Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 67 Complete by Boss Bature

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 67 Complete by Boss Bature

Takun Ƙarshe

The Unexpected Guest

Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba.

"Me ke damun ki"? Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara.

Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta,

Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki buɗewa kamar zata saka kuka.




Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali? If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"?




Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta.




"Fada min meke damun ki? Baki da lafiya ne? Ai ko ki akayi guri na? Ko kinzo ne don ki gaishe dani'?




Cikin rawar murya tace"am sorry,  bansan na shigo ba, ba wanda ya aiko ni, "




"Look, ni nasan ba hakanan ki ka zo ba, dole akwai abunda ya kawo ki daki na, just Calm down and tell me   "




Batare data juyo ta dube shi ba tace"ka ba Unaisah akwati, ni baka bani ba kuma inaso"



Murmushin gefen fuska ya saki"Akwati biyu nace ta dauka, daya nata daya naki"




"Ai daya ne tazo da shi, kuma tace nata, ita kadai ka ba mawa"


juyawa yayi tare da kallon inda ya ajiye akwatinan daya ya gani.


"Oh, ina tunanin ta manta bata ji ni dakyau ba..." ya juya ya nufi akwatin ya janyo handle dinshi ya mika mata"ga naki kema" maimakon ta juyo ta kar6a sai ta mika mashi hannun ta ta baya don ya bata.




"It's improper ki juya mun baya ina magana, if you wanna me to give it to you, Turn around and face me"


sarai ya fahimci shakkar shi take ji, kuma tana da kunya. 



Dakyar ta juyo ta fuskance shi idanunta na kallon floor.



dayasan haka zai ganta inya matso kusa dabai ce ta juyowa ba, saboda gaba daya shatun nipples dinsa sun fito sosai ta jikin rigar baccin ta, bata saka bra ba, da sauri ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, Ya mika mata akwatin hannunta na kerma ta ruƙe handle dinta cike da zumudi ta juya zata fuce ya dakatar da ita.




"Kar in kuskura in ƙara ganin kina yawo babu mayafi akanki! Ki dinga suturta jikinki dakyau" 



gabanta na faduwa ta amsa mashi da toh, Ya raba ta gefenta Ya danna code din kofar ta buɗe da sauri ta fuce, tsayawa ya yi yana kallonta yayin da take jan akwatin ta nufi stairs, sai dadi take ji har zukunnawa tayi kan stairs ta shasshafa jikin akwatin batasan yana kallonta ba, sai da tagama kalle shi ta mike cike da zumudi ta karasa sauka down ta nufi dakinsu don taje ta gwado ma Unaisah itama ya bata suitcase.


Sakin kofar yayi ta yi locking kanta, har zai juya idanun shi suka sauka akan siraran gashin kanta da ya kakkaba a kan floor, wasu irin dogaye masu kanannaɗa.



 juyawa yayi ya nufi tissu box dinsa dake ajiye gaban mirror ya yago tissue ɗin ya dawo ya zukunna gaban gashin Ya daura tissue din Ya nannaɗo su aciki, Kafin ya mike ya nufi drawer, ya bude Ya sanya Tissue din a ciki.



______________________________🔥🔥🔥




Bayan Kammala Sallar Juma'a around ƙarfe biyu da yan mintuna, Hamshakan Motoci Suka fara tururuwar shigowa Obie Estate, bakowane a cikin su ba face yan uwa da Abokanan Chief Owais yan team dinsa na isod tare da U.s Armies.




Raba hanya motocin su kayi wasu suka nufi Gidan Baba Obie yayin da wasu suka nufi Gidan Chief Owais..



*CHIEF OWAIS🔥💪*




Yana atsaye Cikin Lift, ya dauki wankan tuxedo suit, anyi masu adon Gold Gem stone dark blue, sai kyalli su ke yi, kayan sunyi fitting dinsa, ga wannan hadadden ducktail hair style din da yayi ma sumarsa.


 idanunsa na akan wrist watch dinsa kirar patek philippe wanda sai dan wane da wane suke sanyata.



