Kuskure Ɗaya page 9 Complete by Jiddah S Mapi
Health College

Kuskure Ɗaya page 9 Complete by Jiddah S Mapi

 

Kuskure Ɗaya

KUSKURE ƊAYA

        Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 9*

                  ~Abayan wani mashin ta ɓoye, tana kallonshi yana nemanta toshe bakinta tayi da hanunta ko numfashin kirki batayi, zama tayi kasa daram tana sauke ajiyan zuciya ganin ya koma cikin shoprite ɗin, me mashin yazo domin ɗaukan mashin nashi, da sauri yace "subhanallah baiwar Allah lafiya?"

shesheƙa take da kyar ta harhaɗa magana tace "ruwa"

ruwa ya ɗauko daga mashin ɗin ya bata, karɓa tayi data ɗauran goran a bakinta saida ta shanye kana ta sauke, kallonshi tayi tana fashewa da kuka tace "ka taimaka ka kaini gida banida kuɗi"

cikin tausayi yace "shiga muje"

da kyar ta tashi tana ɗingishi ta shiga, ta cikin madubi sukayi ido huɗu da Abba, da karfi ta bubbuga bayan kujeran driver ta kasa magana yace "menene?"

nuna mishi Abba tayi tace "kayi gudu dan Allah ka ka tseratar dani daga wancan mugun"

kallon Abba yayi kana ya kalleta, jan mashin ɗin yayi ya fita da gudu, kwatance take mishi har ya kaita kofan gida, fitowa tayi ta durkusa har kasa tace "na gode"

girgiza kai yayi "karki damu"

tashi tayi ta ciro makullin data rike a hanunta taki yadda ta sake duk abinda ya faru, buɗe kofan tayi da sauri ta shiga, a tsakar gidan ta wurgar da makullin da takalminta, yasar da mayafinta tayi ta shiga ɗakin tana layi kamar wacce tayi shaye-shaye tsaban wahalan da tasha, faɗawa tayi kan madaidaicin gadonsu runtse ido tayi tana ganin hoton meerah da mutumin data gansu, da sauri ta girgiza kai "no no  najwa kada ki fara wannan tunanin"

sai kuma tace "gaskiyan Abba ne ta tafi ta barni taje wajen wannan?"

hawaye masu ɗumi suka fara gangara har kan katifan da take kwance, tunawa tayi da murmushin da meerah take tayi jiya zuwa yau, wannan hotunan sunfi komai yimata ciwo, barinta da tayi a hannun Abba yafi komai tsaya mata arai, har akwai ranan da zaizo unty meerah ta kyaleni a wajen wannan azzalumin ta tafi wajen wani?"

kuka ta fashe dashi tana janyo pillow tana rufe kanta, saida taci kuka har kanta yana ciwo sannan tace "meyasa kike kuka najwa? ba kece kikeso ta samu wanda take so kuma yake santa ba? meyasa zakiyi kuka?"

share hawaye tayi saide hawayen sunyi tsayawa, cikin kuka tace "sam na tsaneshi wallahi na tsani wannan mutumin, tun kafin na ganshi nakejin tsananshi yau dana ganshi tsanan da nayi mishi ya kara karuwa a cikin zuciyata"

ta karashe maganan tana rufe bakinta sakamakon wani kuka daya kufce mata, ganin babu maganin kukanta ta tashi taje inda meerah take aje mata maganinta, ɗauka tayi duka tazo ta zauna a kasa kusa da gadon, kallon saces saces na magungunan tayi, duka bibbiyu zatasha safe da rana da yamma, ɓallewa tayi duka a hanunta, ruwa tasha kafin ta juye maganin a bakinta, da kyar ta haɗiye kana ta kara buɗe baki ta shanye maganin gaba ɗaya bata bar ko ɗaya ba (over dose yanada matukar illa ga rayuwar ɗan adam a kiyaye"

idonta ne ya fara ya fara rufewa domin magani ne masu karfi, ko biyu tasha suna sata bacci balle ta shanye duka cikin ɓacin rai, kwanciya tayi a kasa ta fara bacci.


