AUREN WATA UKU..!*
48
*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*
Wasa wasa an shafe sati uku da mutuwar Auren Ummul da kuma Haidar. A wann lokacin Daddy ya shafe a k’alla sati guda da dawo daga SouthAfrica, kuma labarin scandal din da yai erupting wajen bikin tariyar Haidar d’in Ya cimmasa. Hankalin Mommy duk ba’a kwance yake ba sanin mijinta mutum ne da ko kad’an baiso wani abu ya shafi Kasuwancinsa. Yanda rayuwar ahalinta Ya soma daidaita bata fatan abinda zai kawo musu wani mishkila ko sab’ani. Ga mamakinta sai Daddy ya tari abun bisa lumana ba kaman yanda Ya saba a baya ba. Dan ko zancen bai bata k’ofan ta masa ba dikda taso yi masa. Bai canza ko kad’an daga irin kulan da yake bata ba tin bayan da suka daidaita tsakaninsu. Hasalima k’ara janta jiki yai yana fad’in irin kewarta da yai. Ta d’an dubesa a sanyaye tana so suyi zancen sai Ya kuma janyo hannayenta yace “Kwaise na gaji da tafiye tafiyen nan. Inaga lokaci yayi da zan mik’a ma yaron nan ragamar kasuwancin.. Koda wani portion ne. We are not getting any younger.. Shekaru k’aruwa suke..”
Mommy ta jinjina kai duk jikinta a sanyaye. Alamun shigowar mota sukaji. Daddy ya lek’a window sai Ya murmusa yace “Ina tunanin Yaronnan ne … Na kira shi yana company.. Na sanar dashi Ya bar aikin da yake yazo gida magana zamuyi.”
K’irjinta ya bada dam.! Dan tuni jikinta Ya bata ba magana mai k’aramin mahimmanci bane zaisa ya kirawo Haidar ya bar aikinsa yazo gida dan kawai suyi magana.
“Let’s go downstairs..” Ta sinkayo muryar Daddy yana k’ok’arin nufan k’ofa.
Jikinta babu wani k’wari tabi bayansa.
A parlor suka iske Haidar Har ya k’araso yana jiran sauk’owa mahaifin nasa.
Haidar ya risina ya gaida iyayensa. Duk suka amsa masa da sakin fuska saidai kallo guda zakai ma Mommy ka fahimci tana cikin damuwa.
Daddy ya dubi Haidar cikeda kulawa “Aliyu.” Ya kirasa da asalin sunansa.
Haidar ya amsa cikeda girmamawa.
Daddy yaci gaba “Na dawo na taradda abubuwa marassa dad’in gani da kuma sauraro. Garin yaya al’amra suka lalace har haka.?”
Haidar ya jinjina Kansa a hankali sai yace “Daddy Kai hak’uri.. Ban.. san abubuwa zasu zama haka ba.. Amma tuni nasa jam’ian bincike su binciko yanda Dareen take.. Kai hak’uri Daddy.. Idan duka wann ya saka Kasuwancinka cikin had’ari..”
Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an sai ya girgiza kai yace “Ba wann nake son ji ba.”
Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yaci gaba “Ba batun Kasuwancina da abinda zai shafesa nake son ji ba.. A’a naka batun nake son ji.. Al’amarinka da iyalinka. Because you matters to me more than any business.”
Haidar yaji wani abu can k’asar zuciyarsa. Yau Daddy ya zab’i ya fifita al’amarinsa sama da Kasuwancinsa da a baya yake d’aukakawa.
Jikin Mommy yai sanyi musamman da taga Haidar yayi shiru. Duka laifin nata ne. Gwara ta sanar da Daddy yanda al’amarin ya kasance.
Jiki a sanyaye Mommy tace “Dama..” Haidar bai bari takai aya ba yai karaf yace “Daddy scandal din da ya faru ya.. janyo sab’ani tsakanina da Ummulkhair.. Kuma har ta kaiga na mata saki.. d’aya.”
Sai Mommy ta dubi Haidar cikeda tausayawa.. Ta fahimci yasan duk abinda tai amma ya zab’i ya rufa asirinta. Bazai bari mahaifinsa yaji ga abinda ta aikata ba gameda AUREN WATA UKU. Allah sarki D’a da uwa. Sai taji girma , k’ima da soyayyan d’an nata ya k’aru a kwayan idonta. Fatan ta Allah ya albarkaci rayuwarsa Ya daidaita al’amarinsa da iyalinsa.
Daddy ya dan numfasa sai ya dubi Mommy yace “Rankidad’e, can I have a moment with my son.?” Ya k’arashe yana dan mata alama da ido.
Mommy tace “Badai cireni akai daga cikin ahalin ba.”
Ya dan murmusa kad’an “Waye ya isa ya cire ran gida cikin ahalinta. Magana ce tamu. Men talk.”
Ta d’an murmusa “Kace dai kawai wariya. Toh bara na baku waje dama inada abinyi.” Ta k’arashe tana mik’ewa.
Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Haidar banji dad’in abinda kai ba dukda sanin saki a musulunci ba haramun bane amma sai idan Ya zama dole akeyi. Idan akace daga samu sab’ani za’a dinga saki da ko mu nan iyayenka bamu kawo har wann lokacin muna tare ba. Kai shaida ne.. Kaga k’alubale da iftila’i na rayuwa da mukaita fuskanta. Amma dukda haka muka jajirce. Har hakuri ta kawo mu yanda muke yau. All marriages have ups and downs but this decision should not arrive easily.” Sai Daddy ya mik’e tsaye kaman Wanda ya tuna wani abu “Kaga tashi muje.. Akwai yanda nake so ka rakani.”
Haidar ya jinjina Kai yana amsawa. Suka jera suna tafe shida mahaifinsa. Ta window Mommy ta hangesu sun jera Sun fice. A ranta tace ko ina D’a da mahaifin suka nufa sai Allah. Ta murmusa tana jin dad’in yanda sabo ya fara shiga tsakaninsu.
