KAWA ZUCI
©SALMA AHMAD ISAH
Page 02
Kauyen Kinkin, yankin kabilar Hadzabe, kusa da tafkin Eyasi, arewacin Tanzania, Africa.
Matasan ƙabilar ta Hadzabe ne su biyar durƙushe a saman wasu ciyayi, yayin da suke fakon wata barewa da take cin ciyawa a cikin daji. Gabaki ɗaya su biyar ɗin na sanye da tufafi iri ɗaya, bayan T-shirt da wando sai wani zani da ko wannensu ya ɗaura bisa kafaɗarsa, sarƙoƙin dake wuyansu kuwa sun wuce ƙirge.
“Nikamba jittiko nabsi kokuram, shidafo” (Nikamba kai zaka fara harbinta, yanzu)
Cewar wani sirirn saurayi cikin samarin biyar da yaransu Hadzane, ga ɗaya daga cikinsu da ya ƙira da Nikamba.
Saurayin mai suna Nikamba ya jinjina kansa tare da ɗaga hannunsa na hagu dake rike da kwari, sannan ya daga na daman dake rike da kibiya, ya saita barewar da ta yi nisa a cin ciyawar da take, sai da ya tabbatar da ya saitata yadda ya kamata, kafin ya saki kibar, kan kace kwabo barewar ta faɗi ƙasa tana shure-shure, sakamakon kibiyar da Nikamba ya harba ta sameta a gefen wuyanta. A sukwane samarin suka miƙe suna ihu tare da sowa suna ta kuranta Nikamba cikin yaransu mai suna Hadzane .
***
Zaune take a bakin wata bukka, ta aje wani gajeren sashin dutse da ta ɓantaro, ta saka wani ƙashi mai kaifi tana zane bisa dutsen. Bayan wata doguwar shirt da wani dauɗaɗɗen zani da aka saƙa da zaren audiga irin saƙar kabilarsu babu komai ajikinta. Shi ma kuma zanin ba wai ɗaura shi ta yi gaba ɗaya ba, ta ɗaure shi a kafaɗa ɗaya ne kamar dai dinkin da a zamanance ake ƙira da one shoulder, duk da dauɗa da ta yi wa fatar jikinta cover ba za ka kasa gane cewa fatar jikinta baƙa ba ce.
Wani irin ƙugin yunwa cikinta ya yi, alamun yana buƙatar abinci, da sauri ta dafe cikin nata tana zare ido, ƙashin dake hannunta ta aje, sannan ta shiga sosa kanta tana kallon zanen da ta yi jikin dutsen, zanen dogayen tsaunikan da suke kewaye da ƙauyensu ne, kuma ta zanasu a siga mai ban mamaki, domin kana kallon zanen zaka gane cewa ƙwararriya ce a fagen. Dutsen ta ɗauka tana kallon abin da ta zana da hannunta, sai kuma ta yi murmushin da ya bayyanar da daffafun haƙwarenta wanda dauɗa ta musu kwalliya. Har wani kore-kore suka yi, kamar gansa kuka na rayuwa a jikinsu. Iface-ifacen da ta soma ji a cikin ƙauyen yasa ta gane cewa samarin da suka tafi farauta yau wanda suka haɗa da yayanta sun dawo.
“Nikamba?”
Ta furta sunan tana miƙewa tsaye, kafin ta falla da gudu ta bar sashen bukkar tasu, dan gidan ba a kewaye yake ba, kamar dai sauran gidajen ƙauyen. Wata mata da dauɗar dake jikinta ba zai bari ka ce ga kalar fatar jikinta ba ce ta fito daga cikin bukkar, wata T-shirt ce a jikinta, wanda alamu suka nuna cewa milkcolor ce a baya, amma yanzu ba ka isa ka tabbatar da hakan ba saboda yanda datti ya fitar da rigar daga hayyacinta, duk duniya wannan rigar ita kaɗai ce rigar da take da ita, ita ma ɗaya daga cikin ƙungiyoyin tallafi da suke zuwa ziyartar ƙauyuka irin nasu ne suka bata. Ba ma ita kaɗai ba, kusan duk kayan zamani da za ka ga a jikin wani na ƙauyen to masu kawowa tallafi ne suka ba shi. Saboda a da can baya jama’ar ƙabilar Hadzabe ba sa saka tufafi, da tafiya ta yi tafiya ne suka fara saka wasu tufafi na fatar dabobbin da suke farautowa, domin farauta na ɗaya daga cikin al’adun da ƙabilar ta shahara a kai. Sai dai duk da yanzu zamani ya fara shigarsu ba su daina ta’ammali da kayansu na al’ada ba, domin iyaka tufafinsu kawai suka sauya, har yanzu suna saka sarƙoƙi irin na al’adarsu da su da dai sauransu.
