Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 18 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 18 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_
                     سجن القد💋🔥💞                      ~Takun Ƙarshe🔥~
            Dedicated to Aunty Kubra💋💞
قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘
Daga alƙalamin Boss Bature💋✊


__________________________✍️
💫HAJIYA SARATU💫

_safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abun da Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanuƙarta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ƙwarin gwiwar yi mata haka? ruƙe qugu tayi da hannu ɗaya fuskarta babu annuri_


Maganganun da suka Tattauna jiya ita da su Har excellency ta soma tariyo bayan fitowarsu daga hall kafin su nufi gidan prime minister."Meyesa pravin zai ja hannunta abainar jama'a? Menene alakarsu? Wai ku ba ku zargin wani abu atsakanin su"? Hajiya laurace ta fada babu wasa akan fuskarta


"Najima ina zargin matar nan, na dai yi shiru ne ban fada maki ba, saboda bana so in shiga tsakanin ki da mijin ki, amma ni kwata kwata hankalina bai kwanta da ita ba, tun daga kan yanayin yadda take daukar wanka zaki fahince akwai wata a kasa ba banza ba, ni ay ban ta6a ganin yar aikin da ta samun ƴanci kamar hajjaty ba"! Her excellency muhibbat ce tai maganar,

Hajiya jamila tace"yanzu wani hukunci zaki yi masu"? ta fada tana kallon hajiya saratu.


Da sauri Hajiya madina tace"please, ku daina tunzurata ku bar ta taji da abun da ke damunta, ni banga abun ɗaga hankali a maganar nan ba!"


Hajiya saratu da ke sauraronsu ɗaya bayan ɗaya sai da ta cika ta batse kafin tace


"Wallahi bazan ƙyalesu ba! Daga ita har shi sai sun fuskanci 6acin raina, sai tayi danasanin kasantuwarta yar aiki a gidan nan"! Ta fada a tsiwace tana huci


"Ni shawarar da zan baki kawai ki kore ta daga gidan ta koma can kasarsu acigaba da bautar shanu, idan ba haka ba Allah kaɗai yasan munaƙisar da take shirya maki, ƙwara tun wuri ki yi maganinta kafin ta jaza maki matsala" Acewar hajiya Muhibbat


Dafa kafaɗarta hajiya laurat tayi"idan da zaki bi shawarata kada ki tanka masu! Nasan yanzu hankulansu atashe yake saboda sun san dole ki tuhume su, abun da yakamata ki yi shine ki manta da zancen hukunta su, ki yi tamkar babu abun da ya faru, za su yi zaton kin kyale su ne, ki bari sai sun shagala tukunna ke kuma ki fara bincike akan su, ta haka ne kadai zakisan meke atsakanin su amma yanzu idan kikace zaki hukuntasu to ba za ki san menene alakarsu ba, kwara ki fara bin diddiginsu har zuwa lokacin da zakiyi nasarar kama su dumu dumu"


Jinjina kai hajiya saratu tay alamar gamsuwa da shawarar Hajiya laurat..


Bayan ta dawo daga duniyar tunanin taja gauran Numfasawa haɗi da ɗan jinjina kanta, cikin takun sauri ta nufi wayarta dake ajiye kan pillow ta dauka ta kira landline na kitchen.


Tana fara ringing akayi picking, kara wayar tai a kunnanta.


 "Inason ganin Marwa, ta same ni adaki bana son bata lokaci" 


ta fada tare da katse kiran ta ajiye wayar


Cigaba da zagaye bedroom din tayi, yayin da take dunkule tafin hannunta na dama tana tura shi ana hagu kamar ƴar dambe.


Knocking kofar da akayi mata ne yasa ta dakata.


"Wanene"?


"Aunty ni ce marwa"


"Okey shigo ciki"


Turo kofar tayi, Jikinta sanye da uniform na ma'aikatan gidan ta shigo, cikin girmamawa ta gaishe da hajiya saratu, bata amsa mata ba, sai tay tamkar ba ta ji me tace ba.


Tuni marwa ta sha jinin jikin ta, tsoranta kada ace wani laifin ta aikata da yasa hajiya saratu ta kira ta don tasan halinta masifaffiya ce.


Muryarta na rawa tace"Am.. Aunty gani, naji kina nemana"


Wurga mata harara hajiya saratu tayi da sauri ta dukar da kanta kasa

Tsawon lokaci bata tanka mata ba, gani ta ke kamar zubda ajine ta nemi taimakon yar aiki, sai dai ba yadda zata yi itace kadai hanya mafi sauki agareta.


Zama tayi gefen gadonta, cike da isa ta dubi marwa"ke zonan"! da sauri marwa ta dawo ta zukunna agabanta.


"Wani aiki nakeso kiyi min, bana so kowa ya sani daga ni sai ke! Na yaba da hankalin ki ne shiyasa na za6e ki saboda nasan zaki Iya......" Tun da tafara magana marwa ta soma zare idanunta cike da fargaba.


"Kafin na faɗa maki, zan gindaya maki sharadi, Idan har na kuskura naji maganar nan abakin wani, ko kika bani matsala wallahi thumma tallahi na lahira sai yafi ki jin dadi...." Wani irin yawu marwa ta haɗiya jiki na bari tace"in sha Allah zan kiyaye."


Ta6e baki tayi kafin ta ɗaura da cewa"    me kika sani dangane da head maid din gidan nan? ya mu'amalarta daku take? Sannan Wacece aminiyarta acikin ku?  Shin tana fada maku sirrinta"?


Shiru marwa tayi aranta ta ayyana to fa! Ko me hajjaty ta aikata ma aunty masifatu da take neman karin bayani dangane da ita? Watakil watan cin ubanta ne ya tsaya


A fili kuma tace "Abun da nasani dangane da ita, macace mai saukin kai, tana da mutunci kuma tana kyautata mana, ba ta shiga sabgarmu, sannan bata cika zama yin fira da mu ba, macece mai kamun kai bata da surutu, sannan bata da aminiya acikin mu balle har wani yasan sirrinta, wannan shine Iya abunda sani"


Tur6une fuska hajiya saratu tayi, ita ba haka taso taji daga bakin Marwa ba.


