Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 56 by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 56 by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Wani irin burki suka ci, ganin babu khala adakin ta, abun daya jefa su arudani gaba ɗaya dakin nata a hargitse yake, harta gadonta Ya jirkice, tukwanan furannin dake a dakin duk an faffasasu, Ga jinin dayake malale kasa.. YA ILAHI❗❗

 Alkalamina bazai Iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba.

Sun rasa gane meya faru da tsohuwa khala? Jinin wanene suka gani a kasa? babban abun da suke ma zullumi Fursinonin da suka turo akawo gurin ta, basu san awani hali suke ciki ba, fargabansu kada ace jinin fursinonin ne!


badan zuciyar Imani ba da tuni Chief Ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin da Elders suka kunsa masu.


La66ansa na kerma ya furta"La'haula walaqu wata Illah Billa, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un....." wani irin zafi jikinshi ya dauka rau...


Cike da ruɗu Commender James Ya furta"ni fa bangane ba, meke faruwa ne? Ina prisoners din da muka kubutar? Ina tsohuwar take? Jinin menene wannan"? ya faɗa yana nuna jinin dake malale kasa...


Yawu mai ɗaci thompson Ya hadiya ga radadi daya addabe shi, cikin sanyin murya yace"bana fata abunda nake hasashe ya zamana gaskiya, Zai iya yiwuwa Matsafan ne suka kawo mata farmaki watakil sun gano hada sa hannunta gurin kawo masu farmaki..." 


bai ƙare maganar ba, Chief yai hanzarin katse shi ta hanyar girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya furta"in kuwa hakane Elders sun kashe ni, sun gama dani..."


kamar zautacce ya dinga nanatawa 



Kanshine ya fara juya mashi wata irin juwace ta fara kokarin daukar shi da sauri Ya dafe bangon dake abayan shi, Yana huci hadi da jan numfashi kamar mayunwacin zaki..


"Ba zamu bar Nigeria ba, har sainaga bayan Elders, dole su fuskanci mummunan hukunci mai tsanani"


 rai a6ace commender James ya fada...



"Me yakamata muyi yanzu? Bana bukatar mu 6ata lokaci gurin nemo su"! Commender haroon ne ya fada...


Captain lewis Yace"Where should we begin searching for them? Do you think they're still in this prison?"



Dukansu fa arauna ce suke, gabban jikinsu duk sun raunata ga yunwa da bacci dole su jigata tun dare ake gabzawa har gari ya waye batare da sanin su ba, amma saboda karfin hali irin na soja, burinsu su karasa aikin da suka dauko bata kansu suke ba, dare guda ba bacci sai zallar tashin hankali...."


"I don't think they're here, We should return to Nigeria and devise a new plan, we've lost our soldiers, and we're too weak to fight them now. We need to know what's happening with the soldiers we left outside" 


(bana tunani suna nan, ni dai shawarar da zan bamu shine mu koma Nigeria, In yaso saimu sake sabon shiri, tunda yanzu duk mun rasa sojojin mu, Mu kanmu a raunace muke bamu da karfin da zamu iya yin faɗa da su a halin yanzu" acewar lieutanant Jackson)


Numfasawa Chief yayi"in sha Allah, karshensu ne yazo tun da har mu ka yi nasarar shugowa kurkukun nan, kuma mun yi masu barnar da ba zasu iya gyarata ba, nasan sun tsoratane shiyasa suka gudu, hakan ma wata nasarace...." 


ya faɗa yana jan numfashi kafin Ya ɗaura da cewa"Zaku Iya tafiya amma ni bazan Iya barin kurkukun nan ba, saboda ɗan uwana Danish, zan jira har zuwa lokacin da Allah zai fiddo dashi daga cikin rijiyar zamu dawo tare da shi..." 


ya faɗa idanun shi cike tab da kwalla, tsananin tausayin shi ne Ya kamasu, commender james Ya dafa kafadarshi Cikin kwantar da murya yace"ka yi hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..." 



Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba.


cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?"



Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin haɗari, sai kuma mu tafi mu barshi?


Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu.


"Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon.


Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..."


da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke ƙwala mashi kira haɗi dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba tsammani ginin Kurkukun Ya fara Jijjiga kafin kace me tuni ginin ya fara tsastsagewa, hankalin Su commender ba karamin tashi yayi ba, akan idon su komai ke faruwa yayin da Chief kwata kwata bai lura ba saboda baya acikin hayyacin sa.


wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, wasu irin marmarar duwatsun da akayi ginin ne suka fara 6a66akowa daga sama Kaitsaye suke rubzowa ƙasa da wani sauti suka tartwasewa, duk wanda kuwa tsautsayi yasa suka afkwa kanshi tofa Ya tashi aiki.


Chief daya rikice bai kaiga isa hall din ba, Wani Gingirimeman dutse Ya yanko mai girman gaske Gaba daya ya zube ƙasa, ya shiga tsakanin chief da hall din, ras gaban shi ya faɗi ya zare reddish eyes dinsa sam ya kasa motsawa, Wlh zuciyarshi ta gama karaya ya riga daya fidda rai da Danish.


Saboda ya rude kokari yake ya nemi hanyar da zai bi ya karasa ga hall din, wani ginin ne ya zazzago daga saman ceilling din dayake batare daya ankara ba, Cikin zafin nama commender james Ya damƙi damtsen hannun shi ya jefar da shi gurin Su captain da sauri Suka rurruke  shi Yana kuka Yana kokarin fisge kan shi daga hannunsu ahaka suka sanya karfi gurin ingiza shi.


bawan Allah sai waiwayon ginin hall din daya rushe yakeyi..Yana ji Yana gani ahaka suka tafi da shi kamar yayi hauka sai sambatu yakeyi 


_tun da na fara aiki ban ta6a faduwa ba sai yau da nagaza taimakon ka, Naji kunya Danish, i'm a looser, ka sani ba kai kadai bane danish, Kana da Allah kuma kana da dani, Danish bazan bari ka mutu ba, zan dawo Danish, zan dawo dole na ɗaukar maka fansa..........😭😭😭_


(Finally Su Chief Sun yi nasarar fita daga kurkukun kaddara bayan kalubalen da suka fuskanta)



*__________________________ELDERS 🔥*




A zazzaune suke kan Sofas cikin wani Daki mai duhu, saika kura ido zaka Iya ganin su da taimakon wutar Candles dake Ci, round table din dake agaban su shake Yake da kwalaben Giya sun sha sun bugu har ta kai masu karo.


Idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, fuskokinsu babu annuri ko miskala zarratin basu taba fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba, sunyi babbar asara ba kaɗan ba.....❗


"Sune na farko da suka fara kawo mana farmaki! sun latata ginin da nayi wahalar kafawa tsawon shekaru! Sun san komai da muke aikawata, sun san sirrin mu, sun gani da idanunsu, sun kuma kashe rabi da kwata na Giants din mu, bayan irin 6arnar da sukayi mana na, sun 6ata shagalin black Night,  sun kashe dubban matsafan da basu ji ba basu gani ba..." 


ya faɗa yana jan numfashi cikin fushi, kafin ya daura da cewa"hakan bai ishe su ba, sai da suka kwashe Fursinoni da muka raina tsawon shekaru don mu amfana da su, sun tarwatsa duk wani shirin mu"


"Yaron da muka raina da hannun mu don ya zama garkuwar mu yaci amanar mu ya koma garkuwar su, tsohuwa Tamira da Salsabeel haka suma suka ci amanarmu, abunda yafi karya min zuciyata, wadda na damƙa ma yarda ta da amanata, hada ita cikin waɗanda suka bada gudummuwar kawo mana farmaki! meke shirin faruwa da mu ne? Meyasa waɗanda muka yarda da su suke cin dunduniyar mu"?


bai karasa maganar ba Yana huci Ya ɗaga kwalbar giyar dake a  hannun shi Ya rotsa ta kan table din gaban shi nan take ta tarwatse.


Ran Elder yayi mugun 6aci, a wannan gabar komai zai iya faruwa.


