Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 58 Complete by Boss Bature


Health College

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 58 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Jikinta yai tsauri har tsawon kwana Uku  batasan inda kanta ya ke ba, abu daya da take iya furtawa sunan My man da yaki barin bakin ta, sai da takaiga kullum sai docs sun banka mata Sedative injections saboda bugun barazanar da zuciyarta keyi mata ta hakanne kadai suke Iya sarrafa ta har su samu tayi bacci, duk da karfin allurorin da sukeyi mata hakan bai hana ta yin sambatu akan shi ba, saboda shi ne aranta, su kansu docs din dake duba lafiyarta sun tausaya mata matuƙa sun kumayi mamakin kaunar da takeyi ma shi, a cikon kwana na hudu ne ta dawo hayyacin ta sai dai bata iya magana kamar kurma sai dai tabi mutane da ido, saboda bakar azabar ciwo data sha har rama tayi, kwana uku kamar wadda tayi shekara Tana jinya saboda fadawar da tayi, har addu'ay tay Allah ya dauki ranta ta huta ko ta huta da radadin da zuciyarta keyi mata, bata ta6a dasanin bata masa rai da ta dinga yi ba sai yanzu da babu shi duk in ta tuna rayuwarsu a kurkukun da jan shi fada data dinga yi yana kyaleta tayi azaton baida karfi tsoronta yake ji ashe yana da karfin da zai iya ramawa amma saboda kaunar da yake yi mata ya dinga kyaleta saboda baya son ya cutar da ita, Ya Ilahi tay babban rashin da har abada ba zata ta6a samun madadinsa ba😭 

Ba irin nasihar da ummi batay mata ba akan tay hakuri ta rungumi kaddara, shima taj yana kokarin yi mata nasiha amma abun yaci tura zuciyarta taƙi bata hadin kai, azabtar da ita kawai takeyi, duk da haka basu fasa lallashinta da kwantar mata da hankali ba ta ko'ina take samun kulawa musamman docs da nurses din dake kula da ita.


A ranar da suka Cike kwana hudu  Chief ya ce a sallame ta, Duk da docs sun ce lokacin sallamarta baiyi ba, ya nuna yafi son A sallame tan su koma gida inyaso sai acigaba da yin jinyarta  acan, badan sunso ba suka bada sallamar Unaisah.


Abun dayasa Chief ya nemi su sallame ta saboda Hankalinsa bai kwanta da zamansu a asibitin ba, yana yawan Jin faduwar gaba aduk lokacin daya zo dubata, duk da ba ita kadai ke kwana asibitin ba shi ya nemi alfarmar Abar ummi da Batool su zauna gurinta yayin da Taj da Chief suke zuwa dubasu sau uku arana amma saboda Halin dayake shiga Na jin faduwar gaba yasa shi cewa  A sallame ta, kuma hada ƙarin Obie International Hospital Yana a under Suspect saboda mafi rinjayen matan family dinsu dake haihuwar yara ba araye ba anan asibitin ake kawo su idan suna Labour taya hankalinsa zai kwanta da zaman Unaisah asibitin.



~_______________________________~✍️



*🌹UNAISAH ANGEL💔* 



Slowly take kokarin buɗe idanunta waɗanda su ka yi mata wani irin nauyi ga kasala data baibaye gabban jikin ta, biji biji take ganin kamar mutane kewaye da inda take akwance sai dai bata iya tantance su wanene ba, kokarin ɗago da hannu tayi don ta murza idanunta ko ta samu ganinsu dakyau sai dai kafin tay hakan taji anyi saurin damƙar wuyan hannun nata, hakan yasa ta zare gray eyes dinta tare da wurga eye balls din ta kan wanda Ya ruke hannun nata, da farko sai ta dinga ganin kamar Danish ne la66anta na kerma ta furta"My Man kai ne"? Girgiza mata kai yai"ba shi bane Unaisah, madadin shi ne" 


 ras ta ɗan ji gabanta ya faɗi ganin Chief Owais a zaune kan kujerar dake a gefen gadon su, muryarta kasa kasa ta furta"Chief" lumshe mata idaninshi yayi cikin sauri ta dubi hannun ta daya ruke, Iv drip ne aka sanya mata, goshin ta anade yake da bandage sakamakon raunin da taji ma kanta har treatment sai da akai mata.