Koda suka fito Haidar ya tambayi Daddy ko Yai masa kiran driver d’insa amma sai Daddy yace a’a shi Haidar d’in zai tuk’a motar. Nan ma cikeda girmamawa Haidar ya amsa masa. Daddy ya shige mazaunin mai zaman banza yayinda Haidar ya shige wajen driver. Suna tafe Daddy yace dashi gidan Alhaji Gimba suka nufa. Kai tsaye Haidar ya d’auki hanyar gidan aminin mahaifin nasa.
Koda suka isa Daddy yace da Haidar yai parking daga waje. Nan ma yabi umarnin mahaifinsa. Suka fito Daddy na d’an gaba kad’an yayinda Haidar ke take masa baya. Sai Haidar yaga Daddy ya nufi masallacin k’ofan gidan Alhaji Gimba. Suka gaggaisa da mutane ya tambayesu Ya Sheikh bai fito ba. D’aya daga cikin mutanen yace “Ai zai wahala Ya Sheikh ya fito yau sabida tun jiya yake cewa bai gane jikin ba.” Daddy yai masa fatan samun lafiya. Ya kuma yi ma mutanen Sallama Wanda kusan dukansu Dattijai ne kaman sa da ma Wanda suka fisa. Da alama duk sun saba dashi dan tare suke d’aukan karatu a nan masallacin tsakanin sallar magrib da isha wajen Imam ya Sheikh.
Sun fito tareda Haidar kenan saiga Alhaji Gimba. Nan suka tsaya suna gaisawa. Haidar ya dan matsa gefe ya basu waje.
Alhaji Gimba ya dubi Daddy ya dan girgiza kai “Lafiya dai naga ka taho tareda Haidar..?”
Daddy ya dan sauk’e ajiyan zuciya yace “Lafiyan zance ba lafiya ba tinda kanada masaniyar abinda ya faru lokacin bikin tariyarsa da iyalinsa.. Tinda Har business competitors dinmu sun so suyi amfani da wann su sokemu.”
Alhaji Gimba ya jinina Kai “Haka ne.”
Daddy yaci gaba “Toh Wato abinda ke faruwa shine.. Wann abu da ya faru har ya haifar da matsala tsakanin shi Haidar d’in da iyalinsa.. Kuma kaga abu da yara tashi d’aya yayi saki.. Kasan da yawan samarin nan ba’a zama a fahimtar dasu menene ma Auren kansa kafin su shigesa which is wrong.. As a parent musamman ma Uba inaga yanada kyau idan D’anka yakai munzanin Aure ya kuma zo maka da batu na Aure idan Har zaka nemar masa Auren ‘yar wani. Ko dai kai ka zaunar dashi ka fahimtar dashi menene Auren kokuma ka kaisa yanda za’a zaunar dashi a sanar dashi Auren tareda hakkokinta da hukunce hukuncenta.. Dan nima har yau ina nadaman wasu kurakuren da nayi a baya kuma bana fata irin haka ya faru da D’a na. Idan ka duba da yawa yanzu Shiyasa zakaga mace macen Aure yayi yawa dan shiga cikin Auren kawai ake ba karatun sanin hukunce hukuncenta.. Shine kaga na kawo shi nan dan Sheikh Imam ya fahimtar dashi wasu abubuwa. Sai kuma akai rashin sa’a Sheikh yau bai fito majalisi ba.”
Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Wann gaskiya ne Abokina. Ina ma iyaye da yawa zasuyi yanda kayi da an rage wasu mace macen Auren da babu gaira babu dalili. Amma tinda yanzu Sheikh baya nan ni zan zaunar dashi mu d’an yi magana ta fahimta.. Kasan kai zai iya jin nauyinka a wasu abubuwan.. Sann idan son samu shima kasa ya dinga zuwa d’aukan karatu ko ba lokacin da muke ba.. Akwai lokacin da aka Ware dan samari kaman shi. Lallai yanzu Babu mai zama da jahiltan addini sai Wanda yaso.”
Daddy ya jinjina Kai “Wann haka ne.. Toh zan bar maka shi. Zan kira driver yazo ni ya d’aukeni.”
Alhaji Gimba yace “Akwai driver na ai sai ya kaika.” Nan sukai sallama Daddy ya sanar da Haidar shi zai tafi
A d’an wani hut dake haraban gidan suka zauna yayinda Alhaji Gimba ya soma jan Haidar d’in da hiran Kasuwanci kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Haidar, ni aminin mahaifinka ne nasan kasan da wann.”
Haidar ya jinjina Kansa a hankali. Alhaji Gimba yaci gaba “Kaman yanda musulunci yace abokan iyayen mu iyayen mu ne. Idan sunga munyi wani abu ba daidai ba zasu iya kiranmu su mana gyara.. Idan ma ta kama su tsawatar mana duk zasuyi.. Haka ne.” Nan ma jinjina kai Haidar yai. Alhaji Gimba yace “Ma sha Allah. wato Haidar, mahaifinka ya sanar Dani abinda ke faruwa, ba wai dan ya bud’e min sirrinka ba sai dan so da yake a samo maslaha.”
Haidar yai shiru yana sauraronsa.
