Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 31 by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 31 by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Bayan komawar Unaisah cikin parlour, a dining room ta hango ƴan uwan ta, har sun fara yin breakfast sunyi neman ta har sun gaji ba su ganta ba, suna jin takun tafiyarta gaba ɗaya suka dago suna kallon ta.....

"Sister! Ina kika shiga muna ta neman ki"? Batool ce tayi mata maganar, bata tanka masu ba, sai faman sakin murmushi takeyi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Allah, yau ranta fari fess, cike da zumudi taja kujera ta zauna tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, tasan in har ta sanar da su Azeeza game da zuwan auntyn ta aneelerh ba karamin dadi zasu ji ba saboda tasha basu labarinta agidan kurkukun ƙaddara,

abunda bata sani ba tun da ta zauna suke ta kallon ta

"Aunty ummi Ina kwana.. " wani kallo ummi tabi ta da shi, har saida tasha jinin jikin ta

Kafin ummi ta furta kalma Sajeed Ya riga ta cewa"Sister baki da lafiya ne? ko kinyi kuka ne"? lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza! Kwata kwata ta manta da abun da ya faru daren jiya, saboda murnar zuwan Aunty Anila, maganar sajeed ce ta tuna mata, tuni murnar da take yi ta koma ciki.

"Sister kinyi shiru baki ce komai ba? Meke damunki"? Cike da tashin hankali batool tayi maganar, su Parveen duk sun kura mata ido suna kallonta, jemimah tace"le6enki ma ya kumbura kamar yankan tumatur"

"Unaisah! Lafiyarki kuwa"? Acewar ummi ta faɗa tana kare mata kallon ƙurulla

Adabarbace ta furta"am.. Umm.." sam ta kasa ƙarasa maganar, idanunta azazzare take kallon su.

gani take kamar sun san komai daya faru da ita adaren jiya, da sauri ta miƙe jikinta na kerma tace" aunty ummi babu komai, ba abunda ke damuna, lafiyana lou..." bata ƙare maganar ba, kamar mara gaskiya ta nufi hanyar fita daga dining room din zuciyarta cike fal da tashin hankali

Gaba daya sun lura da tashin hankalin dake akan fuskarta

Deeja na dariya tace"wallahi Allah kumatunta sun kumbura suntum kamar alkubus, wama ya sani ko bugun tsiya akai mata..." bata kare maganar ba, Haris ya toshe bakin ta..

Miƙewa ummi tayi sam hankalin ta bai kwanta da yanayin unaisah ba, miƙewa batool tayi da niyar tabi bayansu, da sauri ummi ta dakatar da ita"ki zauna ku karasa cin abincin, zanji da ita" jiki asanyaye ta amsa mata da toh..

Da sauri ummi ta nufi dakin su Unaisah, tana shiga tajiyo sautin kakarin amanta a toilet kamar zata fasa makoshin ta.

Knocking ƙofar toilet din tay"unaisah ina son magana dake" 

Fitowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye, hannun ta ruke da ɗan pant din ta.

"Meke damunki ne"? tana faman jan numfashi tace"bakomai aunty ummi..." katse ta ummi tayi"kada kiyi min karya, yanayinki ya riga ya nuna baki da koshin lafiya, kawai ki fadamin meke damunki! Idan ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba..." cikin nuna damuwa tayi maganar, shiru tayi jim tana tunanin ko dai ta fada mata watakil ta taimaka mata....

Miƙa mata pant din hannunta tayi, waro ido ummi tayi"me zanyi da shi" matse shi tayi, tana faman noƙe kai tace"jiya da tsakar dare na tashi da matsanancin ciwon mara, kamar bazan rayu ba, bayan na shigo toilet na duba sai naga jini ne ya dawo min"

cike da jin tausayinta ummi ta ruko hannunta suka zauna gefen gadon. 

"Sannu unaisah, wallahi daga gani kin ji jiki ba kaɗan ba, meyasa a daren baki neme ni ba? Ay da na taimaka maki, halan ko magani baki sha ba"?

"Ban shaba ba aunty ummi, saboda naji saukin ciwon, kuma lokacin dana farka da safe banga jinin ba ya dauke! Aunty ummi dama Yana haka"? ɗaga mata kai ummi tay alamar eh"kada hakan ya dameki, nima sometimes yana yi min haka yaje ya dawo, in har bai wuce kwanaki goma shabiyar ba, to still jinin ne, amma da zarar kinji ya dauke duf babu shi sai kiyi wankan tsarki ki cigaba da sallah" ajiyar zuciya unaisah ta sauke, sam tagaza fada mata abun da ya faru jiya.

