Abu Cikin Duhu page 1 - 15

Abu Cikin Duhu page 1 - 15

 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅


1️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA


BISSIMILLAHI RAHAMSNIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI INA GODIYA GA ALLAH DAYA BAN DAMAN FARA WANAN LITTAFIN,  UBAGIJI INA ROKON KA YADDA MUKA FARA A SA,A MU KARASA SHI CIKIN FARIN CIKI DA JIN DADIN JUNAN MU.

    YAN UWA MASOYANA HAR KULLUN INA MAI KARA BAKU HAKKURI DA KUYI HAKKURI DA ZAMAN TARE ZOMU ZAUNA ZOMU SABA DA FATAN ZAMU FAHINCI JUNA DAKU DON SAI KUN KARA HAKKURI DANI SAMA DA FARKO A YANZU KASANCEWA ZAN HADA TAURA BIYU A BAKI LOKACI GUDA.

   BADON KOWA BA NAI HAKA DON KUNE MASOYA NA MASU KAUNATA A KULLUN FARIN CIKIN KU SHINE NAMU DON DA BAZAN KU MUKE RAWA A KODA YAUSHE.

   FADA KARWAN DAKE CIKIN LABARIN NAN UBANGIJI YASA MU AN FANA DASHI AKAN MU DA YAYAYEN MU ALLAHUMA AMIN.

    DARI UKUNE HAR YANZU BAN KARA BA IDAN KINA SO SAI KU TUNTUBENI A LAYINA DON HAR YANZU DASHI NAKE AMFANI BUT ONLY TEXT DON DA WUYA KIRA YA SHIGO MIN A NAN YANZU.

  2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MTN KO EIRTEL NAGODE ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMOMIN SHI AMIN.


A hankali take saukowa daga matakalan jirgin jirgin mai tambarin Nigeria Air way daya sauka a filin jirgin malam Aminu kano.

    Fuskanta yana saye da bakin glass din ido sai takunkumin dake saye a fuskan nata bayan ta yan samari biyu ne masu tsanin kama suna mara mata baya.

   Doguwar rigace baka a jikin ta sai gyalen shi data yafe har zuwa kanta    takalman dake kafanta flat ne basu da wani tudu sosai .

    Sai handback din hannun ta data riko wanda ba wani babba bane sosai dan madaidaici dashi.

   Kallo daya zakai mata ka gane hamshakiyace ita din don siffan shigar da tayi kawai ya isa ya nunama hakan.

    Hjy Iyami ke nan matar tsohon Ambasardor din kasar America wanda ya wakilci Nigeria a 1986 zuwa 93 .

   A hankali ta runtse idanuwan ta kafin ta bude su ta kara kallon yanayin kasan nata na haihuwa wanda a yanzu ya zama mata abin kallo.

    Duk da dadewan da tayi bata a cikin kasan hakan bai hanata ganin wasu abubuwan da ta bari ba a tsawon shekarun data kwashe bata kasan.

    Da mamaki irin halin gwauntin kasan ta Nigeria a ranta taci gaba da saukowa a matakalan jirgin sannu a hankali duk da yanayin kasan nata hakan bai hanata son ganin ta dawo kasan ta na gado ta zauna tare da iyalan ta ba.

    Easy hajjajo daya daga cikin samarin dake bayan ta ya fada don ganin irin yadda take bin ko ina da kallon mamaki don rashin ganin wani cigaba da da kasan tayi  sosai a zuwa nan lokacin data dawo.

   Don tun bayan barin mijin ta aiki sai take can da iyalinta dake kararu inda itama take aiki da wani company a can hakan ne ya dauke mata hankali da gida sosai.

  Sai yanzu take ganin dacewan dawowa gidan a cikin yan uwa da abokan arzikin su da suka bari badon komai ba sai don tarbiyan yaran ta da jikokin ta dake tasowa yanzu.

  Saboda yawan haramtatacen al,adan da yanzu ya mamaye duniya sai take ganin namu tarbiyan na malam bahaushen kamar daban yake da sauran tarbiyan wasu al,umman na duniya a yanzu .

  Don shi malam bahaushe yana mayar da al,ada ya zama addini sosai a gareshi balle kuma abinda addini din ya koyar damu.

   Duk da lalacewan duniya a yanzu malam bahaushe yayi kokari wurin ingata wasu tarbiyan da su koma kamar addini a garshi wanda yake taimakon al,umma a yanzu.

    Hakan yasa ta yanke shawara ba tare da zaunawa ta shawarci kowa daga cikin a halin nata ba a yanzu da take shugaba a gidan ga baki daya.

    Ba karamin tashin hankali ta fuskanta ba a gurin yaya da jikokin ta don jin zancen komawa sun gida Nigeria da sukayi.

  Wanda hakan yasa ta rufe ido taciwa kowa daga cikin su mutumci kan umurni ta bayar ba rokon su takeyi ba.

    Hajiya Iyami bata fada ma kowa ba saida komai ya gama kammala daga banhareta a yadda take son komai yazo mata daidai idan sun dawo.

  Gama daga gyaran gida zuwa company da sauran abubuwan rayuwa ta rigada ta kammala komai yadda zai tafi mata idan sun zo ba tare da sun sha wahalan komai ba tunda akwai kudin su ta fitar aka aiwatar masu da komai yadda take bukatan shi.

    Har zuwa yanzu da Allah ya nufa sun tataro sun dawo Nigerian da zama inda duk tawagan nata suke ransu a bace don suna ganin ta rabosu da rayuwan inda suka saba dashi yanzu ta kwasosu zuwa kasan da duhun kai da jahilci yayi katutu a ko ina.

   Alhamdullahi a bangaren hjy don ta isa da kowa na ahalin nata daga mazan su har matan su babu mai iya musa mata ga bukatan nata idan ta fada.

    Haka yasa abin ya kara zuwa mata da sauki sosai don bata samu tangarada a kowan su ba sai gun babban danta koshi ta daga mai kafa saboda irin aikin shi ne a can don shi tun gama karatun shi yake zaune a kasan chaina inda yake aiki tare dasu.

    Ta yarda da imanin shi dari bisa dari don ta auna shi taga yana da riko da addinin shi yana kan tarbiyan da suka bashi tun farko.

   Wanan dalilin yasa ta yarda ta barshi a can inda yake aikin wanda a yanzu zamuce shine dauke da nauyin komai da kowa na ahalin don iya sarrafa na,uran computer daya iya da wasu fasahana zamani kasan na chaina ta dauke shi yake aiki tare dasu dama wasu company na kere keren zamani.

    Motocine a jere a da suka zo daukan su wanda duk gaba daya nasu ne da aka saye da sunanyen kowa a gidan.

    Baya bo ba fallasa fuskan hjy iyami a dan sake tana farin cikin ganin yan uwanta dana mijin ta da sukazo filin jirgin don tarbon su.

   Aka dan gagaisa a gurguje inda kowa ke son nuna kulawan shi a garesu kamar dai yadda akeyi ga kowani mai hali a cikin zuria, 

    Bayan shigar su motane inda sai a lokacin ta fata samun natsuwa a hankali ta runtse idanuwanta tana mai tuno da mijin ta marigayi Alh ma,azu ambasado.

  Wanda shine dalilin gatansu a yanzu har suka kai hakan ga Allah ya azurta yaran su da ma wasu dake zaune a karkashin inuwan su ta sanadiyar shi.

  Saidai ubangiji bai nufi yaga wanan baiwan ta yayan nasa ba a duniya don yanzu shekara kusan goma ke nan da Allah ya karbi rayuwan mijin nata.

    Duk da hakan suna zaune a can waje kamar yadda suke zaune tun farko da yake raye rasuwan shi bai sa sun dawo gida ba tun wanan lokacin saboda aikin ta dana yayan ta da sukeyi a can.

   Dan tafiya sukayi kasancew nisan kano da kaduna ba wani tazara mai tsawo bane sosai yasa basu kara wani wahala ba sosai.

   Duk hjy na cikin halin tunanen irin rayuwan da zasuyi a nan din yanzu cikin yan uwa da abokan arziki a haka suka shigo garin kadunan don ita bata ga wani nisan tafiyan da yaran nata keta faman jan tsukin nisan sa ba  .

    A nan ma sun samu dandazom yan uwa na kusa da suka cika gidan suna murna da zuwan wanan family din.

  Anci ansha an gagaisa tare da tambayan bayan rabo inda yaran nata da duk mazane sai autar ta da matar danta dayayi aure saidai bata yarda ya auri yar can ba yar nan cikin dagi ta aura mashi aka kai mata ita can suke zaune lafiya da ita don iya zama da sarakuwar nata da ta iya.

   Tun wanan ranan rayuwa ta koma masu sabo a gidan ga yan uwa na nisa da kusa dasuke zuwa taron su da murnan dawowan su gida lafiya.

    Dawowan ta kasan yasa ta dauko diyan yan uwa mijin ta mata biyu ta hada da yarta suke zaune a tare.

  Saidai asali ba itace ta dauko su ba sudin ne dai sukaga wurin zama suka zauna a gidan tare dasu.

   Hajiya bata nuna komai ba illa kara jan su a jikin da tayi suka zauna a tare da sai yar sister daya suka cike su hudu yan mata a gidan.

   Rayuwa na jin dadi da sakewa sukeyi don hjy iyami na tsaye da saka ido ga motsin kowa a gidan.

    Saidai ta fanin karatu da jin dadin rayuwa a cikin gida duk abinda suke so a ransu tana ganin ta kawar masu da shi don kawai kada su gani ga wani har su saka rai sukai ga dauko mata magana.

    Ta farko itace salma yar gurin kanin mijin nata dake kula da duk wani al,amarin su daya shafi gida don shi suke sakawa a gaba tankar maigidan nata yana raye don mutumin yana da fahinta dakuma biyayya daya dace.

    Sai Rufaida diyar autar su maigidan nata dake aure a jos a can suke zaune da mijin ta da yaranta Rufaidace yarta ta biyu itama dawowan hjy nan kasan .

   Daga zuwa da sunan hutu tun lokacin bata koma ba take zaune tare dasu don jin dadin irin rayuwan da ake a gidan.

   Sai ta uku jamila ke nan diyar autan su hjy da ita kanta hjy ta dauko ta don ta sahalewa yar uwan nata nauyin yaran da suke a gaban ta zata debe mata wani kewan itama a matsayinta na yar yar, uwan haihuta.

   Tankar yar cikin ta take ganin ta a wurin ta don hakan ta daukesu gaba dayan su tankar diyan data haifa a cikin ta suma ba laifi a nasu bangaren hakan suke kokarin nuna mata kamar yadda itama din take kokarin nuna masu duk daya suke a wurin ta.


     ANCAU


Tun a soron gidan nasu take jiyo muryan Asabe kakar su data haifi mahaufisun tana faman zazzaga bala,i.

 Dukda bata shiga gidan ba tasan bada kowa Asabe ke wanan fadan ba haka illa da mahaifiyar su.

  Don inda sabo aita saba da wanan hali na Asaben don tun bata da wayo da wanan hali ta bude idanuwanta a gidan.

    Kusan kullun fitinan Asabe ne ke tayar dasu daga barci na yau daban na gobe daban.

   Yau ma daga inda take take jiyo muryan Asaben tana fada akan iccen girki da innar tasu.

    A haka ta karasa ciki rai bace duk da gajiyan ranan data kwaso ga yunwa ga kishin ruwa don tun safe da ta fita bata karya ba .

  Hakan kuma ta juyo gida da kafa duk da nisan dake akwai daga makaranta zuwa gidan su.

   Shigowan Abu gidan bai hana Asabe fadin abinda take fadawa mahaifiyar tasu ba a lokacin.

    A daidai lokacin inna ke fadin adan maraice umma dama ba wani icce mai yawa bane dashi nayi koko da safe yanzu kuma na danyi muna danbun tsakin da akwai don yaran nan idan sun dawo su samu abinci.

    Duka bakin wutan baifi guda hudu da guntu indon ruwan dumine barin hada gawayin nan sai ruwan yayi dumi ki samu ki watsa din.

  Salman Abune yasa su juyowa gaba dayan su sai dai inna ce tayi karfin halin anwa a lokacin duk da tana cikin rudu da rikecewan bala,in Asaben.

   Asabe na fadin to sannu issasa mai diya ke kika san zafin diyan su kin iya kokarin nema masu abinda zasuci.

   Niko nawa dan dabai damu dani ba ai haka yasa kafa ya fita bai damu yasan da damuwata ba.

   Saukin abindai kema yaya matane a gaban ki,  kinkin zuciya duk da gorin da kike sha a gari ki haifa mashi ko da naji dayane da zai taimaka mai idan karfin shi ya kare yasan yana da magaji.

  Ke kenan kullun dauksn ciki kina zuba mai diya mata a gida yau ace kitso gobe kumshi sai ko na omo.

  Ta yaya zai samu ya aje kullun laluran su yana kara yawa gareshi kullun yana fita nema ba matai maki sai Allah.

  Da maza kika haifa ai zai sa ran zasu taimaka mai a wani gurin ga wanan data saka kanta wani karatun boko da baida amfani a gurin ya mace.

   Abu dake kallon ta da mamaki tana cire takalmin makarantar dake kafanta wanda duk ya sude a titi saboda rana da yawan bin hanya ga ba kudi balle a saya mata sabo dole haka take maneji dashi.

   Saukin abin ma yanzu duk da karancin shekarun ta amma haka ta samu don kokarin ta ba,a taba mayar da ita baya ba har takai aji shida tana neman fitane yanzu.

  Duk irin matsin da Asabe kewa mahaifi su akan karatun nasu baida wani rana garesu kasancewar su na yaya mata gareshi.

  Don a cewar ta aure zata masu da zaran Abu ta cika shekara goma sha biyar da haihuwa a duniya don ko yanzu wasu daga cikin sa,annin ta sun riga da sunyi aure suna gidajen mazan su zaune daram.

    Muryan Asabene ya dawo da ita ciki tunanen da takeyi tana fadin ke kuma munafuka ki kura mi ido kuru kuru kina kallona dasu.

  Don rashin kunya rashin tarbiyan da baku samu ba tun farko ga uwar ku babba na magana yara suna kashe shi da ido don rashin kunyan da kuka gada a wurin uwar ku.

  Karya nake fada ba gaskiya na fada ba komai ya samo yana gurin ku keda yan uwan ki da makiran uwar ku ku gaku ga bawa na haifar maku ko ?

  Ice ma da mutum zai saka ruwan dumi ace an kona shi a gidan nan gaba daya wanan wani irin masifane yaron nan ya haifar min a gidan nan.

  Baki na turo gaba don jin irin cin zarafin da kullun Asabe ke muna muda mahaifiyar mu har wata rana takan tsaya sai baba ya saki inna ko kuma ya kara auren macen da zata zo ta dinga haifa mai diya maza a gidan mu.

    Da kyat Abba da wasu makwabta sukan iya shawo kan Asabe idan ta fara wanan bambamin nata lokacin.

   Inna dai tana duke a bakin murhu tana kokarin  hura wuta da gawayi ne data dan kashe dazun sai faman fifita wutan take don ya kama.

   Daki na shiga na kwabe tufafin makaranta dake jikina don sanin bamu da clean din da zamu wanke a yau don gobe haka yasa na kwabe su na baza a dan gambun langa langan kwanon dake kofan dakin namu nafito.

   Wurin madafin namu na hara ina fadin inna kawo in hura kije ki huta hakana da ranan nasan tun safe baki huta ba.

    Barshi inna ta fada tana kokarin boye fuskanta gare ni don kada inga hawayen dake zubo mata a idanun ta a lokacin.

   Wanda nasan ba komai inna kewa hawaye ba sai gorin diya matan da Asabe ke mata don indan don fadan barana da Asabe ke fadin tanayi ne ta saba da wanan  sai dai wana gorin ne inna bata iya shayewa a ranta sai ta nuna gazawan ta anan.

    Da kyar inna ta yarda ta bani maficin tana fadin kije ki huta yar mairo dan inna bata kiran sunana kasancewata yar fari a garesu.

   Ina tsugune bakin murhun Abba ya shigo gidan da kayan aikin shi idannun shi ya sauka a kaina yake fadin yar mairo kece har kika shiga girki daga dawowan ki haka?

   Dagowa nayi daga inda nake ina fadin Abba sannu da zuwa na nufo shi don amsar ledan dake hannun shi.

    Bayan na karba na juya don zuwa dakin su in aje Asabe ta fito tana fadin to to mai zaki tura daki daga kawowa yar nema data gaji kilibibi a gurin uwarta.

   Kai haba umma ba komai bane a ciki sai dan     garin tuwo da kubewa ko za a samu a dan tuka da dare a samu naci .

  Don na fita dazun ban samu bada ko sisi ba a samu ko abin karyawa a gidan nan ina can na damu da tunane tun safe ina faman babu kwasta duk masu zuwa sai cewa suke ai masu bashi idan sun samu zasu kawo kudi.

   Kai Amma mutane sun lalace yanzu da son bashi facin ma shi kanshi bashi za ai masu shi kai Allah ya rabamu da fititinun duniyan nan .

   Sai lokacin Abba yakai kasa yana fadin barka da wuni umma mun wuni lafiya ya gidan kuma.

   Mun wuni lafiya ba lau ba dai tunda ko ruwan da zan dan samu in watsa a gidan nan ban kaiga samu ba har yanzu.

   Don kawai nace bazan iya wanka da farar safiya ba sai kawai a hana min ruwan ina kallo wanan matar taka ta hura wuta a gidan nan har ta gama abinda take saida taga icen ya kone ga baki daya .

  Amma yarinyar nan ta kasa saka min ruwan dumi in watsa don bakin ciki da rashin sanin muhinmancina a gidan nan.

  Daga inda Abba yake tsaye yana jin Asabe takai ayah yace kiyi hakkuri umma .

    Kin sa halin da nake ciki yanzu aikin ne nawa babu kasuwa ko ina ya rufe yau kwana uku sai ita saudatune ke dan dabara a cikin aljihun ta muna samu muna dan tabawa.

  Asabe tace da mamaki karara a fuskan ta take fadin haka ka koma ban sani ba dan nan ?

   Kai bakaji kunyar fadin wai ashe mace ke ciyar damu duk kwanakin nan a gidan nan ba.

  Mafarin abin gari ana yadamu da fadin talaucin mu yakai haka har mace ce take ciyar damu a gidan nan kai ka kasa.

    Kaga amfanin haihuwan da namijin da nake fadama ke nan da yanzu yarinyar nan namiji ne aida ta fara taimaka maka ta wani gurin.

   Inna ta fito dakin ta nufi wurin madafin danbun tsakin masaran data hadane ta shiga rabawa yayin da tsakar gidan namu yayi shiru kowa ya zuba idanu yana kallon inna.

    Na Asabe ta fara zubawa ta mike ta nufo ta tana fadin umma akai dakine ko a kawo maki nan aje anan in gani Asabe ta fada a hasale.

  Saida Inna  ta kai kasa don girmamawa ta aje kwano a gaban ta inda take zaune saman kujera dan tsugunno.

  Bude kwanon samiran tayi tare da juya dan danbun dake cikin kwanon a yatsune tana tabe baki kafinta dago kai tana fadin.

   Saudatu wanan abincin fa kamar za,aba dan goye shi ta juya wurin Abba tana fadin ka duba dai ka gani da idanuwan ka yanzu dan abinda aka zubamin.

  Don kawai kace itace ke ciyar damu a gidan yanzu  ai dole wullakanci ya shigo a bani abinda akaga dama don kawai rainin da kaja muna don kasawan ka yanzu da gidan.

   Umma ba hakana bane kiyi hakkuri tsakin ne baida yawa iyakarshi ke nan dan gyara don yaran nan dake.

  Nasan nida malam ba samu zamuyi bama a karshe tace duk da haka a kara min don wanan dai ba isane zaiyi ba ehhe.

   Kallin Asabe nayi lokacin da naji ta fadi hakan ina mamaki hali rashin tausayi irin nata duk da jin zancen inna din da tayi.

  Dakuwa ta jefo min da hannun tana hagu tana fadin daina kallo na yan nema mai kama da yanyawa.


ZAINAB  IDRIS MAKAWA

🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅


2️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


   

Ki daure ki guji shiga hakkin wani abinda ka raina shike zama babba gareka don Allah yar uwa mu guji daukan hakkin a kan mu ki daure ki biya ki karanta don Allah.

   Hjy ce zaune a falon ta hannun ta rike da waya kaya take oder da za, a turo masu dan yanzu ba sai ka fita zuwa waje ba idan kasa hutar da kanka waya ya wadatar da komai ga kowa.

    Sallaman da akayi daga kofane ya dawo da ita cikin hankalinta ta dago kai tana kallon kofan shigowa falon nasu.

   Da fara,a a fuskanta tana aje wayan daga gefen kujera take fadin kune tafe sannun ku da zuwa a cikin fara,a kamaf yadda ta saba tarbon duk wani dan uwa da zaizo gidan musanman daga bangareta kona mijin ta .

   Yanzu ma yan uwan mijin tane su biyu sula shigo gidan barin abinda takeyi tayi ta tari bakin nata.

    Yau kan mun taki sa,a kina waje don zuwan mu biyu ana fada muna kina ciki bazamu ganki ba.

    A daidai lokacin ta sauke glass din dake idon ta tana fadin abako fada min zuwan ku ba gidan nan ko sau daya.

    Dayan tace yau dai aimun taka sa,a mun samu kina wajen dan dariya hjy iyami ta sakeyi tana fadin mun dade bamu haduba.

   Safiya ya bayan rabo wace ta kira da safiya tace wallahi haka al,amari yakan kasance ai rayuwa ke nan idan na tuna baya sai nakanji kamar abubuwan da su dawo sabo.

    Dariya sosai hjy iyami ta sake tare da fadin kin tuna zamanin kurciya ke nan dai ga wanan zancen naki.

    Safiya ta lumshe ido tana bin lafiyan kujera sanyin AC yana ratsa jikin ta a hankali tare da fadin bari matar yaya ai kowa tuna bara baiji dadin bana bane.

    Jin hakan hjy ta fahinci mai take nufi yasa tayi saurin kawar da zancen tana fadin bari a kawo muna abinci muci nima yanzu na dawo gidan .

   Yau na fita ziyarane har gidan su Ado da salihu nake don tun zuwa na garin ban leka kowa ba bako dadi mutum yana kulaka kai baka mayar da kara akace.

   Tana fadin hakan ta mayar da hankali kan wayanta dake gefe dauka tayi ta kira mai aiki tare da umartan a kawo masu abinci tana da baki a falo.

    Kai matar yaya wai wasu baki har yanzu dai wanan halin naki yana nan ashe ance idan kasan mutum ko shekara nawa ne kada ka tambayi halin sa.

    Murmushi hjy tayi tana fadin meye duniya sa,ade wanan duniyan har nawa yake ga bawan sa.

   Idan badon muzo mun gani da idanun mu bazamu taba yarda da kina nan a yadda kike ba a yanzu.

    Wai sa,ade ina da wa yanda sukafi min kune a rayuwa duk mace mai hankali da tasan ya kamata ai baki nata ba ko yaya yake kuwa.

    Don samun duniya sai idon ka ya rufe ka mata da goben ka ko makomar yayan ka yau fa in mune gobe bamu bane.

  Wani lokacin koda kana raye sai kaga anayi ba tare da kai haka abubuwan suke zuwa ai kinga gara mutum ya gyara tun duniya bata kisa ba.

    Mai aikin data kirane ta shigo dakin dauke da katon ture da manyan kuloli abinci saman shi dining ta nufa da zuman jerawa yadda ta saba.

  Sai hjy iyami take fadin ki kawo muna nan yau a kasa zamu zauna muci dan dariya suka kwasa tare da fadin za a tuna da baya ke nan dai.

     Lokacin da yaya yake aiki lagos muna gida tare dake ake zuba abinci a cikin katon ture mu taru munaci ana hiran arziki.

   Ai wanan abin duk shigowan sadiya ya kawar muna dashi tana fadin wai muna taruwa ana gulmanta bazan manta da zuwan wanan yar uwan hjyn mu datazo daga kauye take fadin kema ai saiki fito ayi gulman dake.

  Budan bakin sadiya sai cewa tayi ni ba zan shiga cikin su rainani ba ko ita wanan don diyan tallakawane ita bata san kanta ba.

   Dan murmushi hjy iyami ta sake don tuna wanan labarin da safiya ke fadi yanzu sa,ade tace yau ina arzikin nata dana gidan su datake tun kaho dashi din.

   Duniya ke nan alokacin tana dauka tafi kowa da komai bata san me gobe zai iya haifa ba a gare ta.

   Hjy ce ke fadin bissimilah ku muci abinci   ko juyowa sukayi a lokaci guda suna kallo abincin da mai aiki ta hada masu gwanin ban sha,awa kai kace wani dinner aka hada hakan .

  Haka kamshin shi abin sone ga mutum balle ya kai ga baki yaji dandanon shi.

  Daidai hjy na zama a kasan take fadin ance yanzu koyarwa kikeyi safiya ke kuma sa,ade nursece asibiti ?

    Ashe kina da labarin mu ke nan har yanzu tana daukan cokali take fadin haba aiba zan taba mantawa da kuba a rayuwana .

    Adaidai lokacin data fara bude kulan tana mika masu plate a gaban su da spoon da fork ga kofuna da lemoka don sha aka tabardar masu.

   Nan kowa ya shiga dirkawa cikin sa abinci suna danci suna taba hira yayin da sanyin AC ya fara ratsa jikin su.

   Sai da anty safiya ta hadiye naman da take tauna a bakin ta na kaza take fadin a gaskiya mun gode daz bamu lokacin ki   da nuna rashin kyama ko babbanci a garemu yadda ake nuna muna har yanzu a gidan mu.

  An mayar damu bare a cikin dangi duk kokarin da baba yayi yaga ya hada kan zurian shi kafin ya bar duniyan nan .

  Zan iya cewa daga ke sai mijin kine baku nuna muna wani bambanci a tsakanin sabanin sauran dake yawan nuna mu barene a cikin su ko yaushe wani abu idan ya taso na family din mu.

    Din kawai mu uwarmu kadai ta haifa a cikin su lokacin da yaya ke raye yana iya kokarin shi damu amma tun bayan rasuwan yaya din abubuwa suka kara lalace muna ga baki daya.

   Wani abin saidai mu tsunci labarin faruwan shi a gare bamuci arzikin da za,a fada muna ba mu.

   A hsnkali ta lumshe idanuwan ta tana maijin zafin yadda ake yawan nuna masu a cikin yan uwan su din.

   Tace ku dauka har yanzu ma yayan ku yana a raye ne safiya don ya barni ya bar zurian shi komai ke damun ku kofa a bude yake dakuzo da bukatan ku nan mudin dai abin baifi karfina ba agidan nan.

    Sallama yan matan hjy ne da suka dawo daga school saida su ukune kawai don farida yar wurin hjy ba a kaduna take karatun taba tun dawowan su suka sama bata gurbin karatu Abuja can take zaune tana karatun ta.

  Sai hutu take dawowa gidan haka yasa idan ba hutu akeyi ba zaka gansu su uku ne kawai a gidan.

   Kansu a sama suka gaidasu kamar basu sheda ko suwaye su din ba garesu don kawai raina masu arziki da sukeyi.

    Safiyace take fadin wai ba Rufaida bace da salma nan dan juyowa salma tana fadin nice daga haka tasa kai tana kokarin shigewa daki.

    Rufaida salma kuzo nan hjy ta fada a kausashe saiga su sun dawo da sauri suna fadin gamu mommy ta nuna su safiya da hannu tana fadin baku san wa yan nan bane halan ?

   Mun sansu mama gwaggo safiyace da gwaggo sa,a salma ta fada a dan yatsune kafin hjy tace duk da kun san su saidai kamar baku san yaya suke da mahaifan ku bako ?

   Nan kan shiru sukayi suna kokarin dukar da kawunan su kasa don sun fahinci mai hjy take nufi da fadan hakan.

   Karna kara ganin kunyiwa wani babba wanan gaisuwan koda basu din bane wai salma sai yaushe zaku gyara halin kune don Allah ta fada a dan hasale .

   We sorry mommy gajiyace dama ya hana mu tsaya dan Allah ku ban guri marasa ta ido kawai ta fada a dan hasale.

    Bayan shigewar su dakunan sune anty safiya ta sauke ajiyan zuciya tana fadin kindai gani yanzu ke nan ai.

  Wanan ba akidar kwarai bane ka nunawa yaro ga yadda kake da dan uwanka har abin yazo ya shafi naku yayan nan gaba.

    Mikewa sa,ade tayi tana fadin antyce ma dai ta damu da wa yan nan mutane,  nina dade da zubar da duk wani wanda ya nuna baison wata alaka zumunci dani ai.

    Zancen ta baiwa hjy dadi ba ta fahinci akwai bacin rai a cikin halaiyan da yan uwa ke nuna masu kasancewar su su biyun yan uba ga yan uwan haihuwan nasu.

    Sallama sukaiwa hjy tare da mata godiya da nuna jin dadin su irin taron data nuna masu din bata nuna masu halin da yan uwa suke nuna masu a cikin su.

   Ita kanta bata samu mahaifiyar su a gidan raye ba saidai ga yadda take jin labari zamane akayi bana dadi ba a cikin gidan lokacin da mahaifan su suke a raye wanda itama ta dan ga wani abu a rayuwan datayi dasu gidan kafin Allah ya azurta mata mijin ta harsu bar gidan zuwa lagos karshe ma suka bar kasan ga baki daya.

  Lokacin ita kanta sarakuwanta tana yawan nuna mata tayi hankali da yaran don su din ba jinin taz bane diyane kawai na maigidan ta da aka haifa mai auren baya daya kara na karamar yarinya daya auro.

   Ga yadda take ji sarakuwar ta itace mata ta farko a guri mijin su saida sukai kusan shekara hamsim a tare ya auro mahaifiyar su safiya din.

    A cewar hjy ita ba a hadawa diyan ta yan uba don haka ta hana mijin nata kara wani aure daga baya .

    Surukin nasu yana sana,a a kauye har ya shigo birni ya fara sayar da kayan mata irin su dan kune da sarka da jakkuna.

  Daga baya kuma daya bun kasa ne ya fara sayar da gwala gwale wanan ne ya kawo mai tarin arziki mai yawa har ya tamfasawa iyalan shi katon gida da suke zaune a ciki.

   Bawai bokaye kawai ko asiri taga sarakuwar nata nbi ba saidai iri matan nan ne masu ji da izza da isa da gadara wanda take ganin yanzu diyan nata da jikoki suna koyi da wanan halin.

   Saidai daga bayane kariyan arziki ya afkawa mijin nasu bayan siyasan shehu shagari da mazajen arewa da dama suka samu wanan koma bayan a sanadiyar canji da gwaunatin soja mai a lokacin ta kawowa mutane yayi sanidiyar karewa wasu bayin Allah da dama a cikin su har da surukin nata ya samu wanan iftila,in tare dashi.

     

  ANCAU KADUNA STATE


Kamar yadda Asabe ta sha alwashi akan Abban mu dole sai ya kara aure hakan ne ya faru don Asabe taje nema mashi auren yar wata mata da ta dade tana zawarci batai aure ba a kauyen mu.

  Tun innan mu bata san wanan zancen ba har yakai ta sani saboda bakin Asabe dake sake suratai barkatai na rashin ilimi da jahilci tare da kiyayya ga inna damu diyan ta.

  Da yake Allah yayi inna mu mace ce mai hakkuri da kawar da ido ga komai koda tasan kaine ke cuta mata din.

  Sai ma bata nuna tasan Asabe nayi ba a gidan don bata nuna damuwata ga abinda Asabe ke yawan fadi ba ko yaushe.

   Mu kan mu bamu tsira ba gurin Asabe don tana nuna muna tsana karara kamar ba jinta muke ba mudin .

   Daga zagi sai dungura dan abu kadan yanzu zata sauke muna bala,i a kanu komai mukayi bamuyi daidai ba.

  Ainihi Asabece mahaifiyar data haifi mahaifin mu ta hayayyafa da dama basa tsayawa da sun dan tasa  an yayesu sai zazabi ya kama su su mutu.

  Sai ya kasance ga mahaifin mu ta samu ya fara tsayawa sai mace da muke kira da gwaggon birni don a birni take yanzu da mijin ta daya samu wani ubangida a can ya daukesu bayan aure ya mayar dasu a birnin.

   Sai ya kasance mahaifin mu yanzu kawai a gaban ta sai yan jikoki da take dashi ta tsatson shi wanda kiyayyan fitowan mu diya mata a duniya yasa bata kaunar mu har cikin ranta.

    Ni dana dan kawo wayau a cikin mu nasan halin da muke gidan na zaman Asabe da innar mu don su sauran yan uwana gorin inna bai taba tayar masu da hankali ba sai ma kawai ja baya da sukayi da al,amarin ta.

  Don yawan fada da zagi da take muna a gidan duk da Abba ya dan kewayewa Asabe gefen ta ma,ana ya dan raba tsakanin mu da ita sai dai hakan bai hana Asabe fitowa zaman sa ido ga inna damu.

    Wajen karfe dayan rana kasancewar yau asabar muna gida bamu zuwa boko mun dawo islamiya tun sha daya muna gida.

   Ina daki ln mu na yara don shigata ke nan na gama wanke tufafin mu da suka dan taru nayi wanka ina shafa mai.

  Naji muryan innar mu tana kwala min kira da yar mairo na amsa da Na,am inna daga dakin tare da saka hijjab a jikina na fito da sauri.

   Ina fadin gani inna tace yi maza ki dauku abincin nan ki kaiwa umma kada yayi sanyi nace tau inna tare da dukawa na dauki kwanon samiran abincin Asabe.

    Munace mata Asabe ne don dukka gari haka ake kiranta dashi in ka debe Abban mu da innar mu koshi Abba sai zuwan inna ne gidan ya canza mata suna dama da Asaben yake kiranta.

   Na isa kofan Asabe ina ta sallama bata karba min ba haka yass na kunna kai dakin na aje mata abincin a gefen kofan ta kadan ko waige banyi ba na fito daga dakin.

    Dawowa nayi na karasa shirina kafin mu zauna cin abinci tare da yan uwana don a tare mu hudu ake hada muna abinci don yana kawo dankon zumuci inji manya sukace.

  Muna gab da gamawa sai ga Asabe tun kan ta karaso wurin mu take kwalawa inna kira cikin tashin hankali.

   Gaba dayan mu hankalin mu ya koma gare ta muna duban hanyar kofanta tana zuwa take tambaya wa yakai min abinci a dakina ?

 Cikin sanyi murya irin na innar mu da kusan kowan mu ya gado hakan take tambayan Asabe wani abin ne inna ?

   A hasale asabe ke fadin tambaya nakeyi wa kika aika yakai min abincin don yanzu na aje dankali na fito bangani ba .

  Haka yasa nasan duk wanda yakai min abinci shine ya daukan min shi dama an dade ana min sata a daki ina hakkuri banda dama in aje yan kwabbaina sai in nema in rasa.

   Da sauri na furta Allah ya tsareni da daukan abin wani nina kai abinci kuma ko kallon dakin ki banyi ba na fito.

   Ke rufa min baki kwadayayya satan naku har yakai haka ban sani ba dole in kira mai gyara ya saka min kuba a kofana don watarana kada kuyi min wanda yafi wanan.

   Wani irin bakin cikine ya rufe ni a lokaci daya ina jin idona kamar zai rufemin a wurin don satan dankalin da Asabe ta laka min.

  Da ba don nasan itace ta haifi mahaifin mu da naja mata Allah ya isa a gurin duk da hakkurin inna saida tayi magana wanan karon.

   Haba umma a gabana yarinyar nan ta shiga takai maki abinci ta fito kuma ban ganta da komai ba a hannun ta.

  Ai dada goyon bayan ta zakiyi ta fara mugun abu tun a gida idan yayi karfi sai ta zauna maki a gida ai don babu mai kwasan barauniya yakai gidan shi.

   Abbane yayi sallama ya shigo ganin mu cirko cirko a tsaye bai hannashi fadin yanzu dankaline har yai yawa haka a gidan aka barwa Akuyan umma tana ci haka?

    Gaba dayan mu kallon Asabe mukayi don jin abinda baba ya fada nan kuma ta fara kame kame tana fadin .

   Hannu na dora akai na fasa wani uban ihu ina fadin Asabe mai nayi maki kika dafa min sata a gaban kowa.

  Ashe akuyan kice ta daukar maki dankalin ki kazo kina fadin nice na satar maki harda kudi nake shiga dakin ki in sata.

