ya rike masu ita amana su je can su yi aure, hawaye ne suka wanke fuskarshi, jiki asanyaye yasa hannu ya ruƙo hannun danejo,yayi masu alkawarin bazai ta6a bari ta nemi wani abu ta rasa ba, zai dauki dukkan wani nauyi nata zai bata kulawa, sunji dadin abunda ya fada masu a karshe sukayi bankwana da junansu, yaja hannun danejo suka nufi rigarsu Habu.
har sun fidda rai da sake ganin shi, tsawon kwanakin da yayi a rigarsu danejo kusan kullum sai sunzo neman shi a yar bukkarsa, sunyi mamakin ganin ya dawo masu tare da yar matashiyar budurwa, cikin harshen fulatanci danejo tayi masu bayanin komai dangane da taj...."
labarin tajudden da Angel ya ta6a zuciyoyinsu, har hawaye suka zubda masa saboda tsananin tausayin shi da suka ji, bayan komai ya lafa ya sanar da su zancen tafiyar shi, ba don sunso ba sukayi mashi fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa yaga yarinyarsa, kafin tafiyarsa saida suka hada mashi shatara na arziki, bayan haka suka yi masu rakiya har zuwa bakin titi, ba su tafi ba sai da sukaga ya samu motar hayar da zata shigar da shi cikin garin joss tukunna sukayi mashi bankwana.
Tun da suka shiga motar, danejo ta kankameshi, kamar wani yace zai kwace mata shi, wani irin mugun tsoron mutane take ji, mutun ɗayane ta yarda dashi ta kuma damka amanarta agareshi saboda tasanyawa ranta cewa bazai ta6a cutar da ita ba.
Kafin su karasa cikin garin, tuni bacci yayi awon gaba da ita, a yayin da kanta ke asaman kirjinsa, hankalin taj sam ba akwance yake ba, saboda fargaban kada miyagun da suka kai mashi farmaki su gansu, yasan muddin sukasan cewa bai mutuba, to kuwa zasu nemi hanyar da zasu kashe shi ne kamar yadda suka kashe dan uwansa uzair, mutuwar da tayi matuƙar girgiza shi, dabara ce ta fado mashi da sauri ya sanya hannu ya cire gyalen danejo da take daure qugunta da shi, ya lullu6e fuskarsa, Idanunsa ne kadai suke a bude.
Bayan isarsu joss, motar ta sauke su a tasha, driver yace ina kudin mota, sai lokacin ya tuna da baida ko sisi, sai dai kayan da fulanin nan suka bashi, hakuri ya bashi ya hada shi da katon dawon fura, mai motar baiyi gardama ba ya kar6a, ruko hannun danejo yayi suka soma tafiya atare har ya sama masu abun hawan da zai kaisu unguwar da su ke, kafin isar su tuni dare ya ritsa da su.
Da farin cikinsa Ya zo unguwar, amma lokacin dayaga gidajensu a kulle, nan take murnar ta koma ciki, tunkafin ma yaji abunda ya faru hankalinsa yai mugun tashi, baisan ina zai tsoma kanshi ba, ga yar mutane da yake ta yawo da ita, harta fara yi mashi kukan yunwa take ji, tausayinta ne ya kama shi, da ya san hakan zata faru dabai yi kuskuran tafowa da ita ba..
A bun hawa ya kuma tsaida masu, suka nufi gidan uncle abdalla da ita don ya ga ko sun dawo daga south korea, tunkafin me abun hawan da ya kawo su ya sauke shi ya hango gate din gidan a kulle alamar basa nan, tamkar ya daura hannu aka ya fasa ihu haka yaji.
Tunawa da amininsa muhsin wanda Angel ta ta6a sace ma matarsa waren takalmi yasa shi yanke shawarar zuwa gidan shi tare da danejo, yasan acanne zai ji komai daya faru bayan 6acewarsu
Basu sha wahala ba, cikin sa'a suka same shi agida, tare da matar shi, lokacin dayaji sallamar taj a firgi ce ya mike zaune yana kallon kofar shigowa falon, bai gane shi ba har saida ya cire mayafin danejo dake akan fuskarsa tukunna ya shaida shi, muryarshi na rawa yace taj! Dama kana araye? Tsawon lokaci muna ta neman ku babu kai ba uzair duka an nemi ku an rasa"? A rude yake jefa mashi tambayoyin, matarshi da sauri ta nufi danejo ta ruko hannunta suka zauna kan sofa, kafin ta mike ta shiga ciki ta kawo masu abinci da ruwan shi.