Alhaji Gimba yaci gaba “Wato shi Aure wani abu ne da yakeda mahimmanci Haidar a rayuwar Al’umma gaba d’aya. Dalilai da dama suna sawa ayi aure haka dalilai da dama Suna sawa Aure ya mutu Wanda ba’a so. Daga cikin dalilan mun sani Aure ibadah ne bautan Allah ne kuma d’abbaka sunnnar Ma’aiki (SAW) sann duk Wanda ya d’auki aure matsayin ibada bautan Allah zai samu dacewa da tsira harma da farin ciki a cikinta. Hakan nan Aure yana sa kamewa daga fad’awa tarkon zinace zinace. Kaman yanda yazo a hadisin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara yarda a garesu. Yanda Manzo (SAW) yace yaku taron samari ga Wanda ya samu iko daga cikinku yayi aure. Shi aure yana tsare gani sann yana kame al’aura. Har yake cewa ga Wanda bai samu hali ba toh yayi azumi. Shi azumi garkuwa ne.. Sann dalili na gaba samun nagartacciyar Al’umma. Ta hanyar Aure ake haihuwa a samu Al’umma nagartacciya. Bazamu fad’ad’a ba amma kaga ko wad’ann muka d’auka Sun ishemu dalili. Haka zalika shi Auren nan ba’a barmu kara zube ba saida aka koyar damu yanda zamu zauna cikinta ta fuskar shari’a da koyarwar addini. Ta yanda d’aya bazai zalunci d’aya ba a cikin zamantakewar. Domin kuwa addinin musulunci addini ne mai kyau da tsari da kuma adalci. Haka zalika idan rabuwar Aure ta kama dole, Wanda ba’a fata toh nan ma saida aka koyar damu yanda zamu rabu bisa kyautatawa da mutuntawa.” Ya dan gyara zamansa kafin yaci gaba “In Islam, it is believed that married life should be filled with mercy, compassion and tranquility. Sann Zaman aure zo mu zauna ne zo mu sab’a.. Ko harshe da hakori watarana ana samun mishkila.. Toh idan an samu sab’ani ba haka kawai ake saki ba sabida girman al’amarin.. Akwai hikima da musulunci ya saka saki hannun namiji. Dan idan mace ne zakuyi fad’a sau d’aya amma tana iya cewa ka saketa sau dubu. Kaga tunaninta da naka ba d’aya bane.. Hangen nesanka da nata ba d’aya bane.. Kai ko a halitta ta fuskar k’iran jiki kaida ita ba d’aya bane. Ita haka Allah ya halicceta mai rauni kai kuma mai jurewa. So idan al’amara irin wann suka taso endurance dinka da tolerance d’inka ya kamata yafi nata. Idan an samu rashin fahimta ko matsala a zamantakewa a tsakanin. Kuyi k’ok’arin samo maslaha tsakaninku ba sai third party ya shigo ba, idan kukai trying a tsakaninku still ba’a samu maslaha ba sai a saka manya ciki dan amfani manyan kenan. Bama a fata har takaiga zuwa gaban manya toh amma idan ya zama ba mafita sai a mik’a matsalar gaban magabata. Idan ya gagara a mik’a matsalar gaban jagororin Al’umma wato malamai. Idan shima baiyi working ba toh fah ka sani duk yanda ake son wani Auren rabuwan shi yafi alkhairi. Sann idan Allah ya k’addari ba sauran zama dole za’a rabu.. Toh sai a rabu cikin mutuntawa da kyautatawa..” Ya dan gyara zamansa “Shin ya ma ake sakin.? Saki yana nufin furtawa. Intention na saki ba saki bane. Idan kace ma matarka zan sakeki, wann ba saki bane.. I intend to divorce you, this is not a divorce. I think we should get separated, this is not a divorce either.. It has to be a statement or a verb. In the sense that Na sakeki, .. Or you are divorced. Shikenan ta saku. Shi da yayi sakin yanada chances na kome guda biyu, idan yayi na uku babu kome Har sai ta auri wani mijin bashi ba. Idan miji ya saki matarsa sau d’aya, meaning one down two to go. Sann Anfi so matar ta zauna gidan mijin tayi iddarta. Akwai hikima da musulunci yace ayi hakan. Dan a wann zaman zai iya maida matarsa kuma ta maidu ba sai anje ana biko da sauransu ba. Menene Iddah.? Shine waiting period after the divorce. Ga macen da batada juna biyu iddah period dinta shine 3 monthly cycles.. If she’s too old like If she’s in her menopause ma’ana wacce ta daina Al’ada ko kuma yarinya k’arama wacce bata fara ba their iddah period is 3 months.. Idan mata mai juna biyu ce kuma iddarta shine ta haihu.. And this may be 2 months, 3months, 7months.. Depending on her pregnancy.” Sai ya dan gyara zamansa “Now, it is prohibited for a man to divorce his wife a lokacin da take al’ada, or when she’s in the state of purity yet he had intercourse with her in that state of purity. An hana saki a wad’an nan lokutan. Wann shine saki na bidi’a. Innovated divorce. Mafi rinjaye Sun tafi akan it is sinful but valid. Ma’ana kuskure ne hakan amma matar ta saku. Idan mutum zai saki matarsa. God forbid, yet they had intimacy few days, few weeks ago. Musulunci yace he waits until she gets her menses. Idan tai tsarki ba’a samu intimacy ba sann sai ya saketa. Kaga zai wahala ma yayi sakin idan har zai jira wann lokacin. Amma da yawa hakan baya faruwa sabida mafiya yawan sake sake cikin b’acin rai akeyi. Akwai hikima cikin duk abinda musulunci yayi umarni ko yayi hani..”
Yaci gaba da bayani kan hukunce hukunce da hakkoki Haidar na saurarensa.. Har ya fara tuna nashi sakin da matarsa Wanda sun samu intimacy kafin ya saketa. Ya lumshe idonsa kad’an yana karanto istigfari. Har saida ya sinkayo muryar Alhaji Gimba yana tambayarsa “Be open with me Haidar. Shin kana son matarka.?”
Haidar ya jinjina masa kai “I love her with my life Uncle… But..”
“There’s no but if you truly love her..”
Jiki a sanyaye Haidar ya girgiza Kai yace “I choose to be the problem Uncle.. I choose to carry the burden..” Ya dan girgiza kai a hankali “Mahaifiyata ta wahala sosai.. Tanada kurakurenta, but.. I can’t let her carry it all alone.. Bazan iya barinta ita kad’ai ta fuskanci matsalar ba sabida ita din ta fahimci kuskuren ta kuma ta tuba.” Yaci gaba da jinjina Kai “I choose to be her shield in this.. Idan hakan na nufin sitirta kuskurenta, even if it would destroy me.!” Ya k’arashe cikin yanayi mai ban tausayi.