 Time yake kallo, Yana karasa saukowa down Lift din ta buɗe Ya fito Ya nufi Dining area Tun kan ya karasa fragrance dinsa Ya daki kofofin Hanci nan su kusan atare suka dago suna kallon shi, ya yin da  su ke a zaune kan Dining Chairs suna cin lunch din su.



kasa haɗiye kingin abincin dake a bakunan su sukayi saboda rudewar da sukayi na ganinsa, Ya tafi da imanin su, Ba ummi ba ba taj ba har Unaisah da Batool sun shagala da kallon shi..



Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka gyara nutsuwar su..




Cikin girmamawa Ummi da Taj suka gaishe da shi, fuskar shi asake ya amsa masu kafin ya mayar da dubansa akan Unaisah dake ta kallon shi a fakaice Ya kashe mata ido ɗaya, gaba daya ya ƙara dagula mata lissafi, sai ta dinga ganin kamar Danish ne.



"Happy birthday Chief namu, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka, Allah ya kara girma da daukaka, Allah ya kare mana kai daga sharrin makiya da mahassada"


"Ameen, Thanks, Allah yabar zumunci atsakanin mu"




"Bangane ba, Yau ne birthday din Chief, shine ba'a fada mana ba"? Ummi ce ta faɗa tana duban Taj




"Am sorry, Laifi na ne da ban fada maku ba, yau ne Birthday dinsa, ya ƙara shekara daya, saura kaɗan ya cike 40yrs" ya fada da zolaya yana murmushi.




"Amma dai banji dadi ba, da an fada mana da wuri ay da mun shirya muma anyi celebration din da mu"! 




ta faɗa tana kallon Chief, tattausar murmushi ya sakar mata.




"ay min afwa, Idan na dawo da anjima zamuyi wani celebration din agida.."




"Allah yakaimu anjima lafiya, sannan nima ina tayaka murnar birthday dinka, Allah ya cika maka burikanka na rayuwa, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya mara yankewa arayuwarka, Allah ya ƙara maka lafiya, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cika makon jin dadin rayuwar ka..."



 a hankali yake amsa mata da ameen ameen, Unaisah tun da taji an ambaci mata tagari kuma taga ya kalle, ta dan saki murmushin gefen fuska tare da kawar da idanun ta gefe ɗaya.




"Happy Birthday Chief, Allah ya faranta maka rai kamar yadda kake faranta mana" 


Batool ce ta faɗa da murmushi akan fuskarta, kallonta yayi ganin ta yi rolling mayafi akanta hakan ya tabbatar masa da taji warning din da ya yi mata.




"Thank You,"




Wani kallo Taj yai ma Unaisah hakan yasa tace"happy birthday My husband to be, Allah ya baka nasara akan abunda kake nema, Allah kuma ya cika maka burikan ka"



Waro idanu Ummi tayi"What"? cike da jin kunya ta sunnar da kanta ƙasa, Batool ce kadai bata fahimci me tace ba, shi kuwa Chief ƙayataccen murmushi Ya saki idanun shi akan fuskarta, Taj sai faman sakin murmushi yakeyi Yaji dadin abun nan.




"Amen, shukran laki wife to be, Allah ya cika mana burin mu" cike da jin kunyar daddynta ta amsa mashi da ameen.




"Zan kai karfe shida, pls kafin na dawo Ku shirya kanku, zan ma Chefs magana su hada maku Cake..."


 haɗa ba ki su ka yi gurin yi mashi godiya, tare da fatan Alkhairi.


har ya juya baya basu daina kallon shi ba, yadda yake tafiya cike da aji ba karamin kayatar da su yayi ba, kafin taj ya dawo da duban shi gare su tuni Unaisah ta gudu zuwa daki saboda kunyar kada ta hada ido da shi.