"Me kike son nuna min a jikin pant din . " cike da jin kunyarta tace"wani abune da nake gani kamar kunu gayanan kyankyamin shi nake ji .."

kiris Ya rage ummi ta fashe da dariya ganin yadda ta kwa6e fuska tana gwale la66anta.

"Nuna min in gani .." buɗe mata pant din tayi.

Shiru ummi tayi jim alamar tana nazartar abunda ta gani, tabbas sperm ne amma meya kawo shi? Cos Bata tunanin unaisah ta fara feelings...rayawa tayi aranta watakil ba abun da take tunani ba ne

"Unaisah, dole fa sai kinyi takatsantsan, kamar yadda nayi maki bayani zan ƙara jan kunnanki, daga yanzu kada ki kuskura ki ƙara ba wani namiji damar da zai ta6a jikin ki, ko da ruƙe hannunki ne! In ba haka ba ke zakija ma kanki zunubi, saboda duk wasu hukunce hukunce na musulunci sun hauki, Idan kika aikata mai kyau za'a rubutaki, haka zalika idan kika aikata zunubi za'a rubuta maki.  .."nan dai tayi mata takaitaccen bayanin dalilin dake kawo hakan dallah dallah yadda tasan zata fahimta, hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba.

"Kuma idan kika bari Namiji yana wasa dake yana tattabaki, you can get pregnant, a yadda kike ƙaramar nan har ranki zaki iya rasa wa...." ummi bata kare maganar ba Unaisah ta daura hannayenta biyu akai la66anta na kerma ta furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." da biyu ummi ta fadi hakan saboda taja mata kunne.

Tayi mamakin ganin Yadda jikinta ke kerma, da gudu ta fada toilet taja kofa ta datse.. " lamarin ya daurewa ummi kai, arude ta mike tana kwala mata kira"unaisah! Unaisah? Lafiyarki kuwa? Meya faru? ko dai maganar dana fada ce? To meye na damuwa"? Shiru bata amsa ba, bugun kofar ummi ta dinga yi kamar zata balle ta"ki bude min kofa, keda baki jira kin karasa jin me zance ba, meye na tada hankali kamar baki da gaskiya"? Ta faɗa tana kumshe dariya a bakinta saboda ta bata dariya.

"Unaisah, ki fito muyi magana, watakil baki fahimci me nake nufi ba, zan yi maki bayani..." cikin disasshiyar murya ta furta"aunty ummi ki tafi dan Allah, cikina ne Ya katsa, idan na gama zan same ki a daki muyi magana" ajiyar zuciya ta sauke"shikenan zan jiraki" 

Sai da taji alamun ummi ta fita daga dakin, kafin ta fito fuskarta sharkaf da hawaye baiwar Allah, hankalinta yayi matuƙar tashi, ta raza da jin kalaman ummi, fargabanta kada ta samu ciki!

Wani irin ciwon kaine Ya farmata, ga wani bacci da ta fara ji mai hade da kasala, Pant din da ta bari kan floor ta ɗauko ta koma toilet din,

Wankan tsarki tayi tare da alwala, daga bisani ta fito sanye da towel, da wata irin kasala ta dauko wasu kayan tasa tare da hijab ta zura a jikin ta.

Bayan ta kammala sallah ta zauna kan darduma ta ɗaga hannayenta tana addu'a hawaye na sintiri kan kuncinta, ko da ta gama bata motsa daga kan dardumar ba.

Bakomai ne Ya faɗo mata aranta ba face Danish, ko ya ci abin ci? taga bata ganshi a dining ba, har cikin ranta ta damu da shi, bata son yana ke6e kan shi a ɗaki, batasan meke damunshi ba...

"Sister dina!" muryar batool ce ta katse zancen zucinta, da sauri ta mike tare da juyawa ta kalle ta.., sam babu walwala atare da ita, duk ta damu da yar uwartata

"Dan Allah ki fadamin meke damunki" ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta

"Calm down your mind! Ni Ba abunda ke damuna, lafiyana lou, ciwon ciki nayi jira da daddare naci wahala sister, amma yanzu da sauki jikin nawa..." huggin dinta Batool tayi sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.

"Ni kadai na kwana jiya adaki"

tausayinta ne Ya kara kama Batool

"Da na sani jiya na tayaki kwana, amma kodan saboda ke zan dawo kwana dakin nan"

Murmushi unaisah tayi"kada ki damu,  ay naji sauki ma"

Kallon dakin Batool tayi"duk yayi datti bari na taimaka maki"

"Nagode sister," ta fada tare da zama kan mirror chair tana jiran batool ta kammala gyaran.