"Okey, ki nutsu ki saurareni," jinjina mata kai tai

"Daga yau inaso ki fara shisshige mata, saboda ina zarginta, inason kisan duk wani sirrinta, ki zama aminiyarta, bayan haka duk wani motsinta ya kasance a tafin hannunki, idan har kikaga wani abu ba dai dai ba, to kiyi hanzarin sanar dani," amsa mata tayi da toh


"Idan har na samu abun da nakeso nayi maki alkawarin zan baki mukamin da take da shi agidan nan, bayan haka zanyi maki kyauta ta musamman, kin dai san wacece ni, basai nayi maki bayani ba" 


Wani irin farin cikine Ya lullu6e marwa musamman da taji Hajiya saratu ta ambaci zata bata mukamin hajjaty ga kuma kyautar da zata samu, aranta ta ƙudiri aniyar saita yi ma hajjaty kutse koda kuwa bata kama ta da laifin komai ba, ita zata ƙala mata sharrin da za'a sauke ta daga kan mukaminta.


Shu'umin murmushin gefen fuska tasaki.


"Baki da matsala dani aunty, in sha Allah zaki samu abunda kikeso"


"Zaki iya tafiya" mikewa marwa tayi zuciyarta cike fal da murna, dama ta jima tana jin haushin hajjaty saboda yadda tayi masu zarra agidan, komai itace akan gaba, gata head maid ga farin jini awurin mutanan gida, bayan ba wani aiki takeyi ba acikin gidan sune masu wahalar girka abinci, ita aikin ta tsara  abunda za'a girka ne da kuma bada umarnin yadda abu zai kasance.


Dole ta ɗana mata tarkon da bazata Iya  fidda kanta ba, ko dan ta ƙwace mukamin ta, wannan alwashine ta daukarwa kanta!


Ta fada aranta, yayin da take nufar hanyar komawa kitchen


Bayan fitar marwa, hajiya saratu ta sauke ajiyar zuciya, yanzu ne ta samu kwarin gwiwar shiga toilet yin wanka


Lokacin da fito, A zaune ta same shi gefen gadonta, sam bataji alamun shigowarshi ba.


Tun da ya ɗago suka hada ido da ita yai saurin sunnar da kanshi kasa, wani irin nauyinta yaji, baisan ta ina zai fara shawo kanta ba, Yasan dole ta tuhume shi akan abun da Ya faru jiya.


Kau da ido tai daga kan shi, Ta juya ta  nufi closet, jim kaɗan Ta fito har ta sanya riga bubu ta atamfa, gaban mirror ta tsaya tare dakai hannu ta dauki turare ta soma feshe jikin ta da shi, yadda ta share shi kamar batasan da zaman shi a dakin ba.


Shi kuwa gogan Ya kasa dauke idanunsa daga gareta.


Kamshin turarenta ne yakai mashi karo har ya gaza jurewa duk da shakkarta da ya ke ji ƙarfin hali yai wurin furta"Har Yanzu fushi kike dani? Banza tayi da shi

Mikewa yai tsaye ya nufeta, daga bayanta ya dan dakata Yana bin ta da kallo.


Kafin cikin sanyin murya yace "Tun jiya nake ta so na baki hakuri, nasan ban kyauta maki ba, ni kaina ba'a hayyacina na aikata hakan ba, bansan meyasa na ruko hannunta ba, wallahi sharrin shaiɗanne"


Murmushin gefen fuska tasaki, ba tare da ta bari ya gani ba, dama dagangan ta dauki wankar da zai zautar da shi


"Na cancanci kowani irin hukunci daga gareki, a shirye nake dana kar6e shi, ni dai bana son 6acin ranki"


ya faɗa tare da ɗaura kansa saman kafadarta saboda karfin hali irin nashi

Lumshe idanunsa yai tare da shakar kamshin turarenta.


"Kinyi shiru baki ce min komai ba" sai da ta mula tasha iska tukunna Tace"laifin me kayi min"?


"Kin riga da kin sani"


"In dai dangane da abunda ya faru jiya ne to ka manta kawai, bana son tada maganar, ko alokacin abunda yasa raina ya 6aci saboda ina kishin ka ne banji dadi ba, amma yanzu komai ya wuce"


Tsabar mamakin kalamanta yasa shi saurin ɗagowa yana duban fuskarta ta cikin mirror.


"Amma dai wasa kike min ko"? Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"na taba maka wasa irin wannan"?

Girgiza kanshi yai"a'a, baki taba min ba, amma dai nayi mamaki, Allah yasa ba mafarki nake ba" juyowa tayi suka fuskanci juna, fuskar ta dauke da ƙayataccen murmushi ta ɗaura hannayen ta a kan kafadunsa.


 Lamarin ya ɗaure masa kai gaba daya ta canza mashi kamar ba hajiya saratun daya sani ba.


Cikin sanyin murya tace"hubby, kada ka ƙara maimaita kuskuran da kayi, bana so, kasan inada kishi, akan ka zan iya komai daga ciki har da kisa"


Zaro idanunsa yayi"in sha Allah hakan bazata faru ba, zanyi kokarin ganin na kiyaye duk wani abu da zai bata maki rai"


Ba zato ba tsammani yaji tayi huggin ɗinsa tare da zagayo da hannayenta kan waist dinsa, tuni yafara jin shi awani yanayi.


Sumbatar wuyansa tayi kafin ta dago da bakinta saitin kunnanshi cikin muryar raɗa mai hade da kwarkwasa tace"fadamin me ka ke so nayi maka wanda zai faranta ranka"


"Nagaza yarda da abinda kike fada min, anya kuwa kece? Ko dai aljanune suka shige ki? Nifa ina kokwanto bana so saina shagala ki canza min ainihin kala dinki"


 dariya tayi cike da nishadi tace"ka daina kokwanto akaina, ni ce dai hajiya saratun daka sani, matarka uwar ya'yanka"


Murmushi pravin yai cike da jin shaukinta


"Ka yi breakfast ko insa a kawo mana mu yi a daki nima banci komai ba"


"In ban da abunki ay kinsan bana iya cin abinci idan ba atare dake ba, don ma ke dince wani lokaci baki jira na"


"I'm sorry Yanzu bari na kira akawo mana a daki, me kake son ci"?


Yana faman washe baki yace "Duk abin da zaki ci, zabinki ay shine nawa"


 Shu'umin murmushin gefen fuska hajiya saratu tasaki tare dakai hannu ta dauki waya ta kira layin kitchen ta isar da sakon akawo masu abinci, bayan abla ta kawo masu atare suka zauna suna ci, kamar sabbin ma'aurata abaki ta fara bashi har sai da suka cinye kafin ta soma jan hankalin shi.


Gaba ɗaya nema take ta zautar dashi da salonta, kasa jurewa yayi da sauri ya ƙara tighting nata a jikinsa.


_________________________________❤✍️Bayan shigar chief bedroom dinsa a zafafe Ya faɗa Bathroom dinsa don ya watsa ruwa ko ya samu zuciyarsa ta lafa daga radadin da ta ke yi masa.

