Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 29 Complete


Health College

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 29 Complete

Novels Elite English

 ✍️



Dafe kirji tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ganin likitan dake kula da benazir ne


"Are you okey"? Daga mashi kai tayi alamar eh,


Ganin tana mashi kallon kamar bata yarda da shi bane yasa shi cewa"zan tashi daga aikine, Na shigo na kara duba lafiyarta ne, kafin na tafi...." murmushin Yaƙe ta sakar mashi"mungode dr, Allah Ya saka da alkhairi, agaida gida" ya amsa mata da toh, harya fuce daga dakin Yana mai mamakin Hajiya layla, abun ya daure masa kai yadda ta fito daga toilet a haukace anya kuwa tana da lafiya"?


Komawa cikin toilet din tayi, sam babu nutsuwa atare da ita, shaf shaf ta ƙarasa alwalar ta fito da sauri ta nufi closet din dakin ta dauko darduma ta shimfiɗa tare da kabbara sallah.

Da zarar taji motsi adakin sai gabanta Ya faɗi, bayan ta ida sallar, ta zauna tayi addu'o'i ta kai kukanta wurin Allah,

Kafin ta mike ta koma kan chair din dake fuskantar gadon benazir ta zauna tana kallon ta, patient gown din dake ajikinta launin light blue tayi mata kyau, A hankali ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta, tuni taji ƙwalla sun cika idanunta.


Idan muka koma bangaren su Aneelerh, bayan komawarsu gida, A falo suka zauna kowa Yana jimamin halin da Benazir take a ciki, Ummi ta fito daga daki hannunta dauke da Baby junaid bawan Allah tunda Mahboob ya dauko shi daga makaranta, Ya dinga kuka Yana ambaton mommynsa, dakyar mami ta samu ta shawo kanshi Har yaci abinci tayi mashi wanka, har bacci Yayi, sauke shi ummi tayi da gudu Ya nufi Aneelerh ya faɗa jikinta Yana kuka, Ta rungune shi tana lallashin shi, dakyar ta shawo kanshi har suka sasanta junansu...


Lokacin da hajiya sara ta shiga falon gidan, kasa yin sallama tayi saboda fargaban hukuncin da Alhaji musa zaiyi mata, Cikin sanɗa ta nufi bedroom din su ko sallama batayi ba, ta shiga ciki,


A kwance ta same shi kan shimfiɗeɗan gadon shi, Ya tada kanshi bisa pillow, zeenatu na arungume da shi, ta daura kanta bisa kirjinsa, daga ita har shi kayan bacci ne a jikin su


Tayi tsammani bacci suke Yi, ajiyar zuciya ta sauke, ta lalla6e ta nufi cikin dakin, ta daura key dinta akan mirror, ta nufi toilet ta shiga, alwala tayo tana kokarin fitowa daga toilet din suka ci karo da shi, wani irin bugu kirjin ta yayi, tuni gumi ya lullu6e fuskarta, la66anta na kerma tace"yanzu na shigo, nayi tunanin bacci kake Yi, fatan na same ka lafiya..." tsare ta da idanunsa yayi masu matukar gigitata, gaba daya yayi mata kwarjini


"Ki faɗa min wani hukunci Ya dace Inyi maki"! Rass taji gabanta Ya fadi, marairaice mashi fuska tayi"am sorry bazan ƙara ba, wallahi bansan na ɗaga maka murya ba, dan Allah Ka yafe min.."

Fuskarshi babu annuri Ya furta"cewa nayi ki fada min wani hukun ci Ya dace nayi maki"?

 Shiru tayi batare da ta furta kalma ba, duk tasha jinin jikinta....fargabanta kada Yace zai turata U.s

Saboda bata son duk wani abu da zai rabata da shi, shiyasa take yi mashi biyayya sau da kafa, duk wani abu da tasan zai bata masa rai, tana kokarin ganin tayi takatsantsan da shi

"Daddy kayi mata hakuri tun da ta gane kuskuranta," muryar zeenatu ce ta ratsa kunnuwansu,

"Kinci sa'a, da yau sai kin yaba ma aya zakin ta" nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata wuce ya sake shan gabanta, a rude ta kalle shi

"Ya jikin benazir din?

"Jikin nata yayi tsauri, kwata kwata bata a hayyacin ta, baiwar Allah tana jin jiki"


"Allah Ya bata lafiya, in sha Allah gobe da safe zanje dubata" har cikin ranta taji dadin jin zaije dubata,

"Allah ya kaimu lafiya.." 

