Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 26 Complete

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 26 Complete

Novels Elite English

 Rass Taji gabanta Ya faɗi La66anta na kerma tace"Zahra itama ainihin sunanta Unaisah, Angel da muke kiranta nickname ne da daddynta Ya sanya mata, ɗiyar wacece ne a family din su"? 


Hankalin zahra ba karamin tashi yayi ba, ganin yadda aneelerh ta ruɗe ita kanta aruɗen take

 


"Na manta ban faɗa maki labarin Yaran ba, Kamar Yadda naji daga bakin chief owais, kamar ba su da alaka da su, hasalima a daji suka tsinto su..." tiryan tiryan Zahra ta kwashe duk abunda Ya faru a wurin dinner din dangane da su Unaisah ta sanar da aneelerh


Kusan zaucewa tayi hannunta dafe da kai, ganin tana tangyal tangyal kamar zata faɗi Yasa Zahra Yin saurin ruƙo Aneeelerh ta taimaka mata ta zauna gefen gado


"Wallahi itace, Angel ce, Har abada bazan ta6a mantawa da fuskarta ba, ko shakku banayi wannan Yarinyar ANGEL ce tun da har kika ce tsintar su akai....


Gaba ɗaya rudanine akan fuskokin su, 

"Hakan na nufin Junaid Shi Ya fara gane itace? 

"Bangane me kike nufi ba yaga hoton ne"!

Jinjina mata kai tay lokacin dana buɗe hoton don in nuna masa da karfi ya kwace wayar daga hannuna Yana fadin Angel Angel..." 


"Zai iya yiwuwa saboda Yawan nuna masa hotunanta da nake Yi shiyasa Ya gane ta, Ni dai Yanzu Ki taimaka min zahra! Inason na tabbatar da abun da nake hasashe! Taya zamu Iya ganin ta"❓❓❓


"Auntyna Ganinta ba abune mai sauƙi ba, dama ace bangaren su hajiya saratu suke da zama zaifi min sauki in nemi alfarmar ganinta, amma gaskiya tunkarar chief owais ba abune mai sauƙi ba! Kinsan Yanayin aikin su na jami'an sirri wallahi in ma suka ji maganar zasu Iya tuhumarmu"


"Wallahi zahra In har ban samu ganin Yarinyar nan ba Hankalina bazai ta6a kwanciya ba, ke koda Zasu tuhume  ni ne, gobe sai naje estate din nasu..." da kwarin gwiwa tayi maganar


"Ƙwara mu bi komai a sannu, kada mu ce zamuyi gaggawa tun da bamu da tabbacin in itace dagaske...." kafin zahra ta ƙare maganar Aneelerh ta katse ta da cewa"zahra itace! Nifa ba makauniya bace, wallahi unaisah ce Yarinyar nan, tun fa tana jinjirarta muke kula da ita, shayar da ita ne kawai banyi na, tayaya bazan gane fuskarta ba"? Idanunta cike tab da kwalla ta furta maganar

"Ki taimaka min zahra, dan Allah, ko dan saboda Halin da mahaifiyarta take a ciki, wallahi bakiga tashin hankalin data Shiga ba a lokacin dana sanar da ita zancen 6acewar su, ba dan zuciyar imani ba da tuni zuciyarta ta buga...." 


Ruƙo hannunta zahra tayi a cikin nata"ki kwantar da hankalinki aunty aneelerh, kada ki bari hawayen dake taruwa a cikin idanunki su zuba, muyi hakuri zuwa gobe inyaso sai muje can estate din nasu watakil adace su barmu mu ganta..." cikin kwantar da murya tayi maganar donta fahimci nema take ta zauce har lokaci bata daina kallon hoton ba


"Mezai hana mu tuntu6i Ziyad? tun da shi yasan da zancen 6acewarsu kuma yana da hotunan Unaisah da na tura masa ko shi zai iya yi mana hanyar haɗuwa da ita"


"Good Idea Auntyna, Yanzu Ki kwanta Ki huta, Gobe saimu ƙarasa maganar" 


Jinjina kai tayi"shikenan zahra, Allah yasa zan Iya runtsawa, Bakisan Yadda na ƙagu da son ganin Yarinyar nan ba, fatana Allah Yasa itace ɗin."


"Amma  kunyi waya da su aunty Benazir din? Sun isa gida Lafiya?


"Na kira layinta bata ɗaga ba, sai zuwa gobe zan sake jaraba kiran ta.."


Suna Cikin Yin magana Baby Junaid Ya fara mutsu mutsu zai farka daga bacci 


"Junaid zai farka, Ki koma gurinsa, ni zan wuce aunty aneelerh,


Miƙa mata wayar tayi"mu kwana lafiya zahra"


Fucewa tayi daga dakin, Aneelerh ta koma kan gado ta janyo junaid on her chest ta rungumesa


Babu alamun zata Iya runtsawa saboda zumudin jiran gobe tayi, abu biyu ne suka tsaya mata aranta, na farko damuwar Benazir, na biyu yarinyar nan mai suna Unaisah...