 

ganin ya shiga toilet yasa big guy sauke ajiyar zuciya, yayi tunanin zaiyi yadda ya saba ne idan ransa ya 6aci da wuya in bai yi ma kan shi illa ba, wani lokacin mirror yake kaima naushi ya tarwatsa shi har sai hannun shi ya faffashe saboda tsabar zuciyar dake gare shi.


Kafin fitowarshi da sauri big guy ya fita na tsawon mintuna ya dawo hannun shi ruƙe da wooden tray mai dauke da breakfast din chief.


Yayi mamakin ganin shi kwance kan gado, jikin shi sanye da bathrobe ya ɗaura hannunsa ɗaya kan lallausar sumar kanshi, ya lumshe wadannan kyawawan idanuwan nashi, bakomai yake tunawa ba acikin zuciyarsa face tarihin rayuwar prisoners, labarin yai matuƙar ta6a zuciyar shi.


"Allah Ya huci zuciyarka Yalla6ai, ga breakfast dinka, nasan kana jin yunwa" cikin girmamawa yayi maganar


Tamkar bazai tanka mashi ba, sai da ya dauki lokaci kafin Ya furta"ka koma da abincin bana jin zan iya ci"


Cikin sanyin murya big guy yace"ka yi hakuri Sir, kasan ni mai biyayya ne agare ka, bana yi maka jayayya amma yau bazan iya bin umarnin ka ba, saboda na damu dakai, abun da ke damunka nima shike damuna..." ya fada yana cigaba da kallonsa.


"Sir, ƙin cin abinci bashi bane mafita, kana buƙatar kwanciyar hankali da nutsuwa, wanda hakan bazai samu ba sai ka jajirce wurin ganin ka kauda damuwarka, sannan yanzu ne ya kamata mu dage damtse mu yi aiki tuƙuru don ganin mun gano su wanene azzaluman mutanan da suke aikata 6arna a kasarmu"


Daɗaɗan kalamai Big guy ya cigaba da zayyano masa yana kara karfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, A hankali Ya fara jin saukin radadin da zuciyarsa ke yi mashi.


"Sir, har yanzu kana akan bakanka na bazaka ci abincin ba"? Ya faɗa yana duban cute face din Ogan nasa


Slowly ya ɗan motsa tausasan pink lips dinsa in a low voice ya furta"zan kokarta" gyaɗa kai yai 

"Zan tafi yalla6ai, Ka huta lafiya" ya fada tare da sara mashi kafin Ya juya har ya kusa ficewa daga dakin muryar chief ta ratsa kunnansa"nagoda da kulawarka agare ni"

Murmushi big guy yai"kada ka damu yalla6ai"

Har zai fuce ya kuma dakatar da shi"please ka duba dakin Yaron nan, kaga Awani hali Yake a ciki, Idan ya farka a tabbatar Yayi breakfast dinsa, idan ya gama ka tambaye shi me yake bukata in ya fada maka ay gaggawar yi mashi, zuwa anjima sheikh Imam zai zo duba shi"


"Okey, Sir"


Ya fada tare da bude door room din Ya fito waje, dakatawa yayi da tafiya yana tunanin tawace hanya zai faranta ran chief? Don ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa aranshi, tunawa da Unaisah yasa shi saurin  zaro wayarsa ya danna ma boss kira, tana fara ringing yai picking Call din

Da zolaya yace"masu Ƴa, halan Har yanzu kana nan maƙale da ita"


Sautin muryar boss da alamun dariya yace"To ɗan sa ido, ka fara tsokanar taka ko"?


Dariya Big guy yayi" inatayaka murna abokina"


"Nagode sosai mutumina, Ina chief ne ina fata yana lafiya"


"Ba lafiya, Har yanzu akwai damuwa aranshi, Kuma kasan halinshi mutunne mai zuciya, yanzu haka ina a kofar dakinsa, na kai masa abinci yace min bazai iya ci ba"


Muryar bos da jimami yace"amma banji dadi ba, pls ka yi kokarin kwantar masa da hankali kafin inzo"


da sauri big guy yace"anya zan iya? Ko dai zaka turo unaisah ko da godiyane tayi mashi, watakil hakan Ya kwantar masa da hankalinsa"


"Nima nayi tunanin hakan, yanzu zan turo ta in sha Allah" murmushi big guy yai kafin yai mashi sallama a hanzarce Ya nufi bedroom diny Danish.*❤GARKUWA💪*A kishingiɗe Yake kan gadon shi, Ya hakimce kamar wani basarake, wasu hadaddun sleeping dress ne a jikin sa launin red colour sunyi bala'en yi mashi kyau, hannunsa ɗaya rungume da pillow, lallausar sumar kanshi ta lullu6e gefen fuskarshi, yayin da kyawawan fararen idanunsa ke akan hadadden ceilling din dakin, tun da Ya farka daga bacci bai ta6uka komai ba, gaba ɗaya ya shagala da tunanin Hateem, wani irin kewarsa yake ji, mutumin ya kwanta masa aransa saboda yadda ya tarairayesa ya bashi kulawa kamar wani nashi, bai ta6a tsammanin zaiji tsantsar kaunarsa ba, sai gashi zuciyarsa takasa samun sukuni saboda tunaninsa, da zarar ya lumshe idanunsa fuskar Hateem yake gani dauke da murmushi......" 


Yana son ya sake sanya shi a idanunsa, kwata kwata bai fahimci cewa prime minister kasar ya bari ba.


Har Yanzu kamshin turaren daddy hateem bai bar jikin shi ba, saboda rungumarsa da yadinga yi jiya kamar zai maida shi jikin shi, fragrance din Yana da karfi sosai shiyasa ya kama jikin sa.


Kalaman hateem ne suka fara dawo mashi 


 _zan tafi da kewarka, dan Allah kada ka manta dani, inaso ka ɗauke ni tamkar mahaifinka, aduk lokacin da wani abu ke damunka ka sanar da chief zai fada min, zamu dinga yin waya akai akai, daga yanzu inaso ka dinga kirana da  sunan daddynka_


A hankali ya dago da yatsan hannunsa yana kallon zoben da ya sanya mashi ayatsa mai kyan gaske, wannan ne karo na farko daya fara sanya zobe,

Daura yatsan yai kan kananun la66ansa Ya sumbace shi a hankali yanayin fuskarshi kamar zaiyi murmushi.