Alhaji Gimba ya dubesa cikeda tausayawa. Yanada masaniya gameda family issue da ahalin Aminin nasa suka fuskanta. Yau Haidar ne yake sacrificing farin cikinsa sabida mahaifyarsa lallai rayuwa ta sauya kuma Haidar ya cika D’an da za’ayi alfahari dashi. Sai yaci gaba da jinjina Kai a hankali murmushin saman fuskarsa yake duban Haidar d’in.
“Idan na fahimceka Haidar, kayi komai ne sabida mahaifiyarka. Kuma duk d’a nagari irin haka zaiyi.. Ba ina nufin sakin ba.” Ya d’anyi gyaran murya “Ka zab’i ka sadaukar da farin cikinka sabida mahaifyarka.. Amma rabuwa da iyalinka bazai zama mafita ba. Bansan menene wann kuskure na mahaifyarka da Kake son sitirtawa ba, ka sani duk Wanda Ya rufa asirin wani musulmi Allah zai rufa nasa ranar gobe balle Mahaifiya. Saidai akwai hanyoyi da dama da ake bi dan shawo kan matsala. You can’t let yourself be destroyed in the process.. Because Destruction is not the solution and it will never be. Mahaifyarka sai tafi shiga tashin hankalin idan har hakan yai destroying d’inka. You are a man, and you supposed to act like one.. Be brave enough to face your problems..Kar ka guje ma matsalolinka dan idan ka guje masu zasu bibiyeka ne har k’arshen rayuwarka.” Ya dan numfasa “I’ll ask you this question again, do you love your wife.?”
Dubansa kurum Haidar keyi, ya shiga jinjina Kai ba tareda ya iya furta koda kalma ba.
Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Then what are you waiting for, go and reconcile with your wife. Kaje ka dawo da iyalinka.”
Sai Haidar ya d’anyi shiru yana tunanin irin k’iyayyar da ya hango a kwayar idanun Ummul. Ya sani a halin yanzu Babu abinda tafi tsana Watak’ila sama dashi.
Jin yayi shiru yasa Alhaji Gimba murmusawa yace “Bansan Aliyu da rashin k’warin gwiwa ba dukda ance rauni na cikin soyayya.” Ya k’arashe cikeda barkwanci.
Sai Haidar ya d’an k’ak’aro murmushi yana jinjina Kansa “In sha Allah Uncle, zan dawo da ita. Kuma bazan tab’a sarewa ba. Na gode k’warai.. Allah ya saka da alkhairi ya k’ara girma.”
Alhaji Gimba ya murmusa “Yanzu naji Zaki na magana. Allah ya maka albarka ya mana jagora.”
Haidar ya amsa da Ameen had’ida k’ara godiya ma Alhaji Gimba.
Alhaji Gimba ya mik’e suka jera zuwa motan Haidar a tare tamkar yana ma Haidar d’in rakiya.
Haidar bai tab’a tsammanin rana irin wann zata zo ba. Mutumin da a baya yake masa kallon tarayyarsa da mahaifinsa babu wani alfanu. Mutumin da yai masa mummunar fahimta a baya. Sai gashi yau wann mutumin ya zamto tamkar mutumin da ya jefa masa igiya cikin rijiya mai duhuwa yace ya kama ya fito. Tabbas zaka k’i wani abu wann abun alkhairi ne a gareka, zaka so wani abu wann abun sharri ne a gareka.
Fatan alkhairi Alhaji Gimba ya kuma yi ma Haidar d’in. Ya kuma ce a duk lokacin da wani abu ya shige masa duhu ko yake nema shawari his door is always open yazo ya samesa matsayin Uba a wajensa. Godiya Haidar ya kuma masa cikeda girmamawa kafin ya wuce.
Tinda ya fito daga gidan Alhaji Gimba yake ji kaman ya k’ara masa k’warin gwiwa ne.. Yayi alk’awarin zai jira Ummul Har tayi healing koda zai d’aukesa tsawon shekaru ne.. Amma yau da Alhaji Gimba ya nusar dashi zai iya wasa da damarsa sai yaji bazai iya jira ba. Zai tafi yayi yak’in dawo da Ummul cikin rayuwarsa da taimakon Allah.
Washe gari sassafe yai shiri da zummar d’aukan hanya garin Kano. Ya shigo ya gaida iyayensa sann ya k’arada “Daddy, Mommy.. Ina so zan tafi garin Kano yanzu.. Zanje na dawo da Khairy.”
Farin cikin Mommy ya gaza b’uya. Duk a ‘yan kwanakin ta kula ko zancen Haidar baiso a masa sai gashi yau yace zaije ya dawo da matarsa. Suka saka masa albarka tareda fatan alkhairi.
Daddy ya dakatar dashi.
Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yace da Haidar ya jirasa a mota yana nan fitowa.
Mommy tace “Engr. Ya naga ka tsayar dashi..?”
Ya murmus “With your permission Rankidad’e, I’m going with him.. I want to be a father to my son..”
Har k’walla saida suka ciko idon Mommy. Ta tuna farkon Auren Haidar da Ummul d’in Daddy cewa yai ba hannunsa ba ruwansa tayi yanda take so da rayuwar D’anta. Yau sai gashi ya saka kansa tsamo tsamo a al’amarin Haidar d’in.
Ta murmusa tace “Toh kodai nima nayo muku rakiyar ne.?”
Daddy ya girgiza Kai yana d’aura wristwatch d’insa “A’a wann tafiya ce tamu ta maza. Daga baya sai kiyi naki.”
Murmushi kawai Mommy tai ta musu fatan sauk’a lafiya baida dacewa.
**
Koda suka isa garin Kano sun samu an kaisu Har k’ofar gidan Malam Isubu mai Manja kaman yanda aka fi saninsa.