“AKIRA!”
Matar ta ambaci sunan da ƙarfi tana hangen ƙurar AKIRA da ta kusan kaiwa tsakiyar ƙauyen da gidajen cikinsa ba su fi a ƙirga ba, saboda ba su da wani yawa na ku zo mu gani.
“AKIRA nujjara batikim?” (AKIRA ba za ki dawo ba?)
Ta sake faɗi cikin harshen Hadzane da suke magana da shi a ƙauyen, amma Akira ba ta juyo ba ballantana ta dawo, ba ta taka birki ba sai da ta isa tsakiyar ƙauyen nasu, inda fadar sarkin ƙauyen nasu take, duk mutanen garin sun fito domin ganin abinda samarin ƙabilar da suka fita farauta suka farauto. Ta cikin jama’ar garin ta kutsa ta shiga gaban filin domin ganin ɗan uwanta dake kan gaba.
“Nikamba!”
Ta ambaci sunan dan uwan nata cike da farin cikin ganinsa. Nikamba dake ɗaya daga cikin samarin da suka je farautar wanda suke durƙushe gaban sarkin garin yana musu kalamin jinjina yan juyo ya kalleta, murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata hannu.
***
A saman dogayen tsaunikan da suka kewaye ƙauyen na Kinkin, a saman korayen ciyayin da suka lulluɓe dogayen tsaunikan, Akira ke tsugunne gaban wutar da Nikamba ya kunna, shi kuma Nikamba na zaune kusa da ita yana gasa naman da suka farauto yau, bayan an raba a fada an bawa kowa kasonsa.
Ta ɗaga kanta sama, tana kallon hasken farin watan da ya zame musu abokin raya dare, dan bayan hasken farin watan ƙauyen nasu ba ya amfana da hasken komai idan dare ya yi sai hasken wuta shi ma idan sun hura ke nan. Nikamba ya janye naman da ya kara a wuta yana gasuwa, sannan ya shiga juya shi yana kallo domin tabbatar da gasuwarsa, saitin hancinsa ya kai yana sinsinar naman, kafin ya saka yalayen hakwaransa ya yagi naman yana jinjina kai.
“Akira jo tu oje” (Akira dandana ki ji)
Ya furta cikin harshen Hadzane da aka san ƙabilar ta Hadza na amfani da shi wurin magana. Jin Akira ba ta amsa ba ballanatana ta karɓi naman da ya miƙa mata yasa ya kalleta, ta tattare gwiwoyinta ta ɗaga kanta sama tana kallon farin wata, murmushi ya yi wanda ya bayyanar da haƙwarensa da suka dafe da datti. Kafin ya saka ɗayan hannunsa ya dinguri kanta, hakan yasa ta juyo da sauri ta kalle shi.
“Guggu mukilla?” (Tunanin me kike?)
Kanta ta girgiza tana gyara zamanta, ta juyo gaba ɗaya tana fuskantarsa.
“Nikamba?”
“Hmm”
Ya amsa shi ma yana kallonta.
“Kiku nitalu an bakifu ji kuna?” (Yaushe za ka akaini cikin birni?)
Nikamba ya yi ‘yar dariya, domin ta tuna masa wani wuri da har gobe ba ya fatan komawa, wurin da rayuwa a cikin daji tare da namomin daji ta fiye masa shi sau ba adadi, wurin da aka taɓa muzanta shi, inda aka nuna masa cewa shi ba ɗaya yake da sauran ‘yan adam ba, dan kawai shi ɗan daji ne. Jin shirunsa ya yi yawa yasa Akira ta shiga jijjiga shi.