Knocking din kofar dakin da akaine Ya sa shi daura idonsa kan kofar, bakomai Ya fado masa arani ba face Angel dinsa, yasan ita kaɗaice zata Iya zuwa duba shi awanan lokacin, Idan ba ita ba sai kuma yan uwansa, saukowa yai daga kan gadon bayan ya jefar da pillow hannunsa, da sauri Ya nufi kofar don Ya tarbe ta, saboda yayi kewarta jiya, idanunsa sunyi maraicin ganin ta,, shi kanshi baiyi tsammanin zai Iya mintuna batare da ita a gafen sa ba, sai gashi jiya daddy hateem Ya sace zuciyarsa.


Ko da ƙofar ta bude yai arba da big guy tuni yanayin fuskarshi Ya canza, shi da ya taso da zumudinsa don Ya nuna ma Angel dinsa kyautar zoben da mutumin nan ya bashi, sannan Ya bata labarin abunda Ya faru atsakanin su ashe ba ita bace.


"Barka da safiya danish" big guy ya fada da fara'a akan fuskarsa, ko kallo danish bai mashi ba, Hankalin shi na akan bayan shi, burin shi Yaga Angel don har yanzu bai fidda rai da ganin ta ba


Da mamaki big guy ya waiga baya don yaga me yake kallo sai dai baiga komai ba.


"Ina fata ka tashi lafiya" ya fada aranshi yana mai mamakin Girman Jikin Yaron ga tsawo tubarkalla uwa uba ga kyau kamar shi ya zana kan shi.


"Magana na ke yi maka ka yi shiru ba ka ce komai ba, ko har yanzu ba ka jin daɗin jikin naka ne"?


cikin sanyin murya ya furta"My Angel? Tana Ina"? 


Dafa kafadarsa big guy yai"kwantar da hankalinka tana nan  cikin koshin lafiya, nasan zata zo dubaka..." kafin Ya kare maganar danish Yace"Ina son ganinta, " ya fada yana kokarin bi ta gefen shi Ya wuce, A hanzarce big guy yai saurin Shan gabanshi, gudun Kada Ya ruguza masa plan dinsa na zuwan angel part din chief.


Wani kallo da danish Ya watsa mashi sai da yaɗan ji fargabansa, Karfin Hali Yai wurin furta"Ka yi hakuri bawai ina son dakatar dakai bane, daga gani yanzu ka farka daga bacci ko wanka ba ka yi ba, a haka zakaje wurinta? Itama bazata ji dadin ganin  ba, kaje kayi wanka, kafin ka fito zan sa unaisah ta kawo maka breakfast dinka har daki"


cikin sigar lallashi yakeyi mashi magana, badan Ya yarda da kalaman sa ba, ya amince mashi, juyawa yayi tamkar wanda ya rasa kuzarinsa, harta bugun zuciyarshi ya canza ji yake kamar wani abu na faruwa ko yana shirin faruwa

Bayan ya shiga toilet Ya maida kofa ya rufa, ajiyar zuciya big guy ya sauke aranshi ya ayyana wai Allah daga ganin yaron nan zaiyi kafiya, dole saina mike tsaye idan ba haka ba zai iya zame min matsala.


Ya fada tare da juyawa ya fuce daga dakin, Ya nufi sashen kitchen din su don Ya hada masa breakfast dinsa.


*❤UNAISAH ANGEL💋*


Bata jima da fitowa daga bathroom ba, sai rawar kai takeyi saboda daddynta Ya fada mata zancen zuwa dakin chief don tayi mashi godiya bisa ga irin kyautatawar da yayi mashi, ruwan ido Ya hana ta canki kayan da za ta sanya, tayi tsaye gaban faskeken closet dinsu, sai faman bin jerin kayan take yi da kallo, fuskarta dauke da murmushi tarasa gane meyasa take jin wani irin nishadi da annushuwa kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna.A ƙalla ta shafe mintuna kafin ta fito sanye cikin wasu riga da wando launin pearl pink masu kyan gaske, tsayawa zayyana kyawunta acikin kayan 6ata baki ne, abun sai wanda ya gani.


Takalma ta ɗauko masu tsini launin kayan, ta zura su a kafarta, bayan ta dauko mayafi ta tsaya gaban mirror ta  ta soma laga shi akanta.


 Ita kanta data kalli madubi sai da ta firgita da ganin wani sihirtaccen kyau daya bayyana akan fuskarta, murmushi tadan saki har dimples dinta suka lotsa.


"Daughter I'm waiting For You, Kin bar daddy awaje Yana ta jiranki"


Muryar taj tajiyo daga waje yana magana, da sauri ta nufi kofar ta fito, waro idanu waje taj yai arude Ya furta"Tabarakallahu ahsanun khalikin! My Angel? Kinga kuwa kyan da kikayi kamar hurul aini" sunnar da kanta kasa tay, fuskarta sauke da murmushi

Ruko hannunta yai a cikin nashi suka nufi dakin chief.

Abakin kofar dakin suka dakata suna kallon juna

Lokaci daya suka sakar ma juna murmushi

Raɗa yai mata a kunnanta"ba'ay mashi rashin jin magana ba kamar daddy bane da aka raina" dariya tayi jin abun da yace.


Sakin hannunta yai"ki kula min da kanki," amsa mashi tayi da toh, kamar karsu rabu yana tafiya yana waiwayonta itama sai kallon shi take yi

Ɗaga murya tayi tare da cewa"daddy kada ka tafi ka jirani in fito"


"Ba nesa zanyi ba, Zanje gidane bazan jima ba zan dawo" ta6e mashi baki tayi kamar zatayi kuka, hakan ba karamin nishadi ya sanya shi ba.


Zuciyarta Cike fal da fargaban haɗuwa dashi tay knocking kofar, Almost 3 times ba'a bude ba, harta fara tunanin ko dai bacci yakeyi ne ko baya a dakin har zata juya kofar ta soma zugewa a hankali ta buɗe, kamshin turarensa ne Ya fara dakar mata hanci har saida ta dan lumashe idanunta.


Kasa shiga tay saboda zullumin hada ido da shi, da kuma jin nauyn magana da shi.


Sai da ta shafe kusan mintuna biyar, tana saƙe saƙe a zuciyarta ba tare da ta motsa ba, kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta kwatsam kofar ta soma kokarin rufe kanta, da sauri ta ratsa ta tsakankanin door din da karfi ta faɗa dakin kamar wadda aka jeho, ƙiris Ya rage ƙofar ta datse da jikinta, wannan gangancin nata ba karamin mamaki ya bashi ba, sai faman nishi take yi hadi da sauke ajiyar zuciya, sai da tagama yan kame kamen ta, kafin a hankali kamar maijin tsoronsa ta soma bin dakin da kallon, Lokacin da ta daura idanunta akan shi har saida gabanta Ya fadi ganin surar jikin shi, Har yanzu bai motsa daga kan gadon shi ba, kamar yadda Big guy ya barshi haka ta taras da shi sanye da rigar wanka, ya daura Apple laptop dinsa kan waist insa, Yayin da kanshi ke akan pillow ya dan lumshe idanunsa, tuni kamshin turarenta yakai mashi karo


Yawu ta haɗiya, a tunaninta baya ganin ta cikin sanda ta matsa daga gaban gadon tana faman zare gray eye dinta ta furta"ina kwana, ka tashi lafiya" magana takeyi hankalinta na akan kwantaccen sajen fuskarshi.