"Daughter"! Muryar daddynta taji a cikin kunnanta, da sauri ta wurga eye balls dinta kan fuskarshi, ta kura mashi lumsassun idanunta Yana daga zaune kan wheel chair dinsa a gefen gadon, Fuskarsa da damuwa yayi maganar...


"Sister naji dadi kin fara samun lafiya Ya jikin naki", shiru tay bata amsa mata ba, A hankali ta mayar da duban ta inda suke a zaune ita da Ummi sun kura mata ido suna bin ta da kallo mai cike da tausayawa tsawon kwana hudu rabon da suyi wanka saboda rashin lafiyarta, La66anta na rawa ta furta"Har yanzu Danish bai dawo ba"? 


Sunyi mamakin jin tayi magana kuma sunyi farin ciki da hakan, Shiru sukayi aka rasa me bata amsa, lumshe idanunta tayi tana jin wani irin ɗaci da zafi a cikin zuciyar ta...


"Unaisah" chief ne ya ambaci sunan ta cikin sanyin murya sai ta dinga jin kamar muryar Danish din ta, kasa buɗe idanunta tay, hawayen da suka taru cikin idanunta suka fara zarya kan kuncin ta.


"Ina so ki nutsu ki saurare ni" jinjina ma shi kai tay,


Still Chief bai saki hannunta ba ya furta"meyasa kikeso kiyi ma kanki Illah? Shiru tay bata furta kalma ba..



Cikin sanyin murya ya soma yi mata nasiha mai ratsa zuciya, yace a matsayinta na musulma wadda tayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, wata irin jarabawace bata shiga ba kuma Allah yakubutar da ita, sbd haka tayi hakuri ta rungumi wannan jarabawar, har yanzu bamu shaida mutuwarsa ba, don haka kada ki yanke kauna da rahamar Ubangiji, ni'imomi nawa Allah yayi maki Unaisah, bayan kadddara ta rabaki da mahaifinki kin taba tunanin zaku rayu harku Sake hadu? Bama wannan ba, Kin taba tsammanin zaki fada gidan kurkukun kaddara harki hadu da shi Danish din da sauran yan uwanku? Allah fa shiya hadaki da shi bakisan da zaman shi ba, don a yanzu ya raba ki dashi sai ki nemi butulcewa? meyasa bazakiyi hakuri ki rungumi kaddara ba? Unaisah ki cire damuwa aranki, Kiyi hakuri dukkan tsanani yana tare da sauki, komai mukaga ya same mu da sanin ubangiji shi yasan dalilin dayasa abun ya faru da mu.


Nasihar Chief ta karya zuciyarta, Jikin ta yayi sanyi sosai, Taj yaji dadin yadda Chief ke kokarin shawo kan Unaisah, Hankalinsa Harya kwanta, Ummi da Batool sun nutsu suna sauraron Nasihar chief sun kasa kunne har mamaki sukeyi jin yana magana sosai a yadda sukasan shi da miskilanci.



"rashin lafiyar ki ta haifar mana da rauni a cikin zukatanmu, hankalinmu ba akwance yake ba taya kike tunanin zamu samu kwanciyar hankalin da zamu gudanar da bincikenmu akan Elders? Ko kina so ki mutune batare da kin cimma burinki ba? Girgiza kai tay cikin shesshekar kuka tace"in..ina so na rayu ko dan na daukar masa fansa"


"Good, Docs sun fada mana, Ciwonki kwanciyar hankali da nutsuwa yake bukata, dole ki cire damuwa aranki ki dauki dangana ki fawwalawa Allah komai, In sha Allah zaki ga ribar hakurin da ki kai, yanzu Tsakaninmu da Danish addu'ace kawai"


Cikin shesshekar kuka ta furta"ay ba musulmi bane, ya mutu bai yi imani da Allah ba..."


