Dr. Sadiq page 56 by Nana Ƙanwar Soja

Dr. Sadiq Hausa Novel

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO 

    BY


    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama 

5️⃣6️⃣

    TITTLE:  

   "Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

       

  



    


    

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*



    

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 



THANK YOU FOR UR CARE UMMU KULSUM I ARE ALWAYS IN MY MINE


    


    KUNA SAMUN UPDATE SAU BIYU A RANA ,,AMMAN BANA GANIN SHARHIN KU FA ME YAFARU NE 🫰 


    

    A class, Indo ta zauna quiet kamar ba ita bace waccen yarinyar da kullum suke hira da dariya.

Kafafunta a haɗe, fuska ta kumbura, biro a hannunta tana ta danna shi kamar tana son ya mutu Ilham—kawarta mai nishadi—ta shigo da gudun “sabon labari”, ta zauna gefenta ta tura mata hannu Ilham

“Indo… meye haka? Me ya faru yau? Kin yi kama da wacce aka shekara biyu ba’a biyata kudin kati ba.”


Indo ta harare ta.

Ilham ta murmusa jin harin ya yi full effect.


Indo ta ce da harara:

“Ilham… please leave me alone.” Ilham “Ai ba zan bar ki ba. Haka duk lokacin da kika yi fushi kike tunanin zaki kubce min? Forget it. Ni ce mai kula da ke.”Ta matsa kusa sosai har Indo ta matsa gefe Indo

“Ilham wallahi na yi fushi. Kuma tun daga safe nake.”Ilham (kamar mai jiran labari tun jiya):

“Kin yi fushi da waye?”


Indo ta juyo da sauri “Da Dr Balarabe!”

Ilham ta bude baki kamar tayi tsalle Ilham:

“Indo! Why??  Faɗa yamiki i?

Ko phone dinsa kika buɗe kika ga wani abun ?”


Indo ta rude ta doke desk ɗin:

“ ASHE YANA DA MATARSA "Ilham ta zauna straight. “Wait. Kin ganta?”


Indo:

“Eh wanan rusashiyyar Atika ce da tazo kwana nan kinsan ai tana tukaramin to shine yau yazo ta nema ne da faɗa , tace min ita matar sace ". Ilham ta dafa kanta:

“Ina so na fahimta… kina fushi da shi saboda ya ce ‘nothing , ko kishi kike ye ai da ita ƙaiƙaye faɗan badashi ba ??”


Indo “Eh! Ba ya gaya min gaskiya.” Ilham ta fashe da dariya tana bubbuga ƙafarta.

Gaba ɗaya class suka juya suna kallonsu.


Ilham:

“Indo… Indo… ke fa ba matar sa bace. Ki natsu ,ke kanwar sace kika ce ya kawo ke don kiye karatu !

Wacce kika gani Atika ce, ɗiyar kawar Mommy dinsu. Ba matar sa ba ce. Ai har yanzu babu mace a zuciyar Dr ɗin nan ina jin yaya na yana cewa shi ba ruwansa da mata ”

Indo ta turo baki.

“Ni ba ruwana. Ko dai ya fada min komai a fili ko kuma sai na daina mishi magana.”


Ilham ta girgiza kai:


“Kin ga? Wannan shine ‘Indo style’. Rigima da wacce bata san tace lafiya nawa ba.”


Indo ta miƙe tana jan hijab “To yanzu ina zaki?” Ilham ta tambaya.


Indo ta ce:

“Zan je kiosk in sayi chips. Tunda abincin da na samu a safe an kwashe min…”


Ilham ta tsaya cak.

“Wait… AN KWAYE MKI ABINCI?? Wanene?!!”


Indo ta juyo da murmushi mai rikitarwa:

“Tunda na dawo gidan nan… kowa sai ya nemo rigima da ni Atika ce ta zubar .”


Ilham ta rikice:

“Lallai yau zan ji labari. Dare yau ba zai kwana lafiya ba! 

Karfe huɗu na yamma ne lokacin da motar Dr. Sadeeq ta tsaya a gate na school. Indo ta fito tare da kawarta Ilham, suna yi wa juna bye-bye da dariya mai laushi, amma a ranta, Indo tana ɗan ɗaga hankali saboda zata sadu da Dr. Sadeeq. Ilham kuwa tana ganin yadda Indo ke ɗan jan hankali da sauƙin murmushi, tana taɗawa cikin natsuwa.