"Lafiya" taji ya amsa mata da sanyin murya, tayi mamakin jin voice dinsa irin na danish.

 Shiru tayi tana faman wurwurga eye balls dinta, bata ta6a jin nauyin wani dan adam ba sai akan shi, kamar ma kunyar shi take ji

Wasa takama yi da yatsun hannunta, batasan cewa yana kallonta ta cikin laptop dinsa ba.


"Idan kingama tsayuwar zaki iya tafiya" sexy voice dinsa ce ta kuma ratsa kunnanta, muryarta da en ena tace"am.. um. wai Dama daddy ne yace inzo in yi maka godiya"


Shiru yayi yana maimaita maganarta a zuciyarsa kafin ya furta"bake ki kayi niyar zuwa ba? Shiya tursasa maki kizo"?


Dafe kai tay da hannu daya alamar ta kwafsa.


"Mantawa nayi, ni nayi niyar zuwa inyi maka godiya".


Ta6e pink lips dinsa yai na ɗan wani lokaci kafin yace"ba'ay min godiya, duk wani abu da nayi nayine don Allah, ina fata kin fahimce ni" amsa mashi tayi da toh,

shiru suka kuma yi, Ganin yaki sake tanka matane yasa tai kafin halin cewa"tun da bakason ay maka godiya, to ka fadamin wani abu da zan dinga yi maka tunda kaima ka kyautata mana duk da nasan bazan iya biyan ka ba" ta faɗa tana cuke la66anta.


A hankali ya dan ware reddish eyes dinsa, duk wani motsinta akan idonsa sai dai ita batasan Yana kallonta.


 "Will you do whatever I tell you?"da kwarin gwiwa ta amsa mashi Eh

"Okey," ya furta tare da sauke Laptop dinsa gefe ɗaya, a hanzarce ta juya mashi ƙeya, Ganin zai mike kuma taga bathrobe ce a jikin shi, murmushin gefen fuska ya dan saki.


Saukowa yai daga kan gadon Ya nufi walk-in closet dinsa, Jim kaɗan Ya fito sanye da thobe launin ruwan toka, tamkar a jikinsa aka dinka ta tsabar yadda ta bayyana surarsa.


Kamar yadda yabarta haka ya same ta atsaye ta juya baya.


Zama yai gefen gadon da alama bata san ya dawo ba.


"Zaki Iya zuba min abinci"? ɗan zaro idanunta tayi kafin ta amsa mashi da toh, juyawa tayi a hankali ta saci kallonsa Idanunsa na akan wayar hannunsa, taji dadin ganin hankalinsa baya akanta


Cikin takun sanda ta karasa daga gaban table din.


"Me kakeso nafara zuba maka"


"Duk abun da yai maki" farfari tayi da idonta hada ɗan gumtse baki alamar mamaki, sam batayi zaton zai kulata har haka ba, kallo ɗaya da tai masa ta fahimci mutunne mai ji da kansa 


Coffee ta mika masa yasa hannu ya kar6a A hankali Yake kurbarsa, Angel sai faman satar kallon la66ansa take Yi, ba karamin rudarta yakeyi ba, ga kamshin turarensa dake ta kai mata hari.


Komai ta zuba masa cinye shi yake yi, mutumin da bai cika cin abinci ba, amma yau har saida yaso ya ƙwari cikin sa, ba tare daya ankare ba..


Bayan ta kammala serving nasa tace"ko akwai wani abun da zanyi maka? Ko in gyara maka bedroom din ka"

"Idan kin ji zaki iya" ta6e baki tadanyi kafin tafara tunanin shiga toilet dinsa ta gyara masa shi, watakil kafin ta fito shi kuma Ya fita sai ta gyara dakin


Juyawa tayi da sauri ta nufi toilet din, sai lokacin Ya dago Yana bin bayanta da kallo har sai da ta 6ace ma ganinsa tukunna ya kau da idonsa.*🤍ZAHRA🤍*A ƙudundune take kan darduma ta lullu6e jikinta da hijabi, tun bayan sallar asubahi bata farka daga bacci ba.


Shigowa Dakin Aneelerh tayi, hannunta ruƙe dana baby junaid, sakin hannunta yai da gudu ya tunkari zahra Ya faɗa jikinta yana fadin"aunty zahra Ina tsarabar da kika ce zakiyi min jiya! Shine ma baki tada ni daga bacci ba" 


Janyo shi Aneelerh tayi tana fadin"meye haka? Ba ka ga bacci take yi ba"? Zahra dake sauraronsu tayi shiru batare da ta motsa ba ashe idonta biyu.


Da shagwa6a baby junaid yace"mommy ay itane tace zata min tsaraba, Ni ta tashi ta bani abuna kamin taci gaba da baccin..." bai kare maganar ba, ta rufe bakinsa da tafin hannunta.


"Yi shiru kada ta farka, mu tafi zuwa anjima sai mu dawo" maƙe mata kafaɗa yayi"nidai ba inda zani Allah, sai ta bani abuna" kwace hannunsa yai daga na Aneelerh Ya fada kan zahra yana kiciniyar tada ta daga bacci, duk yadda taso tayi pretending sai da takasa tana faman fitar da numfashi mai ɗan huci ta sanya hannu ta janye junaid kafin ta mike zaune ta tu6e hijab din jikinta ta jefar da shi gefe ɗaya


Har saida gaban aneerlah Ya fadi ganin jirwayen hawaye akan fuskar zahra, idanunta sun kumbura suntum da su, da alama tasha kuka har ta gaji.


Waro idanu waje baby junaid Yayi "mommy mun shiga uku, aunty zahra kuka tayi wani ya buge ta . " bai kare maganar ba, zahra tai saurin sanya hannu ta dan buge bakinsa"kada na kuskura nasake ji kayi magana," ta6e mata baki yai alamar zai yi kuka da sauri ta janyoshi tare da manna shi kan kirjinta, wani sabon kukan ne ta kuma fashewa da shi.


