Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete
Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete

Takun Ƙarshe

Ex-Prisoners💓

Gaba ɗayan su suna zaune kan sofas na falo.

"Aunty ummi wai yaushe angel dinmu zata dawo gida ne? Jemimah ce ta faɗa tana faman haɗe fuska.


Sajeed yace"ni ma na damu da rashin dawowarta gashi tun jiya ko awaya bata kira munji muryarta ba.."


Batool tace"dan Allah aunty ummi ki kira mana ita mu gaisa, ko hankalinmu ya kwanta" tayi maganar tana kallon Ummi, gaba ɗaya hankalinta yana akan wayar hannunta da alama chatting takeyi batasan ma me suke cewa ba.. 


"Dama kun daina wahalar da kanku gurin yi mata magana, saboda hankalinta ba akanku yake ba.." acewar Parvin.


ɗaga murya batool tayi"Aunty Ummi..." aɗan firgice ta ɗago da ido tana kallon ta"batool! Lafiya kike kwala min kira kamar baki san ina akusa ba"? Dariya su naufal sukayi

Batool ta marairaice mata fuska"aunty ummi muna ta yi maki magana kin yi shiru baki amsa mana ba.." maida hankali tayi akansu 


"Okey, Ina sauraronku lafiya"?


Kafin wani ya furta magana acikinsu ba zato ba tsammani, sallamar Unaisah Ta katse masu hanzarin su, kusan atare suka miƙe da gudun gaske suka nufeta hada masu tuntu6e garin sauri, Batool ce ta fara karasawa gareta ta faɗa jikinta suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya sai faman tikar dariyar murna sukeyi, gaba ɗaya sukayi mata rumfa kamar zasu lasheta yadda kasan sunyi shekara basu ganta ba,

Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya bayan daya tayi hugging din yan mata, sajeed Ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin  ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi saboda gudun kada ta samu ciki.



*_______________________________Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*




Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya baya daya tayi hugging din yan mata, sajeed ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin  ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi, gani take kamar ciki zai shiga, har naufal ya kai hannu zai yi hugging dinta again ta ƙara ja da baya hadi da girgiza kan ta, mamaki ne ya kama su Naufal ganin yadda ta hana su ta6a ta kamar taga wani mugun abu. 


"Meyasa mu bazaki rungume mu ba, ko bakiyi kewarmu ba"? murmushi ta sakar masu"kuyi hakuri ba haka bane, nayi missing dinku gaba ɗayanku.." girgiza kai sajeed yayi ni ban yarda ba Allah, naufal yace"kinfi son su batool shiyasa kika rungumesu ko"? Javed ma yace"ni banji dadi ba, wariya kike nunawa atsakanin mu.." gwalo parvin tayi masu, Sarah tace"nan fa ba prison bane, mun riga da mun gane jinsin mu, ku maza mu mata don haka kuyi hakuri no more hugs atsakanin mu ehe" dariya suka sanya.


Batool tace"bayan haka aunty ummi ta fada mana babu kyau mace ta rungume namijin da ba muharramin ta ba, koda ruke hannunsa ne"  wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Unaisah dake sauraronsu taji dadin yadda suka fara gane abunda ake koya masu.


Gaba daya kalamansu akan kunnan chief dake abakin kofar shigowa falon maganar Batool ta faranta ranshi dama yajima yana son a fahimtar dasu game da mannewa juna da sukeyi amma yanzu alhamdulililah sun fara hankali


Mubeen yace"amma ay a prison mu na yi kuma baku ta6a hana mu ba"

Harara Parvin ta watsa mashi"ay lokacin muna a jahiliya period ne, yanzu kan mage ya waye..."


maganarta ta basu dariya, fashewa ummi tayi da dariya ashe tana tsaye abayansu.


Unaisah na ganinta tayi sauri nufarta suka rungume juna

"Oyoyo my babe Unaisah, welcome back home munyi kewarki abar kaunarmu"  


"Nima nayi kewarku aunty ummi fatan na same ku lafiya..." ta fada tare da dago da kanta


"Lafiyalou Unaisah, ya jikin patient din? Ko har an sallame ta"!


"Yau za'a sallame shiyasa na taho gida, taji sauƙi sosai, tama ce in gaishe mata da ku" murmushi ummi tayi"Allah sarki muna amsawa, wlh naji dadin samun lafiyarta..." 