Meerah tana kwance akan gadon hanunta ɗauke da drip kanta ansa mata farin bandage sun nannaɗe har goshinta, saiya zame mata kamar siririn ɗankwali, haydar ne zaune a gefenta hanunshi cikin nata marar drip ɗin, jamal cikin tausayin halin da abokinshi ya shiga yace "meya sameta ne?"

yace "jamal ba zan iya dogon magana yanzu ba ka tayani addu'a Allah yasa ta farfaɗo"

shiru jamal yayi, bai taɓa ganin haydar yayi irin wannan ruɗewan ba kuma akan mace, macen ma marar class domin da ganin wannan ba ƴar gidan kowa bace, sai kyau kamar ka wanke hannu ka taɓa, tashi yayi yace "kaga banyi sallah ba gashi dare yayi ana neman 12 idan na idar zan dawo"

girgiza kai yayi "no karka damu kaje gida gobe da safe sai kazo mana da breakfask"

jamal yace "idan na tafi ba komai?"

gyaɗa kai yayi "ba komai ai akwai mutane a asibitin ka manta akwai masu kwana da marasa lafiya?"

yace "to saida safe zamu rinƙa communicating a waya"

jijjiga kai kawai yayi, bayan tafiyan jamal ya kurawa fuskanta ido, a hankali ya kai hanunshi zai taɓa innocent face nata sai kuma ya janye da sauri, kallonta yake babu ko kyaftawa yana jin wani irin abu tun daga kan yatsan kafarshi har zuwa ƙwaƙwalwanshi, ji yayi kamar ace zai rinƙa kallonta har tsawon karshen rayuwarshi, bai san dalili ba idan yana kallonta sai yaji nutsuwa ya alakanta hakan da yanayinta me sanyi da rashin hayaniya, yayi nisa cikin tunanin ta fara motsa hanu a hankali, a hankali ta fara buɗe ido da sauri ta kuka rufewa domin hasken data gani, saida tayi minti uku kafin ta kara buɗewa, kallon silin ɗin take tana rarraba ido, a hankali ta fara bin bangon ɗakin har zuwa kofa da kallo, sai kuma ta maida idonta kan drip ɗin dake ɗaure a hannunta, a firgice tayi niyan tashi da sauri ya riketa yana maida ita, cikin tsoro tace "ina najwa?"

shiru yayi yana kallonta, yayinda zuciyarshi ta bada wani sautin gib, jin sunan data fara ambata, ganin bai bata amsa mata ba ta kuma cewa "ina najwa?" wannan karon da karfi tayi magana tareda yunkurin tashi, saide taji kanta ya sara kamar an ɗaura mata buhun siminti goma, da sauri ta koma ta kwanta tana ciza leɓenta na kasa, cikin sanyin murya tace "ka kaini wajen najwa"

hanunta yake murzawa a hankali yace "ki nutsu domin akwai ciwo a jikinki idan kin samu sauki zuwa safe saina kaiki gida"

cikin raunin murya tace "a,a nidai ka kaini yanzu"

tausayi ta bashi, ya kwantar da murya abinda bai taɓa yiba kenan yace "kiyi hakuri yanzu dare yayi na miki alkawari da safe zan kaiki gida"

girgiza kai tayi hawaye ya gani yana bin kuncinta tace "ba zan iya kwana a wani waje na bar najwa ba ka taimaka ka kaini yanzu"

ji yayi ranshi ya fara ɓaci da sunan najwa da take kira, daurewa yayi yace "ba abinda zai sameta"

cikin kuka tace "ka kaini najwa ba zata iya bacci ba idan bana gidan"

cikin tsawa yace "saiki tashi kije tunda ba zaki jini ba, najwa, najwa najwa, tunda kika farfaɗo kike kiran sunanta nace miki ba abinda zai sameta"

