Dr. Sadiq Page 69 Complete

Dr. Sadiq Page 69

6️⃣9️⃣

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM

    

💔❤️‍🔥DR SADEEQ❤️‍🔥💔

   BOOK TWO

    BY

    NARNAH KANWAR SOJA 

My 15Novel love, comedy drama 

"Love is a flame that burns bright, even in the darkest night." ✨

  💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)   

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 


  MORNING UPDATE 

ENJOY YOUR DAY 


    BUSSINES GROUP    

    👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT    

    COMMENTS SECTION 

   👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1

    

 NOVEL ELITE   CHANNEL FOR MORE NOVEL'S

    👇👇👇👇👇👇

  https://whatsapp.com/channel/0029VaGtQnP96H4UODNQaq35     


    Happy birthday , enjoy your day more money and healthy sister Khadijah Noorah Safiyan wish you the best.....


  


    


    


    


    


    


         

Washegari da safe

Atika ta tashi ɗan sauƙi. Zafin wancan bala’in ya lafa, sai kuma ta fara ɓata rai tana zargin aljannu.


Ta sha pain-relief, ta shiga wanka cikin mandarin-sabon wanka, ta fito tana jan gashinta da tawul. Ta buɗe drawer, ta ɗauke lotion ɗin ta mai ƙamshi ta shafa a fuska.

Ta ja baby-powder a wuya, ta shafa foundation, ta ɗan yi make-up sama sama saboda taye late na fita aiki a  zuciyarta:


“Allah ya kiyaye. Wannan zafi fa ba na duniya ba ne. Aljani ne ya biyo ni shakka babu.”


Ta yi tagumi, ta girgiza kai, amma ta yi shiru.


A gefe kuma…


Indo ba makaranta yau kasancewar suna midterm break Tana zaune a ɗakin Kaka, tana lumshe ido, tana shan tea mai madara sosai, tana jin shiru daga bangaren Atika ta taɓe baki A ranta tace:


“Hmm… yau shiru? Tunanina ko ƙaiƙayi ne zai fara mata yau  To ai ba komai. Wannan kuwa da nayi… farawa ce. Indo ba a raina ta.”

Ta ɗan murmusa ta kai cup ɗin tea a baki.

Kaka kuwa tana kallonta tana jin ƙamshin shayin nata 

“Indo, kin yi kyau wallahi yau. Naga kin fara murmushi da kyau. Alhamdulillah.”

Indo ta yi murmushi kaɗan, cike da kasaita ta ce “Eh kaka, daɗi nake ji yau.”

Ta kuma dariyarta kaɗan, ta ce a zuciyarta:

“Yau sai kin san wacce ce Indo Atika. Yanzu na rama ɗan abu, saura babban hukunci…”

Ta ɗan sharɓi tea ɗinta.

Gidan dai yau cike yake da shiru… amma shiru na kafin rigima.”

Indo ta zauna a gefen gadon Kaka tana shan tea, idonta a kan agogo.

Ta ga lokaci ya kusa — lokacin da Atika ke fitowa zuwa aiki 

Ta tashi a hankali, ta gyara veil ɗinta, ta fito sansanin gidan tana jingine da bango, tana jiran Atika kamar wacce ke jiran kallo mai daɗi Atika ta fito… Tana tafiya tana kararrairraya, kamar wacce aka sa masa ƙusa a takalmi.

Fuskarta ta dan rame, hasken da ya dinga fitowa ya sa Indo cikin zuciyarta ta ce:


“Tooo… ai alamar hukuncin na farko ya fara aiki.” Amma Indo ta daure fuskarta, kamar ba ta da wata mugunta a zuciya.

 Atika ta iso, Indo ta durgusa da ladabi irin wanda ta san zai kara fusata Atika:

“Ina kwana aunty Atika.” Atika ta tsaya cak da mamaki.

Bata saba jin gaisuwar Indo ba, balle har da durƙusawa.

Ta murguda baki, tana kallo kamar tana duban tsuntsu mai ban haushi.

Indo ta ƙara saki murya cikin sanyin jiki:

“Ki yi haƙuri aunty Atika… sai kin dawo aiki.”

Da sauri Atika ta zaro ido:


“Me?! Wato ke ba wai lafiya ake miki bane? Kin fara raina manya kenan?”


Ta harare Indo ta juya tana tafiya — amma har yanzu tana gwalewa ƙafarta kamar mai ciwon tsutsa.