“Ni bikira Nikamba?” (Ka fada mini mana Nikamba)
Nikamba ya dubeta, yanda ta ɓata fuska kamar za ta yi kuka yasa ya sake dukan kanta.
“Rayuwarki a cikin wannan ƙauyen ta fi daɗi sama da rayuwar da ake gudanarwa a cikin gari, waɗannan mutanen da suke jin cewa sama suke da mu saboda suna amfani da kayan more rayuwa na zamani ba za su taɓa kallonki da daraja ba!…”
“A nan ɗin ana kallona da daraja ne?”
Ta tari numfashinsa kafin ya kai ƙarshe.
“Duk ranar Lahadi sai sun yi addu’a ta musanmman a kaina, kai kanka ka san zaman dole suke da ni, kowa ya tsaneni, kuma sun ce babu wanda zai taɓa sona saboda tsinuwar abar bauta ce a kaina. Nikamba a wasu lokutan ina jin da ace ni ce na samu damar da ka samu ta karatu a cikin gari da ba zan taɓa barinta na dawo cikin wannan ƙauyen ba. Domin rayuwa a nan babu marabarta da mutuwa, na sha fatawa kaina mutuwa saboda wata ƙila idan na mutu komai zai ƙare”
Nikamba ya sauƙe numfashi, sannan ya sake matsawa kusa da ƙanwarsa. Ya miƙa mata naman dake hannunsa ta kalle shi, kafin ta kalli naman ta sake kallonsa, ya mata alama da ta karɓa, ta karɓa ta soma yaga tana ci.
“Kina ji ko Akira?... Ni na je na yi rayuwa tare da sauran mutanen dake cikin gari, kuma rayuwar da na yi a cikinsu ta koyar da ni abubuwa da dama, abu mafi muhamanci da na koya daga garesu shi ne yaren da suke magana da shi a cikin Tanzania, sai kuma wata kalma mai sunan banbanci da suka taɓa faɗa mini…”
Ya ɗan yi fasali yana grigiza kansa, ita kuma Akira dake cin naman da ya bata ta tsaya tana ta kallonsa, duk duniya idan da akwai abin da take so the most bai wuce labarin yanda wasu mutane ke rayuwa a cikin gari ba, domin duk sanda masu kawo musu tallafi ko ‘yan jarida za su ziyarci ƙauyen nasu tana ɗaya daga cikin masu zuwa kallonsu, domin yanda Nikamba ke bata labarin rayuwa a ckin gari yasa ta fara sha’awar rayuwa a wurin. A tunaninta wannan wata hanya ce da za ta rabata da ƙauyen Kinkin, inda ba ta taso ta ga komai ba sama da ƙunci, damuwa, kyara da tsana. Hankalinta ta maida kan Nikamba da ya ci gaba da faɗin.
“Mts sun ce akwai banbanci tsakaninmu da su, sun ce ba za mu taɓa zama irinsu ba, sun ce mu ba kamar mutane muke ba… Akira? Idan har mu ba mutane ba ne yaya sunan hallitarmu?”
Tambayar da ya mata ta sa ta yi dariya.
“Zan so a ce wata rana na haɗu da hallitar mutane a cikin muhallinsu… Zan so ace na zama ɗaya daga cikinsu!”
“Ina fatan hakan, duk da abu ne mai wuya ki iya rayuwa a cikinsu, domin su ba sa cin abinci irin namu, tufafinmu da muke sakawa a yanzu yana kama da nasu, tun da su suka ba mu su, amma kuma sam ba sa shiga irin tamu. Na san yaren da ake a Tanzania ba zai baki wahala ba tun da na koya miki Swahili, amma idan har rayuwa ta kaiki wurin da ba nan ba zai kasance wani sabon ƙalubale ne gareki koyan yaren da suke magana da shi?”
Akira ta dube shi cikin alamar kokwanto tana faɗin.
“Da ma bayan Swahili akwai wani yaren?”
