Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 64 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 64 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

Fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa buɗe baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"?

A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata.

Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta.

Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci..

"Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ƙato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya..

Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...."  

Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta"

Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan.

 Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba.

Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi.

Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya ɗauke ƙafa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi.

Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko ɗaya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su. 

Lokacin da  Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba.

Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba.

Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata.

Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai.

badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh.

Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ƙara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta faɗa ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su.

Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya ƙyale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta.

a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta da ke bacci akan kirjinta, Sai ga sheikh Imam Ya fado dakin Yana huci Ya tashe ta daga bacci Yace ta tashi tabar gidan bai son ganinta, Ta yi nesa da shi idan ba haka ba zai kashe yarta, Ya tsaneta baya son ganinta kuma wlh in har ta bari wani yasan tayi cikin shege ta haihu Sai Ya lahantata, tace mashi baba kada kayi min haka! Idan ka kore ni a cikin daren nan ina kake tunanin zan tafi? Bayan ka hana in nemi taimakon dangin mu, nifa yarka ce baba, amana ce agare ka, nasan da mahaifiya ta, tana araye wlh koda ace ni karuwace ba zata kore ni ba, saima taja ni a jikin ta don in shiryu, balle kai da ka taso tare dani ka sanni ciki da bai, ka tarbiyantar dani, kuma ka yarda dani amma a yau kaine kake korata? Saboda kaddara ta afka min? Bai Saurareta ba, Tana kuka ta sauko daga kan gadon, ko Aunty laura bata sani ba adaren ranar shekh imam Ya kori aisha daga gidan Har bakin gate Ya rakata Bata dauki komai nata ba sai yar wayar data tsira da ita.

a bakin gate din gidan Alhaji Ubaid ta tsaya hannayenta rungume da jinjirarta dake ta sharar baccinta.

Tana kuka Ta kalli sararin samaniya taga hadari ya hadu bakikkirin Babban tashin hankalinta kada a barke da ruwa sama batasan Ina zata sanya yarta ba.

Anan ta yanke shawarar kiran dr shureim duk da bata da tabbacin yana nan ko bai nan don tunda abun nan ya faru bata kara jin duriyarshi ba tun da ba fita ta ke yi ba,  wayarta kuma akashe take, ko ya kira ba sani zatayi ba.

sau uku tana Kira baya Picking, sai ana hudune taci sa'a yai picking tace"shureim ina a kofar gidanku, Baba Imam ya kore ni daga gida, Ka zo ka kar6i yarka, idan ba haka ba zaka rasata ne"! Tana karasa maganar, ta kashe kiran.

Ko mintuna biyar ba ayi ba sai ga dr shureim Ya fito jikin shi sanye da jallabiya, kallo daya da yayi ma Aisha saida gaban shi ya fadi ganin yadda ta rame idanunta sun kaɗa jawur sun kumbura, A lokacin yaji kunyar hada ido da ita kamar ya haƙa ƙasa ya binne kanshi, tsantsar tausayintane ya kama shi sam bai ma lura da babyn hannunta ba.

Karasawa yayi kusa da ita, harya bude baki zaiyi mata magana ta dakatar da shi"ban kiraka don muyi magana ba, Yaya shureim nagode da abunda ka saka min da shi," ta fada tare da manna mashi yarinyar da ke a nannaɗe cikin towel dinta a kirjin shi yai sauri rungumeta wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyar shi.

"Gatanan Itace abunda muka samu, nabar maka ita amana, badan bana sonta ba na baka ita, sai don bana so tasha wahala tunda ni yanzu bani da kowa banma san inda zan tafi ba, wata rana zan dawo in kar6i abuna, Inaso kayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata FATIMA BATOOL, Idan har kabari rayuwarta ta cutu ka sani Allah yana sama yana Kallonka, Nima kuma bazan yafe maka ba, akwai ranar hisabi"

 maganganun Aisha sun karya mashi zuciya, baisan sa'adda ya fashe mata da kuka ya dinga yi mata magiya akan kada ta tafi tabarshi wlh yana sonta ashirye yake da ya aureta yayi mata alkawarin zai wanke laifinsa zai share mata hawayenta, zai kula da rayuwarta, tace mashi ya makaro, Lokacin daya kamata ya furta mata hakan ya riga daya wuce, sai bayan daya 6ata komai, sannan ita bazata taba auren namijin daya santa ba.