A farfajiyan gidan aka saka masu tabarma daga nan k’ofan su Ummul d’in dan Tani bata bari ‘yanuwan Mahaifin Ummul da suke uba d’aya Wanda suka amshe kudi hannun Asshe farkon Auren Ummul d’in sun shiga cikin maganar ba, sanin abinda ka iya zuwa yazo. Dukda maganan na maza ne amma kamawa take Shiyasa tazo wajen tinda tasan da cewa akan kudi ba abinda su d’in bazasuyi ba. Sann basu san da mutuwar Auren Ummul d’in ba. Bayan sun gaisa Nan take sanar dasu Daddy har kawo wann ranan basu saka Ummulkhairi a idonsu ba. Sun bincika duk yanda ya kamata amma babu labarinta.
Haidar ya dubeta cikin shock “Khairy bata nan..? Toh ina take.?”
Tani ta sauk’e ajiyan zuciya “Duk yanda ya kamata mu bincika gidan ‘yanuwa da zuri’a mun bincika amma Babu labarinta. Tin a lokacin naso mu koma mu sanar daku halinda ake ciki amma mahaifiyarta tak’i hakan. Ta d’auki duk laifin ta aza ma kanta..A cewarta wann hukuncinta ne take karb’a.. Sannan har rana mai kaman wann Mahaifin Ummulkhairi dake cikin jinya baisan Aurenta ya mutu ba.. An dai sanar dashi tayi Aure a haka yana jinyar amma baisan da wann labarin ba dan jinyar tashi abu ne da ya danganci zuciya. Likitoci suna bada shawarin ba komai za’a sanar dashi kai tsaye ba duba da irin yanayin jinyar. Sann baisan da cewa mu kanmu bamu san yanda Ummulkhairi take ba.”
Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban Daddy “This is all my fault Daddy.. Duka laifina ne.. Daddy idan na rasa Khairy.. Bansan ya zanyi ba..” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa.
Daddy bai kaiga furta kalma ba Azeema ta fito da murmushi saman fuskarta. Kai tsaye ta furta “Bazaka rasa ‘Yaruwata ba Sirkinmu Dangayu. Domin kudin kuna son junanku.. Naga haka a k’wayan idonku.. ‘Yaruwata..” Bata kai aya ba Khulsum ta fito da sauri dan dama tin baya dawowar su Umma daga Abuja suka d’auko Khulsum da Abba daga gidan Inna Dije. Tani ta kuma d’inke bakin Inna Dije da fad’in idan taji fit wani abu ya fita daga bakinta ya karad’e dangi gameda Auren Ummul toh ta tabbata itama nata Auren ya Mutu kenan sann itada D’anuwanta Malam Isubu har abada.
Khulsum ta girgiza kai tana duban Azeema “Kiyi shiru Azeema..”
Duk sai suka maida dubansu ga Khulsum da Azeema.
Azeema tace “Khulsum ki k’yaleni na sanar dasu.. Baki gani ne Yayanmu naso ya maida matarsa.. Meyasa bazaki bari a sanar dasu ba..”
Khulsum na huci tace “Sabida ‘Yaruwata tace bata so a sanar dashi.. Sabida ita d’in bazata tab’a komawa gareshi ba.” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.
Haidar da baisan tuni ya mik’e tsaye ba ya isa gaban Khulsum yana girgiza kai “Kinsan yanda Khairy take..? Tell me, where is she.. Where can I find her.?”
Ta dubesa sai ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye.
Haidar ya kuma jefo mata tambaya “Please tell me, kinsan yanda take..? Ina take.. Dan Allah ki sanar dani..”
Azeema tace “Bazata sanar dakai ba. Dan nima bata sanar Dani ba.. Kaf gidan nan babu Wanda ta sanar dashi. Nima abinda yasa naji tana waya ne na lab’e na saurara nan naji da Addarmu Ummulkhairi take waya.”
Mama Tani ta mik’e tana duban Khulsum “Ke Khulsumu meke faruwa..? Yanzu dik irin d’aga hankalin nan da kikaga munyi munata neman Ummulkhairi dama kinsan yanda take.. Shine kika kyalemu cikin duhu.. Muna nan muna tunanin Har yanzu fushi kike da ita Shiyasa baki tada hankali wajen neman ina take ba Ashe kina sane..”
Kuka Khulsum take tana girgiza kai “ ‘Yaruwata bata sanar Dani yanda take ba.. Amma nayi waya da ita kuma ta sanar dani cewa tana nan lafiya kar na damu ta kuma tambayeni jikin Abba.. Sann tace na kula da Umma kuma na nemar mata yafiyar Umma.. Sann..” Sai ta dubi Haidar da yai mutuwar tsaye yana dubanta, taci gaba “Sann tace ko ka zo nemanta kar na sanar dakai cewa munyi waya.. Dan har abada bataso ta sake ganin ko mai kamanninka..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.
Cikin wane irin yanayi Haidar ke furta “No please.. Don’t do this.. Please tell me.. Tell me idan ta sanar dake yanda take.. Ko kuma.. Ina layin da ta kiraki dashi..” Duk a daburce yake.
Khulsum ta girgiza kai “Ta rufe lamban bai fito ba..”
Ya lumshe idanunsa yana dafe kai “No.. There has to be something.. Just think please.. Or maybe we can try to retrieve all the calls from your line.. And see if we can track the number..”
Ganin duk ya daburce yana neman ficewa hayyacinsa yasa Daddy d’an yin gyaran murya yace “Haidar, taho nan ka zauna.. Abi komai a sannu..” Ya dubi Khulsum yace “ ‘Yanmata jeki abinki ko.” Khulsum ta risina ta tana mai jinjina kanta kafin ta shige tana share ragowar hawayen da suka zubo mata. Azeema na take mata baya.
Tani ma ta dawo mazauninta ta zauna.
Daddy ya dubi Haidar yai gyaran murya “Haidar ina so ka natsu ka kuma natsa zuciyarka. Yanada kyau mubi komai cikin lumana dan tada hankali bazai tab’a kawo mana maslaha ba. Idan har Ummulkhair tana cikin k’oshin lafiya wann ma abun mu gode ma Allah ne. Kuskure ne an riga anyi shi dama kuma shi gyara sai a hankali.”
