Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 24 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 24 Complete

Novels Elite English

 _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

                     سجن القد💋🔥💞    

                  ~Takun Ƙarshe🔥~

            Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع   تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

 Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba


Gaba ɗaya ya fasa laptop din, ya raba ta gida huɗu, hakan bai masa ba sai da Ya zuƙunna a gaban pieces ɗin Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa


Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya ɗaure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara.


"Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun 


Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" ɗagowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba ɗaya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya buɗe ma prime minister hanyar da zai iso gare sa.


"It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo


Ƙarasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing


Da sauri Ya ɗaura laptop pieces din kan couch kafin Ya ɗauki wayar yai picking


"Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji ɗuff ya katse kiran"


"Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"?


"Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse"


"Uncle Ya 6alla laptop ɗin, gaba ɗaya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara"


Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"?


"Saboda ka ƙi fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne"


Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi......


Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na ɗan wani lokaci, kwatsam sautin shessheƙar kukan prime minister hateem Ya karaɗe kunnansa lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aruɗe ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"? 


Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba, da ace ya taso cikin kulawar iyayensa koda  ba dan masu hali bane zai samu ilmin addini dana zamani dai dai gwargwado....." yana magana sautin na fita da alamun kuka maitsuma zuciya.


Lumshe ido chief yai kafin Ya furta"pls ka kwantar da hankalin ka uncle, zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ya samu ilmi akansa, kamar yadda nayi maka alƙawarin bashi kyakkyawar kulawa..."


"Owais idan zai yiwu ku sanya shi makaranta, Ni zan ɗauki nauyin karatunsa because I want him to be like everyone else. ni wallahi da zaka bani dama zansa akawo min shi nan canada"


Cikin kwantar da murya owais yace"Uncle zuwansa canada bazai yiwu ba, akwai abun da ban fada maka dangane da rayuwar su ba, amma dan Allah kayi min Uziri uncle nan badajimawa ba zan sanar da kai komai....."


Yana jiyo sautin ajiyar zuciyarsa"Toh zan jira har zuwa lokacin, Allah yasa inji alkhairi, yanzu sai yaushe zan sake yin magana da shi saboda bangaji da ganin sa ba"


"Ka bani lokaci uncle, zanyi kokarin fahimtar da shi yadda zaiyi amfani da laptop din"


"Okey, nagode my son, sannan ina mai baka hakuri amadadinsa"


"Kada ka damu uncle, ay ba yin kansa bane rashin sani ne"


 kwantar masa da hankali Yaci gaba da yi har ya samu ya shawo kanshi kafin daga bisani su ka yi sallama zama yai gefen gadonsa zuciyarsa cike fal da tunanin abun da ya faru.



_________________________✍️



"Deeja! Deeja" kamar daga sama taji ana ƙwala mata kira, firgigit  ta ware idanunta masu ɗauke da bacci ta sauke su kan ceilling da alama batasan daga ina ake kiran ta ba sai faman ƙyafta ƙyafta idanu ta ke Yi, fuskarta ta ca6e da jan bakin ta


"gani anan tsaye ina kallon ki" wurga ido tai kan Unaisah da ke yi mata magana, tana a tsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, wata hadaddiyar riga doguwa ta sanya a jikin ta black colour tabi shape dinta ba karamin kyau tayi mata ba, hada light make up akan face dinta, tayi rolling veil ga wani daddaɗan fragrance dake tashi


Zumbur khadeeja ta miƙe zaune fuskar a jagule take kallon ta


"Sorry na katse maki baccin ki, safiya tayi tun ɗazu, ga shi ko sallar asuba bakiyi ba, yakamata kije kiyi sannan ki yi wanka ko kin ji dadin jikin ki"


Yamutsa fuska Khadeeja tay"to ke din wacece ne? Kin cika ni da surutu Ina yaya salsabeel da su rubina"? 


Murmushi unaisah tayi"Yar uwarki ce unaisah baki gane ni ba"?  Harara ta jefa mata"ni bansan ki ba Allah, ki fadamin ina yan uwana suke"?


Zuba mata ido unaisah tayi da alama zatai kafiya, don ma tasan halin kayan ta.


"Yan uwanki suna nan a cikin gidan nan, amma waye ya kawoki ɗakin mu jiya"? 


Sosa ƙeya tayi kafin tace"harisuna, shine Ya rakoni in kwanta" 


"Okey yanzu ki tashi ki shiga ga toilet can" ta fada tare da ɗan juyawa ta nuna mata kofar da hannu, saukowa tayi daga kan gadon tana miƙa tare da hamma ta nufi toilet ta shige, unaisah nata bin ta da kallo har ta shige.


"kin canzamin kamar ba deejana ba, naso ace kina acikin hayyacinki komai Ya faru nasan zakiyi farin cikin saurayin rayuwar da muka samu, Allah Ya baki lafiya my sister"


Bakomai take tunawa ba, face ranar da giant ya tafi da khadeeja da kuma lokacin da aka dawo masu da ita taje gaban gadon ta tana shessheƙar kuka ta tada ta daga bacci taja ta suka shiga toilet har take fada mata abun da akayi mata bayan an ɗauke ta


Tuni taji jikinta yayi sanyi lakwas rayuwa kenan, babu wanda yayi tsammanin zasu kai wannan lokacin araye sai gashi Allah ya raya abun shi, dama ance wuya bata kisa sai in kwana sun kare.