Kallon su Naufal tayi sun haɗe fuska babu annuri duk don saboda taƙi hugging dinsu, jemimah ta tuntsire da dariya tana fadin wai ma haushi suke ji don kinki rungumarsu jibar su ma kattai da su.."bata ƙare maganar ba, Sajeed Ya tallabi keyarta nan take ta fara ta6e baki zatayi kuka, 

Naufal Ya ɗaga hannu zai buge bakin da sauri ummi ta ruƙo hannun shi tana dariya tace"ya isa haka pls, wasa takeyi maku" 


"Pls Angel, To mu gaisa da hannu" Sajeed Ya fada tare da mika mata hannu shi, shiru tayi jimm har ta miƙa hannu zata ruko nashi ba zato ba tsammani chief ya shigo falon yayi hanzarin daura hannunshi akan na Sajeeed, gaba daya suka shiga nutsuwarsu sam basu san da zaman shi ba.


cikin girmamawa suka fara gaishe da shi, ummi ma ta gaida shi ya amsa mata, Sajeed baki ya ki rufuwa saboda sunyi musabaha da chief, yaƙi sakar mashi hannu.



"Pls chief can you hug me"? Ɗaga mashi gira chief yayi tare da yin huggin dinshi, wani irin dadi ya lullu6e shi.


"Nima pls" acewar Naufa, miƙa mashi hannu yai da sauri naufal ya rungume chief harwani bude hanci yakeyi yana shakar kamshin turaren shi


Kunya ta hana Haris yin magana, lura da hakan yasa chief mika mashi hannu da sauri ya matsa kusa da shi suka rungume juna, bayan ya saki haris Ya rungume javeed da mubeen wayyo dadi, tsabar murna kamar anyi masu albishir da gidan Aljanna, Ummi sai satar kallonshi takeyi saboda kyan da yayi mata, kai ko amafarki bata ta6a tsammanin zata haɗu da chief face to face ba sai gashi cikin ikon Allah ƙaddara ta haɗa ta zama da shi agida ɗaya, ta yaba da hankalinshi, nutsuwarshi, wayewarshi, saukin kanshi da ilminsa komai Allah Ya bashi uwa uba ga tarin Dukiya.



Gaba ɗaya yan matan sun ɗaure fuska, ganin su naufal sun fara yi masu gwalo saboda chief ya rungumesu..." bubbuga ƙafa Jemimah tayi muryarta da shagwa6a tace"wayyo Allah, mu ma dan Allah  yaya chief ka rungumemu..." dariya sajeed yayi tare da cewa"no bazai rungumeku ba, jinsin ku daban namu daban, kowa ya rungumi jinsinsa koba haka ba guys"? Ya fada cike da shakiyanci yana kallon su Javed,

Naufal yace"haba kamar dai a jahiliya period? ay haramunne na mijin ya rungume mace, nan fa ba prison bane kan mage ya waye.. " gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Unaisah hada dafe ciki, chief dake atsaye ya goya hannayenshi kan kirjin shi, idanunshi na akan fuskarta wani irin kallo yake binta da tashi ta saki baki tana ta dariya fararen hakoranta tass da su bata ta6a jan hankalinshi irin na yau ba.. Babu wanda Ya lura da irin kallon da chief yakeyi mata gaba daya ya shagala

A hankali ya kau da idon shi Ya juya Ya nufi part din shi.


"Wallahi inason ku yan uwana, kuna faranta min raina, Allah yabarni daku, wallahi mai rabani daku sai Allah, shiyasa naketa zumudin in dawo gida saboda nasan anan ne kadai zan samu farin ciki da kwanciyar hankali...." cikin jin dadi tayi maganar,

Ummi ta ruko hannun"mu shiga daga ciki, mun barki atsaye.." gaba ɗaya suka nufi Sofas din falon,  kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, shi dai sajeed kalmar muharram ta tsaya mashi arai, so yake yaji wanene muharramin nan da shi kadai zai iya rungumar mace, abun da bai sani ba ita kanta Batool din batasan wanene muharram ba, tabbas ummi ta ta6a faɗa mata amma karatun bai zauna akanta ba.


"Kinyi breakfast acan asibitin" cikin kulawa ummi tayi mata maganar,

"Eh, nayi" labari ta fara basu na Benazir duk suka kasa kunne suna sauraranta

"Matar tana sona nima ina sonta aunty ummi, mun shaku da juna, har grandma dinta muna mutunci da ita dayake adaki daya muke kwana kuma kinsan wani abu aunty ummi.." girgiza mata kai tay alamar a'a


"bata gane cewa ni ba yarta bace, bansan wani hali zata shiga ba idan ta farka daga bacci taga bani akusa da ita..." cikin sanyin murya tayi maganar.