*HAJJATY*


Can cikin bacci ta soma jin motsi a dakin ta wanda yayi silar farkar da ita, tayi zaton pravin ne Ya shigo shiyasa batai yunkurin tashi ba sai ma ta ƙara gyara kwanciyarta, kwatsam kamar daga sama tajiyo ƙarar faɗuwar wani abun firgigit ta zabura zaune tana faman zare idanunta jikinta Ya hau 6ari ta fara laluban fitila zata kunna hasken ɗakin, akan kunnanta taji takun tafiyar mutun adai dai lokacin ta samu damar kunna light din kamar walkiya taga gifcin mutun Ya lullu6e jikinshi da bargo, wata irin zufa ce ta keto mata numfashinta na hauhawa take kallon ƙofar cike da mamakin wanene Ya shigo? don kwata kwata baiyi kama da pravin ba... 


Wurga ido tai akan tsakar dakin bakhhoor burner din da take ajiyewa kan mirror shi ta gani kan floor daga gani kado shi akai


Lamarin Ya ɗaure mata kai, saukowa tay daga kan gadon ta, gaba ɗaya tsoro Ya kamata, dama ƙwarin gwiwarta pravin ne gashi baya nan Yana can dakin Hajiya saratu.


Tayi mamakin ganin bedside drawer dinta a buɗe, zukunna tayi gaban drawer din yatsun hannunta na kerma ta curo album din dake a ciki mai ɗauke da hotunan auransu, cike da tashin hankali take bubbuɗe su ganin ba'a ɗauki hoton Ba Yasa Hankalinta Ya ɗan kwanta, da sauri ta mike taje taja ƙofar ta datse, ta sanya key


Komawa tayi gefe gado ta zauna har time din jikinta bai daina 6ari ba gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, tun da gashi har an fara kawo mata hari adakin ta, Allah Allah take gari ya waye pravin yazo don ta faɗa masa abun da ya faru


______________________BATOOL✍️


Tsakar dare ta farka sakamakon fitsari da ya matse ta, saukowa tayi daga kan gado


Miƙa tayi kafin ta nufi toilet din tana dab da zata shiga, tajiyo sautin murya ƙasa ƙasa Ana magana har sai da taji gabanta Ya ɗan faɗi da sauri ta kalli gadon su duk a tsammanin ta ummi tana akwance ashe bata nan fululluka ta lullu6e da bargonta sai yai kamar mutun na akan gadon


Kanga kunne tayi don ta ƙara tabbatarwa da kanta muryar waye take ji ƙasa ƙasa kamar ana raɗa


"Kaima kasan bazan ta6a yin kuskuren da wani zaisan ina a tare da kai ba, yanzu haka da nake Yi maka magana ina a cikin toilet saboda bani kaɗai bace a ɗakin, akwai ɗaya daga cikin yaran da muke kula da su, Yarinyar tana sona, a tare muke kwana da ita........"

 

Ɗagowa batool tayi da kanta, Idanunta aɗan zare babban abun da take jima tsoro da wa aunty ummi take magana a tsakar daren nan kuma acikin toilet? Wanene? Da har take faɗin bata son asan tana waya da shi?


Gaba ɗaya tashiga ruɗani, Ƙara kanga kunnan tay jikin ƙofar


"Bazai yiwu ba, Ni Bazan Iya yakice ta daga gare ni ba, na faɗa maka Yarinyar bata da matsala, she is innocent bayan haka bata da wayon da har za ta sanya min ido..." 


"Meyasa baka son kowa Yasan Ina atare dakai? kamar wani mara gaskiya kodai bakasan sunan ka Ya 6aci ne a idon jama'a"? 


Ta sake ji ummi ta faɗa, can kuma sai tajiyo tayi wani sauti mai kama da nishi nishi da jan numfashi


Kwatsam tari Ya kubcewa batool waro idanu tayi kafin jiki na 6ari ta watsa aguje ta kashe light din dakin  ta haye kan gado ta ja bargo ta lullu6e tana faman sauke ajiyar zuciya


A fujajen Ummi ta fito daga toilet din, yar rigar bacci ce a jikinta shara shara, kai tsaye ta sauke idon ta kan gadon, ganin batool a kwance tana bacci Yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, juyawa tayi ta koma cikin toilet din taja kofa ta datse


Batool dake a kudundu ne cikin bargo jin alamun ta rufe kofarne Yasa ta ƙara jin hankalinta Ya kwanta, ta kudiri aniyar saita faɗa ma Unaisah maganar da aunty umminsu keyi a toilet, saboda ta tsorata gani take kamar akwai wani abu a ƙasa duk da bata zarginta.