Faɗowa Dakin Haris Yayi, fuskarsa dauke da tsantsar farin ciki sai faman sakin murmushi Yake yi, ba don komai ba sai don zumudin ganin deejansa jiya da ita Ya kwana Aransa yanzu haka yazo ne don Ya ƙara ganinta ya kuma tabbatarwa kansa ba mafarki bane abun da Ya faru Jiya. 


Unaisah Na ganinsa Tace"ba sallama? Me ma Ya kawoka dakinmu da sassafe"?


Shafa sumar kansa yai"ina deejana"? Aɗan ruɗe tay pretending"deeja kuma? Kayi mafarki da ita ne"!


Hankali atashe Yace"bangane me kike nufi ba, wani irin mafarki bayan jiya sun zo gidan nan har mu ka yi shagali, da kaina ma na rakota dakin ku da tace min tana jin bacci.


Fuska adaure tace"haris? Ko dai ka fara samun ta6in hankali ne? Meya kawo maganar deeja? Bayan ta riga da ta rasu tun a prison"? Yanayin yadda tayi magamar ba karamin kayar masa da gaba tayi ba jikin shi yai sanyi gwiwarsa ta sage


"Kina nufin mafarki nayi jiya" ɗaga masa gira tay"zai iya yiwuwa" shiru yayi zuciyarsa ajagule yake kallon unaisah gaba daya so take ta rikita lissafin ƙwalwarsa ..


"Lafiya ka tsaya kana kallona? Meke damunka ne"? Ƙwalla ce ta ciko idanunsa muryarsa na rawa ya furta"deeja na ta mutu? mafarki nayi jiya sunzo? har ta buɗe baki zata bashi amsa Kwatsam Deeja Ta banko kofar toilet din kamar an wurgo ta da karfi ta furta"Laahh! Haris kaine? Yana jin muryarta a ruɗe Yakai dubansa gareta lokaci ɗaya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da gudu Deeja Ta nufe sa ta ƙanƙame shi tana fadin"wallahi jiya har mafarkinka nayi harisuna"


"Deejana Kin tashi lafiya"?


Tana faman Washe Baki tace"lafiyalou wlh, nima muryarka najiyo ina ga daga Cikin toilet, Har na fara alwala na katse ta"


Unaisah dake kallonsu tana dariya gaba daya mamakin ƙaunarsu ya gama cikata, wani abu daya ɗaure mata kai yadda deeja Ta yarda dashi bayan jiya sukai ta fama da ita akan ta tuna shi amma taƙiya sai gashi da yake kaunar tasu a jini take har sun shaƙu jiya izuwa yau


"Sister kada ki sake yi min irin wannan wasan, zuciyata zata Iya bugawa Allah" Yai maganar idonsa akan Unasah


"Naji romeo, bazan ƙaraba, Yanzu sai kabarta ta koma ta karasa alwalar ko fa salla batai ba" Harara deeja ta watsa mata"waike ina ruwanki dani in ma banyi sallar ba, ay ni ba kullum nakeyi ba sai na ga dama, Ko su hawwa basu min dole balle ma ke da bansan wacece ba' muryarta da shagwa6a take magana hakan bakaramin dariya ya basu ba


Lalla6ata haris yayi"rabu da ita, kishi takeyi da take don taga kinfi ta kyau, " washe baki tayi jin Yana yabonta


"Yanzu ki koma ki karasa alwalar in kin gama ki yi wanka sai ki fito muje muyi breakfast" amsa mashi tayi da toh da gudu ta juya tana fadin Kada ka tafi harisuna ka jira ni in fito Yana murmushi ya amsa mata da toh har ta shige bai daina kallon ta ba


Da zolaya unaisah tace"Hankali Ya kwanta Haris, deeja Ta dawo, No more heartbreak " dariyar farin Ciki Ya saki" ba zaki gane ba, wlh daren jiya bayan na rakota dakin ku ta kwanta dana koma dakinmu har nafila nayi saboda in nuna godiya ga Allah daya sake hadani da ita, Ina son deeja Allah Yabar mun ita har abada, in ma mutuwa zata dauke ni ta dauke mu atare" idanu abude Unaisah ke kallon shi aranta tunani take tsakanin deeja da haris da kuma ita da danish suwaye sukafi son juna tsakani da Allah? anya idan danish Ya rasata zaiyi ciwon zuciya kamar yadda haris yayi akan deeja? Ko kuwa ita idan tarasa shi zatai hauka? tabbas A yanzu bata iya ganewa tun da wani bai ta6a rasa wani a cikin su ba, kuma bata fatan abun da zai raba ta da muradin ranta, her eternal lover 


"Haris Ina tayaka murna, Allah Ya nuna mana ranar auranku mu sha biki" da mamaki ya maimaita kalmar aure" yar dariya tay"cikar burin masoya kenan idan time yayi basai na maka bayani ba" murmushi kawai yayi duk da baisan me akeyi a auranba but maganarta tasa shi fara jin son ganin auran nasu.


Ƙarfe tara daidai agogo ta buga, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa daga dakunansu zuwa dining Room kowan nan su yayi wanka Ya shirya sunyi kyau daga ganin fuskokinsu zaka shaida Anyi kwanan farin ciki daren Jiya....


Da wani irin ɗaukin junansu suka fara  ƴan rungume rungumen juna, gwanin ban sha'awa, ƙaunar su  a jini ta ke, harta chefs din dake a dakin cin abincin kallon su sukeyi saboda sun siye zuciyoyin su.