Ummi tace"baiwar Allah, wallahi ta bani tausayi, ubangiji Allah Ya bata lafiya, inayi mata fatan Allah ya bata wata yar" suka amsa mata da ameen


"Wani abu daya bani mamaki aunty ummi, matar tana kama da Batool yadda kikasan ita ta haifeta Allah..." murmushi ummi tayi, batool ta washe baki jin an ambaci me kama da ita"wallahi har naji ina son ganinta" murmushi unaisah tayi"hmmm ai ba ita kadai ke kama dake ba, ranar dana fara ganin yayanta dr shureim saida na ɗan razana, yadda kikasan yayi kakinki, ke gaba dayansu kamar family dinki ne..."  wani irin faduwar gabane Ya darsu a zuciyar Ummi, sunan dr shureim da Unaisah ta faɗa ya tsaya mata aranta.


"Dan Allah daske kike? Acewar batool,

"Wallahi dagaske nake, Allah ya zuba masu ruwan kyau, grand ma dinta balarabiyace..."


dafe kai ummi tayi da hannu ɗaya, gabanta na cigaba da faduwa.. Gaba daya sun lura da yanayinta, 

"Aunty ummi lafiya" da sauri ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace ba komai unaisah, can kuma tace.


"Unaisah, kikace sunan yayanta dr shureim! Ita kuma Ya sunan ne"?




Murmushi Unaisah tayi kafin tace"Aunty Benazir"  ummi tayi jimm kamar mai nazarin wani abu.



"Namanta ban fada maku, wani abun farin ciki daya faru ba.." har suna hada baki wurin furta"menene" dariya ta danyi kafin tace"kun tuna auntyna da nake yawan baku labarinta a prison" kallon juna sukayi batare da sun iya gano wacece ba.


"Duk wanda ya tuna sunanta zan bashi kyauta ta musamman" ta fada cike da nishadi


Nan fa suka fara canki canka,

Hawwa tace"na tunata, sunanta Aunty adama" girza kai unaisah tayi"a'a ita wannan mommy adama take"


"Kamar aunty bahijja ne" acewar hibba, dariya unaisah tayi"no ba haka sunan yake ba"


Sajeed yace"Sunanta aunty laila" dariya unaisah tayi"no ba haka bane Allah indai baku fada ba, bazan baku tsarabar da nayi maku ba.." ta fada tana karkaɗa kafarta gaba ɗaya kamar ta manta da zancen Danish kamar an goge mata tunanin shi a brain dinta.


"Sunanta Aunty Aneelerh, indai ba haka sunan yake ba to kuyi min dundu abayana" dariya Unaisah tayi tare da kallon batool"kin canka dai dai, aranar kafin in bar gida kunsan meya faru...."? Girgiza mata kai tayi, nan fa tafara basu labarin zuwan aunty Anila ko gajiya batayi, sai surutu takeyi kamar parrot, gaba daya hankalin ummi baya atare da su, kamar bata acikin nutsuwarta har saida kunnuwanta suka jiyo mata muryar Unaisah tana fadin"ashe ita aunty aneelerhn kawar aunty Benazir dince, atare mukaje asibitin abun da ya farantamin rai Aunty Aneelah ta haifa min dan kani sunan shi baby junaid, tama yi min alkawarin zata kawo min shi har gida..." wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Su Batool.


"Wayyo Allah Angel maimakon ta shigo mu gaisa da ita, meyasa baki fada mata irin kaunar da muke yi mata ba.." parvin ce tay maganar, batool tace"Yaushe zata kawo mana ɗan kaninmu junaid mu gan shi, wlh munji dadin haduwar ki da aunty Aneelerh, saura muma mu hadu da ita amma dai zatazo nan ko"? Daga masu kai tayi"don ma namanta ban kar6i number dinta ba, amma zan ma daddyna magana nasan bazai rasa layinta ba"


"Unaisah! da sauri Ta kalli ummi na'am


"Wai ni kam dama can anan abuja kuke zaune keda daddynki"? Girgiza kai tayi"a'a a joss muke" gaban ummi ne ya ƙara faduwa, karfin hali tayi wurin furta"okey, amma ita auntyn naki Aneelerh, ya kike da ita ne? Ta fada cike da son jin karin bayani


"Matar uncle dina ne Uzair"


Shiru ummi tayi bata kara yin magana ba 


Motsin shigowar mutun a  falon ne Yaja hankulansu ga kallon kofar, Senior agent din da ya kai su Unaisah mall ne ya shigo hannun shi ruƙe da shopping bags, ya goyo backpack dinta abayan shi, miƙewa tsaye sukayi suna jiran ya karaso

A tsakiyar falon Ya ajiye mata shopping bags din kafin Ya sauke backpack din bayanshi ya ajiye ta"i'm sorry na tsaya amsa kira ne"_ murmushi tayi tare da cewa nagode sosai"

Yace"Never mind" ya fada tare da juyawa ya fuce daga falon

Gaba ɗaya suka zagaye bags din suna kallon su ummi tace"tsarabar mu ce wannan"? Unaisah tace"eh nakune, nima akwai nawa ciki"


Zukunnawa ummi tayi agaban shopping bags din A hankali ta fara curo kayan tana ajiyesu kan rug, su Azeeza sai tsalle suke suna murna ganin cookies da chocolates kala kala dama mayinsu ne, kamar shazu mamu suke wurin shan zaki.