  Abba ya daka min tsawa tare da fadin ke ke meye haka kike fada da sauri kanwata Fatima dake bi mun take fadin Abba yanzu fa Asabe ta gama fadin wai Abuce ta sace mata dankalin ta a daki daga kawai takai mata abincin ta da innarmu taba takai mata.

   A wani irin yanayi na bacin rai da mamaki lokaci guda Abba ya juyo yana fadin sata kuma umma ?

     Ina yaran ne jinin kine umma koda itace ta daukar maki ai ba zaki kira hakan da sunan sata ba.

    Ta daka mashi tsawa tana fadin yi min shiru wanda baisan abinda yakeyi ba.

  Yau aka fara sata min abu a gidan nan bana magana don gudun irin haka in magana ku karyatani a gaban diyan ka da matan ka.

  Waya sani ko itace ma ta dauko din ganin za,a ganeta ta jefawa Akuyan nawa.

  Allah ya sauwaka Abba yace ya nufi hanyar dakin su bai shiga ba ya duka ya dauki buta zuwa ban daki.

  Asabe ma ta juya zuwa sashenta tana fada inda take shiga ba nan take fita ba wai Abba da innar mun suna lalatamu da gurbatacen tarbiyan da suke bamu.

   Inna kan daki ta shige tana kuka hankan yasa dole na tsayar da nawa hawayen don komai ya wuce a ran inna.

  Tun faruwan wanan abin na ja baya da lamarin Asabe ba ruwa na da tsabganta iya kana da ita gaisuwa ban yarda in shiga ko lungunta.

    Muna kallo idan jikokin ta na birni sukazo yadda take ji dasu take nuna kamar su kadaine ta haifi   uwarsu sam mu bamu isa mu rabe ta ba.

   Shi yasa ake fadin kakanni sun fison jika na wurin diya mace don ni na tabbatar da wanan maganan gun kakantamu.

   Sannu sannu har lokacin Auren data nema wa Abban mu ya karaso buki ya tashi sosai Asabe ita tayi uwa tai makarbiya don Abba yace shi baida zarahin kara aure a yanzu.

   Ta saka aka tayar damu daga dakin da muke kwana munaji muna gani aka gyarashi tsab wace kullun take kukan bata da kudi sai gata ta fitar da kudi don kawai taga ta kuntatawa innar mu rai .

  Sai fadi take Allah dai ya kawo amaryan Abba tazo ta haifa masu magaji a gidan ko suma zasu shiga fagen zurian dake tun kaho da diya maza a gari.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


3️⃣


ZAINAB  IDRIS  MAKAWA


LITTAFIN KUDINE DARI UKU NE KACAL DON SAMUN SHI ZAKIYI TEXT A WANAN LAMBAN DON LAYIN BAYA KASAN A YANZU KO KI TURO KATI WAYA KO KI TURA BANK DA WANAN LAYIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK NAGODE DA KULAWAN KU GAREMU, , , , Ta dade zaune tana son mikewa zuwa daki don ta dauko takardan da take son turawa saidai jikin daya fara manyanta tana jin kiuya da nauyin tashi daga falon ta zuwa daki a lokacin.

   Wani wawan tsuki taja a ranta take raya ya kamata dai ta samu wanda zai dinga taimaka mata wanan dawainiyar yayi yawa a yanzu gareta.

    Wayan ta dake gefen tane ya dauki kira ta dauko tana kara jan tsuki sai dai ganin bakon lamba dake kiranta ne kuma ga layin special nomba ne ya bata mamaki.

  Taso share kiran don bata san mai layin wayan dake kiran nata ba a lokacin wayan yana gap da tsukewane ta samu ta daga.

    Muryan namijine yake mata sallama ta amsa da mamaki don har lokacin bata gane mai kiran nata ba dai.

    Bayan sun gama gaisawa ne mai magana ke fadin hjy nasan ba zaki sheda mai kiranki ba a yanzu don an dade bamu hadu ba tun muna US rabon damu gaisa.

   Sai mamaki hjy keyi a ranta tana fadin waye wanan kuma wanda ban gane ba dan tunane tayi kafin tace isma,il soba ko ?

    Dan dariya ya sake tare da fadin abin mamaki gaskiya kinyi kokarin sheda muryana is about 20 years yanzu da bamu hadu ba.

    Ai ba zan manta da muryan ka ba a duk inda naji shi ta fada tana daure fuska kamar wanda take wayan yana kusa a lokacin.

   Yace hjy sai naji kina kasan har kusan shekara daya da rabi abin ya ban mamaki matuka har ki shigo kasan nan muna jaha daya ban san da hakan ba.

    Yanzu ka sani ai wakila don bai zama dole irin ku su sanda dawowan nawa bane nan ta bashi amsa.

   Watau halin na nan a yadda nasan shi hjy baki barin ko ta kwana har yanzu ashe ?

    Jin tayi shiru ba amsa yace hjy dama naso muyi wani magana dake ne wanda ya shafi rayuwan ki sai dai naga kamar baki maraba da wayana a yanzu.

   Kai isma,il kafi kowa sanin halina don haka babu abinda ya shafi rayuwan ka dani a yanzu dama nasan don ka bata min rai ka nemi layina don haka ina maka warning da kada ka sake kirana.

   Dan murmushi taji ya sauke dama yasan za a rina idan hjy iyami ce don bata daukan maganin raini ko kadan.

  Shidin yasanta ta dalilin yin karatu a tare ne duk da ya girme mata sosai ga haihuwa amma haka suke shan fama da ita don akwaita da kwazo da basira a lokacin da sukai karatun tana goyon danta na uku ne .

     Kawar da zancen yayi ta hanyar tambayan ta yaran don sunayen su bai bace mai ba har wanan lokacin.

   Wanan tambayan yaran daya jefo mata yasa ta dan sasauta mashi tare da amsa mai da suna lafiya .

  Ance in kana son kama uwa rike yaranta yanzu zaka zama masoyi a gurin ta hakan ko ya faru da hjy har ta manta da fadan ta dashi take fada mai rayuwan yaran ta a yanzu.

   Karshe dai yace sai sun zo don bashi kadai ne zaizo ba akwai magana mai muhinmanci da zasu so suzo yi da ita.

   Nan ma saida hjy tayi korafi akai kafin ta kashe wayan tana kara jadda mai cewa idan yasan shirmene zai kawo shi kadama su zo din .

  Shi dai dariya yayi yana fadin sai idan sunzo din zataji sukai sallama ya kashe wayan.

   Kai hjy ta girgiza tana fadin mutane akwai tsegumi har suna daukan  zancen abinda bai shafesu ba suna dangantawa da lamarin su.

    Mikewa tayi don dauko takardan datake so daki har lokacin tana maijin zafi a ranta na ba gaira ba dalili wata kila kuma har yanzu haushin wayan da abokin karatun ta yayi matane oho ?

   Kiuyan fitowa dakin tayi zuwa falon ta har akai kiran sallah ta samu ta mike don zuwa sallah.

  Yanzu idan akwai abinda hjy ta tsana shine rashin son motsa jikin ta don hutu yariga da ya gama ratsa ko ina nata ga yaran da take zaune dasu baka more ne gaba dayan su son jikin su yama so yafi na hjyn yanzu don gatan da ake nuna masu.

   Sai dai duk da hakan tana dan kokartawa tana sakasu wani abin can ba,a rasa ba sai dai zata sha mita da jini duk tana hakkuri da wanan.

   Wani lokaci kuma zata zage tayi masu fada sosai akan rashin son motsa jikin da basa yi dan abu kadan zasuce sun gaji.


    KAUYEN ANCAU


An kawo amaryan Abba wata bakace gajera bata da tsayi saidai akwai mazauna irin na mata gareta.

  Ni dai banga abinda nagani gareta ba sai halin kiyayya kawai da Asabe ta dagwarawa mahaifiyar mu in bashi ba babu ta inda ta kama kafan innan mu.

   Zaman su ba yabo ba fallasa don inna bata shiga tsabganta ko yaushe tana kofanta ita kuma amarya tana lungun Asabe.

    Idan muna gida mune abokan hiran innar mu sai kuwa ranan da akace itace da girki ranan zan fara labe labe don ban yarda da tsarin Asabe ba .

   Na cewa mu dinga kwana dakin ta haka yasa na share dan karamin dakin da ake tara tarkace a gidan mu dakin ba wani girma ke gareshi ba asalima madafane Abba yayiwa innan mu don da dama tana wahalan girki a ruwan sama.

    Abba yayi fada har ya gaji don ko naje lungun Asabe da sunan kwana bana shiga dakin ta saidai in tsaya daga waje.

   Idan na faki idon Abba ya shige zan dawo wanan dan dakin in kwanta dama mu uku ne masu dan wayau da muke zuwa kwana dakin Asaben.

     Zakaji tunda asuba Asabe na fada wai an jawo mata kwanan wahala a daki yara sunzo sun hanata shakat daki suna damun ta da tusan dare ko tace wai an mata fitsari a daki.

  Ranan da tace fitsari kanwata dake bi mun tace itama daga ranan a inda nake kwana zata dinga kwana don sherin Asabe ya isheta.

   Sai lokacin Abba yasan ban kwana dakin dole yakawo ido yasa mun hakana muka mayar da dan dakin wurin zaman mu koda da rana ne a nan zamu zauna muyi tsabgogin mu.

    Wanan baiwa Asabe ba don ganin yadda mukan saka innan mu a cikin nishadi wani lokacin har mu zauna ana hira da dariya .

  Sai kuma hakan ya fara basu haushi suka kulla wani sherin a kaina wanda ya girgiza mu ga baki daya yan dakin mu.

  Ranan monday da safe muna ta shirin makaranta tunda naga Asabe ta fito daga lungunta zuciyana ke bani akwai wani abu da zai faru a gidan don daga dakin da muke ina jin muryan ta a tsakar gida tare da Lantana Amaryan  Abba suna dan zance kasa kasa.

  Don ranan inna muce da girki a dan dakin mu muka kwana inna tunda ta fito ta dama kokon safe da zamu karya dashi kafin mu fita ta koma daki don ta shirya kananun da basu iya shirya kansu sai an taimaka masu.

   Na fito da sauri kada in makara kofan innar mu na isa ina fadin inna ni zan tafi kada in makara.

    Na juyo inda su Asabe suke da zuman in sallame su lokacin Abba daga daki yake fadin kin karyane Abu ?

   Na karya na bashi amsa daga waje don ban shiga dakin ba tunda na girma innan mu ta koya muna hakan idan Abba yana ckin dakin namu.

   Zoki karbi murtala ki rike ko fanke kya saya a hanya Abba ya fada daga dakin.

  Tsiyan banza dama nasan kai ke koya masu kashin kudi don baka gudun Abin kunya kai kan wa yan nan yaya matan naka.

  Karatun bokon dole  duk  yan uwanka wa kaga ya dage kan sai diya mace tayi boko haka ?

   Badani za, ayi wanan abin kunyan ba kuke nan ko yaushe ku dorawa ubanku wahala don kawai baisan ciwon kanshi ba.

  Gani kunan haihuwan yuyuyu da aka tara mai agida ace har mace bakwai ko daya ba kawar ba a cikin ku.

   Daku da uwarku kunki ku barshi ya ji da abinda zai ciyar daku da wanda zai tara yai maku aure nan gaba.

  Amma kullun in sata in maita sai ya lalube aljihun shi ya baku dan abinda ya kwana dashi ko kuma in bakuje makarantar ba uwar ku ta lalabe shi a daki.

  To hakan ba zai yuyu ba don baku da uwar ku kadai na haifarwa shi ba don haka daga yau na kashe wanan bokon naki.

   Aure zan maki shekara goma sha hudu ai kin isa aure har kina batun wuce munzali.

   Gwanda ki tafi dakin mijin ki yaji da sauran yan uwan ki da suka rage kafin suma a fitar dasu sai gidan ya koma hondaku .

  Bansan lokacin da Abba ya fito daga dakin inna ba don tunda ta fara magana na zuba mata ido ina kallon ta cikin al,ajabi da mamakinta.

   Muryan Abba naji yana fadin haba dai umma aure fa yanzu ga Abu  haba wani irin aure kuma kamar yadda taken nan.

    Hae guda nawa Abu take da za ace za,ai mata aure a yanzu akaita gidan miji ?

   Wani tsawa ta dakawa Abba tana fadin yi min shiru shanyaye kawai wanda baisan ciwon kanshi ba.

   Dame su hansai da Adawiya suka fita ga shekaru da akai masu aure kuma suna zaune kalau a dakin mazan su har yanzu.

   Abba yace Allah ya huci zuciyar ki umma ni gani nayi har guda nawa Abun  take ne da za a ce aure yanzu.

  To ai gaskiya umma ta fada inji lantana amaryan Abba ta fada aure ga ya mace shine wajibi.

  Ba wani karatun boko ba can da yanzu shike kara lalata yara yanzu haka idan ance ma yarinyar mnan tasan komai game da aure kada kayi musu.

    Ke lantana ahir dinki ga bata min diya da wanan kalamin naki sai Asabe tace kaji sauna yo ai gaskiya ta fada ko karya nakeyi Asabe ta tsatsareni da idanuwan ta na tsufa.

  Bansan lokacin da kuka yazo min ba na juya zuwa cikin dakin da na fito don jin sherin da ake kokarin lakaka min da farar safiya haka a gidan mu.

    Sauran magana ban jisu ba saboda kukan da nakeyi makarantar da ban tafi ba ke nan ranan don maganan Asabe tankar umurni ne ga Abba gama kowa a gidan.

    A karshe dai na fito yin alwala nake jin lantana na fadin toke umma tunda kowa yasan kyauta na dan maciciji ne babu masunsuni gareta.

  Ai baki kyale haka a zuba mata ido ba dadai kin nemi wani a cikin kauyen nan ki hadata dashi zaifi sai aji da sauran .

   Don muddin tana gaban ku haka ba wanda zai kula sauran duk sai ai masu daukan daya kinsan halin garin nan sarai.

   Duk wanan zance da sukeyi inna tana jin su bata ko nuna tasan ana zancen ba ta kawo ido ta sakawa kowa don nuna ka waici ga wasu mata na karkara.

   Har kwana hudu sati na batun shigewa ban shiga school ba na gaji da zama daki  mu don ko tsakar gidan mu na daina fita idan ba wani abu zanyi wajen ba.

    Daki  innar mu na shiga na saneta tana nade kayan data wanke na yara gaida ita nayi ta juyo tana amsawa fara nade kayan nayi sai inna tabar min nadin ta juya tana fadi.

   Saliha tazo tambayan kitso nace ta tafi ta dawo don nasan halin ki sarai dan ajiyan zuciya na sauke ina fadin.

  Ni inna banwa kowa kitso a barni inji da abinda yake damuna sai naga inna tayi murmushi tana kaiwa zaune gefen gadon famekan ta.

  Tace ai dama haka ake son a ganki cikin kuntatawa da damuwa sai bukatan lantana da umma ya biya idan sunga kina wanan takura dama abinda ake so ke nan damu.

    Shiru nayi ina nazarin maganan inna da bata kara dora wani lafazi ba bayan wanan data fada hawaye ne yadan biyo fuskana na share da sauri.

  Don nasan ran innan mu ba zaiyi dadi ba itama don ban taba jin ta furta komai cikin zancen hanani zuwa makarantar ba sai yau da tayi mi  hannun ka mai sanda.

   Dan hira muke jefi jefi  mukaji muryan saliha ta dawo tana tambayan kitson ina jin tana kwada sallama lantana na fadin wai waye haka ke damun mu da sallama ne.

  Fitowa nayi daga dakin inna ina amsawa tare da fadin saliha shigo dama yanzu inna ke gaya min kin zo ai ina barci.

   Saliha race wallahi nazo ko zan samu ki kwashe min kai zamu birni wurin bukin dan uwan maigidan mu ne.

    Nace bissimilah shigo bari na dauko tabarma na juya zuwa dakin innan mu na dauko mata tabarma muka zauna zaman kitson.

  Na koyi kitsone akan yan kanne na don yawan yawon neman kitso da kashin kudin da inna takeyi kan kitson mu.

     Wanan yasa har na koyi kitso ina zama in masu har na hannu na iya ba wevean ba kawai don ina dake son kitson hannu wanan kuma a kanta na koya.

    Yanzu kuma in muna makaranta nakan koyi kumshi a pepper har na fara zanawa kannena sai  dai ba sosai na iya ba.

   Wasa wasa tun daga ranan da naiwa saliha kitso mutanen unguwan namu ke shigowa wurina yin kitso ko su turo yaran su in masu.

   Sai ya kasance har na fara mantawa da zancen hanani karatun da umma tayi yanzu.

   Ga kudi baya katse muna dan abinda zamu kashe a kauye baya buwayan inna yanzu.

   Don a wuni akalla muna dan rike dari biyu ko dari uku tundai idan akave weekend ne don ba wani kudi bane mai yawa kudin kitson kauye talati hamsim ne wani a kyauta zan mai ya tashi.

   Ga Abba abin kara lalacewa yayi mai tun shigowan Lantana gidan shi abinda zamuci ma yana batun gagaran mu a gidan.

    Don haka muke dan dora karamin tukunya mu dafa dan cimar da zamuci iyamu damu don Asabe ta fara a gaban mu zata dan dafa abu.

 Saidai muji tana kwalawa Lantana kira tazo ta karba idan lantana ta karbo a gaban mu zasu zauna suci har tana santi don muji haushi.

  Wani lokacin yan kannen mu sai su sa ido suna son ci sai inna ta doke su ko Asabe ta dinga fada ita ba zata iya ciyar da taron yan mata ba uwar mu data haifo mu ta nema ta bamu muci.

   Da ku mazane ai da bamu kai haka ba a gidan nan da yanzu kuna wurin nema kuna taimakawa mahaifin ku.

  IIrin wanan maganganun na kakar mu yasa muka dan fara dafa tukunyar gefe don kada kannen mu su koyi daukan ido ta wanan dalili.

   Ranan inawa wata makwaciyar mu kitso kanwa saratu tana dafa fate don shi zamu gyara muci don Abba bai kawo komai a gidan ba tun safe.

    Girkim ya dauko kamshi duk ya dume gidan da kamshi saratu na bakin murhu tana faman fita wuta don iccen baya ci sosai.

  Sai ga lantana ta fito lungun Asabe gurin kwata inda muke wanke wanke kakarin amai ta fara da karfe da yaji.

   Sai duk mukayi tsaye cirko cirko muna kallon ta da mamaki don bamu dade da jin dariyan su ba da asabe kamar ba sarakuwar ta bace lantana.

    Sai ga Asabe da sauri ta fito tana salati tare da fadin yau may zangani haka Lantana lafiya meya same ki ?

  Asabe ke tambayan ta a rude sai ga inna ta ma tafito daga dakin ta tana fadin Lantana meya faru.

   Ganin Lantana na nuna gurin da saratu ke girki da hannun ta alama dai warin girkin namu wai ya jawo mata aman a yanzu.

    Ja inna tayi baya don ta fahinci makircin da Lantana ke shiryawa a kan girkin da mukeyi din don muci tun safe bamu karya ba.

   Wani guda mukaji Asabe ta sake wanda bamu fahinci ko na menene ba sai da tace .

   Ahhaye nanaye Allah nagodema yau magaji ya bayana a gidana da yardan Allah.

   Ta juya wurin saratu tana fadin ke kashe wutan nan ki bar girkin nan kada kija min hasara a gida don ku ba damuwan ku bane tunda bata son kamshin dahuwan naku.

   Saratu ta mike tsaye ta fara buga kafa tana yaya zan kashe wuta kina ganin tun  safe bamu karya ba.

  Kada ki kawo min diban albarka nace a kashe wutan ku mutu idan bakuci ba mana waya damu daku wanan matsalan uwarku ce.

    Wallahi bazan kashe ba tunda bai dahu ba saratu ta bata amsa saiga inna ta laiko daga daki tana fadin saratu jaye itace don Allah banson gardama da manya.

    Tamayi gardaman dani Asabe ta fada tana nufar wurin randan ruwan mu ta debo ruwa a roba tana zuwa ta lemawa itacen da garwashin wuta lokaci guda wutan ya mutu.

   Aiko saratu ta sake wani uban ihu tana fadin wallahi ban yarda Asabe tunda ba bamu abinda zamuci zakiyi ba tana magana ta nufi wurin murhun tana hawaye.

    Muryan innace ke fadin karkiyi barshi hakana kuci ko bai dahu ba idan zai ciyu.

  Wallahi inna bandade da zubawa ba tazo ta kashe wutan matar makwabtan mu da nakewa kitsone tace dauki dahuwan ki shiga gidan mu ki karasa girkin naki don Allah ku bar wanan magana.

  Saratu tana sharan hawaye take fadin wallahi Asabe saina rama don ba yarda zanyi ba kun dafa naku kunci zaki hanamu dafawa yanzu.

   Ranan dai sai gidan makwabciyan mu saratu ta karasa dafa abincin da zamuci ga Abba bai dawo ba har dare don haka da bafon faten ba haka zamu kwana da yunwa a ciki mu.

    Saida safe ne nake jin  muryan Abba cikin jin dadi yana fadin masha Allah abu yayi kyau Allah ya raba lafiya.

   Ma,ana dai watau lantana ta samu ciki a gidan mu ke nan ni banji komai a raina ba a lokacin .

    Don ban gama mallakan hankalin kaina ba da zan gane may hakan ke nufi damu sai can naji muryan Abba nawa saratu fada don me tayiwa Asabe rashin kunya kamar Abba zai doki saratu din.

   Ban san ina Asabe ta tafi ba wai ashe ta fitane zuwa gidan wata mata mai bada magani ta ansowa lantana maganin baki kada innan mu ta zubar mata da cikin jikin ta.

  A daidai wanan lokacin saratu ta shige lungun Asabe ta fasa mata babban randan ruwanta ba wanda yasan da shigan ta har ta fito daga sashen.


   ZAINAB IDRI MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


4️⃣


 ZAINAB IDRIS MAKAWA


LITTAFIN KUDINE DARI UKU NE KACAL GA MAI BUKATA TARE DA IMANI DA SANIN AKWAI HISABI GOBE KIYAMA.

    DON ALLAH YAN UWA MUJI TSORON ALLAH GA DAUKA HAKKI A KAN MU TA WANAN HANYAN SAYAR DA LITTAFI A ONLINE MUKE SAMUN CIGABA DA RUBUTUN DA MUKE MAKU KADA KIJI HASARAN BAMU HAKKIN MU KODA KADAN NE .


Sai salatin Asabe mukaji a tsakar gida tana ta faman rabka salati da fada tare da zagi ga duk wanda yai mata wanan aikin.

   Babu wanda ya tanka a cikin mu har innan mu saiga Lantana ta fito tana fadin meya farune umma ?

    Meye ma bai faru ba randar ruwana tun tele tele na samu a fashe yau sai nasan wanda yai min wanan ta,asan a gidan nan ta fada tana zare ido.

   Lantana tace kema umma da wani zance kike ai wa zaiyi wanan banda yaran gidan nan ko Akuyar ki ta fada mata.

  Badai Akuya ba su din daine zasu aikata min haka saboda bakin ciki da mugun hali yau dai ai za,a yita ta kare ko a biyani randan ruwana ko kuma yasan inda zaiyi dasu nagaji wallahi .

  Ta karasa tare da juyawa wurin randan ta nufa tana hada guntayen sakainan da suke wurin a warwatse a kasa.

    Ranan wuni jininin wanan abin tayi babu wanda ya fito yace shi ya aikata hakan sai lantanane ke taya ta fadan.

   Abba na dawowa da wanan zancen aka tare shi kira ya kwalawa innan mu dake daki ta fito.

   Cikin yaran nan wayaiwa umma wanan barnan ya tambaya yana kallon fuskan ta.

   Malam ina zan sani tunda ba yawo nake dasu ba balle duk cikin su babu wanda ke yawan shiga wajen umma ko tana nan balle bata gidan yau tun safe.

    Asabe tayi caraf tana fadin waya sani ko ita dince tayi wanan abin don kawai tsaban bakin ciki dake cinnta.

    Aure daine na karawa dana ga kuma abin arziki har an samu saidai bakin ciki ya kashe mutum din sai anyi ma yayan ki dan uba a gidan nan.

    Wanan bai taba damuna ba umma kin sani in ma za a karo mai biyune rana guda su shigo su haihu a rana daya bai taba damun rayuwana.

   Kana dai jin wuyan matar ka yayi kauri har tana fada min bakar magana haka a gaban ka.

   To kisha kurmin ki wanan din ce dai guda na aura mai kuma baki so hakan ba dake da diya matan naki da suke tayaki kishin.

  Allah ya baku hakkuri umma randan ruwa ne dai ban san wanda ya kashe maki shiba .

    Makirci daine kiyi tayi aiga diya mata nan maki zube a gida har yau babu wanda ya sallama da sunan kiran su.

    Shiga dakin inna yayi daidai da soma fadan Abba Asabe na fadin in fito da miji cikin samarina Abba yace kwarai kuwa da gara dai in fara rage su nima zaifi min sauki tunda har sunyi wayau yin hakan yanzu.

  Idan ma bata da tsayayyene akwai wanda zan hada ta dashi ai shi a shirye yake ko yanzu idan har na bashi.

   Abba yace a, a umma gara dai a bari ta kawo din da kanta zaifi tunda kin ga yadda yar gidan muddi suka kare kan hakan yanzu.

  Gashi kullun maigari maganan shi ke nan a bar yara su zaba da kansu da ai masu dole.

  Ai ba dole bane tunda shidin wanda zan hadasu din yana son ta ai itama zata so shi tunda bata kaishi gata ba.

   Koma dai menene umma don Allah kada a soma hakan banda zarahin zuwa birni sharia tunda kinga can ake kai mutun kai tsaye.

    Jin hakan yasa Asabe tabe baki tana juyawa zuwa wurin ta tare da fadin ni banga ranan haihuwan diya mata ba a rayuwana ko kadan.

  Inna dake daki kuka take darza a hankali batare da fitar da sauti ba balle wani ya jita.

  Alwala nayi na nufi dakin ta sanin Abba ba dakin yake ba na samu inna zaune tayi tagumi a wurin data idar da nata sallah.

    Inna kada zancen su Asabe ya tayar maki da hankali har ki shiga damuwa tunda bake kika ba kanki diya mata ba ai.

  Meye laifina a cikin wanan zance yar mairo don kawai na haife a mata yasa umma ta dauko tsangwama ta dora min ni meye nawa a ciki.

    Su suke raina diya mata ina saboda in kin kula Asabe ba da bukatan ilimin addini ko kadan ne matar da ko alwala bata tsaya ta koya ba .

  Idan kuma za a gyara mata tace ina mutum ya fito ta kashe shi ai kinga fadin hakan daga bakinta ba abin mamaki bane jahilcine ke damunta daga ita har yar koran nata.

   Bashi yafi damuna ba yar mairo yadda yanzu mahaifin ku yake kokarin juya min baya tun lokacin  zancen cikin  matanshi da umma tayi.

  Ina kallo zai sayo mata abu a gaba zai bata idan nayi magana yace min tana da lalura dole a lalabata ai.

   Inna kema idan kina son abin ai sai ki fitar da kudi ki saya idan baifi karfin ki ba kiyi hakkuri ki saka masu ido Allah ba azzalumin kowa bane ai.

   Sallah nayi har na idar tana zaune tana faman tunane kafin ince niko inna sai nake ganin kamar saratu ne tayi wa randan ruwan Asabe ta,asa don abinda tai muna ranan .

  Don dazun naga sanda ta fita zuwa lungun Asabe bata dade ba ta dawo daki tana dariyan kyata.

  Amma idan itace ta aikata hakan sai na bata mata rai yau inna ta fada a hasale.

  Da sauri na tare inna ina fadin a, a inna idan kin doke ta zasu gane kiyi mata fada kawai don Allah idan ta shigo.

    Kwafa innayi ba tare da kara furta komai ba ta mike tsaye ta tada sallah don isha,i da ake kira lokacin.

   A daidai lokacin saratu ta shigo gida tana wakan ta mai kama da habaici a fakaice .

    Gamu munzo taron dangi,  bama tsoro kugafar bama tsoro har zuwa karshen wanka tanayi tana rawa kafin sallama ta shigo dakin inna kai tsaye.

    Ganin muna sallah yasa itama ta juta ta suri buta ta shiga bandaki ta dade a ciki kafin ta fito tayi alwala lokacin har sauran sun shigo dakin ko suna sallah.

    Nice na fara idarwa don Inna ta tsaya dogon adduan da takeyi bayan sallah.

    Fatima ki tashi kuci abinci kada kiyi barci bakuci abinci ba cewa da yar karaman kanwar mu data kwanta tana shirin barci.

    Mikewa nayi don in raba muna abincin da mukayi tunda rana tuwo ina tayi muna da miyar ganye da gyada shine mukaci da rana sai koko da take cika roba ta aje don mai yara bata yarda ta rabu da koko a dakinta a kauye.

   Saratu na shigowa take fadin yanzu ma tuwon ne zamu kara ci nace idan kin tanadar muna wani abin ba sai kici ba.

  Sallah ta tayar har ta idar daga inda take fadin Abu bani abinci na zanci in kwanta ne yau barci nake ji.

    Ba zaki biya karatun ki ba ke nan yau barci zakiyi tace na gaji ne yau  sosai na dibar muna abincin sai da muka faraci dakin hayi tsit a lokacin.

  Don inna ta horemu da hakan tun muna yara har muka gama kowa yaje ya wanke hannu muka dawo tana gyara wurin kwanciya inna tace.

  Saratu may yakaiki wurin inna har kika fasa mata randar ruwanta yau don kawai ki jawo min sabon masifa cikin gidan nan ina fama da kaina.

   Juyowa tayi inda nake ta dan kalleni kafin tace wani inna wallah, , , ,  bata karasa ba don tsawan da inna ta daka mata da rufe min baki tun kan na mareki wurin nan.

    Shiru tayi har inna ta kare mata fada bata sake magana ba don fada sosai inna tayi mata  tana shiru har inna din ta gama.

    Ina jin tayi shiru nace ni inna gaskiya gobe zanyiwa Abba maganan karatuna gashi har zamu fara exam din shiga wani zango ban tafi ba.

     Idan kinga zaki iya ai gaki gashi nidai babu ruwa na tunda kikaji umma tace kin daina boko to ki barwan nan zacen a hakan.

   Har muka kwanta ba kara magana ba sai faman tunane nake a raina don ba abindake damu kamar rashin karatu da ban fita yanzu na riga da na kwallafa rai ga boko nace ni nurse zan zama idan na girma.

  Washe gari baba bai fito dakin lantana da wuri ba har kowa ya gama shiri ya fita don sauran suna zuwa makaranta basu fada kangin Asabe.

   Hankalina yana wurin fitowan  baba daga daki  lantana sai wuran goma ya fito tare da ita tana mai rakiya don kawai kada yace zai biya wurin innar mu su gaisa.

    Har yasha dan kwanan fita daga ciki gida na fito da sauri na same shi ina fadi  Abba ina kwana.

   Ya tsaya tare da juyowa yana fafin yar mairo kun tashi lafiya ina kannen naki sun fita ko ke nan ?

  Nace a sanyayaye sun tafi baba sai na fara hawaye daga inda nake tsungune ina dan gogewa da gefen hijabi na.

   Me ya sameki kike kuka haka da safe Abba ya tambayeni cikin kullawa kasa bashi amsa nayi sai sharan hawayen da nakeyi a lokacin.

    Lantana dake tsaye gefen shi kamar bodyguard din shi ta tabe baki tana fadin ya wuce dai zancen auren ta da umma ke fadi.

   Kai haba lantana wani zancen aure kuma yanzu gun yar mairo adaiyi hakkuri ta karasa karatun nan datasa a gaba har kwana nawa yarage ta karasa idan muna raye.

   To ai naga kai umma take tausayawa a cikin zancen nan kamar rage maka nauyine umma ke kokarin yi ga hakan.

  Ya juyo wurina yana fadin kinga yar mairo kije kiyi hakkuri har in zauna da umma in fahintar da ita ko Allah zai bamu sa,a a kanta.

  Lantana dake jin mu ta karyar da kanta gefe tana fadin gamu gani ai indai umma ce a gidan nan.

  Na bude baki da kyar ina fadin don Allah Abba ka taimaka min na karasa karatuna ko iya secondary din ne in tsaya.

   Taysayinane ya kama Abba lokaci guda sanin yadda gun ina kankanuwa nake son boko har irin dagewan da nakeyi kan karatun a yanzu.

  Yayi karfin halin fadin kada ki damu yar mairo insha Allahu zaki karasa karatun ki har ki more a rayuwan ki,  duk da lantana na fadin malam kasan fa ka makara kada kwastama su dinga mitan hakan.

    Haka yasa Abba ya wuce badon yaso ba don tausayina da yaji a lokaci guda ya rufe mashi zuciya.

   Bayan fitan baba lantana ta juyo ta dubeni a lalace tana fadin iska na wahal da mai kayan kara.

    Lantana wurin Asabe ta nufa ta fesa mata yadda mukayi da Abba tunda naga ta nufi can zuciyana ya raya min hakan.

      KADUNA GARIN GWAUNA


Wanka tayi ta shiya a gurguje cikin shigar manyan mata da boko ya gama ratsa su.

   Fuskanta babu wani kwaliyan zama a tare da ita sai dan maikon mai data shafa sai man lebe data murza don yanayin garin.

   Gurin takalma ta nufa ta saka wanda yai shige da kayan jikinta da sauri ta fito daga dakin duk da sauri takeyi amma idan ka ganta sai ka dauka takon isa da iza takeyi saboda wayewa.

  Makullin mota ta dauka don bata bukatan driver a  inda zata tafi yau don gidan safiya take son kaiwa ziyara da sa,a.

    Tana bude falo sukayi kicibis da bakin ta dake hawo steps din da zai sada mutum da kofan shiga gidan.

   Tsayawa sukayi suna kallon kallo a tsakanin su   kafin hjy iyami ta fara fadin kune tafe banda labarin hakan.

  Sai lokacin Alh isma,il yayi dan murmushi yana kawar da abin kunyan dayaso yi lokaci guda don ganin hjy dayayi a yau bayan tsawon shekarun daya dauka basu hadu ba.

   Shima ya wayence da fadin af na manta da gidan bakar baturiya zamu ziyarta dole saida notice.

  Kai ta girgiza tare da kallon wanda suke tare tana fadin sannu da zuwa kaidai shi wanan har kullun baya tsufa halin shi na kurciya yana nan a yadda yake da zolaya.

    Ke kuma zolayan ne bakya so ba bissimillah ku mana ku shigo kasa na tsaya mun bar bako a waje.

   Bako ko baki don nima bokon ne tunda ban taba zuwa gidan ba ai kinga na zama bako.

   Hjy iyami tace kaidai ka sani tana ja dan gefe guda tare da nuna masu hanyar shiga don bata yarda su sakata gaba ba kasancewar su maza.

   Falon suke bi da kallon yadda ake tsara komai zakace a kasan turai gidan yake don tun a waje suke bin ginan gidan da kallon sha,awa.

   Zama sukayi saman kujerun alfarman dake falon kafin aka fara gaisawa tare da tambayan iyali.

   Alh isma,il yana tambayan samarin hajiya daya sani take fadin kai ai yanzu sun zama magidanta in ka debe shi  na biyun da har yanzu baiyi aure ba yana chaina yana aiki dasu a yanzu.

     Kai masha Allahu Alh yace sai kuma yayi mata gausuwan rashin mijin ta don tun lokacin basu hadu ba dashi yace koda suka zo gaisuwa mata sunyi yawa basu shigo ba.

   A lokacin yanayin hjy yadan canza take fadin hakane saidai bamu dade ba muka koma don yara dake karatu a can.

    Bayan sun dan sha abin shanda aka cika masu gaba dashi yake fadin hjy dama kamar yadda nace dake magana ce tafe damu sai fuska da fuska zamuyi maganan .

  Hjy tace kwarai hakan kace yanzu ku nake saurare ai dayan mutumin ne ya karbe zancen da fadin hjy nasan baki sanni ba ni.

   To ni sunana Aliyu zaki kubau dan majalissan dake wakiltan nahiyar uku dake makwabtaka damu.

    Munzo nan ne da wani bukata ko shawara na duba a gareki wansn ba wani zance bane sai sunan ki da muke son mu bayar don zaman ki macen data cancanci wani mukami da muke son a samu a tamu nahiyar a cikjn gwaunatin nan.

   Ni kuma Alh har yaushe na dawo kasan nan da zan iya shiga wanan harkan na siyasan kasan nan yanzu.

  Bayan haka kuma ni yanzu duk wani mukami na gwaunati ko wani aiki ban ra, layin shi saboda hutu nake so a yanzu a cikin iyalina.