Mutun ukune ke babu acikin su, ummi da batool sai Danish, su kadai ne ba su kaiga ƙarasowa ba.


Sun cika dining room din da surutu Ko zama sun kasa yai, 


Gyaran murya chef Yai masu Hankalinsu Ya dawo kan shi


"Barkanku mu da safiya yan mata da samari, ina fata kun tashi Lafiya" a tare suka amsa mashi da lafiyalou


"Yawwa, Yanzu ba lokacin surutu bane, lokacin bama ciki hakkinsa ne, nasan kunyi kewar Juna amma Ku ɗanyi hakuri ku zauna mana"


 murmushi Kowan nan su Ya saki, ɗayan Chef din Yace"Amma in ba damuwa zamu iya sanin sunayenku? Don gaskiya bansan sunanku ba unaisah kadai nasani' Ya faɗa Yana nuna ta da yatsa


"Ba damuwa ni zan faɗa maku sunayen su," unaisah ce tayi maganar, kafin ta fara faɗa masu sunayen


"wadannan biyun masu kama da twins sunayen su Jemimah sai Azeeza" ta faɗa tana nuna su da yatsa sai faman sakin murmushi sukeyi.


Ɗaga masu hannu chefs din sukai alamar suna miko gaisuwa


"Sajeed Naufal and Javed" ta nuna kowannansu da yatsa


"Wannan Kuma sunan sa Haris ga deejarsa a gefe, kamar anta da jini suke" 


"Kina nufin masoya ne"? Ɗaga masu kai tay alamar eh" 


"Wow masha Allah, shiyasa suke bala'en kama da junansu ashe soyayyace atsakani, Muna miƙo maku gaisuwa" chefs din suka fada suna ɗaga masu hannu, washe baki deeja tayi shima haris din murmushi ne kan fuskarsa


"Ita kuma wannan sunanta Hannah" ta nuna hannah dake tsaye gefen parven, ga kuma Parveen acici" dariya sukai don sunsan Halinta na cin abinci"


Juyawa tayi kan su Rubina"rubina, eve and yasmin sai hibba" da sauri eve tace"kin manta jiya na fada maki yaya salsabeel Ya canza min suna hawwa" 


"Yeah Na tuna sunanta Hawwa, ga kuma sarah da mubeen" ta nuna su da hannu


"thank You unaisah, kunga yanzu munsan sunan kowan nan ku saura mu saba da juna koba haka ba"? Atare suka hada baki wurin amsa masu da Yeah


"Yanzu zamu fara shirya maku wurin zamanku tun da mun samu ƙaruwa" 


Ba tare da 6ata lokaci ba, mutun sha Biyu daga cikinsu suka zauna akan 12-seater dining table din da suka saba cin abinci akan shi, sauran suka samu gurbin akan 6-sitter dama ukune a dakin cin abincin.


Har sun fara cikin abincin, sautin cokulansu Ya cika dining room din kamar a restaurant yanayin yadda suka zauna, chefs din suna daga tsaye suna kallon.


Miƙewa unaisah tayi tare da kallon chefs din tace"zanje na kira aunty ummi da batool" bata jira amsar su ba tay saurin kama hanya don tasan zasu iya tsayar da ita..


Har takusa isa ga stairs, sai ga su sunfito daga daki, Hannunsu ruke cikin juna yadda kasan uwa da ɗiyarta, ummi na asanye da abaya maroon tayi rolling, batool tun kayan jiyane a jikin ta riga da wando na bacci 


Suna ganinta a tare suka sakarwa juna murmushi da sauri batool ta saki hannun ummi ta nufi unaisah suka rungume juna kamar sun jima ba su a tare


"Barka da safiya My own sis, jiya ko ki neme ni, aunty ummi ta ƙwace min ke" ta faɗa tare da raba jikin su daga na juna.


"Ni da ke waye mai laifi? jiya kamar zanyi hauka wurin nemanki, ina kika je baki fada min ba"? rai aɗan 6ace tayi maganar suna kallon juna


"I'm sorry, nima bada son raina na tafi nabarki ba, naga kuna firar yaushe rabo kuma bana son in katse ku shiyasa na tafi...."


"Ina kike je ne"? Ummi ce ta jefa mata tambayar


"Part din daddyna dake acikin gidan nan, " da mamaki ummi tace"oh dama anan yake zaune? Ko da yake naga gidan ba karamin girma ne da shi ba, ay ko zan haɗu da shi maimakon ya gayyace mu muje baki ɗaya shine ya ware ki ko"? Ta fada da zolaya


yar dariya unaisah tayi"wlh ba haka bane, yace min next time kuma zai gayyace ku kuje part dinsa wurin auntyna danejo"


Murmushi ummi tayi"ai ko bai gayyace ni ba zanje da kaina, ko dan ingano danejo, inyi mata godiya saboda taimakon da tayi mana wurin ceto rayuwarki" 


Fuskarta dauke da murmushi tace"naji dadin maganarki aunty ummi, Allah yabarmu atare" amsa mata sukai da ameen


"angama shirya mana breakfast a dining, naga baku futo ba shi ne nazo don in kira ku" 


"Yanzu haka da kika ganmu yunwar ce ta koro mu nida baby girl dina" ta faɗa tare da ruko hannun batool har zata ruko na unaisah donsu tafi a tare tayi saurin cewa" zanje na kira danish ne" amsa mata tai da okey, bayan sun tafi ta nufi bedroom dinsa tana gab da zata shiga taji motsin fitowarsa kusan atare idanunsu suka shiga cikin na juna kwata kwata fuskarsa babu annuri ganinta da yayi ne yasa shi ɗan sakin fuskarsa tun daga kan yatsan kafarta ya fara kallonta ba karamin kyau tayi mashi ba, rigar ta ƙara fito mata shape dinta.