Yana fitowa Falo Yayi Arba da motocin da ke shigowa Villa Dinsa, a jere suka tsaya a parking Space.


Ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga Cikin motocin, Kowan nan su Ya ɗauki wankan expensive Suits na kece raini, tun daga kan CO, CI, Agent zahra and Osman, tare da U.s Armies, fuskokinsu dauke da farin ciki suka nufe shi, aransu sai yaba kyawun shi su ke yi su kansu wankan shi ya tafi da imanin su, Gaba daya sai yaji bakin Ciki Ya mamaye zuciyar shi saboda rashin Ganin Omar atare da su, Farin cikin shi ragagge ne, suna karasowa suka sara mashi, shima Ya sara masu, tare da mika masu hannu daya bayan daya sai da ya yi Musabaha da su, a mutunce suka gaisa da junansu, bayan sun yi mashi happy birthday, Saida suka fara shigowa Cikin gidan suka duba jikin Taj kafin suka fito, ahanzarce security officers suka bude masu Cardoor suka shiga cikin motocin a jere suka nufi Cikin Obie Estate.




Daidai Lokacin da za'a fara gudanar da Shagalin, gaba daya Hall din a kewaye yake Da sojoji harma da Isod Soldiers, baka jin komai sai sautin  kidan Isod Anthem dake ta shi.




A gaban Hall din motoci suka dinga yin parking.




Ahanzarce Jami'an suka soma bude masu cardoors...




Yana ƙoƙarin fitowa daga Cikin motar, Idanunsa suka sauka akan Daddynsa dake fitowa daga cikin motar shi, Karaf idanunsu suka shiga cikin na juna, nan da nan Ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi gefe ɗaya.



Girgiza kai sharafuddeen yayi duk sai yaji ba dadi, badan ya damu da shi ba, da ba abunda zai sa shi zuwa birthday dinsa sai dai shi bazai biye mashi ba.


gaba ɗaya Uncle dinsa sun fito daga cikin motocin su hada Baba Obie, jikokin family din bakowane Ya samu damar halarta ba, wasu uzuri ne ya ruke su, kowan nan su Ya dauki wankan shadda geztner blue sky, sai ya zamana kamar sunyi anko da Chief ne.


Akan Idon shi Chief Ya nufi Baba Obie yayi hugging dinsa tighly tare da manna masa peck a cheeks dinsa, bayan sun gama gaisawa ya nufi Hateem Yayi hugging dinsa kafin Yabi sauran Uncle dinsa da Yan uwansa duk yayi hugging dinsu, amma shi ko arzkin gaisuwa bai samu ba, hakan ba karamin taba zuciyarshi yayi ba.


babu wanda ya lura da hakan sai Hateem dama tunda yazo ya fahimci akwai wani abu dake damun Dan uwansa, bai dai tambaye shi ba, sai yanzu yaga amsar tambayar shi lamarin ya daure mashi kai sosai.


Gaba ɗaya suka dunguma izuwa Cikin Hall din da aka kawata shi da decoration, makada da mawaka da akayi inviting Sun hada kai sai kirari suke yi ma Chief.


basu dade da shiga Ciki ba, Saiga Mommynsa gimbiya malik tare da hajiya laura da kanwarsa hindu sun shigo, gaba dayansu Laces ne a jikin su, yana ganinsu ya nufe su, tun kafin Ya karaso hindu ta riga shi isa tayi hugging dinsa tighty tana fadin"happy birthday Big bro, we're so proud of you"


fuskarshi dauke da murmushi Ya dan bubbuga bayanta da tafin sa.


Kafin ya dago ya rungume mommynsa, shafa sumar kan shi tayi"happy birthday, my beloved son, You're the light of our family, and I'm so grateful for your kindness, compassion, and leadership, May this year bring you happiness and success."



"Ameen mommy, I can't thank you enought, kin gama min komai, kece silar daukakana" ya fada tare da raba jikin shi daga nata, murmushi suka sakar ma Juna.


