Abu Cikin Duhu Page 16 - 30

Abu Cikin Duhu Page 16 - 30

 🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣6️⃣  ZAINAB IDRIS MAKAWAYAU DA GOBE NA ALLAH NE YAN UWA MU RIKA SHUKA ALHERI DON WATA RANA A FADE MU KO BAMA KUSA, UBANGIJI ALLAH KA KARA MUNA IMANI DA DOGARO DA KAI YA ALLAH, , , 


IDAN NACE KI BIYA INA NUFIN NA KUDINE YAR UWA KI GUJI SHIGA HAKKIN DABA NAKI BA DON ALLAH ALLAH YASA MU DACE .

   DARI UKU NE KACAL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI.


Zance tafiyan su rufaida baimun dadi ba don gidan ya kara komawa silent yanzu da suka tafi ashe dan mutum ko yaya kake dashi yana da rana a gareka.

    Yau na kara fahintar hakan wanda dama nasan da hakan tun barina gidan da har nakan ji kewan yan gidan mu ga baki daya har Asabe da lantana.

  Sai gashi dan sabon da nayi da zama da ukuban su Rufaidama yanzu ina kewan hakan gareni.

   Sai ya kasance in zauna ni kadai ina faman tunane a guri daya idan kowa ya fita zuwa nasa tsabgan sai in rage dagani sai gwarawan yan aikin nan dake gidan.  Gashi ni ban saba dasu ba don ko yaushe a cikin yare suke su yau ma kamar kullun bayan fitan mami da Aisha data wuce school na gama gyaran dakin mami na koma dakina nayi wanka.

    Na shirya a cikin wani bakin dogon riga da Anty Aisha ta ban zuwan mu Abuja don ganina da yan kayana kala hudu dana dauko da zamuzo kullun.

    Dan kalin rigan na daura a kaina mai kawai na shafa a fuskana don ni ba gwanan kwaliya bace dama haka.

    Duk da hakan fuskana ya dan fito fayau falo na dawo na zauna ina karyawa ina kallon tv daya zama min abokin hira yanzu.

   Cibi biyu na kai ga bakina na orth din da nake sha muryan Nuriya matar yaya mamud ya ziyarci kunnena don ni nikan manta da itama a gidan tunda ita bata shiga mutane kuma bata barin yayan ta suna mamuwar kowa a gidan.

    Fadi take ke zeey ki zo ki gyara min part dina yayi datti da yawa yau ina son a gyara min shi don Abbani yai magana kan hakan da cewa yaya mamud kamar yadda take kiran da dashi.

    Yau kan na turza don bansan sanda bakina ya furta anty Nuriya yanzu nake karyawa idan na gama zanzo na bata amsa.

   Ke yaushe har raini ya shiga tsakanin ni dake haka ta fada niko a raina nace wata sabuwa kuma waini mena tarewa mutane haka kowa yake jin haushina dan abu kadan zai zama min matsala babba ga kowa.

     Maza ki tashi kije kiyi abindana sakaki kafin na bata maki rai ta fada a hasale tana mai tsureni da idon warning gareni.

   Kokarin aje cup din dake hannuna nake naji muryan Jamal na fadin ke dauki cup din ki ki karasa karyawan ki kafun ya juya wurinta yana fadin.

   Baki da tausayi wallahi yarinyar nan tun safe take tsaye sai yanzu ta samu kanta take karyawa zakice ta bar karyawa tazo maki aiki.

   Wani juyawa tayi tana masa wani kallo tare da fadin kai kuma fa dan rainin wayau da zakazo kaja min raini a wurin yar aiki haka.

   Aiki na sakata a part din mu kuma dole ta tashi ta tafi yanzu don yanzu nake bukatan ai min shi.

  Bazata ba sai ta gama karyawa ya kara bata amsa yana kallona tare da fadin koma ki zauna nace ki karya idan kin gama sai ki tafi.

  Ba abun mamaki bane don ka fadi haka jamal tunda kaganta haka kana da mugun nufi a kanta kamar yadda kuka saba yi a turai ai.

   Sheri zaki min ya fada a hasale yana nufota ni kan hannu na dora a kai ina shirin yin ihu don yadda ya nufota sai Allah zai gyara yau a tsakanin su.

   No no no jamal don Allah please kada ka tabata be a man kada ka karasa wurinta please.