"My man, ina fata ka tashi lafiya," lumshe mata ido yai alamar eh


"Oh ba zaka min magana ba, kasan kuwa yadda na ƙagu da inzo ganinka" ta faɗa tana jifar shi da kallo mai kama da harara irin kallon da ke jan hankalin shi gareta


"Saboda kaga na damu kai ko" ta fada tana ruƙe qugunta


Daƙyar Ya iya haɗiyar yawu Ya furta"kin tashi lafiya"


Ɗaga mashi gira tayi"ina lafiya, pls ka shiga ka canza kayan baccin nan, sauran yan uwanmu suna jiranmu a dining muyi breakfast" 


"Mu shiga atare" maƙe masa kafada tai"a'a zanjiraka anan, ka shiga ka fito" batai aune ba taji yaja hannunta cikin dakin, ba yadda ta iya dole tabi shi ciki.

Juya mashi baya tayi bayan ta cire hannunta daga nashi tace pls ka sanya kayan suna jiran..." kafin ta ƙare maganar ba zato ba tsammani taji Yai huggin din bayanta gaba daya ya kwanto da kanshi kan shoulder dinta tare da zagayo hannayensa kan waist dinta, a matuƙar ruɗe ta furta"meye haka"? Ta fada tana kokarin raba jikinta daga nashi, kamar ya ɗaureta da igiyoyi sam ta kasa ƙwatar kanta ƙara tighting nata yai tuni taji wani irin yanayi da bata ta6a fuskantar shi ba, rai a6ace ta fara zazzaga mashi masifa kamar baisan tanayi ba


Muryarshi tamkar tame jin bacci Ya furta"ki taimaka min na sanya kayan" gaba ɗaya nema yake ya burkita mata lissafin kwalwa, muryarta na rawa ta furta"wai meke damunka ne? akan wani dalili zan taimaka maka ka sanya kaya"? A hasale Ta faɗa tare da kamo hannunsa dake akan cikinta tasoma kiciniyar banbare shi bakomai take jima fargaba ba face ɗan mayafin data ɗaure kirjinta da shi muddin ya warware danish zaiga abun da yajima yana jira kuma tasan sauran in har ya gani sai wani abu ya faru.


Kamar zata fashe da kuka tace"danish ka sakeni banaso, Babu kyau! Ka matse min cikina! tsabar masifa idanunta arufe ta furta maganar

Babu akamun zai saketa sai faman goga tsinin hancinsa Yakeyi akan fatar wuyanta wani irin Yanayi da bai ta6a jin makamancinsa ba.


A lokacin da baiyi tsammani ba, Yaji ta gartsa masa cizo A hannunsa, ba don Yaji zafi ba Ya saketa, da wani irin kallo Yabita har ta fuce daga dakin da gudu.....


Fitarta keda wuya Yaji kamar ancanza mashi tunaninshi, lokacin ɗaya yafara tunanin me yasa yayi mata hakan❓


Tun akan stairs jikinta ke kakarwa kamar wadda sanyi ya kama, Gaba ɗaya Ya jefata cikin Yanayi kamar bata a hayyacin ta


Sam bataji takun tafiyar sa ba, har sai da muryarsa ta katse mata zancen zucin ta"Good morning daugher"! Wani irin firgita tayi don sai taji kamar muryar danish ne ganin daddyntane Yasa tayi saurin daidaita nutsuwarta gudun kada Ya fahimci wani abu Ya faru.


Jiki asanyaye ta nufe shi ta fada kan kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya ta furta"daddy Ina kwana, Ina auntyna danejo, Ina fata kun tashi lafiya" 

Dago da fuskarta yai suka hada ido cikin na juna, farat ɗaya yaɗan fahimci wani abu na damunta

"Kamar wani abu na damunki? Ko baki da lafiyane" adan rude ta girgiza masa kai"bakomai daddy lafiyana lau" 

Ajiyar zuciya ya sauke

"Auntynki tana gaisheki, Kamar zata sanyamin kuka tun jiya bayan mun yi maku rakiya mun koma gida ta dinga yi min surutu akanki, yau da safe har ce min tai zakizo nace mata aa sai tace min tana son tazo taganki  dakyar fa na lallasheta ta hakura'  Murmushi unaisah tayi"Allah sarki auntyna. Kada ta damu har sai ta gaji da ganina'


Ruƙo hannunsa tai acikin nata"daddy muje muyi breakfast"


"Am sorry daughter bana Jin yunwa, aunynki ta cika min cikina, but da anjima idan na shigo zamu ci dinner a tare yanzu zan tafi dama na shigo ne don inga sanyin idaniyata" farfari tayi masa da ido yakai hannu ya ɗan ja kumatunta


huggin dinta Ya sake yi kamar karsu rabu


"Ki kula min da kanki, Allah Yayi maki albarka," amsa mashi tayi da ameen daddyna kaima ka kula min da kanka