tashi yayi a fusace zai tafi, hanunshi ta rike cikin tsoron tsawan da yayi mata tace "kayi hakuri"

jikinshi yayi sanyi shiya kamata ya bata hakuri ba ita ba, amma wannan sunan da take kira yana tafasa mishi zuciya, dawowa yayi yace "ki kwantar da hankali gobe da sassafe zan kaiki gida nan special room ne na asibitin well care kina tare da mutane dayawa bamu kaɗai bane, ki nutsu drip ɗinnan karfi zai kara miki"

gyaɗa kai tayi, a yadda ya lura tanada tsoron zuciyan mutum, yace "na gode"

a hankali tace "dame?"

yace "da ceton rayuwata da kikayi"

rufe ido tayi bata amsa mishi ba shima bai kara magana ba ya fita domin neman abinda zaici, rabonshi da abinci tun na safe, koda ya tashi dawowa ya dawo da mata da abinci a takeaway, da fari taki ci saida ya ɓata rai ya koma asalin haydar kafin ta yadda ya taimaka mata ta jingina kanta a jikin pillow bayanta kuma a jikin gadon, abinci ya fara bata, da kyar take turawa tsakani da Allah hankalinta ko kaɗan baya nan yana wajen najwah amma ita kanta tasan ba zata iya tafiya da wannan azababben ciwon kan ba, ta kasa nutsuwa domin tana tunanin yadda najwah zata kare da Abba, tunawa da hakan tayi sauri zata dira a gadon, riketa yayi har yayi zaton ko kanta ya taɓu

"ina zakije?"

tana rike kanta dake sarawa tace "najwah"

wani irin tsawa ya daka mata wanda yasa ta nutsu waje ɗaya ko numfashi da karfi bata kara ba, "idan kika sake kika fita saina sakar miki karnukan hospital ɗinnan sun rakaki har kofan gidanku"

a rayuwarta babu abinda take tsoro kamar kare jin sunan daya ambata na kare ma yasa ta nutsu, komawa tayi ta kwanta luf, blanket ya lulluɓa ta dashi, kana ya janyo kujera ya zauna akai, bai jima ba bacci ya ɗauketa sakamakon alluran bacci da jamal yayi mata a cikin drip domin ta samu hutu, ido ya zuba mata ya rike hanunta dake ɗauke da drip ɗin sabida kada tayi birgima ko ta motsa hanun drip ya karkata, da haka har bacci ya ɗaukeshi akan kujeran.


momy saida ta ɓacewa ganin kowa kafin ta tsaya da gudun ta ɗaga wayarta ta kira numbern kabeer, cikin ɓacin rai da tsananin haushin da takeji ta daka mishi tsawa "dakata da wannan gudun da kake nice nake binka ba kowa ba"

tsayawa yayi bai kara ko taku ɗaya ba, gwiwanshi ya dafa da hannu sabida gajiya, juyawa yayi yana kallonta, cikin tsananin ɓacin rai take taku kamar zata tashi sama, saida gabanshi ya faɗi ganin fuskanta, shi kanshi yasan momynshi muguwa ce ko shi baya gama yadda da ita dan zata iya kasheshi idan yana kawo mata cikas, tana zuwa ta ɗaukeshi da mari, kafin ya ɗago ta kara ɗaukeshi da wani, dafa kunci yayi yana kallonta, cikin fusata tace "ko zaka rama ne?"

shiru yayi kanshi a kasa, tace "meyasa bakayi aiki yadda ya kamata ba? na tabbata da yanzu saide ayi maganan wani bashi ba, meyasa ka bari wannan tsinanniyan yarinyar ta kareshi?"

shima ranshi a ɓace yace "momy bansan time ɗin da tazo ba fa, baki kaini jin haushin abinda ya faru ba, wallahi bansan ya akayi tasan zamuyi hakan har tazo ta kareshi ba, ko dai tana bibiyanshi domin ta kareshi ne a koda yaushe?"