Tun kan aje ko'ina suka fara kokarin kai hannu zasu ɗauka, ummi tace su tsaya ta raba su.


"Unaisah wadannan uwayen kaya haka? Wanene ya siya maki su?  da mamaki ta fada tana kallon fa.."


"Atare da chief mukaje shopping mall, bakiga wurin ba ya hadu, ni fa bani na zabi kayan ba, shi yace mutumin daya kawo kayan komai yaga idanuna sun kalla ya daukar min shi ko da mara amfani ne" jinjina kai ummi tayi cike da mamakin maganar ta maida dubanta ga kayan, gasunan tili guda.


ta fara ɗaga kayan tana ambaton sunayen su a fili, Fragrance set, hair accessories, gel nail kit, skincare set, jewelry box, lace robes, slippers, diary with a lock and key, throw blankets, shaving kit, smartwatches, earbuds, sports jersey, bluetooth speaker, da sauran su ga Writting material kala kala, can idon ta ya hango mata bras har kala uku da yan panties biyu, dagowa tayi tare da kallon unaisah baki asake tace"waɗannan fa"? Dariya Unaisah tayi tare da sunnar da kanta ƙasa wata irin kunyace ta kamata"wlh Aunty Ummi bansan hada bras acikin kayanba, sune suka daukarmun" dariya ummi tayi"ah toh ni dama nasan bada saninki ba, wannan ay sai dai Batool duk da bansan size dinta ba amma nasan zasuyi mata, ke kuma saiki bari in naki sun kara cukowa" gaba ɗaya su Naufal suka tsuntsire da dariya, daure fuska tayi rai a6ace take aika masu da harara, ummi tace"ku kuma meye nayi mata dariya kawai daga anyi abu cikin raha" kumshe dariyar sukayi


"Sorry my babe, kada ranki ya 6aci, ni da wasa nayi maganar" ta6e baki tayi tana faman wurga masu naufal harara.


Ummi tace"abun dai da yawa wlh, ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi.." ta fada tare dakai hannu tana kara dudduba kayan"suma dai waɗanda suka daukar maki kayan sun iya taya 6era barna.."ta fada tana yar dariya.


"Hada phone, bayan kina da waya? Da sauri unaisah ta kalli phone box din"


Da sauri batool tace"dan Allah sister ki bani dama bani da waya..." saejeed yace nima inaso dan Allah, haris yace wlh na riga ku dan Allah ni za'a ba, rigima suka sanya da sauri unaisah ta ɗauke phone box din, ta ruƙe a hannunta, ummi tace"kin raba gardama, ki ajiyeta agurin ki" ta amsa mata da toh,


Kwashe kayan Unaisah da Ummi sukayi atare su ka maida su cikin bags din, ummi ta dibar masu chocolates da cookies ta rarrabamasu kowa ya buɗe nashi yana ci, sauran tace"za'a ajiye su adakin unaisah, duk rana zamu dibi kaɗan mu sha idan ba haka ba nasan ba zaku raga masu ba, duka zaku shanye su" amsa mata sukai da toh.


"Unaisah ke da Batool, Ku kwashe kayan ku kai dakin ku, ku ajiye su dakyau" atare suka amsa mata da toh, kafin suka fara kwashe jakukku nan suka kai su dakin su.


 *UNAISAH ANGEL*


Around karfe biyu na rana, tana a kwance kan bed dinsu ta ɗaura kanta bisa pillow, ta ɗan lumshe idanunta bakomai take tunani ba face Aunty Benazir, tun bayan data dawo gida hankalinta yaƙi kwanciya ta damu da son sanin awani hali take a ciki? Meya faru bayan ta farka daga bacci? 



"Ya Allah kasa kada aunty Benazir tayi kukan rashina, bana son tayi maraicina rashina akusa da ita! Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana taje wurin chief ta tambaye shi awani hali Benazir din take a ciki tun da yar uwar shi.


da sauri ta sauko daga kan gadon, ta dauko mayafi ta yafa akanta, taje gaban Shopping bags din da suka ajiye ta ɗauki ɗaya ta zazzage kayan cikinta a gidan drawer, ta ɗebi turare biyu ta hada da chocolates da cookies kala shida ta sanya a ciki  tasan ma ba lallai ya kar6a ba, kawai tayi tunanin takai mashi ne.