“Sai dai mu ƙirasu da yaruka… yarukan duniya sun fi a ƙirga, sannan akwai ɓabilu da ban da ban, akwai garuruwa, akwai yankuna, akwai ƙasashe, kafin kuma ita duniyar kanta…”
Nikamba ya ci gaba da bata labarin rayuwa a cikin sauran mutane, domin abu ne da ba ta sani ba, ba ma ita kaɗai ba, idan ka ɗauke Nikamba da wasu abokansa uku, babu wani rai dake ƙauyen da ya taɓa experiencing yadda rayuwa take a cikin gari. Su ma su Nikamban wata ƙungiya da ta zo daga cikin Tanzania ta ɗauki nauyin fitar da su cikin gari domin koyar da su yanda rayuwa take a cikin gari, har ta kai ga an sakasu a makaranta, tsangwama da kyara da suke samu daga wurin sauran jama’a yasa suka gudo, domin tsabar muzanci har a waya ake zuwa ana ɗaukansu ana cewa ga birran Africa, Wannan dalilin yasa zamansu a cikin garin bai yi tsayi ba suka dawo inda suka fi wayo.
*Masarautar Dutse, Jigawa State, Nigeria.*
SA’AD POV.
A hanzarce ya sauƙo daga stairs, ya shiga main falo na sashin Fulani Amarya wato mahaifiyarsa yana saka links a jikin hannun rigar shaddar dake jikinsa, a lokacin ya lura da wanzuwar mahaifiyarsa dake zaune a falon, likitarta na zaune kusa da ita tana ɗaura mata blood pressure monitor a damtsen hannunta.
“Wai da ma ba ki da lafiya Ammi?”
Ya tambaya yayin da ya ƙarasa cikin falon yana kallon Ammin tasu da alamunta suka nuna cewa ba ta da lafiya. Fulani Amarya ta ɗaga kanta ta dube shi, ya shirya tsaf cikin shigar manyan kaya na wata shadda milk color, babu aikin komai a jikin rigar kayan, sai hula da ya saka a kansa wadda aka yi wa aiki da baƙin zare.
“Tun jiya nake jin jikina babu daɗi, shi yasa na sa aka kira min Dr. dan ta dubani!”
Sa’ad ya kalli Dr. Mannira likitar masarautar, wadda ke duba matan sarki da kuma yaran masarautar.
“Ina kwana Dr”
“Lafiya ƙalau Sa’ad fatan an tashi lafiya?”
“Lafiya ƙalau… Yaya jikin nata?”
“Kai! Ni kar ka bi ka ɗaga mini hankali, jinyar tawa da ba ta kai ta kawo ba za ka naimi sakani a bakin duniya.”
Ammi ta yi saurin katse shi, sai kuma ta shiga binsa da kallo tana faɗin.
“Ina za ka je na ga ka shirya?”
“Asibiti za mu je tare da Maryam?”
Ya amsa mata kansa tsaye, take Ammi ta sauya fuska tana furta.
“Maryam?... Me za ku yi a asibitin?”
“Zan kaita ne domin a dubata?”
“Uhumm”
Kawai Ammi tace tana taɓe baki tare da ɗauke kai.
“Ni da za ku ɗauki shawarata da daga ku har Takawa kun daina ɓata lokutanku a kan wannan ciwon na Maryam, domin ko makoho ya shafa ya san cewa ciwon hauka ne yake damunta…”
Sa’ad ya miƙe tsaye yana gyara zaman hular kansa.
“Kar na ɓata lokaci da yawa, bari na tafi”
Ammi ta bi shi da ido tana jinjina kai dan ta gane cewa zancen nata ne ba ya so shi yasa ya ce hakan, har ya mata sallama ya fita daga falon ba ta sake cewa da shi komai ba. Sa’ad na fita ya hangi ƙanwarsa Aysha na dosowa sashin mahaifiyar tasu.
“Aysha”
Jin an ƙira sunanta yasa ta janye idonta daga kan wayarta da take latsawa tana tafe, ta zubesu a kan sa lokacin da ya tsaya a gabanta.
“Daga ina kuma ayawe?”
“Ka aikeni ne?”
Ta faɗi cike da tsiwa tana kallonsa, ranƙwashi mai zafi ya bata a ka yana cewa.
“To rasa kunya ɓeran tanka, ba rashin kunya na tambayeki ba, motarki za ki ara mini za mu je asibiti ni da Maryam!”