Hankalin Aneelerh ba karamin tashi yayi ba, tuni yanayin fuskarta Ya canza, matsawo tayi kusa da zahra ta zauna, cikin sanyin murya tace"ni dama tun jiya da kika dawo gida hankalina bai kwanta da yanayin ki ba, saboda na lura da yadda kike kokarin danne damuwarki saboda kada mu gane! Meyasa zahra eyeh? Adan tsawace ta fada tana dubanta

"Ki fadamin me ya faru dake ne? Waye ya ta6a min ke yanzun nan in ɗaura ɗamarar yin yaƙi da shi"! ta faɗa babu wasa akan fuskarta, Cikin shesshekar kuka zahra tace"a.. Aunty Aneeleerh zayn! Na shiga uku! Hajiya saratu ta haɗa ni da masifa, ashe lokacin da ta turamin sakon nan tace min in zabi daya daga cikinsu nayi kuskuran rubuta sunan zayn a maimakon zaid shine fa ta haɗa ni dashi, aunty aneelerh baki ji kalaman daya furta min ba.........' a tsanake tafara bata labarin abun da ya faru jiya bayan da hajiya saratu ta kira ta.


Fitowa tai daga hall din tana ta faman yan kalle kalle can ta hango hajiya saratu tsaye abakin motarta, Cikin girmamawa ta ƙarasa daga gefen ta, bayan sun ƙara gaisawa zahra tace "mommy gani" murmushi hajiya saratu tasakar mata tare da ruko hannunta acikin nata"mu shiga ciki, inaga zaifi muyi magana a tsanake" ta fada tare da buɗe murfin backseat, bayan sun shiga taja kofa ta rufe, Zahra sai faman bin cikin motar take da kallo, saboda haduwarta ga sanyi a.c dake ratsa fatar mutun


Shiru sukayi babu mai magana, Hankalin hajiya saratu na akan wayar hannunta da take ɗan daddanawa, 


"Zahra," ta ambaci sunanta, da sauri ta amsa da na'am

"Ina fata kin nishadantu da dinner din nan," tana dan murmushi ta jinjina kanta tare da cewa"Eh mommy, Alhamdulillah, naji dadin gayyatana da kikayi, I can't thank you enough"


Murmushin dattako hajiya saratu tayi"kada ki damu, kin cancanta ne, ni kaina najima ina mamakin yadda kika kwanta min araina, saboda ba kowa nake mu'amala da shi ba, ina da wuyar sha'ani zahra " ta faɗa ba tare da ta ɗago da idonta dake akan screen in wayarta ba.


Zahra sai faman sakin murmushi takeyi taji dadin maganar da hajiya saratu ta furta mata.


"Kinsan meyasa na kira ki"!


"A'a"


"Idan ba zaki manta ba, Kwanakin baya na tura maki hoton twins dina, har nace idan na baki za6i wanne kike so acikin su, ashe kin bani amsa ban samu damar duba sakon ba sai daga baya na gani"


 Dakatawa tayi da yin maganar, zahra nata kallon gefen fuskarta burinta ta karasa maganar nata, sai dai ta fahinci bata cika son magana ba.

ba ta zaci zata dago ba, aikuwa karaf suka hada ido cikin na juna, wani irin kwar jini tayi ma zahra da sauri ta dukar dakanta kasa tana wasa da yatsun hannunta


Daura wayar tayi akan laps dinta, ta ruko hannun zahra acikin nata, kafin ta soma magana

"Zahra na yarda dake, Kamar yadda na fada maki kin kwanta min araina, kuma na yaba da hankalin ki, kyawawan ɗabi'unki da halayen ki sune suka sa har nafara kwadayin ki zama wani bangare na rayuwana, Ina nufin ina so ki zama surukata zahra" cikin kwantar da murya hajiya saratu take yi mata magana tamkar ba aunty masifatu ba

Zahra jikinta yayi wani irin sanyi, ga wani annurin farin ciki daya lullu6eta duk da tana jin fargaban wanda za'a haɗa ta da shi Yaki amincewa...


"Naji kinyi shiru bakice komai ba, Ni bazan maki dole ba, kada kiji nauyn fada min abunda ke aranki, saboda nima bazan bari ki auri wanda zuciyarki bata so ba"


Numfasawa zahra tayi fuskarta da ɗan murmushi tace"mommy wa zai ki jinin ki? Ni ay abun farin cikine agare ni, saboda nima kin kwanta min araina, bazan 6oye maki ba, nayi mamakin tayin da kikayi min, saboda ni aganina ban kaiba mommy, ya'yanki sunfi karfi na, sannan inajin fargaban wanda zaki haɗani dashi yakini, tun da bamusan juna ba....." ta ƙarasa maganar idanunta cike tab da kwallar murna.


Jinjina kai hajiya saratu tayi kafin ta furta"kada wannan ya dameki zahra, bana so na sake jin kin furta matsayin ki bai kai ba, ni na za6e ki don haka kada kiji komai, ƴa'ƴana kuma ni nake  iko da su, abunda nakeso shi zasuyi don haka ki kwantar da hankalin ki, wadannan hawayen da nake gani ki share su" ta fada tare da zaro mata hanky ta mika mata, yatsun hannun zahra na kerma ta kar6a tafara shaye hawayen ta.

Wayarta ta dauka tare da dannama zayn kira, bayan yai picking cike da bada umarni tace"ka sameni abakin hall yanzun nan Ina jiranka"! Bata jira amsar shi ba tai rejecting call din, tare da mayar da dubanta ga zahra

"Nayi mashi magana yanzu zaizo sai ku fahimci juna" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, sam bata kawo ma ranta zata ga akasin zaben da tayi ba.


Kusan mintuna Kafin akayi knocking, murmushi hajiya saratu ta saki, tare da kallon zahra"ki gyara nutsuwarki, Yanzu zai shigo ku gana da juna" amsa mata tayi da toh, bayan fitar hajiya saratu, da sauri zahra ta bude purse dinta ta curo hanky ta goge fuskarta, ta zaro yar hodarta ta barbaɗa, hada jan baki ta murza ma la66anta, Jin motsin buɗe motar yasa tayi saurin maida kayan kwalliyar cikin purse din. tun daga kan kamshin turarensa daya daki hancinta tafara jin wani irin fargaba, a wani slow ya zauna kyakkyawar fuskar nan tashi a haɗe Yaci mur, ko kallon inda take baiyi ba balle ma ya nuna alamar yaga mutun a motar, da farko bata gane wanene ba acikin su, 


Dakyar ta furta"ina wuni"


Banza yayi da ita, saima ya zaro wayarsa yaci gaba da dannata, nan take ranta ya bata cewar ZAYN ne, Hankalinta a matukar tashe take duban gefen fuskarshi, mutun har mutun ga kyau sai dai babu mutunci ko miskala zarratin, gaba ɗaya tarasa sukuninta tun kan aje ko'ina harta fara danasani, mamakinta tayaya akai zayn ya kasance wanda za'a hada ta dashi bayan zaid ne ta canka ba shi ba? Ko dai hajiya saratu tayi kuskure ne..."