Ga fitsari cike da mararta amma saboda abun da Ya faru Ta hakura da yin shi, ta matse shi kuma cikin ikon Allah wani baccin Ya sake daukarta


____________________UNAISAH ANGEL


Kiraye kirayen sallar asubahin da aka farayi ne Ya farkar da ita, addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin headboad


Kayan baccine a jikin ta, Milk colour riga da wando masu kyan gaske da alama baccin bai sake ta, sai faman lumshe idanu take Yi


bakomai take tunani ba face Aunty pretty ɗinta, bata ta6a damuwa da ita irin na Yau ba, Wani irin marmarin son jin muryarta take Yi aranta ta ayyana ko awani hali take a yanzu? 


Canza akalar tunanin nata tayi akan danish, murmushi tayi tunawa da haukansa na jiya har yanzu inta tuna abun da yai mata sai taji wani irin yanayi atare da ita


Ta ɗau lokaci tana ƴan tunane tunane, kafin ta ware gray eyes din ta,   hannu takai ta ɗan bubbuga kafadar deeja dake bacci tana jan minshari


"Sis ki tashi time din salla yayi" cikin magagin bacci deeja tace"Ni ki kyale ni, waike kullum sai munyi sallah ba a hutawa...." 


Murmushi unaisah tayi"Pls kada ki wahalar dani..."


Daƙyar ta samu khadeeja ta farka daga bacci, bayan sunyi alwala suka sanya hijabi a jikinsu, 

Ko da suka kabbara sallar khaddeeja ba ibadar ce agabanta ba, da zarar unaisah tayi sujjada ko ruku'u sai ta daddage ta ɗuma mata dundu abaya


Baiwar Allah, ahaka ta daure suka kammala sallar, bayanta har wani zogi Yake mata, 


Batasan Ya zatai da ita ba, Haris ne Yaja mata shi da ya fara kawota dakin su don ta kwana, 


Akan darduma bacci Yai awon gaba da khadeeja


Miƙewa tay da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan mirror cike da zumuɗi ta danna ma aunty pretty call tasan i warhaka ta farka Yin sallar asuba


Almost 3 times wayar tana ringing ba'ay picking ba, duk da haka bata hakuraba ta sake jaraba kira


Cikin sa'a Akai picking batare da anyi mata magana ba


Calmly unaisah tay mata sallama tare da cewa aunty pretty barka da asuba, kin tashi lafiya....." shiru ba alamar za'ay magana

"Naji kinyi shiru bakice komai ba, dan Allah kiyi min magana jiya har mafarkin ki nayi ..." kafin unaisah ta ƙare maganar wata murya ta ratsa ta da cewa"Wacece Ke? Kuma wa kike nema"?


Wani irin shock taji, Har saida gabanta Ya faɗi jin muryar Yarinyar sai taji kamar ta ta6a jinta awani wuri


"I'll hang up if you don't talk!'"


Da sauri tace"sunana unaisah, aunty pretty nake nema"


"Oh ko ke ce kika kira wrong number rannan"? 


"Ni ce"


"Okey,  me wayar ba ta farka daga bacci ba..".


"Wacece ke"?


"Cousin dinta ce, sunana zeenatu" lokaci ɗaya taji yarinyar ta shiga ranta, ta rasa a ina ta ta6a jin muryarta tabbas akwai wadda ta sani mai irin voice din ta


"Dan Allah, Idan ta farka daga bacci ki faɗa mata na kira,"


"Toh sai anjima" tana fadan hakan tay rejecting call din


Ƙurawa screen din ido Unaisah tayi, yayin da kwakwalwarta ke cigaba da tariyo mata voice din zeenatu.


A bangaren zeenatu bayan sun gama waya da unaisah, mikewa tay daga kan darduma jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ɗaya ruƙe da wayar cikin sauri ta fito ta nufi dakin Benazir 


Kamar yadda suka bar shi jiya haka ta same shi a garkame, dr shurem daya kwana awurin kiran sallar asuba ne Ya farkar da shi lokacin da zeenatun tazo baya awurin sun tafi masallaci


Knocking kofar tayi"aunty benazir dan Allah ki buɗe min ƙofa, inason ganinki, jiya na damu da halin da kika shiga, ko baccin kirki bansamu nayi ba..." shiru babu alamun zata buɗe mata.


"Zeenatu ki daina wahalar Yi mata magana ba buɗewa zatay ba, halin ta ne tun tana ƙarama in Ranta Ya 6aci sai munci wahala kafin mu shawo kanta..." hajiya layla ce tay maganar, baiwar Allah daga ganin idanunta ko bacci batay ba sunyi ja idon Ya ƙanƙance


Muryar zeenat kamar zata fashe da kuka tace"tun jiyafa take a daki kulle! Bata magana, Idan wani abu Ya same ta fa..." 