"Dan Allah abban muhsin kabarshi Ya huta, bakasan daga ina yake ba, sannan bakasan meya faru dashi! Idan har bai samu nutsuwa ba tayaya zai iya fayyace mana abunda ya faru da su"? Fuskarta a yamutse tayi maganar, jinjina kai yayi fuskarsa da tsantsar al'ajabi yace da taj su shiga ciki yayi wanka ya canza kayan jikin shi, yaga duk sun jigata kamar na almajirai,
Bayan sun huta, sunci sun koshi, har bacci yayi itama danejo ta dan runtsa, wuraren karfe shabiyu na dare yafarka ya taras da muhsin ya zabga uban tagumi yana kallon shi, mamakine yacika shi.
"Ka yi hakuri taj, kada kaga na takura maka, wallahi na damu da rashin ku, hankalina bazai ta6a kwanciya ba har sai ka fadamin meya faru da ku da har kuka gudu aka neme ku aka rasa......"
Mikewa zaune taj yayi, kafin a tsanake ya labarta masa komai daya faru, wani irin matsanancin kuka mai cin rai muhsin ya fashe dashi, bakomai ya firgita shi ba ya kuma bashi tsoro face mutuwar amininsu uzair ta yi matuƙar girgiza shi, cikin shesshekar kuka ya ke fadin"taj dama abunda ya faru daku kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan wata irin masiface, Uzair ya mutu, Angel ta 6ace, rana ɗaya an tarwatsa farin cikin zuri'arku, in sha Allah sai Allah ya saka maku wannan zaluncin da akayi maku....."muhsin ya yi kuka tamkar ransa zai fita,
Lallashinshi taj ya somayi yana fadin yayi hakuri komai ya riga daya wuce, yanzu shi damuwarshi ina aneelerh take matar uzair"?
Daƙyar muhsin Ya samu nutsuwa, ya fara mashi labarin abunda Ya faru bayan 6acewarsu,
Yaji dadin jin cewa Aneelerh tana agidan iyayenta, abun da ya faranta ranshi, Yaron da yaji ta haifa masu, tunkafin ma yaganshi Yaji Ya kamu da kaunarsa, kaunar da yake yima uzair gaba daya ta koma akan yaron da bai ta6a ganinsa ba......' acikin labarin da muhsin ya fada masa abu ɗayane bai sanar da shi ba, rasuwar iyayensa gudun kada zuciyarsa ta buga, kwara idan ya samu nutsuwa ya sanar dashi daga bisani.
A daren ranar kafin muhsin yabar dakin taj, Sai da taj ya gargaɗesa akan kada ya sanar ma wani cewa yagansa saboda rayuwarsa tana acikin hatsari, idan mutanan da suka kashe uzair suka san da zaman shi tabbas zasu cigaba da bibiyarsa har sai sunga bayan shi.
Cikin sanyin murya muhsin yace in sha Allah babu wanda zaiji zancen dawowarshi, zai rufa masa asiri yaci gaba da zama a gidansa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mashi mafita....
Tsawon wata guda suna agidan muhsin, a cikin kwanakin da yayi baya iya runtsawa saboda damuwar rashin angel, duk daren Allah Sai yayi nafilfili saboda angel dinsa, duk ya fita hayyacinsa sam baya da koshin lafiya ciwon kafarsa tamkar ana fama masa shi abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa, muhsin yaso ya bi shi suje asibiti a duba lafiyarshi gudun kada ya rasa ranshi amma yaki yarda saboda bayason wani yaga fuskarshi, ya ƙwammace idan ma mutuwarce ta dauke shi agidan muhsin zaifi mashi sauƙi akan wadannan azzaluman mutanan su kona shi.
A daren wata rana ne, Yana cikin Yin nafilfilin dare, Yajiyo dirar motoci a cikin gidan muhsin, A firgice Ya mike daga kan darduma Gabansa na faduwa, baisan su wanene sukazo gidan muhsin ba, a irin wannan lokacin karfe kusan sha biyu na dare, zuciyarsa na bugawa ya nufi falon gidan don ganin su wanene,
Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, ganin matasan samari masu jini ajika suna shigowa kowannansu sanye cikin shiga ta bakake kaya sun rufe fuskokinsu da facemask.