Bayan sun raba jikinsu daga na juna. har ya juya zai fita sai kuma Ya ɗan dakata tare da waigowa Ya kalleta tana atsaye bata motsa ba itama shi din take kallo


"Kin shiga wurin chief "? Girgiza masa kai tay alamar a'a,"pls ki dinga zuwa kina gaishe da shi, inaso kina kyautata masa dan Allah"


"In sha Allah daddy, zanyi kamar yadda kace"


"Ina wayarki ne" 


"Nabarta adaki"


"Okey, zan tura maki sakon contact dinsa, ko da baki samu zuwa wurinsa ba, ki dunga tura masa sakon gaisuwa ko ki dinga kiransa awaya kuna gaisawa" cike da ladabi ta amsa mashi da toh, murmushi suka sakar ma juna kafin taj Ya fuce daga dakin


Gaba daya abunda suka tattauna akan kun nan danish dake tsaye kan stairs Ya ɗaura gwiwar hannunsa na dama akan handrail, fuskarsa kamar jan gauta tsabar 6acin rai, ashe Yaji maganar Taj na cewa tadinga zuwa part din chief lallai kam akwai ƙura mai hayaƙi 


Saboda abunda danish Yai mata gaba daya taji breakfast din Ya fita aranta, kamar an dauke mata yunwar cikinta, wani irin fitsari Taji Ya ɗaure mata mara, ba arziki ta nufi dakinsu duk Yana kallonta, tana shiga ta faɗa toilet taja ƙofa.


Tunda tafara sakin shi take ganin wani bakon abu da bata ta6a gani ba, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, bayan ta yi tsarki, gaban madubi ta tsaya zuciyarta na harbawa da wani irin sauri, In har fa bata gano menene ba hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba...


A 6angarensu ummi bayan sun zauna a dining chairs din, cikin girmamawa su rubina suka gaishe da ita, da fara'a ta amsa masu yayin da take kallonsu masha Allah, Gida Yayi albarka, dagowa tayi suka hada ido da chiefs din dake kallonta daga masu hannu tayi"hi sannunku da kokari" amsa mata sukai Da yawwa madam ba tare da sun daina kallon ta ba, ba tun yau ba indai zasu ganta sai sun bita da kallon mayuntaka wato sunga sura..


Gwanin ban sha'awa suke cin abinci, sam babu wanda Yayi tunanin Ina danish da Unaisah saboda firar da suke ɗan tabawa da su rubina taja hankulan su ...


___________________________Hajjaty✍️


Wuraren karfe 11 na safe ta fito daga kitchen hannunta ruke da madaidaicin faranti mai dauke da mug na green tea da kayan marmari


Tuntana tafiya take jin motsin mutun abayanta alamar akwai wanda ke bibiyarta, da zarar ta juya sai taga wayam babu kowa, hakanan ta dinga jin tsoro da fargaba, gashi babu kowa main falo din gidan duk suna a part din su.


Tana tafiya tana ƴan waige waige kamar zatayi tuntu6e, cikin takun sauri ta ƙaraso dakin baba obie, sallama ta fara yi masa daga ciki tajiyo muryarsa ya amsa mata sallamar tare da bata iznin ta shigo


 a kishingiɗe ta same shi kan gadon shi, Ya tada kansa a pillow, hannusa ɗaya ruke da cazbaha yayin da idanunsa ke a lumshe, tuni kamshin turarenta Ya karaɗe ilahirin dakin har saida Ya ɗan buɗe idanunsa..


A hankali Ta ɗaura masa tray din kan table


"Barka da safiya baba, Ina kwana, kun tashi lafiya"? Murmushi ya sakar mata kafin yace"lafiylou Alhamdulillah, Ina fata kema haka" ta amsa masa da eh


Mug din ta dauka ta mika masa yasa hannu ya kar6a tare da yi mata godiya'


"Ko akwai wani abu da kake buƙata" ta faɗa cikin kulawa, bakomai ya fado masa aransa ba face maganarsu ta jiya shi da owais lokacin da yace masa ko yana son ta, shi kanshi yana yaba kulawarta da kyautatawarta agaresa matar tayi ta ko'ina, ga iya daukar wanka....jin yayi shiru  bai amsa mata tambayarta ba yasa ta ɗan ɗago ta kallesa ganin kamar ya koma bacci yasa tace"baba ko ka koma bacci ne"? Girgiza kai yai alamar eh, 


"Idona biyu ke nake kallo" waro idanu tayi waje jin abun da yace da sauri ta sunnar da kanta ƙasa


Ƴar dariya yayi ganin yadda ta ruɗe"kwantar da hankalin ki, ay ba laifi bane don na kalle ki, kinyi min kyau ne" gaba daya ta ƙara kame kanta, dakyar ta kakaro murmushi kan la66anta


"Tashi ki tafi, nagode da kulawarki agare ni"nike da godiya" ta fada tare da mikewa ta nufi kofar fita kwatsam tajiyo sautin takun mutun, lokacin da ta fito bata ga kowa ba, tunani tayi anya ba wani ke bibiyarta ba? ga dukkan alamu anyi masu la6e, tuni tasha jinin jikin ta, da sauri ta miƙi hanya ta koma dakin ta, kamar yadda tabar pravin haka ta same shi kwance ya lullu6e rabin jikinsa da barko.


Zama tayi gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya.