Ba yadda baiyi da ita ba amma ta kafe, har cewa yayi ta shigo ta kwana agidansu amma takiya, ta juya zata tafi yabi bayanta yace sai dai su tafi atare saboda bazai iya rayuwa batare da ita ba, sannan Yar da tabar masa, shi baida abunda zai shayar da ita ta taimaka ta dawo suyi aure su rufawa kansu asiri da kuma yarsu.

Aisha bata saurare shi ba, da taga dagaske Dr shureim binta zaiyi sai ta watsa da gudu Shima yabita aguje a karshe ta bace ma ganin shi... 😭

Tun daga wannan Lokacin dr shureim bai kara ganin Aisha ba, babu wanda yasan Ina ta dosa, Anila saidai taga sakon data tura mata.

Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu."

A daren ranar bayan Dr shureim Ya koma da baby cikin gidan, batare da sanin kowa ba, Ya nufi daki da ita Ya kwanta kan gadonshi yayin daya rungume Yarshi a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da bakin cikin abunda yayi ma Aisha shine silar komai, yaji takaicin tafiyarta, yaji kunci da radadin rasata da yayi.

Dakyar ya samu nutsuwa, ya buɗe fuskar babyn ya zuba mata idanunshi da suka kada jawur yadinga kallonta kamar zai hadiyeta, A hankali ya sumbace ta a saman forehead dinta da cheeks dinta, wani irin tsantsar sonta ne ya lullu6eshi kamar ya mayar da ita cikin shi, a kalla ya shafe rabin awa yana kallonta, aranshi ya ayyana inama ace ta hanyar aure suka same ta da sai yafi kowa farin cikin zuwanta duniya, amma ahakanma Ya gode ma Allah daya bashi ita, addu'o'i sosai yayi mata har yai mata huduba da sunan*FATIMA BATOOL*

Bai tashi sanin yana a cikin musibaba, Saida Ta farka tsakar dare ta fara tsala kukan Yunwa, A firgice ya farka ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi duk yabi ya Ruɗe, ya sungumeta akan kafadarshi ya sauko daga kan gadon ya dinga zarya da ita a tsakar dakin yana lallashinta haɗi da jijjigata.

Sakamakon kukan data dinga tsalawane Yaja har mutanan gidan suka farka daga bacci, Cike da mamakin jin kukan jinjira a cikin gidansu.

Da gudu Suka nufo Dakin Dr shureim Alhaji ubaid da hajiya layla sai Mai aikinsu zainab, suna shigowa suka iske shureim ya rungume baby a kirjin shi.

Cike da mamaki suka tambaye shi yar wacece? Donsu kwata kwata basu san Aisha ta haihu ba, sun dai san abunda ya faru tsakaninta da shureim.

Jin yayi shiru bai basu amsa ba yasa hajiya Layla ta doka mashi tsawa tace shureim ba kaji ina magana ba? Yar uban wacece wannan"?

Cikin sanyin murya yace"ƴata ce, babyn da Aisha ta haifa mince, Baba Imam ya koreta daga gidansa, shine ta kawo min ita jiya da daddare"

Bai ƙare maganar ba Hajiya layla tayi tsalle ta dire tace"Wlh bazata sa6u ba! Shegiyar zaka kawo mana acikin gida? So kake kaja mana surutu agurin mutane? Wato shi uban nata ya koreta saboda gudun abun kunya sai mu zaka jajubo mana annoba ka kawo mana agida? Saboda baka da hankali"?

Ta inda take shiga bata nan take fita ba, Kamar zata rufesa da bugu, Kalamanta sun Kona ransa, musamman data kira yarsa da sunan shegiya, bai kula ta ba hankalinsa na akan fatima dake ta kuka surutunsu Ya kara hargitsa kwakwalwarta duk tabi ta rude ga yunwa tana ji.