    Nan dai hayaniya ya kaure a tsakanin su ta fadi ya fadi karshe dai ta juya tana fadin ke kuma karamar yar iska kada kizo ki min abindana saki kiga abinda zan maki yau gidan nan.

   Ba zatazo ba din kiyi duk abinda kikai niya a kanta jalal shima ya fada a hasale ta juyo tana fadin sai ku gayawa wanda baisan abinda kukeyi da ita ba a gidan nan.

    Innalillahi ai bansan lokacun dana dora hannu a kai na fara rusa kuka ba karyawan da banyi ba ranan ke nan.

   Don sukan tana wucewa suka tafi suna fadin yau zasu gamu a gidan nan dole sai ta fada abinda take nufi ko su casa ta son ransu nan suka barni tsaye ina kukan takaicin zargin da maman su Amir da Amirah tayi min kan tagwayen mami din.

     Banda yadda zanyi duk da sunce kada in tafi haka na aje abin karyawa na na nufi part din anty nuriya din da zuman mata aikin data sani.

   Gaskiyane part din kan yayi datti kamar ba mace a cikin sa da take rayuwa ko namiji yabar gutin shi haka za a iya kiranshi da kazamin namiji.

  Sai kaga mace fes a waje amma kaje muhalinta sai ka raina mata wayau kan rashin gyaran wurin zaman ta.

   Kayan dake saman kushin na duka na fara nadewa hankalina ya dauku ga abinda nakeyi kawai ba tsamani naji saukan mari a fuskana lokaci guda.

   Na dago dan gani waye yai min wanan aikin na kara jin wani a tsakiyan fuskana tana fadin gobe in kara saki aiki wani dan iska a gidan nan yace kada kiyi.

    Ke har kin isa me kika dauki kanki banda matsiyaciya kaskantatar yar aiki kawai kina nufin ni kyauki da wani halin ki can zai rudeni ne matsiyaciya mai zubin karuwai kawai.

    An walla, , , ,  kofan da aka bankadone yasa ta kasa karasa maganan da take son furta min ta juya tana kallon wanda ke tsaye a kofan nasu.

 Ni dai ina tsaye har lokacin zafin marin bai gama sauka min ba sai wani dishi dishi nake gani idan nayi yunkurin bude idanuna lokaci guda.

   Muryan Jalal ne yake fadin idan kika kara dukan ta yau sai kin raina kanki gidan nan wallahi kinji na fada maki.

    Jalal ya juya gareni yana fadin ke kuma fito part din nan tun kan ranki ya kai ga baci yayin da Nuriya ke kokari daukan waya don kiran mijin ta tana durawa jalal din zagi ta uwa ta uba.

   Bayan mun fita part din ne ta kira mijin ta fada mai karya da gaskiya shi kuma ya hau karfe uku duk suna gida gaba dayan su don mami tace su hadu a gida.

     Yayin da har lokacin ina daki tundana shige ban fito ba ga fuskana gefen idanuna ya hau ya rufe sosai har bana gani dashi.

   Sai faman tunane nake a raina duk kokarina wajen kaskantar da kaina a garesu don gujewa faruwan irin haka .

    Wanda mami da yaranta a kullun suke kokarin jana a jikin su suga dai na sake a cikin su wanda ni na kasa hakan don kada in shaga irin wanan matsalan a cikin su.

  Ina nan a kwancen da nake ina faman tunane muryan Anty Aisha ya daki kunnena tana fadin zainab mami na kiranki a falo.

    Na dago dan mata sannu da dawowa tana ganin fuskana tace ke meye haka fuskanki ya sauya lokaci daya ?

 Cikin dakewa da karfin hali nake fadin sannu da dawowa Anty Aisha yyawa me ya sameki haka ta kara fada.

   Ba komai anty na fada ina kokarin tashi daga saman gadon ta juya ta fita daga dakin.

   Ina tafe na sa gefen gyalen dake kaina na dafe idon dashi abu ga farin mutum lokaci daya fuskan nawa gaba daya ya canza kala ga alamun hannun Nuriya radau a fuskana.

    Gaba dayan su sun zuba min idanuwan su a kaina har na karaso inda suke zaune na kai kasa na fara gaida mami data kura min ido kamar ta suma da mamaki.

  Kafin in dan dago ina kare fuskana ina gaida yayan nata zeey meye wanan ya bata maki fuska haka mami ta fada tana kallona don jin abinda zan fada.

    Kowa falin ni yake kallo yayin da mami ta kara maimaita maganan ta gareni kafin in magana Nuriya tace nice na mareta.