"Kije kiyi sallar, kafin kin kammala zan kira tani ta shirya maki dinner dinki, nasan kina jin yunwa, kin wuni baki ciki komai ba" ya fada tare dakai hannu Ya shafa flat tommy dinta, aruɗe hajiya sarah take kallon shi, kamar ba Alhaji musa ba,yadda kasan badaga bakinshi kalaman suke fitowa ba,

Kamar sakarya haka ta kura mashi ido tana kallon shi, murmushin gefen fuska ya sakar mata, gaba daya ya nemi zautar da ita, dakyar ta samu nutsuwar sanya hijabi ta kabbara sallah,......"

Sallamar su Alhanji ubaid ce ta karaɗe kunnuwansu, da gudu Zeenatu ta diro daga kan gado ta fuce kamar walkiya, tunkafin ta karaso dr shuriem Ya hangota, murmushi ya saki tare da bude mata hannayenshi ta faɗa kan kirjinshi tana dariya

"Yaya shureim sannu da dawowa, naji dadin ganinka, dama ina ta zullumin kada kaki dawowa gida.." bata ƙare maganarba, Alhani ubaid Yayi mata gyaran murya, waro idanu tayi don gaba daya ta manta da shi awurin cike da jin kunyarshi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta

Dariya Alhani ubaid Yayi"zeenatu, meya hanaki yin bacci..." muryarta da yar shagwa6a tace"yaya shureim nake jira ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa

"Sannunku da dawowa, ya mai jikin"?

Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"?

Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba.


wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi.


Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci.


*EX-PRISONERS*


Around ƙarfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta, 

Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet


Murmushi tasaki haɗi da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., ɗaya bayan ɗaya ta fara farkar da su


"Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta miƙe tana ƴan soshe soshe


"Wuce kije daki" ta amsa mata da toh, 

"Praveen ku tashi..." cikin magagin bacci ta buɗe ido bakinta cunkushe da apple din da bata karasa cinyewa ba, bacci yayi awon gaba da ita, miƙa tayi tare da yin hamma ta nufi dakin su, ganin tana tangal tangal kamar zata fadi ne Yasa ummi yin saurin cafko hannunta, a lokacin ta samu hannah ta mike, ta ruko hannayensu a cikin nata har ɗaki takaisu, sai da taga sun kwanta kan gadonsu kafin ta dawo falon

Taci gaba da tada su"sajeed! Naufal ku tashi dan Allah, Mubeen Haris! Javed! Wai baku ji ina magana ne"? da wata irin kasalar bacci kowan nan su Ya mike har kwara mazan da kwarin su, suka nufi bedrooms dinsu


Wurinsu jemimah ta nufa, sun cunkushe kan sofa mai mazaunin mutun biyun yadda kasan kifin gwangwani, hannu biyu tasa ta dauki jemimah, ta daurata a kafadarta, kafin ta sa ɗayan hannun ta ɗago Azeeza, ta daurata a dayar kafadar ta, ahaka ta nufi dakin su, ta kwantar da su kan gadon su, sai da ta kashe masu switch din dakin kafin ta fito ta koma falon,

 "Sarah! Wake up, rubina! Hibba! Pls ku tashi! Mana, Yasmin"! Har ta fara gajiya da tada da su, mikewa sukayi kamar babu laka ajikinsu, raka su tayi bayan sun kwanta ta dawo tana kallon waɗanda suka rage, Eve ce kwance kan rug tare da Deeja..Sai unaisah dake a naɗe kan sofa,

"Deejatun haris, Ta shi muje ki kwanta..." cikin magagin bacci ta fara sambatu tana fadin"wai meye haka ne? Ni ku kyaleni wallahi kada wanda Ya ƙara min magana..." Hannu ummi takai da niyar ta dago da ita, aikuwa ta daddage takai mata naushi a gefen bakin ta, tsabar zafin da ummi taji ne Yasa tayi saurin dafe bakin, ta lalla6a ta koma kan sofa ta zauna tana faman yarfa hannunta, ranta ya 6aci taji haushin naushin da khadeeja tayi mata, hakan yasa ta yanke shawarar barin ta a falon ta kwana, gudin kada ta lahantata garin tada ta daga bacci

Mikewa tayi ta nufi hawwa ta dan bubbuga kafafunta, cikin sa'a ta farka

"Ki je daki ki kwanta" amsa wa tayi da toh, bayan tafiyar hawwa ummi ta nufi unaisah

Bata tada ta daga baccin ba, daukarta tayi akan kafadarta, ta nufi bedroom dinsu da ita, tana shiga ta kwantar da ita akan gadonsu, ta kashe mata switch dakin,