Kafin chief ya bata amsar maganarta Ummi ta kar6e da cewa"Allah mai rahama ne kuma mai jin kai ne, ba zamu yanke mashi hukunci ba, saboda gaba daya rayuwarsa bayin kan shi bane, hakkinsa ya rataya akan wadanda suka tafiyar da shi, Allah ne kadai yasan menene makomarsa..."


 maganar Ummi ta kwantar mata da Hankalinta har taji sanyi aranta..



A hankali ta dan buɗe idanunta akan fuskar Chief


"Akwai inda keyi maki ciwo"? Girgiza mashi kai tay"No, I'm feeling better now."



"Okay, the doctor will continue coming here for regular check-ups, your aunt will take care of your treatment plan" ya fada tare da nuna Ummi


"Ga daddynki akusa and your sister Batool, Komai kikeso ki fada masu, zasuyi maki in sha Allah, We are all here for you, a shirye muke da mu taimaka maki gurin ganin mun yaƙi abun da ke damun ki har sai kinji saukin jikin ki, In sha Allah zamu share maki hawayenki In har kika bamu hadin kai"


Har cikin ranta taji dadin Kalamai Chief ya faranta mata sosai, ko dan saboda yarda ya nuna damuwa akanta zatay kokarin faranta masu


Ummi ta ce"Ciwonki Yana bukatar kulawa sosai, Dole sai kin cire damuwa aranki in ba haka ba zaki rasa tunaninki ne, Ga mahaifinki nan bashi da koshin lafiya, Ciwonki yana kara jefa shi cikin damuwa, Yakamata kodan saboda shi ki jure Unaisah..." idanunta cike tab da kwalla ta furta"in sha Allah, Chief nagode sosai da kulawarka agareni.." ta fada tana kallon Cikin idanun shi, jinjina mata kai yai batare daya furta kalma ba



Ajiyar zuciya Taj ya sauke kafin ya dubi Chief"ya zamuyi da sauran yaran, nasan hankalinsu ba akwance yake ba, in shirun yai yawa zasu sanya damuwa"


Ummi tace"ɗazu na kira danejo awaya na ce ta kwantar masu da hankali, tace min basu da wata damuwa kawai dai suna tambayar shiru bamu koma ba"


Chief yace"bana so su sani yanzu, bansan ya zasu dauki abun ba, abun daya kamata ku dinga kiransu   awaya kuna kwantar masu da hankali ta yadda bazasu fahimci wani abu ba, kada ku fada masu komai daya shafi abunda ya faru dangane da zuwanmu kai farmaki, karma su san munje just muna acikin shiri ne, har zuwa time da Unaisah zata wartsake" with respect suka amsa mashi da toh


Wayarsa ce ta fara ringing, mikewa yai tare da kallon Unaisah still idanunta na akan fuskar shi"me kike son ci? Zan sa akawo maki" girgiza ma shi kai tay"bana jin yunwa, sai dai ko zuwa anjima" Okay ya faɗa tare da yi masu sallama kafin ya juya a hanzarce Ya fuce daga dakin Ya nufi part dinsa zama yai daga gefen gadonsa Ya zaro wayar daga aljihu, missed calls ya taras sunkai dari daga gurin yan uwa da abokan aikin sa.


Wani kiran ne ya kuma shigowa, saboda mahimmancin kiran yai picking tare da kara wayar a kunne Yai shiru yana sauraron shi


"A daren ranar da kuka kai farmakin mutun ɗaya ne daga cikin family ɗinka bai kwana agidan shi ba, Mahaifinka  adaren ranar Ya yi fitar sirri batare da sanin kowa ba, bayan shi gaba daya sauran Uncles dinka sun kwana agidajen su.


Runtse idanun shi yayi, bakomai yake tariyowa ba, face lokacin da suke tsaka da yin Faɗa Akan idonshi daya daga cikin Elders Ya murda wuyan evil giant din daya kusa tura kanshi cikin kaskon wuta, Bayan haka Ya jefa shi cikin daki Ya kulle duk da baya acikin hayyacinsa Allah ya nuna masa yaga komai da idanunsa.


Meyasa zai taimake shi shi kadai a filin yaki? Tabbas yana ji aran shi koma wanene na Jininsa ne, yayi masa hakanne don kada su kashe shi.. 