Miƙewa tayi hannunta ruƙe da ledar da sauri ta fuce daga dakin atsanake take tafiya.. 


Adaidai lokacin Danish Ya fito daga bedroom din shi yana daga tsaye a second floor, ya sanya singlet da boxer shorts a jikin shi, ya dafe handrail da hannayen shi, yana bin down stairs da kallo kwatsam idanun shi suka hango mashi ita, kamar a mafarki Yake kallonta, kwata kwata baisan ta dawo gidan ba, saboda bai fito waje ba, yana adakin shi yana karatu bacci ya ɗauke shi bayan ya farka ya shiga bathroom yai wanka hakanan yaji yana sha'awar fitowa waje yasha iska cikin ikon Allah yaci karo da ita...


Yaji dadin ganinta sosai, har saida yaɗanyi murmushi dimples dinsa suka lotsa, ji yayi kamar yaje gurinta yayi hugging din ta ya faɗa mata irin kewarta da yai, sai dai yasan ba abune mai yiwuwa ba, saboda sharuddan data gindaya mashi, kuma yayi alkawarin bazai ta6a karyawa ba, in har ba ita da kanta ta janye kudurinta ba. 


Yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, zuciyar shi ta karaya ganin ta nufi upstairs kuma yasan bai wuci part din chief zataje ba, duk yadda ya kwallafa rai akan son ganinta amma ita bata damu da shi ba kamar ma ta manta da shi, da ace lokacin bayane kafin su samu sabani yasan shine mutun na farko da zata fara nema idan ta dawo daga wani guri.


Kifa kan shi yai jikin handrail din yana jin wani irin ɗaci aran shi....


Lokacin da ta je part din chief bata iske shi ba, sau uku tana yin knocking bai buɗe ba, ranta ne ya bata ya fita hakan yasa ta juyo ta nufi stairs a hankali take taka matakalar, ranta ne ya bata kamar ana kallon ta, da sauri ta wurga eye balls dinta tana bin downstairs da kallon ganin ba kowa yasa ta maida dubanta ga second floor ganin zata ganshi yasa shi sauri juyawa ya buɗe room door dinsa zai shiga tsayawa tayi cak da yin tafiya tana kallon bayan shi har saida ya shige..


"Danish" acikin zuciyarta ta ambaci sunansa, sam takasa karasa cigaba da tafiya sam ta manta da shi sai taji wani irin a zuciyarta kamar bata kyauta ma shi ba.


ganin shi da tayi yasa taji kewar shi ta mamaye ta sai dai bata jin zata iya zuwa gurin shi, ta san dalilin dayasa shima baizo gurin ta ba, saboda alkawarin da ya daukar mata, tun a prison tasan halin shi da ruƙe alkawari in har ba ita ta janye sharuddan ba, danish bazai ta6a kusanta kan shi da ita ba koda hakan zaiyi silar da zuciyarshi zata daina bugawa ne, shiyasa ta matsa mashi akan ya daukar mata alkawarin don tasan ta hakanne kadai zasu nisanta da juna.


Ƙwallace ta cicciko idanunta jikinta yayi sanyi lakwas ji take kamar bazata iya jure rayuwa guri ɗaya da shi, batare data kusanta kanta da shi ba, har yanzu akawai kaunar shi a zuciyarta kuma har abada bata jin zata iya daina son shi, la66anta na kerma ta furta"I'm Sorry Danish, bani da mafita ne, nasan dagani har kai zamu cutu amma muyi hakuri da juna na ɗan wani lokaci..." karasa saukowa tayi daga kan stairs din ta nufi bedroom dinsu, tana shiga ta iske Batool zaune kan mirror chair, da alama ita take jira 


Jin motsin shigowarta yasa batool ta kalle ta


"Sister ina kika je? Muna ta jiranki a adining, kizo mu yi lunch"


In a low voice ta furta"pls basai kun jira ni ba, kuje ku ci abincin ku, zan zo"


"Toh" Batool ta amsa tare da saukowa ta fuce daga dakin


Zukunnawa tayi agaban drawer chest, ta buɗe ta karo chocolate da cookies masu yawa ta tura a jakar hannunta, ta dauko shaving set tana tunanin ko zai bukace su? mezaiyi da su, danish bashi da gashin da zai aske cos ta san shi tun a prison haka halittar shi take bai da underarm hair, hatta fuskarshi smooth take ba gashi, hakanan dai ta sanya mashi a jakar, ta ɗauki sport jersey ta sanya mashi, gani take kamar kayan sunyi mashi kaɗan, sai da ta kara mashi wasu akai, ta curo paper da pen ta rubuta mashi


"I'm back, my man. I hope I find you safe. nayi kewarka, ga tsarabarka nan, Take care of yourself for me." 



acikin shopping bag din ta sanya mashi letter din, sam ta manta bai iya karatu ba, ita a tunaninta ya fara iyawa tunda daddynta ya fada mata chief ya fara koya ma shi, mikewa tayi da sauri ta fito ta nufi upstairs, a bakin kofar dakin shi ta ajiye mashi kayan, ta sanya hannu tayi knocking kafin ya fito ta watsa da gudu ta sauko down ta dawo bakin room door din su ta tsaya tana leken shi.