Bakomai ne ya tsoratar da shi ba face tunawa da wadannan body guards din da suka budewa alhazawannan motocinsu, nan take ranshi ya bashi cewar sune, hakan na nufin muhsin Yaci amanarshi, bayan yayi mashi alkawarin zai rufa masa asiri shine yabi ta bayan fage ya tona masa asiri, zuciyarshi ajagule ya furta meyasa zaiyi min haka! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankalin shi danejo kada suce zasu haɗa da ita su kashe...
A lokacin zuciyarshi ta riga ta gama hasala, Jininsa akan akaifarsa yake, tunkararsu yayi muryarshi a fadace yace"kun biyo ni nan dinma donku kashe ni? Laifin me nayi maku ne? Da ɗaci aransa ya furta maganar, kamar daga sama yaji muryar muhsin daga bayan shi yana fadin"taj, ka tsaya zanyi maka bayani" a sukwane ya juya ya kalle shi a fusace yace"wani irin bayani zakayi min muhsin? haka mukayi dakai? ka cuce ni muhsin, ba zan ta6a yafe maka ba, yanzu dakai za'a hada baki don akashe ni"? Hawaye cike tab da idanunsa yayi maganar, fitowa danejo da matar mushin sukayi daga dakin duk suka tsaya suna kallon su....
Matasan da suka tsaya abakin kofar falon sun harɗe hannayensu akan kirjinshi suna kallon shi, babu alamun zasuyi magana..
"Taj bazan ta6a cin amanarka ba, abun da ya faru da kai ba kai ka ɗai ya shafa ba, hada ni kaina saboda ina jinka tamkar ɗan uwana na, waɗannan matasan da kake gani, ba su zo da niyar su cutar dakai ba, sai don su taimaki rayuwarka, Idan ka basu hadin kai in sha Allah zakuyi nasarar nemo Angel dinka data 6ata, bayan haka zasu tayaka daukar fansa akan mutanan da suka kashe uzair"
"Har yanzu ban fahimci inda zancenka ya dosa ba .." murmushi muhsin yayi kafin yaci gaba da cewa"su ɗin jami'an hukumar ISOD ne, nasan ba zaka rasa sanin CHIEF OWAIS ba, ɗan gidan Sharafudeen Obinna......" wani irin al'ajabi ne ya kama tajudden muryarshi na rawa ya maimaita sunan Chief Owais da tsantsar mamaki yace"muhsin dagaske kake min ko wasa? Tayaya akai ma su kasan da zamana"
Kafin muhsin Ya bashi amsar tambayarshi, Chief owais Ya shigo bakin shi dauke da sallama cikin shiga ta kakin isod, da sauri matasan nan suka buga kafa tare da sara mashi, muhsin kamar zaiyi mashi sujjada tsabar yadda yake washe baki yana yi mashi sannu da zuwa yalla6ai, shi dai taj ya gaza yarda da abunda idanunsa suke gane mashi, kai ko a mafarki bai ta6a tsammanin zai haɗu da chief owais ba, mutumin da a tv kadai yake iya ganinsa, sai gashi yau a zahiri Allah Ya nuna masa shi.
Cike da qasaita, Chief Ya nuna masa sofa alamar Ya zauna" jiki na 6ari taj yaje ya zauna yana ta faman bin shi da kallo a lokacin shima ya zauna kan sofa din dake fuskantar ta shi.
Cikin harshen turanci yace"nasan zaiyi wuya ace baka sanni ba, amma duk da haka zan gabatar maka da kaina, da farko sunana owais sharafudeen Obinna, chief na hukumar Isod...." ya faɗa tare da ɗan dakatawa yana dubansa, tun anan taj ya fahimci ba karamin mutunne bane mai ji da kansa.
"Malam taj, kamar yadda kake mamakin ganina nima haka nake mamakin kasantuwana acikin rayuwarka, ko a mafarki ban ta6a tsammanin akwai ranar da zan hana idona bacci saboda damuwa da mutumin da bansan wanene shi ba...." kalaman chief owais sun girgiza shi matuƙa, har dai ya gaza jure wa yace"dan Allah ka fadamin meyasa ka damu dani bayan baka sanni ba"
da buɗar bakinsa sai cewa yai"ƴarka ce sila" waro idanu waje taj yayi da tsantsar mamaki yake binsa da kallo fuskarsa da rudani yace"meyasa kace haka"?