Indo ta shiga motar, ta gaida shi cikin ladabi:

“Good afternoon, Dr. Sadeeq.”


Ya ɗan sosa kai ya amsa gajeren murmushi, amma ba tabka mata ba; ido shi kadai ke kallonta cikin nutsuwa da tunani. A ransa, yana nazarin yadda ta girma, yadda take motsi cikin hankali, kuma yadda fuskar ta ke ɗaukar haske duk da ƙarancin magana.


A lokacin, Indo ta lura cewa yau ya sauya hanyar da ake zuwa gida. Ta ɗan ɗaga murya:

“Ina zamuje ne, Dr.?”


Ya yi murmushi, idanuwansa na taɓa haskaka ɗan dariya mai laushi:

“Somewhere… somewhere ne kawai,” ya amsa, ba tare da ya faɗa dalla-dalla ba.


Indo ta fahimci cewa ba zai yi magana sosai ba, sai ta yi shiru, tana bin motar shi kamar ragumi. Cikin zuciyarta akwai ɗan tsoro da ɗan sha’awa, saboda ba ta san inda zai kai ta ba. Sai suka iso har gidan su Kamal, motar ta tsaya a harabar gida, babu kowa a waje.


Ta fito daga motar cikin hankali, idanunta suna zarewa da tsoro, tana lura da duk wani kusurwa da dakin. Part na Kamal ya yi shiru, babu kowa a ciki, sai Indo ta fara jin cewa wannan gidan shi ne inda zata fuskanci abubuwan da ba a saba gani ba. Cikin silence ɗin, zuciyarta na buga da sauri, tana mamakin yadda abubuwa ke canzawa cikin ɗan gajeren lokaci.


Ta ɗan tsaya a bakin kofar gidan, ta gyara uniform ɗinta, ta tattara gashin kanta a hankali, sannan ta shigar cikin lobby ɗin cikin tsoron da son ganin cikin gidan lokaci guda. Wannan shi ne farkon wani sabon yanayi a rayuwarta, inda zata fara fuskantar abubuwa daban-daban a part na Kamal, da kuma kasancewar Dr. Sadeeq a cikin tunaninta.


Da sauri ya tsaya a gefenta, idanuwansa na kallonta da nutsuwa, zuciyarsa na ɗan bugu da ɗan sauri. Sai ya miƙe hannu ya kama nata cikin ladabi, amma ƙarfi da tabbaci a lokaci guda. Hannunta ɗan tsorace, amma bai bari ta janye ba; ya ja ta a hankali, suna wucewa daga lobby zuwa parlour ɗin babban gidan.


Indo tana tafiya a baya, idanuwanta na kallon dakin da kewaye, zuciyarta na cike da tsoro da sha’awa gidan , tana jin kowane motsi na Dr. Sadeeq. Parlour ɗin ya yi shiru, kayan ado masu tsada suna sheƙa a hasken fitila, duk da kyan gidan, amma Indo ba zata iya natsuwa ba; duk motsin hannunsa da matsin da yake yi a kanta na jikin ta, yana sa ta jin wani irin yanayi mai ɗan ban mamaki.


Da suka  iso private room, ya tsayar da ita a hankali, ya saki hannunta ɗan kaɗan, amma idanuwansa sun tsaya a kanta har sai da ta ɗaga kanta ta kalle shi. Sai ya ɗan yi murmushi mai laushi, yana jin yadda zuciyarsa ke buga da sauri.


“Indo…,” ya fara da murya mai ɗan sanyi, “kaɗan kaɗan ki natsu, babu abin da zai faru.”


Ta ɗan shafe cikin ta, tana gyara numfashi, tana jin sanyi ya ratsa jikinta duk da yanayin private room ɗin. Wannan wuri yanzu ya zama sanctuary a gare ta—wuri da zata iya ɗaukar natsuwa, ta fara fahimtar cewa Dr. Sadeeq yana son ya kare ta, ba wai ya cutar da ita ba.


A hankali ya matsa kusa da ita, yana lura da kowane ɗan motsi nata. Indo kuwa tana jin butterflies a cikin ciki, zuciyarta na buga da sauri, amma tana ƙoƙarin yin kwanciyar hankali. Wannan farkon haduwar su a private room ya sa dukkan tunaninta ya mayar da hankali ga Dr. Sadeeq, kuma a hankali tana fara fahimtar cewa rayuwarta nasa ne..


    


    

???????????????????????

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post