A farkon kowace alaƙar soyayya, ƙananan kalamai kamar “Ina sonki” ko “Na yi kewarki” kan iya sauya yanayin zuciyar mutum gaba ɗaya.
Kowane ɓangare yana ƙoƙarin zaɓar kalamai masu daɗi cikin nutsuwa, tura saƙonnin soyayya, da yin ƙoƙari wajen sanya farin ciki a zuciyar wanda yake so.
Amma kuma kwatsam wani lokacin bayan aure, waɗannan kalamai suna fara raguwa, wani lokacin ma har su ɓace gaba ɗaya.
Shin hakan yana nufin soyayyar ta gushe?
Ba lallai ba ne.
Akwai dalilai da dama da ke bayani akan wannan canjin:
1️⃣ Jin samun aminci fiye da kima
Wasu daga cikin ma’aurata suna ɗauka cewa bayan an daura aure, sun samu tabbacin abokin rayuwa yazo hannu, don haka babu buƙatar sake cigaba da tabbatar da soyayya ta hanyar kalamai.
Amma zance na gaskiya shine: zuciya tana bukatar kalamai masu daɗi da zasu ciyarwa da ita, kamar yadda jiki ke bukatar abinci.
2️⃣ Matsalolin hidindimun rayuwa na yau da kullum
Kama daga kasuwa ko wajen aiki, daukar ɗawainiyar gida, kula da yara, da sauran ƙalubalen rayuwa suna iya sacewa mutum kwarin gwiwa ko sha'awar bayyana soyayya.
Amma ku sani ita soyayya ba ta wadatuwa idan aka ce ana jinta a jiki kawai, dole ne a fito da ita fili ta hanyar magana sannan kuma a nuna ta.
3️⃣ Sabo da juna da rashin samun damar burge juna
Idan ma’aurata suka daina bayyana shaukin soyayyarsu, alaƙar dake tsakanin su na iya sauya zuwa yin rayuwar sabo da juna a kullum, babu wani abu da zai motsa zuciya.
A wannan lokaci, shaukin zuciyoyin su na nisantar juna ba tare da ɗaya daga cikinsu ya ankara ba.
⚠️ Me ke faruwa idan kalamai masu daɗi suka ɓace?
Zuciya takan shiga kadaici duk da kasancewa suna rayuwa tare a ƙarƙashin inuwa ɗaya.
Wani lokaci, ɗaya daga cikin ma’aurata kan fara neman abinda ya rasa a waje, ba tare da sanin illolin yin hakan ba (Wa'iyazubillah).
Mece ce mafita?
✳️ ku tuna a koyaushe cewa “ya san ina son shi” ko “ta san ina son ta” kadai ba zai wadatar ba
✳️ Ka ware lokaci a kowace rana domin ka faɗa mata kalamai masu daɗi.
✳️ Ko da kana gajiye, jumla mai sauƙi kamar:
“Ina godiya ga Allah da kasancewarki a rayuwata” na iya yin tasiri fiye da yadda za ka iya tunani.
Kalamai masu daɗi ba su da tsada, abu ne mai sauki dake taimakawa soyayya wajen dorewarta.
Kada ka daina bayyana soyayyarka, domin kalma mai daɗi na iya karawa soyayyarku danƙon da zata daɗe tayi karko sosai.
Kuma duk tsawon lokacin da za'a dauka, ka kasance mutumin da yake zaɓar ya faranta zuciyar wanda yake so, ba wanda zai nisance ta a boye ba tare da sanin ta ba.