Bayan ta fito falon, Ko kallon inda deeja take akwance batayi ba, don ranta Ya 6aci, kaitsaye ta nufi hanyar komawa dakinta, har ta kusa shiga taci karo da Batool kwance kan matattakar benan sai faman sharar baccinta take Yi

da alama zamewa tayi awurin ta faɗi cikin magagin watakil tayi azan gadone shiyasa taci gaba da baccin ta

Ɗaukarta ummi tayi da hannu biyu ta cucci6eta, ta haura da ita upstairs, bayan ta shiga dakin, ta kwantar da ita kan gadon su kafin itama ta haye ta kwanta tare da rungumota a jikin ta....



*❤‍🩹UNAISAH ANGEL💔*


Around ƙarfe 1:30 na dare, ta farka da matsanancin ciwon mara mai azababben zafi, hannayenta dake kerma ta ɗaura su akan cikinta, sai faman murzarshi take yi, sai faman yin birgima take akan gadon, daƙyar ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur da su, cikin mawuyacin hali ta kai hannu jikin bedside lamp ta kunna fitilar haske ya gaure zagayen gadon da take, wani irin gumi ke tsastsafowa ta jikin ta, hatta pajama din dake a jikin ta sun manne ma fatarta,

Yunƙurawa tayi daƙyar ta sauko daga kan gado ta shiga toilet, ta haye kan toilet seat, tayi fitsari anan taga jinin da ya dawo mata jawur yana gangarowa ta tsakantsakin cinyoyin ta, runtse idanunta tayi da karfi duk irin ɗaukin da take na son ya dawo mata sai da taji abun ya fita ranta saboda raɗaɗin da mararta ke yi mata

Bayan tayi tsarki ta fito, babu wandon  ajikin ta, can ta baro shi a toilet....a gaban drawer chest na wardrobe din kayan su ta zukuna ta buɗe tare da sura hannu ta ɗauko pad daya, ta haɗo da pant, akan mattress ta ɗaura su tana faman sakin nishi kamar mai naƙuda, 

"Can I give you a hand ."! kamar daga sama ta tsinkayi muryar mutun a kunnanta, sai tayi tsammanin gizo muryar shi keyi mata...kwatsam hasken ɗakin ya dauke ɗuff duhu ya gauraye ko'ina, a firgice take kallon duhun daya mamaye idanunta, gashi bata ƙarasa sanya pad din ba, cikin duhu tafara laluban gefen gadon don ta kunna fitar, ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun akan mararta, a matuƙar firgice ta zare gray eyes dinta, muryarta na kerma ta furta"de...deeja? deeja? Shiru ba'a amsa mata ba...tasan su biyu suke kwana dakin shiyasa ta ambaci sunanta, tunani tayi kadai batool ce

"Batool ke ce? Shiru ba amsa,"dan Allah wanene? A tsananin tsorace tayi maganar.

"Daddy...." bata kai ga ƙarasa maganar ba, Taji gaba ɗaya anjayota, ta faɗa kan kirjin shi, farat ɗaya ta gane koma wanene namiji ne kuma kakkarfa, Kware baki tayi zata fasa ihu yayi saurin haɗe bakinsu guri guda, jikinta ya fara kerma tafara kiciniyar kwace kanta, kamar yar dambe ta dinga ɗuma masa dundun da hannayenta waɗanda ke abayanshi, tayi kuka tayi haukan ko gizau baiyi ba har gartsa mashi cizo tayi wuri uku a kirjinshi amma babu alamun yaji zafinda zai sake ta

Fashewa tayi da matsanancin kuka"wayyo Allah daddy na, Aunty ummi, my man kana ina? Kana gani za'a cutar dani, na shigo uku wayyo Allah..." da iya karfinta na karshe ta bangaje shi gaba ɗaya ta kife kan floor, bata iya ganin komai da rarrafe tana laluban hanyar fita daga ɗakin, ƙafafunta taji ya ruƙo da hannayensa biyu ya ɗago bai direta a ko'ina ba sai akan gadon ta