Shigowar Su dr shureim ne Yaja hankulansu ga dubansu, Su ukune tare da Alhaji musa da Alhaji ubaid duk sun sanya jallabiya a jikin su.


Zeenatu na ganin daddynta, da gudu ta nufe shi, ta faɗa kan kirjinshi tana kuka take fadin daddy aunty benazir taƙi buɗe ƙofa tun jiya, dan Allah kasa a balle ƙofar, bana so wani abu Ya same ta...'  


Fuskarsa babu annuri Yace"meyasa zaki damu kanki akanta? Ba ita ta kulle kan ta ba ne? Ko wani Ya rufe ta ne..." bai kare maganar ba hajiya layla ta katse shi cikin 6acin rai tace"wai kai wani irin bauɗaɗɗan mutun ne? Baka da tausayi ne kwata kwata arayuwarka? Jiya kana ganin halin da ta shiga har faɗa maka akai amma saboda rashin imani sai cewa kai a kyaleta in ta gaji zata buɗe kofar saboda ba yarka bace ko..."?

 bata ƙare maganar ba Alhaji ubaid Yai hanzarin katse ta da cewa"dan Allah kiyi hakuri ki daina ɗaga masa murya, jiya agajiye muka dawo gidan shiyasa  Yace haka" harara ta wurga masa"kai ay saboda yarkace jiya ka hana idon ka bacci duk da agajiyen ka dawo gida, na tabbata da ace yarsace ke ahalin da benazir take aciki wallahi ba zaka iya runtsawa ba...." tun da tafara magana Alhaji musa Yake bin ta da kallo, arayuwarsa Ya tsani mutumin dake masa faɗa Yana ɗaga masa murya, babu wanda ya ta6a gigin yi masa hakan sai hajiya layla....


Dr shureim Bai tsaya kula su ba, ya juya ya nufi dakinsa zuciyarsa sam bata masa dadi, lamarin Family dinsa Ya fara gundurarsa kwata kwata ba zaman lafiya daga wannan sai wannan


Jinjina kai Alhaji musa Yayi, ba tare daya tanka mata ba, har Ya ɗaga ƙafa zai wuce Hajiya layla ta dakatar da shi ta hanyar shan gaban shi 


Da mamaki Ya dago Yana kallon ta


"Wallahi babu inda zakaje! In har bakasa an buɗe kofar dakin benazir ba ni kuma bazan ta6a bari kabar wurin nan ba..." tana huci ta faɗa haɗi da ruƙe qugun ta, wlh a lokaci niyar kwashe ta da mari yayi amma sai Ya fasa Yatsun hannunsa har kerma su ke tsabar 6acin rai, wai shi yau mace zata tari gabansa? Batare da jin shakkarsa ba? Wacece ita? Dame take  taƙama ne"?


"Layla ba haka mukai dake ba! Kin manta alkawarin da kikai mun na cewa ba zaki ƙara shiga huruminsa ba"? Azafafe ta kalli Alhaji ubaid"ban manta ba, amma wallahi Yau bazan raga masa ba, ay shi yasan ta yadda zaisa abude kofar, don haka bazan tsaya inaji ina gani in rasa ƴata ba dole yasa aballe kofar can" ta yi maganar tana watsa masa harara...


Fashewa da kuka zeenatu tayi jikin ta har jijjiga yakeyi, cikin shesshekar kuka tace"daddy dan Allah kasa a bude kofar, ni bana son inga kuna samun sa6ani atsakaninku, dan Allah daddy ka taimaka mana..." kukan zeenatu ba karamin tafasa zuciyarsa yakeyi ba

Gauran numfashi Yaja, tare da ɗan jinjina kansa Yana huci kamar mayunwacin zaki ya dubi hajiya layla da tai masa ƙerere kamar zata rufesa da bugu

 A fakaice taga Ya sakar mata wani shu'umin murmushi har saida taji gabanta Ya faɗi 

Sassauta fushin fuskarsa Yayi"naji zan buɗe ƙofar, ki bani hanya na wuce" matsawa tayi idanunta akan fuskarshi Ya nufi kofar dakin benazir


Yana ƙarasawa bakin ƙofar, Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa, turata yayi wani iko na Allah sai ga ƙofar ta buɗe

Kallon Juna Alhaji ubaid da Hajiya layla sukai, abun da daure kai tun jiya suke gabzar kofar donta buɗe babu wanda bai jaraba karfinsa ba amma duk abanza ko motsi batayi amma shi daga turawa ta buɗe wani irin ƙarfi ne da shi? Basu tsaya dogon tunani ba, jiki na 6ari suka nufi ɗakin zeenatu da gudu ta rigasu faɗawa a ciki.