"Sister an kaiwa danish abinci a dakin sa"?

"Eh, Haris Ya kai ma shi, ni bansan meke damun shi ba, kema kin lura da yanayin shi naƙin shiga cikin mu"? Ta faɗa a yayin da takai hannu tajanyo zanin gadon da yayi uban squeezing kamar an ƙwatoshi daga bakin kura.

"Batool na lura, abun yana damu na, nayi masa faɗa yaƙi dainawa to ya zanyi da shi? ta faɗa da damuwa akan fuskarta"ko da yake halinsa ne ko a prison bai fiye shiga cikin mu ba, yafi son yaganshi kwance kan gado" daurewa kawai takeyi sam bata son batool ta fahimci halin da take a ciki.

Adai dai lokacin Batool ta fara kakka6e zanin gadon, Kwatsam ba zato ba tsammani unaisah ta hango zoben da ya faɗo ta cikin bedsheet din..saukowa tayi daga kan kujerar, ta nufi inda Yake ta zuƙunna tana kallon  shi, zoben azurfa ne sai kyalli yake a hankali tasa yatsanta daya ta ɗago da zoben, hankalin batool kwata kwata baya akanta, sai surutu takeyi mata....

Ƙura ido tayi sosai akan zoben, was wasi ta fara yi kamar wanda prime minister ya ba danish❗

Anya kuwa shi ne?❓ kokwanto ta shiga yi, tayaya akai zoben ya shigo dakin su idan na shi ne ...? yunkurawa tayi a sukwane ta mike, batare da sanin batool ba, ta fuce daga dakin.

"Sister jiya kafin mu kwanta aunty ummi ta kunna min kallo a laptop din ta...." dakatawa tayi da yin maganar ganin babu kowa adakin.

"Unaisah! Unaisah! "ranta ne Ya bata kodai ta shiga toilet, hakan yasa taci gaba da gyara mata dakin......."

________________________________✍️

Prisoners shield💔

Fitowa yai daga toilet, jikinshi a sanye da bathrobe, baijima da tashi daga bacci ba Ya shiga wanka, yayi wani fresh dashi, sumar kanshi ta lullu6e bayan shi.

Walking slowly Ya nufi dressing mirror, zuciyarshi cike fal da tunanin Angel dinsa, yayi maraicin ganin ta idanunsa sun kwaɗaita da son ganin ta, tun safe baici komai ba, abincin da haris ya kawo mashi yana nan ajiye kan table ko buɗesa baiyi ba.

Har ya yunkura zai zauna kan mirror chair, sautin knocking din kofar Ya dakatar da shi . ....

Cike da zumudi Ya nufi kofar, fatan shi Allah Yasa Angel dinsa ce,

Buɗe ƙofar yayi a hankali, tun daga kasa Ya fara kallon ta, ko takalma babu a kafarta kamar an korota,

Gown din jikinta tayi mashi kyau sauke idanunsa yayi akan fuskarta har saida gaban shi Ya faɗi, ganin yadda ta kumbura gashi babu fara'a ko kaɗan ta haɗe rai, ido cikin ido suke kallon juna har na tsawon mintuna biyar kafin sanyayyar muryarshi ta katse mata shirun ta

"Mu shiga ciki" yayi mamakin ganin batayi mashi musu ba, ta nufi ciki da sauri yabi bayanta, a tsakiyar dakin suka dakata 

"Meke damunki? Idanunki sun kumbura kamar kinyi kuka, faɗamin waya ta6a min ke"

Lumshe idanunta tayi kafin ta buɗe su a hankali.

Takawa tayi har zuwa gabanshi ta tsaya suka fuskanci juna

"My man, Ina zoben da prime minister Ya baka"? Cike da fargaba Ta furta maganar ita kanta tsoron amsar da zai bata take ji saboda bata son zargin da take yi ya tabbata.

da sauri Danish Ya ɗago da yatsun hannun shi Ya kallesu kwata kwata babu zobe

aruɗe ya furta"ban gan shi ba, bansan a ina ya faɗi ba, bari na duba toilet watakil na manta shi a ciki"

 Juyawa yayi da sauri ya nufi toilet ya shige ciki.

 tana atsaye cikin jin kunar rai, take kallon shi har ya 6ace ma ganinta, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshinta, hankalin ta yayi mugun tashi, zuciyarta ta karaya jikinta yayi sanyi, ta gaza yarda da abunda take zargi!!

dagaske danish ne ya aikata mata rashin imanin nan? babu tausayi babu imani Yana ganin tana fama da azabar radadin ciwo ahaka Yayi abun da yakeso yayi? Tunawa tayi da lokacin daya wurgar da ita kan gado, Ya sa hannu Ya hambareta har kanta Ya daki pillow, abun ya tsaya mata aranta.