Kafin ya dubi Hajiya laura, suka gaisa a mutunce itama ta yi mashi fatan Alkhari.




Shigowa Hall din Hajiya Saratu tayi, jikinta sanye da pakistan na manyan mata riga da wando, tayi rolling veil akanta, ga wani hadadden shade fari data saka, ta wanku iya wankuwa, pravin Yana a gefen ta, yayin da su twins ke abiye da bayansu, gaba dayansu Indian outfits ne a jikinsu, sunyi bala'en kyau, sun fito da ainihin suffar su ta indiyawa.




Hajiya laura na ganinta ta nufe ta da fara'a suka yi hugging din Juna sai yaba kyanta Hajiya laura take yi, bayan su twins suna gaishe da ita suka wuce Gurin Chief, suna karasowa Ya yi hugging dinsu atare sukayi mashi happy birthday.


 Pravin ma Yaje yayi mashi, kafin Hajiya saratu itama ta matso kusa tayi hugging dinsa tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kafin kace me tuni Hall din ya cika da yan uwa da abokan arziki, Sai yan gaishe gaishe suke yi atsakanin su, 


Hatta U.s Armies da Senior agents saida Chief  ya kai su gurin baba Obie suka gaishe da shi, ya kuma kaisu gurin Mommynsa suka gaishe da ita cikin girmamawa, haka sauran Uncles dinsa duk saida su ka gaisa da abokan aikin sa mahaifinsa ne kadai bai kai su wurin shi ba.



daga bisani Mc ya hau kan Stage, hannun shi ruke da mic, ya farayi ma Baki maraba da zuwa, tare da gabatar masu da kan shi, dayawa sun gane fuskarshi shine yayi mc A farewell dinner na hateem, Baba Obie ne ya yi inviting dinsa a wannan karo ma.




Bayani ya soma korawa, Hankulan Kowa Ya dawo kan shi.




_"Ladies and gentlemen, esteemed guests, family, and friends, welcome to Chief Owais's birthday celebration!"_




_Today, we gather to honor a remarkable leader and an extraordinary individual"_ ya fada yana nuna Chief Owais.


 gaba daya suka fara tafa mashi, bayan ya kammala Speech dinsa Yayi inving Iyayen Chief don suyi speech dinsu, bayan Gimbiya Malikat Ta kammala nata mutane sunata tafa mata, Mai girma sharafuddeen ma yayi nashi Speech din mai ratsa zuciya, sai dai ko kadan Chief bai nuna Yaji dadin yabon da yayi mashi ba, saima yaki dagowa su hada idanun su, hakan ba karamin bata ran Mai girma shafuden ya yi ba_




Time da Mc yayi inviting Chief don yayi speach dinsa, Hankalin Kowa na hall din ya dawo kan shi...




Cikin nutsastsiyar muryar shi mai Jan hankali Ya kora jawabi mai matuƙar taba zuciya, abun da ya kara daurewa Uncles dinsa Kai Jin ya yabi mahaifiyarsa tare da su,  amma bai sanya sunan mahaifinsa ba, basu kawo komai aran su ba, saboda sun yi tunanin ba dagangan ya yi ba.




Bayan Ya kammala speech dinsa Mc yace"I'm inviting his wife to give a speech on stage"


 Tunkan Ya kare maganar Hajiya saratu ta ɗaga murya tace"ai har yanzu bashi da aure, tazuru ne"


 gaba daya hall din suka kama dariya cikin nishadi, sun sa shi jin kunya.




Cike da zolaya Mc Yace"Chief what are you waiting for? Me ka nema ka rasa? Zankadedan saurayi kamar ka, burin kowace ya mace uhm? Ya faɗa yana kallon sa, kamar baisan yanayi ba, idanunsa na akan wayarsa da yake dannawa..