"Yalla6ai kayi shiru baka ce komai ba!" muryar agent zarah  ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula


"Kaka na fa"?


"Agent din da muka tura donya bi diddiginsa Ya tabbar mana adaren ranar Kakanka baije ko'ina ba, yana atare da amininsa..


"Praveen Shima Yana tare da su"?

"Eh, shima a masaukinsa Ya kwana"


 ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da baba obie bai fita adaren ranar ba dakuwa ya shiga cikin wadanda Yake zargi.


"sannu da kokari agent, Aikinka Yana kyau, ka cigaba da sanya ido akansu..." sallama sukayi da junan su, kurawa screen din wayar ido yayi, bakomai idanunsa ke hasko mashi ba face fuskar Mahaifinsa Yana jin wata irin karaya da faduwar gaba da ya ke ji.


Shiru yayi jimm na ɗan wani lokaci yana nazarin maganar sa, kafin ya danna ma baba obie video cos yaga missed calls dinsa.


Kafin yai picking ya dauko hanky ya rufe bandage din dake akan goshin shi don kada yaga raunin dayaji gudun kada ya tayar masa da Hankali.


Bayan yayi picking, ya nutsu Yana kallonsa ta cikin screen din wayar, Yana daga kwance kan wani hadadden  royal  bed da ke a wani hamshaƙin bedroom wanda ya gaji da haduwar kayan alatu, jikinsa sanye da jallabiya.



"Meya hana ka yin bacci"? Ya fada tare da kallon clock din dakinsa Karfe tara na dare.


Yana dariya yace"mutumina mana, kasan shi da surutu kamar aku, gayanan ya tsare ni da fira.." ya faɗa tare da kara mashi wayar saitin fuskar Jan kunne fuskarsa dauke da murmushi cikin harshen turanci yace


"owais bani na hana shi bacci ba, kai shaidane ban cika surutu ba, ya isheni da firar yan mata, tsofe tsofe da shi ko kunya bayaji, yakamata ka aurar da kakan nan naka, yana bukatar mace" girgiza kai chief owais yayi, lamarin su na bashi nishadi in suka fara zolayar juna kamar matasan samari.


"Jikalle, wlh karya yake yi maka, kai kasan mace bata agabana, so yake ya ƙala min sharri, shi ne yake bukatar auren, In ka tashi aurar dani ka hada da shi ka auran da mu mu duka"


 6a66akewa sukayi da dariya kamar zasu fasa mashi kunnanshi.


Murmushi chief Owais ya saki yana kallon su kamar ya samu tv, ba karamin nishadi suka sanya shi ba.


"Kaima ka shirya, da zarar na dawo gobe In Allah yakaimu, zamu fara shirye shiryen auranka don nagaji da kiwon tazurai a estate ɗina" ya fada da zolaya, yar dariya chief yai tare da sunnar da kan shi ƙasa 


Jan kunne Yace"Owais Ya fara kula mata ne"? Ya tambaya yana kallon baba obie


"Tun yaushe? Kai kake mashi kallon Ustaz, Yaron fa Ya girma aure yake so, Mata har biyu" baki asake jan kunne yace"Serious"?



"Kwarai kuwa, nan bada jimawa ba za'a shafa fitihar auransu, first wife din shi will be Nazli and his second wife umm..I forgot her name..."


 su6ul da baka  yayi wurin furta  Unaisah, gaba ɗaya suka sa dariya, Jan kunne yace"ah lallai he really wants to, yaro ya gaji da tazuranci, amma owais mata har biyu a lokaci ɗaya kamar wani hariji ko dai kakanka da mace ɗaya ya fara..."


Wata irin Kunya ce ta lullu6e Chief Owais, ji yai kamar ya kashe wayar.


"Meye naka aciki? Kai dai baka ƙi yin auran ba? Ka zauna nan, babu kai ba samun ni'imar da ake samu a aure, duk wata garabasa ta lada ta wuce ka..." bai kare maganar ba, Jan kunne Ya rarumi pillow Ya buga mashi akai, kokayi suka kamayi kamar wasu kananun Yara sam sun manta da Owais yana kallon su, yayi shiru tamkar ya samu tv, can yaji ɗuff kiran ya katse..