Tani ta jinjina kai “Wann gaskiya ne.”
Daddy ya kuma jinjina kai kafin yace “Amma yaya jikin Maigidan..? Yana asibiti ne Har yanzu kokuwa..? Mai likitoci suka ce gameda rashin lafiyar nasa.?”
Tani ta dan gyara mayafinta “Toh jiki Alhamdulillah zamu ce. Sann asibiti kuma sai jikin ya d’anyi tsanani ake zuwa.. Yana nan a gida. Saidai maganar ne ba sosai ba.. Amma yakan fahimci wasu abubuwan.. Rahotannin asibitin nasa duk yana wajen d’iyarsa Khulsumu dan kusan tareda ita akai jinyar nasa gaba d’aya. Ba abinda zamuce ma yarinyar saidai Allah shi mata albarka.”
Daddy ya jinjina Kai yana fatan lafiya ga Abban kana ya mik’e yace “Ko zamu iya ganin shi.?”
Tani ta jinjina kai “Eh yana d’aki yana kwance. Mu k’arasa. Bismillanku..” Tai gaba Daddy da Haidar na biye da ita suka nufi wata ‘Yar k’aramar k’ofa da zai sadaka da d’akin Abba.
Suka d’an tsaya daga waje kafin Tani ta shiga ta tadda Umma ciki nan take sanar da Umma su Haidar da mahaifinsa zasu shigo su gaida Abba dama tuni Tani d’in ta sanar da ita zuwansu.
Umma ta gyara zamanta ta dan gyara Abba ma kafin ta rufe kanta da mayafi, Har rabin fuskarta saida ta rufe sabida surkunta.
Tani Tai masu iso. Daddy ya soma d’an rage tsawonsa ya shige d’akin Haidar na biye dashi.
Suka gaisa da Umma suka tambayi mai jiki kafin Tani ta d’an matso kusan Abba tana sanar dashi ga Surkin Ummul da mai gidanta zasu gaishe shi.
Allah sarki Abba sai ya soma k’ok’arin mik’ewa jin an ambaci Maigidan Ummul d’insa da surkinta. Daddy yai saurin taimaka masa yana masa sannu da jiki dukda muryar Abban ba wani sosai yake fita ba.
Bayan sun gaisa da Daddy sai ya fice amsa wayarsa dake ruri.
Cikin muryarsa da bai fita sosai irinta majinyaci mai Jin jiki Abba yace “Ina Maigidan Ummulkhairina.?”
Haidar ya k’araso cikeda risinawa yana gaida Abba zuciyarsa ya kuma cika da tausayin Khairy da ahalinta. Sai Abba ya soma k’ok’arin d’ago hannu yana mik’a ma Haidar alamun yana so suyi masabaha. Haidar yai saurin tallafo hannun Abban ya rik’e cikin nasa suka gaisa. Sai yaji Abba ya rik’e hannunsa gam yana fad’i da kyar “Kaine Aliyu mijin Ummulkhairi na..?”
Sai Haidar ya jinjina kai a hankali “Eh.. Eh Abba ni ne..”
Abba yaci gaba “Ina matuk’ar son ‘Yata Ummulkhairi, tanada zuciya mai kyau.. Ka rik’e mun.. Ita da amana kaji koh..”
Dukda tausayin Abba had’ida wani abu mai kama da rauni da Haidar keji yana taso masa tin daga can k’asar zuciyarsa bai hanasa jinjina Kai cikin sauri, ya soma furtawa cikeda k’warin gwiwa “In sha Allah Abba.. Zan rik’eta… Zan rik’e Khairy amana.. Na maka alk’awari.!”
Abba ya murmusa had’ida jinjina kai sai kuma yace “Ina Ummulkhairi.. Maiyasa bata biyoka ba..? Na jima ban ganta ba. Ina kewar.. ‘Yata sosai.”
A nan ne kuma jikkunansu gaba d’aya yayi sanyi. Babu ya Haidar Wanda ya gama d’aukar ma majinyacin mutumin alk’awarin kular masa da ‘yarsa wacce baisan ina take ba.
Sai Tani Tai karaf tace “Ai.. ai laulayi take… K’aramin juna gareta shiyasa bata samu zuwa ba.” Ita kanta Tani da tai maganar saida taji banbarak’wai. Yayinda Umma tai saurin dubanta da idanunta masu cikeda rauni. Shi kaw Haidar sai ya sadda kansa kad’an.
A haka dai Har suka fito zasu tafi. Baffanin Ummul guda biyu da suka amshi kud’ad’e hannun Asshe suka bada Auren Ummul d’in nan suka jeru suna jiran fitowar su Haidar ganin hamshak’iyar motar da ke k’ofar gidan nasu. Sai jinjina lamarin suke suna fad’in albarkacin bakinsu gameda mijin Ummulkhairi da mahaifinsa Wanda Tani ta hana su gana dasu a cewarsu.
Ai ko suna ganin fitowar su Haidar suka k’arasa kaman zasu kwanta suna mik’o ma Daddy hannu alamun musabaha. Daddy da Haidar suka tsaya suna gaisawa da mutanen cikeda girmamawa. Nan sukai introducing kawunansu matsayin K’annen Mahaifin Ummulkhairi kuma Wanda suka bada Auren ita Ummulkhairin. Nan suka sake sabon gaisuwa na musamman suka kuma cikasu da goma na arziki daga Daddy har Haidar din babu wanda aka bari baya. Kowa kokari yake yayi alkhairi daga aljihunsa. Alkhairin da ya bar su Baffah Ado cikin tsananin al’ajabi. An masu kyautan ban girma sai kawai suka fara wasa Ummulkhairi cikin gidan suna cewa ta kawo alkhairi. Wacce a baya suka kyamaceta da k’addararta Har cewa suke tana bata sunan zuri’a da muguwar bak’ar k’addararta yau sai gasu nan suna rigen kiranta jininsu. Rabon da su shiga sashen su Ummul su duba D’anuwansu tinda Abba da Khulsum suka dawo daga Jigawa can gidan Inna Dije. Yau sai gasu nan tsamo tsamo suna kiran Abba Yayansu. Tani kaw ta masu d’add’aya tana fad’in maza aci arziki. Ummulkhair da suke ambato da Ummulsharri a baya yau sai gashi suna k’aryata harsunansu dan cewa suke ta amsa sunanta Uwar alkhairi.