"Cikin yan matan nan da suke hauka akanka ya kamata aba daya dama mana" dariya suka sanya, 




Hajiya saratu tace"He has a fiancee, Insha'Allah, we will soon invite you to his wedding celebration"


Gaba daya jama'ar dake acikin Hall din suka sanya shewar murna.



Daga Bisani Labulan daya Lullube ke6ataccen gurin da aka tanada saboda Chief ya soma ɗagewa sama  a hankali gaba daya hankulan mutane ya koma kan shi




Wata katafariyar throne Chair ce da aka kawatata saboda shi, daga gaban kujerar wani hadadden table ne anan aka daura katon cake din da akayi domin sa, mai hawa 10 hada sunan shi a jikin Cake din da wani salon rubutu me jan hankali akayi shi, daga saman silin din gurin an kawata shi da navy blue balloons da steamers, wurin Ya burge mutane, friends dinsa ne suka yi mashi rakiya Ya hau kan kujerar Ya zauna tare da daura kafarsa ɗaya kan ɗaya like a King on his Throne.




Minti 30 aka ware saboda baki su samu damar Cin abinci, bayan kowa yaci yasha anyi kullu wash rabu hani'an Mc Ya sa Mawaka suka fara wake Cheif Owais, wakar tayi mashi dadi hatta yan uwansa sunji dadin wakar birthday din da akayi masa.




Lokacin da Mc Yayi inviting Yan uwa da abokan arziki donsu fito tsakiyar filin su taka rawa, nan fa suka fara hawa kan dancer floor din cike da nishadi suke taka rawar girma, kowa saida Ya taka In ka cire Mutun daya Mai girma sharafudden da ransa yagama 6aci, Jira yake kawai agama shagalin su shiga family meeting don Ya fallasa abun da ke faruwa tsakaninsa da owais, saboda hakurinsa ya ƙare ya ƙwammace kowa ya ji.




Lokacin da aka kusa kammala shagalin, Yan uwa da abokansa suka taya shi Yanka cake, ya 6allo cake din Yaba momynsa abaki, bayan taci itama ta debo ta saka mashi abaki yaci.


 ya bi Uncle ɗin sa daya bayan daya ya gutsuro cake ɗin ya sanya masu abaki suka ci, ko da yazo kan sharafudeen Saida Ya fara aika masa da harara kafin Ya bashi cake din, badan idon mutane ba da ba abun da zaisa ya ci cake din nan, hakanan ya jure ya bude baki Ya sanya mashi cake din kamar anyi masa dole.


Bayan ya gama basu Hindu ta debo cake din ta bashi abaki, shima ya bata abaki, Baba Obie Ya ballo Ya tura masa abaki, kowa ka kalla fuskarsa dauke da farin Ciki banda mahaifinsa.




Mintuna talatin da suka rage kafin A kammala Birthday din, photographers suka fara daukar su Hotuna da videos, sai da Chief Ya dauki hoto da kowa daya halarta amma banda mahaifin sa, Ko kusa da shi Yaƙi bari Yazo, balle yasa ran zai yi hoto da shi.




Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, Yan uwa da abokan arziƙi sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, bayan kammala addu'ar tashi daga taro da Mc ya gabatar tare da yi ma Baki fatan sauka gida lafiya.



*HAJJATY🍁*



Tana akwance kan gadonta, Ta lullube kanta cikin bargo, Jikinta sai makekketa yakeyi saboda zazzabin daya lullu6eta, duk yadda taci burin ta halarci birthday din Owais, Allah bai nufa ba, Tun safe take fama da zazzabin har magani tasha amma yaƙi sauka, har kiran layin Pravin ta yi don ta fada mashi halin da take aciki amma bai yi picking call din ba, rabon ta da shi tun bayan  kammala sallar asubahi daya leko dakin ta bata ƙara ganin ƙeyarsa ba.