Ta yunkura zata gudu Ya hambareta da gwiwar hannunsa, kanta ya daki pillow, kafin tayi yunkuri sake mikewa, mutumin ya toshe mata baki da tafin hannunsa gaba daya ya sakar mata karfi, ta yadda ko yatsan hannunta bazata iya motsawa ba, numfashinta dakyar yake fita, wani iri danshi danshi ta fara ji agabanta kamar ana zuƙe jinin dake fita ta farjin ta, runtse idanunta tay zufa ta fara tsastsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, ga wani azababen zafi da matsananciyar kasala da suka rufeta a lokaci ɗaya, ta fara jan numfashi tana nishi, hawaye masu ɗumi suka wanke fuskarta, gaba daya ta zauce ta rasa tunaninta, lamarin kamar a amafarki take jin afkurwarsa, ta kasa ta6uka komai, sunan danish dana daddynta da aunty ummi kadai take iya ambato cikin zuciyarta a karshe raci gaba da ambton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... ❗


Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Shin wanene Yayi ma unaisah wannan aika aikar❓


_____________________________✍️


A zaune Yake kan darduma, Cikin shiga ta farar jallabiya, Hannunsa ruƙe da qur'ani Ya nutsu Yana karanta shi,


"Assalamu alaikum"! Cikin kunnanshi Ya tsinkayi muryar abbansu, sai da yakai aya kafin daura kur'ani kan prayer mat din Ya dago da ita Ya dube shi,

Yana asanye cikin kakin shi, zama yayi daga gefen gadon shi Yana duban fuskar dan nasa dakyau,


"Ina kwana daddy, Kun tashi lafiya"! 


"Meke damunka"? Kai tsaye Ya jefa mashi tambayar,


Sunnar dakai kasa yayi kafin ya furta me ka gani daddy"?


"Abubuwa da dama! Na farko kwata kwata baka acikin nutsuwarka, tun zuwanka Nigeria na lura da akwai wani abu dake damun ka! Bayan haka me ya hana ka komawa bakin aikin ka!?


Shiru yayi ba tare sa ya furta kalma ba, baiso daddynsu Ya fahimci halin da yake aciki ba, saboda baya son Ya ɗaga hankalin shi,


"Kada ka 6oye min komai, duk duniya baka da kamata, kasan tsakanina dakai babu sirri, Idan wani abune ke damunka, ka sanar dani, in sha Allah zan taimaka maka mu sami mafita atare..." Ya faɗa cikin nuna kulawa


Bayajin zai iya 6oye mashi damuwar shi,tun da harya riga daya gano da kan shi, kwara kawai ya fada mashi gaskiya, 

Cikin sanyin murya ya zayyana mashi komai, tun farkon haduwarsu da Benazir, da irin rayuwar da sukai har izuwa rabuwar su..." dagowa yayi idanunshi jawur cike tab da hawaye ya kalli daddyn nasu


"Daddy ka tayani da addu'a, Allah Ya jarabceni da sonta, ko baccin kirki bana iya yi saboda rashin ta atare dani, bansan awani hali take a ciki ba, nayi jiran hajiya laurat shiru har yau bata neme ni ba..., bana jin zan iya barin kasar nan in har ban hadu da ita ba....."


Tsananin tausayin shi ne Ya kama Daddyn nasa, 


"Meyasa baka fada min ba tun farkon zuwan ka"?


"Banyi tunanin yin hakan ba, na bari sai in na hadu da ita sai in sanar dakai..."


Murmushi sir mubarak yayi aranshi yana mai mamakin zaki, mutumin da bai ta6a ganin wata ƴa mace Ya nuna yana son ta ba, Aikinsa kadai Yasa agaba, al'amarin so da girma ya ke...


A hankali Yasa hannu ya zaro wayar shi daga aljihu, ya ɗan daddanata, zaki dake kallon shi bai son me zaiyi ba. 


Kara wayar yayi a kunnansa, kafin Ya furta"Assalamu alaikum mutumina, Ina fata kana lafiya"?

On the other hand muryar mutumin ta amsa masa da cewa"wa'alaikum salam! lafiyalou, Ina fata kaima haka"?

"Alhamdulillah, naji muryarka kamar daga bacci ka tashi .."

"No na jima da tashi, ya iyalin naka"?

"Suna nan lafiya lou...Tambaya ce nake so inyi maka..." gaba daya zaki ya nutsu yana kallon sir mubarak, baisan dawa Yake magana

"Ina sauraronka..."

"Yar wurin Yayanka benazir da ta bace, ta dawo gida ko hanyar yanzu ba labarin ta .."?

"Meyasa ka tambaye ni? 

"Ka fara bani amsar tambayar da nayi maka..."

"Ta dawo gida..." azabure Zaki Ya miƙe tsaye da alamun rudani yake kallon daddyn nashi

"Nagode mutumina, Idan muka hadu zamuyi magana"

"Okey saina jika" katse kiran yayi, fuskarshi dauke da murmushi Ya kalli zaki, zubewa yayi agaban daddyn nashi, ya dafe gwiwowin kafafunsa da tafukan hanneyansa


"Daddy wanene ka kira a waya.. "?

