*AUREN WATA UKU.!*
*02*
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Zubair yai parking idanunsa kan Ummulkhairy da tun isowar motarsa wajen ta kasa komai sai hawaye dake bin k’uncinta. Ba yau ne rana na farko da aka kawo sadakinta aka amshe ba balle wani Kayan lefe saidai a yau d’in taji wani irin abu da bata tab’a ji ba a baya. Ta sani ba wai son Zubair take ba sabida zata iya cewa zuciyarta ta k’ek’ashe da batun wani aba mai suna soyayya. Batajin ko a gaba zatayi wani abu wai shi soyayya. Tayi na’am da aurensa ne dan cikan burin mahaifiyarta kaman dai sauran aurarrakin da ake saka mata ana fasawa. Dikda hakan bazata bataji ciwon abinda ya faru cikin zuciyarta ba. Ta zaci wann shine na k’arshe. Ta zaci komai zaizo k’arshe. Ta zaci burin mahaifiyarta zai cika daga k’arshe. Sann kowa zai salama saidai abun ba haka bane. Da alama ita dai wann shine k’addararta bazata tab’a aure ba kaman yanda mutane ke fad’i akanta. Lumshe idanunta tai hawaye masu tsananin dumi suka gangaro mata. Shin yaushe ne komai zai kare.. Yaushene komai zaizo k’arshe.? Tambayar da ita kanta bata da amsar sa.
Khulsum kaw ko tsayawa kula su Hajiya Dudu batai ba balle ta kula da Zubair Wanda bai jima da k’arasowa wajen ba. Sai zuba ruwan masifa take tana nuna su Maman Sahal tana fad’in duk macen da bata fasa kokawa da ita bata haifu ba.
K’arasowan wasu matasa sukai k’ok’arin raba fad’an. Sai huci Khulsum take tana gyara mayafinta. Ta d’auki mayafin Ummul da akai jifa dashi can gefe ta rufa mata. Ta shiga janyo hannunta tana fad’in “Adda Ummul muje aurenki kuma in sha Allah ba fashi Akan idanunsu za’ayi saidai mata ta mutu..”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Hajiya Dudu tana fad’in “Aure ba fashi a gidan uwarki.? Mai za’ayi da mace mai dambe a titi..” Ta jiyo tana duban Zubair da ya kasa koda bud’e k’ofar mota balle ya fito “Ka daiga abinda nake fad’a maka ko.. Ka gani da idanunka.. Allah ya ceceka bazakai asaran sadaki ba.. Yo wann ai asaran sadaki ne.. Dama da na fada maka wann yarinyar ballagaza ce. Yanzu zaka yarda da batu na. Aure kaida wann ballagazar ko a k’iyama ehe..!” Ta k’arashe tana jefa kit d’in hannunta cikin boot d’in motar da tuni sauran matan sun dire akwatunan hannayensu ciki.
Har lokacin idanun Ummulkhairy a k’asa suke hawaye d’aya na bin d’aya.
Gaba d’aya sai jikin Khulsum yai sanyi musamman da taga yanda Zubair ke aikama Ummul wani irin kallo da ta gaza tantance na tsana ne ko na mamaki.
Sunaji suna gani Hajiya Dudu ta k’arashe maganganun ta suka shige mota da sauran matan. Tuni Zubair yaja mota Sun bar wajen saima k’ura da ya bud’e su Ummulkhairy dashi.
Jiki a matuk’ar sanyaye Khulsum ta kamo hannun Ummul. Saidai kafin tace wani abu Ummul ta janye hannunta ta nufi gida cikin saurin wani kukan na kuma b’alle mata.
Jiki a sanyaye Khulsum ta take mata baya.
Suna shigowa gidan suka tadda mahaifiyarsu zaune dirshan tsakar gidan sai cazgan kuka take. Ga Mama Tani wato kishiyar mahaifiyarsu kuma uwar gida a wajen mahaifinsu tayi bak’e bak’e a tsakar gidan sai ‘yan wak’e wak’enta na habaici take.
Ummul ta k’araso a sanyaye ta duk’a gaban mahaifiyarsu dake cazagan kuka. Jiki a sanyaye, murya na tsananin rawa Khairy ke fad’in “Umm..Umma.. Umma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.
Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa. Cikin kuka take duban Ummulkhairy tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Ummul na gaji.. Wllhi na gaji.. Na gaji dake.. Na gaji da wann fashe fashen auren da ake akanki.. Ummul na amso Miki rubutu.. Na Kai sunanki gaban Malamai an baki rubutu an miki addu’o’i.. Ke k’arewa har ruk’iya an miki.. Ummul anya ke ‘yaradam ce..” Ta k’arashe tana kuma fashewa da kuka. Yayinda Kan Ummulkhairi ke duk’e kukanta na k’aruwa da Jin kalaman mahaifiyarta.