Shugarsu keda wuya kowan nan su Yaci burki, Abun da suka gani Yayi matuƙar ɗaga hankulansu, kamar matatta haka suka hangota kwance kan floor rabin jikin ta a cikin toilet dake a buɗe, kamar irin tayi gudu ta kife awurin har kanta Ya daku goshin ta Ya fashe 


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji!"un"! hajiya layla ce ta zagba salati tana tafa hannayenta, zeenatu da ta gama ruɗewa agaban benazir ta zube bisa gwiwowinta, takai hannu tana tatta6ata Aunty benazir! Meke damunki dan Allah ki tashi inna lillahi..mami daddy ku ce ta tashi dan Allah....


da sauri Alhaji Ubaid Yaje Ya ɗago da ita, jikinta duk Ya saki ya ɗauko ta da hannu biyu ya kwantar da ita akan gadon ta, sumar kanta duk Ta yamutse 


Fita hajiya layla tayi jim kaɗan ta dawo da robar ruwa ta buɗe murfin ta kur6i ruwan tare da furzar da shi kan fuskar benazir


Ruwan na dura tayi wata irin zabura tana ambaton sunan taj ... adai dai lokacin shureim Ya shigo dakin ganin su tsaitsaye bakin gadon ta yasa shi saurin karasawa

Tunkafin yayi magana Hajiya layla tace"shureim ka gani ko? Abun da nake gudu kenan! bansan ya akai ta faɗi kasa daga cikin toilet, kanta Ya bugu..."


Hankalinsa atashe Yake kallon Benazir yatsun hannunta sai kerma suke, ta runtse ido tana sambatu kwata kwata bata acikin hayyacin ta 

Zeenatu duk ta damu, Hannunta ruke dana benazir sai faman shesshekar kuka take

"Ya akai kofar ta buɗe"? 

"Uncle din ku ne Ya buɗe kofar," ta bashi amsa ataikaice, Alhaji ubaid Tuni Ya fuce Yabi Alhaji musa don Ya fada masa halin da benazir take ciki


A lokacin Har Ya koma Part dinsa, sallamar Alhaji ubaid ce ta katse sa kamar bazai fito ba, don saida Ya ɗau lokaci har sai da hajiya sara tace da shi baiji ana sallama bane? Tukunna Ya mike cikin takun izza Ya fito daga dakin

"Me kuma zanyi bayan na buɗe ƙofar"? A faɗace Ya faɗa Yana ƙanƙance idanunsa

"Dan Allah ka yi hakuri da abun da layla tayi maka, bata jin maganata naja mata kunne taki bansan ya zanyi da ita ba..." ya mutsa fuska  Alhaji musa yai"naji, Yanzu awani hali benazir din take a ciki? 

 

Kamar mai jin shakkarsa Alhaji ubaid Ya furta"mun sameta akwance kan floor, rabin jikin ta a toilet, kamar faɗuwa tayi don har kanta Ya daku sosai, ta farka sai dai kamar bata a hayyacin ta shiyasa nazo don na sanar dakai...." ta6e la66ansa yai kafin yace"zanyi magana da likita na, zaizo Ya duba ta" godiya ya yi masa kamar zai masa sujjada, komawa cikin dakin yai hajiya sarah dake a zaune kan darduma ta miƙe tana tambayarshi meya faru ne? Ko benazir ta buɗe kofar ne' amsa mata yai da eh jiki na rawa ta fuce daga dakin don taje dubota...


Gaba ɗaya sun hallara a dakin Benazir kowan nan su Ya shiga hali na damuwa, bada jimawa ba Dr Mark Ya shigo gidan, wani basamuden Likita ne irin african american din nan, yadda kasan Jinin Alhaji musa, Fuskarsa babu fara'a, sumar kansa hada kitson zane, tun da Hajiya layla tayi arba da fuskar dr mark kuma taji cewa Alhaji musa ne Ya kira shi don Ya duba lafiyar benazir, tace wallahi bazai ta6a benazir ba, ai kwata kwata ita baiyi mata kama da likita ba, ta dinga surfa bala'e duk yadda alhaji ubaid Yaso Ya shawo kanta shi da su hajiya sarah akan ta bari aduba ta, amma abun Ya faskara a karshe sai dai Alhaji musa Ya sallami likitan Ya tafi ba tare da ya duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ƙara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da abun da layla tayi Alhaji ubaid har Ya gaji da yi mata faɗa, hajiya sarah ce ta basu shawarar su yi gaggawar kaita asibiti don abinciki  laifiyarta, ba su tsaya bata lokaci ba, dr shureim Ya dauko benazir da hannu biyu ya tallabota, suka fito daga falon, A mazaunin baya na motarsa ya shigar da benazir, hajiya layla ta shiga ta rungume ta a jikinta, Alhaji ubaid Ya zauna a front seat tare da shureim, yayin da hajiya sarah ta shiga motarta tare da zeenatu kusan atare motocin suka nufi Gate din gidan, Waɗannan gabza gabzan security officers din suka tari gabansu har sai da suka kira Alhaji musa Ya basu iznin su barsu su fita kafin suka basu hanya

Direct suka nufi Obie International Hospital. 