Jin motsu motsin pravin yasa ta kalli bargonsa, murmushi tasaki ganin Ya fara buɗe idanunsa alamar zai farka, da sauri ta faɗa kan jikinsa muryarta da yar shagwa6a take fadin"babyn baby, tun ɗazu nake jira ka farka, ina fata ka tashi lafiya....." da wata irin kasala Ya ware manyan idanunsa da suka kada jawur saboda bacci ya sauke su kan fuskar hajjaty, manna masa sumbata tayi kan lips dinta kafin ta sumbaci karan hancin sa

"Honey, ina alkawarin da kayi min jiya? ko har yanzu ba agyara wayar bane? ta fada kamar zata sanya masa kuka tsabar shagwa6a


Har ya motsa la66ansa zai furta magana, unexpected sautin motsin ƙofarsu Ya daki kunnuwansu, lokaci ɗaya suka dakata tare da kallon ƙofar dake lilo alamar an ta6a ta...



Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, aruɗe hajjaty ta furta"wanene ke ta6a min kofa" muryar marwa ce ta karade kun nan su"Ni ce marwa" kallon juna sukai ita da pravin cike da mamaki, saboda babu wanda ke shigowa dakinta, tsakaninta da sauran ma'aikatan gidan daga kitchen sai in sun haɗu a main falo ko wani part na gidan, kwata kwata bata sakar masu fuskar da zasu zo dakin ta, balle har suga sirrinta..


Muryar pravin kamar tame yin raɗa ya furta"wannan wani irin ganganci ne"?


Hankalinta atashe tace"wlh ba laifi na bane, bansan meya kawota dakin nan ba, kaima ka sani bazan ta6a gangancin yin hakan ba" 


"Je kiji me zata ce maki, kada ki bari ta shigo" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta sauko ta nufi ƙofar ta buɗe ta leƙa karaf suka haɗa ido da marwa dake ta faman washe mata baki, da sauri ta ƙara babbake bakin ƙofar don  kada ta samu damar ganin meke a dakin


"Marwa! Ta fada da mamaki da sauri marwa tace"am...um..barka da safiya.." bata amsa mata gaisuwar ba, sai cewa tay"ina fata lafiya? Don banta6a ganinki a ɗakina ba..." washe baki marwa tayi muryarta da alamun rashin gaskiya ta furta"dama..um inaso zan fara aikin dinner ne da wuri to na shiga kitchen din sai naga store a kulle kuma babu makulli a bakin kofar, na tambayi abla ko ta dauka shine tace min yana a wurinki" wani kallon tuhuma hajjaty take jefa mata, abun yaso bata mamaki, 

Murmushin gefen fuska tayi"hmm marwa kenan, kina abu kamar wadda ta samu cutar mantau, in ba ni ba waye dama yake ruke makullin store? da har zaki tambayi abla ina Yake bayan haka wani girkine zaki fara a yanzu? Bayan breakfast da kuka kammala ko dai baki kalli agogo bane? 

Sosa ƙeya tayi"wai da afara dinner din da wuri" 

Kaitsaye tace mata"a'a babu bukata, kamar yadda kuka saba haka zakuyi dole sai lokaci Ya cika, sannan pls idan kinason Yin magana dani basai kinzo dakina ba! Ki kirani da landline din kitchen kamar yadda kuka saba kirana ku sanar da ni abu"! Ko amsar marwa bata jiraba, taja kofa Ta datse


Rai a6ace marwa take kallon kofar, dakin wai har ita hajjaty zata ja ma kunne kan karta kara zuwa mata daki? Lallai buri ya yi kama da mutun da alama maganar hajiya saratu zata tabbata matarnan bata da gaskiya Allah kadai Yasan makircin da take kullawa da har batason wani Yazo dakinta, dani kike magana hajjaty saina zame maki karfen ƙafa agidan nan..." acikin ranta tafada Harta fara tafiya zata koma kitchen sai kuma ta dakata tana tariyo abunda Tajiyo adakin farkon dataje tafara yin la6e a kofar, tabbas taso tajiyo muryar hajjaty kamar tana magana da wani sai dai bata kaiga shaida hakan ba


Murmushin mugunta marwa tasaki a fili ta furta"ni da ke ne" tayi maganar tare da kama hanya tabar wurin.


Bayan komawar Hajjaty dakin, a zaune ta iske pravin yana jiran ta fuskarsa a yamutse saboda Ya tsani duk wani abu da zaija asirin shi Ya tonu 


"Ta fada maki abun da ya kawo ta"? Ya jefa mata tambayar, zama tayi gefen shi kafin ta sanar da shi maganar da sukai da marwa


"Ni sai nake ga kamar leƙen asiri ta zo yi min saboda babu kwanciyar hanlali atare da ita" ta faɗa tana kallon fuskarsa


Pravin yace bana tunanin haka, just ki bar komai a hannuna idan ta ƙara yi maki wani abu da hankalinki bai kwanta da shi ba ki sanar dani" ta amsa mashi da toh



___________________________ANEELERH✍️


Yau saboda da zumudin zuwan benazir ko breakfast batay ba saboda tafi son idan benazir tazo su ci abincin a tare, 


Su uku ne a kitchen suke aikin girka ma bakinsu abinci, gaba ɗaya kamshin abincin Ya cika ko'ina


"Pls ku yi sauri mu kammala ta faɗa min da wuri zasu zo, dakyar ma in basu tafo ba" 