"Uncle dinta ne Alhaji musa, baka san cewa shi mutumin mu bane, ay da tunfarko ni ka fara tuntu6a da maganar ta, da baka sha wahalar yi ma hajiya laura magana ba..." wani irin annurin farin cikine ya bayyana akan fuskar zaki,  

"Idan har kana so In haɗaka da ita, sai ka bani cin hanci" ya fada da zolaya

"Daddy me kakeso na baka? Ka fada min koma menene...." dariya sir mubarak yayi

"Farin cikin ka da kwanciyar hankalin ka nakeso .." dariya zaki yayi 

"Ka bani mamaki son, ji bi yadda soyayya ta jigata ka, kamar ba dan sir mubarak ba...." sunnar da kanshi kasa yayi cike da jin kunyar daddynsa

"Ni kamarma na ta6a ganin yarinyar? Halan 6oye ta kake yi idan naje canada don kada na ganta ." girgiza kai yayi"a'a daddy, bana 6oyanta zaka iya saninta, duk wanda yaje gida sai yayi tsammanin yar aiki na ce, shiyasa baku ta6a lura da shakuwar dake atsakanin mu ba..."

"Gaskiya zanso inji meya faru da ita? Meyasa ta gudu tabar Yarta? Amma kaima da laifinka, fisabilillah ina maka kallon uztaz ashe har mace kake 6oyo agidanka, almost 16years haba zakina! Kunyi ma kanku adalci kuwa? Da hankalin ka ka ajiye matar aure kuma kasan guduwa tayi daga gida bakayi yunkurin neman danginta ka fada masu ba!meyasa"? 


Ya faɗa fuskarsa adaure alamar baiji dadi ba


"Daddy sonta ne Ya rufe min ido na, nasan na aikata babban kuskure amma nayi nadama, kuma ni harga Allah ban ta6a neman ta ba, abun dayasa ban nemi kowa nata ba saboda ta faɗamin ta tsani danginta, bata son ta dawo Nigeria, nayi kokarin shawo kanta donta amince in dawo da ita amma sai tace idan na matsa mata zata kashe kanta ne, shiyasa na kyale ta, daga baya mijinta ya turo mata sakon saki ta wayarta, daga ganin hakan saina kara samun kwarin gwiwar killace ta agidana saboda in mallake ta........." cikin sanyin murya ya kare maganar yana kallon daddyn nasa,

"Kayi kuskure da baka sanar dani ba, ay da nayi maka hanyar auranta, yanzu koda ka hadu da ita zata iya bijire maka ta koma ma tsohon mijinta...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya"daddy ka tayani da addu'a, Allah yasa rabona ce..."

"In sha Allah zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ka samu abunda kakeso.." ajiyar zuciya ya sauke, kafin wani ya kara magana a cikin su, 

Sallamar hajiya turai ta katse su, atare suka amsa mata, ta shigo fuskarta dauke da murmushi"i'm sorry na katse maku firarku, my son barka dai, fatan ka tashi lafiya" da fara'a ya amsa mata"lafiyalou mommy,

Kallon sir mubarak tayi"na kammala shirya mana breakfast, ka taso muje kaci kada ka makara" ruko hannun zaki yayi acikin nashi atare suka mike suka nufi dining din


Adai dai lokacin, dr Jazz ya fito sanye cikin black trouser da shirt, Ya daura lapcoat akan kayansa, idanunsa manne da farin glass 

"Barka da safiya daddy..."

"Yawwa Son, Harka shirya kenan"

"Eh,"

Ya faɗa tare da samun wuri kan dining chairs suka zauna, turai ta fara yin serving nasu

"Big bro Ina kwana.." murmushi ya sakar mashi kafin yace"lafiyalou, ina fata kaima haka" ya ɗaya masa kai alamar eh,

Har sun fara cin abinci, Ibad Ya fito daga shi sai ɗan short,

"Mommy ni an manta dani, shine ba a kirani inzo inci abincin ba . " ashagwa6e yayi maganar

Turai tace"sorry babyn zaki, Ay nayi zaton zaka jira ne Ya kammala in ya rage sai ka ci.." murmushi sukayi

"Oh wai har yanzu bai daina wannan ɗabi'ar ba"? Sir mubarak ya tambaya yana kallon zaki

"Daddy bai daina, abun nasa kullum ƙara gaba yakeyi, bansan ya zanyi da shi ba, har friends dina sun gane halinsa, Na cin sauran abincin da na rage...."kallon shi sir mubarak yayi da sauri ya juya baya yana faman noke kai