Alhaji Ubaid Yace"shureim, kayi hakuri da abunda zance, badan bana son jininka ba, sai don gudun abun kunya, kuma kaga an kusa fara zabe in har maganar nan ta fita wlh za ka ja min asara ne, don Allah ka dauki yarinyar nan ka kaita gidan marayu su kula maka da ita, Inyaso sai ka dinga zuwa kana dubata..."

 sai a lokaci Ya fuskance su da wata irin fusatacciyar murya yace"ɗan ku ne shegen da yayi wa uwarta ciki ta haifeta, wallahi ba inda zan kaita! Ban taba sanin baku da imani ba sai yau da kuka nuna min, Yarinyar nan koba dan kasancewarta jinina ba Yakamata ku tausayamata, Jaririya ce fa? Ta rasa mahaifiyarta, ni kadai na rage mata, ya kuke so tayi da rayuwarta ne"? Idanunsa cike tab da kwalla yai maganar.

Aunty Zainab tayi kokarin tayashi fadan amma Hajiya layla ta koreta daga dakin ta fuce tana kuka saboda sun bata tausayi.

Kusan dare suka raba ana abu daya, kowa yana akan bakanshi.

Hakika dr shureim Yaci wahalar Iyayenshi, kullum sai sunyi barazanar kashe mashi ƴa in har bai fitar masu da ita daga gidan ba amma Yakiya.

 wulakancin yau daban na gobe daban Sun daura mata karan tsana ba gyaira ba dalili, Aunty zainab ce ke shayar mashi da ita a boye batare da sanin su ba.

Hajiya layla har ɗaukar babyn tayi batare da sanin shi ba, ta fuce da ita daga cikin gidan, a lokacin yaje  masallaci yin sallah sai da ya dawo ya duba dakin shi bai ganta akan gado ba, ya fito arude yana nemanta, Aunty zainab ce ta fada mashi taga hajiya layla ta shiga dakin shi, tana da tabbacin itace ta ɗauke ta, hankalinsa ya tashi, ya dinga kiran layinta bata picking, time data dawo cikin motarta ta shigo gidan ya nufeta yana huci yace ina yarshi tace tabada ita sadaka.

Ji yayi kamar ya dauketa da mari, ya dinga rokonta akan ta dawo mashi da yarshi tayi banza ta kyale shi, yai hakuri Ya jira time da Alhaji ubaid ya shigo gidan, ya tuntube shi da maganar ya dinga rokonsa akan ya yi ma mommynsu magana ta dawo masa da yarsa, Alhaji ubaid bai kulasa ba saima yace tayi abunda ya dace.

rai a6ace Ya nufi Kitchen Zainab tana a ciki tana yin girki taga yashigo ya dauki wuka Ya fita da ita aguje tabi bayanshi.

A lokacin Hajiya layla tana a zaune kan kujera tana danna waya batai aune ba, taji ya ɗaura mata wuka a akan wuyanta, ta zare ido gabanta na faduwa, shureim yana huci yace"kodai ta fada mashi inda takai mashi baby, ko kuma ya kasheta"

 adabarbarce tace"nashiga uku shureim ni zaka kashe? Mahaifiyarka? Saboda kawai na kawar da ƙazantar zina daga cikin gidan mu"?

Ihunta da Alhaji Ubaid ya ji yo ne yasa shi watso wa da gudu Yafito daga dakin shi ganin abun da Shureim ke kokarin yi ne Ya tada hankalinsa kafin Ya karaso Shureim Yace"kana karasowa zan hada dakai in kashe!" ba arziki Alhaji ubaid Yaci burki yana lallashin shi akan ya aje wukar zasu dawo mashi da yar shi, Zainab tana kallon komai dake faruwa, ko kadan bata sa baki ba, saboda taji dadin barazanar da Shureim yayi masu, tun da su ba Allah aran su.

Hajiya layla data gama tsorata cikin shakakkar murya ta fada mashi sunan gidan marayun data kai Batool.