   Me nake nema a yanzu wanda Allah bai ban ba sai hamdala da shukura ga ubangijina ga yara sun kawo karfi suma Allah yana duba mana duk a yanzu.

    Mun san da hakan hjy sanin hakan ma yasa mukaga cancantan ki ga wanan matsayin don kece zaki tsaya muna badon kudi ba sai don tausayawa jama,an mu.

    Kada kace haka Alhaji don shi mukami da kake gani ba haka yake ba na rike na kuma san meke cikin sa sarau.

   Balle mukamin irin gwaunatin kasan nan sai a hankali don mutane ba gaskiya suke so ba a yanzu niko kasan a bisa tubalin mijina nake komai shine gaskiya.

   Don haka tun zancen baiyi nisa ba ina rokon ku da ku janye wanan magana a duba wata da ake ganin ta cancanci hakan a bata don Allah.

   May na fadama Alh isma,il ya fada yana kallon abokin nasa cikin dan murmushi nasan wanan matar ba zata canza ba ai a yadda na santa tun farko.

    Kaji ke nan ina nan a yadda nake har yanzu hjy iyami ta fada sai dayan mutumin yace hjy zamu baki lokaci kiyi shawara yadda ya dace don bamu son wanan daman ya kubbuce muna a yanzu.

  Don dama ne da hujja da muke dashi akan ki na mace mai ilimi da matsayi irin wanda ake nema a wanan nahiyar tamu a yanzu.

    Shiya sanni yasan ko wacece ni banda ra,ayin irin wanan mukamin ko a majalissan dunkin duniya danayi aiki dasu acan da ka fadi sunana sun san dani a wurin.

    Hjy ki dai kara shawara a duba abin kamar yadda nake fada maki a yanzu don wani abin ansan badon kudi mutum ke rike sa ba sai don al,umman nahiyan ka.

   Zatayi shara yanzu dai mun fada maki bukatan mu don Allah muna son kiyi duba ga wanan abin kafin mu sake dawowa muji shawarab da kika yanke akai.

    Hakana dai sukai sallama ba tare da sunga alaman yarda daga gurin hjy iyami ba shi dayan mutumin daya kira kanshi da Ali zaki kubau yana cike da mamakin hjy iyami din don bai dauka akwai irin matan nan a jaharsu ba haka.

    Unguwar da hjy bata fita ba ke nan a ranan don bayan tafiyan bakin ta sai taji kasalan fita ya kamata lokaci guda don tunanen maganan bakin nata da sukazo mata dashi.

   Tsuki taja tana gyara kafan ta saman kujera data dagwara don taji dadin zama da kyau tana fadin ina zaman zamana kuja min sabon zagi da tonon asiri da tsufana.

    Nikan dariya nayiwa hjy ina fadin hjy ina tsufan yake a nan saidai inda babu tsofin ko za a kiraki da tsohuwa ko dadtijuwa din.

   Don babu mai ganin ta a yanzu yace itace mahaifiyar wa yan nan yaran nata a yanzu.

    Sai data dan dade zaune ta tuna da zancen unguwar da zata tafi do  yau taso ta ba su safiya mamaki ta ziyarci gidajen su su sanda suma yan uwane kamar kowa.

  Don kawai sun fito ba ciki daya da yan uwan su ba bai kamata ana ware su haka ba a cikin dangi don tasha alwashin ida nufin marigayin mijin ta duk akan yan uwanta idan tana raye a duniyan nan .

  Saidai muce Allah ubangiji ya ida nufi na alheri hjy da haka mata suke duka wurin raya zumucin da zumunci a yanzu bai tabarbare ba a duniyan nan.

   Shigowan yaran ta dake gida suna hutu ne ya dawo da hankalinta garesu gurinta suka nufo kamar yara kanana muhsin ya zauna a gefen ta tare da rankwafo kanshi saman wuyan ta yana fadin wallahi mami na gaji sosai.

   Kafin dayan ya zauna a makari kujera dayan gefeb yana fadin hajjaju zaman garin nan fa ya fara isata wallahi.

    Gashi ko a nan zaku zauna don ba zan yarda wani cikin ku ya kara niss dani ba kamar yadda kewan dan uwanku ke wahal dani a yanzu.

   Wai mami idan an tashi magana sai ki kawo zancen yaya jackson shifa ina jima yanzu ya manta da Nageria a ranshi.

   Dan duka takai mai ga kai tana fadin daga min ya daga da sauri yana fafin wassh Allah na yana shafan wurinda ta dukeshi din.

  Tana fadin har daku cikin batawa dan uwanku sunan shi na musulunci da kiranshi wai wani jackson cen ba dadin ji.

    Allah hajjaju idan ba kince haka ba a turai babu mai gane shi ake afadi don jackson din ko jack ya rufe sunan nasa a yanzu.

   Bai rufe ba ta fada a hayayyake shima idan yazo zan mashi magana kan hakan idan baso yake yaje lahira ana tayar dashi da wanan sunan kafiran ba.ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


5️⃣


 ZAINAB IDRIS MAKAWA


YAN UWA MASOYA ANNABI ALLAH YA KARAWA ANNABI DARAJA YABA MU IMANIN A MAI ANFANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , , 


DON SAMUN LITTAFI BA TARE DA DAUKAN HAKKI DA NAUYI A KANKI BA SAI KI TURA DARI UKU A BANK DINA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA TA WANAN LAYIN 08036959257 KO 09036Tun bayan fitan Abban mu ban koma daki ba wankin dana tara na farayi muna kafin yan kitso su fara shigo min su hanani aikin komai.

   Ina shanya kayan ne nake jiyo zagin da Asabe ke durawa wanda ba sosai nake jiyo su ba daga inda nake har na samu na gama ruwa na diba naje nayi wanka.

   Ban kai ga karasawa aikai sallama ko ban leka ba nasan masi kitsonane suka fara shigowa lokacin .

  Makwabciyar mu hassana ce da yaranta yan mata biyu da zan wa kitso suka shigo fitowa nayi na dauko tabarman da innan mu ta bani don yan kitso din na shifinda tare da gaida ita.

     Dakin inna na shiga tana zaune tana gyaran sarkan kanwarmu daya katse nake fadin inna ko zan dora abinci ne kafin in zauna.

  Jekiyi tsabgan gaban ki gunda ga mata sun fara shigowa barni in gama in dafa muna fate da guntun tsakin daya saura muna shekaran jiya.

    Ko zai kaimu har dare tunda ba abinda zamu dafa da daren  inna Allah zai bamu da yardan ubangiji tunda ga yan kitso nan sun fara shigo min yanzu sai a sayo ko taliyan hausa a dafa da daren.

   To kije ku zauna kada matar mutane ta dade a zaune inna ta fada na juya na fita raina babu dadi a lokacin don a yanzu kan ina iya fahintar halin da mahaifiyar namu ke ciki na mijinta da sauran mutanen gidan mu din.

   Daga kofan innan mu kadan nake zama muyi kitso don Asabe tace bata yarda ana sake masu gashin mata barkatai a gida ba kada azo a barbada masu tsiya a gida.

   Ina kitson ina tunanen halin da innar namu take ciki na bakin cikin rayuwa duk saboda kasancewan mu mata a gareta don kila badon mun fito a yaya mata ba da bata fuskanci duk wanan nakin cikin haka ba.

   Muryan lantanane ya dawo dani ga dogon tunanen dana lula ina rike da kan yar karamar yarinyar dana farawa kitson lokacin.

  Wai har an zauna wanan bakar sana,an da babu karuwa a kullun a cika muna gida da yan gulma da sunan kitso nikan malam ya dawo ya tare min wurina don wanan abin ya isheni hakana.

  Kai ke nan duk abinda kakeyi idon mace na kanka a zubama ido a fita dakai waje ana baradawa a cikin gari.

    Dagani har matan da nakewa kitso ba wanda ya tanka a cikin mu don idan da sabo  sun saba da wanan halin na habaici idan sun zo kitson don kiri kiri ake nuna min hassada ga yin kitson kuma.

    Maimakon ta shiga dakin datayi niyar shiga da farko sai kuma ta juya ta koma lungun Asabe ta dade kafin ta fito.

    Lokacin har na gamawa yaran duka biyu na farayiwa uwar saura kadan mu karasa kitson namu tana yan wake waken ta na hausa mai kama da habaici.

  Naji matar da nakewa kitson tace uhumm wanan matar baban naki da jan magana take naga dai kullun nazo kitso gidan nan sai ta samu abindata fada a kanmu.

  Ina jin dadin yadda baki kulata kike aikin gaban ki ba tare dakin damu da ita ba don irin su saboda bakin ciki suke haka don tayi sanadin da zata saka a hanaki kitson ga baki daya tunda sun san kina samu a nan.

   Ba komai ai wata ran sai labari na fada mun gama ta dauko dari biyar sabuwa ta mika min na girgiza kai tare da fadin a, a wallahi ki ban dari ko dari da hamsin .

  Haba Abu kullun na turo yara a kyauta kike min kitson nan ki karba baban sune ya bamu mu kawo maki da nake fada mai alherin da kikewa yaran shi kullun.

   Dole na karbi kudin badon naso ba damun wanan kudin ya zama kamar buduwar hanyar alherina ranan don duk wa yanda sukazo kitso mun samu alheri sosai a wurin su.

  Bansan yaya Asabe sukayi da mahaifin mu ba ya dai bani hakkuri kan in hakkura da karatun nan kawai a yanxu.

   Ranan nayi kuka sosai kamar ba gobe tun innan mu na ban hakkuri har ta gaji ta kyaleni ta saka min ido.

   Saratu ne abinka da dan uwa data dawo innan muke fada mata wuni nayi ina kuka a daki yau don Abba yace ba zancen komawa makaranta a wurina.

  Tashi tayi ta sameni a dakin tana ban hakkuri tare da ban shawaran da muke ganin zai fitar dani daga kuncin da Asabe ds lantana ke shirin jefani s ciki.

   Fitowa nayi don taya innan aiki gitkin dare haka ma su sararu da sauran yan uwan mu suna debo ruwa daga rijiyan uguwar mu suna cika duk kayan dake gidan na ruwa.

   Har sun kusa cika na kofan lantana don sheri kawai lantana tace wai habiba ta saka hannu a ruwan don haka bata so sai dai su zubar su debo mata wani.

  Wanan ya kawo rikici a gidan mu sosai ranan don har inna takai ga tanka masu Abba kuma ya dawo ya hau innan mu da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba.

  Wai inna ke goya muna baya muna iya shegen da mukaga dama a gidan ai lantana ma kamar uwa take a gurin su tunda tana auren shi.

    Saratu dai taki komawa diban ruwa kuma ta hana yan uwa zuwa su debo suka kada guga a riya karshe dai ruwan da ba,a deboba ke nan har Abba  ya dawo hake wanan fadan .

  Kwala min kira yayi wai na kwashe ruwan randan innan mu guda in zubawa lantana a nata randan in yaso mu mu zauna ba ruwan tunda saratu ta zama abinda ta zama a yanzu duk gaba daya zai hadamu yai muna aure lokaci guda tunda ba finta nayi da wani girma ba.

   Inna kan bata da aiki sai kuka don hakane kowa ke kokarin takata yadda yaso a gidan don rashin maganan da bata yi idan suna mata abinda sukaga dama,  mu a namu ganin ke nan.

   

   Hjy iyami abin duniya y isheta ga matsin da gwaunati da yan siyasa ke mata dole ta zauna da yaranta da yan uwanta kan maganan.

  Inda suka bata shawaran karban mukamin don taimakawa rayuwan tallakawa da sauran al,umman nahiyar su din.

    Haka yasa ta shedawa Alh Aliyu zaki kubau amincewan ta wanda ba karamin farin ciki yayi da jin hakan ba daga bakinta ,.

  Duk da yana hangen da wuya su iya tafiya a yadda suke so da ita don ra,ayin daya hango a tare da matar duk da ba laifi ko yaya ne ai wayau maza yafi na mata ya fada.

  Tawaga guda sukayo zuwa gidan sun dade suna tataunawa da ita kafin suyi mata godiya su tafi.

  Hakan yasa taji duk ta gaji ga ranan don yan aikin ta kawai bazasu iya mata abinda take so ba daidai a hakane safiya suka zo gidan suka same ta cikin gajiya.

   Bayan sun gaisane tare da mata murnan abin arzikin dake shirin faruwa da ita take fadin anya safiya zan iya wanan abin yanzu.

  Yau kawai duk nabi na gaji dan dawainiyar dana wuni inayi da jama,a agidan nan .

  Shiyasa nake son a samo min yarinya yar maidaidaciya da take da rikon Amana in zauna da ita don wa yan nan kinga su ba zama sukeyi ba ko ba school sai sun kirkuro fita sam basu zama a tare dani.

  Na rasa inda zan samu irin yarinyar da nake bukata na kusa wace zata dinga min hidima ko yaushe.

    Dan shiru safiya tayi kafin tace za a duba a gani indaya dace sai a samo maki yarinyar kamar yadda kika bukata.

   Zanje kauye in duba maki mai dama mu gani idan zata iya idan kuma ta gaza sai a mayar da ita a sake duba wata.

  Dakin mun hakan dana gode kuwa safiya shiyasa nake kara jin dadin ki wallahi na dade ina tunanen ta ina zan fara duba yarinyar data dace yadda nake so nan gari.

   Da wanan maganan suka rabu ranan inda safiyan ta koma gida da tunanen inda zata duba yarinyar data dace takawowa hjy a yanzu gashi tayi alkawarin hakan gare.

    Kafin gari ya waye ta yanke shawara a ranta zata duba ta gefen mahaifiyarsu ta gani idan hakan zai samu garesu.

  Don koma meye zata iyayiwa hjy iyami indai zata iya baifi karfinta ba don ko meye hjy ta cancin hakan garesu .

  Don ta nuna a duniya su  yan uwan mijintane a yanzu don ko wani wuri zata tafi na alfarma suna daga cikin masu mata rakiya.

  Wanan abin yana ba mutane da dama haushi har suka fara fadin asiri sukai mata suka shiga zuciyan hjyn a lokaci guda.

    Daga hjy harsu suna jin ire iren wanan magana saidai ba abin mamaki bane hakan da mutane suke fadi don yanzu mutane basu dogara ga Allah sun manta da ba duga aka zama daya ba.

  

       ANCAU

 Tunda safe na samu masu kitso don haka na zauna muna kitson ga innan mu tana aikin girkin gida don yau Abba yayo cefane ana dafawa aci duka gida.

   Ditin mota mukaji a kofan gidan mu sai dai bamu dauki hakan wani abu ba don ba wanda zaizo gidan mu da mota ai.

  Haka yasa muke zaton ko makwabtan mu motar  tazo yin wani abu sai can mukaji sallaman mata na shigowa gidan namu lokaci guda.

  Amsa masu sallama mukayi dani da matan da nakewa kitso sai inna ta dago dan ganin masu shigowa gidan lokacin.

   Tarbon su tayi tana fadin wa nake gani yau kamarsu hjy safiya garin namu ?

   Ba kama bane mune dai din kike gani don kasancewar su kamar tobasai tunda tana auren yaya a garsu.

   Dakinta ta kaisu don Asabe bata gidan lokacin   ba laifi don dakin inna duk da yawan mu koda yaushe tsab yake don tsabtan ina yara basu hanata gyaran daki da tsakar gida har din muka koyi hakan.

  Don ko a kauye akwai masu hali irin na yan birni da zaka samu a talauci amma komai nasu yana tsab.

   Tabarma ta shimfida masu saman sumintin dakin dake sheki sai dan kamshin turaren wutan dake tashi ba wani mai kamshi ba amma duk da hakan ba laifi dai dakin don ba zakace dakin mai yara bane.

    Ruwa ta kawo masu a kofin silver tana fadin ga dai ruwan namu babu sanyi don har yanzu yayan naku baija wuta ba gidan nan.

    Ikon Allah duk wutan nan daya kewaye garin nan ba a ja maku wuta ba har yanzu inna dai bata ce komai ba kada zancen yayi nisa a hakan.

  Safiya ta dauka ta dan kurba kadan ta mikawa anty Sa, a kaita girgiza alaman ba zata sha ba ta aje kofin a gefen ta.

  Lokacin na sakewa matar kai nazo don in gaidasu da zuwa a dakin innar mu din .

  Saida nakai har kasa na  fara gaida su da zuwa anty safiya na fadin wai kada dai ince wanan ce nan wa take da sunama don mantawa da sunana da tayi a ranta.

  Inna tace ki dai tuna don kinsan niba fada maki zanyi ba dai ta fada tana mikewa don barin dakin.

    A hankali nace Abu sunana gwaggo tace naji dayan da ake kira da anty   sa, a tace min haba wani irin Abu kuma keda kanki kike batawa kanki suna haka?

     Zainab din ne kike kira da Abu wai kamar sunan wani abu can daban wanan ai suna tsofine nagani.

  Nidai na fita ina dan murmushi don jin may suke fada a gatin nan kan wa zai tsaya kirana da wani zainab can.

  Nakai kofa naji tana tambayana ina yan uwan ki suke nake fadin suna makaranta na fita daga dakin kai tsaye na koma inda nake kitso .

    Yaro inna ta nema ta tura a kira mata Asabe datace zata shiga makwabta tana jin lokacin da take fadawa Lantana hakan.

  Ba, a jima ba sai ga Asabe da dan saurin ta ta shigo tana fadin bakin daga birni su waye umma yayan kine su safiya inna tace.

    Sai lokacin na tuna dasu da suna yawan zuwa gidan muna kanana amma daga baya suka daina zuwa ban san dalilin hakan ba garesu.

   Suna ina Asabe ta tambaya inna ta nuna mata dakinta sai ta dan tabe baki ta nufi dakin inna din .

  Muryan lantana ne ya dakatar da ita shiga dakin lokacin lantana na fadin umma kin dawo ashe ?

   Na dawo yar nan yanzu yaro ya sameni wai nayi baki daga birni sai lantana tace au baki akayi ashe mu dake gidan ma bakin ciki ya hana a sanar damu.

  Dago kai nayi na kalli lantana da take maganan don nasan da innan mu take wanan maganan haka.

  Asabe ta shiga basu dade ba suka fito zuwa sashen ta tare da bakin sai lokacin lantana ta tafi gaida su.

   Don a nata nufin bazata shiga dakin innan mu ta gaida bakin da zuwa ba don innan mu bata kai mata can ba .

  Inna tana gama abinci ta zuba masu a kwano mai kyau ta dauka takai masu ta dawo ta debi ruwa ta sake kai masu a can.

    Abba ya shigo gidan yana fadin yanzu ake fadamin anga munyi baki a gidan yasa na garzayo in ga su waye suka zo.

  Can ya samesu a aurin Asabe suka zauna sun dan dade a tare kafin su fito suce zasu tafi sai da suka sake shiga dakin innan mu sukai mata alheri kafin su fito su tafi din.

    Bayan kwana biyu naji lantana na fadin duk kyau da bokon wasu ga aikatau zasu kare rayuwan su karshe ma su kare ga auren maigadin gida.

   Dagani har innan mu kallon juna mukayi lokaci guda don ba wanda ya fahinci may zancen ta ke nufi a lokacin.

   Share ta kowa yayi abu kadan yan kwanajkin nan zata ce kyau wasu ya kare ga banza tunda zasu tafiyin bauta a gidan wasu.

    Banga wanda ya isa ya tura min dana yawon bauta ba a gidan kamar banda kowa a duniya har dai ranan da dare muna zaune muna hira a dakin inna gaba dayan mu inna ke fadin.

  Nikan wanan zancen bautan da amaryan baban ke fadi na rasa gane inda maganan ta ya dosa da fadin haka ko yaushe .

    Wanan inna ai ita ko ba dalili kirkiro magana take ta yabawa mutane don kawai ayi fitina tunda bata son a zauna lafiya ita na fada.

   To dan wataga za,a tura yin bauta da take fadin haka inna karma magananta ya dameki don Allah saratu ta fada tana jan tsuki.

    Shiru mukayi kowa na nazari a cikin ranshi kan zancen don innan mu tafimu fahintan da akwai wani abinda zai faru da diyan ta don haka kawai bai saka lantana tayi ta gorin haka a tsakar gida.

   Aiko ranan da safe baba yai kiran mu nida innan mu yana lungun Asabe muka tafi don amsa kiran Abba din.

   A zaune muka same su a dakin kowa yai shiru saidai yanayin su ya nuna kowa na cikin bacin rai a lokacin.

   Wuri muka samu muka zauna nikan ina daga kofan dakin don ban shiga ba a lokacin inna tace gamu malam.

   Zuwan lantana yasa yayi shiru ya kasa maganan da zaiyi sai Asabe take fadin kayi magana ka tsaya kana wani kimbiya kumbiya kamar kana tsoron matar taka da yarka.

     Ke yahanasu bawani abu bane yake son fada maku ke da yarki sai zancen tafiyan yar ki birni da nace a turrata aikatau.

   Koba komai zai dan samu abinda zai rage saya mata kayan daki a nan tunda kunki bari ya aje komai gashi sun cika muna gida zagada zagada dasu.

  Aikatau kuma umma ina ta fada da mamaki karara a fuskan ta sai naji asabe tacd eh aikatau ko yar taki tafi karfin yin sikatau din ne.

   Ina ko tafi umma wanda yake nema ya samu duk wata za,a lalo mashi yaji dumus ai yafi zaman wanan kitson da takeyi kullun tana tara muna munafukai a gida lantana ta fada daga inda take.

   Koba zaki bari ta tafi bane Asabe ta fada a hasale tana duban inda inna take zaune.

   Abba yayi karfin halin fadin a barta suyi shawara da yarta umma don kinga daga sama sukaji wanan maganan yanzu.

    Shawaran me zasuyi wanda yafi wanda na fada yanzu a gaban ta kuma ko kuma sai abinda tace zamubi tunda itace ta ajemu bamu ba.

  Ai shike nan tunda kace haka dama ni kai nakejiwa nake tausaya maka tunda hakan ne kawai zatayi ma a matsayinta na ya mace ta taimakawa rayuwan ku na dan lokaci.

   Umma ai Allah daya bamu su yasan yadda zai iya mana dasu basai mun kaisu inda bamu san kowa ba don neman abin duniya.

  To mara kunya akan yar fadin ki kike kokarin musayan magana dani to kiji ki karaji zuwa birni babu fashi ga Abu.

    Idan ta samo kudin bakuso ku bani wani ya hana ki haifota a namiji halan birni daine kamar taje tagama yanzu haka na fada babu fashi ga zancena kuma.

   Inyaso idan ta tafi ta shiga duniya karewan rashin sanin kowa inds zata ke nan aikatau daine sai ta tafi.

  Wani kuka ne na fashe dashi lokaci guda don jin hukuncin da asabe ta yanke min yau a gidan mu.

  Ta hanani karatu don wani manufanta yanzu kuma zata turani birni yin aikatau do  kawai a musgunawa innan mu.

   Daki inna ta sameni ina rusa kuka itama kukan ta shigo dashi a dakin muka taru muka rasa wanda zai ba wani hakkuri a cikin mu lokaci guda.

   Sai nice nayi karfin halin fadin inna kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zan tafi yin aikatau ba a birni.

   Yar mairo me nayiwa umma take min haka a raguwana ko yaushe take kokarin sai taga bakin cikina a rayuwan ta.

  Ita ya mace ba diya bace da za ai alfahari da ita cikkn zuria da wasu basu gane hakan.

   Ban taba bakin ciki da nadaman samun ku a diya matan da kukazo min ba don ban san kyautan da Allah yai min ba don haka bazan butulcewa Allah na ba.

   Amma umma kulun magana ya tashi a gidan maganan ta daya ne shine na cika masu gida da diya mata bafa san yadda zatayi da diya matan da nake haifo masu ba.

  Innan mu kiyi shiru ki barsu nasan munafuncine aka kula a turani yin bauta a gidan wasu.

   Koda Allah ya nufa zan tafi inna nayi maki alkawarin kula da kaina a duk inda na samu kaina din.

  Balld ba zaki tafi ba yar mairo muddin nina haifeki ba zaki tafi wanan bautan da umma ke nufin kije ba don kawai ta musgunawa rayuwan mu a gidan nan.

   Innan mu don Allah kada kice zakiyi wani abinda auren ki zai tamu gun Abba tunda shima ya nuna baison hakan a gaban mu amma asabe tace sai na tafi.

  Kiyi hakkuri ki bini da addua a duk inda zasu kaini ya zama kariya a gareni ko yaushe.

  Sai naji ta kara rushewa da wani kukan nima kukan na fara lokaci guds mun dauki lokaci a haka a dakin.

   Ranan da wanan bakin cikin gaba dayan mu muka kwana tare da tunanen ina za,a turani shine abinda ke damuna a raina .


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


               6️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA


 YAR UWA LITTAFINA NA KUDINE DON DARAJAN ALLAH KADA KI KARANTA KI DAUKI HAKKIN HAKAN A KANKI   SAI WACE TA BIYA TAKE DA ALHAKIN KARANTAWA A SAUWAKE NA FITAR DA HAKKIN KI NA FADA MAKI GASKIYA.Don Allah ki guji daukan alhaki akanki don gujewa fita ko yaushe abinda ka raina shike zama babba gareka wata rana.

    Ban gaskanta zancen tafiyana ba sai ranan da anty safiya ta dawo garin  wanan karon ita kadai tazo ba tare da yar uwarta ba.

    Ina wa wata mata kitso kamar yadda na saba yiwa mata kitso a kullun aka tare ta cikin mutunci ta samu Asabe na gida a lokacin.

    Bata wani jima ba a dakin naji asabe ta kwalawa innan mu kira daga lungunta inna ta amsa taje sai Asaben ke fadi Abun ta shirya don anzo tafiya da itane yanzu kamar yadda na fada maku za a kaita birni aikatau.

    Cikin karfin hali inna tace basan da wanan zance ba tunda tun ranan  na fada karatunta nake so ta karasa ai.

   Yahanasu ni kike fadawa hakan ko kinyatani kike son yi a bainar jama, a yanzu ki nuna min kina da iko kan yarki ko ?

    Tama nuna in bashi ba umma zaki bada umurni har ta tsaya tana gardama a kanshi don kawai ta nuna ta isa lantana ta fada.

   Eh ai naga alaman hakan kedai yar nan don kawai tana ganin an zuba mata ido dasu a gidan ko ?

    A,a umma anty safiya ta fada kin san fa irin wanan abin natsuwa yake so tun farko idan har baku sharwace ta bane ta hanyar daya dace gskiya ba,a kyauta wa matar yaya ba Anty safiya ke fadin hakan.

   Wani irin a fada mata ko yau kika zo daukan yarinyar nan nace na yarda ga abindana tsara ai in ita mai tunane ba zata tsaya jayaya dani ko ?

   Umma ni ba jayyaya nake dake ba gaskiya ta na fada don yatinyar ban diya mace ce kowa ko bs zaiso hakan ga nasa ba a dauki yarinya akai inda ban sani ba kamar bata ds gata.

   Eh lalai magana kike son daukowa kanki yahanasu umma tace tana kumfar baki ga innar mu wanda hakan yasa nayi shiru ina sauraren shiru na sauraren su daga inda nake zaune zaman kitso.

  Hawaye ne ya fara zubo min sannu a hankali don na fahinci akan me suke magana naga Abba ya shigo gidan da kyat na iya budan baki na fara gaidashi.

  Bai tsaya amsa min yadda ya saba ba ya nufi shiyan Asaben inda yake jin muryan Asabe yana tashi a can.

    Wai yaya ne meke faruwa kuma ya fada lokacin da yake shiga wurin Asabe din yana mai binsu da kallo gaba dayan su wurin.

  Wanan matar takace ke son ta raina min wayau yanzu wai bata sanda wanan zancen ba ita ba mai tafiya da yarta do  ita keda abinta.

   Anty safiya tace a, a umma bata fadi hakana ba ta dai nuna bata san da zancen ba sai kuma ra,ayinta na son yarta taci gaba da karatun ta tace.

   Abba ya juya wurin inna yana fadin idan mugun wuri za a kai yarunyar nan ai ba za,a hada baki da safiya ko muba a kaita.

  Tunda umma tace a kaita din ke meye naki a ciki yanzu banda yiwa yarinya fatan alheri kawai.

   Amma dai malam kasan ba ai muna adalci ba idan akai muna haka ke nan bamu da inci daga har yaran sai yadda akayi damu ke nan.

   Gunma dai kaji da kunnuwan ka yanzu abinda take nufi ke nan tun dazun ita yar nan bata fahinci hakan ba da cewa anty safiya.

    Kinga ki kwantar da hankalin ki kada ki tayarwa yarinyar nan da nata hankalin taje can ta kasa tsayar da hankalin ta wuri daya.

   Inna batacewa anty safiya komai ba illa mikewa da tayi ta bar dakin muna jin Asabe na fadin in ba wanan ba wani taimakone ya mace zatayi a gidan nan dayafi wanan na dan lokaci.

   Dagani har matan da nakewa kitso a gurguje don inyi in gama mata ta tafi kada taji me gidan mu ke ciki batu yabi gari.

   Matar ke fadi wai rikicin me ake hakane nace maganar sune ta manyan gida kawai .

  Ina gama mata ta tafi na wanke hannu na na nufi dakin inna kuka na samu inna nayi wiwi zaune a dakin haka yasa nima na samu wuri na fara rera kukan kamar yadda innan mu takeyi.

  Muryan Abban mune ya leko falon yake fadin wai ina yar mairon takene ta fito su kama hanya kada a yi yamma a hanya.

    Kin tashi nayi sai gashi dakin ya shigo yana fadin  bakiji me nace ba tashi ki shirya ku tafi Allah ya tsare hanya.

    Wani kuka mai karfi na sake tare da ambatan sunan Abba din ina fadin don Allah Abba kada ku kaini birni bauta.

   Har zai fita ya dawo ya tsaya yana fadin kinga kin saka yarinyar nan hankalin ta ya tashi ga tafiyan nan.

    Na rasa me kike nufi da hakan gaba daya yanzu kin canza a gidan nan kin dauko rayuwan banza kin sakawa kanki saboda bakin kishi dake cin ki.

   Ji Abba fa wai duk haklurin da inna keyi a yanzu Abban mu bai gani har yake fadin haka kai tsaye.

  Wani tsawa ya daka min tare da fadin zaki tashi a nan ko sai na makeki wurin nan maza ki tashi ku kama hanya.

  Ai gaskiyan umma data kawo sharan turaki birni aiki idan kin zauna nan uban me zaki tsinanawa mutane a nan in bada kullun ku saka uwarku a daki tana koya maku kilibibin baza.

   Mikewa nayi ba shiri na shiga daukan kayana a dakin inna ya juya ya fita ganin na fara tsuntar kayana.

   A cikin muryan kuka inna ke fadin yar mairo kiyi hakkuri da halin da muka riski kanmu a ciki ki tsare mutuncin ki ibadan ki da kima.

  Kije har kullun Allah yana tare da mai gaskiya komai wuya komai dadi ki kula da yin addua kinji sai kuma ta kasa karasa sauran zancen saboda kukan da yazo mata lokaci guda.

   Anty safiya ce tashigo dakin inna  da kanta tana fadin na fahinci halin da kike ji yahanasu.

    Babu dadi ace ba,a fitar maki da hakkin ki ba su sanar dake ku sasanta kanku sai dai nayi maki alkawari insha Allahu wanan tafiyan nata zai zama alheri a gareku baki daya.

  Yanzu na kara fahintar rayuwan dake gudana a gidan nan naku na fahinci komai yan mintinan danayi daku a  nan .

   Murmushin karfin hali inna tayi cikin kukan da takeyi take fadin na yarda dake safiya Allah ya iya muna ya tsare min ita aduk inda take .

   Ba komai kitafi da ita din tunda haka suka zabar mata insha Allahu tafiyan nan nata zai zama maku alheri tunda bada zuciya daya suka tura maki itaba.

  Ta bude jakka ta ciro kudi masu yawa tana fadin hjyn da zan kaitane ta bada wanan kudin aba iyayyen ta.

  Nayi niyar baiwa umma su sai na fahinci akwai kulli cikin harkan nan don haka ki karba kiyi maza ki boye albashin tama idan an bayar nasan yadda zan dinga maku dashi insha Allahu.

  Don sam ban dauka ita za a bamu ba nadai zowa umma da zancen muna son yarinya a garin nan idan da akwai yadda za a samu.

  Sai yau danazone naga ashe itace zamu tafi da ita ki dauka kamar tana gaban kine insha Allahu.

   Jin hakan da anty safiya ke fadi ya kara kwantarwa umma da hankali sosai muryan Asabe ne ke fadin .

  Wai ina safiyan take ne in kin soma ki bar bata bakin ki wurin lalashin ta ko ta yarda ko kada ta yarda tafiyan nan ba fashi .

    Muna ji muna gani haka muka kama hanya da yan kayana cikin ledan bacco don banda jakkana tafiya da zan saka kayan a ciki.

    Inama na taba zuwa hana rantsu daga makaranta mukazo zaria kuma ba a bari an kwana ranan muka koma gida wurin iyayyen mu.

   Har kofan gida wurin mota asabe ta biyo mu da lantana tana fadin atafi can a dandadi duniya aji yadda take.

   Kina nan zaune gida ba wanda ya taya balle a sallama muna da sunan kiranki zance.

   Umma wa zaiso ta a haka tana zama ko yaushe kamar kucaka gari kamar a kansu talauci ya kare a duniya.

   Allah yasa dai ta iya abinda taje yi din kar taje ta jawowa mutane abin kunya a can don dai sanin hakin kam.

    Kallon Abba nayi don jin abinda lantana ta fada sai naga Abba ya kawar da kanshi gefe daya na mayar da kallona kofan cikin gida namu ko Allah zaisa inga inna ta leko sai dai har motar ta daga banga inna din ba.

  

         KADUNA


Hjy iyami zaune a dining din gidan bata da hutu a yanzu tun soma wanan zancen aikin data samu din koda yaushe tana makale da waya a kunnen ta.

   Yanzu ma wayan ta kare da wani lauyanta kan kammala mata duk wani takarda da take bukatan samu wanda za a tura abuja a tura zauren majalissa.

    Abincin dake gaban ta ta kalla tana dan jan tsuki kafin ta kai hannu ta sama warmer din abincin dake gaban ta.

  Budewa tayi sai ga tururin abincin dake cikin kulan yana tashi kamshi ya daki hancin ta tabe baki tadab yi don tasan ba lalai ne yayi dan danonon da take so ba.

   Plate ta jawo zuwa gaban ta ta fara diban abincin kadan ta tsakura don ba gwana bace wurin loda abinci a cikin taba.

  Lemo ta tsiya ta fara kaiwa a bakinta tana lumshe ido do  sanyi da dandanon shi dake shiga cikin ta lokaci guda.

   Sallama akeyi a kofa ta amsa tana ba maishi umurnin ya shigo tafiya yake a cikin isa da izza har ya karaso inda take zaune.

    Daga tsayen da yake suka fara gaisawa dashi idon shi ya sauke kan abincin dake gaban ta kafin ya amsa mata gaisuwan nata.

   Bissimillah ka zauna take nuna mashi kujeran zama dake wurin yace ba zama nazo yi ba nazone in kara jin abinda kika yanke ga maganan mu.

    Alh Adamu ina dai yanzu kasan ba,a karskshin ku nake ba don mai rabawa ya raba tsakani da yayan ku ko.

   So banga wani abinda zaisa ka jefa kanka a cikin lamarin rayuwana ba kuma.

  Yara daine babu taulali a cikim su gaba dayan su sun kawo girma don haka ka barmu muyi rayuwan mu a cikin sallama don Allah.

  Jin abinda ta fada yasa ya dan sakd murmushi a fuskan shi yana jawo kujeran yakai zaune tare da fadin zaki iya fadin haka tunda baki so  gaskiya.

    Kin sani sarai wanan abinda nake neman ki dashi ba haramttacen abu bane sunnan ma aiki zamu raya ta hakan.

   Wani kallo ta watso mai tare da fadin Alh Adamu na fada ma ka fita hanya da maganan banzan ne shin wai yin aure dolene ?

   Ya dan kara sake murmushi yana fadin amma kinsan aikin ladane ko na rasa meke damun ki kan hakan idan don ta matatace kinsan dai a yanzu kinfi karfin ta ta ko ina.

   Mikewa tayi a fusace tana nuna mai kofa tare da fadin fita min daga gida tunda kai bakasan abin arziki ba.

   Kai ko kunya bakaji kazo ka kalli idona kace wai aurena kake son yi don kawai kunga kasa ya fufewa mijjna ido.

   Yace shi kansh miijin maki ai da zai tasone a yanzu zaiyi alfari da abinda nake shirin aikatawa a yanzu.