juya baya momy tayi tace "lalle ko ta tsoma rayuwarta cikin tsaka me wuya, sai nasa ta kasa bambance tsakanin rayuwa ko mutuwa wanne tafi so, sai nasa ta gwammaci bata taɓa sanin wani me suna haydar ba, a duk lokacin da nayi shiri itace take rusamin wallahi bata isa ba"

yace "momy nidai kada ki kasheta ki bari sainayi koda 2days ne da ita"

harara me zafi ta watsa mishi kafin ta ɗau dutse a kasa, har ya tsorata ya mayar shi zata harba, sai kuma yaga ta buga wa goshinta, waro ido yayi ganin goshinta ya fara jini 

"momy jini fa"

ɗaga mishi hanu tayi kafin tace "kafin ka samu wani abin saika rasa wani abin"

yace "amma momy karki illata kanki"

tace "kabeer illata kaina a yau shi zai tabbatarwa haydar ina sanshi kamar yadda maminshi take sanshi, idan na koma haka ba wani ciwo ba zai tabbatar da nabi makiyinshi ba, amma hakan zaisa ya yadda dani"

tafa mata yayi kana yace "that's my mom"

da hanu tayi mishi alaman ya tafi, hug yayi mata kana yace "bye sai munyi waya"

saida taga yayi nisa kafin ta koma, bata koma wajen da abin ya faru ba dan tasan tabbas haydar ya kaita asibiti, gida ta koma ta ɗaurawa goshinta bandage kafin ta kwanta akan gadonta tana tunanin plan ɗin da zata haɗa.


*washe gari*


shirin kaita gida yake domin ta tashi ta zauna tunda tayi salla take zaune a gefen gado tana jira gari ya ɗanyi haske ta tafi, saida ya idar da salla ya tashi yace "good morning"

a hankali ta gaisheshi, amsawa yayi tareda ce mata "ya jiki"

a hankali tace "da sauki"

shiru yayi bai kara magana ba, yana jiran jamal ya kawo musu breakfask ita kuma tayi zaton shima yana jira gari ya fara haske ne, suna zaune su duka sunyi shiru, turo kofan akayi a zatonshi jamal ne, da mamaki yaga momy rike da katon basket da flask ɗin tea da kuma plates a gefe, da sauri ya tashi yana tayata karɓa, kallon goshinta dake ɗaure da bandage yayi, yace "meya sameki?"

tace "karka damu ba komai"

aje plate ɗin tayi ta kasa kasa take aikawa meerah wani kallon da ko ita kanta batasan na miye ba, meerah ji tayi zuciyanta ya tsinke ganin matar kawai taji bata mata ba, murmushi momy tayi mata sannan ta karasa inda take a zaunen, ciwon dake kanta ta danna, kara meerah ta saki, da sauri momy tace "sorry, sorry my dear ban san zai miki ciwo ba"

a hankali tace "ba komai"

murmushi tayi tace "da gani kinada hakuri, wani lokaci muna kuskure ba tareda munsan munyi ba, wannan kuskuren zai rinƙa bibiyanmu har karshen rayuwarmu, wani lokacin ma kuskuren yakan iya zama ajalinmu..."

a firgice meerah ta kalleta, itama kallonta tayi tareda yi mata murmushi, sai binta da kallo kawai meerah take hankalinta yaki kwanciya, haydar yace "momy meya sameki a goshi?"

shiru tayi kamar batason bada amsa sai kuma tace "jiya bayan nabi wannan da yayi niyan buga maka karfe aka saida na kamo riganshi na juyo dashi sai naji ya bugamin goshi ban kara sanin inda kaina yake ba, saida wasu mutane suka taimaka suka kaini gida"

da sauri yace "sannu amma ya kikejin ciwon?"