Khulsum kaw girgiza Kai kurum take tana duban mahaifiyar tasu cikeda mamaki Jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta. Ita kaw Mama shewa tai harda tafi kaman ta samu tv haka take dubansu. Sai dariya take cikeda nishad’i.
Khulsum ta aika mata mugun kallo kafin ta maido da dubanta ga mahaifiyarta da kuma ‘yaruwarta.
“Umma dan girman Allah ki daina irin wann kalaman Akan ‘yarki.. Ke fah uwa ce Umma..” Khulsum tace ranta na tsananin sosuwa.
A hasale mahaifiyarsu ta d’ago tana fad’in “Ke dalla can rufe min baki.. Mai kika sani..? Ki bari randa kika zama mahaifiya irin k’addarar da ya samu ‘Yaruwar ki ya samu d’iyarki sann ne zakiji ciwon da nake ji.. Wayyo Allah.. Wayyo ni Suwaiba laifin mi nayi aka jarabceni da ‘ya irinki Ummul.. Ke ba wani tawaya bane tattare dake d’an hasken nan baki rasa ba. Ke duk wani abin da mace zatai tink’aho dashi daidai gwargwado Allah ya baki amma a rasa Wanda zai aureki kowa da yazo sai Ya gudu.. Haba Ummul..!” Ta kuma fashewa da wani kukan..
Idan da sabo sun Saba da dramar mahaifiyarsu. Khulsum ta girgiza Kai. Tinda aka soma amsan kud’in auren ‘yar uwarta Ummulkhairy ana fasawa cikin damuwa da tashin hankali mahaifiyarsu take. Batada da burin da ya wuce taga Ummulkhairy tayi aure ta bar gidan ko ba dan komai ba sai ko dan gori da maganganu da take fuskanta Kama daga kan Abokiyar zamanta har izuwa kan ahalin gidan dama sauran jama’an unguwa. Mahaifiyar Ummulkhairy ta kasance irin mutanen nan ne masu saka damuwan maganganun mutane a ransu. A akasarin lokuta mutane suna mata kallon sakarya wacce batada wani wayo ko cikakken hankali. Sann tin Ummulkhairy tana k’arama taci burin ta aurar da ita da k’anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k’ananan shekaru taita mata wak’e tana karanto baitika tana mata rawa tana fad’in saura k’iris ta aurar da ita saura k’iris ta kaita d’akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab’a mata maganganu da fad’in ta jira dai taga girman ‘yar tata sam bazata tab’a tankata ba. Umma Ta kasance irin mutanen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad’a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad’a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu itada Khulsum yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko.
Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda bata sonsa zatai hak’uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d’inta tai aure ta tafi d’akin mijinta.
Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yara uku gareta kuma duk sunyi aure suna d’akin mazajensu. Badi’a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d’akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d’aya daga cikin matan unguwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad’in ita nata yaran kaf suna d’akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta.
Mahaifinsu baida wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k’arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k’ok’arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k’asan zuciyarsa na damuwa da al’amarin ‘yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum cikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d’iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d’anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba.
Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da Umma ke ci gaba da yi tana fad’in “Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za’ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k’irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min mafita Wayyo ni Suwaiba..” Ta k’arashe tana kuma rusa wani kukan.
Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai ‘yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne masu nuna kulawa da k’auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan ‘Ya’yansa da danginsa dukda kuwa k’annensa dake zaune cikin gidan basu d’aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu nasiha da wasilci da zumunci ba.
Cikin b’acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad’in “Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?”
Batace komai ba sai gunjin kuka da take ci gaba.
Ya kuma girgiza Kai “Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k’arshe ba tinda dai kink’i amincewa ‘yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d’in ke so.”
Cikin zuban hawaye ta d’ago tana duban mijin nata “Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.”
“A ina kika tab’a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka nawa Ummul d’in take ne..?”
Umma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d’in take. Tai karaf tace “Ta fah haura talatin Abban Ummul.”
Taci gaba “Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k’ok’arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.”
Abba ya kuma katseta “Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb’ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d’aura Miki ba.. Ko an fad’a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Amma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab’awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu’an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata domin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki keda amfani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..”
Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye “Haba Abban Ummul dan Allah ka fad’a alkhairi..”
“Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad’in alkhairi gameda ‘yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su ‘ya’ya amana ce Allah Ya bamu kuma za’a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe.” Ya k’arashe yana mai janyo kwanon tuwon sa.
**
A can d’aki kuwa Khulsum ce ta duk’a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak’umi tana fuskantar ‘yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka.