  Eh na yarda lalai namiji baida kunya yau Adamu kaine da kanka wai kazo neman yardana akan in aureka don kasa ya gama rufe minin idon miji ko ?

  Har kamanta da irin tsana da kiyayyan da matarka ta saka min a gida lokacin da kuke ganin kowa a banza a idon ku shine yanzu don baka da kunya zaka dawo da wani zance a kaina.

   Matsalan ku ku mata ke nan dawo da abinda ya wuce baya kada ki hada wancan lokacin kurciya da yanzu garemu.

  Ni niyana na alheri ne gareki nasan ko yaran ki zasu farinciki da zaben dan uwan mahaifin su a matsayin mijin ki a yanzu.

   Ka fice min gida kafin in saka a fitar min dakai ta tsiya ya ce bazan gaji da tunkaran ki da wanan zancen ba har lokacin da  zaki sauko don kanki.

   Yana fadab haka ya juya ya bar gidan bishi tayi da kallon takaici da kunan rai wanan yana daya daga cikin abinda ya hanata dawowa kasan tun rasuwan mijinta.

   Yana fita gidan wuri motar shi ya nufa kai tsaye yashiga ya dade a zaune yana karewa gidan kallo yata da motar ya tafi.

  

    Mun kawo lokacin yamma baiyi ba sosai don la, asar ya wuce a lokacin kai tsaye gidan anty safiya muka nufa.

   Gidane tsarare mai ban sha,awa gaskiya ba laifi gidan ya hadu ni dai a ganina ciki muka shiga yayin da muka zauna a falo.

   Tau zainab kinga gida yau dai don har umma bata san inda muke zaune ba duk zumuntan mu da ita yau sai gashi ke Allah ya kawo ki gidana.

   Mikewa tayi zuwa wurin fridge ta dauko min ruwa mai sanyi a fridge ta aje min tare da fadin sha ruwa kafin ki shiga ki watsa ruwa kiyi sallah sai ki fito muci abinci.

  Daukan ruwan nayi da zuman sha sai naji sanyin shi yayi min yawa a bakina ta yadda bazan iya sha ba.

  Mayar da kofin nayi na aje saman dan table din ta dawo tana fadin taso in nuna maki dakin da zaki zauna kafin in kai gidan da zaki aikin.

   Dakine da gado sai mirrow ta nufi wani kofa tana fadin nan bandakine  ki shiga kiyi wanka da alwala ki fito.

  Tana fadin hakan ta juya ta fita daga dakin kayana na fara cire na nufi bandakin kamar wace za,a cewa na sheka na sheka da gudu.

  Ina shiga naja na tsaya wuri daya ina karewa wurin kallo da mamakin ban dakine haka a gyare tsab.

   Saida na gama karewa wurin kallo na nufi bakin famfon dake ciki badon na taba amfani dashi ba a fili amma dai nasan yadda ake kunnawa ruwa yazo.

  Don an koyamu a makaranta nagani wanka nayi a tsanake zuciyana fam da tunanen inna mu da yan uwana.

  Sai kuma tunanen Abban mu dasu Asabe irin maganganun batanci da sukeyi lokacin da zan baro gida don wai kawai ina ya mace suke min hakan.

   Sallah na tayar saman kafet din dakin ban tsaya neman sallaya ba don wurin tsab yake ni a ganina ina zaune a gurin bayan na idar da sallah.

  Sai ga anty safiya ta shigo dakin tana ganina kasa take fadin subbahanallahi zainab badai a kasa kiyi sallah ba sam na manta da na kawo maki abin sallah a dakin taso muje kici abinci ko ?

     Mikewa nayi na biyo ta zuwa falon na samu yaranta da sukaje islamiya sun dawo gida a  lokacin.

   Ku gaida anty tace wa yaran da suke kallona da mamaki a fuskokin su suka fara gaidani din kamar yadda mahaifiyar nasu ta umurce su.

  Wuri ta nuna min na zauna tana fadin ki saki jiki ki nan kamar gidane a gare ki zainab.

   Nakai zaune ina murmushi abincin ta debo ta kawo min a gabana tana fadin ci abinci nasan rabon ki da abinci tun safe.

   Kallon abincin nayi dan shikafane da miya sai taliya da ganye da nama tsoka uku a sama.

 Dan tsakura nayi duk da ya zamo min bakon abincin daya dace inyi dsukin cin shi a lokacin tunda ban saba cin abinci haka ba.

  Sai gashi halin da zuciyana yake ciki ya hanani cin abincin sai tunanen yan uwana da innarmu nakeyi a raina.

  Gashi yan uwa basu gida aka wuto dani balle ko sallama in samu inyi dasu tunda bansan tsawon lokacin da zan dauka a wurin wanan bautan ba dabazo yi garin kaduna kamar yarda umma tace.

    Bansan mijin anty yana gidan ba saida naji yana magana da yaran shi na dago da sauri ina kallon shi.

   Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana kallona tare da amsa min gaisuwan da nayi mai yake cewa.

   Itace kuka zo din tare eh yar dan uwanane sukai min karamci suka ban ita kaga abin yazo min da sauki ke nan.

   To Allah yasa a dace sai ki ja mata kunne sosai don kin san zama a irin  gidajen nan ba kowane zai iya rawayu dasu ba.

   Daki na mike zan koma anty ke fadin zaki shiga cikin ne kuma kifa sake jiki nan gidane na fada maki.

  Nace zan kwantane ina shiga naji mijin na anty na fadin wanan yar yarinyar suka turo ban san me yasa mutanen kauye suke da wanan akidar ba kan yaya mata.

    Yadda wanan rayuwa take a yanzu kosu masu dauko yarab dasun gane su dogara da shiga fadawa wani rikici sam duniyan nan cike yake da rudani daban daban.

   Sai dai daman ita wanan din da kika dauko ansan gidan su da kuma inda zaki kaita din in don haka ba gaskiya da zan baki shawara ki mayar masu da yarsu inda kika dauko ta.

  Nima kaina saida naje naji banji dadin ganin wanan yarince zasu ban ba don uwarta ba karamin rikici akayi da ita ba kafin ta yarda muzo nan din.

    Yace ke nan uwar tasan kanta da abinda take yi ga yarinya kallo daya zaikai mata kasan tana cikin wani yanayi.

    Zaka iya sani tunda aikin kune hakan ai don nuna fin karfi kawai aikai masu daga ita har mahaifiyar ta aka ban ita.

   Shine kuma kika dauko masu ya safiya baki tsoro  abinda kaje ya dawo nan gaba kada faki lalata maku zumunci .

  Wallahi don dai hjy iyami ce kuma na riga da nayi mata alkawarin hakan kaga idan na saba mata ba zataji dadin hakan ba.

  Yace Allah ya sauwa ka saidai kija mata kunne sosai kafin ki kaita na fada maki zama irin gidan nan akwai kalubalin masu yawa ga wanda bai saba hakan ba.

  


ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅7️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


RAYUWA KE NAN YAN UWA MU FADI ALHERI KO MUYI SHIRU SHINE KOYI DA SUNNAN ANNABI SAW , , , , DON ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KI GUJEWA KAYAN ALLAH YA ISA A KANKI


   2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 300 NE KACAL ZAKI TURA SABODA ALLAH SHINE HAKKINA GAREKU.Na dade kwance a dakin badon nayi barci ba tun ina jin karan tv da muryoyin su a falon har nazo na daina jin komai ina jin anty ta shigo tana ja min abin rufa sai naji sonta na yan uwan taka ya kara shiga raina sabanin dazun da nake jin haushinta ina ganin da hadin bakin ta wurin rabani da yan uwana da innan mu.

  Tambayan kaina na karayi karo na batkatai mai Asabe da lantana suke nufine a kaina.

  Mau ye lafin innar mu da bata ganin laifin Abba shi tunda ba inna kadai ta haifomu a mata ba.

    Meye laifin kasancewar yaya mata da asabe ke gani ga innan mu damu wanan halin shi a kowani gida da yaya mata sukafi biyu zuwa ukku kamar mu.

   Ba addinine yace a kyamaci diya mace ba wanan hain rayuwane na wasu mutane da hakan ya zama masu al,ada.

  A ganina duk da da aka haifa ta sunna walau mace ko namiji albarkan rayuwa ya kamata iyayye su newa yaro.

  Ni dai ba zan iya cewa nayi wayau naga inna da Asabe a cikin dadin raiba a gidan mu duk ko da irin biyayyan da ina ke mata sau da kafa.

   Ba zan manta a da can baya har talla asabe ta fara dora min idan na dawo boko zan dauki tallan goro ko gyada in fita dashi duk da ina kankanuwa a lokacin.

  Da kyat Abba ya samu ya hana wanan tallan ranan kan yasha fitina wurin Asabe ba Abba kawai ba har innan mu ba,a barta ba don cewa Asabe tayi inna ce ta zuga Abban mu don tana bakin ciki ina fita mata talle.

  Haka muke abu kamar marayu a gidan mu bawai don mun rasa uwa da uba a raye ba sai don kawai zama da fitinaniyar uwar miji da Allah ya hada inna da ita.

   Yanzu kuma tsanar yakai har Asabe ta turoni yin aikatau a birni ba tare da kowa ba gidan mu yasan inda za a kaini ba.

   A haka naci gaba da sake saken abinda zan tafi in taras gidan da Anty safiya zata kaini din.

  Juyawa nayi ina lumshe idanu tare da fadin Allah yasa hakan shine alherin mu gaba daya kamar yadda anty safiya ta fadawa inna da zamu zo.

   Har barci ya daukeni ban sani ba ga dai gadon laushi ga fanka a dakin na samu amma haka bai hanani barci a cikin damuwa ba.

   Karfe biyar da wani abu na falka kamar yadda inna ke tayar damu don sallah asuba idona bude nabi daki da kallo .

  Sai a lokacin na tuna da inda nake a yanzu da sauri na sauko saman gadon na fada bandakin dake dakin da nake ciki .

  Alwala nayi a gurguje na fito na tayar da sallah ina idarwa na dan zauna nayi addua kafin in mike na bude kofan a hankali na fito dakin.

  Duk da sauran duhun dare gari bai gama haskawa ba a lokacin amma na gane hanyan kitchen din anty safiya da jiya naga tana shiga tana fitowa da abinci.

    Wanke wanke na sama tare a kitchen din ban tsaya jiran komai ba na shiga wanke su a hankali don kada in tayar da mutanen gidan don har lokacin banji motsin kowa a gidan ba.

   Na gama na share kitchen din na fito zuwa falo na fara shara da kakabe kujeru da suka kewaye falon can naji motsi alaman wani na fitowa daga dayan dakunan su na kwana.

   A, a naji muryan anty safiya na fadi zainab kece a nan kuma har kin tashi ashe ban sani ba yau na gajine sosai dan tafiyan nan da mukayi jiya duk jikina ciwo yake min wallahi.

  Ban bata amsa ba sai kaiwa da nayi kasa ina gaida ita da kwana ta amsa min a gurguje tana shiga kitchen din ta.

   Sai kuma gata ta fito tana fadin ke yaushe kika tashi halan da kikayi wanan uban aikin haka zainab kin koyi barci da dare ko kin kasa barcine kina tunanen gida.

    Nace nayi barci dana tashi nayi sallahne na fito na wanke su tace ikon Allah toh sannu da kokari ashe tafiya zatayi kyau tunda baki da son jiki haka ?

   Abinci ta hadawa yaranta yayin da ni kuma na share ko ina na gidan sai gaidani da aiki takeyi tana fadin kinga idan har zakici gaba da hakan ina mai tabbatar maki zaki ji dadi sosai a wurin hjy.

   A raina nace watau ma wurin hjyce za a kaine kenan matar mai kudine tunda naji harda hjy anty ta kirata matar yanzu.

   Ni tace in shiga in shirya yaranta a wani daki nayi ta bin dakin da kallon mamaki a raina tana min bayanin abinda zan masu.

   Ta fita ta barni da yaran a dakin ina shirya su bayan nayi masu wanka da broshe tsab suka fito a tare muka fito daga dakin tace dani kinga koma ki gyaro min dakin nasu in karasa shirya su a nan.

   Dakin na koma na fara tattara kayan da suka watsar kafin in hau gadon dakin da gyara kafin wani lokaci sai ga dakin tsab dashi kamar bashi bane suka bata dazun da tarkace ko ina.

  Nan anty safiya ta yaba min sosai tana kara min bayanin kinga tun da safe idan kin tashi kinyi sallah.

   Kada ki tsaya sanyin jiki ki yi duk wani aikin da kika san naki ne a gidan tunda kina da kwazom tashi haka da safe.

  Don Allah zainab kada ki yarda ki bani kunya don inda zan kaiki nima gidan kunyanane can tayi bugun gaba ne dani tasa in samo mata yarinya natsatsiya mai kwazo da  tsabta da amana.

   Idan kinga abu ba a baki ba kada ki yarda ki taba shi komai son da kikewa wanan abin a ranki.

   Na amsa da to anty tace zaki ga kudi kamar a banza mai yuyuwa zata gwada ki na dan lokaci taga idan kina da amanan hakan kafin ta yarda dake bandai sani ba.

   Zan fada mata gaskiya ke din yar uwatace ta jini don ba zan lamunci suyi maki wullakanci irin wanda akewa yan aiki ba ke kuma sai ki rike min amana sosai don Allah wanan abin taimakon kai da kai zamuyi tsakani nidake zainab.

   Insha Allahu anty na fada don idan ta kirani da zainab din nan yanzu sai inji kamar badani take magana ba.

   Wasa wasa na share sati daya gidan anty safiya banji zancen tafiya gidan da za a kaini din ba,  nima kuma ban tambaya ba.

    Ashe hikimar ta na barina a gidan ta don dai in koyi wani abinda ta fahinci ban sani ba kada ta kaini a sha wuya a can .

  Gashi kullun cikin yi min bayani take da fahintar dani komai na rayuwa a birni wanda mu can kauye bama yin su.

  Har na dan fara sabawa da yaranta yanzu sosai ranan da dare muna zaune falo muna kallon wani shiri na yara naji anty ta ambaci sunana .

  Hakan yasa na juyo ina kallon ta cikin ladabi take fadin ina ganin gobe zan kaiki wajen hjy dazun muyi waya da ita take tambayana ke .

    Wani irin ba dadi naji a raina lokaci guda damuwa da fargaba ya dira min a zuciyana lokaci daya.

    Ganin canjin yanayina take fadin ki kwantar ds hankalin ki can ma nafada maki gidane a garemu ai tunda gidan babban yayan mu ne saidai shi a yanzu bai raye matarce kawai da yaran su a gidan kuma yaran ba yara kana bane sun girma kananan ma zaku zo yan sa,a daya dasu.

   Sai dai daga mazan har mata kada ki shiga tsabangan kowa duk abinda suka saki indai baya kaucewa idini bane wanda kuma ya shafi gaban kowa a cikjn gida kiyi.

   Na fahinci may anty ke nufi a nan ma, ana na kama mutuncina da kimata ga kowa a gidan dai.

    Haka na kwanta da tunane mai yawa sai kewan gida ya dawo min sabo sosai a raina don haka ban samu barci sosai a ranan saboda tunane.

   Karfe goma na safe muka bar unguwan su anty safiya wanda nake jin ana kira da barnawa muka doshi inda zasu kaini a motar mijin anty safiya din.

   Anty ta ban wani jakka nata na saka yan kayana wanda ta sai min kala hudu dana zo don tace nawa ba zasu tafi ko ina ba a haka.

  Sai bin garin nake da kallo yayin da anty suke gaba da mijinta zaune suna dan hiran su da ban san ko a kan wa suke zancen su ba.

   Kafin mu bar gidan anty safiya sai da sukai min nasiha sosai mjin anty safiya yace in kiyaye ibadana inyi hakkuri da duk yanayin da zangani a gidaba, ainyi biyayya ga wa yanda na sama a gidan.

  Shiga nan bullo nan har muka kawo unguwar mai kama da kasan waje muka fita ba jahata na kaduna ba.

   Uguwar kanshi abin kallo ne ba mutane sai motoci jefi jefi da suke wulgawa saman shimfudeden kwaltan da aka zuba a titin.

  Idan kaga wanan ginan sai kace shiyafi kyau sai kuma idan kaga wani kallo ya koma sabo.

  Wani katon gida daya tafi da imanina tundaga nisa mijin anty ya tsayar da motan shi yana danna horn.

  Kafin wani mutum daba tsoho ba ya fito yana dan lekowa naji anty na fadin bude get mune da mijina.

   Ya amsa yana washe baki tare da saurin komawa sai naga kofan na budewa kamar injin.

   Ya danna kan motar zuwa cikin gidan naji mutumin gidan yanayi masu sannu da zuwa da alama dai yasan anty din sosai .

     Saida mijinta ya tsayar da motar shi ne take fadin amma dai kasa yau zaka shiga ku gaisa da hjy ko ?

    Yace zan shiga kodon ta san yarinyar nan tana da muhinmaci sosai a garemu ai don ni dai da kinbi tanawa da ba, , , 

   Please dear ina mun gama wanan zancen tun a gida sai kuma ta juya da harshen turanci tana magana.

  Ko ta dauka bokona baikai indanji abinda take fada bane oho do maganan da sukeyi da alama mijin nata yace a mayar danine kota rikeni tunda yar uwarta nake.

   Allah sarki nace a raina wanda ma suka haifeni suka san zafina sun kasa  barina a gaban su balle anty da daga sama ta ganni haka.

    Don ina jin tana fada mai taso hakan amma kawo ni nan din shine mafita a gareta naji yace to shike nan Allah ya tsaya mata da hausa.

    Su suka fara fita daga motar kafin anty din ta zagayo ta bude min gefen da nake tana fadin in fito.

    Na fito sai bin gidan nake ko ina da kallon mamaki ina rayawa a raina wai yanzu mutane ne sukai wanan ginan haka da hannun su ?.  

    Nidai ina bisu a baya ina karewa gidan kallo ta danna wani abu a bango ba, a dauki lokaci ba sai ga wata yar dattijuwa farace tafito tana fadin waye sai sukayi arba da anty dake tsaye a kofa.

    Hjy kece take cewa anty safiya nice kande ko  hjyn tana ciki ta tambaye ta  ?

   Tana nan yanzu ko tashiga daga cika ta fadi tana matsawa daga kofan da take tsaye.

   Shiga mukayi kai tsaye saida naja baya don abindana fara takawa ko ina na falon sai kyali yake da daukan ido.

     Zama sukayi a kujerun dake katon falon yayin da nakai kasa daga gefen anty din mijinta ya kalleni tare da fadin ki zauna saman kujera mana.

  Naji anty tace kasan ta ai da halin su na yan kauye barta kawai zata zo ta saba wata rana ai.

    Matar da naji anty ta kira da kande ne ta dawo falon dauke da tire da abin sha a ciki.

  Ga kan shin girki yana tashi a wani bangare na gidan duk da kamshi  da falin keyi bai hana na girkin ziyaran hancina ba.

    Ga abin sha hjy kafin hjy ta fito,  ta fada tana ajewa a gaban su bin abinda ta aje din nayi da kallo.

  Saida suka dan taba hira da mijin ta muna zaune ni dai sai bin hotunan dake tsaye a falon manya manya dasu kamar mutun ne tsaye a wurin nakeyi da kallo.

   Sai ga matar gidan ta fito da fara,a a fuskanta tana fadin ashe kuna tafe yanzun nan na shiga ciki.

  Tun safe yaran nan suka tayar dani da rigimar su na fito tarba na mutunci naga tana masu tana saki fuska da jiki dasu.

   Ta kalli mijin anty tana fadin yau baka fita aiki ba ke nan ta fada tana kallon shi.

    Ban fita daga nan zan wuce ya bata amsa da kara fadin yarinyar nan muka kawo dama.

  Ta juyo tana kallona tare da dan kuramin ido na dan lokaci tace masha Allah.

  Yarinya kamar kin shiga zuciyana kinga irin age din da nake so ta kasance min gashi ko kin samu ai anty safiya ta bata amsa.

  Menene sunan ki ta juyo tana tambayana kafin ince Abu naji anty safiya tace zainab ce sunanta.

   Kai zainab kice uwata ce ashe yarinya kin samu suna mai kyau kuwa tana kallona da kulawa.

   Aikuwa na manta sunan mama na unguwar rimi ke nan fa dacewa kanwar mahaifiyar hjyn .

   Mijin anty ne yake fadin ni zan tafi hjy don Allah sai a hada da hakkuri don kin san yarinyar akwai kurciya da kauyanci a tare da  ita yanzu.

   No no no kada kuji komai wallahi muma ai kauyene asilin mu a da ko kowa ka gani daga kauye yake ai.

   Shigowa wasu yara kanana su biyu mace dana miji falon yasa zancena ya tsaya a nan suka juya magana kan yaran.

  Anty ke fadi a a ashe mutanena suna nan sai hjy tace wai yau hutu sukeyi basu je school ba sun shiga meet time break ne.

    Hannu anty safiya ta mika masu suki tare da make kafadun su suka nufi sirin kakan su kai tsaye.

  Tafiya ya fara yi tare da fadin to zainab a kulla kinji banda rashin ji anty safiya tace in tayi rashin ji ai zata gamu da nine sosai.

  Karfe nawa zaka dawo yace na fada maki sai yamma don haka idan kin gama ki koma gida don yara kada su dawo school bakya nan.

     Wai har yanzu motar bai tashi bane hjy ke tambayan anty motar ta kafin anty tace wanan motar ai sai wata yanzu gashi yaki ya saya min wata ina ta faman bin shi yana ja mi rai.

    Ki bar kanina ya huta safiya indon motace zan sa a duba maki idan ba zaki raina ba dai kai kai kai kice wanan zuwan takice ashe mijjn ta ya fada .

    Kasan ai safiya ta hannun damana ce sosai tafi danan a gurina in dai tana so.

   Ya tafi tare da ma hjy sallama nabishi da dan kallo kamar ince don Allah kada ya tafi ya barni.

  Anty ta mike tabi bayan shi bayan tafiyan tane falon ya danyi shiru tana ta danne danne a wayan ta sai ga anty safiya din ta dawo falon.

   Zama tayi sukaci gaba da hira a cikin hiran nasu ne take fada mata yadda muke da ita .

  A hiran na kara fahintar irin zumuntar dake tsakanin mu da ita din wai ashe mahaifiyar su da Asabe ce ya da kanwa.

    Asabece ya mahaifiyar su kanwarta tace kai kice min ita din ta gidace ashe eh ta gidace gaskiya sai dai gaskiya kin san yadda zumuncin zamanin nan yake ai.

  Koma dai yaya ne ai takice ita zan duba inga yadda zamu zauna sai ta kira wanan matar ta dazun data kawo ruwa tana fadin.

  Kande ga bakuwa ki bata daki wanan na kusa dani zaki bata don ni tazo gidan nan don kula da harkokina.

  Don haka zaku zauna tare sai dai kowa da aikin shi daban ke naki kula da kitchen ne da sauran ayukan da kika sa kinayi.

  Ita din dai ki barta dani sai zuwa gaba idan ta saba zan fara nuna mata aiyukan ta yadda ya dace.

    Sannu da zuwa kande tace min tana kokarin daukan jakkar kayana da anty ta shigo dashi ta aje a kuss dani.

  Kagin anty tace na karbs ni har na mike ina karba matar na fadin ai da ki barta bakuwace fa nace a a mama kawo in dauka.

  Jeki ta kaiki daki  da zaki zauna kafin in shigo hjy ta fada tana dora kafanta saman dan table din dake kusa da ita.

   Muka nufi cikin gidan wanda bai isata da kallo matar na gaba ina binta har zuwa cikin dakin da akace ta kaini din.

   Dakin ta bude tana fadin bissimila shigo daga ciki nabi bayanta muka shiga.

    Wanan shine dakin ki sai ki zauna ki huta kafin girki ya sauka  a wuta muci ni nawa dakin yana can daga waje kadan ta hanyar kitchen idan kina nemana.

  Daga haka ta juya ta barmin dakin ina tsaye sai bin dakin nakeyi d kallo nida ke santin gidan anty safiya sai gani a wanan dakin da fadin tsaruwan shi bata lokaci ne.

    Anty safiya bata bar gidan ba sai karfe dayan rana bata tafi ba saida ta shigo dakin ta kara min nasiha kan nayi biyayya ga kowa a gidan .

   Ta tafi ta barni cikkn kadaici da damuwa a gidan da ban san kowa a cikinsa ba ban ma san a inda nake ba dai.

   Wani irin kuka ne na rushe dashi ganin ta tafi ta barni daga ni sai halina sai wa yanda a yanzu zan zauna dasu din.

   Ganin kuka ba zai min bane yasa ni tashi na shiga bandaki dukda ba a nuna min ba dan zaman da nayi gidan anty na dan fahinci ya ginan birni yake yanzu.

  Alwala na dauro nazo na tayar da sallah ban daga ba na dade a wurin ina addua kafin na dan kai kwance sai ga barci ya daukeni a haka  ba tade dana sani ba a wurin.

  Babu komai a raina sai tunanen halin da mahaifiyata take ciki a yanzu tare ds yan uwana a raina.

  Nasan innan mu zata kara shiga wani hali a yanzu don barina kusa da ita dan taimakon su daya ne wanan kudin da ban san ko nawa bane da anty ta bata da zamu zo.

  Irin wanan tunanen nakeyi sai hawaye yazo mi lokaci guda don tunanen hakin da inna zata shiga yanzu da ban kusa dasu dama da dan kudin kitson da nake muke tallafawa ake samun abinda akaci.

  Gashi yanzu lantana da Asabe sunyi makarkashiyan da aka raba tsakanina da mahaifiyata da yan uwa anya zan iya mantawa da wayan nan mutanen a raina kuwa , ?

.


    ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


8️⃣


   ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH KA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN RANAN TA JUMMA,AT ALLAHUMA AMIN , , , , , , 


DOMIN SAYA SAI KI TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DON KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , , , , , Ni Abu ban taba tunanen zan gani a cikin irin wanan dakin ba ko a mafalki ban taba hango wanan irin gidan a malkina ba.

  Yau sai gani nayi barci na falka na ganin cikin wanan gidan ga sanyin AC da kande ta kunna kafin ta fita ya hade dana  ties din dakin yana ratsa balgon jikina a hankali.

   Duk da sanyin yana damuna ban tashi a yadda nake kwance ba a kasan na dunkule a wuri daya sai faman tunane nakeyi na rayuwa.

   Muryan hjyn ce yasani dagawa daga inda nake kwance wanan karon ta sauya kayan dake jikin ta zuwa dogon riga mai laushi da daukan ido jikin shi wani dabbara dabbara ne kamar jikin zabra.

    Taci gaba da fadin ke zainab bakya gudun sanyin kasan nan ya ja maki illa kiyi ciwo fa.

   Da sauri na dago ina gaida ita dakin take bibda kallo ta sauke idon ta ga jakkan kayana tana fadin ga wardrobe nan ki saka kayan ki a ciki .

  Taci gaba da fadin ki dunga kula da kani ki kula da tsafta sai muyi zaman mu lafiya.

   Mu gaimaki juns tsakanin mu don kingani nan bana shiri da wanda baida tsafta sam.

  Iyakar sikin ki a gidan nan yanzu shine kula da sashina da komai wanda ya shafi rayuwana a cikin gidan nan.

  Yarana duka manya ne kuma duk zasu girme maki kinga kenan suna matsayin yayyin ki ne.

   Ni a yanzu yar kasuwace kuma mai rike da mukamin gwanatin kasan nan .

  Kinga ina da manyan hidimomi a tare dani wanda hakan yasa banda lokacin kaina shine dalilin da yasa nace a samo min yarinya da zata dinga taimakamin.

   Sai gashi ke Allah ya nufa a sama min na kuma yaba da irin yanayin dana ganki dashi na natsuwa .

  Ina fatan zaki zauna damu gaba daya gidan nan da zuciya daya cikin amana da yarda.

   A hankali na dago kai tare da fadin insha Allahu hjy nayi alkawarin hakan.

   Ban iddasa rufe bakina ba tace ba hjy nake a gurin ki ba mami nake don ni uwarkice a yanzu ki dauke ni yadda sauran yaran gidan nan suke daukana.

   Da fatan kin fahince ni tace ta fara tafiya don fita dakin tare da fadar ki fito kici abinci a falo yanzu idan kin gama saka kayan a ciki.

   Na amsa da to hjy da sauri nace mami tayi murmushi ta fita yayin da baki na yake dafe don katobaran dana farayi.

  A gurguje na jera kayan kamar yadda tace saidai saida nasha wahala wurin gane yadda zan bude wardrobe din.

   Falon na fito na dauka ita kadai ce kamar dazun sai dai naga sabanin hakan don  sun kai su gama zaune wurin a ganina.

    Ja nayi na tsaya dan nisa kadan dasu ban karasa wurin da suke ba hjy ce ta dago tana fadin.

   Zainab zo ki zauna mana kici abincin tana kallon inda naja na tsaya dan nisa dasu kadan.

    Firgigit nayi daga sana,ata dana fara watau  tunane don yanzu ya zama min abin yi ko yaushe.

   Sai lokacin sauran dake zaune suka farga da fitowana falon gaba dayan su juyowa sukayi suna kallona lokaci guda.

    Karaso mana kizo nan ga abinci nan ki diba ta kara fada sai naji sun kwashe da wani dariya.

   Wai mami sabuwar  mai aikice kika dauko kuma take tambayan hjy tare da juyawa taji amsan da zata bayar.

    Haba dai mai aiki a haka kuma sai a rasa wace za a dauko aiki sai wanan yar kauyen haka irin yan kauyen nan fa wahalan sha,ani garesu kafin kansu ya waye don basu iya komai ba sai shirme da kauyanci wata yar farafara ta fada.

  Dayan ta yamutsa fuska tana fadin but she is dirty mami don Allah kada ta karaso nan inda muke.

  Ai kin san halin hajjajo da son mutane yanzu haka wani wurin ta kwasota itama ya fada yana mayar da kai ga abincin da yake ci.

   Yar uwan gwaggon Safiya ce kuga kenan kuma ta zama yar uwarku ai .

   Yanzu a nan gidan zata zauna damu ke nan ko dai tazo yin wani abune Rufaida ta tambaya a yatsune ?

    A haka mami zata zauna damu Nazifa ta fada tana kyabe baki tare da fadin ashe zamu sha kauyanci a gidan nan kuwa.

  Hjy tayi murmushi tana fadin in dai wanan da kuke ganine cikin kwana biyu zata goge ta zama yar birni tayi fes kamar kowa.

   Dariya suka sa gaba dayan su a lokaci guda nidai ina tsaye a inda nake ina kallon su kasa kasa ina jin cin mutuncin da suke min.

   Zainab kinja kinyi tsaye karaso mana ki dibi abinci kici hjy ta fada tana yafutoni da hannu.

   A, a mami don Allah dai karta matso nan ta bari idan mun gama sai ta zo ta diba amma ai haka raina mu zatayi ta dauka daya muke da ita.

  Tsawa hjy ta dakawa mai maganan tana fadin karna sake jin haka daga gareki ita din ba mutum bace kamar kowa nima a haka mahaifin ku ya daukoni ai.

   Shiru sukayi suna cigaba da cin abincin su yayin dana karaso inda hjy take na dan labe ina kaiwa kasa na fara gaida su.

  Ku duba yadda ta baku girma yanzu a cikin mutunci amma ku kuna kokarin zubar da darajan ku a idanunta,  baku san cin fuska baida dadi ba.

   Shiru sukayi kowa na kai abinci ga bakin shi tashi ki dibi abinci hjy ta sake fada karo na barkatai.

    Plate wace batai magana ba ta jawo ta fara zuba min salma ke nan ta juyo tana fadin may za, a zuba maki ?

    Na nuna wanda ke cikin plate din dayan namijin dashima baiyi magana ba sai kallon banza da yake min.

   Dariya suka kwashe dashi ya dago kai yana tambayan menen suke cewa choice din ku daya da yarinyar nan abincin ka ta nunafa.

  Ware idanuwa yayi waje tare da fadin ke ni sa,arkice bakiga kowa ba a wurin nan saini halan.

   Yana fadin haka yai kwafa ya ture abincin ya tashi daga wurin sai suka kara fashe mai da dariya.

   Miko min abincin tayi na karba tare da dan rusunawa ina fadin nagode na juya zan bar wurin naji hjy na fadin ina kuma zaki tafi kici abincin ?

   Dan marairaicewa nayi ina fadin dakina hj, ,  mami ba zaki sake jikin ki ba har yanzu kina kewan gidane ko nidai na danyi murmushi na juya na tafi.

   Ina kallon abincin wai duka wanan naman da aka zuba a ciki nawane ni kadai kai yan birni kan suji dadin su.

  Wanan ai shine zamuci duka gidan mu da sallah idan yazo don sallah kadai muke cin nama sai ko idan rabo ya ratsa Abba ya sayo muna a ci.

    Gaba daya na cinye abincin tas na dauko plate din zuwa kitchen don na fahinci a nan kitchen din yake dazun da mama kande ta fito da abinci.

  Na canka daidai na samu baba larai tare da wata mata tana juya miyan da zasuci da dare miyan kaine saidai ban san ko kan me bane na daiga ya ciko tukunya sosai tana motsawa.

   Gaida su da aiki nayi kande ke fadi kin kamala ci yar nan ina jin marasa ta idon gidan nan dazun sunayi maki shakiyanci da suka iya.

    Ki fita batun su dan haka halin su yake da rainin wayau tsiya tundai in sun raina da kuran mutum sai suso su raina shi.

   Don ma hjy tana taka masu burki aida abin nasu yafi nan wallahi dayan matar ta fada.

    Inda wanke wanke suke na nufa na shiga hadawa da sauri kande tace yar nan me zakiyi nace wankewa zanyi mama.

  Rufa min asiri kada hjy tazo tagane ki tace na baki aikin da yafi karfin ki ko dazun saida ta kara jaddamin zance a kanki.

    Zan iya ai basu da yawa na fada ina kokarin hada kayan wa yanda sukaci abinci dasu da yamma.

    A gurguje na wanke kayan tas dayan matar da ake kira larai tana saka min albarka na kare tare da fadin aikwai wani aikin da zanyi kuma mama na tambaya ?

   Babu yar nan sai dai kizo muje dakin hjy na fara gwada maki aiyukan datace a nuna maki na bangaren ta.

   Hannu ta dauraye tana gaba ina binta baya muka nufi inda sashen hjy yake don gyarawa a kofa muka tsaya.

   Tana kwankwasawa kafin a bamu izinin shiga daga ciki hjy tana kwance kishingide saman wani kujera mai kaman gado a dakin.

  Ga wani abu babba kamar waya a gaban ta tana latsawa ta dago tana fadin kande baki bar yar nan ta huta ba yau yau da kawota.

   Ai sai taga aibun kan hakan to hjy nayi laifi wai gani nayi dai ta fara sani tun yanzu ai ba aikin zatayi ba a yanzu gani kawai zatayi ta koya.

  To shi ke nan hjy ta fada tana mayar da hankalin ta wurin abinda takeyi a lokacin.


          KAUYEN  ANCAU


Iska na wahal da mai kayan kara a gidan nan yarinyace dai ta tafi ba dawowa zatayi ba balle mutum ya shige daki yaki fitowa.

    Lantanace ke magana ita kadai a tsakar gida inna na daki tun bayan tafiyan mu har yara suka dawo boko suka tafi islamiya taki fitowa waje.

   Gashi sai tambayana suke inna ina yayar mu bamu ganta ba tun dazun tace dasu ta fita kawai daga haka kowa ya shiga harkan gaban shi.

   Sun tafi islamiya sun dawo sun samu inna a yarda suka barta haka yasa saratu mai dan wayau a cikin su sake tambayan inna.

  Inna wai lafiya kike yau kuwa ina yayan mu tajene tun dazun bata dawo ba kuma ban santa da zuwa unguwa haka ba ai.

   Hawayene ya fara zubawa inna da sauri saratu ta juya wurin jakkan kayana tana dubawa tare da fadin inna sun dauke yayan mu sun turata aikatau ke nan ?

    Wani irin kuka inna ta kara fashewa dashi lokaci guda saratu ma kukan ne yazo mata sai hakan ya jawo hankalin sauran yan uwan mu dake wasa kofan inna.

    Saratu ke fadin wayo yayan mu ki dawo kada kije aikatau don Allah an ce ana lalacewa wurin aikatau din nan.

   Haba dakin inna ya koma dandalin kuka da tashin hankali don kuka sosai yaran keyiwa inna.

   Da gudu lantana taje ta kira Asabe tana mayar mata da karya wai ga inna can ta tasa yara a gaba sai kuka sukeyi don tafiyana.