    Har mijin ta saida ya juya yana kallon ta don abinda ta fada lokaci guda cikin rashin damuwan da hakan.

    Akan me kika duketa haka Nuriya mami take tambayan ta cikin mamaki har lokacin.

    Don me zan sakata aiki mami take zuwa lokacin dana umurceta tazo don kawai wanan dan rainin wayau yace kada taje tana nuna jamal a hasale.

   Shi dagowa yayi don yin magana sai lokacin Jafar ya dakatar dashi don tun zuwana kanshi na kasa yana dakilan wayan shi cikin ko in kula da wanda ke wurin gaba dayasu.

    Jamal me zaka fada tunda ta riga data fadi itace tai mata hakan da bakinta yanzu ta kuma fadi dalilin yin hakan gareta.

    Sai akace a duketa haka ko boyace na sayo ai ba za ai mata wanan dukan ba haka balle ba boya bace karbo ta nayi hannun iyayyen ta don kawai ta taimakawa rayuwana.

   Ban kawo don wani aiki ko aikin wani a gudan nan sai nawa bukatan ni kadai da take min kuma tana da kokatin wurun aiwatar min da komai tun kan na fada mata abinda zatayi min.

  Haba wanan dukan haka ai abin yayi muni komai tayi maki ai zaki bari in dawo ki fada min sai nayi mata fadan hakan .

   Koni dana karbota wurin iyayyen ta aiba zan taba mata wanan duka haka ba don itama mutum ce kamar kowa a gidan nan.

  Ok mami ke nan dai yanzu na fahinci da sa bakin ki yaran nan sukai min rashi mutunci ke nan wanan banzan yarinyar mara mutunci da asali ta fini yanzu a gidan nan.

    Nuriya mind your language bakin ki yasan abinda yake fada bayan kiyiwa yarinyar nan irin haka kuma zaki kirani ki fada min karya don kawai ki hadani fada da yan uwana.

    Dama nasan haka zai kasance ai don wanan yarinyar ba karya su Rufaida ke fada ba ta asirce kowa a cikin ku har mami din gaba dayan ku tasa an maku asiri a kanta.

   Enough enough Nuriya bakin ki yasan abin fada a nan kada ki kawo muna wanan shirmen naku ba banza yaya mamud ya kara fada a hasale.

   Tashi tayi tana fadin aida rama mata kayi zaifi da wanan hasalan da kakeyi don kawai na mari wanan .

  Mami ne ta daka masu tsawa tana fadin ya isa haka ki dawo ki zauna idan ki gama fadin abinda ke ranki.

    Kamar ba zata zauna di ba kome ta tuna sai ta kai zaune din tana kada kafa mami ta sauke ajiyan zuciya ta fara magana.

    Da farko ke Nuriya a kanki zan fara don ba zan tsaya kina fada min magana cikin rashin mutunci a gaban diyana ba haka.

   Don dan kuka shike jawa uwar shi jifa, sai dai  kinci albarkacin darajan abu biyu da kike ci  gareni har kullun a wurina.

  Shine  auren dana da kuma kasancewar ki uwar jikokina a yanzu wanan damar kike ci har kullun a wurina don ba zan so saka matar dana a gaba idan ba haka ba ke kinsan wani abin ko ance kiyi min shi ba zakiyi shi ba duk da kudin da kike takama iyayyen 

   Sai yaya mamud ya dukar da kanshi don ya gane me mami take nufi da maganan ta saboda halin Nuriya a ku)un magana ya taso itace bata da gaskiya.

   Mami taci gaba da fadin saidai zanso ki gane cewa ba zan lamunci aibanta mi diya ba ko zargi su a kan zina.

    Mami ni kar,a laka min abinda ban fada ba fa a nan don kawai ana jin zafina kowa ya taso sai yace banyi daidai ba .

   Don hakane nake nisantar kowa a gidan nan hakan baiyi ba har sai wani ya takaleni kuma inyi magana ace banyi daidai ba.

   Yanzun wanan mara galihun tafini daraja da kima a wurin ku ake nufi tunda itace mai gaskiya ke nan don kawai taimin ba daidai ba na hukuntata.

   Who are Nuriya who are you by the way har kina wani fadin tayi maki laifi kin hukuntata akanahi ke kika dauketa aiki a gidan nan ko wurin ki take.

