Amfanin Gwanda 5 A Jikin Dan Adam

Amfanin Gwanda 5 A Jikin Dan Adam

Lafiya Uwar Jiki

Amfanin Gwanda 5 A Jikin Dan Adam

Gwanda

Gwanda wata dan itaciya ce daga jerin ‘ya’yan itace da ganinsu ma ya isa ya sa ka dauka ka kai baka. Ferarriyar, lafiyayyiyar, nunaniyar gwanda na da daukar ido da sanya sha’awar shan ta. Ko shakka babu wannan fa’ida ce da duk wani abinci da ya cika sunansa abinci ya kamata ya samu. Shi yasa ake shawartar iyaye mata da a duk lokacin da suka tashi shirya abinci ga yaransu, musamman ma yaran da ba sa son cin abinci sosai, to, sai su kawata abincin da kaloli ta yadda zai dauki ido tare da motsa sha’awar cinsa.

Bayan ga kasancewar gwanda abinci mai daukar ido, gwanda na da zaki a baka, dadi da karawa kuma da tsoka mai taushi ta yadda gutsara da taunawarta ba ya wahalarwa. Har ila yau, gwanda ba ta da wuyar samu. Ana iya samun gwanda a duk kwanakin shekara, kuma babu wani yanayi da ya ke sa tsadar gwanda ta kai mutum ya kasa sayenta.

Banda wannan kuma ga wasu dalilai har dozin guda za su sa ka sanya gwanda a jerin abincin da ka ke ci a kowace rana:

Dalili na 1:

Gwanda na dauke da sinadarin fibre da na bitamin c da ke hana wani nau’i na kitse da ke taruwa har ya toshe hanyoyin jini ginuwa. Wannan kitse ana kiransa da suna Cholestrol a turance. Sinadarin Cholestorol da na lipid wadanda suna da nasu amfanin a jiki, in suka yawaita suna toshe hanyar jini wanda hakan ke komawa ga sai zuciya ta wahala kwarai kafin ta gudanar da aikinta, wanda hakan kuma kan juye zuwa ga ciwon zuciya. 

Dalili na 2:

Gwanda na taimakawa wajen rage kiba ko taiba, saboda kowace gwanda mai matsakaicin girma na dauke da Calories 120. Calories wani nau’i na zafi ne da ke samawa jiki karfi tare da narka taiba. Kasancewar gwanda abinci maras nauyi kuma dauke da sinadarin dietary fibre da ke taimakawa wajen rage nauyin jiki da kuma yawan bukawa ga abinci, gwanda abinci ce da duk mai bukatar rage kiba ya kara a abincinsa na yau da gobe.


Dalil na 3:

Gwanda na dauke da kaso 200 na adadin bitamin C da jikinka ke bukata a kullum. Wannan bitamin C da ke ciki.

Dalili na 4

Likitoci sun yi bayanin cewa gwanda na ƙunshe da sinadaran da ke ƙara wa ɗan'adam lafiyar jiki, musamman ma ido.

Idan mutum ya ci yankan gwanda sau ɗaya a rana ya ishe shi ya samu vitamin C da yake buƙata,

Haka nan, tana taimakawa wajen rage hawan jini, da ciwon zuciya, da kare kumburin cikin jiki, da kuma rage kaifin cutukan da tsufa ke jawowa.

Dalili na 5

Gyaran Fata

Gwanda na daya daga cikin ’ya’yan itatuwa da ke dauke da nau’ukan sinadaren da ke kara wa mutum lafiya. Yawan cinsa na taimakawa hanjin ciki wajen nika abinci a sawwake sannan yana taimakawa wajen gyara fatar jiki domin yana dauke da sinadaren bitamin A da C. Wadannan sinadaren na sanya sulbi da sheki da kuma hasken fata a fuska ko a jiki. A yau na kawo muku hanyoyin da za abi domin amfani da gwanda a fatar jiki.

Idan fatar mutum ta kasance tana da gautsi walau a fuska ko a jiki, yana da kyau a nika gwanda sannan a zuba cokali daya na zuma sannan a shafa a inda ake da matsala na tsawon minti talatin kafin a wanke.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post