Dr. Sadiq Page 68 Complete

Dr. Sadiq Page 68

Page 68

 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM

    

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO

    BY

    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama 

"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

  💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 





  NIGHT UPDATE 

ENJOY YOUR NIGHT 


    BUSSINES GROUP   

    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    

    COMMENTS SECTION 

   👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1


    

      

 NOVEL ELITE  CHANNEL FOR MORE NOVEL'S 

    👇👇👇👇👇👇

 https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35     


    


    


    Indo ta dawo daga plaza, tana ɗauke da jakar ta da maganin zawo, zuciyarta tana cike da ƙarfin hali da shirin yin mugunta—musamman ga Atika.

Ta shiga part nasu a hankali, ta ga kaka tana zaune tana shirye-shiryen wasu abubuwa.

Indo ta gaishe ta da ladabi  “Assalamu alaikum, Kaka.”

Kaka ta daga kai, idanuwanta cike da kulawa, murmushi a fuska  “Lafiya lau? Sai farin ciki, kikiye.”Indo ta yi dariya, ɗan wasa da murya:

“Lafiya lau, Kaka… kai bare na yi sallah! banyi la'asar ba yanzu.”

Kaka ta ci gaba da murmushi, amma ido na kallonta cikin kulawa “To Allah ya kiyaye, karki manta lokaci.”




Indo kuwa ta shiga dakin ta da sauri, tana dariyar mugunta a ranta.

Yau ta shirya wa Atika abubuwa daban-daban—ba wai kawai tana jin haushi ba, har ta shirya wasu tsare-tsare don ta tsokana ta gwada.


Ta zauna a gadon ta, ta miƙa kafafunta a saman bargo, idanuwanta cike da hasashe:

 “Yau za a ga wacce take da hankali sosai… Atika ba za ta san inda na fara ba.” Dariya tana sauka a gefen baki, amma zuciyarta akwai nufin shirin tsokana da mugunta da zata yi da Atika.


 INDO TA SHIGA DAKIN ATIKA A BOYE


Bayan Indo ta shafa blue gloss, ta gyara ribbon ɗin  ɗinta, sai ta tsaya gaban madubi tana murmushi:

 “Atika yau sai kin gane ba kowa ne kin iya takura masa ba…”

Ta dinga jin zuciyarta na ɗan rawa saboda shirin da ta yi—ba wai don mugunta mai cutarwa ba, sai dai don ta rama zalunci da dariya.

Ta sace hanya ta gefen corridor ɗin part ɗin Mommy, tabi ƙananan matakan da ke kaiwa bangaren Atika.

A hankali kamar ƙwararriyar ’yar satar hanya, ta zare takalmanta domin kada su yi sauti.


Da ta iso bakin ƙofar dakin Atika, ta saurara—shiru! tasan sai ƙarfe shidda na yamma yake dawo wa  Indo ta ce a ranta:

 “Perfect…”


Ta shiga dakin a hankali kamar iska. Dakin Atika yana cike da turare da jan kwalliya, komai cikin kwalliya kamar sarautar shagalin 'yan mata.


Indo ta ƙaraso toilet ɗin da ke haɗe da dakin.

A saman shelf ta ga powders da Atika ke amfani da su: pepper body scrub, red spice mask, da “hydro-boost whitening mix”.


Indo ta murmusa.

Wannan ba zai cutar ba, amma zai ba Atika darasi da kyau ta ɗauko barkono mask ɗin nan da Atika kanta ta saya don kunshin fuska wanda yakan yi zafi kaɗan.

Ta zuba ƙanana cikin ruwan cistern na toilet ɗin—ba mai cutarwa, amma zai ba da sautin zafi da ƙamshi mai ƙarfi idan mutum ya zauna.


Ta ce da wata muryar wasa  “To Atika… yau ki sha ƙamshi da zafi kaɗan.”

Sannan ta ɗauki hydro-boost whitening mix (wanda shi ma ba cutarwa bane, kawai yana sa sanyi sosai) ta zuba kaɗan cikin liquid soap ɗin da Atika ke amfani da shi.

Indo ta ɗaga gira:

 “Ai wannan ba duka bane… wannan rigima ce ta mata.”

Ta gyara komai, ta goge rigingine, ta juya kamar wata sirri agent ta tafi da gudun shiru, tana dariya ta rufe baki.Tana barin dakin ta ce:

 “Wallahi sai na rama duk abin da kika min, Atika. Amma yau—’yar wasan dariya ce.”



Atika ta shigo part ɗinsu da nishaɗi, tana waka da murya:


 " babbar yarinya nai Sa'a tunda mai dace a ƴan mata ”

Ta jefa jakarta, ta ciro wayarta tana duba notifications, tana tafe tana swag kamar wata supermodel Ta shige toilet ɗinta ta kulle ƙofa, ta cire rigs, ta kunna warm water.

Sai ruwan shawa ke kwarara, tana wanka tana ta waka.


Tana gama wanka, ta ɗauki towel ta ɗaure. Ta zauna a saman toilet tana sakin jikin ta kamar wata Madam Relax Ta yi kashi tsaf.

Ta danna flush.

Ta miƙa hannu don ta yi tsarki da SPRIT SHOWER BIDET wancan ƙaramin bututun da ke fitar da ruwa...


Ta jawo lever ɗin bidet ɗin da ƙarfi kamar yadda ta saba…


KWATS!!!

RUWAN SPIRIT BIDET ya buge ta —

amma ba ruwan zafi ko sanyi ba…

ruwan SPIRIT + hydrogen peroxide + ƙananan barkono powder,  mixture da Indo ta zuba tun da yamma....