Tayi zurfi a tunaninta muryarshi ta ratsa kunnanta"wani tsautsayine yakai ki amincewa da zancen haɗani dake? Kinsan wanene ni"? Adabarbace tace a'a amma in ranka ya 6aci kayi hakuri ni ma bada son raina ba.."

"Meyasa tun farko bakice mata baki sona ba"! A kausashe ya furta maganar, 


Muryarta na rawa tace"saboda bazan iyaba" 


"Wallahi idan kina son zaman lafiya ki janye zancen hadani dake da gaggawa idan ba haka ba ciwon zuciyane zaiyi silar mutuwarki, saboda ni nan da kike gani na ba mutumin kirki bane ɗan iska ne ni, sannan bani da mutunci .."  Ras taji gabanta ya fadi, tunda yafara magana bai kalle ba, baima san wacece 


wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, amatukar rude take kallon shi jikinta na kerma


"Nasan bazaki so ya'yanki su yi rashin dacen uba ba, shiyasa nake gargadinki, tun kafin kiyi danasani mara amfani, ke in banda ma haɗama da rashin sanin ciwon kai ina ke ina Zayn pravin obinna? Nayi maki kama da sa'ar auranki? Wai ke yar wacece ma"? 


Hawayen dake taruwa a cikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta

Hankalin shi kwance yaci gaba da cewa"Ni nasan ba hakanan kika kyale mommy ba, Allah kadai Yasan me kika kulla da har ta amince zata hada ni da ke, idan ma kwaɗayin abun duniyane ya rufe maki ido to ki fadamin nawa kikeso tun daga miliyan biyar har abun da yai sama zan baki kije kija jari ki rufawa kanki asiri...." sautin shesshekar kukanta ne ya cika masa kunnansa, a zafafe ya juya da niyar ya dauke ta da mari kamar an ruke hannunsa ya dakata cak Yana huci idanunsa akan fuskar zahra da hawaye ya gama wanke ta, bakomai ne yaja hankalin shi ba face kyawun fuskarta ba laifi tana da sura dai dai wadaidai saidai baya jin zai iya kula macen da bata kai matsayinsa ba

Sassauta muryarshi yayi"ke, yi min shiru in ba haka ba zan 6ata maki rai"


yatsun hannunta na kerma ta toshe bakinta, sam takasa kallon cikin idanunshi gashi ya matso kusa da ita kamshin turarensa duk Ya gama kashe mata jikinta

"Idan kinason zaman lafiyar, Kije ki fada mata, baki sona banyi maki ba"muryarya da shesshekar kuka tace"kayi hakuri amma ni bazan iyaba, saboda ina ganin girmanta, sai dai kai ka je ka faɗa mata" dakyar ta kare maganar tana faman jan numfashi


"Tausayinki nake ji bana so kiyi danasani, wallahi bani da mutunci, ni banma shirya yin aure ba, saboda baya agabana, Ni nafi sha'awar inyi sharholiya ta son raina" ya fada yana shafa sajen fuskarsa" yanzu ke kin yarda ki auri dan iska mai mu'amala da matan banza"? Ya fada yana cizon lips dinsa da masifa

Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ita kanta batasan tayi hakan ba, batasan ya akai zuciyarta take jin kaunarsa ba, a maimakon taji haushin kalamansa.


Dafe kanshi yai da hannu ɗaya kafin ya furta"look, Idan burgeki nakeyi naji zan baki kaina, amma ki janye batun nan, saboda ni ban shirya ma aure ba, ko auran zanyi bazan auri wadda batakai aji na ba, bana so ki jefa rayuwarki cikin hatsari, kada kiga kamar ina lallashinki mommyn mu kaifi ɗayace idan ta furta magana babu wanda ya isa ya dakatar da ita, shiyasa nake lalla6aki saboda ke kadaice zaki canza ra'ayinta" zahra dake ta faman yin shesshekar kuka muryarta na rawa tace"har abada bazan iya tunkararta da maganar nan ba sai dai kai kaje ka fada mata..." bata ƙare maganar ba ya daka mata tsawar data firgitar da ita

Nuna ta yayi da yatsan hannun shi"Share hawayen kan fuskarki, ki tashi muje ki fada mata baki sona banyi maki ba" muryarta kasa kasa tace"ay na fada maka bazan iyaba..." bata kare maganar ba, taji ya haɗe bakinsa acikin nata, wani irin bugu zuciyarta tayi mata, gaba ɗaya takasa tabuka komai, har sai da Ya gama abunda zaiyi kafin ya zame harshensa, Yai saurin zuge glass din motar Ya tofar da yawun bakinsa.


tsabar wulakanci Ya zari hanky yana kara goge bakinsa kamar wanda ya ta6a najasa, rushewa tayi da matsanancin kuka ganin irin wulakancin da yai mata, abunda yafi ƙona mata rai sanya mata harshe da yai abakinta, arayuwarta ta tsani namijin da ba muharraminta ba ya ta6a ta, 

Tsawa yakuma daka mata tuni ta shiga taitayinta.


"Kaɗan kika gani, wannan so mun ta6ine idan har baki janye kudirinki akaina ba, zan cigaba da amfani dake ne" ya faɗa yana mai kara jaddada mata

"Ki share hawayen nan, Ki tashi muje ki faɗa mata kinjanye" muryarta na kerma ta amsa mashi da toh, shu'umin murmushin gefen fuska yasaki, dama yasan zata amince ko dan saboda abinda yai mata don ya fahinci ba yar hannu bace tana da kamun kai shiyasa ya tsorata ta.


Hanky ta zaro ta share hawayen fuskarta, sannan ta daidaita nutsuwarta, kafin ta buɗe motar, ta fito shima ya fito ta ɗayan bangaren suka nufi hajiya saratu dake atsaye can nesa da su.


Tunkafin su karaso ta nufosu, fuskarta da fara'a tace"Son, Ina fata kun sasanta kanku"!

Nunata zayn yai"ki fada mata abun da kika gaya min acikin mota" amsa mashi tayi da toh kafin ta kalli hajiya saratu zuciyarta cike fal da tsoronsa ta ce"Mun gama magana dashi, Kuma mun fahimci juna" a gigice zayn yake kallon zahra jin abunda tace, zuciyarsa ba karamar hasala tayi ba, bai ta6a tsammanin yarinyar zatay taurin kai ba.