Badan Ya gaji da kallonsu ba.


*🥀ANEELERH🥀*


Around ƙarfe shabiyu na dare, Aneelerh tana tsaka da yin bacci sambatun da baby junaid ya ke yi cikin magagin bacci ne yayi silar farkawar ta sautin muryarshi da shesshekar kuka haɗi da razana Yake fadin"mom...mmy dodo...dodon daya kashe Ana, zai cinyeni, mommy mu gudu!! mu gudu!! mu ma zai kashe mu!!...wayyo mommy...Cikin duhu ta kai hannu ta kunna bedside Lamp Haske Ya kawo fuskarta a yamutse ta dubi junaid, gumi ta gani yana tsastsafo mashi akan fuskarshi, jikin shi kerma yake kamar wanda sanyi ya kama, kanga kunnanta tayi saitin la66ansa ta kasa kunne tana sauraron sambatun nashi.


Lamarin ya fara damunta, kwanakin nan junaid baya iya bacci batare dayayi mafarki ba, kuma mafarkin nasa duk akan dodon daya kashe Ana ne, duk da bata dauki maganar tashi serious ba, amma ta fara kokwanto anya abunda ya gani ba gaske ba ne? in har karya yayi mata meyasa zai dinga mafarki yana razana❓❗


Kirjin shi ta shafa da tafin hannunta cikin disasshiyar murya ta wanda bacci bai ishe shi ba, ta furta"My baby Boy, wake up,..junaid ɗina Yaron kirki"


firgigit ya farka arazane ya ware manyan idanunsa, ganin yadda ya tsoratane yasa tace"junaid, Nice fa" wurga eye balls dinsa yayi akanta, Yana ganin mommynsa Ya fada kan kirjinta ya fashe da kuka yana fadin"mommy nidai tsolo nake ji Allah, dodon daya kashe Ana Yana acikin gidan nan, Nima Zai kashe ni, Kema zai kashe ki sannan ya kashe kowa ba.." 


lallashin shi ta shiga yi"in sha Allah junaid, Bazai ta6a cutar dakai ba, saboda Allah Yana atare dakai..."


 bata kare maganar ba, cikin shesshekar kuka yace"Ni mommy tsolo nake ji, Mu gudu mu bar gidan.."



"A'a junaid, ba inda zamuje, zan cigaba dayi maka addu'a Allah zai kare mu, in banda abunka yanzu idan muka gudu Ina zamu dosa junaid"?


"Gidansu Angel mana.." ya faɗa yana cigaba da sharar kwalla...


"Shikenan, kabari gobe zan kira daddyn Angel din Yazo ya dauke ka, hakan yayi maka" amsa mata yayi Eh, ta fada masa hakanne donta kwantar masa da hankalinsa ko ta samu ya runtsa.


"Mu koma mu kwanta" 


Make mata kafada yai "Ni Tea zan sha" ya fada yana faman zumbura baki.


"Okay, ka jira ni inje in hada maka" maƙe mata kafada yayi"Allah sai dai muje atare kitchen din"


"Pls junaid, bana son fita dakai, da tsakar dare, Ka jira ni kawai" 


Kamar zai fashe mata da kuka yace"toy ai in kika tafi dodon zaizo ya cinye ni" murmushi tadan saki, kiri kiri Ya saka mata rigima Yaƙi bari ta bar shi.


Dabarace ta fado mata, waya ta dauko ta kunna masa kallo ta mika mashi, tun da ya kar6i wayar ya shagala Yana ta yan kallace kallacen shi, har ta fuce daga dakin bai ma sani ba..