Wani irin kallo ta masa tana sosa kanta dai-dai inda ya bata ranƙwashi.
“Motata?”
“Eh mana motarki, da ta wa?
Baki ta turo gaba tana juya kai alamun ita ba za ta bashi ba.
“Ko ba za ki bayar ba ne?”
“Gaskiya Ya Sa’ad ka bi mini motata hankali, na san halinka da tuƙin ganganci, ga saurin kisan mota…”
Kwacewa keyn motar da yayi daga hannunta yasa ta bi shi da kallo, sai da ya dungure mata kai sannan ya raɓata yana faɗin.
“An jima ki sa Kasim ya je ya karɓo miki ita a gareji…”
“Ya Sa’ad mana!”
Ta fruta kamar ta yi kuka, bai ko juyo ya kalleta ba ballanata ya kulata, kai tsaye sashin Takawa ya wuce, mai girmna Alhaji Saminu Garba Wakili, sarkin Dutsen jahar Jigawa.
*
Shiru ya yi tare da sunkuyar da kansa bayan ya gama furta abin da ke bakinsa. Alhaji Saminu Wakili ya yi shiru yana kallon ɗansa da ya sunkuyar da kansa cikin ladabi irin nasa, zaune yake a saman carpet, kusa da ƙafafun mahaifin nasa, yayin da shi kuma yake zaune kan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da aka ƙawata hamshaƙin falon nasa da su, a hankali ya aje jaridar dake hannunsa, sannan ya sauƙe numfashi.
“Alamu sun nuna cewa ka fara nutsuwa Sa’ad!”
Alhaji Wakili da suke ƙira da Takawa ya furta yana wani gajeren murmushi, Sa’ad ya yi murmushi jin an yabe shi.
“Haƙiƙa tunanin da ka yi ya dace, a matsayinka na babba, amma akwai buƙatar mu sanar da shi Sadiq mijin Maryam, domin jin daga bakinsa…”
Sai da ya kai aya kafin Sa’ad ya sake sunkui da kansa yana furta.
“Ban raina azancinka ba Takawa, amma a ganina ba sai an gayawa Sadiq wannan batun ba, tun da shi da kansa ya dawo da ita gida domin a naima mata magani, kuma na san ko da an tambaye shi shi ma ba zai ƙi batun zuwa asibitin ba, shi da kansa ma ya sha kaita asibitin, banbancin wannan da wancan kawai shi ne mu za mu kaita ga likitan ƙwaƙwalwa ne, saɓanin shi da ya saba kaita a duba lafiyar jikinta”
Cike da ƙasaita Takawa ya saki wani murmushi yana jinjina ƙafarsa t, domin bai yi tsammanin samun wannan amsar daga Sa’ad ba.
“Shike nan Sa’adu… Mun baka dama ka kai ‘yar uwarka asibiti domin a duba lafiyarta”
“Godiya muke Ranka ya daɗe”
“Sa’adu!”
“Na'am Takawa!”
Ya amsa yana sake duƙar da kansa kamar mai shirin yin sujjada.
“Satin da wuce an ga gilmawar fitar naira dubu dari uku daga account ɗinka na banki… A sanina kai ba mata ce da kai ba, ba ka ciyar da kanka, babu nauyin wani a kanka, gidan da kake haya a Abuja ma mu ne muka kama maka, hatta da kuɗin mai da za ka zuba a mota mu ke biya maka, mun san babu nauyin kowa a kanka, me ka yi da kuɗaɗe masu nauyin waɗannan?”
Wani irin siririn yawu ne ya wuce ta maƙogwaron Sa’ad, kansa ya sake sinnewa a ƙasa yana saƙe-saƙe, domin ya rasa wata amsa zai bawa Takawa game da fitar kuɗaɗen, sanda zai cire kuɗaɗen sam ya mance cewa Takawa na lura da duk fice da shigen kuɗaɗen da yake kashewa, ba ma haka kaɗai ba, ya san da Takawa ya san duk abubuwan da yake aikatawa, hakan ma yasa ya saka ƙafa ya take burinsa da yake fatan ya cika masa shi.