 Hankulan sauran Elders din ba ƙaramin tashi yayi ba, wata irin kururuwar ihu Ya fasa tare da tallabe kan shi da tafukan sa.


Lallashin shi suka fara yi cikin kankan dakai da girmamawa dakyar suka shawo kan shi.


Gyaran Murya Jan harshe yai kafin ya furta"Karaya ba tamu bace, Ba'a san elders da rauni ba, har yanzu muna da damar da zamu Iya dawo da ran kurkukun ƙaddara...." 


bai ƙare maganar ba, Elder Yana huci Ya tari numfashin shi da cewa"tayaya zamu iya yin hakan? Bayan sun riga da sunsan komai, sanin ka ne muddin wani yasan sirrin inda muke yin tsafinmu abu na farko da zai faru lalacewar ginin kuma ya riga daya faru, abu na gaba shine karyewar sihirinmu In har hakan ta faru cikin sauki zasu shafen tarihin da muka daɗe muna kafa shi...."gaba daya sukayi shiru suna sauraranshi, da alama sun kadu sosai.


 dakatawa yayi da yin maganar wani irin kululun bakin ciki da takaici ne ya tokare makoshin shi"a matsayin mu na mashahuran da duniya tasan da zamammu, abun kunyane asan me muke aikatawa, Ina jin tsoron mu rasa kimarmu da darajarmu fiye da yadda nake jin tsoron mutuwata, mutuncinmu zai zube a idon duniya, girmamamu da mutane suke yi suna ganin martabarmu zai tashi abanza, daga nan basai nayi maku bayanin abun zai faruwa ba, kun riga da kunsan sakamakon bazai ta6a yin kyau ba..." ya fada yana binsu da kallo daya bayan daya.


bakowane daga cikin su ya karaya ba, shi dama Elder mutunne mai wata aƙida tun fil azal baya son duk wani abu da zaisa mutuncin shi ya zube yana girmama ƙimarsa.



muzkutawa Jan le6e yayi kafin da wata irin muryar mai tattare da zafin fusata Yace"garkuwar kurkuku Ya zama garkuwar Fursinoni, ƙaddarar kurkuku ta zama mummunar ƙaddara agare mu, babban kuskuren da muka tabka shine barin tsohuwa Tamira da ranta, a lokacin da muka kashe Habibulllah, da mun sani mun haɗasu duka mun kashe su, shima garkuwarmu da ace bamu kawo ƙaddara gidan kurkukun mu ba, nayi imanin bazai ta6a cin amanar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa"ita kuma Khala Elder Kayi hakuri da abunda zan faɗa, tunkafin zuwan wannan lokacin saida muka baka shawarar ka kasheta saboda ita din tana da kyakkyawar zuciya kuma tana ƙyamatar abunda muke aikatawa amma saboda kaunar da kake mata, shi yaja har ka gaza Yanke mata hukuncin daya dace"


Cike da danasani Elder ya sunkuyar da kan shi ƙasa, tunda suka fara magana, Jan wuya Yana a kishingide Yana binsu da kallo babu alamun kaɗuwa atare da shi, shi kuwa Jan kunne kamar yafi su shiga damuwa dama duk cikinsu shine mai raunin zuciya.


Jan Ido Yace"kada ku bani Kunya, duk wani abu daya faru ya riga daya faru, Mu fa Elders ne,  babu wani mahalukin daya isa yaga bayan mu, abun nawa muka aikata bamu ta6a karaya ba sai wannan lokaci don kawai wasu kananun kwari sun kai mana farmaki? Rai nawa muka salwantar? Ya fada cike da gadara.


"sai wadannan zasu gagaremu! In har muna so mu dawo da karfin ikonmu dole mu bi abun da allon tsafinmu ya nuna mana, dole mu aiwatar saboda itace dama takarshe da ta rage mana wadda zamuyi amfani da ita gurin dawo da ran kurkukun ƙaddara" 


Ya faɗa tare da dan dakatawa yana dubansu"a wannan karon dole mu cire sonkai atsakaninmu, bi'amana mu kashe duk wanda Yasan sirrinmu koda mafi soyuwa ne agaremu..." 


sarai Elder Ya fahimci da shi yake magana.