Lokacin daya fito baiga kowa ba, har zai juya yai tuntu6e da shopping bag din da sauri ya dubi jakar, yayi mamakin ganin ta baisan wanene ya ajiye mashi ba.


Zukunnawa yayi tare da buɗe jakar, ya fara zaro kayan yana kallon su, akan idon shi letter din ta fado ƙasa da sauri ya dauka ya buɗe yana kallon rubutun shiru yayi jim ya rasa gane me aka rubuta bawan Allah, Ya shafe mintuna yana harhada haruffan amma ya gaza karantawa, handwritting ɗin ta ya haɗu saika rantse da Allah babban mutunne Yayi rubutun saboda ƙwarewarta.


Unaisah dake a la6e tana leƙen shi fuskarta ɗauke da murmushi sai dadi take ji amma data fahimci ya kasa karantawa sai taji wani iri aranta, daga inda take ta yi mashi gyaran murya kafin ya ɗago da ido ya kalleta tayi saurin juya mashi baya ta ruke qugu da hannu, ta yi mashi hakanne don yasan cewa itace ta kawo mashi kayan.


Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, nutsuwa yayi yana kallon bayanta har saida ta shige daki kafin ya tattara kayan ya maida a cikin jakar ya mike da sauri ya shiga dakin shi bayan ya daura jakar kan gado, ya ɗauko paper da pen ya  daura kan bedside drawer ya fara kokarin yin rubuta, bawan Allah idan yana so ya rubuta Ni sai ya fara daga Na ni no nu ne kafin ya canko wadda ta dace ya sanya..


Dakyar ya samu ya rubuta mata letter ɗin ya mike da sauri ya fito ya sauko down Yaje bakin kofar dakinsu Ya ajiye mata tare da yin knocking ɗin  kofar, kafin ta fito yayi saurin komawa upstairs Ya tsaya yana jiran ganin ta


Tana fitowa taci karo da letter din daya ajiye mata, zukunnawa tayi tare da daukar takardar ta buɗe ta...


"Welkam bak hom, i miss yu so much, tanku" hawaye ne suka ciko idanunta wani irin tausayinshi ne Ya kamata da sauri ta dago ta kalle shi hannu ya ɗaga mata, a hankali itama ta ɗaga mashi hannu sai yanzu ta gane ashe shine ya tura mata text message awayarta lokacin da tana a hospital, hartana dariya tayi zaton karamin yarone ya dauki wayar babarsa.. 


Juyawa tayi da sauri ta koma cikin dakin su, ta dauki wayarta dake kan mirror, ta kwanta kan gado ta fara scrolling ta shiga messages dinta, murmushi tasaki tana kara karanta sakon shi bata san sa'adda kuka ya kubce mata ba...cusa kanta tayi jikin pillow tay kuka mai isarta kafin ta share hawayenta ta dago, ta kalli screen din wayar, yanke shawarar kiran shi video call tay, da number din daya tura mata sako ta danna mashi call yana shiga yai picking"Turn on your Wi-Fi, I'll call you on a video call." ta faɗa tare da katse kiran bata jira amsar shi ba, fatanta Allah yasa ya iya kunna wi-fi din, ta kunna na wayarta har zata danna mashi video call, Unexpectedly, taga kiran shi ya shigo via facetime.


Picking tay tare da kanga wayar saitin fuskarta ta ƙura ido tana kallon doguwar fuskar shi abun da ya ɗaure mata kai ya lumshe idanun shi, da alama akwance yake kan gadon shi ya tada kai saman pillow kamar yadda tayi.


Ta ɗan yi mamakin canzawarshi, kamar akwai rama ta wurin kwarin idanun shi fatar wurin tayi jajir ga zira ziran eye lashes dinshi da suka ƙawata kewayen idanun, la66an shi sun bushe ƙamas launinsu ya ƙara ciza wa, ga wani haske da yayi skin dinshi har salki take, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi har saida taga ya fara kokarin buɗe idanun shi kafin tai saurin kau da nata gefe, kallo ɗaya da yayi mata saida yaji wani irin yanayi atare da shi, ta canza mishi ta ƙara yi ma shi kyau kamar yaune rana ta farko daya fara ganin ta haka ya nutsu yana kallon soft pink lips dinta, kafin ya maida duban shi ga grey eyes dinta, taƙi yarda su haɗa ido sai dai ta wutsiyar idonta take satar kallon sexy face dinsa ta screen din wayar..