"Daddy pls kada kamin faɗa, ni wlh na saba, kuma nafi jin dadin cin ragowar abincinsa, daɗi Allah" dariya suka sanya gaba dayansu


"Calm down Your mind, kai fa last born ne, shalelan mommy da daddy, ba wanda zaiyi maka faɗa, kayi abunda kakeso" yaji dadin maganar turai,

"Zo ka zauna in zuba maka abinci.." da sauri ya samu guri ya zauna, Yana satar kallon daddyn su da jazz wanda tun ya zauna, hankalin shi baya atare da su, gangar jikinsa ce kadai atare da su ruhinsa yana wurin faryat daya kwallafa rai akai.


"Jazz kaci abinci mana! Salon sai ka makara ko"? Cikin kulawa Sir mubarak yayi masa magana

Kamar baisan cin abincin Ya dauki cuf of tea mai zafi Ya ɗan kur6a

"Daddy dan Allah kace ma yaya zaki mu koma toronto, ko dan saboda karatuna, in ba haka ba zaija amaida ni baya..." da damuwa akan fuskarsa yayi maganar

Harara zaki ya dan watsa mashi"kada na sake ji kayi magana!..."

Sir mubarak ya katse shi da cewa"ba haka yakamata kace mashi ba.." ya faɗa tare da maida dubansa ga ibad wanda Ya haɗe rai.


"Next month zaku tafi, in sha Allah"

Murmushi ibad yayi"yawwa daddy thank you.."


"Wato na lura gudunmu kake Yi ibad..

"No momy wlh saboda school, kuma na manta bibina a gida..." Yana nufi magensa, miƙewa jazz yayi"zan wuce" atare suka haɗa baki wurin yi mashi Allah kiyaye hanya, sai da yabi kowan nan su ya manna masu peck kafin  ya tafi......


________________________________✍️


Tun da garin Allah ya waya, Aneeleeh ta rasa kwanciyar hankalin ta, ta kasa tsaye taka zaune kamar mai fama da ta6in hankali, tayi matuƙar kagara ta kosa hajiya Saratu ta kira zahra, duk bayan yan mintuna sai ta leƙa dakin zahra don ta ji ko ta kirata shiru har yanzu babu wani labari, kamar yadda ta matsu haka hajiya layla ta matsu suzo da yarinyar, itace ta fara farkar da ita daga bacci da sanyin safiya ta kira ta awaya, tana kara jaddada mata akan kada ta manta tayi kokari su yi magana da iyayen yarinyar, ta rasa ya zatayi gaba daya ta daura ma kanta damuwa, daren jiya dakyar ta runtsa..


"Aunty Aneelerh"muryar zahrce ta ratsa kunnanta, Jiki na rawa ta juya da sauri ta nufi zahra dake shugowa dakin, tana sanye da hijab, hannunta ruko da wayarta...

"Zahra ta kira? Ko har yanzu"? shiru zahra tayi fuskarta babu walwala.. Hakan ba karamin ɗaga hankalin Aneelerh yayi ba

"Kinyi shiru baki ce komai ba"? fuskarta dauke da matsananciyar damuwa ta furta"muyi hakuri aunty Aneelerh, ta kira tace wai yarinyar ba unaisah ɗinmu bace....." 

"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Hankali atashe Aneelerh ta zabga salati tare da ɗaura hannayenta biyu akanta

"Nashiga uku zahra! Ya zanyi? Ga shi nayi masu alkawarin yau zanzo da yarinyar, dan Allah ki taimaka min zahra, ki nema mana alfarma awurin hajiya saratun su bamu aronta...." gaba daya tabi ta ɗaga hankalin ta...

"Aunty Aneelerh, ki kwantar da hankalin ki, tace muje gida mu same ta yanzu watakil ko zasu ba mu aronta ne.." nauyayyar ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, jiki na 6ari tace"bari na shirya sai mu tafi, mahboob Ya dawo ne"?

"Bai kaiga dawo ba" amsawa tayi da toh, da sauri ta nufi toilet ta shige don tayi wanka

Fitowa zahra tayi daga dakin, jikin ta duk yai sanyi, 


Bayan sun kammala shiryawa,sai da suka fara zuwa dakin mami suka sanar da ita kiran da hajiya saratu tayi masu, mami tace Allah Yasa muji alkhairi, idan kun isa komai ake ciki ku kira ku sanar dani,suka amsa mata da toh...