Fitowa yayi daga toilet din, ya ɗago suka hada ido, wani irin faduwa gaban shi yayi ganin kallon tuhuman da take jefa mashi, tuni yasha jinin jikin shi

"My man, kaga zoben"? La66anta na kerma ta furta maganar

Girgiza mata kai yayi"ban gan shi ba, bansan a ina Ya faɗi ba..."

Murmushin takaici ta sakar mashi, kafin tace"Ni na ganshi"! da mamaki Ya kalle ta, hannu ta zura cikin aljihun gown din, ta zaro zoben ta miƙa mashi

"A ina kika gan shi"? ya faɗa tare da matsowa kusa da ita, ya miƙa hannu zai karba, daddagewa tayi da iya karfinta na karshe ta ware yatsu biyar ta wanka mashi zazzafan mari kan kun cin shi, tashin hankalin da ba asaka mashi rana! lamarin ya gigita shi da sauri ya dafe kun shi, jikinsa na 6ari ya ɗago amatuƙar ruɗe ya kalli fuskarta...la66ansa na kerma ya furta"my.. Angel? Kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kika mara"?

Harara ta watsa mashi da kakkausar murya ta furta"idan akwai abun da yafi mari zanyi maka shi! Mugu Azzalumi, fasiki ɗan iska... " waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata fado ƙasa He was completely confused

"Danish me nayi maka dana cancanci haka daga gareka? Danish kaida kanka? Sai yanzu na gane dalilin dayasa ka tsareni jiya akan in faɗa maka idan na fara period, dama abunda kake jira kenan, Ina fata yanzu hankalin ka Ya kwanta, tunda ka samu abunda kakeso ...." rushewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai, bawan Allah Yama rasa bakin magana, har yanzu baisan kan me take magana ba, ko kaɗan baiji zafin marin da tayi mashi na, babban tashin hankalin shi miya faru da ita a daren jiya❓

"Kiyi min bayanin meya faru dake"? Tsawa ta daka mashi kamar zata rufe shi da bugu tace"kana nufin kamanta abunda kayi min? Saboda ba damuwarka bace in rayu ko in mutu ko"? Ta fada tana cije la66anta da hawaye suka jiƙa su.

"Idan ka manta bari na tuna maka, jiya ka shiga dakinmu da daddare...." zayyana mashi komai tayi tunkafin ta karasa gabansa yayi wani irin mugun bugu na tashin hankali, miƙa mashi zoben tayi"a jikin zanin gadonmu na tsince shi, ina fata yanzu ka tuna komai....."

Runtse idanunshi yayi, wani irin ƙunci yaji aran shi, jikin shi ya hau yin kakarwa kamar wanda Sanyi ya kama . shirun da yayi ne ya ƙara tabbatar mata da zarginta akanshi.....amsar shi kawai take jira.. Duk da bata bukatar wannan

"Bani bane! Bazan Iya cutar dake ba Angel! bansan ya akai zobe na Yaje dakin ku ba..." 

wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wlh yafi ta jin radadin abunda akai mata, yaji zafi kamar ya fasa ihu! Wai Angel dinsa ce wani yayi ma wannan aika aikar?

"Danish baka ta6a min karya ba sai yau, baka da wata hujja da zaka kare kanka awurina, zoben ka ba ƙafa gare shi ba, balle kace shi yakai kan shi dakina...Danish meyasa kayi min haka? Ko amafarki ban ta6a tunanin zakai min haka ba? A zato na kai garkuwane agareni mai bani kariya a duk lokacin da wani yayi yunkurin cutar dani sai gashi kai da kanka ka cutar dani, saboda idonka Ya makance burinka kawai ka samu abunda kake so ko"?

 Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya saboda wani irin sara masa da yai, ƙafafunsa sungaza daukarsa baisan sa'adda Ya zube kan gwiwowinsa ba.