"Tell me, have you forgotten me? Are you still angry with me? Or have you stopped loving me?"


Sanyayyar muryar shi ce ta ratsa kunnanta, har saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta furta"bana fushi da kaina, ban manta da kai ba, kana araina, kana tunanin daina sonka abune mai sauƙi agare ni"?


Lumshe idanun shi yayi, yana jin nutsuwa tana shigar shi, kalamanta sun sanyaya zuciyar shi.


"If you're even thinking about that, you should stop" ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kamar yadda nayi maki alkawari bazan ta6a karyawa ba, amma inaso mu dinga yin magana ko da ta waya ne pls give me permission to call you every day" ya faɗa yana kallon fuskarta yadda kasan suna aguri ɗaya.


"Okay, I give you permission, but you will call me only two times, and you can send me a message anytime, idan na gani I will reply to you immediately. After that, I don't want anyone to know what is going on between me and you, in har muka haɗu a falo ko hanya ta haɗamu indai ina atare da wani zan iya yi maka magana kaima haka..." tana magana idonta na kallon gefe ɗaya kwata kwata bata son su haɗa ido saboda yanayin da yake jefata kuma idon tana kallon shi, sai zuciyarta ta dinga tariyo mata abunda ya faru adaren ranar daya shugo dakin su.


Shiru taji bai amsa mata ba, sai ma motsin buɗe leda da taji a kunnanta, aranta ta ayyana ko meyake ki? ko dai ya ajiye wayar ne? A hankali ta ɗan saci kallon screen din karaf idanunta suna shiga cikin nashi lokaci ɗaya taji faɗuwar gaba.


Hankalinshi kwance yake kallon ta, Yana cin chocolate din data kawo mashi, yanayin yadda yake moving lips dinsa, sai taji wani iri zuciya da sake sake sai taga kamar da gangan yake don ya rikitar da ita cos he looks so sexy a yadda yake shan chocolate ɗin har wani lumshe idanun shi yakeyi alamar dadin yana kai mashi karo, sam takasa janye idanunta daga kallon lips dinsa, hatta yanayin fitar numfashin ta saida ya canza lokaci ɗaya ta nemi zaucewa da sauri ta kifa wayar jikin pillow tayi shiru tana jin wani irin abu mara misaltuwa ta rasa gane me yasa take jin hakan? chocolate kawai ya bude yana sha duk ta rasa sukununta har wani shauƙi take ji a jikin ta.


"Hello, Angel? Are you there? Muryarshi ce ta fargar da ita


Numfasawa tayi har ta fara motsa lips dinta zata bashi amsa muryar daddynta ta katse ta"daughter! Kina ina? Shi ne kin dawo ko ki neme ni ko"?



Cutting din kiran tay, ba don ta gaji da kallon shi ba, ta miƙe da sauri ta sauko daga kan gadon, ta nufi door room din ta buɗe, yana atsaye bakin kofar fuskarshi dauke da murmushi yake kallonta"welcome back, my Angel" hugging dinshi tayi, fuskarta dauke da murmushi ta zagayo da hannayenta kan bayanshi"daddy ina wuni ya aiki, Ya aunty danejo na, wlh nayi missing dinka, kana araina tunda na dawo nake ta dakon zuwan ka.." dago da kanta yai daga kirjin shi ya dubi fuskarta dakyau"nima nayi kewarki, ay na yi zaton zaki kira ko awaya ne ki fadamin kin dawo gida, ni gaskiya ban yarda kinyi missing dina ba, kina can kin samu uwa kin manta dani ko"! Ya faɗa da zolaya

Girgiza kai tay"a'a daddy, ba haka bane, ay bani da tamkarka a duniyar nan, mu shiga ciki kaga kayan da chief ya siya min..."


Taja hannun shi suka shiga dakin, cike da zumudi ta dauko shopping bags din ta buɗe ta fara curo kayan daya bayan daya tana nuna mashi

Waro ido ya ɗanyi alamar mamaki yace"Eyeh gayu mutanan Allah, duk ke kadai wannan? Amma naji dadi ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi Allah Ya ƙara mashi buɗi da daukaka"


Fuskarta dauke da fara'a tace"ameen daddyna, wlh nima nayi mamakin kayan daya siya min amma fa bani kadai ba hada su Batool yace in daukarmawa inyi masu tsara..".


"Kin nuna ma auntynku"


"Eh, harma ta dibar mana chocolates da cookies sauran kayan tace mu ajiyesu adaki kafin lokacin da zata raba mana"



Murmushi yayi har cikin ranshi yaji dadin jin chief ne ya je da ita mall da alama burin shi Ya kusa cika na ganin Ya kulla alaka mai karfi atsakanin su.