Nan da nan Atika ta yi tsalle kamar an soka mata wuta.

Ta fisge towel ta wurgar:

 “INNAAAAA LILLAAAHI!!! WAYYOOO ALLAH ƊUUUU NA !!!”

“ME YA ƘONE MIN WAAAAJEN NAN?!”

“WAYYO ALLAH NA!!! DUUU! DUUU! DUUUU!!”




Ta fara tsalle a toilet kamar an kunna gas a ƙarƙashinta.

Hannunta biyu ta sa tana rufe kanta

amma ƙasan jikinta shi yake ƙonawa!


Sai ta fara rige-rigen ihu:

“Haaaaa!!! Me ya zuba RUWAN TUKUNYAN ALJANU a BIDET ɗinaaa?!”

“KUWANAN WUTA KUWANAN WUTA!!!”




Ta buɗe ruwan tap da gudu ta yi tsarki a hanzari.

Sai ta yi raurau da kuka:

 “Na kone! Na ƙone! Na ƙoneee! Allah dai yasa ba gumi ne ya sa ruwan ya yi zafi ba… wannan ba normal bane!”




Ruwan ya ɗan rage mata zafi, amma har yanzu ƙasan jikinta yana yi mata taushin zafi kamar ana saka mata hot balm a private area.


Ta fice daga toilet tana tafe tana tafiya da ƙafafunta a buɗe kamar wacce aka yi wa wanka da tukunyar miya:


Ta yi ihu tana girgiza towel ɗin  “WAYYO AC!!! WAYYO FAN!!!”




Ta dire a kan gado, ta kunna AC, ta kunna fanka, ta buɗe ƙafarta sosai tana janyo iska kamar wayewarta zata tashi:

 “Haaaahhhh… hahhh… zafin nan bai naƙasa ba!”

“Waye ya zubar min RUWAN MUTUWA A BIDET?!” Sai kuka, sai gunji, sai rawar jiki.


Indo daga cikin ɗaki na KAKA tana jin ihu tana dariya a ranta:

 “Kinga yanda zafi ya ratsa?

Sai ki san kin tsokani A'ishatu Indo.”

Tayi tsoki ta kalli Atika da idon ƙyama:


“Baki addu’a Atika! Kin shiga ba addu’a kin fito da ihu. Wakar ki ce ta banza dai.”


Ta juya ta fita tana girgiza kai kamar wacce ta gaji da halin taAtika kuwa ta ƙara kurma ihu:


“ALLAH NA!!! ZAFI YA KASHE NI!!!”

Ta buɗe ƙafa tana matsa iska daga AC zuwa gaban jikinta, amma maimakon sauƙi sai taji ƙarin zafi kamar ana hura wuta.


A gefe kuma…


Chan Indo ta fito daga ɗaki don neman magana da Kaka, amma tana jin ihun Atika ta tsaya.

Sai ta zabga wata dariya ta ɓoye a wuyanta tana taune lebenta.


Ta ɗebo abinci ta zauna a parlour cikin relax mood, ta ɗaga spoon, ta fara cin jollof ɗin tana jujjuya kai.


Ta saki waka a hankali kamar ba ita ta aikata komai ba: “Chassss… chasss…

Indo ce ’yar duniya…

Wanda ya raina mu sai ya gane …

Chasssss…”


Ta yi murmushi mai cike da mugun wayo, ta ci gaba da cin abincinta kamar ba ta jin ihun Atika da yake echo duk gidan.


Har Kaka ma ta leko ta tambaya“Wai miye wannan ihun kamar ana yanka akuya?”

Indo ta jinjina kai tana tauna nama ta ce da sallama:


“Kaka bansaniba wataƙila a maƙobta ne " 

Ta juya ta kuma domin taye lazumin ya

Ta cigaba da wakarta:

“Chassss… chasss…

Da wanda yaci amanata sai ya san Indo ba wasa ba ce…

Chassssss…”Ta tauna abinci cikin annashuwa, tana jin irin yanda Atika ke ci gaba da ihun da ko makwabta za su ji


    


    


    


    


    


    .........


        🤲 ADDU’A SHIGA SABUWAR SHEKARA 🤲


Ya Allah,

Muna shiga wannan sabuwar shekara ne da sunanka Al-Rahman, Al-Rahim.

Ka sanya ta zama shekarar alkhairi, salama da albarka a rayuwarmu.


Ya Allah,

Ka gafarta mana dukkan kura-kuranmu na shekarar da ta wuce,

Ka karɓi kyawawan ayyukanmu,

Ka gyara abin da muka ɓata da rahamarka.


Ya Allah,

Ka ba mu:


lafiya mai ɗorewa 🤍


natsuwar zuciya 🕊️


halal mai yalwa 💫


ilimi mai amfani 📖


imani mai ƙarfi 🌙



Ka kare mu daga:


bakin ciki,


tsoro,


cutar zuciya da ta jiki,


makircin mutane da shaidan.



Ya Allah,

Ka cika zukatanmu da haƙuri, yafiya da soyayya,

Ka sanya mu zama haske ga kanmu da wasu.


Idan akwai buri a zukatanmu,

Ka cika shi idan alkhairi ne,

Idan ba alkhairi ba ne,

Ka kawar mana da shi ka ba mu abin da ya fi alkhairi.


Ya Allah,

Ka sanya wannan shekara ta zama farko na farin ciki, nasara da kusanci da Kai.

Ka sa mu gama ta da Imani kuma ka karɓe mu da Rahama.


🤲 Amin Ya Rabbal ‘Alamin 🤲

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post