Burinsa na son zamowa Manager a kamfanin saye da siyarwar motoci na ‘WAKILI MOTORS’ wanda ya kasance mallakin Takawa ne. A halin yanzu babu wanda yake kula da kamfanin, sai wani daga cikin amintattun Takawa da aka ba shi riƙon ƙwarya. Kuma hakan ya samo asali sakamon babu mai kula da kamfanin. Babban ɗa cikin ‘ya’yan Takawa wato Khabir Wakili ba shi da ra’ayin yin kasuwanci, sarauta ita ce abin da ya fi muradi.
Hakan yasa tun bayan kammala karatunsa aka ba shi muƙamin Shatima, ɗa na biyu cikin’ya’yan Takawa kuma shi ne HAMMAD, wanda ya bawa Sa’ad wattani uku a tazarar haihuwa, hakan yasa suka taso kamar sa’anni, duk da ba sa shan inuwa ɗaya. Tun tasowar Hammad ba shi da wani buri da ya wuce zama babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa, tun da burinsa ya cika sai ya zamana kasuwanci da sarauta ba sa burge shi.
Daga shi kuma sai Sa’ad, wanda tun tasowarsa ba shi da burin da ya wuce zama Managern WAKILI MOTORS. Kasancewar cikin ‘yan uwansa maza biyu babu mai burin zama ɗan kasuwa ko shiga harkar da ta shafi kasuwanci sai kowa yake ganin daga zarar Sa’ad ɗin ya kammala karatunsa Takawa zai ɗauki ragamar kamfanin kacokam ya ba shi.
Amma sai abin ya zo da saɓanin hankalin kowa, domin bayan ya kammala karatun Takawa yace ba zai iya ɗaukan ragamar kamfaninsa ya danƙawa wanda bai san ciwon kansa ba, matsawar Sa’ad na son a ba shi ragamar kamfanin dole sai ya fara aiki daga ƙaramin mataki, kasancewar a duniya babu burin da ya ɗara na zama managern kamfanin a ran sa’ad yasa ba musu ya amince da sharaɗin Takawa a lokacin, aka naima masa aiki a wani gidan talabijin dake Abuja.
Har kawo yau Takawa na lura da duk wani takunsa, ba ya jin zai bawa Sa’ad damar jagorantar kamfaninsa matsawar bai shiga hankalinsa ba, domin ko kaɗan Sa’ad bai san zafin naiman kuɗi ba ballantana kashesu, kuma wannan dalilin yasa shi ma Takawa ya tsaya a kan ra’ayinsa.
“Magana nake maka ka yi shiru”
Takawa ya furta cikin shirun da falonsa ya ɗauka. Sa’ad ya rasa inda zai sa kansa, kuma babban kuskuren da zai tafka a duniya shi ne yi wa Takawa ƙarya, domin ya san idan har ya masa ƙarya to ba zai sake yarda da shi ba. Ya ɗan lashi lips ɗinsa da tashin hankali ya sa suka soma bushewa.
“Na… na… na… siyi tufafi… ne!”
“Ina na ka tufafin suke?... Ko estate ɗin da kake ya yi gobara ban sani ba?”
Saurin girgiza kansa ya yi yana fadin.
“A’a a’a… Na wa ne suks tsufa”
Takawa ya ɗan zamo daga kan kujerar da yake zaune kai kaɗan yana tsayar da dubansa a kan ɗansa.
“Naira dubu ɗari uku har da tamanin? A kan siyan sabbin tufafi kawai Sa’ad?”
Shi dai bai yi gigin wanke kansa ba, dan ba shi da wannan damar.
“Allah ya shiryeku… Saura kwana nawa hutun da ka ɗauka ya ƙare?”
Kansa a ƙasa yace.
“Sati biyu ne ya rage ranka ya daɗe”
Takawa ya jinjina kansa yana ɗaukan jaridar da ya aje, ya gyara zamansa kan kujerar tare da ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya furta.
“Na rage maka shi zuwa sati daya…”
“Amma Tak…”
“Idan ka sake cewa ƙala sai ka bar garin nan a yau ko ranka ba ya so!”