"Daddy, na jima banga mutun mai mutunci irin chief ba, yana da saukin kai, ga shi wayayye ni dama can inason mutum irin haka..." ta saki baki tana surutu cikin rashin sani ta zazzago bras daga cikin shopping bag din dake ruke a hannun ta.


Waro ido taj yai cike da zolaya ya furta"Subhanallah, daughter wannan fa na wanene"? da sauri ta dube su, wata irin kunyace ta kamata, da sauri ta sunkuyar da kanta kasa sam ta kasa kawar da su"


Taj dake kallonta dariya ce kumshe abakin shi bai ta6a tsammanin Angel tana da kunya har haka ba.


Tunawa yai lokacin da tana karama har fadi mashi take dan Allah ya siya mata ƴar bra irin na aunty anila idan ta girma boobies dinta suka fito itama ta dinga sakawa, ranar yaci dariyar maganarta, komi tagani anila tayi itama sai tace zata yi idan ta girma, anila itace silar da Angel ta fara kwadayin tayi aure ay gani take babu rayuwar da tafi dadi irin ta gidan aure. Tasha fada ma taj itafa house wife takeso ta zama, kuma bazata auri talaka ba, saboda ita matar manya ce, hamshakin mai kudi zata aura, inda zata sakata ta wataya bata aikin komai sai dai yan aiki suyi mata ita tana daga kwance, shiyasa taj yakeso yacika mata burinta, bawai don kwadayin abun duniya ba sai don baya son yakaita inda zata sha wahala, saboda ta cancanci tayi rayuwar farin ciki, ta auri miji nagari nagartacce.


Jin yayi shiru bai ƙara tanka mata bane yasa ta dago da ido ta saci kallon shi, hankalin shi kwata kwata baya akanta, yayi zurfi cikin tunanin shi, da sauri ta kwashe bras din ta tura a cikin shogging bag din, kafin tace"daddy! " kallon ta yai"meye faru naga kamar kana tunanin wani abu" murmushi yayi mata.


"Ke nake tunani" farfari tay mashi da ido"me kake tunani akaina" calmly ya furta"inaso ki faɗamin gaskiya kina son aure har yanzu"? Rass taji gabanta ya faɗi da sauri ta cusa kanta tsakankanin gwiwowinta, yar dariya yayi"wai ni waya koya maki jin kunya? Kamar ba Angel dina ba, ko dai anyi min musayarki ne"?

Muryarta kasa kasa tace"a'a dadi ni din ce dai daka sani, Angel dinka,"


"Okey, fadamun amsar tambayar da nayi maki'!


Miƙewa tayi da gudu ta shige toilet, taja kofa ta datse, murmushi yayi yana kallon kofar.


Daga cikin toilet din yajiyo muryarta"daddy zan baka amsa ba yanzu ba, ka ɗibar ma aunty danejo tsarabar da nayi, kaima ka dauka..." dariya yayi haɗi da girgiza kan shi yana kallon kofar toilet din.


Chocoletes da cookies ya dibar masu  a dakin ya samu plastic bag, ya sanya a ciki, kafin ya mike yana fadin"ni zan wuce toh, ba zaki fito muyi sallama ba"


Dakyar ya samu ta fito daga dakin, tana faman noƙe kai taje gaban shi ta tsaya"na manta ban tambayeki ba, ya mai jikin?


"Taji sauƙi sosai, wlh kamar kar in barta, ina kaunarta sosai, lokacin ma da zan tafi, saida dr jazz ya bani sleeping pill na bata tasha saboda bazata bari atafi dani ba.." muryarta na rawa ta kare maganar kamar zata sanya mashi kuka"daddy dan Allah  zuwa jibi ka kaini gidansu daga nan sai muje gidan su aunty anila inason inga babynta.." tun da tafara magana ya kafe ta ido yana kallonta, mood din fuskarsa ya canza sosai, tsantsar tausayin su ne ya kama shi, dama yasan dole su kaunaci juna, jini ɗaya ba wasa ba, tsakanin uwa da ɗa sai Allah.


Cikin sanyin murya yace"ki kwantar da hankalinki, kada ki sanya damuwa aranki, zan yi kokarin kaiki gurin ta, amma ba yanzu ba, ki ƙara hakuri, ita kuma auntyn naki zan baki contact dinta, ki kira ta waya ku gaisa sai kiyi mata maganar junaid din nasan zata kawo maki shi" 


Nagode daddy,"da murna tay maganar, Taje ta dauko wayar ta bashi ya sanya mata layin aunty Anilah


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post