RAINONTA ZANYI🔞
ROMANTIC LOVE STORY
7
*FREE PAGE ZAI ƘARE A PAGE 10 GA MASU BUƘATAR BIYAN KUƊIN LITTAFIN RAINONTA ZANYI REGULAR PAYMENT ₦500 VIP GROUP ₦1000 SPC PAYMENT ₦1500 VIA 6037312299 MOHAMMED AISHA KEYSTONE BANK*
Hajiya Kaka yanzu haka nan za'a cigaba da zuba ido ana ganin Wannan al'amari kullum gaba yake yi fa ba baya , Girman yaro ba wuya ne dashi ba ". Wata farar tsohuwa ce zaune bisa tanfatstsen Carpet mai laushin gaske , Mai launin Milk mai haske , sanye take cikin ado na gwala gwalai da Alama Ƴar Gayu ce ko a ƙuruciya ga kuma uwa uba tsafta , doguwar bafullatana ko a ido ”. A gaban ta kuwa Al'ƙurani ne mai girma tana sanye cikin Shigar mu ta hausawa amma a hakan sunan a falo take sai da ta Ɗaura hijab wanda aka yi masa Ɗinkin zamani kace Yarinya zata saka , ta daure kanta da madaurin hijabin... Ɗagowa tayi tana kallon Hajiya Suwaiba Mahaifiyar Abdul Malik dake maganar cike da Ɓacin Rai da tsantsan jin haushi ”. Cike da Rashin fahimtar inda ta dosa Hajiya tace “ Wani Al'amari ne haka Suwaiba kike magana? , wacce ban san dashi ba?”.
....Hmmm Hajiya ke kuwa kika san shi sai dai idan kin manta , zaki ce kin manta da Yarinyar dake hannun Hajiya Nadiya ne? Har da yanzu tana nan suna rainonta, wanda a yanzu zata kai shekaru goma ....Sakin baki Hajiya kaka tayi cike da mamaki a zuciyar ta kuma tana jin ɓacin rai ƙwarai dama basu mayar da yarinyar nan ba ? Har ila yau tana nan kike nufi?”. Hajiya ta furta cike da sarƙewar murya ”. Gyaɗa Kai Hajiya Suwaiba tayi tare da Saurin cewa “ Abin takaicin shine Nan gaba bamu san Asalin yarinya ba , dama ƴar Asali ne da sauki kar yazo ƴar Zina ce , mu dinki riƙon ta a a halin mu...Cike da Ɓacin Rai Hajiya kaka tace “ Me yasa tuntuni ba'a sanar mun ba ?, Yanzu yanzu ko kirawo mun Alhaji Abdu yazo ina son ganin sa ”. an gama Hajiya , gaskiya ya kamata a san yanda za'a yi d Yarinyar nan abin da na gani a yanzu Hajiya inda zan sanar Miki wallahi ba zaki iya haƙurin zama wai ki jira isowar Yaya Abdu ba ”.
“Kallon ta Hajiya Kaka tayi cike da mamakin maganar Suwaiba ,don tabbas tasan halin ƴar nata ba mai kawo irin wannan Maganar bace , Wannan yasa Hajiya tambayar ta da cewa “ Suwaiba sanar mun meke faruwa ne? Maza ina sauraren ki bana son ki ɓoye mun komai kamar yanda kuka ɓoye mun zaman Wannan yarinya da ban san da ita ba a cikin ahali na zuriya na ke Rainonta ”....Hmmm ,nan Hajiya Suwaiba ta sauke gwauron numfashi tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi kana daga bisani tace “ Hajiya Yaya Abdu ɗan sa ɗaya ya mallaka Wato Afeef kin san da wannan , a yanzu Afeef ya zama standard person mutum Wanda yake tsaye da ƙafafun sa , yana da kuɗin sa fiye da yanda muke tsammani , kuma kullum da ɗa bunƙasa yake yi , kin san ya mallaki Asibitoci yana da kadarori wanda yanzu haka yana shirye² buɗe companin sa na kan sa , tun kamin ya dawo Nigeria yake da wannan plan ɗin nasa , don haka Yaya Abdu sam baya ta kan sa , yasan ko baya da rai Afeef yayi gaban da ba zai dawo baya, Alhmdllh tun da muma haka muke so muga ƴaƴan mu sun zama ...Ƙwatsam ina Zaune yau sai naga Saƙon Yaya Abdu ya Turo mun da Shi Wai nasa hannu signature na akan Ɗaya daga Companin sa na Taki wai ya mallaka ma Aleena halak malak ko bayan ransa na ta ne ”. Saurin dafe ƙirji Hajiya Kaka tayi domin kuwa tasan wannan Company yana cikin manyan kadarorin Alhaji ABDU NASIR ”. Girgiza kai Tayi irin nasu na manya ,kana tace ki sanar ma kowa ina da Muƙatar kowa ya haɗu a cikin gidan nan a safiyar gobe kowa ya kashe ayikan sa ,ina da Taron haduwar gaggawa , ba sai kin kira Abdu Nasir ba , sai gani ta inda kuke turawa ”. Eh Hajiya Wannan yayi WhatsApp group ɗin mu zan tura inshallah, yau Yana hanya da misalin 5:30pm Jirgin shi zai sauka ”. Yayi ƙyau duka a sanar da kowa ina buƙatan ganin ku duka har jikoki ba Ƴaƴa kaɗai ba ”.