Sakin wukar yayi da gudu Ya fuce daga gidan Cikin motar shi Ya tafi.

Kafin marecen ranar sai gashi ya dawo da babynsa, ya rungume abunsa a kirjin shi, baiwar Allah tayi kuka har ta gaji idanunta sun kada jawur dakyarma ya samu Caregivers din dake rainon yaran suka bashi ita, saida ya basu cin hanci harna Dubu dari shidda kafin suka damka mashi ita.

Abun da ya ɗaurewa shureim kai, Mugayen halayan da iyayensa suka sauya wanda ada ba haka suke ba, har kwara hajiya layla yasan tunfil azal bata da mutunci, batason talaka, ta tsani talauci, ga girman kai, amma mahaifinsu Alhaji ubaid ba halinsa bane, Shi shaidane babansu mutumin kirkine amma tunda ya faɗa harkar siyasa ya canza shima, Ya rasa gane meke faruwa ne? Duk wannan badakalar da aka sha Benazir bata sani ba, ko awaya inta kira su don su gaisa ko suka kira donsu gaisa da ita babu wanda ya taba gigin faɗa mata.

 don wlh da ace ta sani zasu sha ruwan mamaki saboda masifarta, har hajiya layla data gado shakkarta take ji, zata tsayama shureim ne kuma babu wanda ya isa ya ɗaga ma yarsa yatsa agidan.

Shureim harya fara tunanin sun hakura, ganin kwana biyu basu bi takanshi ba, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba, ashe wata wutar bala'en ce zasu kunna mashi.

Alhaji Ubaid yasa aka kulle mashi bank account dinsa, Ya hana shi abincin gidan shi, duk wani abu da yayi mashi a matsayin uba saida ya kwace shi, hada key din motarsa ya kwace ya kasance baida ko sisi, ita kuma zainab da hajiya layla ta gano tana shayar da yarsa kuma tana satar abinci aboye takai ma shureim aikuwa tayi mata shegen duka da girmanta da komai ta kuma koreta daga gidan gashi bata da kowa a nigeria danginta da komai suna a egypt haka tayi ta gagari cikin gari.

Dr shureim ya shiga matsananciyar damuwa, da shi da yarshi suna a tsaka mai wuya, Ya rame yayi duhu, Itama jinjirar ba lafiya, ga yunwa da rashin bacci, kwana su ke yi idon su biyu har rokon su yayi kan su taimake shi kada ya rasa yarshi suka kiya saima su ka ce In har yana so su mayar masa da komai nashi da suka kar6a to ya mayar da Batool gidan marayu, kusan kullum sai ya jaraba kiran layin Uncle musa don ya fada masa halin da ya ke a ciki saboda yasan shi kadai ne zai goyi bayansa sannan ya taimaka masa amma ko ya kira layin a kashe ya ke samun shi, baisan ya zaiyi ba, ga Hajiya layla tace in har ya kuskura ya kira wani nata don ya taimaka mashi Allah ya isa bata yafe ba shiyasa ya kasa kiran Ammin su.

Baida wata mafita daya wuce ya gaya ma Allah, A karshe ya dauki yarsa yabar masu gidan.

Ko a jikinsu damuwarsu daya kada su rasa dan su amma donta yarinyar basu damu ta mutu ko tayi rai ba.

Baisan Ina zai nufa da ita ba, a wannan zamanin bakowane zai kula maka da dan ka tsakani da Allah ba, gashi bakowa ya sani a joss ba, saboda rabi da kwata na rayuwarsa a gurin amminsu yayita can Kasar egypt.

Tafiya ya ke yi Jikin shi ba kuzari, ya rungume babynsa a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da tunanin makomar rayuwar yarsa.

Tuntana kuka har ta gaji tayi shiru bacci ya ɗauketa, kwatsam aka fara ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya rasa ina zai sama masu mafakar da zasu zauna, Baiwar Allah tana tsaka da baccinta ruwa ya farkar da ita, Ta dinga tsala kuka ya rasa ina zai kaita don kada ruwan yai mata illa.

a karshe dai ruwan gaba daya akansu ya ƙare, Har dare ba adaina ruwan ba, saida daren Ya tsala ruwan Ya dauke a lokacin Ya ma fidda rai da ita saboda Zuciyarta ta daina bugawa Jikinta ya saki.