__________________ANEELERH


Wuraren ƙarfe tara, Aneelerh ta kammala shiryawa cikin abaya tayi rolling, gaba ɗaya ta ƙagara su karasa estate din kamar tayi fiffike haka take ji, fitowa tayi daga bedroom dinta ta nufi dakin mami, bayan tayi sallama mami ta amsa mata ta shiga daga ciki ta gaishe da ita

Kallo ɗaya mami tayi mata ta fahimci kamar bata jin dadi

"Aneelerh baki da lafiyane naga idanunki sunyi ja? 

Kokarin danne damuwarta tayi"mami lafiyata lou, ban samu isasshen bacci jiya ba..."

"Meyasa? Kar dai ace damuwar abun da Ya faru jiya ne"? Girgiza kai tay"a'a mami na tashi yin nafila ne shiyasa banyi bacci da wuri ba..."

"Kunyi waya da su benazir din? Inataso inji ko sun isa gida lafiya"?

"Tun jiya bayan sun tafi nake ta trying layinta baya shiga, har da safen nan saida na kira ba'a ɗaga ba


"To Allah yasa dai Lafiya, Yanzu ina zakije ne naga kin shirya ko hakanan kikai gayu"? 

"Mami wani abun al'ajabi na gani jiya awayar zahra, wanda ya daure min kai shiyasa ma na shigo don in faɗa maki"

"To fa, menene ?

Zaro waya aneelerh tayi daga handbag dinta, ta lalubo layin zahra ta danna mata kira, 

Bugu ɗaya tay picking"zahra Kin gama shiryawa? 

"Eh yanzu zan fito"

"Okey Ki same ni adakin mami dan Allah kada ki bata lokaci"


Bayan ta katse wayar ta dubi mami"gata nan zuwa, abun da zan nuna maki yana awayarta" amsa mata mami tayi da toh cike da zullumin abun da zata gani


Jim kaɗan zahra ta shigo dakin da sallama, Itama ta shiya cikin abaya maroon colour, ta yi rolling, hannun ta ruƙe da wayarta, a bakin gadon mami ta zukunna"ina kwana mami? Kun tashi lafiya"?

"Lafiyalou zahrana, Ina abun da za'a nuna min"?

danna wayar zahra tayi bayan ta buɗo hoton, ta miƙa ma mami wayar tasa hannu ta ƙarba.

kura ma fuskar unaisah ido tayi kamar ta ɗan ruɗe can dai ta miƙe daga kishigiɗan da take ta ɗan kalli fuskar zahra da aneelerh kafin tace"wannan ay hoton Angel ne ko? Yaushe akai wannan hoton? Amma ya akai naga kamar ta ƙara girma anan..." at same time zahra da aneelerh suka saki murmushi saboda sunji dadin yadda mami itama ta gasgata abunda idanunta suka gane mata tunkafin ma su fada mata wa suke hasashen itace


"Mami wannan yarinyar da kike gani sunanta Unaisah, a wurin dinner din prime minister zahra ta dauko hotonta a dakin taron..." da tsantsar mamaki Mami tace"oh wai da ba Angel din bace? Me kama da itace kenan"!

"Mami itace, abunda muke hasashe kenan, zahra ki bata labarin abun da Ya faru a wurin dinner din...." gyara zama zahra tayi gaba daya ta kwashe abun da Ya faru ta sanar da mami

Lamarin yayi mugun daurewa mami kai

Aneelerh ta ƙara da cewa"yanzu haka can estate din zamuje, don mu tabbatar da abun da muke hasashe akan Yarinyar..." jinjina kai mami tayi ita kanta ta goyi bayan suje saboda kamannin Yarinyar dana Angel sun 6aci, bugu da ƙari da taji cewa Yaran tsintattune watakil su dace


"Aneelerh zaiyi wuya ace yarinyar nan ba ita bace, amma dai kuje kawai, Allah Yasa adace" 


"Ameen mami, ki tayamu da addu'a Allah Yasa mu samu ganin ta cikin sauƙi, saboda estate din nasu ba karamin tsarone da shi ba, In har ba wani daga cikin Ahlin su Ya gayyace ka ba to basu bari bakuwar fuska ya shiga....."

