Ciwon Ciki Lokacin Al’ada), Dalilai Da Maganinsa.

Ciwon Ciki Lokacin Al’ada), Dalilai Da Maganinsa.

Ciwon Mara Lokacin Al'ada

Ciwon Ciki Lokacin Al’ada), Dalilai Da Maganinsa.

 Ayi sharing domin yan uwa su amfana 

Ciwon ciki lokacin da ake yin jinin al’ada  wani abu ne wanda yake da matukar matsala matsala ne da kuma yawancin mata, ke fama da shi. Mafi akasari ‘yan matan da su ka fara yin al’ada sabuwa, sun fi fama da shi. Idan mace na girma matsalar kan ragu ne, har in ma ta yi sa’a ta rabu da ita gaba daya.

Dalilin da suke kawo shi:

Matsuwar mahaifa (Uterus Contraction): A  lokacin da mace ke  fama da jinin al’ada mahaifarta kan matsu, bayannan kuma sai ta  takura hanyar jinin da ke kusa da ita, wannan takurar na hana iskar odygyn shiga mahaifar na wani kankannen  lokaci. Wannan rashin iskar shi ke kawo wannan ciwon ciki.

Wasu da ga cikin wadanda suka fi fama da shi a cikin mata sun hada da:

‘Yan mata kasa da shekara 20

‘Yan mata da ke fara balaga daga Shekara 11 ko kasa da haka

Zubar da jinni mai yawa yayin al’adar

Rashin haihuwa

Alamomin ciwon cikin kan zo da wa su abubuwa kamar haka:

Ciwon baya da cinyoyi

Tashin zuciya da ama

Hada zufa

Jin Jiri

Gudawa ko sakakken bayangida

Daurewar ciki (constipation)

Ciwon kai

Lalacewar ciki (bloating)

Wasu da ga cikin hanyoyin  magance  ita cutar a gida:

Zama cikin ruwa mai zafi na dan lokaci (hot bath)

Gasa kasan cibi da ruwa mai dumi ta hanyar amfani da ruwa mai zafi a gora ko tawul da makamantansu

Kokarin ganin likita in har abin ya tsawaita

Wasu daga cikin hanyoyin da za a bi don rage shi:

Yawaita cin ‘ya’yan itace (fruits) da ganye (begetables)

Rage cin abinci mai maiko, abinci mai caffeine (sinadarin kofi) da gishiri da kayan zaki (sweet)

Motsa jiki lokaci zuwa lokaci

Rabuwa da shan taba

Rage shiga damuwa (stress)

Daga karshe  duk lokacin da matsala ta dame ki kar ki zauna a gida. Ki yi kokarin ganin likita cikin gaggawa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post