   Asabe ta fito babu ko dan kwali a kanta sai a hannu ta rike tana fadin bamu cikin abin kuka da yamman nan .

   Kuyi muna shiru masu mugun manufa da sheri don tafiyar yar uwarku zaki zauna ki dasa muna kuka ke da yara haka kamar anyi mutuwa a gidan.

   Asabe wallahi sai kin dawo muna da yayan mu ko zaman gidan nan ya gagareki keda munafukanki da cewa lantana.

    Mara kunyar banza da wofi koke can kika nufa idan naji dadin yar uwanki ana turo min kudi irin haka marasa hankali kawai.

  Da kuna zaune a gida kara zube ina zamu samu irin kudin da muka samu yau a gidan  ba gashi har kun dawo kun samu anyi abinci ba yau.

   Kowan nan sai ya dandani wanan hanyar aini yanzu gaba haihuwan ku ya kaini tunda na samu mafita daku.

  Ana cikin hakane Abba ya shigo yana fadin yaya yayane tun a kofa nake jin muryan ki umma.

  Asabe tace barni da mutanen kawai din nan wai tafiyar yarinyar nan yahanasu ta saka yaran nan a gaba suka mayar muna da gida gidan makoki.

    Yahanasu kina da hankali kuwa ke yanzu idan kina da tunane ai wani nauyi aka rage maki  Abba ya fada.

   Fada mata dai ko zata gane hakan ina nan gashi dan kudin da hajiya ta fara bayarwa kowa ya fara amfana dashi gidan nan ba gashi kunci shinkafa da wake ba yau a gidan.

  Umma kyale ta barin ganta ni yahanasu har mamaki take bani yanzu kan yarunyar nan babu nuna kawaici a kanta ko kadan.

   Idan ma bata nuna ba ita ta sani nidai na nuna mata nike da iko da abina daga diyan ko har kai a gidan nan ko wa yan nan na samu mai daukan su bayar dasu zanyi zuwa birni.

  Ba saki bada muba tunda ke kika haife mu cewan Saratu sai inna takai mata duga daidai Abba na shigowa dakin inna din.

   Bar dukan ta rabuwa da dan uwa nada zafi tundai irin wanan na yarsu nima dai ba haka naso tafiyan nataba kai tsaye so nayi muje tare inga wurin.

    Koma dai menene yanzu aikun nuna min kukeda yarku saidai ina son ku sani naji umma na fadin har wa yan nan za a tura min can birni aikatau.

  To wallahi hakan ba zai yuyuba wanan ya isa haka idan da hali dawo da yata zanyi gabana yafi mun kwanciyar hankali idan kasa mukeci mu kwaba muci tare.

  Toto to ya isa haka yana sa hannu ga aljihun shi ya ciro yan dubu guda biyu yana fadin ga wanan kya samu ko sabulun wanki ku saya.

   Da da nake saya kai kake ban kudi katafi da kudin Allah ya isan ka can kuci ku kadai ku gani.

  Kwadan ku ya fada kun raba ni da yata kun rabata da gatan ta da Allah yai mata don kawai tana diya mace.

   Shiru Abba yayi don inna bata taba tsayawa ta fada mai magana ba haka kai tsaye irun ranan.

  Kwafa yayi ya fita bayan ya mikawa saratu kudin yana fafin karbi ki aje mata idan ta sauko zata karba a wurinki.

  Yana fadin haka ya fita daga dakin don kada yayi laifi a gurin lantana dake tsaye ta rike kugunta tun shigan Abba dakin inna.

   Yana fitowa fuskanta ya fara kallo ta watsa mai wani harara ta  juya zuwa dakin ta shima abba yasan sauran zancen ranan a guri lantana don haka wani dabara ya fado mai.

   Yana shiga dakin ta juyo zata fara fada yace me zakiwa fitina kin san dai ba zama nayi a can ba rufe mata baki nayi da dubu biyu ke kuma ga naki dubu biyar ki rike.

   Sai lokacin lantana ta dan saki murmushi tana fadin wallahi yau Allah yaso ka da kakoma can ka kwana surin tsohuwar matar ka

   Nina fara hakan gani da dalleliya kamar ki inje dakin da warin fitsari da  kwamatse ya ciki.

   

      NEW G R A KADUNA 


A hankali mama kande take koyar dani komai duk wani abinda ya shafi mami da zirga zirgan ta na cikin gida nice mai mata hidinar shi..

   Da na zauna zaki ta kirani da zeey zan amsa da na,am mami in zo da sauri don biya mata bukatun ta wanda ba wani aiki bane.

  Sai dauko min kaza jiki mayar da wanan a cikin wardrobe ko dauko min ruwa shine aikin nawa kawai dawai mami bata iyawa sai an dauko mai mata wanan hidimar da ban daukeshi a aikin komai ni.

   Sai gashi cikin sati daya kacal na gane komai na mami nasan lokacin tashin ta daga barci .

   Zan shiga dakin in gyara gado in wanko mata ban daki zan koma in hada mata ruwan wanka tana zaune tana lazumi don mami akwaita da yawan ibada sosai.

   Zan dawo dakina in jirata tana tashi zata kirani in dawo in share dakin duk da ba wani datti ke ga dakin ba amma kullun sai nayi gyaran shi sau biyu a wuni.

    Kafin ta fito wanka nagama hada komai sai in koma dakina can kuma idan ta fito zata kirani da zeey zan zo in je dining in hada mata tea wanda wani ruwa ne baki kawai sai dan sugar kadan bata shan madara da suga ita.

    Idan na gama zan koma dakina inyi wanka in shirya in dan huta kafin ai mi wani kiran kuma inzo.

   Kai masu kudi suna shagalin su banda abin aikin kudi wai wanan dinne aikin da aka raboni da gida do  shi aikin da mutum zaiwa kansa ba sai ya nemi mataimaki ba.

   Amma hjy gashi tana ganin ina aiki sosai sai fadi take yarinyar akwai kwazo da sanin ya kamata.

  Do ita gani take yanzu komai na zuwa mata da sauki a nata bangare har zata samu tayi barci ta huta na dan lokaci. 

   A bangaren yaran gidan hjy kuwa ba ruwab su da shiga tsabgata nima hakan ne dasu.

  Saidai su wani lokacin zasu sakani wani aiki a gidan wanda ya shafi rayuwan su suma ga tsana karara da ko wace ke nuna min.

  Dan gara salma da har yanzu ba zance tsanane ko tausayina ba a ranta don na kasa fahintar inda ta dosa dani a ranta.

   Wani lokaci inji sanyi a wurin ta wani lokaci kuma idan ta daka min tsawa sai na gigice don tsoro.

  Ita irin mutanen nan ne shiru shiru da mugun ta don surutu bai dameta ba ko kadan za a zauna wuri ba zakaji bakin ta ba sai wani lokaci ta furta idan ta furta daya kuma shike nan.

   Duk wanan abinda suke min bai damuna naka ma raya a raina idan naga sun dau wanka zasu tafi school nakan ce inama a ce nice a matsayin su haka.

  Nasan da ko Asabe ba zatayi gigin takani ba balle lantana dana tsana fiye da kowa a gidan mu yanzu.

    Ni dai na rasa dalilin da yasa yaran gidan hjy suka tsaneni a baki dayan su in ka debe hjy da mama kande da suke nuna min kulawa a gareni.

  Tun dai ace yan matan don a fili suke nuna min kin jini da kyama duk da yanzu nasan nima ina tsabta fiye dacan da nake Ancau din mu.

  Na kanyi tunane indon dun kauyancine da kazanta yazu duk na daina wanan a ganina do na canza nayi fes na kara zama shar kamar bani ba.

   Ga mai da turare na yan gagu da hjy taban tace in dinga shafawa idan nayi wanka gun kashe gari dana zo.

  Komai ina yi  shi a taka tsamtsam a gidan ban yarda in ketare iya inda aka ajeni ga aikina dan dama wani lokaci idan zama ya isheni nakan shiga kitchen in taya su mama kande aiki do  su basu da hutu kamarni.

 Ko yaushe a cikk  girki suke dan hutun su kadan ne tundai idan yaran gidan suna gida wancan yace kaza yake so wana  yace baya cin kaza yau.   ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


9️⃣


YAR UWA NOVEL DINA NA KUDINE KIJI TSORON ALLAH KI BAN HAKKINA KAFIN KI KARANTA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI, , , , 


2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI TURO KATIN WAYA DARI UKU NE KACAL BA YAWA, , , , 


Ina daki naji muryan hjy tana kwalla min kira daga dakin ta nima na amsa da karfi da Na,am mami.

   Fitowana daga wanka ke nan lokacin don haka na dauki riga a gurguje na saka a jikina don zuwa amsa kira  hjy din.

    Na sameta zaune tana waya saman gadon da yasha gyara a wurina tunda safe nake gyaran dakin mami din don duk wani aiki da zata kai ga bude baki tace inyi kafin ma tace nayi din tunda yanzu nasan aikina a gidan.

   Bana jin kiuya ko kasala tunda na saba aikin daya fi wanan a kauye don hakane hjy bata samun matsala dani koda an samu din ma saidai gyaran dan abinda ba,a rasa ba kawai.

   Ganin tana waya yasa naja na tsaya daga nesa kadan ina jiran ta gama waya ta bani umurnin abinda zan mata lokacin.

  Wasu kaya data fitar ta nuna min da hannu alaman in dauko mata su ban tsaya ba na juya zuwa wurin kayan na fara  dauko su ina ajewa a gaban ta.

    Sai waya take ta faman yi mai kama da fada da alama dai da danta ne ko wani kanin ta take waya yadda nake jin tana fitar da kalamai gareshi.

    Bayan na gama kwaso kayan ne naje gefe na tsaya don bata ban umurnin in tafi ba.

   Hango tawul din data fito wanka ta goge jiki nayi gefen gadon ta na juya zuwa wurin na dauke tare da nufar kofan ban daki na shiga na baza shi a dan karfen da ake bazawa.

    Unders din da suka taru a duk da na ranan dana daren jiya datai amfani dasu ne kamar rigan nono da buje da handkacin amfanin ta.

   Sai na tsaya na wanke tun ina jin muryan mami tana waya har nazo na daina ji da alaman ta dai gama wayan ne a lokacin.

    Nafito ta bini da kallo tana fadin wai dama kina cikin dakin nan zeey ?

   Ina ciki ina wanke under din da ke ajene tace min kai zee bakya hutu ko yaushe kina cikin aiki ai kiranki nayi kawai don ki miko min kayan nan in gani don jiya aka turo min su daga Dubai.

    Daga min su daya bayan daya nagani na duka na fara dauko kayan ina dagawa daya bayan daya tana daga kai idan na nuna mata.

  Amma sai naga kamar wanan yafisu tsaruwa zeey tana tambayana ta hanyar dago kanta taji me zan fada.

    Mami duk suna da kyau sai dai wanan din zai fi maki kyau gaskiya don kallan jikin ki.

   Ido ta kura min kamar tana nazarina kafin tace ashe kin iya zaben abu mai kyau kema ni dai murmushi nayi kawai ina kawar da kaina gefe.

  Sai dai ke har yanzu dadina dake kinki sake jiki a gidan nan ki nuna nina haifeki kamar kowa .

   Kullun kina abu kamar bakuwa a gidan nina rasa wanan halin naki kodai bakijin dadin zama da mune zainab ?

  Da sauri na dago kai ina fadin mami ina ji haka dai yanahina yake ko a gida nan ma aina sake ke nan .

   Sai tayi dan murmushi tare da fadin a hakan da kikeyi sai na dinga tunane ko bamu kyauta makine wani sa, an.

   Shigowan Rufaida dakin ne a daidai lokacin da nake kwashe kayan zuwa wardrobe din mami kamar yadda ta umurceni inyi.

  Rufaida tayi sallama ta shigo ina jin suna gaisawa da mami din take fadin kunga dama kun tashi ke nan yau weekend kun samu wuri kun kwanta kuna ta barci ina sauran mashiriritan suke basu tashi bako har yanzu ?

    Ban dubasu ba ta bata amsa gefen hjyn naga ta zauna ysyin da nazo wurin da niyar incewa hjy din akwai wani abinda zan matane ko in wuce.

   Kafin in furta Rufaida ta daka min wani uban tsawa malama may kikeyi kuma a nan bakin gama aikin ki ba ki fita magana nake son yiwa mami yanzu.

 No no no Rufaida na fada maku bana son wanan hattaran da kukewa yarinyar nan bari ganin tazo tana aiki a karkshin mu.

  Ku dauka hakan gazawa ne ko wani abu ni da kaina na rokota hannun iyayyen ta kuma aikaimin karamci aka ban ita don haka duk daya na dauke ku gareni don jinta nake kamar diyar cikina itama.

  Bana son wanan halin da kuke nuna mata a gidan nan to ai mami biyan ta akeyi bata daya damu ai.

   Na fada maku ban son hakan da kukeyi nan aikin ta yake tare dani dole kuma ta shigo dakin nan tunda abinda tazo yi ke nan a gidan nan.

    Baki Rufaida ta zunburo wai ita an mata fada ni dai ina tsaye ina sauraren su can nace mami da wani abinda zan maki yanzu ne wanka na fito dama ?

  Yamm yamm yamm don Allah fita kiba mutane wuri inda aikin ma zan karasa mata shi amebo kawai.

   Nidai na juya na fice daga dakin raina bai min dadin hakan ba ko kadan yadda yan matan nan suke min a gidan gashi naga duk da mami na tsawata masu sai dai bata son ransu ya baci ko kadan.

    Yanzun na gama waya da yayan ku yana son ya raina min wayau wai ba zai samu zuwa rantsar damu ba da za ayi.

    Abinda naji mami tana fada ke nan lokacin da zan fita daga dakin bayan korar da Rufaida tayi min.

    Dakina na koma na karasa shirina duk da ba wani shiri bane dan dongon rigar da anty safiya ta sai min sune nake sakawa yanzu saidai naji hjy tana wakan tana son a samu lokaci aje a sai min kaya don tana kunyar wanan kayan da nake sakawa haka.

  Ban sa raina ba sai na gani balle zumudin hakan ya hana zuciyana shakat da damuwa na fito na nufi kitchen don samawa cikina abin karyawa.

    Ruwan shayi da soyayyen dankalin turawa nagani a cikin kula shina diba na hada tea na dawo inda Larai ke  gyara kayan miya na zauna kusa da ita na fara sha ke nan naji muryan Rufaida na kwala min kira da yar aikin hjy don sunan da suke kirana dashi ke nan dashi a gidan in ka debe hjy dake ce min zeey sai su mama kande da suke kirana da zainab.

    Amsawa nayi da na,am  tana karyawa Larai ta fada yadda zata iya jiyo ta tana karyawa shine ba zata zo ba Rufaida ta fada.

    Dole na mike zuwa amsa mata kiran a tsakiyan falo na sameta tsaye ta rike kugu tana jirana a hasale.

   Ina zuwa take fadin ke don uban ki zan kiraki kice kina karyawa haba Rufaida wanan zagin fa haka ?

    Muryan Anty salma ce dake zaune wurun dinning tana karyawa lokacin ba dole in zage ta ba don daukan kanta take daya damu wanan yarinyar.

   Kin san dan kauye bai iya samun wuri ba dama idan yaga ya waye sai yake gani yafi kowa waye wa ki shige dakina kaya na nan na tara a bayi na ki wanke min ta fada tana juyowa inda nake tsaye ina kallon ta da idanuwa da suka ciko da hawaye don zagin da tayi min.

    Bazaki tafi yin abinda nasaki bane ta fada cikin tsawa da sauri na juya na nufi hanyar dakin nata don kwaso kayan datace din.

  Saurara ta fada naja na tsaya cak wuri guda ina saurarenta kada ki fara ki satar min wani abu a dakin nan don ranki zai baci sosai idan kinyi hakan.

    Haba haba hakan baida kyau fa Rufaida and kuma kinsan mami ba zataji dadi ba idan tasan da hakan anty salma tace.

  Mami kina nufin banda right din sakata aiki ko warning dinta akan kayana tana yar aiki gidan nan.

   Nidai na juya na wuce ina shara hawaye don abu biyu ga zagin dana samu ga kuma zargin sata yanzu.

   Dakin na shiga na same shi a ya mutse kamar ba mace ke kwana a cikin sa ba don daki babu gyara ko kadan yadda na ganshi.

   Bai da banbanci da dakin da nake bambancin su dai wanan mirrow shi cike yake tab da kayan shefe shafe sai  manyan akwatuna dake gefe ajiya ga kuma tv bango babba.

  Duk a fakaice na kalli dakin nasan da hakan don wanan ne shigana na farko wani daki daya shifi gidan in kin debe na mami da kullun ina cikin sa.

   Mami bata taba ce min wani abu game da dakinta da zanga kudi ko agogo ko sarka da sauran su sai dai in dauka in mayar inda take aje sarka ko agogo kudi kuma zan daga filo in aje mata shi yadda suke.

    Ina shiga ban dakin idona ya fara arba da pant din ta saman kayan su rigan nono da bujen ciki kai kaya daine na unders da mace ke sakawa a jikin ta ta tara gudan masu yawa a wurin.

   Tattarawa nayi na a bucket din dana gani a bayin nafito tana tsaye tana kokarin cire rigan dake jikinta take fadin ki tsaya ki gyara min daki kafin kije wankin.

  Dole ba yadda na iya tunda nazo cin arziki ne gidan su na fara gyaran dakin ita kuma ta shige bayi don yin wanka kafin ma ta fito na gama na bar dakin.

   Can baya naje inda ake wanki da sauran aiyuka na wanke na shanya mata tunda wanan ba aiki bane a wurina.

   Na gama na dawo na samu ruwan tea di dana aje har yayi sanyi haka na dauka nakarasa shan shi da sanyi.

   Fitowa nayi da niyar komawa dakina na samu yan matan gidan zaune da kawayen su a falo zaune.

    Zuwa nayi zan wuce ba tare da nayi masu magana ba nakai tsakiyan naji muryan Nazifa na fadin amma wanan yarinyar bata kunya.

   Sai duk suka dawo da kallon su wurina wanan wacece yaushe tazo gidan nan cewar wata daga cikin bakin.

   Rufaida dake cin chewing gun ta tabe baki tana fadin a kauye mami ta dauko ta .

   A hakan mami ta dauko yar aiki wanan wani aiki zata iya kazama da ita haka  ga ruwan kauyanci ko ina tare da ita.

  Gaba daya suka sa dariya lokaci guda ke zoki gaidasu ki shige salma ta fada a dake ba tare da tayi dariya ba ita.

  Nazo gaban su na tsuguna ina gaidasu basu amsa ba sai dayan ke fadin kina gani ta nan idan ta waye sai duk kun girgiza a gidan nan.

    Amma dai kin gama damu Laila wanan din ne zamu girgiza don tayi clean .

  Oh kina raina irin kauye ke nan ai barsu yadda kika gansu ba wani zancen clean gareta don tana clran aurin nan ba karamin taksici zakuci ba duk wanda ya zo kanta zai tsaya rabu da mutum ka barshi a ranan da yake kawai don idan kace zaka kaishi innuwa shiko yana turaka rana .

    Salma ta kalleni cikin takaici tace ba kingaida su ba me kike jira kuma a nan yanzu ?

    Sai ta gama jin abinda muke fada mana Rufaida tace tana watsa min harara na mike ba bar wurin ina jin bakin na fadin ke wanan ai idan tayi clean ko yaran gidan nan ba zasu barta ba tana hakama yaya aka kare da suranta duk mai hankali yasan anyi halitta a nan ai.

  Ire iren haka yasa nakan shige daki in zaune in dai ba mami ke gida ba dole ina falon don aike ko wani aiki da zan mata.

    Yan matan basu bar gidan ba har mami ta dawo daga unguwar data tafi tana shigowa ta samesu a falon gaisawa suka farayi bata ko amsa masu ba ta fara fadin ina wanan yarinyar zeey take ne ?

   Sai kawai ta shiga kwala min kira ina cikin daki na kulle kaina naci kuka har na gaji naji an bankado min kofan dakina da karfi .

   Haka yasa na dago kai ina kallon mai shigowa dakin lokacin ba kowa bane sai Nazifa ke kina nan zaune to mami tana kiran ki.

   Mikewa nayi da sauri ban ko tsaya share fuskana daya gama dan hawa ba saboda kukan da nasha.

    Mun iso falin daidai mami ta dauki ruwa zata kurba nake fadin sannu da dawowa mami ta dago kai ta kalleni sai ta furzo da ruwan lokaci guda daga bakin ta.

    Gaba daya hankalin kowa ya koma kanta don ganin me ya faru tana fadin zainab mamana kuka kikayi ne ?

   Kaina na girgiza mata kafin in ce a a ahankali ina wasa da yatsun hannuna haba bana son inganki cikin damuwa ko kadan.

  Shiru ta danyi ta mayar da hankalin ta ga wayan ta kafin tace kwashe kayan nab ki kai min daki.

   Na duka na dauki kayan zuwa dakinta kallo ta bini dashi tana fadin na rasa me yake samun wanan yarinyar taki ta sake jiki damu har yanzu.

   Cikin ko in kula salma tace mami tambayi yaran ki don su suka bata mata rai suka kirata da yar kauye a gaban ta dazu nasan shi takema kuka dai.

   Salma haka take bata shiga harkan kowa kuma bata boye gaskiya fadin shi takeyi komai dacin sa a cikin su.

   Amma na fada maku tun randa yarinyar nan tazo kan ku kiyayyeta a gidan nan ko ban fada ba  ranan kan mami tayi masu tas a kaina a gaban kowa don sauran ma ashe ba baki bane duk yan gidane suma.

    Wanan fadan ne ya kara jawo mi bakin jini a gurin su sosai suka saka kafan wando daya dani dole idan mami bata gidan ina daki ko wurin kande.

  Haka kuma bai hanasu sakani aikin wahala da suke gani  suna ban ba gashi mami bata zama gida yanzu don shirye shiryen da ake na zuwa rantsar dasu Abuja.

  Wanan ya dauke mata hankali daga komai dake faruwa a gidan ba wankin unders ba har tufafin su yanzu suke bani in wanke wai nafi mai wankin gidan iya wankin kaya sufita a cewar su don mugunta kawai.

    Ranan ina dakina kwance mami ta kirani kande aka aiko ta kirani nazo da sauri tare da wani na samesu ina zuwa ta nuna mashini tana fadin ka ganta nan duk ita zaka dinkawa kayan .

   Kallona tellan yayi yana fadin bari a aunata ke nan da sauri hjy tace tana daga mai hannu ina warning din ka da wanan awon da kukewa mata yana daga cikin aikata alfashan zama koda kuwa namijine dan uwanka ko mace yar uwar mace haramun ne yin hakan.

    Hjy za,a kiyaye ya fada yana dan sosa kai tare da dan jin kunyan abinda hjy ta fada mai sai kuma ta dago yana fadin kayab zasu matse ne ko a danyi mata su free ne.

  Kafin mami ta bashi amsa na karbe da fadin free nake so kada ya matseni don Allah.

   Ji mun yarinya kin san abinda yake nufi ke nan ko ni dai nayi dan murmushi kawai ina dukar da kaina kasa cikin kunya.

   Kudi masu yawa taba tella ya tafi yana mata sallama tare da godiya  gareta wuri na samu sama kafet din dake tsakiya a daidai inda mami ta dora kafanta tana zauna cikin  limtsetsen dogon kujeran falon.

     Hjy ta kalleni tayi murmushi kafin tace min wai zee yaushe zaki daina wanan hali naki ga kuja zaki wani zauna a kasa kamar marainiya.

   Dama ina son jin wani abu a dangane da rayuwan ki mahaifiyar ki tana da rai ?

   A bazata tambayan yazo min da sauri na dago kai na kalli hjy kafin ince tana da rai sai kuma tace mahaifin ki fa ?

   Shima yana nan na bata amsa kai tsaye kuma suna tare da babar ki kai na gyada mata wanan karon idanuna yana kawo hawaye.

   Yaya akayi suka barki zuwa inda basu sani ba kina matsayin kina ya mace zeey basu gudun ki fada mugun hannu ne ?

    Hawaye bakeyi sosai tare da fadin Asabe ne tace sai nazo birni suka hada kai da lantana aka turoni don innan mu na haihuwan yaya mata wai.

   Tace idan ba aikatau ba bamu da wani moriya nan gaba tunda aure zamuyi mu barsu gida.

   Tauuu  ita Asaben ta fadi haka diya mace bata da amfani sai aikatau ta tambaya tana kallona.

  Kaina gyada mata alaman eh sai naga tayi wani dan murmushi iya fuska kawai.

   Wacece Asabe ta tambaye ni nace kakar mu ce wacce ta haifi Abban mu tare muke zaune gida daya .

  Mami tace kuma ita ta haifi Abban naki itace ta haifeshi shida gwaggon habiba subiyu ne yaranta kawai.

    Ina ita gwaggon naki take yanzu nace ance tana aure  a zaria ne tace ikon Allah zarian nan dai tamu kaina gyada nan ma..

   Bata san an kawoki gidan nan bane aiki daga garin ku nace nima ban sani ba mami don tana dadewa bata zo garin mu ba.

    Amma ai bata rasa samun labarin an kawo ki kaduna in har yar uwan haihuwan mahaifin kice ta hakika ya kamata acs suzo suga inda kike nawane kaduna da zaria .

  Sai ga hawaye nabin idona nace itama yanzu tunda Abba ya auri lantana ba ruwanta da innan mu kuma.

   Ikon Allah ita innan taku ina yan uwanta suke nace cikin ancau suke da zama saidai it inna iyayyen ta duk sun rasu kafin mu girma bamu sansu ba.

    Tace mahaifin ki kika kwaso da kama ko babar ki nace Asabe kullun in tana fada sai tace wai zubin innan mu kwaso sak.

    Kenan ita kika biyo da dirin jikin kin ga ai wata rana nasan zamu hadu da innar take idan ta kawo maki ziyara nan ko ?

    Yana da wuya inna tazo nan don Asabe ba zasu bari inna din tazo nan ba don ko zuwa za ayi sai dai Abba yazo kila.

   Kina da kanne da kuka fito ciki daya dasu nace mu bakwaine mata innar mu ta haifa shine Asabe ke mata gorin hakan.

   Ta auro lantana yanzu na barta da ciki wai za a haifawa Abban mu magajin gida tunda inna ta kasa haifa mai namiji.

  Innalillahi hjy ta fada tare da rike baki tana fadin har yanzu akwai irin  jahilcin nan ashe ?

    Zata kara magana waya ta yai kara ta dauko haka yasa na mayar da hankalina ga tv dake aiki ga falon .

   Saiga yan jikokin ta su shigo do basu faye shigowa wurin kakar tasu ba uwarsu ma baifi sau uku na ganta a part din hjy ba.

   Daga bayane ma nasan a gida daya suke zaune da ita saidai ita tana nasu bangaren ne daban.

  Tunda nazo ban taba taka ko wurin get din gidan ba kullun ina cikin gida idan ma na fito iyakata backyard din gidan inda su mama kande kan zauna da yamma su sha iska.


ZAINAB  IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅🔟


RAYUWA YANA FARUWA WUCEWA YAKE KAMAR BA, AYI BA ALLAH KABAMU IKON AIKATA ALHERI A KWANAKIN DA SUKA RAGEWA MUSULMI BAKI DAYA AMIN, , , , , 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK DARI UKU KACAL NE HAKKINA KAFIN KI KARANTA NAGODE, , , , Kamar yadda mami ke yawan jana a jiki yanzu na fara sake jiki a gidan mami saidai bada yan matan ta ba dan gara samarin ko a gaban mami zasu sakani wani aiki mami na fada tana komai zan masu shi.

   Hakama yau ya kasance kowa na gidan yana falo zaune ana hira ban dade da fitowa falon ba mami ta kirani in dauko mata wani takarda  sunan shi kawai ta fada min nace nagane shi na juya da sauri zuwa dauko takardun.

   Rufaida ta kalleni tana fadin wanan akwai iya yin tsiya ko ina ta iya karatu balle ta san shi wai ta gane bari ta dauko shirme yau sai na mata tsiya a gidan nan kuwa.

    Yo aini tafi min ku  kodai bata gane ba ai zata dauko din da kwatace ballema tunda tace ta gane ta gane din ne.

   Wani lokaci yarinyar tana bani mamaki sai in manta in mata magana cikin turanci sai kuma ta gane me na fada mata din.

    Hajjaju ko dai tayi karatu ne watakila ta danyi boko a can garin su fa yaya jalal ya fada yana dakilan wayar shi.

   Sai jamal yace boko for ware kana ganin yarinya yar tipical yar kauye da ita na maganan wani education nan.

    Sai gani da saurina nazo har gaban mami ina mika mata takardan mami ta karba tana fadin tau Rufaida dake da ita duk kun kuru yau a gidan nan .

   Lah mami ashe kin hakeni kimin tsiya idan na taba maki yar ki ke nan Rufaida ta fada tana dariya kafin ta juyo ta watsa min wani harara.

    Oh wellcome my boy jalal ke fada don shigowan jikokin hjy falon rike da takardun makarantar su yaron na zuwa ya fada jikin kanin mahaifin shi da sauri.

     Saiga uwarsu a bayan su itama ta shigo falon ashe tare suke tafe har yaran sun fara zuba mami tace oya great us cikin daure fuska.

    Take yaran suka fara bin kowa a falon suna gaida su har zasu gaidani Nazifa tayi saurin fadin she is not your aunt  .

  Nazifa ki fice min a idona akan yarinyar nan kafin rayukan mu yakai ga baci a gidan nan don ba zan lamuci hakan ba.

   Jamal ya mike yana fadin ke stop interrupt your self akan wanan yar mami din a gaban ta don yanzu itace da mami baku ba.

   Ashe ka gane gaskiya bana son ana raina dan Adam a rayuwana idan ka sanni a da ban kokai zeey wayewa ba kuma a haka mahaifin ku yace sai ni.

   Duk aka kwashe da dariya falon wurin Rufaida yarinyar karama ta nufa tana fadin anty ki koya min assigment dina mommy tace bata iya ba.

   Karban littafin tayi tana dubawa kafin da namijin ya juyo zuwa gareta shima ta karba tana duba kafin tace wanan sai Nazifa kila don ban gane me ake nufi ba gaskiya.

    Wani subject ne Nazifa ta tambaya tace mathematics ne fa wanan ai sai ku Nazifa wace nazifan ta fada tana fadin su dai kaiwa salma ta duba.

   Salma dake zaune tana duban wayan ta tace kada ma su haroni don ban iyawa zanyi ba indai maths ne.

   Fuska yaran suka bata mami na fadin amma ko kunji kunya ta mika hannu yaran su kawo ta gani .

  Ban san lokacin da nace  mami barin duba masu ko zan iya ba mami ba kowa dake falon dago kai yayi yana kallona da mamaki.

   Ke wanan fa ba tallan goro bane karatune na boko ake fada don kinji mami tace kina daidai da kowa zaki kawo muna rigima.

  Ban damu da abunda Nazifa ke fadi na karbi littafin tare da jawo yarinyar a jikina.

   Tsayawa nayi tare da nazarin abinda aka basu kafin in fara rubutu duk idanuwan su a kaina yake.

    Tiryan tiryan nakewa yarinyar bayani yadda zata gane har muka gama da nata na dago kai ina fadin namijin ya kawo nasa.

  Sai lokacin naga kallon mamakin da kowa ke min a falon lokaci guda mami tace dani kinyi boko ne mamana ?

    Nayi na bata amsa a hankali duk yan matan mami suka zaro ido waje kinyi boko kike haka kuma a aikatau ?

     Ban kulasu ba naci gaba da koyawa yaron assigment bamu dauki lokaci ba na karasa yaron ya dago yana murmushi.

   Mami ta mika hannu ta karba da wanda nayi mai musali ya kwashe ciki tana bin rubutu na da kallon mamaki.

   Wani maki kika tsaya a karatu ne zeey ta tambaya cikin kureni da idanu tana son jin amsa daga bakina.

  Ina ss3 Asabe ta fitar dani da banan nan zan gama karatu tace wai bata ga amfanin boko gun ya mace ba tunda ba namiji nake ba shine karshe ta turo ni nan.

    Kowa a falon shiru yayi yana kallon yadda hawaye ke zuba min a idanuna lokaci guda don maganan da nakeyi.

    Yanzu kina son karasa karatun ki ko aure zasuyi maki kauye kina da tsayayye acan .

   Kai na girgiza tare da fadin banda kowa sai Asabene tace wai zata sama min miji ta hadani dashi.

    Kai waiko wanan Asaben ita ta haifi mahaifin ku da cikin ta wanan abinda take gwada maku yayi yawa gaskiya.

   Karatun ma da zakiyi ki samu madogara a rayuwan ki saida ta hana kiyin shi gaskiya na tsani wanan matar damai irin halin ta.

    Muryan Nuriya matar yaya mubarak ke fadin mami ashe kuma an daga tafiyan ?

   Mami ta juyo tana ce mata sun daga kedai kin san abin gwaunatin kasan nan baida tabbas ai yanzu kuma sai dai sun kiramu kuma.

    Ai wa yan nan sun kwafsa muna wallahi don kila yaya Jafar ya fasa shigowa kasan nan ke nan sai wani jikon .

    Yasan an daga ne mami ta tambaya tana kallon jamal dayayi magana sai jamal din ya juya yana kallon jalal yana dariya.

    Kudai kuka sani da tsegumi kamar mata haba mami don mun fada mai an daga ranan shine tsegumi shifa ya tambaye mu muka fada mai gaskiya.

    Waya aike ku fada mai da ku barshi sai idan yazo yaji ai ba shike nan ba zai kirani ai zamu gamu dashi ta fada a hasale tana mayar da hankali kan sytem din ta data bude a gaban ta.

    Nice ta farkon mikewa a falin bayan Nuriya matar yaya mubarak data ja yaran ta suka koma part din su ba don yaran sun so haka ba don ko shigowan nan nasu don assigment din yaran tashigo har dasu.

    Dakina na shiga nabi gadona mai laushi na kwanta ga sanyin A C dana sake ya game dakin sai barci.

   Bada masaniya ba mami ta sama min makaranta don inci gaba da karatuna a wani college dake gaba da unguwaelr kadan.

    Ranan da dare take fadamin zancen ci gaba da karatun nawa lokacin nema kowa a gidan yasan da zancen cigaban karatuna yanzu.

   Wanan yasa yan matan nata kara jin haushina sosai banda daman bin motar su kamar yadda mami tace mu rika tafiya tare da safe idan zan tafi.

    Ganin haka ban fadawa mami ba nake takawa da kafa ina zuwa makaranta don nisan shi ai bai kai na kauyen mu dana baro.

   Zan tashi da asuba inyiwa mami duk wani abinda nasan nice mai mata shi kafin gari ya haska na karasa zan karya in taka da kafa inje school.

    Sam mami bata san da zancen tafiyana da kafa zuwa school ba sai wata rana zata unguwa da safe hakan yasa ta fito da wuri daga dakin ta.

  Yan matan ta samu zaune suna karyawa take tambayan ina nake nan suka fara kallon kallo a tsakanin sai salmace take fadin mami wayen garin nan banganta ba ai.

    Tafa tafi school Nazifa ta bada amsa sai mami tace usman ne ya kaita ya dawo ya dauke ku sai sukayi shiru don sun san da kafa nake tafiya school duk dadewan nan.

   Bana son irin haka sai kuyi kwanciyar ku a daki kuna sharan barci sai lokacin da yai maku dadi zaku fito  .

   Alhalin kunsan da cewa ita nasu school din ana duka idan an makara ko shi malam usman din yayi ta zaman jiran fitowan ku.

    Fada sosai mami tayi masu kafin ta fita can ta hadu dani na kusan shiga school din mu ta tsaya tana tambayana yaya akayi na tako da kafa ?

   Nace mami bana sin in makara ana duka idan mun makarane maza shige mota in karasa dake ke baki tsoron wanan titin namu gashi shiru babu kowa a wanan lokacin.

   Har ta saukeni fada take min ta bude jakka ta zaro five hundred tana miko min tare da fadin karbi wanan kiyi break dashi don nasan baki tsaya karyawa ba kika fito.

  Lah mami wallahi na karya kafjn in fito ki bar kudin don mami bata ban kudi sai dai tace na karya kona dauki abinci inje dashi school din.

   Ina kallo ta wuce karfe  biyu da yan mintoci na shigo gida har lokacin mami bata dawo daga unguwar da ta tafi ba.

   Haka yasa na samu daman samun dan barci rana bayan nayi sallah azahar ban sake fitowa ba duk da yunwan da nake ji don kudin da mami ta ban na kasa kashe su don ban saba da kashin kudi ba.