Numfasawa yayi kafin ya soma magana muryarshi tamkar ana busa sarewa saboda dadin sauraranta....
A washe garin ranar dana dawo Nigeria daga U.S anyi min wani kira da ya tsaya min araina....
Fitowa yayi daga cikin bathroom waist dinsa daure da towel, yayin da dayan hannunsa ke a ruke da wani short towel yana tsane sumar kanshi, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, wayarsa dake akan nightstand ta soma ringing, dakatawa yayi da tsane sumar kan da yakeyi a hankali ya nufi wayar ya dauko ta yana duba number din da aka kirasa da ita, yayi mamakin ganin bakuwar number, A matsayin shi na jami'in sirri komai nasu asirrince suke yin shi, harta phone number dinsa special ce, bakowa yasan shi da ita ba, sai mutun yakai yake samun damar mallakar ta, bai yi niyar picking call din ba saboda a ka'idarsa baya ɗaga bakuwar number, ko kiransa akayi indai ba family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi......
Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa...
Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba.
Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"?
Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce,"
Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa,
"kinsan dawa kike magana"?
"a'a," ta bashi amsa atakaice
"Ur age"?
"7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?
"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"
Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa
"Can i call u video"?
Da sauri tace eh,
Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka ɗana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba ɗaya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta...
"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ƙananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon ƙurulla kamar zai haɗiyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba...
Zuciyarsa ba ƙaramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta....
Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin yaɗa aikinsu na ƴan jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba.
Gaba ɗaya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance ɗaya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........
Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar.
Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba ....
Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya ƙwalla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ...
Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su...
A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel.
Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a.
Muhsin yana ɗaya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi ɗayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji ɗuriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba...
Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take,
"Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi,
Da sauri chief ya ruko hannunsa acikin nashi, cikin sanyin murya yace"ka yi hakuri, ni banzo don na fama maka raunin dake acikin zuciyarka ba, nazo ne don na tallafi rayuwarka, idan har ka bani hadin kai nayi maka alkawarin zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baka kariya, na kuma tallafa maka da duk abunda nake da shi, Allah shine Ya hadani dakai ta silar yarka, Ina jinta tamkar kanwata, muhsin Ya sanar dani komai dangane da abun da ya faru dakai wanda yai silar bacewarku, in sha Allah mutanan da suka yi maku wannan aika aikar sai sunyi danasanin kasantuwarsu a doron duniyarnan......."
kwantar masa da hankali chief ya cigaba da yi har saida yaga ya fara samun nutsuwa tukunna yace mashi zai jira ya yanke shawara...." ai tunkafin ya karasa maganar taj yace mashi ya amince, zai basu hadin kai, babu wata shawara da zaiyi, saboda shi bashi da mafita kwara su tallafa masa ya nemo yarsa.....
Sunji dadin yadda taj ya amince masu batare da 6ata lokaci ba chief, Yace mashi su fara shiri zasu tafi abuja tare da shi, saboda Yana so ya sama masa muhallin da zai zauna akusa dashi sannan yace zai sama masa gurbi a hukumar su ta Isod bayan ya kar6i training dinsu, bayan tafiyarsu tajudeen abuja, rayuwarshi ta sauya, chief owais ya gatanta shi, a cikin gidansa ya ware masa part ɗaya, inda zai zauna tare da danejo bayan haka ya bashi kyautar mota, cin su da suturarsu gaba ɗaya shine yake daukar nauyin su, Kafin taj Ya fara kar6ar training din Isod sai da yafara auran danejo saboda yana son su ƙara kusanci da juna, bayason tayi kewar rashin wani nata.
Big guy shi ne mutumin da ya shiga gidan Uzair, aranar da Aneelerh taje gidan har ya ɗauke mata baby junaid, bayan haka sune jami'an sirrin da suka kaita gidansu har su ka yi mata tambayoyi da suka shafi 6acewar su Angel.
Sauke numfashi yayi bayan ya gama basu labarin cikin sanyin murya yace
_"Kunji yadda akai na tsira daga hannun mutanan da suka so rabani da rayuwana, hakika cheif yayi min halaccin da bazan ta6a mantawa ba, ya kyautata min, ya faranta min a lokacin da gwiwata ta sage na fidda rai da rayuwar duniyar nan, badan Allah ya ƙaddarar haduwata dashi ba, da yanzu bansan awani hali zan tsinci kaina ba"_
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*
*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*