"ita kuma dama ɗayan nan data rage mana itace mu cire Zuciyar Yarinyar nan, Mu ba dodon tsafin mu Ya handame ta, sannan mu kashe ƙaddarar kurkuku, ta hakane kaɗai gidan kurkukun ƙaddara zai farfaɗo...."


 wata irin mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, ganin har yanzu suna da saura damar da zasu cigaba da aiwatar da shaidancin su.


Cike da izza Jan wuya yace"abun farin ciki, Garkuwar da suke taƙama da shi, Ya rasa ranshi saboda shi wawane shashasha, Ya sadaukar da kanshi saboda ya basu kariya, duk da muma munyi babban rashi  amma wannan duk ba wata matsala bace da zamu daga hankalinmu akai, Ni ta inda najiye mana dadi gaba dayansu wadanda suka san sirrinmu basu san fuskokin mu ba, tayaya suke tunanin zasu iya yin nasara akanmu? In banda ma sudin dakikai ne iya fa sunayen mu suka sani, sai kuma sirrinmu amma azahirin rayu basu san su wanene Elders Ba...."



Maganar Jan Wuya ta faranta masu rai, ganin sun samu mafita...


"Yanzu wanene Zai kawo mana Yaran?" Jan harshe ne yayi tambayar, Cike da isa Jan wuya yace"kubar komai a hannuna"


tuntsirewa suka kuma yi dariya hahaha 

_________________________________✍️



Shin Ya Labarin Tsohuwa Khala❓



*Bayan wani lokaci*



Farfaɗowa tayi daga dogon suman da ta yi na tsawon awanni, A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhu ne ya mamaye ganin ta, tana ƙoƙarin motsa jikinta taji  kamar an daddaureta.


gumin zufa ne Ya wanke fuskarta, bata gama wartsakewa ba sai nishi take yi tana jan numfashi..



takun tafiyar mutun taji a cikin kunnanta yana tunkaro ta, cikin disasshiyar murya ta furta"wanene"?


 Kakkausar murya Elder ce ta razanar da ita yayin daya furta"me nayi maki dana cancani cin amana daga gare ki"


 Shiru tayi bata furta kalma ba, Hankalinta dai idan yai dubu toh ya tashi, zuciyarta sai dakan uku uku take tasan yau sai buzunta, mai kwatarta a hannun Elder sai Allah.


A hankali Hasken fitilun dake saman ceilling din ɗakin ya haskaka ko'ina tana a zaune kan Kujerar ƙarfe, a rude take kallon igiyar kacar da suka ɗaɗɗaure jikinta da ita, ko yatsanta bazata Iya ɗaga wa ba, Da sauri takai dubanta gare shi yana a tsaye Ya juya mata baya, tun da taganta adakin da suke hukunta wanda yaci amanarsu na gidan kurkukun kaddara Ta tsinci kanta da jin matsanancin faduwar gaba, ga wasu karfafan Evil giants data hango tsaye abakin kofar dakin..


"Tun da naga irin makaman da sukai amfani da su gurin kashe giants nasan cewa koma wanene ya basu makamin acikin mu yake, saboda mu kadai keda irinsu acikin gidan kurkukun nan ake ƙera su, bakowa yazo min araina ba face ke dama kin jima kina gaya min zaki dauki fansa akaina"


Cike da karfin Hali tace"banyi mamakin abun da kayi min ba Elder, Ni angaya maka bani da zuciya a kirjina ne? Taya kake tunanin bazan ci amanarka ba? Dama akwai amana tsakaninmu? Kaida ka rabani da kowa nawa, har kana da bakin furta naci amanarka? Akwai maci amanar daya wuce kai mugu, Hakanan kawai saboda nasan sirrinka bisa kuskure ka rabani da dangina, ya'yana, Jikokina, ka kafe ni da asirinka cikin kurkukun nan."


 idanunta jawur ta faɗa yayin da hawaye ke shararowa kan kuncin ta..ta daura da cewa


"tun lokacin dana nasan sirrinku, a ranar na daukar wa kaina alwashin saina yi silar Tonuwar asirinka, kowa yasan wanene kai, da  miyagun ayyukan da kake aikatawa, shiyasa na dinga satar makamanku ina boye su saboda tanadin zuwan wannan ranar" 


 bata ƙare maganar ba, Taji Ya sheƙe da dariya, cike da izza Ya juyo ya fuskance ta, batare daya furta kalma ba, gently yake jujjuya sandar hannun shi.