Indo ta daga murya cikin wata irin muryar da za ta ƙone jikin mai saurare

“Aunty Atika… me ya same ki ne a ƙafanki? kamar kina ɗinkishi…?”


A nan Atika ta yi juyawa da sauri kamar za ta kai mata duka “Uban ki ne! Ƴar rainin hankali kawai!”


Ta shige mota ta buga ƙofa.

Driver ya tada mota suka tafi, domin bazata iya driving yau ba , Indo ta fashe da dariya


dariya mai sa zuciya ta huce:


“Sai kin gane wace ce Indo. Wannan fa farawa ne. Akwai sauran jerin hukunci .”

Ta dafe cikinta tana dariya, tana wucewa dakin Kaka “Wallahi saura Mommy ita ma yau na ɗan ƙona mata rai.” Dariya kawai ta ƙara mata kyau....


     Indo na daf da shiga part ɗin Kaka, wani ƙamshi mai lulluɓar zuciya ya yi mata tsaye a hanci.

Turare ne — turarensa — wanda ta riga ta haddace, ko cikin mutane dubu za ta iya gane shi ta tsaya cak ta juya a hankali…Sai gani tayi DR SADEEQ.

Yana tahowa cikin farin suit, riga da wando masu tsabtace ido, kamar aka zana shi da biro.

Gashin kansa ya yi kyau, fuskar sa tana sheƙi, takalman sa suna haske kamar sabuwar rana.


Indo ta lumshe ido ta buɗe.

Wani abu ya doke zuciyarta.


Indo (a ranta ta ja tsaki):

“Kai… wannan kamshin… wannan kyau… lallai akwai wata cuta a rayuwata.”

Ta rinka kallonsa daga sama har ƙasa, ta matse baki Indo (a hankali tana tafe a ranta):

“Irrin wannan kyawun kamar aljanni. Ba mamaki Atika ta dake ni akan sa… ai ko ni ma da nayi abin da ta yi domin tsaff zan iya hallaka yarinya idan tace tana sonshi ,to amman ai ne bana sonshi Amman kuma inajin wani abu kawai don ranar aljjanu na ne shiiyasa ma har yakaine wani gida amman ai ina yarda dashi saboda yana min komai ne kuma yana tausayina .”


Sai ta jinjina kai a hankali, ta dan murmusa da ɓacin raiIndo (a zuciya):


“Amma bari na gaya miki Atika… ko dukkan ku Mommy da ke… Dr. Sadeeq nawa ne. Ni kaɗai. Shi kadai akaye shi namiji domin ya zama mallakarta Indo.” Ta kalli Sadeeq da sassarfa ta shige ciki, tana karkarwa saboda kyawunsa, tana ƙoƙarin ɓoye:


“Ai sai na gama hukunta waccan banza sannan na maida hankalina ga wannan doctor ɗin nawa.”

Dr Sadeeq kuwa sai bin ta da ido yake yana mamakin yadda Indo ta tsare shi da kallo kamar zata sha shi


    Indo ta tsaya cak a tsaka-tsakin part ɗin Kaka, zuciyarta na bugawa kamar ta fita daga kirji.


Da ta hango Dr Sadeeq, wani ƙamshi mai ɗaci ya buge mata hanci — turaren sa ya lullube ta.

A hankali ta fara ja da baya, tana ƙoƙarin ɓoye raunin da yake mata.


Dr Sadeeq kuwa, ganin ta fara gudu zuwa gefe, ya girgiza kai — bai san me yasa zuciyarsa ta tashi haka ba.

Bai tsaya ba, ya bi ta kai tsaye cikin part ɗin Kaka, inda babu kowa.


Sai ga Indo ta tsaya, bugun zuciya ya ƙaru, ta ɗan tsaya kafin ta cigaba da motsi.


Da sauri Dr Sadeeq ya tsallaka daga tsaye, ya kama ta a kirjinsa.

Indo ta ɗan yi ƙoƙarin ja da baya, amma numfashin su ya fara haɗuwa.

Hannayen Dr Sadeeq sun haɗu da na Indo a kirjin sa, hannun sa ɗaya a kan hips nata.


Suna kallon juna cikin tsananin shauki da mamaki, ba tare da wata magana ba.