  Ban farka ba sai bayan la,asar wanka nayi lokacin ne naga fashin sallah yazo min don haka nayi wanka kawai na fito na dauki always na kimtsa jikina dashi.

    Abinci ya fito dani naga ashe yamma yayi sosai a lokacin haka yasa na gane na dade ina barcin rana yau.

   Don na samu har yan university sun dawo suna cin abinci mam kande ne ta dauko kuloli take fadin yau kan yar gidan hjy kin sha barcin rana.

    Ba dole tayi barci ba tunda taga arzikin banza wanan irun kune idan kun samu wuri kuke mayar da yan gida daga kofa.

   A a saidai tasan wanda zata mayar Nazifa tace tana amsawa Rufaida sai naji salma tace wai ku meye matsalan ku da yarinyar nan don Allah ?

    Rufaida tace I just hate her wallahi balle yanzu da take clean sai nake ganin gaskiyan maganan dasu Rubby suka fada ranan a kanta.

   Ashe bani kadai ke ganin canzawan yarinyar nan ba tundai wanan kayan da mami ta saka aka dinka mata suna fitar mata da suranta na asali waje.

   Zakace badaga kauye take ba har wani tafiyan sallo take tana yanga idan tana magana yanzu.

    Kai ku din nan kuna da wani magana wallahi koma dai yaya ta koma kunsan ba zata taba kaiku asali ba dai ko ?

   Sallama na fadan haka Nazifa tace yanzu waye ya damu da wani asalin mutum can zamanin nan boko ai mutane basu duban haka idan sunga abinda yai masu .

    Dariya sosai salma ta kwashe dashi don dama irin du baka ganin dariyan su sai ta baci ni dai ina diban abincin ina jin cinmutuncin da suke min kala ban tankasu ba.

   Saidai na kudurta duk ranan da wata daga cikin su ta kara zagan min uba bazan kyaleta ba sai inda karfina ya kare koda hakan na nufin inbar gidan ne na masan hjy ba zata yarda ba da hakan.

   Don takan fada min Zainab ina son in ga na taimakeki kin zama wani a rayuwa ki samu ki taimaki yan uwanki tunda dukan ku matane har ku bakwai .

  Shiyasa nake son ki dage ga karatun don wata rana ki taimakawa innan ki da yan uwan ki Asabe tasan diya mata ma diyane abin alfahari kuma.

 Ire iren wanan tunanen nakanyi inshanye wani abinda ake min a gidan don kawai manufar mami a kaina don kuma burina ya cika.

    Karatuna bai hanani yin abinda nazo yi gidan mami ba har na kai wata shida da zuwa gidan .

  Iyakata da anty safiya idan tazo in fito in gaida ita tare da tambayan yayan ta da mijin ta ta bani amsa da suna lafiya suna gaida ke.

  Sai kuma ta tambaya injin dai baki wani abin asha zainab kada ki manta da kinzo cin arziki ne a nan don haka kiyi biyayya sosai.

    Irin maganan da anty safiya takan min ke nan idan tazo gidan ina nan kafin ta tafi

    Gashi banji wani zancen kudin aikatauna ba ga bakin kowa nima kuma ba damuwa dana san komai a kan albashi na nayi ba.

   Mun samu hutu makaranta naji mami na fadin ya kamata in je in duba gida tunda su basu neme ni ba har yau.

  Don tasan yanzu inna na tacan cikin damuwan halin da nake ciki babu dai yadda zatayi ne ta sawa sarautan Allah ido.

   Ban san mami har ta saka ranan zuwana gida ba sai dai tace inje aimin kitso a makwabtan mu don akwai wata yar makarantar mu a gidan kusan tare muke dawowa da ita kullun.

    Itama takan zo gidan mu in mata nan yan gidan suka san na iya kitso sosai don har mami nakan wa kitso yanzu tunda ta gane na iya kitso sosai da yan matan ta.

   Sai dai bankan so yi masu kitso don muna kitson suna zagina har mu gama.

     Washe gari na shiga wurin mami in gaida ita da kwana sai na sameta zaune ta fitar da kayan data dawo daren jiya dasu don nice na kwaso zuwa dakin ta.

    Sallama nayi ta dago kai tana fadin yawa samu wuri ki zauna dama yanzu nake da niyar kiran ki sai gaki.

    Zama nayi kamar yadda ta umurce ni kafin ta fara fadin kinga wa yan nan turamen ta nuna min su da hannu nace eh mami.

  Tace yan uwanki zaki kaiwa su guda shiddane iri daya ne saidai nasa a bambanta kallar su wanan kuma na innan ki ne ta nuna min wasu uku a guri daya.

   Sai wanan kiba Sabe daya lantana daya wanan shaddan kuma ki ba mahaifin ki sai sabulai da omo kiba yan uwa da abokan arzikin ku .

   Kwana hudy zakiyi ki dawo driver daya kaiki zai dawo ya daukeki ranan ki gaiyar min da innan ki sai wanan ki ba mahaifiyar ki tana miko min wani abu a cikin leda wanan kuma mahaifin ki zaki ba albashin kine na watannin da kikayi a wurin mu na tara maki shine na raba biyu innar ki rabi mahaifin ki rabi.

  Kada ki manta ina gaida innar ku kwarai kice na gode sosai sai watarana idan mun hadu.

    Hawaye na fara yin a wurin ina tsugune sai mami tace ko kin fasa zuwa gidan ne in aika masu da sakon da sauri nace a, a mami na dai rasa godiyan da zan makine yanzu.

   To maza ki tashi ki shiya ga sabbin kayan kinan saman gado sai ki zabi wanda zaki dasu tsufin kuma duk ki hadasu ki kawai kannen ki su karasa su can .

   Ko mahaifiyar ki tana sa kwance ki zaba mata wa yan nan dana ware da za a kyautar .

  Da gudu nace tana sawa mana mami to jeki ki zabar mata kala biyar daga ciki da sauran tarkacen daya dace ki kai mata .

    Na mike don na rasa bakin da zanwa mami godiya don ta hanani yin hakan gareta.

   Kayane mai yawa har na rasa wanda zan cirewa inna sai da mami tace ki cire mata zannu da dogon riga zatafi son su ai.

   Haka muka dauki hanyar ANCAU da tsaraba taf a bayan mota da zankaiwa iyayyena koma in ce mahaifiyata don itace mai tsaraba da yawa ciki.

  Don hjy tafi son inna na fahinta sama da mahaifin mu Abba kodon tana mace yar uwantane ban sani ba.

   Malam Usman driver mami bai tsaya ko ina ba dani sai kofar gidan mu tun daga nesa na hango wata na suyar wani abu an baibaiye ta.

    Saida muka matso kuss ne na gane saratu ce kanwata ashe ganin mota ya nufo kofan gidan ya kuma ja ya tsaya.

  Duk wanda ke wurin ya kurawa motar ido don son ganin kowaye a motar ban fito ba saida na gama dauko kayan dana rike a hannu na fito daga motar.

    Saratu zoki kama min kayan nan kin tsaya kina kallona haka muryana kawai ta sheda yasa ta gane ni a lokacin.

    Ido ta waro waje tana kallona tare da fadin yayan mu maimakon ta yo wurina sai kawai ta kwasa da gudu tayi cikin gida tana fadin.

   Allah mun godema Allah mungodema yau ga yayar mu ta dawo garemu innan mu fito yau Allah ya dawo muna da yar uwarmu gida.

   Ashe ba sayar da ita akayi ba a birni ji  abinda saratu ke fada yasa sayran kanne fitowa da gudu kafin su ja su tsaya suna ina take ta kwasa tayi hanyan fita suka bita da gudu.

  Mun hade dasu a kofan shiga gida sukayo kaina da murnan su da ihu suna jin dadin gani sai ihu sukeyi yayan mu ta dawo yayan mu ta dawo garemu yau.

     Jin ihun da yaran gidan suka dauka na murnan zuwana yasa Asabe fitowa daga shiyan ta dan kwali a hannu tana fadin.

   Shin Abu Abu kuke fadan tazo ina Abun take ne in ganta tana kokarin wuceni da yan uwana.

   Gani nan Asabe na fada ina kokari zuwa wurin ta sai taja baya tana dafe kirji tare da fadin Abuce haka ?

   Zonan na ganki na karasa wurin ta sai ta rungumeni tana kuka tana fadin yar nan ina kika shige haka babu duriyan ki har an fara zargina a gari na sayar dake ga yan birni.

    Ina gidan hajiyar da kuka kaini tun barina garin nan na da kwana bakwai gun anty kafin ta kaini gidan.

    A a ai dada kin dawo garemu ke nab dai yanzu ba komawa wanan birnin kuma dai ta fada tana share hawaye.

  Ni dai ban ce mata komai ba sai waige nake ko zanga innar mu ta fito banganta ba yasani sakin Asabe na nufi dakin mu da sauri ina sallama.

   Ina shiga da hango ina zaune saman dan gadon dake dakin tayi tagumi ns karasa gareta ta da sauri ina fadin inna gani nazo gare ku yau.

  Murmushi inna tayi kawai sai dayan kanwar mu data sawa kira daga dakin a daidai lokacin da yara suka fara shigo da kayana dakin.

   Irin surutun da yaran dake shigo da kayana gidane ya sa hankalin lantana dake daki bakin cikin dawowa ya hanata shakat tunda saratu tazo tana ihun na dawo wani tukukin bakin ciki ya sokar mata zuciya.

   Don Lantana sam bata so in dawo gidan ba a lokacin don so tayi ace ba bata da gaskiya kamar yadda ta kulla sherin haka har zance yabi gari gaba daya kowa ya dauka hakan ne.

  Inna eta bada kudi wai a sayo min ruwan leda nace basai an sayo min ba inna a dai sayawa driver hjy daya kawoni.

    Wai wanan mutumin driver ne yanzu saratu ta fada nace drivern gidan hjy ce shi ke kai yaran ta makaranta ya dauko su idan da aike kuma sai a aike shi.

  Bawada ya ankara da zuwan lantana daki namu tazo ta tsaya a kofan dakin ta tokare hannayen ta da katon kofan dukka gefe biyu.

   Saida ta gama saurarebn mu ta kalleni tsaba ta fara fadin eyya Abuce ta koma haka ?

   Gaba daya dakin muka juyo muna kallon ta lokaci guda taci gaba da fadin halan a cikin injin suka sakaki aka wankeki haka.

   An maidoki kamar wata karuwan birni koda yake wasan abinda kike a burnin wanan bude idon haka lokaci daya.

    Amarya ke nan ai inkiga mutum yayi abu yana da gadon shi ne ban gada ba babu dana da zai taba zina da yardan Allah inna ta bata amsa.

   Kinsan aikin mutum sai ya dauka shi kowa keyi ko ina ya samu kansa ni Allah ya tsare mi  yata a birni don bata gaji watsar da kai ba.

  Kaina yana duke kasa ina tunanen wai yaushe inna ta fara magana haka sai naji lantana na fadin wa kike nufin ya gada to ?

    Wanda yasan ana haka har furtawa yata dashi nakeyi abu yaso zama rigima don har saratu taso shiga maganar inna ta kwabe ta.

   Andaiyi abin kunya ta fada tana batin kofan dakin don bata zaci innan mu zata bata amsar maganan taba.

   A kofa ta hadu da asabe da takawo min zogale data gyara tana shirin ci cewa lantana tayi muna ganin kilibibi a gidan nan.

  Ya tadawo yawo  tazubar har ake wani riritata don kwadayin duniya muna jin ta a daki nace har yanzu wanan matar tana wanan haukan duk data haihu girma yazo mata yanzu.

  Ina girma a nan banda iya shegen data karo cin mutunci dai ne mutum ya guji karshen shi.

   Asabe ta shigo da sallaman ta tana aje min kwanon ganye a gaba tana fadin kici yar nan dan ganye na gyara sai gaki.

   Saratu takai hannu zata diba takaiwa saratu dundu a baya tana fadin mara kunya ba a ke nakawo ba bakuwa na kawowa.

    Sai dana huta nayi sallah kafin malam usman ya aiko wai zai tafi na samu inna ta dan dama fura ta aika mai kafin yayi sallah yasha ga awara da saratu ta cika mai leda dashi har kwan zabbi inna ta aika a nema cikin gari ba a samu dayawa ba hakan ma naji dadi yadda akai mai.

  Bayan mun dawo daga rakashi ne na bude kayan don saratu ta ta demeni da tambaya mena kawo masu ?

  Tundana fara bude kayan jikin kowa yayi sanyi kafin ma in farawa inna bayani kamar yadda mami tayi min.

   Nan dai na labartawa inna rayuwana a gidan hjy saidai na boye mata irin cin fuskan da yan matan hjy kemun a gidan.

   Don tsakanin mahaifa da diyan su sai Allah sararu ce ta dauki na Asabe da lantana takai masu nasan don fitina tace itace zata kai.

    Lantana ta fara kai ta karbi kayan a tsune tana fadin duk da ance kayan zina kamar kayi zinane kaima.

   Amma wanan zani ya shereni ba zan barshi ya tafi ga banza ba tunda a haka aka sameshi.

   Saratu tace dadai yafi tunda ba yau aka fara cin kayan zina ba don har na tsohuwa an saba ci cewa da uwar lantana din.ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


1️⃣1️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWAYA ALLAH KA KAWO MUNA TSARO A KASAR MUNA NIGERIA,  KASAWA WANDA IF,TILLA,I YA FARU DASU HAKKURI DA SANIN KADDARA A RAYUWAN SU, , , , , , , 


DARI UKU NE NOVEL DINA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALLAMA YAR UWA DON TURA KUDI GA NOMBA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN KO EIRTEL NA DARI UKKU.
Abba bai shigo gida ba sai gap da magariba ya dawo lokacin ina alwala a tsakar gidan mu dani ya fara arba.

   Ja yayi ya tsaya tare da fadin wa nake gani nan kamar Abu ya fada cikkn mamaki don bai san da zuwana ba ashe sai wanan shigowan da yayi ya ganni.

  Amsa na bashi ina mikewa a daidai lokacin ina kai dan ruwa a baki kamar yadda yin hakan ya zama min al,ada tun ina gida ba tafi kaduna har yanzu kuma ban daina yin hakan ba idan na idar da alwala don sallah.

   Abba nice na fada cikin dan murmushi Abu ina kika shiga haka babu labarin ki ga kowa ita din da tazo ta dauke ki bamu kara jin wani zance a gareta ba har wanan lokaci.

    Safiya bata kyauta muna ba ta barmu cikin zargi da fargaba don ba haka mukai alkwari da ita ba.

   Ayi hakkuri Abba kasa anty ma,aikaciya ba ko yaushe take da lokacin tafiya ba irin hakan.

  Yar mairo koma menene ai ya dace ta dan waiwayo musan halin da ake ciki dake a can .

   Yanzu kai ganin ta yasa ka tsaya nan kana zuba har ka mata irin bakin cikin data jefa ku a tafiyan ta .

    Lantana ce ke fadawa Abba hakan tare da mika hannu tana fadin ban ledan kafin ka shiga can a wawashe.

  Tana mika hannu ta fisgi ledan daga hannun Abba ta juya tana fada abin kunya yarinya taje gantali tsawon wani lokaci saida tagaji don kanta ta dawo har kuna wani jin dadin hakan.

    Abba yai tsaye kamar ba Abban dana sani ba yana bin inda tabi da kallo kafin ya juyo har na bar wurun ina kokarin shiga dakin innan mu ko.

   Da mamaki a raina yadda naga komai na gidan namu ya kara hargitsewa ga baki daya na tayar da sallah.

   Bayan na idar da sallah muka zauna da inna sai lokacin nayi mata bayanin komai a tsanake har sakon mami na dauko na bata na nuna mata na Abban mu da tace a bashi.

   Inna tace aidai bata don wanan yarinyar tana kyala ido a kansu sai taga bayan su a lokaci guda.

    Nace koma meye ai dai na isar da sako saidai inna nifa wasu abubuwa da nake gani a gidan suna daure min kai tun zuwana.

   Me kika gani daya daure maki kai ai dama shi ramin mugunta kurarene idan wanda akewa yayi hakuri.

   Bai wuce dai abinda kikaji ba tsakanin umma da lantana ko wanda kika gani yanzu tsakanin ta da mahaifin ki.

    Duk waya ja hakan sai umma gashi kuma tun ba,aje ko ina ba abin ya koma tsakanin su yanzu.

   Tana ji tana gani ganin danta yana batun gagaran ta a gidan nan tayi fada har ta gaji ta saka ido idan da can tayi mai aure ne don ni a gidan nan,  yanzu bani  kaida ke ganin bakin cikin ba harda ita.

   Shiru jayi ina tunane a raina tare da fadin mai yai zafi tsakanin Asabe da lantana kuma yanzu.

   Abba bai shigo dakin inna ba sai bayan sallah isha,i zama yayi muka gaisa na mike na dauko mai sakon shi kamar yadda mami tace in bashi.

   Duban kaya  yayi yana juyawa tare da fadin ikon Allah duk wanan matar ta bayar a kawo min nace Abba ai mami mutumiyar arzikice.

   Zamanta mai kudi baisa ta raina tallaka ba nan dai na gutsura mai dan labarin mami din da aiyukan da nakeyi a gidan.

    Abba ya kalli takardan dake hannun shi yana juyawa a hankali kafin ya fara kokarin budewa kudi suka soma zubowa daga cikin takardan yan dubu daya sabbi fil dasu.

    Da mamaki yake fadin yahanasu kudine fa matar nan tayo muna sako a cikin takardan nan.

   Na amsa da fadin cewa tayi kudin aikina ne in kawo maka da zanzo  duban kudin Abba yayi kafin ya juyo ya dubi inna da ko kallon inda yake batayi a lokacin.

   Wanan matar wani irin kudine gareta haka yar mairo ko harda wani sana,a kike mata bayan wanan ?

   Gaskiya matar kwarai Allah ya hadaki da ita a birni don ba kowa bane zai iya maka hakan .

  Mamaki kalaman Abba ya bani don na dauka zai tambaye fiye da hakan sai ga Abba ya buge da fadin in kara kwazo don gaba ta aiko da wanda yafi wanan din yana mikewa.

    Malam iya abinda zaka fada mata ke nan dan ka rike kudin da baka tabbatar daga ina suka fito ba kamar yadda matarka ke fadi kullun.

   Bana zargin tarbiyan diya na ko kadan don nasan tarbiyan da muka basu tun farko.

   Allah yasa a kanshi take don nina tsuke da sakon wanan matar gaba daya hankalina bai kwanta da hakan ba ko kadan.

   Abba yana kokarin tura kudin cikin aljihu yake fadin ance kudi kare magana ganin wanan kudin yanzu ya kara tabbatar min da gidan kwarai diyata take.

    Bayan fitan Abba a dakin ne yai shiru na dan lokaci kafin mu fara jiyo hayaniyar Abba da Lantana daga kofan ta.

  Lantana ba kunya take fadin yau sai dai a rabamu a gidan nan amma wallahi sai ka fada min abinda kajeyi dakin can ranan girkina.

   Kinji ko haka muke fama da fitinan su a gidan nan koda shi koda umma don ni ba shiga shirginta nakeyi ba sai ta koma yi da yara yanzu.

    Allah yasa har na tafi kada wani matsala ya faru tsakanin mu nace lokacin inna ke tambayan kwana nawa zanyi nace kwana hudu mami tace driver zai dawo ya daukeni.

   Ba zan yarda ki koma garin nan ba batare da wani ya biki yaga a inda kike ba koda malam ba zai tafi ba zan hada ki da kawun ki lawal kuje tare.

    Inna hakan yayi daidai don mami ma bataji dadin hakan da aka barni ba wanda ya biyo sawuna tunda naje garesu bayan anty safiya data kaini.

    Matar kirkine tunda tayi tunanen hakan duk wata uwa ta gari wanan tunane ne zaizo mata a rai.

   Yadda za a sake diya mace haka ba tare da wani nata yabi sawunta yaga inda take rayuwana.

  Nagodewa Allah daya karba min addua na danake kullun gare ku hankalina bai taba kwaci ba tun bayan tafiyan ki sai dana samu sakon safiya a boye tana min bayanin halin da kike ciki tare da kwantar min da hankalina.

  Tun wanan lokacin na falwala ma Allah al,amarin na kara dagewa da addua a gareku sosai.

   Mun sha hira ranan don bamuyi barci ba sai da inna ta labarta min abindaya faru tsakanin Asabe da lantana tun bayan haihuwan lantana gidan nan.

  Tunda lantana taga ta haifi namiji kamar yadda umma ke muradin haka a kanta shike nan take ganin ta gama da kowa a gidan nan shi kanshi malam gaba daya an rasa gane kanshi yana ganin itace hasken rayuwan shi ita da danta.

  Bata yarda kowa ya taba danta a gidan nan dama ga dan bai faye lafiya ba wai yana da ciwon numfashi.

   Subbahanallahi gaskiya banganshi ba tunda nazo ai ba zaki ganshi ba don ba barin shi gidan nan takeyi ba wai kada wani ya halaka matashi.

   Tunda an fada masu wurin biye biyen bokayen su cewa wai asiri akai mai yazo hakan ba lafiya.

   Jin hakan yasa na ra,ya a raina har na koma bazan taba yaron ba in Allah ya yarda .

   Me zai kai ki shiga shirmen wanan mara mutuncin barsu ya kare a kan su ranan dai mun dauki lokaci muna tataunawa da inna.

     Washe garin kukan yaron Lantana ne ya karade gidan dashi ina mamakin karfin halin inna data ki kulla al,amarin yaron.

    Na fito don gaida Asabe da Abba da lantana sai na samu Abba yana tsaye yana rarashin yaron a waje sai tsala ihu yakeyi uwar na shafa mai magani.

   Kasa nakai na gaida Abba na juya don gaida Lantana samu nayi tana hararana a wullakance.

  Ban damu da hakan ba na fara gaida ita da kwana kafin nnace Abba meke samun shi tun dare nake jin kukan shi.

  Kafin Abba ya furta Lantana ta karba da fadin kuka kan ai dole ne tunda an jefe shi bamu da hutu shi wahala ni a wahalce kullun idan dan ruwa ya tabeshi ko sanyi.

   An kaishi asibiti na tambaya ina kallon Abba don ban yarda na kalli lantana ba don yadda naji ta fara maganan ke nan zancen innan mu gaskiya ne da take fadin sune suka jefa mata da don ana bakin ciki dashi.

   Ina wanan tsohuwar gidan zata bari akaishi asibiti tace ina saka danta wahala ko yaushe yana kashe muna kudi.

  Tunda ni ban yarda ta juyani yadda ta saba ba ace uwar miji komai danta keyi da matar shi idon ta na a kai.

   Da dai Abba ka daure an kaishi asibitin birni bana kauyen nan ba aji mai zasu fada tunda yana wahala haka.

    Tab abu mai wuya ke nan yaya muka kare da asibitin mu ma na nan balle har nawani birni can tunda ansan abinda aka kulla a kai ai ba a bada shawaran haka ba.

    Koke don bakya nan ne ai da an sakaki a cikin wanan sherin don ni yanzu na san zamana da kowa a gidan nan ai.

    Allah ya sauwaka sannu kaji na fada ina kallon yarin kafin in juya in wuce zuwa lungun Asabe dana sama tana zuba ruwa a buta zata zagaya ban daki.

   Ban manta ba don ban yarda na shiga dakin ba a wajen na gaida ita na juyo na dawo dakin mu inda na samu kannena na shirin zuwa makaranta islamiy a lokacin don boko ana hutu.

    Na taimaka suka shirya saida suka fice bayan inna ta basu ashirin ashirin din cin masa idan sun tafi.

   Don ba ai abin karyawa ba alokacin lantana ce da girki kuma bata dora wanda za a ci din ba don yaron ta da ya kwana yana rigiman dare.

    Wanka nayi na shirya cikin wani dogon rigan atamfa dinkin shi mai kyau ya dan matseni kadan .

    Inna sai fadi takeyi mai za,a sayo min in karya dashi nake cewa ta bari a gyara dumame shi zanci don kada in takurawa rayuwan inna din.

    Sai ga Abba ma ya shigo gida da leda biyu ya tsaya daga tsakar gida yana sa min kira na amsa na fito ya miko min ledan ya tafi da daya dakin Lantana.

    Kosai ne da bread sai kayan shayi a ciki dana bude nake fadin inna ga kosai din ki diba ki karya da bread din don ni ba zan sha ba.

    Nace bazan sha shayi ba inna dan dama kosai din zanci sai inna tace daidai ki sha abin ki mu in da sabo mun saba da wanan ai a gidan nan.

    Inna tunda ga kudi a hannun ki me zai hana ku sai abinci rabi kuma sai ki juya shi kina dan sana,a dashi.

   Shawaran da nayi ke nan a zuciyana Allah ne ya dubemu ya jefoki a lokacin da muke cikin bukata  hakan.

   Amma malam ya canza yanzu gaba daya a gaban kowa gari zai waye zai fita ya samowa matar shi abin karyawa muna kallo a gidan nan.

  Inna ki daina damuwa da wanan tunda ubangiji yana kawo maki mafita da zaki duba diyan ki ki basu abinda zasuci.

   Ire iren hiran da muke tayi ke nan a dakin inda na tillasawa innan mu sai data karya kafin yaran ta su dawo su hana taci tunda nasan tana son sha itama.

    Karfe goma suka dawo gida  da shigowan su abinci suka fara nema a gida suka samu ba a gyara ba zasu ci shi hakana da sanyi na basu kudi suka sayo taliya saratu ta dafa kowa yaci.

     Na zaga wurin yan uwa da abokan arziki irin matan da nai sabo dasu ina masu kitso kafin tafiyana kaduna.

    Har ya saura kwana daya ya rage min duk da zaman gidan namu babu dadi amma nake ji kamar kada in koma kadunan kuma.

    Inna ta danyi kokatin ta sosai wurin yiwa hjy tsaraba irin na kauyen mu da zankai wasu mami din.

   Washe gari karfe goma driver yazo daukana inna taso muje tare da kawuna kaninta yaga inda nake saidai anyi rashin sa, a kawun nawa yana da uzuri a ranan don haka muka dauki hanya dagani sai malam usman driver gidan mami a motar..


   Tunda muka tunda muka tun karo gifan naga wasu canji a cikin dan kwana hudun da nayi bana garin.

   Ni dai sai bin ko ina nake da kallon da mamaki a raina don ganin bakin fuskokin dake gidan namu tun daga get har zuwa cikin gidan.

    Na fito daga cikin motar tare da dora hijjabi da kyau a kaina na nufi hanya shiga gida don na tsaya daukan kayana malam usman yace za a shigo min dasu ciki.

   Da sallama a bakina na shigo falon sai dai abinda nayi arba dashi ne yasa gabana faduwa don ganin mutane a falon gidan kusan kowa na gidan yana falo ga bakin fuska.

  Wa nake gani kamar diyan mami haka muryan mami ya dawo dani daga tunanen dana fara a lokacin.

   Da dan gudu na karasa na fada jikin mami data ware min hannayen ta alaman inzo gare ta a lokacin.

  Kai kai kai mamana me innar taki ta baki haka cikin kwana biyu kika kara kiba haka kinyi wani fresh dake mami ke fadi.

    Tsuki yaya jamal yaja yana fadin ko dai ta kara kauyanci ji wanan bindata saka don Allah da cewa hijjab din jikina wai.

   No dan Allah malam usman bace muna da wanan kayan kazantan wurin nan ka shiga dashi wurin kande suna kice cewar Rufaida dake nufin a kauce masu da kayana a wurin.

    Malam usman dake shirin aje kayan ya dauka da sauri ya nufi hanyar kitchen dasu na dago ina fadin ban jakkana in kai daki bayan mun gama gaisawa da mami ban kalli kowa a falon ba.

    Jeki kai ki fito ki ci abinci wai ai kunsha tafiya don wurin bai kasa ba akwai dan nisa da kaduna.

   Shiyasa nace malam usman yayi sakko yaje ya dauko ki don ku dawo da wuri bana son tafiyan dare.

   Na dauki kayana zan shige naji muryar yaya jalal na fadin baki iya gaisuwa bane ke idan kin samu mutane ?

    Ke tafi ki aje kayan daki ki dawo mami tace haka yasa ban tsaya sauraren shi ba don bin umurnin mami din.

   Na kai kayan na dan dade ban fito ba azatona bakin zasu tafi kafin lokacin sai dai har na fito suna nan a inda suke sai lokacin na gaidasu sai dai sun ragewa a fLin don ko su yaya Jamal basa falon yanzu.

    Abinci na diba kamar yadda mami ta umurce ni na koma dakina ban kara fitowa ba sai dare bayan nayi sallah isha, .

   Don na kwanta ina tunanen gida ina tuna innar mu da na dan saba zama da ita a yan kwanakin danayi a can gida sai nake ji kewan su na damuna yanzu.

   Hjy na samu a falo kishigide saman kujera sai wani matashi dake zaune kasan kafet dake tsakiyan falo.

  Ya mike kafafuwan shi sambala sabala tare da dora daya saman daya kanshi yana daidai cinyar hajiya.

   Suna hira a cikin natsuwa su biyune kadai a falon,  kowa yagan su zasu bashi sha, awa alokacin.

  Ni dai kallo daya na iya masu na kawar da idona garesu don kyawon mutumin da kwarjini ga zati da Allah yai mashi kamar shiyayi kanshi.

   Da ina ganin kyawon su yaya jamal kamar su sukai kansu gasu da iya kwalliya da tsabta shiyasa zaginsu gareni bai damuna da sukece min yar kauye amma sai ganin wanan ya dushe duk kyaun da suke dashi a idona yanzu.

   Zeey ga yayan ku yayan su jamal jiya yazo sai kanwarshi da tazo ranan da kika tafi.

   Sannu da zuwa yaya ya hanya nace mai ina dan rusunnawa don bashi girma da Allah ya bashi a kaina.

  Fuska a sake ya amsa min gaisuwa bazakace bakin shi na motsi ba yadda yake magana da hausarshi da baya fita da kyau.

   Daga haka na mike don barin wurin ina tafiya a harde don rudewa da nayi don ban taba ganin mutum yai min kwarjini irin haka ba a idona.

    Muryan mami naji tana fadin zeey dauko ma yayan ki abinci nan yaci yau a kasa yake so ci yace don kiuya.

   Taci gaba da fadin ki dauko har dani don nima din kiuyan nake ji sosai in samu inci in shige daki  duk na gaji yau munyi yawo sosai yau.

   Kulolin abincin dana gani a jere sabbi fil dasu wanda ban taba ganin irin su ba a idona don kyau.

   Saida na dauko na karshe zan kawo naji karan bude kofa a part din mu wata matashiyan budurwace ta fito daga dakin dake kusa da nawa tana fadin.

  Mami na dauka baku dawo ba har yanzu naga yanzu is aftre eight ashe kun dawo sannun ku da zuwa ta fada fuska a sake.

   Mun dawo mami ta bata amsa lokacin da budurwan ke zama kusa da na zaune a kasa tana fadin bros yau kaga kd ke nan ashe ?

   Yamutsa fuska yayi yana fadin mami ta kaini gurin yan uwanta dana daddy har na gaji a cikin turanci suke maganan wanda ba ko wani abin nake ganewa ba saboda kwarewan su da yaren.

   Ina wuni nace mata da hausa ina durkushe kasa a lokacin lfy ta fada tana kallona kafin ta juya wurin mami tana fadin who is she mami ?

    Zainab ke nan da nake fada maki tayi tafiya yarinyar da nake zama da ita yanzu wace gwaggon safiya ta kawo min yar uwar safiya din ce.

   Oh itace she look quit ai ba kamar yadda su Rufaida ke fada ba a kanta mami tace rabu da yan rainin wayau kawai ban san me yarinyar nan ta tare masu ba gidan nan.

    Mami me za a zuba maki na tambaya sai ta dago tana fadin fara zuba mai shi da baison cin abinci sai shiririta ya saba da abincin su na shirme can.

    Lokacin ne na saci kallon shi na fara bude kulolin abincin ina son tambayan shi abinda zan zuba mai kuma ina jin tsoron ko bai iya hausa ba.ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣2️⃣ALHERIN ALLAH YA CIN MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE A FADIN DUNIYAR NAN ALLAHUMA AMIN ALLAH.


LITTAFIN KUDINE DARI UKU NE KACAL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMAN UBANGIJI BA TARE DA DAUKAN NAUYIN HAKKIN WANI A KANKI BA.


Nidai na kula tun dawowana kowa ke walwala ga yawan bakin dake ta zuwa gidan babu wanda zan dan tambaya ko meke faru a gidan haka.

  Naga kowa na gidan yazo ga kuma baki daketa zuwa daga ban garori daban daban sai gidan ya cika da baki sosai.

   Wurin kande naje ina tambayan ta abinda ke faruwa take fada min ai zancen hjy ne ya tabbata za, a tafi Abuja a rantsar dasu.

   Itace a jahar kaduna wace ta samu mukamin sai wasu daga sauran jahohin kasan nan kafin in furta wani abu larai take fadin.

    Wai mukamin me hjy ta samu hakane wanan cikar da akeyi gidan nan haka mama kande tace waya sani yar nan su dai suka san abinsu can.

    Shigowan anty safiya kitchen din tare da yar uwarta yasa muka katse hiran da mukeyi muka shiga gaidasu da zuwa.

    A, a ke yaushe kika dawo me tafiya babu sallama koda yake baki da laifin hjy ta fada min komai daga baya.

   Tana magana take karasawa cikin kitchen din tare da fadin kande zamu kawo maki wasu yan aikin da zasu kwana biyu suna aiki tare daku a gidan nan don aiki zai maku yawa ku biyun nan yanzu.

   Duk da dai maza da matane zasu zo din ba lalai bane ma ku taba masu aikin su sai dai idan suna nema  wani abu zaku iya basu.

  Iyakar ku ke da larai shine zaku taimaka muna wurin bawa ko wani bako abinci idan an gama daga na karyawa har zuwa dare.

   Ta juya tana fadin ke naji hjy tana neman ki tun dazun ashe kina nan gurin su kande.

   Da sauri na mike zuwa wurin kiran da ake min na barsu kitchen din dasu kande tana masu bayani .

   Cikan da gidan yayi a lokacin yasa na fara dan rabe rabe har na isa wurin hjy din dake dakin ta tare da wasu jiga jigan mata farare tas kamar ta sai dai sunfi hjy jiki da tsayi sosai.

    Haka na rabasu har nakai wurin hjy nake fadin mami gani ance kina kirana ina kitchen wurin su mama kande ne.

   Tace yawa zee wanan kawar tawace ke son kitso sai kuma Autana da naji tana tambayana ke dazun din.

   Kallon matar data nuna min zanwa kitso nayi ina fadin yanzun zamuyi mama naji dayan race kai hjy wanan yar taki tayi min kyau wallahi.

    Kafin daya tace hjy maria ke nan kedai diya mata suna burgeki tace wallahi naso dai in haifi mace kamar yadda hjy iyami ta rufe da ya mace bayan maza amma ban samu ba.

   A raina nace duniya ke nan wasu na gudun mata wasu kuma suna son su kowa da irin bukatan shi duniyan nan.

   Nidai ganin dukkan su manyan matane yasa na juya da sauri na bar dakin tun kan ta bani amsa lokacin da zan mata kitso.

    Ina fita daga dakin mami dakin Anty Nuriya na shiga daga kofa na tsaya ina sallama kafin ta ban amsa in shigo.

  Dakin yana da dan duhu ba haske sosai a lokacin tana kwance saman gadon ta makale da waya a kunnen ta.

    Anty ina kwana na fada tare da dan rusunnawa kadan ta amsa min da fadin ina zuwa please taci gaba da wayan da takeyi abinta.

    A hankali na juya zan bar dakin don ganin ta shagala ga waya naji tana fadin ki dan jirani please kayan da zan tafi dasu Abuja nake son ki shirya min.

   A raina nace masu duniya ke nan kayan ma sai wani ya shirya mashi idan Allah ya ba wasu sai su manta kowa ma rai gare shi ai.

    Dole naja na tsaya din ta gama wayan ta juyo tana kallona tare da fadin yawa tun dazun nake neman ki ai mami tace kina cikin gida.

   Ina gun mama kande na bata amsa tace dama kayan da zan tafi dasu ne nake son ki shirya min su don ba wani dadewa zamuyi a can ba bai wuce ki saka min kala biyar ko hudu ba.

    Nuna min jakka da zan saka mata kayan nayi na nufi wurin tare da tambayanta a ina kayan suke ?

   Bude wanan drower suna ciki na zaba yadda tace hakan nayi na bude kayana daga sama har kasan wardrobe din.

    Kinga na tsakiya din nan sune ban taba amfani dasu ba a ciki so ki dinga daga min dinkin su ina gani ko zanga wanda yayi min.