Da matsakaicin gudu motarsu ta haura kan titi, Aneeleerh ce ke driving dinsu, zahara na zaune gefen ta..


"Auntyna ki bi a hankali mana, naga sai zura uban gudu kike kamar zamu tashi sama!

"Ba zaki gane ba Zahra, wallahi ji nake kamar inyi fiffike in karasa estate din, gani nake kamar bana sauri, ni dai burina Allah yasa su taimaka su bamu yarinyar..." zahra ta amsa mata da ameen,


Lokacin da motarsu ta karaso estate din, da sauri Aneelerh ta rage gudun motar, sunyi tsammanin security officers din zasu dakatar da su irin na jiya amma abin mamaki suna isa, da hannu sojojon suka yi masu alamar su wuce, gaba daya suka sauke ajiyar zuciya 

Bayan sunyi parking din motar, suka fito daga ciki, adai dai lokacin Hajiya saratu ta fito daga entry hall na gidan, ta dauki wankan leshi, idanunta sanye da farin glass

Cike da zumudi suka nufeta, with respect suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu kafin tace"bismilla muje" ta nuna masu motarta da hannu, su biyu suka shiga back seat, security din da zai yi driving dinsu yana a mazaunin driver, Hajiya saratu na daga gefen shi...


Kaitsaye motar ta nufi cikin estate din


"Kamar yadda nake fada maku, munyi magana da shi jiya, nayi masa bayanin komai dangane da zuwan ku, to a gaskiya yarinyar bata wurin ku ba ce, amma yace zai iya baku ita har zuwa time da ita patient din naku zata ji sauƙi...." fuskarta babu fara'a tayi maganar.


kallon juna zahra da Aneelerh su ka yi jikin su yayi sanyi lakwas...

Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"hakan ma yayi mungode sosai..." 


___________________________________✍️


Firgigit ta farka daga bacci tana faman zazzare gray eyes dinta tamkar kwayar idanunta zata faɗo kasa, hannun ta ɗaya dafe da goshin ta, numfashin ta na fita da sauri, kwata kwata babu kuzari a jikinta kamar wadda aka zarewa laka, ga wata kasala data baibaye sassan jikin ta, dakyar ta yunkura ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin pillow, fuskarta ta kumbura suntum, kumatun sunyi jawur, haka la66anta ma sun dan kumbura, idanunta sun ƙanƙance kwarmin idon yayi ja daga gani ta jigata ba kaɗan ba...

Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata abunda Ya faru da ita adaren jiya, runtse idanunta tayi sosai kwallar da ta taru acikin su ta fara ƴar tseral kan kuncin ta, ta rasa gane meya faru? Shin mafarki ne ko gaske? Kokwanto ta soma yi saboda zuciyarta tagaza yarda da abun da ya faru, was wasi ta kama yi tana faman tariyo komai daya wakana adaren jiya, babu wata alama da zata tabbatar mata da abun ya faru dagaske, da sauri ta dubi yar rigar jikin ta, tayi uban squeezing kamar an ƙwatota daga bakin kura, da sauri taja rigar ta rufe santala santalan laps dinta, ta sauko daga kan gado tana faman bin dakin da kallo, mirror chair ta gani yashe ta jirkice kan floor

"Ina wandona Yake"? Ta jefa ma kanta tambayar, 

Ringing din wayarta ne Ya doki dodon kunnanta, jiki na rawa ta nufi toilet saboda tana tunanin kamar anan ta cire wandon

Tana shuga ciki ta iske shi akan hanger, tunawa tayi da jinin daya dawo mata gadan gadan adaren jira aranta ta ayyana shima dagaske ne ko duk cikin mafarkin ne"? Ta kare maganar tare da buɗe laps dinta ta laluba jikin ta, bata ga komai ba, sai dai wani farin ruwa mai yauƙi yauƙi dake gangarowa...

Gaba ɗaya ta gama rikicewa, tunaninta ya kasu gida biyu, ta jima a toilet din kafin ta fara tunanin yin wankan

Bada jimawa ba, ta fito sanye da rigar wanka, har ta kusa isa gaban mirror tajiyo bugun kofa, 

"Wanene"? ta fada tare da kallon ƙofar

"Daddyn ki ne..." sanyi taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta nufi kofar ta buɗe mashi

Tun daga kasa ta fara kallon shi, jallabiya ce a jikin shi maroon colour, sai kamshin turare ke tashi a jikin shi

"Daddy, Ina kwana..." bata ƙare maganarba, ganin yadda yake binta da kallo mai tattare da ruɗani

"Unaisah! Baki da lafiya ne? Meya faru naga fuskarki ta kumbura tayi ja, kamar kinyi kuka..." wani irin mugun bugu kirjinta yayi, babban tashin hankalinta kada ace abunda Ya faru jiya dagaske ne, ba mafarki ba

Muryarta adabarbace ta furta"da.. ddy.. lafiyana lou, meka gani ne."?


 girgiza kai taj yayi"no ban yarda ba, fada min ko dai wani ya buge ki ne"?

