83
🌟⭐DR SADEEQ✨ 🌟
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
Dr SADEEQ ya miƙa mata leader a hannu, yana kallonta cikin kulawa da tausayi. “Daga yanzu, kin fita daga makarantar AL NOOR ACADEMY. Yanzu ana sallah da kwana uku, zaki tafi boarding school kamar yadda kika bukata. Ina kuma mai kara baki hakuri akan duk abin da ya wuce, in Sha Allah watarana zaki fahimci dalilinsa.”
Ya ɗan yi ajiyar zuciya, idanunsa sun haɗu da nata na ɗan lokaci. “Inason ki ƙara mai hankali a karatu kamar yadda kikiye a baya. Bayan sallah zan shirya miki walimar saukar karatun Alkur’ani mai girma, kafin ki tafi boarding school. Wannan kayan sallah ne ke ke zaɓa, idan kuma akwai wani abin da kike bukata, ki nemi ni kada ki faɗa wa kowa. Ke samun ne, in Sha Allah, ni ne zan kula.”
Ya ɗan murmushi, sannan ya ɗan sosa kai, “Ba za a yi tafiya da waya ba, saboda haka zaki ajiye wayarki a gida ke kula da kanki, ki riƙe mutuncinki da darajarki.”
Indo ta tsaya a can, tana kallon sa. Jikin sa yayi sanyi, zuciyarta ta ji wani irin raɗaɗi kamar rabuwar masoya. Ita kanta ta dube shi, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin kamar rabo mai tsanani tsakanin su.
Bayan ya fita daga ɗakin, shiru ya zauna, Indo ta zauna a gado tana ɗan jan numfashi. Kamar yadda jikin sa ya bar mata sanyi, haka zuciyarta ta yi nauyi da rabuwa. Ta ɗan kalle wayarta, amma ta tuna maganar sa, ba za ta yi amfani da ita ba.
Nan ta ɗan sunkuya a gadon, tana tunanin abubuwan da suka faru, da yadda zai kasance gaba da ita. Duk da tsoron da take ji, zuciyarta ta fara ɗan fahimtar cewa Dr SADEEQ yana so ne da gaske, amma yanzu lokaci ya zo da zata riƙe mutuncinta, da kuma fara sabon mataki a rayuwarta a boarding school.
Shiru ya cika ɗakin, Indo tana jin duniyar tana juyawa a hankali a gabanta, zuciyarta na bugawa tsakanin farin ciki da tsoro, tsakanin soyayya da hankali. Wannan shine farkon wani sabon babi a rayuwarta.
AFTER SOME DAY'S
Indo ta tsaya a ƙofar gate tana kallon Kamal da Dr SADEEQ suna hira cikin natsuwa. Idon ta ya ɗan kai ga Dr SADEEQ, amma tana jin tsoro ta kuskura ta kira sunansa. Kamal kuwa ya lura da kallon ta, sai ya ɗan yi murmushi mai cike da wasa, ya tsokane ta:
“Eh Indo, me yasa kike kallon Dr SADEEQ haka? Kina son wani abu ne daga gare shi ko dai kawai kallo kawai?”
Indo ta ja numfashi, zuciyarta na ɗan buga sauri, sannan ta faɗa:
“Eh… Inason… kuɗin saloon da lalle na Sallah.”
Dr SADEEQ ya ɗan yi murmushi, amma bai ce komai ba, sai Kamal ya ɗan girgiza kai cikin dariya:
“To ai haka kike tsoron magana da shi, amma yanzu kike buƙatar kuɗi ne, ko dai?”
Indo ta yi murmushi, ta ɗan ninka hannu a ƙirji, tana cewa:
“Eh, don haka ne na zo, Uncle Kamal Amma da gaske ne, kuɗin ne kawai nake bukata.”
Kamal ya yi dariya, ya ɗan tsokane ta cikin natsuwa:
“Eh, to yanzu gani nayi, Dr SADEEQ fa… ga wannan yarinya tazo tana son kuɗi kuma tana tsoronka "
Indo ta ja numfashi, zuciyarta na ɗan buga sauri, amma tana tsananin bukatar kuɗin. Dr SADEEQ ya ɗan yi shiru, idonsa na kallonta, sannan a hankali ya ce:
“ okay anjima zan kawo miki kuɗin, ki tafi part naku yanzu.”
Indo ta yi godiya, ta miƙe hannu cikin ladabi, sannan ta tafi tana murmushi, amma a zuciyarta tana tunanin yadda Kamal ya tsokane ta da yadda Dr SADEEQ zai kawo mata kuɗi.
Dr SADEEQ yana fita daga parlour, ya ɗauki envelope ya haɗa kuɗin da Indo take bukata, ya je part na KAKA ya same ta yana murmushi a hankali:
“ take this .”
Indo ta ɗauka, zuciyarta na cike da godiya, tana murmushi tace:
“Nagode sosai, Dr… Allah ya saka da alkhairi.”
Bayan ya fita, ta zauna a part ɗin ta ɗan shakatawa, tana ta lissafa abubuwan da za ta siya, sannan ta tashi ta tafi gidan su Ilham.
Da isowa, Ilham ta rungume ta da murna:
“Indo, kin iso lafiya! To mu tafi Saloon yanzu mu gyara kitso da kyau, ki shirya ki yi kyau sosai!”
Suna isa Saloon, suka fara shirin gyara kitso da kyau, Inda aka gyara GYRAH da sukaye masu kyau, kayan su tsabta, turare ya ƙara musu kwarjini, suna dariya da hira, suna jin daɗin lokaci tare kafin su dawo gida.
Bayan sun gama gyaran kitso aka gyara gashinta sosai har yayi luff luff mai sheki da kyau. Sun gama aka musu lalle Black and red , suka koma gida cikin farin ciki, zuciyarta na cike da nishaɗi.
Yanzu a gidan su Indo, kowacce tana cikin gayu da kyau, turare da kayan ado sun haɗu suna ƙara mata daraja. Idan har ka hango Indo yanzu, zaka rantse da Allah cewa ita ma yar gidan ce, ta ƙware, ta fara samun natsuwa da martaba kamar sauran 'yan gidan.
Ranar Sallah ta zo, Indo ta tashi da safe tana jin daɗin sabuwar ranar. Ta shiga wanka mai zafi da sabulu mai laushi, ta shafa jikinta sosai daga kai har ƙafa, tana wanke kowane wuri da hankali, domin ta tabbata tsabta da kwalliya sun haɗu. Bayan wanka, ta shafa lotion mai kamshi mai ɗanɗano na fure-fure, wanda ke bayyana sanyi a fata da ƙamshin da zai jawo hankali.
Gashinta ta tsabtace da kyau, Ta sanya hair oil a ƙarshen gashi domin ya yi laushi da ƙyalli. Fuskar ta kuma ta yi natsuwa; ta shafa foundation mai sauƙi da ɗan blush mai laushi, eyeshadow mai launin peach da zinariya, mascara domin idonta suyi haske, da strawberry lips gloss wanda ke sa lips ɗinta su haskaka da ɗanɗano.
Ta saka abaya fari mai tass, wanda ke bayyana daraja da ladabi, takami fari mai haske, da handbag mai kyau a hannu. Ta ɗan gyara scarf ɗinta a hankali, ta tabbata komai a wuri guda. Ta kalli madubi, murmushi ya bayyana a fuskarta; ta ji tana da ƙyalli, kwaliyyar da ladabi, da santsi, cikakkiyar Indo mai tsabta da annashuwa.
TA FITO HARABA DOMIN ZUWA EID