"da sauki karka damu"

kallon meerah tayi tace "ga wacce zamuyi mata sannu, ina fatan mu rinka yimiki sannu har karshen rayuwa, mun gode da wannan jarumta da kikayi a madadin haydar ina kara gode miki"

dukar da kai kawai meerah tayi, yace "kici abinci saina kaiki gida"

girgiza kai tayi da sauri tace "a'a zan tafi gida"

duk yadda yayi da ita taki cin komai, yace "muje na kaiki"

a hankali take tafiya har ta kai bakin kofa ta juyo ta kalli momy, da mamakinta taga itama momy kallonta take, haka kawai takejin gabanta yana faɗuwa duk idon da zasu haɗa da momyn, saida suka fita ta saki murmushi tace "ba zance zan biku ba sabida zakuyi zargin wani abu, balaraba tana yin abinta ne da wayo da ilimi"

marfin motan ya buɗe mata ta shiga, zagayawa yayi ya shiga ya kunna motan zuwa yanzu gari yayi haske, har suka hau titi gani take kamar baya mata sauri dan so take taje taga najwa, kallonta yayi itama ta kalleshi sannan kowa ya ɗauke kai, yace "meyasa kika taimakamin?"

tace "najwah"

bai kara mata magana ba, har kofan gida ya kaita da sauri ta buɗe zata fita ya rufe motan, kallonshi tayi da dara daran idanunta tace "ka buɗemin"

sanyinta yafi komai birgeshi ko magana zatayi a hankali take yi, wani kwali ya ɗauko ya buɗe ya ciro sabuwar waya ya mika mata, kallo tayi sannan ta kalleshi ganin wayar me tsada ce iphone 15, girgiza kai tayi "banaso"

yace "to zaki kwana a motar nan idan baki karɓa ba"

kallon kofan gida tayi ta tuna najwah dake ciki, hanu tasa ta karɓa, yayi murmushi yasan meyasa ta karɓa saboda wannan me sunan daya tsana ta karɓa, sauri take taje ta ganta, buɗe motan yayi yace "akwai sim aciki sannan na saita tumprint da yatsanki idan kikasa yatsanki na biyu zai buɗe"

sam bata fahimtan me yake cewa sai gyaɗa mishi kai take hankalinta akan kofa, yace "na gode sosai"

hanu tasa ta buɗe marfin motan da sauri ta fita, tsayawa yayi yana kallonta har saida ta shiga gida ya kunna motan ya tafi.


Tun daga bakin kofa ta fara ganin kayan da najwa ta zubar kama daga mayafinta takalminta da makullin, zuciyarta ya tsinke, da sauri ta karasa cikin ɗakin, tsayawa tayi tana kallonta ta kasa karasawa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ta faɗa lokacin da taga kwalayen maganin da kuma najwa wacce take kwance a gefensu tana bacci ta shanye duka, hanu ta ɗaura aka kana taje da gudu ta fara bubbugata "nakwa!!! najwa! na shiga uku me kika yiwa kanki haka najwa?"

girgizata takeyi sosai tana kiran sunanta tareda fashewa da kuka, ɗaga hanunta tayi taga ya saki, da gudu ta fita tana kwala ihu a cikin gidan "ku taimakeni ta mutu"

lekawa tayi kofa bataga kowa ba, bakin titin dake unguwan taje wajen mazan dake zaune cikin tashin hankali tace "ku taimaka min najwa ta mutu"

kallonta sukayi ɗayan ya tashi yace "meya faru?"