"Aunty Aneelerh wacece bakuwar tamu ne"? Ana ce ta faɗa tana kallon ta yayin da take tsaye gaban gass cooker tana aikin soye soye


"Ki bari idan tazo zaki ga wacece, nafi so na baki mamaki" cikin raha ta faɗa


"Allah ya kawo su lafiya, har nakosa na ganta"


"Ameen,"


Kallon zahra tay, gaba ɗaya hankalin ta ba akan su yake ba, tana a tsaye gaban counter, inda ta ɗaura juicer ga kayan marmari shaƙe da bowl da alama ta tafi duniyar tunani, tafi karfi mintuna biyar bata ta6uka komai ba, gaba ɗaya tunaninta na akan zayn, zuciyarta sai azalzalarta ta ke yi akan son ganinsa tayi missing dinsa.


"Zahra! Zahra!!" muryar aneelerh ce ta fargar da ita lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya tare da kallon ta


"Me kike tunanine? Naga kamar wani abu na damunki"? Murmushin yake tayi"bakomai auntyna.."


"Kedai faɗa min gaskiya ko dai damuwar rashin wayarki ne"? Da sauri tace a'a wlh ba haka bane


"To menene tun ɗazu kin ƙi motsawa, Na fa faɗa miki da wuri zasu zo watakil ma sun kamo hanya," 


"I'm sorry bari na fara Yanzu zan kammala in sha Allah kafin ma su ƙaraso mun gama komai"


Har sun kusa kammala girkin Mami ta shigo kitchen din tana fadin"wai wai irin wannan kamshi haka? Tun da ga ɗaki nake shaƙo shi, lallai Yau bakin mu zasu kwashi gyara" murmushi kowan nan su Ya saki


"Mami sannu zuwa, me kikeso na zuba maki" zahra ce tay maganar


"Ni iya juice din nan Ya ishe ni, sai dai bansan ko ummi zata bukaci wani abu ba"


Zahra tace"to mami, bari na zuba maku hada snacks"


"Yawwa zahra na, adan sanya min kankara aciki zaifi dadin sha" ta amsa mata da toh


Kallon aneelerh tayi"har su nawa ne zasu zo naji dazu kamar kince hada Yayanta shureim"


"Eh hada shi tare da ɗiyar Uncle din ta"


Mami tace masha Allah, Allah Ya kawo su lafiya, bari na koma falon kada na cika ku da surutu...." har ta kusa fita ta kuma juyowa tana fadin"zahra ina jira"  


"Toh mami yanzun nan zaki ganni" 


Bata jima da fita ba, zahra taje ta kai masu a falo....




_____________________________✍️


ƙarfe sha biyu daidai benazir tana atsaye gaban mirror ta kammala shiryawa cikin atampha riga da skirt sun kama jikinta, ta tsara make up akan fuskarta wani irin kyawune ya ƙara bayyana ta fito ɗas balarabiyarta, ta kashe daurin dankwali bayan ta gama ta miƙe ta dauko mayafin ta dake a ninke kan mattress ta yafa shi a kafaɗa, jujjuyawa tayi gaban mirror din kafin ta sakarma kanta murmushi kyawawan dimples dinsa suka lotsa..


"Aunty benazir yaya shureim yace in baki fito ba zamu tafi mu barki agida" ta cikin mirror ta hango zeentu da tayi maganar, kamar aljanna ta ca6a uban adon lace launin blue sky mai walwali da daukar ido, ɗan ƙaramin bakinta ta shafe shi da jan baki, ga wani daurin dankwali da akayi mata mai kama da ture kaga tsiya ta sauko da gashin ta, ziririn wuyanta yana asanye da ziririyar sarƙar diamond


A sukwane Benazir ta juyo fuska adaure ta kalle ta har saida tasha jinin jikin ta


Da ƙarfi ta furta"zeenatu? meye haka? Wannan ado sai kace zamu je gidan surukan ki? 


Zazzare idanu tayi"ay ni ba su nayi ma kwalliya ba, ta yaya shureim ce amma idan baki son gani na da ita sai na canza wasu kayan in goge kwalliyar"


Yamutsa fuska benazir tayi"da dai yafi saboda baki kyau ba, ko meye na shafa powder wai ke kinga fuskarki kuwa? Kamar wata fatalwa? Kina fara dole sai kin shafa powder? So kike ki zama zabayyana ne"? shiru tayi tuni annurin fuskarta ya fara daukewa muryarta da yar shagwa6a tace"Aunty benazir ay na fada maki mommy ma tana shafa powder in zatay ma daddy kwalliya, kuma kema ay fara ce sol amma kina shafa powder...." kafin ta ƙare maganar benazir tace"naji, amma ay ban kaiki haske ba, bana son jan magana kije ki canza kaya in har kinaso mu je dake"


idanunta ne suka cicciko tab da kwalla benazir dake kallonta aranta ta ce kawai daga zan kara ki mu fita sai ki fini kyau hada wata sarƙar diamond...."



Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi bazan canza kayan ba, ay yaya shureim yace nayi mashi kyau, kuma yace duk inda zaije ƙafarsa ƙafata don haka dole aje dani aunty benazir" ranta yakai makura 6aci juyawa tayi da gudu zata fuce daga dakin cikin rashin sa'a highhills din kafarda suka turguɗe gaba daya ta tafi zata kife ƙasa cikin zafin nama dr shureim Ya ruƙota ta dawo jikinsa babu wanda yasan da zuwansa a cikin su ashe yabiyo bayan zeenatu.