   Ke ba zaki iya yin aiki ba ki zauna da masu aiki kuma kin hana hakan saboda bakin kishin dake damun ki.

    Mikewa tayi tana fadin na hana ka dauki yar aiki mamud don ban so kai din ban yarda da kaiba da har zan dauko wata yar aikican in aje wurina.

   Daga yau na hana kowa saka wanan yarinyar aiki ko taba lafiyan jikinta wallahi wallahi ko yaya nake da mutum a gidan nan ranan zai hadu da fushina.

   Wanan yazama na farko na karshe a gidan nan da wani zai kara taba lafiyan wani zainab yace kamar kowan ku nan dan haka a bani guri ban son wani magana kuma daga yau.

  Tana fadin haka ta mike zuwa dakin ta a fusace yayin da nake durkushe a gefe kujera tafiyan mami Nuriya ta mike tana fadin wallahi mu zuba da kowa a gidan nan kan wanan yar iskan kowa ya tabani tabashi zanyi.

    Binta da kallo sukayi kafin su dawo da kallon su gareni inda nake rakube ina hawaye don tashin hankali dana gani ranan.

    Da hannu ya nuna min hanya na mike simi simi na basu wuri yaya mamud ne ya kawar da shirun da fadin.

   Ni Nuriya zata watsawa kasa a ido haka kwata kwata banji dadin zaman mu da ita kullun a cikin fitina muke.

   Yau ma nasan haushi fadan da nayi mata na gyaran wuri ne ta sauke akan yar mutane haka.

   Bai bari dan uwan ya gama zancen shi ba ya mike zuwa dakin mahaifiyar su data shige ranta a bace ya sameta dakin.

  Shiko yaya mamud yaci gaba da fada da matar shi ranshi a bace yake fadin.

    Ya mike yana fadin nasan maganin yar iska ai bazata zan mata a gidan nan sai ta gane bata da wayau.

   Saidaya shige jalal ke fadin kamar da gaske din zai iya hakan yanzu kila hakkuri zaije ya bata.

   Suma mikewa sukayi zuwa dakin mahaifiyar tasu suka samesu a nan suna wani hira da dan lelen nata a gurin.

     Karfe biyar na bar dakina zuwa na mami don gyarawa ita kadai na samu a dakin da sallama na shigo dakin na duka har kasa ina gaida ita kafin in dago don fara aikin dakin.

   Kinsha maganin dana aika akai maki dazun take tambayana nasha mami na fada ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali.

   Kamar zata sake magana sai kuma tayi shiru taci gaba da duban takardan dake hannun ta ko ina na dakin saidana gyara kafin in fito dakin kusa magariba yayi nan na samu matar da aka dauka don shara tazo ta fara aikin ta .

  Don faruwan avi  mami tasa a kawo mata yar aiki wanan mai sharan bahaushiyace ita don ina gaida ita take amsawa naji hausanta na gane ita din bahauace ba kamar matan nan biyu gwarawa masu girki bane.

  Tun ranan shakuwa ya shiga tsakanin mu da matar da ake kira da hannatu yar ktsinawa irin matan nan ne da suka dade da fitowa bariki don har sigari take sha a boye.

   Nima dai rabon in gan tane a cikinyanayin yasa na rutsa da ita can bayan daki ta labe tana shan abinta na juya da sauri zan koma naji tana fadin a cikin kokarin kashe tabar  da sauri yar hjy kamar yadda take kirana dashi.

    Ina nan ina wanan jarabar tsiyar da muka sawa kanmu ina dai ba zaki fadawa kowa ba halin da kika sameni wanan zancen.

     Da sauri na girgiza kai tare da fadin indai nice babu maijin wanan a abakina insha  Allahu ina kokatin wucewa don natsani warin taba a rayuwana.

   Duk dan dakata min inzo har lokaci bata yarda dani don ta fahinci jikina yana rawa a lokacin.

   Ina kallo ta ballo goro daga haban zanin ta tura baki tana taunawa ta kakabe zanin inda ta zauna a kasa tana fadin wanan abin ya zama muna jaraba a rayuwa.

  Kinsan a zamani  mu idan budurwa takai budurwa har bata shan sigari to bata cika wayayyan mace ba ke nan.

   Tun wanan lokacin mula koyi wanan cacan kashi  kudin don ko nairan ka ta karshe ke nan sai ka fitar kaya zakaji dadi.

    Ni dai a kage nake na bar wurin nake fadin dama ban ganki bane a cikin gida sai nayi tunanen ko kina nan shine na biyo ki.