"Wallahi daddy ba komai, watakil ko dan saboda firar da muka tsaya yi jiyane ban samu isasshen bacci ba shiyasa fuskata ta kumbura..." kwata kwata hankalinsa bai kwanta da yanayin ta ba, janyota yayi tare huggin dinta, ya daura hanneyensa akan bayanta

"Nayi missing dinki my daugher, ina fata kin tashi lafiya.."

"Lafiyalou daddy ..." dago da kanta yayi"baki jin ciwon kai? Ko zazza6i haka"

Ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta duk don ta kwantar mashi da hankalin shi

"Bana jin komai daddy, ni yau da karfina na tashi..." ajiyar zuciya ya sauke

"Okey, ki shiga ciki ki karasa shiryawa, Chief Yana son ganin ki" waro idanu waje tayi alamar mamaki

"Daddy ni kuma? ɗaga mata gira yai alamar eh

"Ki sanya kaya masu kyau, zan jira ki awaje" cike da mamaki ta amsa mashi da toh,

Bayan fitarshi cikin sauri ta nufi closet dinsu, ta dauko wasu hadaddun riga da wando ƴan pakistan, rigar fara wandon yellow, veil din kayan yellow, ita kanta data sanya kayan saida ta jinjina ma kyan da sukai mata, gaban mirror ta zauna ta fara gyara sumar kanta dakyar take sharce ta da comb, bayan ta kammala gyara gashin, ta shafa powder da lipstick, kafin tayi rolling veil din akanta, takalma ta dauko masu tsini ta zura su a kafafunta,

Komawa tayi gaban mirror ta feshe jikin ta da turare

Har lokacin bata daina tunanin abun da ya faru a daren jiya ba, was wasi take tayi aranta.., kwata kwata bata so ya zamana gaskiyane abun da ya faru da ita....

A hankali ta zura kafarta ta fito daga dakin, 

Walking slowly ta nufi daddyn ta dake atsaye yana jiran ta, babu kowa a falon da alama basu kaiga fitowa ba

"Daddy yunwa nake ji, Ciki na babu komai.." ta fada yayin da ta ruko hannunsa acikin nashi

"Kada ki damu, nima banyi breakfast ba, idan munje wurin chief din zamuyi atare da shi..." amsa mashi tayi da toh

Kaitsaye suka nufi walkway bata san ina za su bula ba

"Daddy ba part dinsa zamuje ba"?

"Eh, yace mu same shi a backyard..


Zazzaune suke akan wasu jigunannun sofas ƴan ubansu, backyard din ya Haɗu an ƙawata shi sosai, chief da hajiya saratu suna a zaune kan sofa daya, Aneelerh da zahra suna fuskantar su, tun da suka zauna Aneelerh take ta jinjina ma haduwar gidan da shi kanshi mamallakin gidan wato chief, kallo ɗaya tayi mashi saida gabanta Ya faɗi, ya ɗauki wankan suit navy blue sunyi bala'en yi mashi kyau


Zahra dake satar kallon shi, gani take kamar a mafarki yau gata ga director general na isod, crush ɗinta, mutumin da tayi haukan son shi a lokacin baya..


Round table din dake a tsakiyarsu, cool drinks ne da Snacks asaman hadadden wooden tray 


"Idan muka baku aron yarinyar sai yaushe ne zaku dawo mana da ita.."? Hajiya saratuce tayi masu tambayar

"Idan da hali har zuwa lokacin da benazir din zata ji sauƙi, dan Allah ayi mana alfarmar nan..." gyaɗa kai hajiya saratu tayi"okey, amma fa zaku bani tukuici tun da ni nayi maku hanya a wurin chief..." ta faɗa da yar zolaya tana kallon su

Murmushi suka saki zahra tace"bakomai mommy, ay duk abunda kikeso zamu baki.." yar dariya tayi"zolayarku nakeyi..." dariya sukai su kansu sun san tafi karfin tukuici, ta dai faɗi ne don ayi raha...


Kwas kwas sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka dago tare da kallon inda sautin ke fitowa....❓



*Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page on monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya✍️* 


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post