"Dariyarka ta bazance Elder, Ni nasan Ayanzu haka Ƴan hanjin cikinka kaɗawa sukeyi saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya, Na kunsa maka bakin cikin da har abada ba zaka manta ba, naja maku babbar asara, koba komai Yau kaga wadanda suka fi karfinka"


 ta fada da murmushi akan fuskarta.


Wata Yar iskar dariya Ya saki, Kafin Ya furta"dame kike takama ne? Da ido Ta nuna mashi sama tace"Allah, shine abun tinƙahona, koken dana daɗe ina kai mashi akanka Yau ya amsa addu'ata, daga Yanzu ka kasance cikin shiri akowani yanayi mutuwa zata Iya riskarka, zaka wukalanta ka zama kaskantacce, kimarka da darajarka zasu zube a idon duniya....." 


bata ƙare maganar ba Elder Ya buga sandar hannunsa ta daki ƙasa har saida ƙura ta tashi, wani irin radadi taji acikin kanta hakan yasa ta dakata da yin maganar.


Yana Huci Yace"kina tunanin kinyi nasara akaina ne? Bayan Duk wani shirinki Ya tashi Abanza, wadanda kike takamar zasu ga bayan mu  a yanzu haka babu ko daya acikin su, duk sun mutu a hannun giants din mu, suma fursinonin da kika ku6utar basu tsira ba zamu kashe su ne"


Wani irin faduwar gaba taji arazane Ta furta"kana nufin Danish da Owais sun mutu su ma" jinjina mata kai yayi" gaba daya sun mutu...Don haka kidaina farin ciki, saboda haryanzu baki kamo hanyar da zaki ga bayana ba, kashe Elder ba abune mai sauki ba, Ita kanta mutuwar tsorona take ji..." a gadarance yai maganar.


ta kiɗima da jin maganar shi, idanunta cike tab da kwalla ta furta"saboda shafewar basira da jahilci kamanta kafin kai anyi wasu azzaluman da suka gabata yanzu duk suna ina ? Ta jefa mashi tambayar bai furta kalma ba.


"mutuwa bata tsoronka Elder Lokacin ka ne baiyi ba, Allah yana sane da duk wani abu da kake aikatawa dama ce ta dan wani lokaci kuma kajira ka gani wlh karshenka bazai kyau ba" ta faɗa tana sharar kwalla


 "kuma karya kake min, Danish dina bai mutu ba, owais dina ma bai mutu ba ina ji araina suna  araye..."


Fashewa yayi da dariya"ki yarda ko karki yarda matsalarki, Kina kurarin kin tona asirina, bayan Har yanzu asirina arufe yake saboda babu wanda yasan ainihin Elder, ko fuskata basu sani ba, taya zasu iya tona min asirina? Bayan Ko tuhumata basu isa suyi ba saboda basu da wata shaida...." ya fada yana sakin dariyar shakiyanki.


ranta a 6ace ta furta"ni zan tona maka asiri..." ta faɗa tana huci.


Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"kin ta6a ganin gawa tayi magana"?


Cike da tashin hankali ta zare ido tana kallon shi, matso da fuskarshi yayi saitin tata"Oh wai kina tunanin zan barki araye? Bayan kece kika san su wanene Elders, Ko da can da kika san sirrina nabarki araye nayi danasani da ban kasheki ba, da nasan zaki zamarmin masifa da tuni najima da fille kanki...." 


gaba daya tabi ta rude da jin maganar shi muryarta nawa ta furta"kada ka kasheni, Kabarni da raina, Ina son naga ya'yana da jikokina, Ina so na koma gurin dangina, ko dan son da kake min da zaman amanar damukayi da juna ka kyaleni da raina.."