Takawa ya tari numfashinsa yana kallonsa da dattijan idanuwansa masu tsananin kwarjini, ƙarfin kwarjininsu bisa kansa yasa Sa’ad saurin sauƙe nasa kasa.
“Allah ya huci zuciyarku, tuba nake ranka ya daɗe, da fatan za a gafarceni”
Ko kallonsa Takawa bai kuma ba, jiki a sanyaye ya miƙe yana masa sallama, sannan ya fita yana jin ransa ba daɗi.
Sashin Adda.
Maryam, Muhibba da Adda ne zaune a dinning room suna karin kummalo, daga Adda har Muhibba gaba ɗaya hankalinsu na kan Maraym dake cin abincin kamar an mata dole. Kana kallonta za ka san cewa ba ta tare da nutsuwarta, abincin take ci, amma ba shi ne a gabanta ba.
“Yaya Maryam!”
Muhibba ta ambaci sunanta tana leƙa fuskarta, kamar wadda aka jefowa tunaninta daga sama haka ta kalleta.
“Na’am Muhibba”
“Lafiya?”
Ɗan gajeren murmushi ta yi tana aje spoon ɗin dake hannunta kafin ta kalli mahaifiyarta da ‘yar uwarta.
“Jiya da daddare na samu bacci”
Muhibba tai murmushi mai faɗi, domin a ganinsu alamun sauƙi sun fara bayyana a ciwon ‘yar uwartata, a baya kwana take idonta biyu, bata komoya lumshe idonta na dogon lokaci, don tace daga zarar ta lumshesu za ta ga wani jan ƙyalle an ɗaure shi da wasu baƙaƙen zare.
“Masha Allah, ki ce har da munshari!”
Cewar Muhibba cike da zolaya. Maryam ta kuma yin murmushi, domin yana ɗaya daga cikin ɗabi’unta da kowa ya shaideta da su.
“Ba irin wannan baccin na daɗi ba Hibba, ina kwantawa baccin na yi mafarkin wani mutum a ƙofar gidana… yana sanye da baƙaƙen kaya, kawai yana ganina ya soma ƙirana yana cewa na zo zai bani magani na warke daga wannan ciwon”
Muhibba da Adda suka dubi juna, kafin suka sake dubanta.
“Ku ma kin je ɗin?”
Muhibba ta sake tambaya tana kallonta, ta girgiza kai.
“A’a ban bi shi ba na farka daga baccin… A ganinku me hakan yake nufi Adda?”
Ta faɗa cikin sanyin muryarta tana raba idonta a kansu, Adda kasa cewa komai ta yi, kawai sai ta miƙe tsaye tana jin wani abu na mamaye zuciyarta. Tana daf da fita Sa’ad ya shigo, kallo ɗaya ya musu ya gane cewa wani abu ne ke faruwa. A ladabce ya gaishe da Adda, su ma su Maryam suka gaishe shi.
“Merry wai har yanzu ba ki shirya ba?”
Yace da Maryam yana ƙarasawa ciki, yayin da Adda ta ƙarasa ficewa.
“Ina za mu je Ya Sa’ad?”
Maryam ta tambaya tana kallonsa da mamaki.
“Ba na ce miki za mu je asibiti yau ba?”
“Assha, wallahi na manta!… Bari na je na shirya!”
--------------------------------
_Anya kuwa wannan jinyar ta Maryam ba da walakin ba?_
_To, ga dai Akira ma ta bijiro da nata ɓangaren, sannan ina mai muku albishir da bayan Akira ma akwai wasu sauran jaruman na nan tafe a gaba, wannan kamar sharar fage ce muke.._
_And Hey! To remind you guys, ƘAWA ZUCI paid book ne, a kan ₦ 400 kacal, idan ya zama complete kuma ₦700 ne za ku iya fara payment tun daga yanzu, domin morewa wannan tafiya mai cike da zallar abubuwan al’ajabi, soyayya sarƙaƙiya, ƙiyayya, fansa ƙunci da dai sauransu._
_Za ku iya tura kuɗinku ta wannan account details da zan runbuta 5487270431 Salma Isah Monie point, shaidar biya kuma ta 08130172702_
#SalmaAhmadIsah
#Candy
#Bahadejia
#KawaZuci