"Zahra kin tabbata yayi maki? Amma meyasa naga idanunki sunyi ja"? Da sauri zahra tace"kaina ne keyi min ciwo, har fada masa nayi, shine yace yakamata na tafi gida na huta, zamuyi magana awaya..." da tsantsar mamaki zayn yake kallonta, gashi ba halin Ya karyatata, don ya fahimci ta kama zuciyar mommynsu.


"Naji dadi my son, dama nasan bazaka ƙi tayin da nayi maka ba, da ace zaid ne ba lallai ya amince ba saboda shi na daddynsa ne kai kuma nawa ne, hakika yau ka faranta raina my son, Allah yayi maka albarka, zahra kema nagode maki sosai da kika aminta da tayina in sha Allah ba zakuyi danasani ba, Ina da tabbacin hakan, Ta fada tare da janyo zayn da zahra tayi huggin dinsu tana ɗan bubbuga bayansu, sai faman farin ciki takeyi yayin da su kuma zuciyoyin su suke a kuntacce da bakin ciki.


"Zayn ko zaka kaita, Gida"? Ta fada bayan ta raba su daga jikinta, da sauri zahra tace"mommy kin manta nazo da mota dina"

"Oh eh hakane, na shafa'a, Muje son mu rakata ta tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba"


"Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan"


"In sha Allah ngde ssae"


Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani,"


 Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba.


Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu ɗaya, tana kallon zahara data kammala bata labari


"Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki ɗauki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi.Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne"

Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan"


kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki ɗaukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba"


Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta.


"Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu.


Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah


Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie

Barka da safiya abie ina kwana"?

"Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina


"Okey ki fada mata, ƙawarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh  bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya faɗa mata."Abie ne ya kira, yace in faɗa maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki"


Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta"ƙawata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata ƙawace gare ni da zan bata layin abie"


"Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin.


Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner,"

Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta buɗe gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data buɗe hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba.*SALSABEEL💫*


Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, ɗagowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun ɗaya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa ɗaya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa.


"Dan Allah ku yi sauri ku ƙarasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh 

"Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar."Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da miƙewa Ya nufi upstairs.


"Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba.


 rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su.


"Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zuƙunnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, damƙo hannunta Hawwa tayi nan fa faɗa ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi 


Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma taƙi ko tanka mashi.


Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe gasar" muryarta da shagwa6a tace"ni dai Allah ba wani nan wayo kakeso kai min don kada inci"

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya"ke zaki fito ko ba zaki fito ba" shiru tayi bata tanka masa ba,

Buga kofar yai da karfi"Khadeeja ranki zai 6ace in baki fito ba" still bata tanka mashi ba 

Banko kofar dakin akay, Mubeen ne ya fado ciki kamar an wurgo shi, Rigar shi duk ta 6ace da jan bakin su rubina

A ruɗe salsabeel ke kallon shi Yama rasa ta ina zai fara 


"Yaya salsabeel, Kaga su rubina sun 6ata min kayana da jan bakinsu, kawai saboda nayi masu dariya suna fada" bai karasa sauraren shi ba yai saurin fucewa da sauri mubeen Yabi bayan shi tunkafin Ya sauko down Ya hango su manne da juna, sun kacame kamar irin kifin gwangwanin nan sai ihu suke Yi,


Wata irin tsawa mai sauti Ya daka masu a firgice suka saki junansu, suna ganin shi suka fara kokarin bare baki zasuyi kuka 

Nuna su yai da yatsan hannun shi"kar wadda ta kuskura tayi min kuka" ya fada yana zare masu idanun shi da alama ranshi ya 6aci, Yaji haushin yadda suka 6ata kayan su, abu tun karfe kusan tara na safe ake ta fama yaki ci yaki cinyewa

Sam yakasa yi masu fada, baisan meyasa yake jin nauyin ya furta masu kalma mara dadi ba.

"Yanzu abun da ku kayi kun kyauta"?  Sunnar dakai kasa sukai har  suna hada baki wurin fadin"dan Allah ka yi hakuri ba zamu kara ba" ta6e baki yai" a haka zamu tafi,tun da kunfi son aganku a haukacen ku" 

"Ya salsabeel dan Allah kabari mu canza wasu kayan," harara ya watsa masu, rai a6ace  Ya kama hanyar fuce wa daga falon Yana Fadin"ni na tafi sai kun taho"

Watsawa su ka yi aguje suka nufi bedrooms dinsu,  Jim kadan suka fito har sun canza kayan jikin su..


Salsabeel Yana atsaye gaban motocin da za su shiga,, Jami'in da zaiyi driving din su Har Ya hallara a mazaunin driver, da gudun gaske khadeeja ta fito hannun ta ruke da takalmanta,  har tana bangaje Su Yasmin, kamar a filin Yaki, gaba daya hankalin Jami'an dake tsaron gidan sai da ya dawo kanta, wani burgujejen wando tasanya yadda kasan kafafuwan agwagwa, ga wata yar yaloluwar riga mai hannu daya, Ta dambara jan baki akan la66anta har saman kumatuntu, mascara din data sanyawa eye lashes dinta ya zazzago har kasan idanunta, babu wanda bai firgita da ganin ta ba, Jami'an sai faman kunshe dariya suke yi a bakunansu, ko mayafi babu akanta sai wannan guntun gashin kan nata mai ɗan yawa data fake shi da ribbom Ya karkarce gefe ɗaya.


Ko ta kansu bata bi, Tana isa bakin motar, ta jefa takalmanta cikin car window, kafin ta daddage ta kama glass din Ta zura kanta aciki ta soma kiciniyar kutsawa ta karfi,  dafe kai salsabeel yay da hannu ɗaya tamkar zai fashe da kuka, ya ma rasa me zaiyi, su rubina duk sun bude bakunansu asake suna kallon ta.


A hanzarce Ya cafko kafafuwanta, Ya zarota daga tagar, tana ta faman haki ta dube shi idanuwan nan nata kamar na babie sai kyaf kyafta su takeyi


_"Ya salsabeel baka ce nayi kyau ba" Cikin sanyi murya yace"kyawun ne ya ruɗe ni shiyasa nakasa magana" ya fada tare da bude mata murfin motar, ta shiga ciki ta zauna, Bayan kowan nan su Ya shiga, A jere suka fuce daga gidan kai tsaye suka haura kan titi_*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*


Mu Haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya


 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,


 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Aslm ina nima kurkuku kaddara takun karshe 14

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post