"Ita zahra ba suna mutunci da mutanan gidan ba"? Acewar mami

Zahra tace"hajiya saratu ce, nasan indai na tuntu6eta zata taimaka mana, duk da nasan mawuyacin abune tun da yaran a hannun chief owais suke da zama, Ba lallai su bari mu gan su ba.....

Shiru mami tayi kafin tace"to me zai hana ku kira ɗan jaridan nan shima badaga family dinsu Yake ba kuma ay yasan da zancen 6acewar yarinyar tun da har bayanan an tura masa....."

"Har kiran layinsa nayi kwata kwata baya shiga, watakil ko Ya shiga wurin aiki ne..." 

Mami ta gyaɗa kai"shikenan Kuje kawai sai ku kira hajiya saratun, sannan dan Allah idan ba abaku damar shiga ba kada ku takura kanku ku dawo gida kawai inyaso sai ayiwa ɗan iya magana tun da shi ya saba hulda da yan siyasa watakil ku samu hanyar shiga ta wurinsa.....

Amsa mata sukai da toh,

Kafin su miƙe mami tay hanzarin dakatar da su"ku jira mahboob Ya shigo gidan, kwara kuje da namiji"

Zama sukai har saida Mahboob Ya dawo Mami ta sanar da shi komai, ay tun da yaji zancen Unaisah ya gaza samun nutsuwarsa dama yajima da burin su gano yarinyar ba dan komai ba sai don jarin da Yake tunanin zai samu da ita shi uban son banza....


Lokacin da Motarsu ta shararo kan titin obie estate Aneelerh ta jinjinama haduwar wurin kasancewar yau ne na farko da suka fara zuwa, bata gama shan mamakin daular ba sai da Mahboob Yayi parking a gaban tankameman gate din estate din, hankalin su ba karamin tashi yai ba ganin Jami'an dake tsaron shi, sojoji da Jami'an Isod 


Babu wanda Yayi gigin fitowa daga cikin motar, Mahboob Yace"mun kawo kanmu, zahra ni fa tsoron tunkararsu nake Yi Allah, Sai dai wani daga cikin ku Ya ƙarasa driving din...


Yar dariya zahra tayi"bansan Iya shege mahboob dalla ka ƙarasa mana sai kace ba namiji ba"?


"Indai saina tunkari wadannan masu fuskar shanun zan zama namiji to wlh na kwammace ku kirani da sunan hajara...." dariya suka sanya gaba ɗayansu....


Mahboob Fa Ya dage akan bazai karasa da su ba...."


Kwatsam biyu daga cikin sojojin suka tunkaro motarsu hannayensu ruke da bindigogi tuni zufa ta fara wanke fuskar mahboob ganin Yana kokarin tada motar Yasa zahra yin saurin cafke hannunsa"haba mahboob meye haka? Wai dama haka kake da shegen tsoro? Harara Ya galla mata"nifa ba tsoronsu nake ji ba, tashin hankali ne ke banso ..." daƙyar Ya ƙare maganar ganin har sojojin sun ƙaraso gare su


Kwankwasa window glass din motar, ɗaya daga cikin su Yayi da kakkausar murya Ya furta"Put down the glass!" Aneelerh ce tayi karfin halin sauke glass din windown Ya zukunno da kansa Yana binsu da kallo idanunsa jawur 

"Su wanene ku kuma daga Ina?

Murya na rawa zahra tace"wurin Hajiya saratu muka zo...."

"Okey, Ku kirata awaya don ba'a sanar damu zuwanku ba"

jiki na kerma ta amsa mashi da toh, da sauri zahra ta kira Layin hajiya saratu, kusan sau takwas baya shiga, Hankalinsu ba karamin tashi Yayi ba

"Bari na ƙara kiran ziyad watakil shi Ya ɗaga" aneeelrh ta fada yatsun hannunta na kerma ta curo waya ta kira layin ziyad tana ringin baya picking, hankalinsu duk Ya tashi

Ƙasa ƙasa da murya Aneelerh tace"mun shiga uku zahra shima bai ɗaga ba yanzu ya zamuyi"?

Mahboob da ya gama tsorata Yace"mu koma gida kawai shine mafita in ba haka ba wlh wannan mai fuskar shanun tsaf zai Iya bombing motar mu... cikin muryar raɗa yai magana

Zahra tace"wait bari na kira zayn duk da nasan mayucin abune yayi picking..." koda Ta kira layin zayn sau uku baiyi picking ba, A kira na huɗu ne Ya ɗaga muryarsa kamar ta mashayin giya ya furta

"Waye"? Ko sallamarta bai amsa ba

Cike da jin shakkarsa ta furta"zahra ce"

"Wace zahra"? Sarai fa Ya gane muryarta har saving layinta Yana da shi awaya

"Am..zahra wadda mommynka ta haɗa ka da ita, a wurin dinner din prime minister

"Okey nagane, lafiya kika kira"? 