Ya rurruƙe ƙafafunta da hannayen shi, hawaye na fita ya furta"Unaish ki yarda dani! Ban ta6a maki karya ba, bani bane! Bansan wanene yayi maki aika aikar nan ba! Garkuwarki bazai ta6a cutar dake ba, ni aikina shine baki kariya kamar yadda kika faɗa" ya faɗa yana fitar da huci mai zafin gaske 

"ki tausayama rayuwata, kada ki yanke min hukunci akan laifin da bani na aikata ba! nayi maki alkawarin zan gano koma wanene yayi miki hakan ..." cikin rauni na murya ya ƙare maganar, yana kallon cikin idanunta.

cike da jin tsanar shi ta sa kafa ta buge hannayenshi daya ruke kafarta da su, ta soma ja da baya tana fadin"wallahi bana son ganinka! Ka fita araina Danish! Na tsaneka! Ka 6ata komai, kullum burina in faranta maka rai ashe kai ba haka bane awurinka, abin da baka sani ba ni nema nake na nema mana hanyar da zamu mallaki juna na har iya tsawon rayuwarmu, sai dai kash gajen hakurin ka da son zuciyarka sun ja maka

wurga mashi zoben tayi kan kirjin shi, da gudu ta juya ta fuce daga dakin.

Jiki amace ya kwanta kan floor,  hawaye suka cigaba da sintiri kan kuncinshi, ga wani azababben ciwon kai da yake ji, tuni zazza6i Ya lullu6e jikin shi, ɗaukar zoben yayi a hannunshi Ya kura mashi ido yana kallon shi, ya rasa ya akai zoben yaje dakin su?wa ya kai shi? Wanene Ya cutar mashi da Angel dinsa? 

 sambatu ya fara yi"bani bane! Bazan iya cutar dake ba! Ni garkuwa ne agareki mai baki kariya, kada ki juya min baya, bana jin zan iya  rayuwa batare dake ba, Angel kada ki fushi dani bani bane❗❗❗

Gaba ɗaya kalamansa acikin kunnanta, tana a durkushe bakin kofar dakinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin lamarin take kamar a mafarki! wai Danish dinta ne yayi mata haka? Wlh ya karya mata zuciya! Ya kunsa mata kiyayyarshi, duk irin burin da taci na son ganin sun rayu a karkashin inuwa ɗaya ya ruguza komai....

Jin motsin mutun yasa tayi saurin share hawayen ta, jiki ba kwari ta miƙe daddynta ta hango yana shigowa, da alama Ita Yake nema...

Sai da ta fara daidaita nutsuwarta kafin ta sauko down ta nufe shi, sam baiji takun tafiyarta ba, sai dai Yaji ta faɗa kan bayan shi ta rungumeshi, bata san sa'adda ta sake fashewa da wani kukan ba, duk yadda taso ta shanye shi takasa har saida Taj yaji, gaba daya yabi ya rikice, kafin yayi yunkurin ruko ta da gudu tabar jikin shi, ta nufi dakinsu ta shiga, a lokacin Batool ta jima da fita, kan gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita.

da gudu Taj Ya faɗo dakin, Ya hau har saman gadon, jikin shi har kerma yakeyi tsabar rudu da tashin hankali, janyota yayi da karfi ya rungumeta sosai a kirjin shi, muryar shi na rawa ya furta

"Unaisah! my Angel! Meya faru? Waya ta6a mun ke? baki da lafiya ne? 

 fuskarta tayi sharkaf da hawaye, hatta temperature din jikinta ya dauki zafi rau.

"My Angel meke damunki? Dan Allah kiyi min bayani? Ko baki da lafiyane?" sai da tayi kukan mai isarta kafin ta raba jikinta daga nashi ta sauko daga kan gadon, ta nufi toilet ta shige, jim kaɗan ta fito da alamun ruwa akan fuskarta...tsayawa tayi nesa da shi tana faman sauke ajiyar zuciya.

"Zonan Unaisah" Ya kirata fuskarshi babu walwala, kamar babu laka a jikin ta ta karasa tare da zukunnawa ta zauna kasan gadon, saukowa yayi ya zauna suka fuskanci juna

Ya ruko hannayenta a cikin nashi"fada min meke damunki? Meyasa kike kuka? 

Shiru tayi jimm har cikin ranta bata jin zata iya tona mashi asiri, koda zuciyarta zata buga saboda bakin cikinsa, ta ƙwammace tabar abun aranta.

"daddy dan Allah kada ka tambayeni meke damuna, ka tayani da addu'a, in sha Allah zanji sauƙi.."

 ta faɗa tare kwantar da kanta saman kafadarshi, ɗaura hannun shi yayi akan bayanta yana dan shafa shi cikin sigar lallashi yace"kiyi hakuri duk da bansan meke damunki ba, tun da kin nuna bakison in tambayeki dole in hakura, amma dan Allah kada ki sanya damuwa aranki! Ki kai kukan ki wurin Allah, Nima zan tayaki da addu'a in sha Allah.." lumshe idanunta tayi har yanzu bata daina jin kukan ba...