Lokacin ya tsaya a tsaka-tsaki, kamar lokacin ya tsaya cak, duk wani motsi da yanayi ya yi tsawo — zuciyoyinsu biyu na bugawa da ƙarfi.




    Dr Sadeeq ya ja ɗan kusa da Indo, idanuwansa na kallon nata da ƙauna mai haɗaka da rashin fahimta.


Ya ɗan matso, murya ta ƙanƙama cikin nutsuwa:

“Me yasa kike gudu na…? Kuma waya daki ke?”


Indo ta ɗan ja numfashi, zuciyarta na buga da ƙarfi, tana ƙoƙarin sarrafa ji da tsoronta.

Ta kasa fuskantar sa kai tsaye, sai ta kalli ƙasa, tana jin ƙyashi da ɓacin rai:

“Ni… ni… ban san… ba…” ta ƙara ɗan murya mai rauni, tana jin ɗan tsoro amma da sha’awa a lokaci guda.

Dr Sadeeq ya ɗan matso kusa da ita, hannu ɗaya ya ɗaura a kan kafadarta, yana ƙoƙarin sanyaya ta:

“Indo… ki dubeni. Banyi miki komai ba, ki sani kawai… ba ni da niyyar cutar da ke.”


Indo ta ɗan yi shiru, zuciyarta na bugawa, tana jin ɗan sassauci amma har yanzu cikin rikici tsakanin fushi 



    Yanayin ya ɗan yi tsanani sosai—zuciyarta na bugawa da sauri, Dr Sadeeq ya ɗaga hannunta a hankali, idanuwansa sun haɗu da nata:“Dube, ido na… gayyamin gaskiya.”

Indo ta yi shiru, ta ɗan kalli ƙasa, sannan ta murmusa da ɗan shakku:

“Ya wuce… ba komai.”


Sai Dr Sadeeq ya ɗan kusanto, ya taɓa fuskar ta da hannunsa, yana jin yanayin zuciyarta.”


Indo, a ranta, ta yi murmushi mai ƙanƙama, tana son ɗaukar hukuncin da kanta, amma yanayin jikin sa da kwarjinin sa ya ɗan tilasta mata shiru. Nan ya ɗan tsira mata idon, sai ya ce:

“To ne… kuma me nayi miki? Zaki daina min magana?”


Indo ta zumɓura baki, ta taki shi a hankali, amma cikin shiru.

Idon Dr Sadeeq ya yi ja, ya karkata kansa ya haɗa lips nasu, ya yi kissing nata na seconds kaɗan.


Bayan ya saki, ya yi murmushi mai laushi:

“Is okay… ke buɗe wayarki, ke kuma duk abinda zai faru, banason ki daina min magana kinji?”Indo ta ɗan yi shiru, sannan ta ce:

“To… Dr.”

Yanayin ya kasance mai ɗan faɗi, cike da ƙauna da jin hankali, amma kuma akwai tsoro da rashin tabbas daga bangaren Indo

Sai yace “Atika ce?”Ko sai tace “Ehh.”


Ya girgiza kai, “Okay, next time kar ki ɓoye min komai.”

Ya juya ya fita, ko Kaka bai jira ba da take sallar ta a dakin ta. Indo kuwa ta tsaya tana kallon hanyar da ya shiga, zuciyarta na bugawa da sauri. A gefe guda, ta ji irin Irrin tunanin hukuncin da baiwa Atika yau, da ke tattare da fushi da ɗan tsoro a zuciyar Dr Sadeeq.


Kaka ta shigo daga ɗakin sallah, ta ga Indo tana tsaye shiru-shiru. Ta matso kusa da ita, ta latsa kafadun ta da murya mai laushi:

“Yarinya, ki kwantar da hankali SADEEQ yaro ne mai nitsuwa da basira ke gayyamasa damuwar ke wanan ba abin ta da hankali bane....."

Indo ta ja numfashi mai nauyi, tana jin dan sassauta a zuciya. Duk da haka, tunanin Dr Sadeeq da Atika ya ci gaba da buga mata a rai, har ta ɗan ɗauke kai ta juya zuwa taga ta kalli gidan gaba, tana jin ƙwanciyar hankali a gefe, da ƙarfin fushi a gefe.

Ta san cewa yau ba ƙaramin rana ce ba—amma kuma, idan zata iya ɗaukar mataki cikin hankali, za ta iya ganin yadda kowa zai bi dokar da Kaka ta shimfiɗa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post