   Bani da zabi sai yadda tace din na shiga daga mata kayan kamar yadda ta umurceni idan na daga wanda yai mata zatace muga wanan ta dan mike ta gwada a jikin ta idan kuma na dauko wani tace No bar wanan miko wancan da nake gani.

   A haka har muka zabi kalla hudu zuwa biyar na gyarasu na saka mata a dan karamin troler na tafiya mai masifan kyau.

    Na gyara sauran na juya don barin dakin take fadin kinga kwaso dagayen rigunan can mu gani.

  Sai naji raina ya baci don dai ba wani gitma na tayi ba kila amma ta kafeni da aiki haka ba wani aiki ba.

  Na nufi wirun kayan tare da kwaso mata ina dagawa take fadin aje wanan nan ko jefa wancan can har muka gama ta sake nuna min wanda zan mayar na nafe na marya inda suke.

    Na juyo in kwashi sauran don in mayar take fadin  wa yanan ki kwasa ina ganin ai zasuyi maki wanda naje dasu school ne wanan time wani ma sau daya nayi amfani dashi.

    Ikon Allah ashe shi yasa ubangiji yace idan zakayi kayi don Allah idan zaka bari kabari don sa.

   Nagodewa Allah da ban nuna komai ba duk da raina ya baci amma na tsaya nayi mata abinda take so a dakin.

  Don kayana na yayan wani da wance masu tsada da kyau sun fi kalla goma wai duk ni kadai keda su tace min.

  Na juya kaina a sunkuye ina fadin nagodd tace kai haba dai da baki nan ma ai duk a nan zan barsu saida hjy ta bayar dasu ga wanda take so.

    Jin dadin kyautan yasa na ranan harda dakin ta na gyara mata da zuciya daya sai dai ta dawo ta samu dakin a gyara na gyara mata ko ina.

  Nayiwa kawar mami kitso haka yaja hankalin sauran matan suke ta kwadayin in masu suma sai naji mami tace su bari a dawo Abuja don tare dani zata tafi.

    Wani dadi naji sosai a raina jin mami tace dani za a tafi abuja din garin da nake jin labarin shi yau gani zan tafi cikin sa duk da nasan ba fita zanyi ko ina ba amma dai zan karasa ince ai na taba zuwa.

    Tun da naji na fara shiri nima duk da naji Nuriya ta fadi ba dadewa za ayi a can ba nima kaya kala biyar na zaba daga cikin wa yanda ta bani ranan.

    Naso sai na nunawa mami kafin inyi amfani dasu hakan bai samu ba don busy da mami take a ranan .

  Bata da lokacin kowa har kanta ma da tashigo zata fice daga gidan ko ace ana mata sallama.

   Sai ya kasance ina daki ko ina wurin su mama kande sai idan zanwa mami din wani abinda ya shafi rayuwan ta za a kirani.

   Dan taron da akayi a dan kwana biyun dana dawo kauyen mu a gidan mami yasa na koyi wasu abubuwa da dama a furin jama,an da suka cika gidan.

   Su kansu yan mata gidan mami suna ta kansu ne yanzu kowa na shirin tafiya saidai na kula cewa kamar ba wani shiri tsakanin su da yar mami din Nuriya don ban faye ganin su a tare ba.

   Ko banza duk tafisu aji da kyau sosai ga wayewa da tsari don ko maganan ta abin koyone.

   Washe garine za ai tafiyan inda wasu zasubi jirgi wasu kuma a mota zasu tafi inda ina cikin wa yanda zasubi mota da farko.

  Amma mami tana duba list din lokacin ina dakin take fadin ban yarda abar zeey nan ba idan mun isa can waye zai kula damu kafin su iso sai dai a cire sunan wani a sakata cikin tawagan da zamu tafi.

   Wayyo Allah na ashe in Allah yasoka tsuntuwa yake maga ko a dakin ka yau nice wai zan shiga jirgi tunda mami ta furta ai kamar na shiga ne in Allah ya nufa.

    Karfe shidda yai muna a filin jirgi ranan nasha zagi gun yan matan mami don tafiyan nan da mami tayi dani a jirgi tare da kawayen ta da yaranta dama wasu daga cikin dangin su.

   Koda muka isa can motoci muka samu sunzo daukan mu nidai basai na fada ba don bakauya na koma a cikin duk da dai kowa yana harkan gaban shine.

   Amma hakan bai hana tsaraguwa ba a cikin su da rakubewa a guri daya tunda ba wanda ya sanni ko nasan shi sai mami da yaran ta sukuma bata kaina sukeyi ba.

  Duk da akwai yan aiki irina kalian da wasu sukazo dasu daga wasu wurare sai dai hakan baisa na mamesu ba ina falo ko da yaushe don kada mami ta nemeni ban kusa kamar yadda naji ta fada kafin muzo.

  Haka komai ke tafiya a tsare kamar yadda suka tsara abinsu gwanin ban sha,awa sai kallon mamaki nakeyi maza da mata ana ta cudanya a guri daya ba wanda ya damu da hakan .

  Da kauyen mune ai da hakan ya zama abin magana a gurin mutana amma nan ba wanda ya damu da hakan .

    Wai washe garine za ayi rantsuwar su mami din tunda muka iso wasu maza sukazo gidan suka fita tare da mami da yaranta manyan mazan biyu.

    Haka yasa kadaicin rashin gabnin su mami a gidan ya dameni na dawo katon falon na zauna tare da wasu mata suna ta hiran su nidai sai sani lokaci nake dan jin hiran da sukeyi din.

  Ina kallon duk mai shiga da fita don na jawo kofan da muka sauka a cikin hikima na zare key din kofan ina ji daga inda naje zaune ana tambaya na kyalesu.

   Don ba wanda zai daukacewa nice na kulle kofan sai dai da mutum yazo ya murda yaji a rufe kofan yake ya juya inda ya fito.

    Har masu tafiya a mota suka iso gidan ya kara rikicewa da hayaniyar jamma, a haka yasa na fito daga cikin falon na dawo waje na zauna.

   Balle tun isowar ya matan suke aika min harara da warning ya karasa na gudo daka ciki na dawo wajen gidan.

  Nan ma motocine ke faman shige da fice tun ina aunawa a raina ince wanan yafi kyau a, a ta dazun tafi har na gaji na zubawa sarautan Allah ido.

    Can naga dawowan su mami hakan yasani mikewa tsaye daga inda nake zaune ina kallo na nufo wurin motar nasu.

   Sannu da zuwa mami na fada daga bayan ta hankalin ta naga daddy su siyama jikokin ta suna magana.

  Hakan bai hana mami dan juyowa tana amsa min gaisuwan ba ta juya taci gaba da maganan da sukeyi na juya zan bar wurin .

   Sai kuma ta juyo tana fadin zeey karbi jakkan nan nawa ki rike min nazo da sauri na karba na ja dan nisa dasu na tsaya.

   Sun dan gama magana ta fara tafiya yana biye da ita yana fadin amma mami sai naga kamar dai bayanin farkon nan shine shawaran bi koda yake barin gashi Jafar din duk da ban san inda ya shiga ba.

    Kuje kuyi shawara dai zan dan shiga inyi sallah kafin wani abu ya dauke min hankali kuma ta fada ta fara tafiya makarrabanta suka biyo bayan ta ruuuu dasu.

    Nima binsu nayi da kallo ina mamaki duk wanan taron haka don mami akayi shi haka ?

   Naji tace on Allah ku bari inyi sallah yanzu zan fito ta nufi kofan dakin da nake zaton shine nata wanda na riga dana rufe tunda na fahinci hakan.

   Mami ai kofan a rufe yake wata ke fadi daga gefenta lokacin da hjy ta murda kofan dakin da zuman shiga dakin..  

   Tun dazun ai dakin yana rufe an rasa inda key din yake da dan mamaki ta tsaya tana juyowa kafin na karso ina fadin ga key din mami a hannu nice na rufo kofan dazun.

  Ok zeey key din yana hannun ki ashe thank god wallahi yarinyar kirki shaf na manta da zan fita in rufo dakin.

   Da sauri na ciro a cikin aljihun dogon rigan dake jikina tunda ta dan jaye wurin na gane nufin ta na isa da sauri ina bude kofan.

   Juyawa mami tayi tana fadin don Allah a dan jirani in fito tasa kai tsshiga tana fadin zeey shigo ki hada min wanan maganin nabi bayan ta muna shiga tace don Allah rufo kofan nan in huta hakana.

   Ki duba akwai magani a cikin jakka ban samu shaba da safe na fita take fadi tana shiga bandakin.

    Maganin na dauko daga cikin jakkata don nasan shi na saba hada mata na balla daidai yadda take sha na dauko goran ruwa mara sanyi dake dakin na a je akusa.

   Daidai tana fitowa ne ake buga kofan taja tsuki tare da fadin mutanen nan idan nabita nasu bana samun sallah ko azahar ban samu yiba yau balle la,asar ga lokaci na shigewa.

    Dukan kofan da aka karayi da karfi take fadin wai waye zeey bude kofan idan maishi ya shigo yaga ina sallah dole yajira idan zai iya.

  Kofan  na nufa na bude daga ciki aka turo ana fadin haba mami kin fita tun safe kin dawo kuma kin shige kin rufe kofa.

    Aisha yar mami ke magana tana shigowa dakin a cikin shagwaba idon ta ya sauka kan mami dake kabara sallah kafin ta juyo tana kallona tana fadin.

    Tare kuka fita ke nan da mami din kai na girgiza bakina kuma na fadin ina nan gida ina falo zaune na bata amsa.

    Wuri ta samu ta zauna tana maida hankalin ta furin wayan ta yayin da na shiga gyara dakin don wanan daman na samu a yanzu tun zuwan mu garin..  

    Har mami ta idar da sallolin dake kanta ta juyo tana fadi Esha ya akayi ne wai ma kunci abinci kuwa ?

   Zeey kinci abinci ita dai wanan din nasan halin ta  balle yau taga wanan taron haka a gidan nan ?

    Kaina girgiza daga inda nake tsaye ba tare da nayi magana ba kina jiran me wanan yarinyar da gidanci kike wallahi ga abinci nan ki tambayi safiya mana tunda ta iso idan baki san wanda zaki tambaya anan.

    Waya ta dauko ta kira wani layi aka dauko ku kawo min abinci na mutum uku a hada komai a ciki ta fada.

   Tana kashe wayan tare da jan tsoki kafin Aisha ta ce mami gobe fa ni dinner kawai zan yi attending.

  Kina haukane gaba dayan ku da tan uwaki zamu tafi don duniya ta san ku ta fada sai yarinyar tace but mami kinsa, , , 

   Hannu ta daga tare da fadin ban son korafi idan na fada kinsan iyakar maganata ke nan aka turo kofa wace ta kirane dauke da abincin wata hamshakiyar hajiya zakace ba zatai bara gidan kowa ba don bunkasanta sai gata itacs mai kasowa mami abincin .

  Bayan ta aje suka dan tsaya magana da mami nidai duk sai naji na takura a cikin su don Aisha ita tana dawainiya ne da wayanta bata ma saurareb su.

    Can mami ta juyo tana fadin zeey zuba muna abincin muci ko ?

     Matar ta juyo tana kallon daidai lokacin dana tashi tana fadin wanan yar ina kika samotane don ban santa ba gaskiya.

   Yata ce ta bata amsa kai tsaye tana jawo plate din abincin dana aje mata a gabanta inda ta idar da sallah.

  Kije ki lissafa min matan nan da suka zo da yamman nan za a kaisu masaukin su idan sunci abinci tafadawa matar.

    Yan kaduna ko na wani gari eh toh zaki iya lissafo min group group daga nan ki kiramin safiya tazo.

   An gama hjy ta fada tana fita daga dakin Esha aje wayan nan ki dauki abincin nan kici ta fadawa yarta.

  Ke kuma zuba naki idan kina zama da yunwa zaki jawa kanki matsala ba ruwana tana kai abinci a bakin ta.

   Zuba wanda nasan zai isheni nayi na dauka zan fita daga dakin take fadin ina kuma zaki dawo ki zauna muci a nan .

    Aka turo kofan yaya Mamud ne daddy su siyama ya shigo dakin da sallama ta karba mai tare da fadin har kun dawo ke nan yace  .

   Eh mami an samu inda ya dace saidai kudin kusan duk dayana ne ma mamud kasan kudi ba matsala bane ai a dai samu inda ya kamata din shine abu yanzu.

  An samu mami kuma danki yace a tura mai ko nawa ne kudin zai biya munyi waya dashi ban samu ganin shi ba.

   Ai da ya barshi tunda akwai kudi a hannu na don gwaunati ta bamu dan kudi a hannun mu ai.

  Sun dade a dakin suna magana shigowan anty safiiya dakin yasa yafita ni dai ins zaune cikin su a tsawale.

   Bayan na gama na fito na barsu tare da anty safiya din suna magana kayan abincin na kwasa nakai kitchen inda ake tarawa.

   Nafito da zuman komawa falo in zauna muka hade da anty Rufaida wani irin shock naji lokaci guda saida na dan ja baya don tsoro.

   Yar iska masuwa mutane asiri kin dauka ba wanda yasan abinda kukewa mami daga ke har wace ta kawo kine gidan.

   Mu zuba dake a gidan nan ki gani idan zaki sha ruwa ya fada maki a ginan nan bakince kun iya mallake mutane ba ku.

  Duk da ban gama fahintar inda zancen ta ya nufa ba na dan gane wani bangare na zancen nata kadan.

  Tana fadin haka ta juya tabar wurin ba anty rufaida ba gaba dayan su yan kaduna dana sani a gidan wani kallo na kyamata suke bina dashi .

  Na kulla da hakan ne idan sun hangoni sai inga suna kallona ana gulmata ma,ana dai sun sani a baki sun tsargeni ke nan a yanzu.

  Wanda bansan wanan dalilin ba kuma banda wanda zaimin bayanin hakan sai kawai na fara kama kaina da kowa fiye da dacan baya dan dama anty salma idan mun hadu ba wanan kallon raini ko wullakanci sai dai idan na gaishe tace zeey din mami ke nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣3️⃣


   ZAINAB IDRIS MAKAWAYAN UWA FATAN ALHERI A GAREKU KO DA YAUSHE UBANGIJI YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA YA TSARE YA KARE MUNA IMANIN MU A DUK INDA MUKE AMIN.

  

YAR UWA KADA KI DAUKI HAKKIN WANI KARAMIN ABUNE KI GUJI CIN HAKKIN DA DAUKAN ALHAKI WASU MAI IMANI A ZUCIYA TA GANE MAI NAKE NUFI NAN KIWA KAN KI DA KANKI HISSABIN IMANIN KI TUN A DUNIYA.


DARI UKU NE NOVEL KI BIYA KI KARANTA CIKIN SALAMAN UBANGIJI BA TARE DA NAUYI KOWA BA A KANKI, , , , , Yau gidan ga baki daya ya kicime da shirin fita zuwa wurin taro duk da tun cikin dare an kwashe baki a gidan an kaisu hotel din da aka kamawa mutane.

   Hakan bai hana gidan cika ba da wa yanda suka kwana a gidan basu samu zuwa hotel ba din mutane sunzo da yawa sosai.

    Ban bar dakin mami ba tunda safe dana shiga don a falo na kwanta abina bayan na gama yiwa mami duk wani abinda zan mata a lokacin.

   Tunda asuba kuma na tashi na yi sallah ko alwala a famfon dana gani wajen gidan na fita nayi alwala duk wanda ya wuce a cikin mazan dake haraman zuwa sallah asuba sai ya dan kalleni.

  Nidai na gama na shigo ciki na shimfida dan kwalina nayi sallah daga gefen da mutane ke bi a lokacin.

    Na idar na dan dade zaune gurin ina kallon masu shige da fice ina dakon mami ta idar don nasan a lokacin tana saman salayan ta tana zikiri ga ubangjin talikai don wanan dabi,an mami ce hakan.

    Can na daidaici ta gama a lokacin na mike zuwa dakin don shine aikina kuma don shi akazo dani watau kula da al,amarin mami din.

  Sai kuma yanzu da nakan dan wa yarta wasu hidima a gidan don bata da damuwa ko ci fuska gata bata shiga lamarin kowa halin su yana yanayi dana anty salma itama saidai salman wani lokaci zumace ita ga zaki ga harbi idan halinta ya tashi.

  Da sallama na tura kofan na shiga sai dai nayi mamakin ganin su yaya mamud a dakin lokacin shida wanan bakon danta da yazo.

   Da gani wani maganan suri suke a tsakanin su a lokacin hakan yasa na juya da sauri zan bar dakin har su fita don ban san shigarsu ba lokacin sai ganin su nayi kawai a dakin.

   Muryan mami ke fadin shigo mana zeey ina kika shiga ne tun jiya da dare ban sakaki a ido ba na dauka nan zaki kwana ai tunda dakunan duk akwai mutane.

  Yaya mamud ya juyo yana kallo na shiko dayan ko dago kai baiyi ba ya kalli inda nake na fara takowa ina fadin.

   Falo na kwana mami na bata amsa kai tsaye kafin in karasa shiga dakin na durkusa har kasa gaban ta yadda na saba gaida ita kafi in jiyo i gaidasu daya bayan daya na mike.

    Kada ki sake kwana a falo baki gudun sanyi ya kamaki ne ko wani abu ya sameki nan.

   Nace mami akwai wa yanda muka kwana dasu ai koma dai menene amana kike a gareni ta fada ta juya tana fadin mamud kana da son gardama.

  Nikan nasa kai na shige ban daki don in fara gyara nan kafin su gama su fuce in gyara dakin ga baki daya.

    Har na gama da bandakin na fito suna cikin dakin basu fita ba haka yasa na koma falo na zauna har su fita .

  Ina nan zaune falon saiga Rufaida ta fito daga dakin da suka kwana tana ganina tace yauwa ke zo nan ki dibo muna ruwa a waje.

   Tashi nayi na karbi bucker din a hannun ta na nufi hanya tana fadin kiyi sauri don gaba daya dakin zaki debo muna ruwa muyi wanka.

  Ni dai na tafi bance komai ba na diba a mayawa na uku ne na samu masu aikin break fast suna wanke kayan miya dole na tsaya jiran su.

    Don gaba daya ruwan gidan ya tsaya ba,a san dalilin haka ba sai ga Rufaida ta fito tana fadi ke karamar yar iska ko ?

  Tun dazun ki debowa mutane ruwa kin tsaya iskanci dama ai tsiyan matsiyata ke nan basu iya samun arziki ba sai su ganshi a banza.

   Excuse me ya fada daga baya ta inda take tsaye da hannuwa saman west din ta sai masifa take dani ni kuma na juyo ina fadin nba tsayawa nayi ba wa yan nan na sama suna aiki wurin.

   Maza ki debowa mutane ruwa ko ranki ya baci shine taji ana ce mata excuse me ta dan juya don jin muryan wanda tayi a bayan ta.

   Da sauri ta jaye mai a  hanyar da tai banga banga tana masifa dani daga saman step din.

  Wurin security din shi ya nufa yana saye da farar jallabiya kal mai sulbi a jikin sai kamshi ke tashi har inda muke saida kamshi yakai ga hancin mu.

   Jin ta gaida shi bai aksa ba ya wuce ina jin matan dake wurin na fadin wanan duk cikin diyan hjy yafisu kyau da kwarji saidai shi din miskilin karshe ne sosai.

    Sai lokacin na dago kai na dan saci kallon shi kafin in koma kallon Rufaida data suma a tsaye wurin da take kan kallon shi.

    Dauko ruwan da ta farga nayi harna zo gabanta ina jin tana sauke wani irin ajiyan zuciya na shige ta biyoni a baya.

    Daga ban dakin dana aje ruwan ina jin tana fadin kai yanzu naga hero a waje ashe fitan danayi bana banza bane tunda har na samu yai min magana yau.

    Wai me kike nufi Rufaida kin san dai alkawarin su daddy ai ko tace ina ruwana da wani alkawarin su can in dai na samu ya kyasa min.

    Da wanan cece kucen har na fito daga dakin suna kanyi na barsu nan dakin mami na nufa kai tsaye daga nan don in gyara.

  Ina shiga ranan ne karo na farko da mami tayi min fada kan aikinta don ina sallama tace zeey mena kawo kinan kiyi tun dazun kin shige ba a ganki kin san zan fita yau da wuri.

  Me ke damun ki yanzu ne tunda kikaje gida naga kina son ki sukurkuce min fa sai ayi ta neman ki kiyiwa mutum abu baki san kizo don kanki ba.

   Mami kiyi hakkuri ba wucewa nayi ba dama daga bayana naji ana fadin is OK mami tunda tazo din.

   Muryan ne ko mai maganan abin kallo na juya don ganin mai magana suka karaso tare da jamal, sai jamal ke  fadin .

  Wata kila wani ne yasa ta aiki don naga tana diban ruwa a waje zuwa ciki cikin harshen turanci yake magana shidai tun maganan farko bai kara magana ba ya samu wuri ya zauna.

    Wa kike diban wa ruwa mami ta juyo tana tambayana tare da tsureni da idanuwan ta a kaina.

   Anty Rufaida ne tace in diban masu ruwan wanka dukka dakin shine na tsayayi dama na bata amsa.

   Wai mai Rufaida take nufi ne akan yar nan mami ta fada da hausa barta zamu hadu bari a watse gurin taron nan in mata tsiya.

   Kayan dake saman gadon na fara tatarawa ina nadewa na tara gefe guda sun dan dade dakin  don maganace mai muhinmanci sukeyi a lokacin naga an aiki jamal mami na fadin don Allah kada ka tsaya don munyi waya dashi yanzu.

    Tare suka fita lokacin mami ta fara shiri tana fadin in miko mata wanan in bata wancan har ta shirya cikin wani rantsantsen lace da akai mata dinki ya sauko zuwa gwiwan ta.

   Ga wani sarka da na fitar a cikin wani gida mai kyau da dauka ido ta nuna min yadda zan saka mata shi.

 Ta tsaya a gaban mirrow dakin tana gyara kwalliyan ta da kyau da sauri na karasa gyaran dakin na share don ta fita zuwa falo.

   Dakin ya koma tsab na saka mai kamshi gadon yayi kamar ba a kwana saman shi ba lokacin.

   Gaba daya mami da yaranta har anty Aisha suka shigo dakin tare da ita sun sha ankon farar shada sai maiko jikin shadan da motsi yakeyi sun saka mami a tsakiya sai Aisha ce da wanab bakon da ban san dunan shi a baya suma magana sukeyi a cikin rada kamar Aisha zata shige mai jiki.

    Ganin yadda suka shigo suna magana haka yasa da sauri na zo fita sai muryan jalal ke fadin ke yarinyar hajjaju ana magana dake fa.

    Key ya mika mai yace ya bani shi jalal din ke min bayani wai inje in gyara mashi dakin shi yana bukatan gyara.

   Na rusunan na karbi key din harna juya sai kuma na juyo ina fadin ina dakin yake yaya ?

    Kwatance jamal ya fara min naji yaya mamud na fadin jeka nuna mata dakin mana har zan fita mami tace ki rike key din dakin nan guda tana nuna min kofa.

  Na tsaya na cire na tafi yana waje yana jirana har muka nufi wani part ya nuna min da hannu.

  Daga kofan shiga part din na hango wasu irin zaratan maza kartai dasu su shida kowa ya saka bakaken kaya a jikin shi.

     Tsoron sune ya kamani da fargaba na nufi wurin na gaidasu na sa key ina bude kofan kafin in tura da sallama in shiga.

    Bin ko ina na falon da nagani nayi da kallo komai yana a tsare ga wani kamshi yana tashi a dakin ta ko ina kada in tsaya kallo wani ya sameni haka yasa nasa kai zuwa kuryan dakin .

  Nan ma nasha kallon saidai ban yarda na tsaya ba ina kallo ina abinda ya kaini dakin ko ina sako da lungun dakin saida na sharo shi tasa na goge kafin in fito sha daya saura.

  Tun tun karowana part din da muka sauka naji gidan yai min tsit babu hayaniya har haraban wajen gidan babu wani motsi sosai kamar yadda  na barshi .

    Babu kowa a part din sai motsin masu aiki da nake ji a kitchen din gidan tsayawa nayi ina tunanen sun tafi ke nan inda zasu ashe ?

    Ke nan na dade a dakin ina gyara ban sani ba har aka wuce akabarni sai kuma naba kaina amsa da fadin ke yar aiki wazai kaiki wurin taron manya haka.

   Wanka bake bukata don haka na nufi dakin mami tunda can kayana suke tunda mukazo ina shiga na rufo kofan dakin na shiga ban daki a gurguje da tsoro nayi wanka har na shirya na fito na rufe dakin.

   Kitchen din gidan na nufa don yunwa nakeji lokacin sosai gaida masu aikin dana sama nayi ina tambayan abinci.

   Daya daga cikin su mai hausar gwarawa take fadin abinci yanzu sun cinye komai nasu sun tafi ai sai ta hada da yaren su kuma naji daya na mata yare sai matar tace in tsaya ta debo min akwai wanda suka ajewa wasu basu zo ba.

    Suna ta yaren su har ta hado min na karba ina godiya tare da dawowa falo na zauna naci saida na koshi na kwashi kayan na mayar kitchen din da zuman in wanke da sauri matar tace ka bari wanan zaita wanke ai.

   Nikan na fito na barsu don jin abinda ta fada na zauna a falon ina kallon tv dake aiki ganin yadda aka bar falin na mike na gyaro ko ina na gidan ban samu kaina ba sai daya da wani abu.

    Alwala nake daidai lokacin dana fara jiyo hayaniyan dawowan mutanen gidan nayi alwalana na shige ciki a falon kamar yadda nayi da asuba ko wanan ma nan na tsaya nayi.

   Suka fara shigowa daya bayan daya kowa a gajiye sai shigowan anty Aisha na mike da dan sakin fuska nake gashe ta.

    Ta amsa min tare da fadin a, a yarinyar mami yaya bakije gurin taron bako kinje banganki bane tana fadin tana magana nidai nayi murmushi kawai.

   Har ta danyi nisa ta juyo tana fadin zo zo zo yarinyar mami tana miko min hannu na nufi gurun ta tare muka shiga dakin bayan ta bude ta fara yarda jakkan hannun ta saman gado na dauka nakai wurin filon na aje mata shi.

    Taje help me to remove dis cloth don Allah tun dazun duk na gaji dasu a jikina ja min zep please ko zanji dadi haba wanan wahalan yai yawa.

   Naja mata zip tana ta tsuki da fada bata tsaya komai ba ta kwabe kayan ina kawar da kaina gefe ta fada ban daki tare da barin kayan a watse.

  Tattara kayan na farayi ina nadewa kafin ta fito wanka na gyara ko ina na fito haka yayi daidai da shigowan mami gidan yan bambadanci suna bayan ta suna fadin saike hjy maryam mace mai kamar maza mata a gidan Alh ma,azu gin sun buga sun barki Allah dai yajikan maza maza sun kwanta.

    Ko yanzu yasan baiyi zaben banza ba yabar baya a duniya uwar zaratan maza kece uwar gwaunan gobe kece uwar shugaban kasa, .

    Wata ta karbe da fadin kece uwar manyan duniya ga gobe gaba sallama baya sallama yar manyan mutane.

   Nikan na suma wurin kallon yadda ake masu barin kudi kamar ba neman su akeyi ba.

     Zama mami tayi yayin da kawayen ta suka kewayeta ta ko ina ni sai lokacin ma naga wasu da ban gansu jiya ba.

   Take falon ya cika da jama, a ta ko ina babu masaka tsunke a gidan wuri ya kaule da ci dasha ina labe daga kofa ina kallon ikon Allah don ni ban taba ganin bukin manya ba irin haka.

    Wasu nacin abincin wasu na haraman sallah wasu kuma suna mayar da magana mai rabon abinci suna rabo kungiya kungiya.

    Nama girman shi yakai dunkulen hannun mutum don girma duk nau,in da kake so na abunci shi za a baka a wurin.

   Daga inda nake rakube naji mami ta fara kiran sunana da sauri na amsa da gani mami na isa guri  ina gaida ita.

   Gaba daya mutanen dake gurin sun zuba min idanuwan su hannu mamu ta mika min na isa wurin ta da sauri tajawoni tana rada min in shiga daki in duba cikin turamen zanin dake zube gefe a kasa in dauko guda biyar in ba matan dake mata kirari .

    Na amsa ina gyada kai na matsu in bar wurin daki naje na bude na dauko kayan kamar yadda taimin bayani nazo dasu falon kowa ya saka min ido.

    Ina takowa da zannuwan a hannu na daya daga cikin matan da akace in kawowa tana kyala ido ta fara fadin kaga inda kyau asali yake farar mace alkyaban mata.

  Diyar hjy takawan ki lafiya dayan tace fari kun gadane ba ku ba shagon maida baka fara kaga jinin larabawa asali irin gado bana gada ba.

    Yarinya sai gidan gwauna ko minister minister ma mai fada aji irin uwarki ba muna minister ba akoma gefe ba office .

  Dayan ta karba da fadin haka yake don yau mun sheda mun gane bambamcin ayyah da tsakuwa a bainan jama, a.

   Nidai har jiri nake gani don idanun da aka watso min a falon na nufesu na mika masu zan juyo mukayi arba da yan matan Rufaida da Nazifa tare da wasu mata a zaune suna magana kasa kasa sai hararana sukeyi.

   Na raba na koma dakin mami na gyara wurin dana dauko kayan na fito har lokacin sai kirari sukewa mami din.

   Ance massadan ka fadawan ka a inda na tsaya idanun su ya rufe basu san ina wurin tsaye suke gulma akan mami.

    Wai haka duniya yake ai gashi bai gina kowa ba sai matarshi da diyan shi kawai ya inganta rayuwan su.

   Har mami tana daga kai dama ba,a san asalinta bane ko yar waye yar hakimin kauye kawai da ita yanzu ta samu duniya taba ganin kamar tafi kowa.

   Jifa kai duniya ina zaki damu kan hassada wai kuma sun zo ne har Abuja dalilin ta don tayata murna fa kuma suka koma gefe suna gulman ta.

  Kafin dayan ta dago kai mu hada ido ina kallo ta zuguri dayan matar dake magana ta dago mukai arba na watsa mata wani kallo don girman ta ya gama zubewa a idona ko tunda na shedata tana zuwa wurin mami ko a kaduna.

   Tun yamma nake ta kallon ana shiri muna idar da sallah mami tayi kirana muka shige dakin da wasu kawayen ta biyu.

    Shiga ta alfarma mami tayi ina ciki sai faman miko muna wancan mayar da wanan dauko muna wancan abin ko mami ta ce zee ina abu kaza din nan ?

    Haka dai har mami ta shirya wai dinner za, a tafi a wani katafaren hotel nan cikin garin Abuja.

   Mami kan hankalin ta ya dauke bata takan kowa a gidan don uzurin gaban ta yau data zauna za a kirata gefe da magana kus kus.

    Har aka fara tafiya gurin dinner din ina kallo su Nazifa da Rufaida da su Rubby suka fito sai wani shakiyanci sukeyi a tsakanin su.

   Wanan na fadin yau kan akwai babban kamu don bazan fito ba sai na sace zukatan mutane da yawa .

   Wanan ta daga tayi wani juyi tana gwada tafiya har suka gama iya shegen su suka fice gidan sai wani yauki da yanga suke yi nasan harda kari don inji haushi.

   Saboda ina jin Nazifa na fadawa wata tsohuwa da ban santa ba a cikin dangin su tsofi da mara gata su zauna gida ba, a zuwa daku taron manya don darajan wasu baikai can ba .

  Tsohuwar dai tayi mata dakuwa da hannu ta fita tana dariya ajiyan zuciya na sauke bayan fitan su falon ina wasa da yan yatsuna sai ga anty salma ma sun fito da wasu yan mata guda biyu ina ganin su nace anty salma sai kun dawo don dai tace inzo mu tafi.

  Tunda nayi dan kwalliyana a lokacin amma sai ta daga min hannu kawai suka fita na koma na zauna ina tunanw kala kala a raina.

  Can an dan dade sai ga anty Aisha ta fito tana tako daya daya tana waya na dago ina fadin anty Aisha sai kun dawo .

  Ta juyo tare da fadin yarinyar mami baki tafi bane daga haka ta sa kai ta fice a gidan  bayan fitan ta naji gaba daya zaman wurin ya isheni.

  Don haka na yanke shawaran fita haraban gidan in sha iska duk da darene amma wajen kamar rana don hasken da ke akwai a wurin.

    Wuri na samu na zauna gefen flowers ni daya sai tunane barkata da kalle kalle nakeyi kafin kamshin turaren nan da tun rana dana aiki a dakin yake a jikina badon na cire kayan na daina jin shi a yanzu ba.

     Ta  dan nisa kadan yazo ya wuce ni zuwa wurin motar shi lokacin ne na san da mutane a wurin sai ga bodyguard din nan nasa dana gani da rana sun taso zuwa wurin shi.

    Kallona ya koma can na samu abin gani da zagi a raina ganin yadda suke mai kamar ba mutum ba dan uwan su.

    Mota ya shiga suma suka shiga dayan motan bayan sun rufe mai suka tayar da motar hasken motar su ya haskani sosai inda nake nayi saurin dukar da kaina kasa.

    Shiru shiru motar bata tashi ba na dago kai da zuman in kalle su sai ganin mutum nayi a gabana yana fadin cikin harshen turanci boss yace ki zo.

    Na nuna kaina tare da fadin ni yace eh ya juya na mike na bi bayan shi zuwa wurin motar tun kan in karaso aka bude motar ina zuwa naji ance shiga mu tafi.

    Murna zanyi ko mamaki duk babu daman wanan saboda tsoron daya rufeni lokaci daya banda zabi na shiga gefen da aka bude min din.

   Wani sanyi da rabane ga kamshi ya dakeni lokaci daya sai dana zauna nake fadi ina wuni a cikin hausa ban sani ba ko ya amsa min don an rufe kofa a lokacin.

    Har muka kai wuri  ba wanda yai magana a motar ga wurin da gidan akwai nisa sosai a nawa ganin.

    Wurin ya cika da motoci da ababen hawa ga jama, a wasu a wajen wurin sai security kala kala dana gani gani da tsoron yan sanda tun a kauyen mu.

   Motar ta samu wuri driver ya tsaya daga inda muke muna jin magana da kidan dake tashi a cikin wurin.

   Duk muna a cikin motar zaune nidai na kurawa sarautan Allah ido sai can aka bude motar duk da an bude ya dan dade bai fito daga cikin motar ba.

  Can ya sauko katan mazan nan suka wani zo suka tsaya wurin motar wani ke fadin in fito na fito da sauri har sunyi gaba na bi bayan su.

   Gap da zai shiga wayab shi yai kara ya tsaya a wurin yana amsa waya haka yasa na yanke shawaran fara shiga cikin inda ake taron.

    Sai masu tsaron get din wurin suka hanani shiga wai sai na nuna masu pass dina wanda mutum yafi a kirga sun shiga ni ina wurin tsaye.

    Har sojan dake kofan yana son ture da hannu biyu kyaleta tare muka zo ya bashi amsa bamu shiga ba saida akai muna bincike.  ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣4️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWAJUMMA, AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADA MU DA ALHERUN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA UBANGIJI YA YAFE MUNA KURAKUREN MU AMIN YA ALLAHU, , , , 


YAR UWA LITTAFIN KUDINE DON DARAJAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BANA FITAR MAKI DA HAKKIN RASHIN SANI NA FADA MAKI ALLAH YASA MU DACE AMIN, , , , , 


  DARI UKU NE KUDIN SHI DON SHIGA GROUP ZAKI IYA TURA WA TA WANAN ACC 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN NA DARI UKU KACAL, , , , , Ina tsaye duk na kagu in shiga inga abinda ake a cikin dakin taron da nake ganin mutane kala kala suna shiga wasu ma ba mudulmai bane daga cikinsu..

   Nayi kamar zan bi wani tawagan yan mata da naga zasu shiga sai sojan dake kofa ya kalleni yai warning dina da bulalan hannun shi .

   Dole naja baya na tsaya ina mazurai da idanuwa tare da dan bin ko ina da kallon mamaki a wurin don gaskiya ban taba zuwa irin wurin nan .

    Sojojin kofan na naganin shi ya gama waya bodyguard din shin sun sashi tsakiya suka fara jayewa a hanya suna girmama shi.

   Hannu ya daga masu yana kokati shiga nayi saurin shiga cikin su da saurina don kada su barni gurin ban san yaya zanyi ba gashi tunda nazo banga wani wanda na sani ba a wurin.

  Sojan ne yayi azaman riko ni sai ya juyo a hankali kamar mai rowan magana yace don't sojan yaja baya da sauri ya kame.