Wasu Littafan
.....How that nonsense da yake magana ina magana Are You mad? Ke mahaukaciya ce ? Daga Wani ƙauye kika zo? ”. Muryar Nasreen ya katse ni inda take mawa mai aikin su sababi”. Jiki na Rawa Asabe ta zube ƙasa tana cewa “ kiyi haƙuri Hajiya , Nayi kuskure....Ina ce Miki Jaloaf Rice ɗin nan an saka curryn da bana so sannan kina so ki ce mun a'a ?, Shin ban san teste ɗin sa bane a baki na?”. Kiyi haƙuri Hajiya ”. Gather all this dishes bana son ganin komai anan ”. Tana furta haka ta miƙe daga saman Dirning area tana wucewa fuuuu izuwa falon Prof Sulaiman ”. Ni Ko bayan ta nabi da kallo Ganin irin shigar ta irin na sangartattun yaran nan , Cikin leg jeans blue irin crazy ɗin nan cinyoyin ta duk a sarari sai riga kaman shirt yar karama, kan ta ko ɗan ƙwali babu ta shige Falon mahaifin nata Wato Prof Sulaiman.
Da shigar ta cike da shagwaɓa ta nufi Daddyn nata tare da Faɗawa jikin sa tana furta “ Dad”...Daughter ya furta yana ɗagowa tare da gyara zaman Gilashin sa na professors , bin su da kallo Honorable Mardiyya tayi kana ta ɗan caɓe baki tana tarar numfashin sa da cewa“ Ohh Prof wai yaushe Nasreen zata girma ne a wurin mu? Ya kamata yanzu ta bar wannan sargancin haka nan , ina jin sababin ta da Masu Aiki na wuce su na yi nan ,don nasan Fadan ne kurum da ta saba. Kallon Honorable Mardiyya Nasreen tayi kana ta fashe da kukan sangarci tana cewa “ You see Dad , Kaga Ni Ko? Na faɗa maka yanzu fa Mom ta chanja kai ne kaɗai kake kulawa dani kake goyon baya na akan komai ”. Cikin tare mawa Ɗiyar tasa yace “ Ko wacce me aikin a sallame ta bana buƙatar ganin ta , Sannan kuma Honorable ki sanar mawa da Habib Gobe duka zamuje gidan Hajiya Kaka da meeting”.