"Munzo estate dinkune an hana mu shiga, sojojin sunce dole sai an basu izni kafin su bari mu shiga

Kafin ta kare maganar Zayn yace"kina hauka ne? Ki rasa wa zaki kira saini? Oh tun yanzu raini Ya fara shiga tsakanina dake! Uban me ma Ya kawo ku estate din? 

Hatta su Aneelerh sai da sukajiyo masifar da yake zazzaga mata

"Dan Allah ka taimaka mana, bamu da wata mafita ne shiyasa na kira ka, wani abu ne mai mahimmanci Ya kawo mu...." kamar zata sanya kuka

"Look, Ku koma inda ku ka fito tun da baku da wani alaƙa damu" Yana ƙare maganar Ya katse kiran, Tashin sense gasu dai agaban estate an hana su shigaa

"Yanzu menene mafita? acewar Aneelerh

"Aunty aneelerh mu hakura kawai tun da kowa yaki ɗaga kiranmu Inyaso ko zuwa gobe sai mu dawo in ba haka ba wahala zamu sha.."

Gurgiza kai aneerlerh tayi"bana jin zan iya komawa gida, sai dai ku tafi kubarni, Ni kawai zanje na roke su su barmu mu shiga ta fada tare da bude car door din Ta fuce da sauri zahra da mahboob suka bi bayanta


Babu irin magiyar da aneelerh batay masu ba, amma suka dage akan dole sai an basu izni, a karshe ma wani fusatacce daga cikin su Ya tsawatar masu akan su koma inda suka fito


Rai a6ace Aneelerh ta dawo jikin motar ta tsaya fuskarta har ta fara zubda gumi, mahboob da zahra sai rokonta suke akan su hakura su tafi gida, amma ta kafe akan ba inda zataje, su kansu sunyi mamakin taurin kan aneelerh abun da bata ta6a yi ba......


Har mami zahra ta kira tayi mata bayanin halin da suke a ciki, tace su ba aneelerh waya su yi magana bayan ta kar6a mami tace tay hakuri su dawo gida kawai inyaso sai ayi ma uncle dan iya magana.." ta amsa mata da toh bayan sunyi sallama da mami, su zahra har sun fara sauke ajiyar zuciya a tunanin su zata koma akarshe sai cewa tayi"ita fa kawai ta amsa ma mami ne, amma fa ba inda zataje sai taga abun da ya turewa buzu naɗi..." kamar su daura hannu akai suyi ihu haka suka ji, sojojin dake zirga zirga sai kallonsu sukeyi su kansu sunyi mamakin taurin kan matar da basu san wacece ita ba, don ma Taci albarkacin Kyan dake gareta ay da tuni sunyi masu korar kare daga Layin.babban abun da Yafi damunta dayasa har ta kafe akan sai sun shiga halin Da benazir ta shiga jiya Ya ɗaga hankalinta da ciwon abun ta kwana jiya tasan mawucin abune in wani abu bai faru da ita ba, wanda yasa har bata neme ta ba kuma in ta kira bata samu


Su zahra har sun gaji da tsayuwa tsawon awanni uku har karfe 1 na rana ta buga, kamar zasu sanya mata kuka fuskokin kowannansu sun Yi jawur


Kiran wayane Ya shigo layin Aneelerh a hanzarce ta duba screen ganin sunan benazir ya bayyana ne Yasa tai gaggawar ɗaga kiran hadi da kara wayar a kunne

Muryarta har rawa take wurin furta"benazir ina kika shiga inata kira baya shiga...." cak ta tsaya da maganar jin muryar Dr shureim

"Aneelerh ba ita bace Shureim ne Ina fata kun tashi lafiya..." tun daga kan yanayin sautin muryarsa ta fuskanci babu lafiya

Gabanta na faɗuwa tace"yaya shurem ina benazir din, tun Jiya bayan kun tafi nake ta jaraba kiran layin ta don inji ko kun isa gida lafiya amma ba'a ɗaga wa...

"Aneeelerh! Kunyi magana jiya da benazir akan mijinta ..."

Murya na rawa tace"eh.. munyi"

"Meyasa kika faɗa mata abun da ya faru da su..."

"Yaya shureim wallahi banyi niyar sanar da ita ba, itace ta matsamin..." gaba daya ta faɗa masa maganar da sukai da benazir har rikicewar da tayi

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..." shine abun da taji Ya furta... Su zahra dake kallon fuskar aneelerh Hankulansu duk sun tashi tunkafin ma suji me suke magana akai

"yaya shureim wani abu Ya faru ne..."

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post