**
Bayan Haidar ya kai Daddy masauk’i nan suke tattaunawa da Daddyn gameda ciwon Abba. Daddy yace “Inaga ko zakaje Asibitin ku tattauna da Likitocinsa na nan. Sai a duba hospital report din nashi kaji shawarwarinsu.. Idan yaso ko can Abuja ko dan ta kama a fitar dashi abroad ne sai su sanar dakai.”
Haidar ya jinjina Kai “Ina da wann plan din Daddy.. Hospital din da na kwanta lokacin da na samu had’arin mota is a prestigious hospital, sunada likitoci k’wararru daga k’asashe da dama sunada advanced technology.. In fact is a foreign hospital.. Because a yanda naga jikinsa ba Lallai Likitoci su bamu shawarin a fita dashi kai tsaye matuk’a akwai solution a nan.. Duba da process din da za’a bi. Dan Ga dukkan alamu yana jin jiki sosai. Amma zan tuntub’i Likitocin nasa kaman yanda kace.”
Daddy ya jinjina kai “Good.. Yayi kyau.. Toh ai inaga ni zan bi jirgin yamma na koma. Zan turo Sadis (Daya daga cikin trustees d’in Daddy ne a wajen aiki) sai ya tayaka ku kula da al’amran.”
Haidar ya dan murmusa yana risinawa “A’a Daddy da ka barshi. Zan kula da komai by myself.. Financially da dik wani abinda ya kamata.”
Murmusawa Daddy ya d’anyi yana jin dad’in yanda D’an nasa ya zama responsible. Sai yace “Even so, Sadis zaizo ya tayaka da wani abin. Jirgin yamma nake son bi.” Ya k’ara maimaita ma Haidar d’in.
Sai Haidar yai saurin jinjina kai “I’ll call the airport right away” Ya fad’i yana mai ficewa. Daddy ya jinjina masa kai.
Haidar bai bar garin ba saida ya tabbata an shirya duk wani abinda ya kamata gameda tafiyan Abba zuwa prestigious hospital din da za’ai treating d’insa. Umma tace fir saidai Mama Tani ta tafi tareda Abba ita zata zauna da yaran. Haidar ya musu goma na arziki dukda cewa da Umma take ya daina d’awainiyar nan musamman idan ta tuna abinda ke faruwa na rashin Ummul. A cikin zuciyar Haidar kaw cewa yake baiyi rabin abinda Khairy ta musu shida ahalinsa ba. Cikin zuciyarsa yana kewarta sosai.. A koda Yaushe k’aunarta k’aruwa masa yake.
Kafin ya bar garin da yamma yana zaune saman tabarma a haraban gidan dan tuni ya zama D’an gida. Azeema sai zuba masa surutu take ta d’auko wani tsohon album d’in Abba tana nuna masa hotunan Ummulkhairi harda Wanda take sanye da uniform na makaranta. Ya jima yana kallon hoton. Sihirtaccen murmushi saman fuskarsa.
Azeema taci gaba da basa labarin k’uruciyarsu Har ta gangaro kan samarukan Ummul da ake saka musu rana a fasa. Har kan Zubairu da su Alhaji Kamilu da yanda kowa ya zata Zubairu zata aura sabida yanda Zubair d’in yaso Ummul. A nan ne fah sukaga Haidar ya had’e rai tamau. Badia sai mintsilin Azeema take tana fad’in Tai shiru haka nan amma inaa Azeema sai zuba take yawa kurna.
Mama Tani ta kawo masa abinci tana fad’in su Azeema su kyalesa haka nan yaci abinci.
Azeema ta dubeta ta dubi tuwon. Tuwon gero ne da miyar yauk’i.
“Haba Mama ya zaki bashi irin wann abincin. Na tabbata bai ma tab’a gani ba.”
Haidar kam ma iya cewa baima abindake faruwa ba. Dan tinda Azeema tai mentioning Zubair tsohon saurayin Ummul ya rasa sukuni.. Sai ya dan dubi Azeema ya girgiza Kai kad’an yace “Amma ina Zubair yanzu.. Yayi Aure.?”
Azeema ta saka ma bakinta sakata tana Zare ido. Badia ta rankwafo had’ida rankwashin Azeemar kad’an ta rad’a mata “Kin gani koh. Ke baki san kishi irin na maza bane kinzo kina labarin tsaffin samarukan Ummul. Yanzu gashi kinsa mutumin na miki wasu tambayoyi. Haba Azeema mutumin nan fah ji yake kaman Ummul ta kufce masa kenan tinda sun rabu.. Idan baki basa k’warin gwiwa ba bazaki basa dalilin rura wutan tashin hankalinsa ba.”
Azeema tai murmushin da yafi Kama da yak’e ta dubi Haidar tace “Wann ai tsohon labari nake sanar dakai Yayanmu. Zubairu ya jima da auren ‘Yaruwarsa wacce ake so a had’asu tuntuni..” Ta shiga tura foodflaks din abincin da aka kawo masa tana fad’in “Kaci abincinka Sirkinmu. Tuwon nan idan yai sanyi babu dad’i.”
Badia ta harareta tana girgiza Kai ta janyo Azeema suka bar wajen tana rad’a mata “Kedai wacce tai jegonki bata farse wann bakin naki ba.”