sauran sukace "karka fara ƴar gidan Ibrahim makama ce kuma kasan yace duk wanda ya shiga gidan yaran da sunan taimako sai yayi shari'a dashi"

komawa yayi ya zauna yace "kai malama gaskiya kiyi hakuri ba zamu iya shiga ba"

durkusawa kasa tayi ta haɗa hannu bibbiyu ta dukar da kai tana hawaye tace "dan girman Allah ku taimakamin itace kaɗai ta ragemin a duniya"

duk rokon duniya tayi sunki zuwa, tashi tayi ta koma gidan, zama tayi ta zuba tagumi a gaban najwa, karan waya taji yana ringing, sam ta manta da haydar ya bata waya, da sauri ta ɗau wayan tana dubawa, sunanshi ta gani yana yawo a gaban screen ɗin, HAYDAR da sauri ta ɗauka ta kara a kunnenta ba tareda ta bari yace komai ba cikin kuka ta gigicewa tace "haydar najwa kazo ka taimakeni ta mutu"

kallon screen ɗin wayar yayi sannan ya kara sawa a kunne jin yadda take magana kamar ma bata cikin hayyacinta yace "relax and tell me meya faru?"

cikin kuka tace "kazo gida yanzu please"

cikin nutsuwanshi yace "okay gani nan zuwa"

juya kan motar yayi ya ɗaga waya ya kira salma me aiki, tana ɗagawa yace "karo na farko da kenan a duniya an kirani kan mami banje akan lokaci ba, inaso ki kula da ita akwai abinda zanyi yanzu"

kashe wayan yayi yana nufan gidansu meerah, idanu ya lumshe sannan ya ciza lips nashi "ko aina nake indai kin kirani zan amsa kiranki meerah, koda bana nigeria kika kirani zan hau private jet na dawo cikin kankanin lokaci, kin zamo ta musamman a wajena, kin min sadaukarwar da babu wanda ya taɓamin a rayuwata"

yana isa kofan yayi parking kana ya fito yayi sallama, da gudu ta fito ta rike hanunshi cikin kiɗima take janshi "muje ka ganta ta mutu"

binta yake da kallo har ta kaishi ɗakinsu, nuna mishi najwa tayi "ka ganta ko? na faɗa maka ba zata jure zama babu ni ba, jiya saida nace maka zan dawo ka hanani, gashi yanzu ta mutu na rasa ta, nima wallahi na zama zanyi ba mutuwa zanyi...."

rufe mata baki yayi yana girgiza kai, bai taɓa jin kalman daya daka mishi zuciya kamar kalman mutuwa data ambata ba, girgizata yayi ta yadda zata dawo hayyacinta yace "ki nutsu mana meerah"

share hawayen tayi wasu suna bin wasu tace "ina bazan taɓa nutsuwa ba saina tabbatar kanwata tana raye kuma lafiya"

sakinta yayi ya durkusa wajenda najwah take kwance, kallo ɗaya yayi mata yaji sam bata kwanta mishi arai ba, gashi dai tafi meerah kyau nesa ba kusa ba, ya jima baiga mace kyakkyawa kamar wannan ba, lokacin da yaga meerah yayi mamakin kyaunta amma wannan ta fita sosai, hanunshi ya kai wajen hancinta sannan ya kalli meerah yace "sa hanunki a kirjinta kiji"

da sauri tasa hanu a kirjin najwa, kallonshi tayi da idanunta wanda suka kumbura tsaban kuka tace "kamar kirjinta yana bugawa"

gyaɗa kai yayi yace "normal tana raye bata mutu ba"

kallon magungunan yayi sannan yace "is she a drug abuser?"

girgiza kai tayi "sam kanwata bata shaye shaye, bata taɓa shan komai ba wallahi"

kallon maganin yayi a ranshi yace "gashi tana kama da ƴan kwaya"

a fili kuma yace "meyasa ta shanye waɗannan maganin?"

cikin hawaye tace "saboda bana kusa da ita, najwa bata jure rashina kusa da ita"

wani haushi ya kuma ji, baiyi magana ba yace "kaita gado zanje na dawo"

da sauri tace "ba zan iya kaita ni kaɗai ba ka taimakamin ka tayani riketa"

hanyan fita ya kama yace "barta anan......




*ku biya ku karanta complete naira 300 ne ta account ɗina 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, katin shaidan biya ta nan 08144818849*



_jiddah Ce....✍🏻_

08144818849

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post