Yan aikin gidanne kadai suka san bata da lafiya, Har abinci suka kawo mata amma takasa cin shi, burin ta kawai taga pravin saboda shi kadai ne zai iya kwantar mata da hankali.




________________FAMILY MEETING🔥




"Owais meya haɗa ka da Mahaifinka? Meyasa kake zarginsa? wani laifine kake tuhumarsa da shi Ya fada min ba yadda bai yi dakai ba akan ka fada masa amma ka ƙi sanar da shi why pls"? 


Hateem ne Ya faɗa Idanunsa a kan Chief owais dake a tsaye yana fuskantarsa, Suna a cikin dakin Baba Obie.




Fuskarsa babu walwala ya furta"zanyi maka bayani anjima"


 girgiza kai Hateem yayi ransa abace yace"No, Yanzu nake son ji Owais, Dole ka amsa min tambayata idan har ba so kake raina Ya baci ba"! 


Shiru yayi saboda ya rasa ta ina zai fara kora masa jawabi.



"Hateem meke faruwa ne? Har an fara shirin Family meeting bangan ku ba, yanzu nake tambayar kuna ina, auta take fadamin taga shigowarku dakin baba "


 Sir mubarak ne ya yi maganar yayin da ya ke shigowa dakin idanun shi akan su.


Kafin wani daga cikin su Ya furta Kalma suka ji an banko kofar dakin gaba daya suka kai dubansu ga mai shigowa.


Mai girma sharafuddeen ne Ya shigo dakin fuskarsa kwata kwata babu annuri, sai huci Yake yi kamar mayunwacin zaki, kaitsaye ya nufi Owais yana karasawa gaban shi, Ya damƙo Arm dinsa da ƙarfi Ya fusgoshi Ya nufi kofar  dakin da shi...



Hankali atashe Hateem da Sir Mubarak suka bi bayanshi suna kokarin dakatar da shi.


Bai nufi ko'ina ba sai falon, A lokacin Baba Obie tare da sauran Uncles dinsa da Hajiya saratu duk suna a Falon kowan nan su yana azaune kan sofa, shigowar Shafudden ne Ya ɗaga hankulan su a razane suka mimmike tsaye , cike da rudu suke kallon su..



"Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..."



"meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"?



 Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza miƙewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ƙasa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa.


Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faɗa maka" 



ya faɗa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya ɗaura min karan tsana, yau wata ɗaya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina  akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faɗa...." 


Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta..


Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa.


Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"?




"Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla.




Gaba daya basu ji dadin abun da  Owais ya yi masa ba.



Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"? 


Ya faɗa yana kallon chief wanda har lokacin bai ɗago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa.




"Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar..




His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"! 



Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, "


 ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka,"




Pravin da ke ƙoƙarin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su.



A fusace Owais Ya miƙe tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi.




Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba.


Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci.


Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi.


Dakyar ya haɗiyi ƙululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi..




Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"?




Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..."




Gyaɗa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana ɗaya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ƘADDARA❗...."



 Aruɗe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"?



Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faɗa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa?



Hateem har ya buɗe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba.




Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji.




"ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..." 


bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya damƙi kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..."


"Haba yaya Sharafudeen pls Owais.."


 Hajiya saratu da ta ɗauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba.




Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!" 


 fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, ɗan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da ɗa suna faɗa atsakanin su.."


 fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace.



Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba.


"Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba..


Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa..


Lokaci ɗaya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi.


bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa.


wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin


"zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...." 


girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa.


"Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa.


Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma.



Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. 


"Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..." 


His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa.


"Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"?



Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba,




"Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba,  kunsan dai ba zai yi maku karya ba....." 



Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..."


dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...." 


juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi.


Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne.


Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi.


Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais..


Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa..




"Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"? 



Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya.


"ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"?  his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar.


Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba.


A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba..




Hannayen shi dake kerma ya ɗaga sama cikin karyayyar murya ya ce 



_"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...."


 bai kaiga ƙarasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaɗe kunnuwan su

*_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_


*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

3 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post