Anan ne ya yanke shawarar binneta, Saboda yaga baida wata mafita, in har ya barta wahala zata cigaba da sha, mutane ma ba zasu kyale ta ba za'acigaba da tsangwamarta ne tunda har iyayensa sun shegantata sun kirata da kazanta inaga mutanan waje?

 Kowa ma zai samu kwarin gwiwar cuzguna mata ne idan ta girma, kwara ya saukaka mata ta huta itama, yasan in ta mutu Allah zaiji kanta.

A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacin shi kamar ya fara zaucewa, Da hannayenshi Ya haƙa rami, Ya sakata a ciki ya kwantar da ita yayi mata addu'a, Yana kallon yatsun kafafunta dake motsi alamar bata mutuba, amma Ya rufe ido saboda bayason taci gaba da shan wahala Ya rufe mata kasa a jikinta ya daddale gurin da kafafuwan shi, anan ya zauna kamar mahaukaci yaci gaba da sambatu shi ka ɗai daga bisani ya suma akan kabarin ta.

Bayan sati Biyu da afkuwar lamarin, Dr shureim Ya farka a gadon asibiti, ya fara lalubar Yarsa Yaji shiru babu ita a jikin shi, Yabi ya rude hankalin shi Ya tashi, ya sauko daga kan gadon Yana fadin Ina yarsa! Ina fatimarsa! Ina batool dinsa! Tana Ina"?

 Likitan dake dubashi Ya rurruke shi Yana kokarin kwantar masa da hankali, aikuwa ya bangaje shi da karfi har saida doc din Ya kife kasa.

Hajiya layla Da Alhaji Ubaid da ke a waje suna jiran tsammani, muryarsa da suka jiyo daga cikin dakin yana kwala ma batool kira yasa suka yi saurin shigo cikin dakin, yana ganin su  ya nufe su yana tambayar su Ina yarsa take? Ta na ina? Hajiya Layla tace suma basu san Inda ya kai ta ba, abun da ya faru bayan ya bar gida suka baza jami'ae don su nemo shi, cikin sa'a jami'an suka tsintoshi a sume a gaban wata bishiya, amma basu ga yar shi ba, shine suka garzaya da shi asibiti, Yau sati biyu kenan baya a cikin hayyacin shi.." 

sai da tayi wannan maganar ya tuna da abunda ya aikata ma Batool, wani irin jiri jirin tashin hankali Ya gani acikin idanun shi, ya dinga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un kamar maganarsa zata kare! wai mike faruwa da rayuwarshi kamar wanda akayima jifa? bala'i daga wannan sai wannan.

Bai karasa jin zancen ba, Ya watsa da gudu Ya fito daga asibitin, suka biyoshi a cikin motar su, Ya dinga gudu kamar zai fadi kasa, har titi Ya hau mota ta kusa bankade shi Allah ne dai Ya tsare shi dakyar Ya gano gurin da ya binne ta, Ya zube kan gwiwowinsa, Jikinshi na kerma Ya haƙa ramin wani irin faduwar gaba Yaji ganin kasusuwanta, Harta mutu ta rube kashinta kadai ya rage, daddafe kanshi yai da tafukan hannayen shi saboda matsanancin ciwon kan da yaji, nan Take Ya yanke jiki ya fadi a sume.

A lokacin motorsu Alhaji Ubaid ta karaso gurin da yake, bayan sun fito suka taras da shureim rai hannun Allah, ga ramin daya haƙa abude sai kasusuwa birjik a cikin sa.

Basu tsaya bata lokaci ba, Alhaji ubaid Ya dauke shi ya shigarshi da shi cikin motar, suka koma asibiti da shi.