“Kallon sa Honorable Mardiyya tayi kana tace “ Ohk Prof. Lallai da magana kiran Hajiya kwatsam haka , tabbas there is something behind, Allah ya kaimu goben lapiya ”. Alright ya furta yana mai daura idanun sai tare da tattara hankalin sa ga Nasreen wacce tace “ Dad har Dani za'a je kenan? , Ya Afeef ma zashi? , . Gyaɗa kan sa yayi yana furta “ Yes the meeting is for the whole family, so shima zai halirta ”. Wow I really miss Him , Dama yau nake shirin zuwa cox ya dawo sannan Abie ma Ya dawo yau ”. Abie ya dawo ?, A ina kika san hakan ? , Honorable ta katse ta , yayin da cikin sauri Nasreen ta furta “ A bakin Mummy Nadiyya na sani ”. Hmmm Ok Bara inje na sanar mawa Habib, Honorable Mardiyya ta furta tare da caɓa jikin ta domin kuwa ƙatuwa ce data amsa sunan ta taf take cika one seater, baƙace black beauty mai ji da Izzar siyasa ƴar gwagwarmaya kuma Cikakkiyar ƴar boko wanda haɗuwar ta da professor an haɗu da an dace , Ba Dangi ba har ta ma'aikatan gidan suna azabtuwa da turancin su 🤣”. Prof da Honorable kenan ”. Prof ƙanine ga Alhaji ABDU NASIR , wanda Hajiya kaka tana da Ƴaƴa maza Alhazai don duka kowa na ji da ƙarfin dukiyar sa su baƙwai Allah ya bata ƴar ta mace Ɗaya ce Wato mahaifiyar Malik kuma itace Auta muje zuwa fans zakuji daɗin labarin Rainonta zanyi kar ku manta free page din mu yana daf da karewa so guyz make your payment sauran enjoyment yana a gaba”.
....What's going on here?
Muryar Honorable Mardiyya ya katse Habib dake Ƙwance House maid ɗin shi ke massaging nashi tana matsa masa ƙafafu kaman yanda ya umarce ta,idanun sa na akan Laptop din sa bakin sa yana dauke da karan sigari ... yana zuƙa a gaban sa kuwa cup ne dake Ɗauke da ruwan barasa”. Ɗago da idanun sa yayi yana mai furta “ Mom...” Oh Habib na faɗa maka ka rage shan Wannan Abin illa ce ga lafiyar ka , kasa Ni Ko? ”. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa na yi nadamar kai ka Malesia ”. Cigaba yayi da duba sakon sa kana yace “ Mom Nasan komai , kada damu ....cike da nuna dan damuwa takai hannunta tana kwashe gwalban tare da cewa “ ka rage Wannan ka bari duk dare sai kana rinƙa shan one cup , plz My Son promise me zaka dai na shan wannan hayakin ?”. Ɗago da idanun sa yayi yana janye ƙafarsa daga massaging din kana yace “ Mom meke tafe dake da wannan yammacin? ”. Kallon sa tayi kana tace “ You didn't say anything, Ha....Mom please yayi maganar yana katse ta tare da miƙewa yana rufe Laptop din nasa , kallon ta yayi yana cewa “ Ina jinki Mammy”. Gobe da meeting gidan Hajiya Kaka ka shirya ”. Alright ya furta yana gyara rigar sa kana ya wuce bedroom ɗin sa ba tare da ya kuma kallon mai Aikin da Honorable Mardiyya ba . Wuce ki je ki cigaba da masa tausan idan yayi barci kizo ina son magana da ke ”. To Hajiya A sauka lapiya . Ba tare da ta tanka ma Zaliha ba ta wuce ta ”.
......cike da izza yake takaawa irin nasa fuska babu alamar wasa , Yake saukowa daga step tare da Nufar ɓangaren Abie wanda a yanzu dare ne misalin 8:15pm. Ko ina haskene tantarwai kaman Rana , haka ma'aikata kowa ya nufi makwancinsa duk wanda ka gani securities ne masu kula da tsoron gida Alhaji ABDU NASIR . Har Afeef ya wuce Windown Falon Daddy sai zai shiga Falon sai ya jiyo wasanni da dariyar Ta ,wannan yasa shi yo baya yana leƙawa ta jikin windown...Aleena da Abie ya gani suna Wasa ta dare cinyar sa yana mata wasa tana dariya har da kyakyatawa, Shigar ta ya kalla inda take cikin wani wando mai kamar pant sai karamar riga wacce ba zata wuce Cibiya ba . Gashin kan ta yasha gyara, Gyefe guda Mummy ne tayi tagumi wanda Sam Afeef bai san Dalilin tagumin nata ba , Idanun sa sunyi ja na ɓacin rai An zuciyar sa yana cewa “ RAINONTA Tasa kenan?”.
*To jama'a kar da ku manta a page 10 Free page namu zai ƙare regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank masu buƙatar littafin RAINONTA ZANYI YouTube zasu na iya magana for the bookings haka bloggers kuma zaku iya magana da wuri🙌🏻💃🏻🔞💯#Uwarteddy08081202932.*