   Wani iri naji kaina ya amsa lokaci guda ganin irin taron mutanen dake wajen gasu zaune saman kujeru masu kyau kowa yayi kwalliya gwanin ban shawa,a.

   Ba zan iya sheda kowa a wurin ba idan ba karya zanyi ba saima ince kowa ya zubu muna idanune shigowan mu ashe ban sani ba mai magana ke sanar da shigowan dan mami dana biyo tawagan su.

   Biye nake dasu a baya kamar jela har aka nuna mashi wurin zama wani table babba yasha kayan ado dana ciye ciye saman shi.

   Da idanu yai nune sai wani ke ce min in zauna wai na dan kai zaune a hankali kamar yadda kowa ya zauna kaina na sade kasa.

   Ba mami ba duk wanda ke dakin taron hankalin shi ya dawo garemu ne ance yaro da kudi abokin manya.

  Wai ashe da Done nake zaune ban sani ba a wurin sai mamakin koni wacece wanda basu sanni ba suke yi.

   Wa yanda suka sanni kuma suna mamakine meye hadina dashi muka shigo tare ni yar aikin gida abinda ko yan gida basu samu gatan hakan ba sai karamar yar aiki kamana.

    Anci gaba da gudunar da shagalin da ake inda mawakan hausa dana sauran yare suke nuna bajintan su a wurin.

    Ga masu rabon gifts suna faman rabawa table table don komai a wurin a tsare ake yin shi tun ina kallo har gajiya ya fara kamani don zaman kurame muke a table din mu.

  Dan gara su dan motsi kadan zaiyi sai kaga daya daga cikin bodyguard din nan sun duka suna magana dashi a kunne.

   Har lokacin da muka tashi sai dai mutane suzo su gaisa dashi su wuce yana zaune bai daga ba sai da zasu tafi ne dayan ke min magana kamar rada yana fadin in tashi mu tafi.

  Haka na taso shike gaba sai ni a baya bodyguard din dun samu a tsakiya kusan ince shine farkon fita wurin da gani baison hayaniya don sai faman murza goshin shi da yake yi kadan kadan zai murza goshi har yakai ga mikewa muka fita.

   Kamar yadda mukazo haka muka koma ba wanda yai magana a motar har muka kai gida ni ban ma sani ba saida naga mota na shiga gidan nasan mun kawo.

   Aka bude motar zan fita na juyo inda yake zaune kamar ba zai fita ba nace na gode yaya don ban san sunan shi ba dan mami bako nake kiran shi dashi.

   Ina hawa steps din ne naji muryan dayan bodyguard din shi na fadin hjy ga wanan wai ki dauka inji boss wai ashe abinda aka rabane a wurin daya yakai a mota shine yanzu suka ban.

   Haka na shiga da jakkan niki niki don gifts din manya daban aka bada su ba irin wanda aka rabawa kowa bane wurin.

   Daki mami nakai jakkar har biyu mai kama data matafiya shake da kayan da ban san ko meye a ciki ba na aje.

  Hayaniya ne ya fara karde gidan lokacin har barci ya soma daukana don ban dauki hakan a komai a raina ni dai nasan ya taimaka min saboda halin kirki irin na uwarsa ya kaini naga buki haka na aje kawai a raina.

   Sabanin sauran jama,an wurin dake tunane kala kala yadda aka ganni dasu kowa da irin nashi fassaran a ran shi.

   Nikan ganin mami bata shigo ba yasa na kwanta kasa nayi filo da jakkunan kayan da nashigo dasu har barci ya daukeni hakana ban sanni ba a wurin.

   Ko da mami ta dawo ta samu ina barci a dakin ta a kasa na dunkule a wuri daya kallon tausayi tayi min yadda na kwanta a maraice a kasa.

   Sai taji komai da take son tambayana data dawo ya kawu a zuciyar ta bata tayar dani ba sai dai can hayaniyar suce ta tayar dani daga barcin.

  Da sauri na mike ina fadin mami sannuku da dawowa maki ina murzan ido .

   Sai mami ta juyo tana fadin tashi kikayi kuma koma ki kwanta nima a gajiye nake ai yanzu sallah zanyi in kwanta.

    Mami me zan maki yanzu na tambaya ta juyo tana fadin bakiji mena fada ba ki koma ki kwanta abin ki dare yayi yanzu sosai.

    Washe gari da safe na tashi kowa nata sallahfita nayi waje ca wurin famfo wajr inda na saba yin alwala nayi na dawo falo nayi sallah.

   Na dan zauna don jiran mami ta idar kafin in kwatanta in tashi zuwa dakin tana zaune suna magana dasu anty safiya da anty sa,a da wata mata.

   Gaidasu nayi na mike na shiga bandaki na fara wankewa kagin in hadawa mami ruwan zafi na fito yanzu sun karu a dakin yasa na fita na barsu a ciki na dawo falo saman kujera na takure a wuri daya  .

    A yadda na lura wasu daga cikin bakin suna shirin komawane a ranan garuruwan da suka fito dan yiwa mami kara sai yanzu nasan mami mutumiyar mutane ne sosai.

  Yauwa zonan yar iska manya kawai mai mugun nufi dama nasan ba banza kika bar mami ba shegiya.

   Na dago kai ina duban dawa anty Rufaida ke wanan magana haka na fara waige waige ina duba sai naga tana nufo inda nake tana fadin .

  Bada ke nake ba kin tsaya kina kallon mutane yar iska nuna kaina nayi da hannu cikin mamaki ina fadin ban san dani kike ba ai anty na mike tsaye.

  Juyawa tayi haka yasa ba gane nufin ta nace anty mami zata nemeni yanzu don tace in bar nisa da ita jiya da kika sani diban ruwa tayi min fada.

  Ke ni kike fadawa wani mami tace kibar nisa da ita kizo dakin mu yanzu ina jiran ki idan baki zoba kuma kin san sauran.

   Juyawa nayi na kalli dakin mami kamar zanyi magana sai kuma na bi bayan Rufaida din zuwa dakin su.

    Ina shiga takai min mangara a kai da niyar kaimin mari saina dafe ta samu kaina kallon mamaki nake mata don ban san abinda nayi mata ba haka ?

    Ke yar iska yaya akayi kibi hero zuwa gurin jiya wai tana zare min idanuwanta waje tana son jin amsa daga bakina.

  Shiru nayi don bansan abinda take magana a kaiba lokacin ra kara maimaita tambayan ta nayi shiru Nazira tace idan ma ke manyace kici kanki kisha bakin ruwa don bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane.

    Sai wace akecewa rubby tace wanan ai na fada maku snake ce a ciki ku ga kyau ga daukan hankali ga duk wanda yasan abinda ake kira da matar manya.

   Don Allah rubby ki daina wanan maganan haka karta dauka ita din wata tsiyane can ta ban amsa kawai don jiya shegiya ta hanani barci da dadi duk na rufe ido yar iska nake gani a cikin su.

  Turo kofan da akayine ya dauki hankalin kowa a dakin  ba kowa bane sai anty zulfa yar gurin kanin mahaifin su Rufaida tana fadin ke kina nan ga mami can na kira ki.

    Ban tsaya jin komai ba na mike na bar dakin da ssuri na nufi dakin mami na dauka zatayi min fadan haka sai naga sabanin hakan tana fadi yauwa zainab don Allah zauna ki hada min wanan kayan kafin in fito wanka zan tafi dasune in sallami mutanen yola don karfe tara jirgin su zai tashi.

   Na amsa da to mami tana fadin ki saka komai daya daya a cikin ko wani jakka tana fadin haka ta shige ban dakin.

   Zama nayi na saka kayan kamar yadda mami ta umurce ni inyi mata tana fitowa ta zauna shafan mai tana umartana dana bude jakkunan ta gani.

    Har ta gama shiri a gurguje tana fadin in kwasa zuwa cikin motar ta dake wajen gidan fake na na aje sai ga driver yazo yana fadin za a saka a cikin motar ne nace eh mami tace in kawo nan zata fito yanzu.

  Sai gata mun hangota suna tafe suna magana ta kawo inda nake tsaye take fadin idan kin gyara dakin zeey ki mayar min da sadkokin ida muka dauko su jiya.

   Sai kin dawo mami na bata amsa ina juyawa zusa cikin gidan kai tsaye dakin na shiga na samu mami ta barshi a bude.

   Gyara komai nayi tsab na shiga ban dakin a gurguje don nayi wanka sai dai kuma har lokacin ina tunanen abinda su Rufaida sukai min wanda bansan akan me suke magana ba akai.

  Mami ta dawo bayan bakin nata sun tafi nan kuma ta shiga sallaman masu tafiya a mota don komawa kaduna.

   Suma tana daki tare da su anty safiya da kannenta biyu suna kasafa abinda ake bawa masu tafiya.

  Zuwa karfe biyu gida ya koma sai mu kadai a cikin sa sai kuma kannen mami da basu tafi ba suna daki da anty salma wace sai yanzun na fahinci akwai mahaifiyarta a cikin su ashe don basu da kama sosai da uwar da mutum zaiyi saurin gane hakan.

    Mami ta tashi don yin sallah azahar saboda dan barcin daya dauketa a lokacin don gajiyan dake jikinta.

  Nima na danyi barci bayan gyara falon gidan danayi duk da girman falon amma hakan bai dameni ba na tsaya na gyara shi fes.

    Ina zaune ni kadai a katon falin sai tv dake aiki jefi jefi nake dan mayar da hankali wurin kallon abinda akeyi a ciki.

    Eyyeh zama ma kikayi saman kujara ke nan ke gaki mara ta ido ko a gidan ku akwai irin sane halan da zaki zaunawa mutane harda dora kafa sama.

    Ina sauke kafan naji muryan Anty Aisha na fadin me kuma tayi yanzu dan ta zauna kawai a kasa kike son ta zauna ke nan .

   Aisha baki san wanan munafukar yarinyar bane wallahi sai ta dinga yin abu simi simi kamar wata ta Allah can da ita nan ko munafukace ta gaske.

    Ku daina yin hakan mana yarinyar nan bata da wani aibun da za,ace kuna mata haka ai tana fitowa daga daki dauke da chip's tana ci a hankali ta nufo wurin mu.

   Wai kin san wanan bata aje kanta a kusa ba jifa jiya harda mannewa yaya  J zuwa wuri dinner.

    Kin san yan kauyen nan da bakin shishigin tsiya ko ya akayi ma tabi bayan shi ko tsoro babu.

    Wanan she most go back to her village kafin rigiman ta ya fi nan don wallahi ni gaba daya nama tsaneta kwata kawata wallahi.

   Haba haba Aisha tace cikin muryan ta na sanyi irin nasu meye a cikin har kina fadin kin tsaneta haka yarinyar nan she is good and beside mami tana jin dadin zama da ita sosai so kima bar wanan magana kada ku hadu da mami.

   Ta mike tana fadin ashe na kusa barin gidan nan don ba zan iya zama da wanan yar iskan ba  da take neman nuna ita watace a gidan nan.

   Har abi  yakai can haba bai kamata ba kina fadin haka kan zainab don ba ruwan mu da ita don Allah kada hakan ya jawo wani matsala mai girma.

   Ina laifin wanan yarinyar a nan itace fa dazun ta gyara falon nan haka muna sharan barci a daki ita bata huta ba.

  Tace a fusace ni dai bana son ganin ta gidan nan ne tare damu I just hate d girl wallahi.

    Aisha tayi murmushi tare da daukan chip's din ta tasa a baki kafin tace ni banga wani aibunta ba wallahi.

   A gadarance tace tana wa mutane shishigi da yawa a gidan nan ko don tana ganin mami na kama matane oho ?

   Ru,faiidaaahta fada a wani irin yanayi kamar mai warning din ta sai kuma taci gaba da cin abinda ke hannun ta ba tare data furta komai ba kuma .

  Juyawa Rufaida tayi a fusace tabar falon ta bita da kallo tana girgiza kai kafin ta dago ta dubeni inda nake tsaye a rakube tace zauna.

   Ba bata lokaci nayi kokarin zama kasa don warning din da rufaida tayi min dazun kan kujeran da har ta zagi gidan mu.

   A, a kasa zaki zauna zauna a nan tana nuna min gefen da take zaune na girgiza kai tare da fadin akan hawa kujera yanzu anty Rufaida ta zageni.

   To ai yanzu ni nace ki zauna ko ta fada cikin rashin damuwa sai dana danyi jimm kafin in zauna a saman dayan kujaran a takure daga bakin kujeran don ban yarda na zauna ciki sosai ba kada kuma a kara zagan min iyayyena wanan karon.

   Kaina a kasa sai wasa nake da yan yatsun hannuna jin ta kira sunana yasani dago kai na dan kalleta kadan tare da kara sunkuyar da kaina a kasa.

   Sai naji ta dan sake murmushi tare da fadin feel free with me zee I am not like Rufaida OK.

   Na kula baki da walwala a gidan nan ko yaushe kamar a takure kike ina son sanin damuwan ki idan ba matsala.

   Jin tayi shiru yasa na dago kai na dan dubeta kadan ni take kallo a lokacin ganin na kalleta ta dan daga min kai tare da fadin ke nake saurare zainab.

  Ta sake fadin tell me meye matsalan ki ne meke damuwan ki ko yaushe kike a takure ?

    Ina son sanin menene sirin kin san ABU A CIKIN DUHU SIRINE,  jin haka yasa na dago kai na dan kalle ta tare da fadin sirin me kuma Anty Aisha ?

   Sirin rashin jittuwan ki dasu mana nake son sani sai da dalilin ai hakan ke faruwa.

   Da kyat na bude bakina na nace banda matsala a komai sai dai su anty Rufaidane suke yawan takura min har tana zagina da iyayyana don kawai taga nazo yin aiki a gidan su.

   Zagi kuma zee koda yake koni yanzu naji yadda kukayi ko dukan ki zata iya ai a yadda ta nuna din .

  To wai me ya kawo hakan a tsakanin ku ne don na kula tunda na dawo hutu da abubuwan dake faruwa a gidan nan.

    Ko kina tunanen wani abune ya jawo hakan ke a tunanen ki zainab don naga dai ba shiga harkan su kikeyi ba ke a gidan nan.

   Idona ya kawo kwalla nace sai nake gani kamar don irin yadda mami take min ne sukewa haushin hakan don mami bata daukeni yar aiki ba kamar yarta ta daukeni ta jini.

   Sai suke ganin kamar ban cancanci hakan ba tunda nidin ba jinin ku bane da mami zata sakani a jikin ta.

    Umm, umm inda wanan da wanan gaskiya amma hakan ai ba zai jawo wanan tsanar haka ba a tsakanin ku tunda mami bata ragesu da komai ba su din ma tana nuna ita ta haifemu ga baki daya ai ga nawa ganin.

  Anyway koma dai meye ki kara nisa dasu duk da nasan kina hakan zangan su inyi warning din su ba tare da zancen yakai kunnen mami ba.

  Nagode Anty Aisha nace a sanyaye koba komai ta nuna min kaunarta a gareni ai tunda na samu kula a wurinta.

    Muryan tane ya katseni tana fadin ke din ce zeey da shegen kyau wallahi kila hakan sukewa kyashi kin san mu mata ai yadda muke.

    Nima kaina shigarki ta jiya saida naji kamar karna baki kayan nan don ban dauka haka suke da kyau ba.

   Saida nagan ki dashi a jiki nasan yadda sukewa mutum kyau ashe idan ya sakasu don jiyan nan gaskiya kin dauki hankalin mutane da yawa gaki kuma tare da big boss da yan mata da yawa a wurin suke son kasancewa tare dashi.

   Sai kawai aka ganki dashi by surprice kin ba kowa mamaki a wurin sosai don ba wanda ya zata hero zai tsaya duban wata mace ko wacece .

    Saidai bamu san sirin ba don abin ya bawa kowa dai mamaki gaskiya har mami kanta tayi maganan haka.

    Tausayina yaji shine kawai anty Aisha kin san irin ku irun tausayin na kasa dasune .

   Kafin tayi magana wayan ta yai kara ta dauka sai naji tana fadin gamu a falo tare da ita yasa nayi saurin dagowa ina duban ta.

   Kije mami na neman ki a daki ina jin haka na mike da sauri zuwa amsa kiran mami din yayin da Anty Aisha ta bini da kallo har na shige dan lungun da zai sada mutum da dakununin gidan.

    Zaune na samu mami tana duban wayan ta,  na shigo da sallama ta dago tana fadin duba min ko masu girki sun gama a kawo min nan don bazan fita dakin nan yanzu ba hutu nake so yau.

   Da sauri na tashi zuwa kitchen din inda na samu anty Aisha tabar falin ita ma na shiga kitchen na fadawa madu aikin sakon mami din.

   Nan danan suka shiga hada hadan hada nata abincin cikin wani katon try na dauko na kawo mata .

   A dakin na samu anty Aisha tare da uwar suna magana shigowana sai sukai shiru mami na kula da tana bina da kallo kafin nace ga abinci mami.

  Yau ajeshi nan don har ruwa da drinks sun saka a ciki na juya zan fita take fadin zo nan zeey na dawo da sauri zuwa gareta.

   Nakai kasa take fadin yau zeey yaya akayi na ganki tare da jafar jiya a gurin buki ?

    Da sauri na dago kai ina fadin Jafar mami a, a bani bace nikan da yayan nan da yazo na tafi koshi an barni ni kadai a gida sai tsofi na fita waje na zauna shine da zasu wuce yace inzo mu tafi shine na bishi mami.

     Ok mami tace yayin da take saukowa saman gadon don wani lokaci mami a kasa take zama taci abincinta.

    Saida na tsaya na zuba mata ta fara ci tana fadin oya dauki wanan sauran kije kici don nasan bakico komai ba yanzu haka.

    Na dauka tare da fadin na gode mami na fita da ture din a hannu na ina murna zan sha ferfesun kai yau har in bari duk da ina ci sai dai diban tsoro nakanyi wa abinci wanan kuma an bani shine kai tsaye.


    ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅


1️⃣5️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


IDAN NACE NA KUDINE INA NUFIN IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI KO ?

   


Ranan nasha dadi don a dan lungun shiga dakin mami na zauna a kasa na kwashi garabasa na a wurin ina tsotson kanshi ne su yaya mamud suka shigo zasu shiga dakin mahaifiyar su su uku babu jamal a cikin su.

     Kunya ne ya kamani yadda suka sameni ina gwigwiyan kashin kafan saniya ina kuma tsotson ruwan miyan da ya lake a cikin sa don dadi.

   See dis village girl jalal ke fadi dubeki don Allah a kasa kika wani zauna kamar wata kazama can.

  Dan kallona yaya mamud yayi ya kawar da kanshi gefe daya yana fadin wai a ina mami ta samo wanan yarinyar ne ?

   Haka yayi daidai da shigar su dakin mami din inda direct wurin da mami ke zaune a kasa Jafar ya nufa ya zauna a kasa tare da karban cibi a hannun mami din.

   Kallo shi mami tayi kafi ta mayar da kallon ta ga mamud tana fadin me naji kana tambayane ?

   Sai jalal din yace dis your village girl mami kinga yadda tawani zauna a kasa tana cin abinci kamar wani zai daka mata tsawa ta sheka a wurin.    Ina ruwan ka da ita  mami tace tana kawar dakai zuwa kallon Jafar da yakai ruwan miya a bakin shi ya fara taunawa da kyat kamar an sashi ci dole.

     Yanzu haka nasan baka karya ba tun safe maimakon yai magana sai cikin shi ya shafa yana lumshe idanuwan shi a hankali.

   Yaya jalal zainab tana da gaskiyan ta ta fita falo kuma a zageta shiyasa ta labe nan nasan tana ci hankali kwance.

   Waye zai zage ta mami ta fada a hasale ciki  ko in kulla kai tsaye tace your daughters don dazun nan na raba ta da Rufaida a falon .

    Wai kawai ta zauna a kan kujera in kaga yadda Rufaida kewa yarinyar nan abin ba kyau wallahi .

   Shine na zauna da zeey din ina tambayanta take fasin bata san abinda tayi masu ba suka tsane ta ita zagin ne ke ci mata rai dasu ai sosai.

   Wanan Rufaidan badon mahaifinta ba da nake jin nauyin shi a yanzu wallahi akan yarinyar na dana mata tsiya sosai a gidan nan ko ta koma gidan su.

    Mami akan wanan yarunyar har kike fadin haka yarinyar fa ba yar kowa bace balle har ki fadi haka nasan shi, , , , 

    Karbi nan jalal mami ta jefa mai dakuwa da hannun ta tana fadin uwarka ma kaji ance ba yar kuwa bace face dagacin kauye.

    A haka kuma mahaifin ku ya aureni har muka haife ku ka san mai Allah zai mayar da ita gobe ita kanta Rufaida data sani da batai mata hakan ba don Allah yasan goben ta.

  Yaya mamud yace ni ban ma san yarinyar ba shine yanzu nake tambaya ko wacece ita ina dai yawan ganin ta gidan nan all d time idan na shigo.

   Ina zaka sani tunda ba a gida kake zaune ba itace yanzu mai koyawa diyan ka karatu a gida .

   Yace so tasan abu ke nan sosai ma mami ta fada tana budan baki ta karbi abincin da jafar ya debo ya bata.

  Ni dai bana son takurawan da su rufaida ke mata Allah mami yarinyar tana cikin damuwa haka sosai wallahi.

    Ido ya runtse kafun ya bude ya juyo yana fadin you are too talkative now  kin fadi wanan maganan tun farko yake cewa Aisha.

   No mami ta tsawata masu su daina muzanta ta don yarinyar she is beautiful sosai sai dai tsiyar abin yar tallakawace ita.

    Mamud ya fada yana gyara zaman shi oh shi tallaka ba mutum bane ko don kawai tana tallaka sai akace a muzantata.

   Is OK mami ku bar zancen nan don Allah ya fada rai bace yana kai mata cibin abinci a bakin ta ta karba.

   Sai mamud ya kwashe da dariya yace mami ba fa nufina ke nan ba kin sani so iam sorry for dat ta dago tana hararan shi kawai.

    Hummm hummm in dai a kan wanan maganan ne mami zatayi fada da kowa ai a gidan nan na rasa me wanan yarinyar tazowa mami dashi haka.

  Anyway naji suna fadan wai sun asirce mami ne ita da , , , , 

    Jalal getout bana son yawan zuba haka tin dazun nayi warning kan zancen nan kun kama magana kan abu daya haka. 

   Yana gamawa ya mike tsaye zai bar dakin mami tace ina kuma zaka zansa a kawo maku abinci kunci yanzu a gabana.

    But mami , , ,  shiru yayi don hannun data daga alaman yai mata shiru dole ya dawo ya zauna waya ta daga ta kira wani layi tare da bayanin abinda za ai mata.

  Kafin wani lokaci an hada dining din tashi sukayi tana gaba suna biye a bayan ta a falon dai nake sai dai ba a zaune ba ina gutfane raben jikina na saman kujera hankalina yana gun kallon tv dake aiki tun safe a falon gashi ban iya canza chenal din ba, don haka nake kallon dole hakana.

    Zeey kina nan kina kallo mami ta fada saina dago da sauri don jin muryan ta danayi ina fadi cikin fara, a sannu da fitowa mami.

    Namike tsaye tace no koma abinki ki zauna don me baki zauna da kyau ba ta fada kamar bata san abinda ya faru ba tsakanina da Rufaida da rana ba.

    Dan murmushi nayi ta nuna min kujeran tana fadin zauna sama daga yau duk abinda kike son yi a gidan nan kiyi shi kamar kowa kinji abinda na fada ko ?

  Na gyada kai ina kaiwa zaune Nazifa dake fitowa daga kitchen a gaban ta mami ke min fada ta juya zuwa dakin su nasan zata fada masu abinda mami ta fada min ne yanzu.

    Mami basu bar wajen ba sai da magariba ya kawo jiki suka mike don zuwa sallah lokacin har na fita naje waje don yin alwalani.

  A wajen suka sameni sai dai ban samu gaidasu ba suma ba wanda ya kula dani kuma sun ganni din wurin ina alwalan.

    Na dawo na samu mami ta shige dakin ta nan falo na tayar da sallah sai da na idarne Rufaida ta fito tazo ta tsaya a kaina tana fadin.

    Sai kin bar gidan nan munafukar yarinya kawai don nayi maki fada kan hawa kujera dazun shine kika fadawa mami ko ?

   Da sauri na dago kai tare da fadin wani bamuyi wanan zancen da mami bani .

  Rufamin bakin nan naki mai warin tsiya zaki cikani da surutun tsiya to bari kiji tunda nan ba gidan ubanki bane sai kin barshi walla, , , ,

    Ke menene haka me tayi maki keki zaginta haka kawai don cin zalin zaki saka yarinyar mutane da zaki haka.

   Yaya mamud ne tsaye daga bayan mu yake fada da Rufaida ta dan tabe baki tana fadin wallahi yaya yariny sai yace wanan ba daidai bane ya juya ya nufi dakin mami rai bace.

    Yana shiga yake fadin mami gaskiyan Aisha yaran nan sun matsawa yarinyar nan haka ashe yanzu na same su a falo rufaida na shirin dukan ta badan Allah ya kawoni ba data kai ga dukan nata ma kila.

   Innalillahi me yaran nan suke nufi newai kan yarunyar nan a to mami indai zamanta nan tare dasu zai zama matsala gara dai ki sallameta yace tare da mika mata ledan maganin daya sayo mata.

   Ranan ma a dakin mami na jena kwanta a kasa kamar yadda na kwana a jiya a takure don gani nake idan nayi dogon motsi zan dameta a dakin ta.

   Washe gari tunda na tashi nake jin kamar zazzabi a jikina hakana na daure nayi duk wani aikin da zanwa mami nayi shi cikin daurewa.

   Inda Allah ya taimakeni mami ta fita tun goma na safe na samu na shige dakinta na kwanta ba tare da nasha magani ba.

   Har lokacin da mami ta dawo daga unguwa data fita ta zauna falo bataji motsina ba kota ganni da ido sai tambayan mutane take suna fadin suma tun safe basu ga giccina ba.

  Aka kama fadin ina na shiga hankalin mami ya tashi ranta kuma ya baci dani sosai kan hakan don dai tasan ban san kowa ba a garin.

   Saida mami ta shigo dakine ta ganni a kwance na dunkule cikin hijjabina ina rawan sanyi.

  Ja tayi ta tsaya da mamaki tana fadin ke zeey lafiya ko kin shige daki kin kwanta kin tayarwa mutane da hankali.

  Jin muryan mami sama sama a kaina yasani bude ido da kyar na buda baki jikina na rawa zazzabi mai karfi nake fadin massarara nake ji mami tunda na tashi da safe.

    Jin haka yasa ta karaso inda nake kwance tana fadin saiki shige daki ba tare da kin fadawa kowa ba ki rufe kanki a ciki don rashin wayau ko me ?

   Da kin fada da an samu wanda ya baki magani ko a kaiki asibiti kinzo kin shige hijjab kina rawan sanyi haka kinki jan bargo saman gado ki rufe jikin ki dashi.

   Tana wanan fadan takai hannun ta a jikina tana tabawa taji zafi radau da sauri naga ta juya ta fita dakin.

  Sai gasu da jamal da Jafar sun shigo dakin da saurin su jamal ne ya kai hannun shi saman goshina yaji zafin da jikina yayi da sauri ya cire hannun shi yana fadin mami dis is serious fa jikin yayi zafi sosai.

    A hankali yaya jafar ya tako zuwa inda nake kwance saman rough shima ya taba jikin nawa wani irin shock ne ya ratsa jikina lokaci guda duk da yanayin zazzabin da nake ciki haka bai hanajin wani yanayi da ban san na meye ba lokacin.

   Idona na runtse daga inda nake kwance nunfashina har yana sarkewa yayin dashi har lokacin yana duke a kaina ya dago yana fadin les take her to the hospital dis is serious mom.

   Mamice ta dagani daga kwancen da nake sai na kasa tsayi tsaye da kyau jamal kamata da kyau a kaita wurin mota mami tace.

    No barta a kira wasu daga cikin yaran nan su taimaka su riketa zuwa motan ya fada yana juyawa ya fita daga dakin.

   Fita yayi ya tsaya yana fadin matar dayaga tana falo ta kira masa sisters din shi dakin su don baisan dakin da suke bama.

    Sai gasu sun zo suka same shi tsaye inda kowa sai mamakin kiranda yake masu sukeyi don da farko da matar tace shine basu yarda ba saida suka fito suka same shi a tsaye yana jiran su din.

   Bai tsaya kallon su ba ganin sun fito ya juya yana fadin help dis girl please kallon juna sukayi don basu gane wace yarinya yake magana a kanta ba lokacin.

    Ganin ya nufi dakin mami suka bi bayan shi sai ga mami ta fito tana ganin su tare dashi tace yawa don Allah wata ta taimakawa zainab zuwa wurin mota mu kaita asibiti.

    Jin an ambaci sunana yasa Nazira ta fara ja da baya Rufaida ko ko motsi batayi ba a inda take sai salma ne tace mami bata da lafiyane dama.

   Wallahi salma ki san yarinyar nan bata da hankali bata jin dadin jikinta ta shige daki ta kulle kanta a ciki haka.

   Salma ta matso tana dafani tare da fadin sannu zainab tana kokarin tayar dani zaune.

    Haka ta dan rikeni har zuwa wurin mota data ganshi tsaye shida jamal an bude kofar motar.

   Mamine tacewa salma shiga salma muje tare don Allah da sauri tace to mami ko mami ta dauka driver ne zai jamu sai ji tayi yace jamal shiga muje tare.

   Turkish hospital ya nufa damu da kwantace har ya gane wurin munyi sa, a akwai likitoci bamu dade ba muka shiga bayan yankar katin da jamal yayi baisan sunan baba na ba dole sunan mahaifin su yasa a katin don sauri.

  Tare da mami muka shiga ganin likitan ya dubani bayan yan tambayoyin da nake amsawa da kyat gareshi.

  Allura da maganguna aka ban sunso wai su dan kwantar dani mami tace aimin dai allura mu koma gida washe gari sai indawo in karbi sauran allura.

    Haka muka juyo muka dawo gida zuwa lokacin har na fara dan jin saukin jikina haka muka shigo gidan a falo muka samu wa yanda suke gidan a lokacin.

  Da ganin su akwai maganan da sukeyi a lokacin don yadda suke gaida mami da dawowa ba wanda ya tambayi yaya jikina daga cikin su.

   Dakin mami ta kaini ina jin anty salma na fadin ku baku iya gaida mara lafiya bane ?

    Ta fada tana shigewa dakin ta suka bita da fadin Amebo Olopopo suna hararan inda tabi zuwa dakin Nazifa tace waya sani.

  Ko taje ta daukowa mutane ciki ne a gida Rufaida tace ko cikin wa yan nan katan na waje wani ya taushe yar iska yafi karfin ta ba.

   No ku daina fadin haka don Allah Ruby dataki bin iyayyenta su tafi ta fada  tace kun san fa wanan zargin abu mai girma idan kun zargeta da aikata zina alhalin batayi ba Allah na iya jarabtan ku kan hakan.

    Kawai dai mu barta da samun wuri don samun wuri kan yarinyar nan ta same shi har ta batun zarta mu a yanzu.

  Ku diba yadda guy din na ya fito a gigice dazun yana neman wai wanda zai taimaka ya kaita wurin mota.

    Kyale dan rainin wayon banza kawai yana wani abu kamar bakin baturen dake jin warin mutane nina rasa me wanan yarinyar tayi haka gaba dayan su suke ji da ita a gidan nan haka Nazifa ta fada tana jan tsuki a karshe.

    Ya kamata dai mu san mafita don wallahi garin kallon wuta kada kwado ya fada ciki muna nan zaune tazo ta samemu har tafimu kima a wurin su .

  To yanzu meye abinyi kawai Rufaida ta fada a cikin damuwa sai Ruby tace a abinyi shine mu san mafita .

  Don wata kila ladabin ta garesu ne yake ja mata kauna a wurin su kin san su don son girma kamar gyabo ai.

   Kai ba wanan bane gaskiya Rufaida tace ni kawai nasan shegiya asiri taje gida aka kara bankadawa mami dasu gaba dayan su.

    Ki duba ko jalal da jamal da muke zama tare duk a yanzu sun bari wallahi ke ni na tsani wanan yarinyar gaba daya sai na halakata ko inyi sanadin barinta gidan barni da yar iska kawai nasan abinda zan mata ai.

  

    Daga dakin shi inda yake zaune yake kallon su shida jamal da shi kanshi baisan gidan akwai cctv ba sai yau ya girgiza kai tare da fadin wasu irin yara mami ta aje haka a gida.

   Yaran nan ko mami ba zasu barta ba idan sun samu wuri ya fada yana mikewa zai shige daki sai kuma ya juyo yana fadin .

    Kada inji zancen tv din nan a bakin wani a gidan nan ko mami kafadawa dashi zamu samu matsala sosai dakai a rayuwan mu.

  Na dade ina zargin yara nan ba zaman banza sukeyi tare da mami ba tunda naji suna gidan nan zaune yanzu.

   Hannu jamal ya daga duka biyu yana fadin believe me yaya kowa ba zan fadawa wana  magana ba ko jalal ne yace is better for you don ban son yawan magana.

   Nikan barci nayi sosai a dakin mami na samu gadon mami na haye ka laushi kamshi da sanyi na tashi yana shiga min hanci a hankali.

    Duk da halin rashi lafiyan da nake ciki bai hanani jin dadin kamahin dake shiga min hanci ba lokacin.

    Sai goma da rabi na dare na falka koshi mami ce da Aisha a dakin suke magana yasani bude idona  sannu zee mami ta fada tana kallona tare da tambayana jikina.

  Me zakici yanzu Aisha ta tambaya tana kishingide saman gadon mamanta da waya a hannunta tana kallo.

   Mami ta kura mi  ido tana so jin amsa da za bayar a hankali hannna ina share wayen dake kokarin zubo min a idona.

   Tambayan ki ake ba kuka akace kiwa mutane ba a na tun safe nasa bakici komai ba a cikin ki .

   Na amsa cikin karfin hali da fadin tea zan sha ina kokarin mikewa tsaye ina kuma zaki Aisha ta fada zanje inyi fitsarine na bata amsa.

    Ina koarin nufar kofan fita daga dakin don ba daman in kewaya mami tana dakin ta don haka nake kokatin fita ba tare da nasan inda zan nufa ba a lokacin.

   Sosai mami da yarta suka kula dani don sun nuna damuwan su a kaina sai anty salma da itama ba laifi don tana zuwa a kai akai tana gaidani da jikin.

   Har naji sauki na fara fitowa falon don in bawa mami dakin da ko yaushe a dan kwana biyun nan ina kwance.

  Ranan dana fara fitowa falon ne naga canji sosai wurin yan matan mami wanda hakan ya bani mamaki don fuska sosai suka sakarmin harda zolaya wai an taya naki sallamawa.

  Ni dai nayi murmushi tunda ba saba haka nayi dasu ba dama duk da yadda nake hakana mike na yi aikin da zanyi a ranan don sai naga aikin da akeyi kamar baya fita da kyau.

  Aiko mami na dawowa ta hauni da fada don ta gane nice nayi aikin cewa kawai nayi naji sauki mami.

    Tadaiyi min fada ta fara cire kayan jikinta na fita dakin don bata wuri ta shirya a tsanake kamar yadda muka sabayi.

   Sai data fito falo na koma dakin na gyara tare da nade kayan data cire a jikinta na wanko har bathroom din tas.

   Tun ina jiran inji ance gobe ko jibi zamu tafi sai naji shiru saidai kawai ranan da muka cika sati da zuwa ranan da dare mami ke fadin su Rufaida su shirya zasu koma kaduna do  hutun su ya kare .

   Ina gurin jin haka yasa na kallo mami don banji tayi magana ba a ciki sai naji mami na fadin ina sane dake zainab ban manta da karatun ki ba ai.

   Wata kila nan karatun naki zai dawo yanzu do zaman mu zaifi yawa yanzu a nan sai dai na duba naga abinda ya dace mami ta fada.

  Basuji dadin yadda mami ta tsara ba don ba karamin dadi duke ji ga wanan zaman namu ba don ko yaushe suna fita shoping da yawo sun samu dakewa sosai don mami bata zana gida sai yamma take dawowa gida.

   Dole ba don sun so ba suka fara shirin komawa kaduna salmace kawai bata nuna damuwanta a fili akan hakan ba wucewab sune yasa mami bani daki na kaina inda zan zauna kamar yadda nake da dakina a kaduna gidan ta.

   Haka ba karamin dadi yai min ba sosai a raina don dama a takure nake saboda zama da mami da nakeyi daki daya.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post