"Daddy, Inaso nayi nesa da gidan nan, na wani lokaci..." tun da yaji wannan maganar Ya fahimci akwai wanda Ya 6ata mata rai, a sannu zai gano koma wanene.

dagowa tayi a hankali suka kalli juna, idanunta sun ƙanƙance sun kaɗa jawur saboda kukan da ta sha..

"Daddy, Ka kaini part dinka, in zauna gurin Aunty danejo, ko kuma ka kaini wurin aunty Aneelerh dan Allah" marairaice mashi fuska tayi kamar zata fashe da  kuka, kallonta kawai yakeyi gwanin bantausayi, arayuwarshi yatsani duk wani abu da zai ta6a lafiyar yarsa, bai son damuwarta.

"Daddy kayi shiru bakace komai ba"?

Numfasawa yayi kafin Ya furta"magana nakeso nayi dake, shiyasa na shigo gidan nan, sai kuma na taras da abunda Ya 6ata min raina..."

"Ka yi hakuri daddy, na daina kukan ay, ba zan kara sanya damuwa araina ba..." ta faɗa tare da ƙaƙaro murmushi akan fuskarta.

Kwantar da ita ya kuma yi ajikin shi don ta samu relief din abunda ke damun ta..

Calmly ya fara zayyana mata maganar da suka tattauna da su chief

"Ita mara lafiyan yar uwarsa ce, kuma kawar auntynki Aneelerh, tana a kwance gadon asibiti kwata kwata bata acikin hayyacinta tun lokacin data rasa yarta da mijin ta, likita yace idan har ba asamo yarinyar da zata iya acting kamar yartaba, to zata rasa ranta ne..." ɗagowa Unaisah tayi a hankali ta kalle shi da alama taji tausayin matar.

"Muna so kije a matsayinta Unaisah, nasan zaki Iya!"

"Daddy na amince muje asibitin, dama najima ina neman hanyar da zan kyautatama chief, na ji dadi data kasance yar uwar shi, Allah yasa in zama silar samun warakarta .." murmushi taj yayi

"Ameen, amma akwai abunda nakeso in ja maki kunne akai! Idan har muka kaiki asibitin kada ki kuskura ki faɗa ma wani ina raye! Ko ki bayyana wacece ke! Saboda har yanzu rayuwarmu tana acikin hatsari akwai masu bibiyarmu unaisah! Waɗanda suka kashe uzair zasu iya kashe ni idan sukaji ina raye!" cikin matsananciyar damuwa yayi mata maganar donta dauki abun serious...girgiza kai tayi"daddy bazan bari kowa ya sani ba, saboda bana so na rasa ka"

"Koda wani ya nuna ya sanki ki ce bake bace, kinji"? Ɗaga mashi kai tayi...

"Ko kinsan mutun kika ganshi kada ki tanka mashi ko ki nuna kin sanshi, tun da haryanzu bamu san wanene ya sadaukar dake ba!" 

Gefen fuskarta yashafa da hannun shi, ki fara shiri zuwa anjima da daddare zamu tafi" ta amsa mashi da toh, jan ta da fira ya farayi duk don ya faranta mata rai ko ta manta damuwar da take a ciki.......

______________________________✍️

wuraren ƙarfe biyar, A jere motocin su Alhaji musa suka kunno kai cikin asibitin, A parking space suka dakata,  da sauri body guard din dake driving din sa ya fito ya bude mashi mota, gently ya fito, ya ɗauki wankan shadda mai ɗaukar ido, fuskarsa na sanye da mask, Iya idanunsa ne kadai zaka Iya gani, fitowa Alhaji ubaid Yayi daga motar, a tare suka nufi ciki, wani irin farin jini ne da shi duk inda ya gifta satar kallon shi ake, daga nurses har drs din kai harma da visitors.

Duk da ya 6oye fuskarsa hakan bai hana wasu gane shi ba, cikin girmamawa likitoci ke gaishe da shi wasu kamar zasu durkusa ƙasa, cikin isa Yake ɗaga masu hannu batare daya furta magana ba....

Kafin su karasa ga medical room din, suka hango dr shureim tare da Aneelerh da zahra atsaye suna tattaunawa....

