BAYANI AKAN JININ HAILA:
Please Ayi Sharing Domin Yan Uwa su Amfana
Kowace yarinya tanada uterus (makwancin yaro) da ovaries (gidan kwai guda biyu) tun haihuwar ta suna nan ashirye amma basu fara aiki ba.
Lokocin da yarinya takai shekaru 12 zuwa 15, gidan kwai zaifara aiki, wato kwai nafarko zai nuna.
Nunan kwai a wannan lokocin zaisa jikin yarinya ta canxa zuwa mace. Ga kadan daga cikin canjin:
1- Mamanta zai girma
2- Zatafara cire gashi a hammata da kuma gabanta.
3- Zatafara Al'ada.
Duk wadannan chanji yana faruwa ne domin yarinya ta samu ikon haihuwa.
To ko wanne wata kwai daya yakan nuna a gidan kwai.
Lokocin da kwai yafara nuna makwanci zaiyi shiri domin yakarbi kwai.
Bayan kwana goma kwai yagama nuna, zai shiga hanyar kwai zaibi hanya zuwa makwanci a wannan lokocin acikin makwanci akoi wani Abu kamar majina cike da jini tariga ta girma dan takarbi kwai kwai zai mutu bayan kwana daya zuwa biyu.
Bayan kwana sha biyu bayan da kwai ya mutu, majina cike da jini na cikin makwanci wanda muka fada shima zai mutu, za tafita waje tare da jini *shine al'adar mace*
Jinin Al'ada yana zuwa da Dan murdan ciki ta dalilin mahaifa ke motsawa waje guda domin fitar da jinin. Da sauran alamomi Wanda ba lalle sai mun anbanta ba.
Kamar yadda mukasani wassu kan fiskanci matasaloli daban daban yayin zuwan alada ta xubar jini ko ciwon ciki mai tsanani (Dysmenorrhea) to wadannan matsalolin mafi yawa tana faruwa ne ta dalilin:
- Shigar kwayoyin cuta
- Ciwon sugar
- Wasu magunguna da baikamata asha ba.
Idan ana samun wannan matsalar yakamata aje asibity.
Abin da mata yakamata su kula lokocin al'ada sabida kariya ga matsaloli shine:
1- Kada ayi amfani da da ruwan kankara ko ruwan sanyi lokocin al'ada sabida amfani da ruwan kankara yakan sa jini ya daskare a mahaifa bazai fita gabaki daya ba , bayan shekaru 5 zuwa 10 sai yakawo ciwon daji na mahaifa.
2- Lokocin Al'ada kada kisawa kanki shampoo ko wacce kala sabida a wannan lokocin kofar gashi a bude take kuma shigan shampoo kofar gashi Yana kawo ciwon kai mai tsanani.
3- Lokocin Al'ada kada kici gurji (cocumber) sabida akoi sinadarai a jikinta wanda zai iya hana jinin yafita gabaki daya , wanda daka karshe zai kawo ciwon daji na mahaifa.
4- Koda wasa kada kiyarda a daki cikin ki , kuma ki kiyaye duk abinda zai daki cikinki sabida dukan ciki a wannan lokocin zaijiwa mahaifa rauni wanda daga karshe zai zama ciwon daji, kuma yana kawo aman jini lokoci guda.
5- kaada ayi amfani da gishiri mai yawa amfani da gishiri (manda) diyawa yana kawo yawan zubar da jini kuma yakan sa ruwa ya taru a mahaifa.
7- Kada kiyi amfani da kwakwa (coconut) lokocin al'ada sabida tana tsananta alamomi.
8- Kada ayi amfani da barasa lokocin al'ada duk da bincike ya nuna tana rage radadi lokocin al'ada, to akoi matsaloli diyawa da zai iya kawowa mace amfani da shi lokocin al'ada.
9- Kada kiyarda kibar pad a jikinki samada awa 3-4 lokocin al'ada koda jinin baya zuwa sosai.
10- Tabar sigari dukkan mu munsani tabar sigari tana da illa ga lafiyar jikinmu bayan haka bincike ya nuna amfani da shi lokocin al'ada tana saka alamomi suyi tsanani.
MEYAKE KAWO JINKRIN AL'ADA
Abubuwa da dama suna kawo jinkiri ko rikicewar Al'ada:
1- Juna Biyu
2- Shayarwa
3- Shigan Kwayar cuta
4- Magungunan tazarar haihuwa
5- kunburin kwan mace (ovarian cyst)
6- Rashin kwanciyar hankali (Stress)
7- Motsa jiki mai tada hankali.
8- Rashin samun lafiyayye kuma isheshen abinci
9- Cututtuka kamar zazzabin typhoid.
10- Matsalar sinadaran hormones.
11- Magunguna irinsu maganin cancer.
Samun juna biyu yana bukatar yanayin al’ada daidaitacce ba rikitacce ba sabida haka rubutu na gaba zaiyi magana akan me yake kawo rashin samun juna biyu.