Girgiza kanshi yayi"ke da ganin su, Sai a lahira, nasoki tamkar raina amma tunda kika nunamun tsantsar kiyayyar da kike min naji nima kin fita araina, Inasonki amma nafi son mutuwarki ayanzu idan nabarki zaki zamarmun annoba"


Ya faɗa tare da dafe saitin zuciyarshi, batay mamakin ganin hawaye da suka cika idanun shi ba..


"bazan ta6a son wata halitta kamar yadda nasoki ba, nasan zanyi bakin ciki da takaicin rasaki arayuwata, zanyi maraicin rashin ki, zan dawwama da radadin kashe ki da zanyi, Bazan ta6a yafe maki abunda kikai min ba, kece silar komai, Kin Ci amanar kaunar dake atsakaninmu, meyasa tun farko kika tsananta bincike akaina? Meyasa  Kika san sirrina? Kinyi silar lalata Farin cikin rayuwarmu, kema kin sani nasoki fiye da yadda nakeson kaina...." zubewa yayi agabanta kan gwiwowinshi...sosai ta fashe da kuka cikin karyayyar murya ta furta"komai ya faru mukaddarine daga Allah, sirrinka dana sani Allah ne Ya kaddara zan sanin, shiyasa har nasan komai, da ace kai musulmine kayi imani da Allah da ka gane abunda nake faɗa maka..


"duk yadda na karya maka zuciya bai kaiga yadda ni ka karya min tawa ba, ina farin ciki na auri miji nagari mai sona da bani kulawa ashe mugun mutum na aura, da kanka ka musuluntar dani ashe kai din kasungumin arnene matsafi da baiyi imani da Allah ba, sannan ka ciyar damu haram, wlh ko bayan ba raina sai Allah ya tona asirinka, in sha Allah Elder saika yi kaskantacciyar mutuwa, duniya gaba daya zata juya maka baya, komai daka mallaka zai lalace.."


bata kare maganar ba, Ya zabura Ya mike tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki...tuni ta hadiye maganarta, Hankalinta atashe take kallon shi.



Giants ɗin dake abayanshi Yaba Umarnin su ɗaure mashi ƙafafuwanta da igiya jikin fankar dake liƙe saman ceilling din dakin, fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita ita ba mutuwar take tsoro ba, abu biyu take ma bakinci zata mutu bata tona asirin Elder ba, abu na biyu zata mutu bata gana da ya'yanta ba bayan tsawon shekaru ashirin da Ya garkameta akurkukun basu san tana raye ba.


tana ji tana Gani, giants din suka kwance igiyoyin da suka daureta a jikin kujerar, daya ya ruketa sai kuka take tana kallon Elder Ya saddar da kanshi kasa don baya son raunin zuciyar shi ya hana shi kashe ta.


a jikin fankar Suka ɗaure kafafuwanta gangar jikinta da kanta suna kallon ƙasa, Da ido yayi sihiri Nan take Kasan inda kanta ke kallo ya wawake ya zama katon rami


wata irin wuta mai balbali ta kama ci...lokacin da hucin wutar Ya fara ta6a kanta, wani irin azababben kuka ta fashe da shi kamar ana zare ranta, wani irin radadin azabane ke rabar kowani sashe na jikin ta, cikin shesshekar kuka Ta dinga yi mashi magiya akan ya kwance ta, Kada ya kasheta ko dan darajar ya'yan dake tsakaninsu amma saboda rashin imani  irin na Elder cikin sauri Ya juya Gints suka rufa take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta.


Ita kadai baiwar Allah ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle tace zata kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta.


sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar daukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke da alama dai Khala rai yayi halinsa, wutar harta rufe ta....Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un 😭😭😭


After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

2 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Thank you, but I'm not happy for owais and his team for losing 😭 Allah sarki unaisa ko ya zatayi🤔😨 Danish Allah ya fito mana da Kai lpy

    ReplyDelete
  2. Wayyo Danish din mu abun tausayi 😭 please don die we need you 😍

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post