"Shureim"! Alhaji ubaid ne Ya kira sunan shi, kusan atare zahra da Aneelerh suka dago tare da kallon su...Rass Aneeleeh taji gabanta ya faɗi ba ita ba hatta zahra saida taji wannan yanayin datayi tozali da Alhaji musa, Yayi matukar jan hankulansu...

Ƙura mashi ido Anila tayi, a lokacin dr shureim Ya karasa wurin su, kamar taso ta gane wanene, sai ta ga kamar uncle din benazir, bazata ta6a mantawa da ɗan tahalikin nan ba, saboda kyautatawar da yayi masu tun da kuruciyarsu, kafin daga baya lokacin daya taka matsayi mai girma gaba ɗaya suka daina jin duriyarshi.

"Aunty Aneelerh wanene wannan"? 

"Kamar uncle din benazir, banga fuskar dakyau ba amma inaji araina shi ne. ." bata ƙare maganar ba, su Alhaji ubaid suka karaso wurinsu, atare suka haɗa baki wurin gaishe da su

Alhaji ubaid ne kadai Ya amsa masu, da fara'a Yace"Aneelerh sannunku da kokari, Ya mai jikin"? Ita yake yi ma magana amma hankalin ta na akan Alhaji musa ya wani kau da ido kamar bai gan su ba.

"Alhamdulillah daddy, Jikin nata da sauki ba kamar jiya ba"

"Aneelerh ga Uncle musa ku gaisa ko baki gane shi ba..." dr shureim ne ya faɗa 

Murmushin yake ta saki"ina wuni..." ƙasa ƙasa da murya ya furta"lafiya..." zahra na gaishe shi ko kallo bata ishe shi ba, Ya wuce Ya nufi dakin Alhaji ubaid yabi bayan shi.

jinjina kai zahra tayi aranta ta ayyana wannan wani irin mutunne? daga gani Yana da girman kai da izza.

"Shureim ko dai Ya manta dani ne? Naga kamar bai gane ni ba, duk sai naji ba dadi..."

Shiru shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin halin ko'in kulan da alhaji musa Ya nuna ma Aneelerh ba bayan ya santa farin sani...

Murmushi ya ɗanyi kafin Yace"bana tunanin ya ganeki"

Ajiyar zuciya taɗan sauke kafin suka cigaba da magana game da yarinyar da suke jiran zuwanta anjima...

Lokacin da su Alhaji musa suka shiga dakin, Hajiya layla tana azaune kan prayer mat, hannunta ruƙe da cazbaha, kamshin turaren Alhaji musa ne Ya fara dakar hancinta kafin sallamarsu ta ja hankalin ta ga duban su, kamar taga wani mugun abu haka ta zabura ta mike tana kallon shi cike da mamakin ganin shi, saboda bata tsammanci zaizo ba tun da bai damu da benazir ba....

Tunda ya shigo idonshi na akan Benazir wadda ke kwance ta lumshe idanunta sai sambatu takeyi ƙasa ƙasa, kai tsaye ya nufi gaban gadon Ya zauna kan chair din dake fuskantarta

"Sannu daughter, Ya jikin naki"? Ya faɗa tare dakai hannu Ya shafa goshin ta, a firgice ta bude ido tana kallon shi, la66anta na kerma ta furta"Uncle! Daddy!  ina babyna? Ina Angel dina, dan Allah ku nemo min taj ya kawo min babyna"

Lumshe ido Alhaji musa yai kafin a hankali Ya furta"calm down your mind, zansa a nemo maki ita, but ki fara kwantar da hankalin ki" rurruke hannunshi tayi acikin nata"dan Allah ku kawo min ƴata da mijina, uncle ku taimaka min kada na mutu ban gansu ba...." 

tun shigowar shi bai dago Ya kalli hajiya layla ba, kamar babu ita adakin, wato yafi karfin yayi mata magana.

Ita ko tayi tsaye tana kallon ikon Allah,  sam batayi farin cikin zuwan shi ba, gani take kamar ba alkhairi ne Ya kawo shi ba...

Gyaran murya Alhaji ubaid yayi mata

"Layla ya jikin nata"?

"Da sauki, mun samu taci abinci har wanka na taimaka mata tayi"

"Ya ake ciki game da yarinyar da Aneelerh zata kawo"?

"Sai zuwa dare zata zo asibitin"

"Allah Ya kawota lafiya, amma iyayenta ba su nemi komai ba"? 

"Sai dai sunzo zamuji"

ajiyar zuciya yadan sauke

"Ba kiga musa ba ne? Naga baku gaisa ba" ya fada tare da nuna shi da hannu...