Wankan shadda ne a jikin shi, zeenatu na jin dumin jikinshi ta ƙankameshi tana fada masa abun da benazir tace


Murmushi yasaki yana kallon benazir dake kallon sa


Da buɗar bakinsa sai cewa yai"ke baki gane ba? Kishi take yi dake saboda kinfi ta haɗuwa, itafa tun tana ƙarama in za'aje unguwa tafi so taga tafi kowa kyau don haka kada ki damu dabi'arta ce" jin wannan maganar yasa zeenatu fashewa da dariya har hakoranta suka bayyana.

Ta6e baki benazir tayi fuskarta da dan murmushi tace"yaya shureim yanzu abun da kai ka kyauta? Agaban zeenatu kake fadin hakan? So kake ta raina ni"?


Ɗaga mata gira yai alamar eh, jinjina kai tay"bakomai, na fahimci kafi son zeenatu akaina, soyayya ta rufe maka ido ya shureim ka rasa ma wa zaka so sai wannan ifritun sa'ar ƴar ciki na" ta fada da zolaya tana nuna zeenatu


"Ahaka nakesonta" ya fada  yana murmushi, zeenatu sai dadi takeji har wani ƙara maƙala hannunta acikin nasa take


"Mu munyi gaba Ki iske mu a mota" yana ƙare maganar Yaja hannun zeenatu suka fuce, da sauri benazir ta dauko mayafi ta yafa a kafaɗa, hannun ta ruƙe da yar purse ta fito 


A falo suka iske su hajiya layla suna fira kamar wani abu bai ta6a faruwa ba, Yanzu ta kwantar da hankalinta tun bayan abun da Ya faru jiya


"Zamu tafi mommy asanya mana albarkar iyaye" dr shurem ne yai maganar, atare suka dago da murmushi akan fuskokinsu


Hajiya sara tace"masha Allah, tabarakallahu ahsanul khalikin kunyi kyau kamar dollars" dariya suka sanya gaba dayansu


Fuskar hajiya layla da murmushi tace"nima naso aje unguwar nan dani amma zan bari zuwa nagaba" ta fada yayin da aranta take jin fargaban abun da benazir zata juyo awurin kawarta aneelerh tasan zaiyi wuya in bata fada mata ainihin abun da ya faru da mijinta da yar ta ba, daga nan zata gane tayi mata ƙaryane, tuna wannan yasa taji jikinta yayi sanyi ji take kamar ta hana au zuwa gidan saboda batason 6acin ran benazir ko kadan, fatanta Allah Yasa aneelerh tayi hankalin boye mata gaskiya.


"Mommy layla ni da aunty benazir wayafi kyau"? Zeenatu ce tay maganar da sokana

"Ay bama haɗi kin fita kyau nesa ba kusa ba" acewar layla da sauri hajiya sarah tace"a'a bana son sonkai Allah, aiko makaho ya shafa yasan wayafi kyau, auntynki tafi ki kyau nesa ba kusa ba, itafa jinin larabawa ce" kwa6e fuska zeenatu tayi jin abun da mommynta tace, da sauri ta kalli benazir dake yi mata dariya zumbura mata baki tayi


"Shureim zata bata maku lokaci, Ku tafi ku kyaleta, dama daddynta dakyar ya amince ta biku," yana murmushi yace"toh mommy mu zamu wuce" atare suka hada baki wurin firta"Allah yakaiku lafiya, ku gaida mutanan gidan"

"Zasuji in sha Allah"

Har sun kusa fita falon hajiya layla ta ce"idan kun isa gidan Benazir ki kirani awaya inason yin magana da aneelerh" amsa mata tayi da toh kafin suka fuce, su zeenatu sai rawar kai akeyi za'aje unguwa...


Abakin motar Dr shureim suka tsaya benazir ta fara daukar su hotuna da wayarta har kusan kala takwas bayan sunyi atare tayima zeenatu tare da dr shureim kafin taba zeenatu wayar tayi mata ita kadai sai kuma tayi atare da shureim......


Shiga motar sukai, Dr shureim yana a driver's seat zeenatu na zaune gefensa, benazir kadai suka bari a backseat.


"yau ni za'a nunawa wariyar, wato  zeenatu ce ta gaban mota, ni kuma ta baya babu komai nima idan mijina ya dawo zan koma ta gaban motarsa ne" dariya sukayi gaba dayansu, 


Bayan yai wa motar key ya fara driving a hankali Ya nufi gate din gidan babu wanda ya dakatar da su saboda an basu umarnin su barsu su fita.


Bayan motarsu ta haura kan titi kowa Ya nutsu, zeenatu sai satar kallon benazir takeyi ta mirror din motar har gwalo take mata saboda ansanyata agaban mota


Murmushi benazir tayi tare da ɗan girgiza kanta aranta ta ayyana bayan sangarta hada ƙuruciya ke damun ki


"Aunty benazir masu number din nan ba su ƙara kiran layin ba"? 


"Namanta ban fada maki ba, me layin ta kirani awaya, yarinya ce kamar ki, ashe ta sanya wrong number ne, ko jiya na kirata awaya mun gaisa saboda ta kwanta min araina"



*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*



 *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank 


Bature Hafsat Muhammad,

 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post