Tun daga wannan Lokacin shureim bai kara hankali ba, ya zama mahaukacin karfi da yaji, bayagajiya da sambatu yana fadin wayyo Allahana, na kashe Batool, da hannuna na binne ta acikin rami, Batool ta mutu ta zama kashi, Naci amanar da aisha ta bani, Allah bazai barni ba"

sai da takai ga ko sallah shureim bai iyayinta cikin nutsuwa, A lokacin Hajiya layla da Alhaji Ubaid sun ji tausayin shi sun kumayi danasanin tilasta mashin da sukayi akan yarinyar gayanan sun ja ya binneta ta mutu, shi kuma Ya haukace.

 saida ya shafe wata daya bai dawo daidaiba, A lokacin Hajiya layla ta dawo da zainab mai aikinsu gidan tana daya daga cikin masu bashi kulawa duk da baya acikin hayyacin shi tayi kokarin tambayarshi meya faru? A haukan nashi Ya fayyace mata komai, tayi bakinci sosai sai dai bata ga laifin shi ba, saboda tasan me yaja mashi ya aikata hakan, haka ta dinga kokarin kwantar mashi da Hankali.

Ganin za6e ya kusa ga mutane sun fara yi masu surutu akan Halin da shureim ya shiga duk da kullan da sukeyi mashi amma an asamu wasu daga cikin ma'aikatan gidan sun fitar da sirrin su a boye, Hakan Yasa suka yanke shawarar tura shi Egypt, to a lokacin ya ɗan fara dawowa hayyacin shi tunkafin ma suje mashi da maganar ya tattara yanashi yanashi batare da saninsu ba ya tafi egypt saboda bayason zama tare da su sun fita aranshi, bayan ya isa ne ammin su ta kira hajiya layla ta sanar da su shureim yazo sai dai bata gane meke damun shi ba, ko magana ba ya iya yi mata.

Hajiya layla tace ta taimaka ta lallashe shi sannan ta bashi kulawa, ya samu tabin hankali ne sakamakon buguwar da kanshi yayi garin tukin mota ya yi accident har jinya yayi a asibiti.

Karya da gaskiya ta dinga fada mata har ammi ta yarda da maganarta tace in sha Allah zatayi kokarin bashi kulawa, hakan ba karamin dadi yayiwa hajiya layla ba.

Bayan komawarsa egypt ya gaza jure radadin da zuciyarshi keyi mashi kullumne sai yayi mafarkin Batool a cikin rami tana kuka, Hakan ya ƙara dagula mashi lissafi har takaishi ga fadawa harkar shaye shaye ya zama cikakken dan kwaya.

(Kunji alakar dake atsakanin Ummi da su Benazir da kuma shiekh Imam malik, da kuma kaddarar datayi silar rabuwar su da ita, Bayan haka duk wata sa'insa da dr shureim yakeyi da iyayenshi bayan dawowarshi daga egypt a lokacin dayaji sauƙi ya dawo hayyacin shi ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne ta❗ shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faɗa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya ɗaure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany,  bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji👍)

Gaba ɗaya suka bita da kallo yayin da take ƙarasa saukowa daga kan stairs ɗin ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta.

cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"!

 Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir.

Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba  kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."?

 Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita.

Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta.

Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu,  a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."!

 Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata  ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaɗaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ƙarasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haɗa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su.

"Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faɗa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna.

Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi.

Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi ..

Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba.

Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ƙara girma ya kuma ƙara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da.

Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla.

"Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu.

Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers"

 Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji

"Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla.

Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?"

Gabansu ne Ya faɗi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta.

Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga!  Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba.

"Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...." 

bata ƙare maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruɗe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru.

"Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take?  Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla.

Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata..

"Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ƴata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"? 

Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani.

Gaba daya maganganun Aisha sun ruɗa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan ɗaya, ya rasa gane inda suka dosa.

Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba"

"Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"! 

Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"!

In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....." 

kasa ƙarasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un..

"Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi,     amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..." 

Benazir bata ƙarasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu.

"Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.." 

Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta  sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ƙofar.

Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️

Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Good morning, da fatan Kina lpy, waiting for the next chapter please

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post