Azeema ta kuma kame bakin ta tana fad’in “Wllhi na sani… Duk yanda akai Inna Dije ce.” Suka dara a tare Badia tana fad’in Allah ya shiryi Azeema.
*
Kafin ya tafi saida ya k’ara tuntuban Khulsum ko ta sake samun kira daga Ummul. Khulsum tace bata sake kiranta ba. Su kansu saida Haidar ya basu tausayi. K’arshe haka ya hak’ura ya bar garin ba don yaso ba.
**
Idanunsa na duban window yake ci gaba da fad’in “It’s been three months Hisham. Wata uku babu Khairy.. And Dareen is nowhere to be found. I feel lost, tiny and insignificant in this world..”
Hisham ya sauk’e ajiyan zuciya “I believe everything happened for a reason.” Ya dan furzar da huci had’ida girgiza Kai “I have never met your wife Haidar.. Amma abinda na kula shine kana k’aunarta sosai, because ban tab’a ganinka cikin yanayi na soyayya irin haka ba..” Ya dan numfasa “Kuma koda ka kasance mutum da bai cika bud’e al’amransa ba jikina yana bani ba k’aramin abu bane ya shiga tsakaninku.”
Sai Haidar ya dubesa amma baice komai ba.
Hisham ya jinjina Kai kad’an “Whatever is the case Haidar, know that I’m here for you.. And you can always count on my support.” Ya jinjina Kai alamun tabbatarwa. “Idan zakaje kaci gaba da Neman matarka ni zance naci gaba da nemar maka Dareen. Ko ba don ka hukunta Dareen ba sai dan D’anka dake cikinta. Ko ya kayi Haidar, that child she’s carrying is still yours.. Kuma baida laifin komai.. Bazaka hukunta shi da laifin mahaifyarsa ba.”
Haidar ya tsaresa sosai da ido wann karon sai ya girgiza Kai yace “Are you even sure that child is mine.?” Shiru Hisham bai amsa shi ba saima tunani da ya soma cikin zuciyarsa ‘Bastard! Zaka sheganta wann D’an kaman yanda Ubanka ya shegantani a ciki.! Kai din baka rage ma Ubanka komai ba Haidar.’
Hisham ya sinkayo muryar Haidar sanda yaci gaba “Wha if babu wani ciki. What if k’arya take, tinda iyakacin tarayyata da ita k’arya ne kawai.!”
Hisham ya dan furzar da huci yana mai d’aga gira sama “Bazan k’i maka ba. Kuma bazanga laifinka ba.. Because you’ve been fooled and betrayed. Amma Kai tunani Haidar.. Kayi rayuwa na Aure da Dareen koda ace rayuwar ta k’arya ce. You were once husband and wife.. You cannot deny that. So ba abin mamaki bane idan tana d’auke da gudan jininka.. I mean, if you neglect that child zai tashi ne da tsanar koma waye mahaifinsa.. Meyasa ‘ya’ya zasu biya kuskuren da iyayensu suka aikata..? Hakan ba adalci bane.” Yanda yake maganar tamkar yana digging ma Haidar past d’insa ne.
Hisham yaci gaba “You can’t let that child pay the price Haidar.. You know exactly how it feels mutum ya girma babu soyayyan iyayensa. You can’t make that child a victim. You can’t let that happen to your own child.!” Ya k’arashe cikin tsananin k’warewa tareda tono ma Haidar bayansa. Yanda ya girma da tunanin iyayensa basa sonsa duk sabida wani kuskure da mahaifyarsa ta aikata. Ya rintse idanunsa yana jin kamar dai duniyar ta dad’a juye masa. Sann gaskiya ne abinda Hisham ke fad’i. Because shi Kansa Haidar d’in was once a victim. Bazai bari tarihi ya maimaita Kansa cikin ahalinsa ba.
Hisham ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kai da ahalinka bakuda daman yin wani farin ciki a wann rayuwar. A lissafi Ummul ta cika watanni uku tin bayan da k’addararren Aurenku ya k’are.. Hakan na nufin ta fice daga iddarka.. Ni kuma yanzu zan tafi na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta…All my sacrifices are finally going to pay off’ A fili k’arasawa yai ya dafa Haidar kad’an fuska fal damuwa. Cikeda kulawa yake furta “Haidar bazan Barka ka koma irin rayuwar k’uncin da ka fuskanta a baya ba. Ka tafi ka nemo matarka yanda ta shiga ta fita.. Ni kuma zan tafi na nemo maka Dareen yanda ta shiga ta fita ko dan wann innocent soul d’in dake cikinta.” Ya k’arashe damuwa sosai saman fuskarsa.
Haidar bai iya ce masa komai ba sai shafe fuskarsa da yai da tafukan hannayensa.
A haka Hisham ya tattari files d’in da ya shigo dasu ya fice fuskarsa d’aukeda mugun murmushin da ba kowa ke iya fahimta ba. Cikin zuciyarsa yaci gaba da ayyana Ummul tasa ce a halin yanzu.
Da wann farin cikin Hisham ya taho garin Bauchi zuciyarsa fari k’al da nufin ya tafi Neman Dareen a zahiri kuma wajen Ummul yazo da niyyan k’ulla soyayyarsa.
Babu Wanda yasan da zuwan nasa. Hajja batai mamaki ba dan dama ya saba mata irin wann zuwan na bazata. Saidai ta kula wann karon da wani irin farin ciki yazo maras misaltuwa.
Suna cikin gaisawa da Hajja yake tanbayarta “Hajja nace ina Ummul kuwa..?”
Bata kaiga basa amsa ba suka hango Ummul da fitowarta kenan daga babban parlorn da Hajja ke sana’arta na d’inki, nan suka hangota tana tafiya da kyar tana dafe garu tana kame kanta dake matuk’ar juya mata.. Kafin suyi wani aune jiri ya kusan kaita k’asa. Hajja ta nufeta hankali tashe ta tallafota tana ambaton sunanta dan tuni idanunta sun soma juyawa.
SameenaAleeyou📚