Lokacin data fito babu kowa, kasancewar dare ne duk sunyi bacci, cikin nutsuwa take tafiya yayin da a zuciyarta take ta tunanin Taj da Unaisah ta damu da rashin samun su awaya, fatanta Allah yasa lafiya.


harta kusa shiga kitchen sai kuma taɗan dakata idanunta akan hanyar dakin ANA bakomai take tariyo ba face irin zaman amanar da su ka yi da juna, cikin sanyin murya ta furta"Nayi babban rashi Ana, meyasa kika tafi kika barni? Idan laifi nayi maki meyasa baki fadamin ba? In wani abu ke damunki meyasa bazaki sanar dani ba? Kin tafi kin barni da tunanin meya faru dake, nidai nasan ban ta6a cutar dake ba, Allah shine shaida ta Ana, ni yanzu inama zan samu yar aiki mai rukon amana Irin ki"?


ita kadai tsaye tana ta yan tunane tunanenta, zuciyarta ce ta raya mata me zai hana ta je dakinta ta ɗan ƙara bincikawa watakail ko ta ajiye mata wasiya kamar yadda mafi akasari in irin haka ya faru zaga mutun ya aje wasiya mai dauke da abunda ya same shi.


sam ta manta da baby junaid, ta wuce ta nufi ɗakin Ana, murɗa key ɗin ƙofar tayi ta tura ta, tasakai ta shiga ciki duhu ne ya mamaye idanunta da lalube ta gano switch ta kunna kwan ɗakin haske Ya gauraye ko'ina, bin dakin tayi da kallo since last da abun ya faru su zahra suka gyara shi wani bai ƙara shiga ɗakin ba.


bincike ta fara yi adakin ta bubbuɗe drawer chest, tarkacen dake aciki ta dudduba bata samu abunda take nema ba, maida drawer chest din tayi, ta koma gaban closet ɗin Ana, gaba daya ta zazzago da kayan ciki ta dinga bincika aljihunan rigunanta da wandunanta, Ba karamar wahala ta ci ba, kafin kace me tuni ta hada gumi akan fuskarta, babu abunda bata duba ba amma bata samu komai ba, a gajiye ta nufi kofar dakin zata fuce  kwatsam brain dinta ta fara tariyo mata wata magana da junaid ya ta6a fada mata.


A wata rana da ta tambaye shi waya koya mashi boye abu acikin pillow case saboda ita tasan ba dabi'arta bace yin hakan, Yace mata Ai a gurin Ana ya gani in ta samu ƴan kuɗin ta nan take saƙe su har tayi dariya tace Allah ya shiryaka junaid bansan a ina ka koyi sanyawa mutun ido ba nidai halina bane.


tuna wannan maganar yasa tay wani irin kakkwaran juya ta nufi gadon Ana, ta janyo pillows ta zuge zip ɗinsu ta dudduba bata ga komai ba, dafe kai tay da hannu ɗaya fuskarta dauke da matsananciyar damuwa take kallon soson pillows din data zazzago kan mattress din Unexpectedly idanunta suka hango mata kamar wani abu baki a cikin Soson Pillow ɗaya.


janyo shi tayi tasa hannu ta farke sosan kwatsam Tayi arba da wayar Ana abun mamaki abun al'ajabi yatsun hannunta har kerma sukeyi gurin daukar wayar arude take kallonta, daga gani Cusa wayar akayi ta karfi cikin sosan, ashe duk neman da sukeyi ma wayar tana a gidan, Kenan Ina Ana take? Wanene Ya saka wayar acikin rigar pillow.


 power button ɗin wayar ta danna bata kawo ba, hakan yasa tayi tunanin ko babu chargy ne.


saukowa tayi daga kan gadon ta tura wayar cikin aljihun wandon baccin ta, kafin ta kashe switch din dakin, saida ta fito ta tuna da tea din da zata hada ma Junaid, cikin sauri ta shiga kitchen zuciyarta cike fal da tunanin Ana, cikin yan mintuna ta kammala hada masa tea din ta fito ta nufi Bedroom dinta.


tana shiga ta iske junaid kwance ga wayarta a gefe daya, da alama yana tsaka da kallon baccin yaci karfin shi.


akan table ta ajiye cup din, ta sanya wayar Ana a chargy, Mikewa tayi ta dinga safa da marya atsakar dakin Allah Allah take wayar ta hau  koda percent goma ne saboda tayi matukar kagara da taga menene acikin wayar..


jefi jefi take wurga eye balls dinta akan wall clock din dakin kusan karfe biyu na dare, ga bacci dake nema yaci karfinta amma ahaka ta tirje don tana ji aranta akwai wani abu atattare da wayar Ana..."


*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post