Harara ta watsa mashi kafin tace"ay shi yakamata ya fara yi min magana bani ba, sai kace dai Nina tursasa mashi yazo asibitin"? 

gaba daya maganganun da suke tattaunawa akan kunnansa ko ajikinsa.

Sun ɗan jima kafin ya miƙe Alhaji ubaid Yabi bayansa suka fito daga dakin

Sai da suka fara zuwa office din likitan dake kula da ita don jin karin bayani dangane da lafiyarta, kafin suka fuce daga asibitin.

_________________________________✍️

Wunin ranar Danish bai leƙo ko kofar dakin sa ba, babu wanda Yasan halin da yake a ciki, kamar yadda ita ma ta killace kanta adaki, wuni tayi kudundune cikin bargo lokacin sallah kaɗai ke tada ta, tuni zazza6i ya lullu6eta jikin ta har kerma yakeyi kamar zatai hauka saboda azabar raɗaɗin da zuciyarta keyi mata, tayi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, danish ya dasa mata tsanar shi a zuciyarta, ko sunan shi bata son ambato, hauka tadinga tana bubbuga mattress da hannayenta kamar yar dambe duk ta hargitse dakin a karshe ta fashe da kuka tana fadin"ka karya min zuciya my man, na tsane ka! Bana son ka! Bana son ganin ka! Ban ta6a tsammanin zaka iya cutar da rayuwata ba! Meyasa kayi min haka? ..." tajima tana haukanta ita kadai kamar zata zauce.

Wuraren ƙarfe takwas na dare, taj ya kirata awaya yace ta shirya ta same su a parking spot, jiki na rawa na shiga toilet, dama a kagare take data bar gidan kodan ta nisanta da shi, watakil ta samu relief din radadin da heart dinta keyi mata.

Bayan ta fito shaf shaf ta shirya cikin abaya, ta dauko kaya kala uku ta cusa a backpack dinta, ta goya jakar abayanta, ta zura takalmanta kafin ta dauki wayarta, babu wanda Yasan da zancen tafiyarta, harta fuce daga gidan.....

Cikin sauri take tafiya kamar zatayi tuntu6e, a parking space ta hango daddynta tsaye, ya sanya face mask a fuskarshi

Kallo ɗaya yayi mata ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa atattare da ita

Baisan ya zaiyi da ita ba, taki fada masa damuwarta, buɗe mata murfin motar yayi, wani sanyayyan kamshin turarene Ya daki hancinta, nan take ta gane kamshin wanene da sauri ta dago ta kalli daddyn nata

Murmushi ya sakar mata kafin yace"ki shiga mana"

"Wanene a ciki"? Ta jafe mashi tambayar

"Chief ne, tare da shi zamu tafi" jim ta ɗanyi kafin ta kutsa kai ciki, har saida gabanta ya dan fadi lokacin da ta sauke idonta a kanshi, yana daga zaune  ya ɗauki wankan shadda blue sky tayi bala'en yi mashi kyau, laptop dinsa ce akan laps dinsa, ya dan lumshe idanunshi....

Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin wani irin sanyi acikin zuciyarta.

Sai da ta zauna gefen shi kafin ta samu kwarin gwiwar yi mashi sallama tare da gaishe da shi...

Calmly ya amsa mata... 

Nutsuwa tayi idon akan glass din motar da bai karasa rufewa ba, tana iya hangen filin gidan....

"Zamu Iya tafiya" chief ne Ya faɗa, security din dake zaune a driver seat Ya tada motar, A hankali Ya fara driving dinsu, motarsu big guy tana abiye da bayansu su biyu aciki tare da daddynta, sai motar jami'ansu dake abiye da su....

Lokacin da motocin suka haura kan titi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta, ta lumshe idanunta, bakomai take tariyowa ba face abunda Ya faru tsakanin ta da danish, tayi fatan ace mafarkine ba gaske ba..........bata san sa'adda hawaye suka gangaro takan kuncin ta ba, kwata kwata ta manta da chief acikin motar,

Ranta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur, karaf idanunsu suka shiga cikin na juna.....

Daga ita har shi sun kasa sarrafa kansu, wani irin kallo suke bin juna da shi mai wuyar fassaruwa 

Ƙamshin turarenshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba..."

Tsananin tausayinta ne Ya kama shi, har yau yana mai mamakin kananun shekarunta da kuma irin wahalhalun rayuwar da ta fuskanta, shi tunda yataso rayuwarsa baisan menene wahala ko rashi ba.

"I don't want to see your tears..."

*✊DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️* 

*Mu haɗu Jibi, Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post