   Yo ai ina nan kedai jarabarce ta motso min shine nazo indan rage zafi kai.

  A tare muka jera zuwa cikin gidan idon ta mirsisi kamar bata sha komai ba taci gaba da sha,aninta

    Cikin sati daya kawai mun saba da hanne wace na lakawa mama hanne nake kiranta da hakan don girmamawa .

   Zama da mama hanne yasani cikin farin ciki da walwala sosai don zata zauna tayi hira dani kamar sa, anta nake gun ban iya bata amsa har yakai yazu ina bata zamu zauna tana ban labari ina kwasan dariya.

   Da sunan kwana hudu sai gashi mun share wata a abuja lokacin ne mami ta fara shirin ziyaran kaduna.

    Wanda gaba dayan mune zamu tafi gidan a yadda naji suna fada mahaifiyar mami ce bata da lafiya shine za a tafi gaida ita.

    Shiri sosai mami keyi don zuwa gida nikan nafi kowa murnan hakan kamar ance damun isa zan tafi ancau ne ranan.

  Ni kan na dauka yaya Jafar ya koma inda ya fito ne ashe wai tafiya sukayi tare da su jamal sai kwatsam gasu sun dawo ana saura kwana daya mu tafi kaduna.

    Mama hanne kan tunda tayi arba dashi tasha jinin jikin ta a zaton ta wai yanayin sa yai kama dana yasanda tunma dataga security din shi ta kara tsurewa da al,amadin shi.

    Take tambayana nake fada mata dan mami ne amma ni ban san aiki da yakeyi ba,  ta sake fadan mutum.haka ba yar dariyan nan ko fara,a a fuskanshi.

   Dariya sosai nayi har ina dukawa a inda nake zaune sai kamshin turaren shi mukaji lokaci guda.

    Key din shi yake miko min ba tare da yayi magana ba, amma na gane me yake nufi dakin shi yake so a gyara mai ke nan.

     Yana miko min ya juya ya futa a cikin wani irin tako na mazan zamani da suka suka san ta kan duniya sosai yake tafiyan.

   Ban tsaya jiran komai ba na mike don cika umurni duk da mami ta hana inyiwa kowa wani aiki ita da kanta takan umurceni da inje in gyara mai dakin nasa.

  Tura kofan nayi na shiga dakin da sallama duk da nasan ba kowa a daKin hakan bai hanani inyi sallama ba.

   Idonane ya fara arba da  wani kwalba dake aje saman table din dakin nasa ga abin cikin sa an zuba a kofi ansha an aje rabi.

   Da mamaki nake kallon abin don ban taba ganin kwalban abin sha irin sa ba nidai na fara kawar da takardun dana gani a saman wani table naji an turo kofa da karfi an shigo dakin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣7️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


YA ALLAH KA GAFARATA MUNA ZUNUBBAN KABA MU IKON AIKATA ALHERI A RAYUWAN MU DUNIYA DA LAHIRA AMIN.


DO MIN SAMUN LITTAFIN NAN CIKKAKE ZAKI IYA TURA DARI UKU TA WANAN ACC 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN NA DARI UKU KACAL NAGODE UBANGIJI YA HORE YA BADA IKON BIYA ALLAHUMA AMIN ALLAH, , , , Idona a kan abin ina dan juyawa a cikin kofi naji wanan tsawan daya daka min sai da hanjin cikina ya kada don tsoro lokaci guda.

    Allah ya gyara ban sale cup din ba ya shigo ya karbi abinsa yana mai bina da wani kallo mai kamar na tsana.

   Wayace ki taba min wanan ya fada rai bace kamar da gangan na taba mashi abin bashi ya turoni dakin in gyara ba.

   Dan marairaicewa nayi ya karbi abin shi zuwa daki sai gashi ya fito da cup din ban san inda ya juye abin ba.

    Fita yayi daga dakin ba tare da yayi min magana ba hakan ya bani daman yin aikin a tsanake.

     A gurguje na gyara komai duk da hakan dakin ya gyaru da kyau na kulle masa na fito na kai key din dakin mami.

   Nikan don doki har na shirya kayana tafiya kawai nake jira washe gari na zata tun safe zamu wuce sai naga sabanin hakan.

    Saida yamma bayan la,asar muka bargidan zuwa filin jirgin ashe da jirgi zamuyi tafiyan kuma.

    Karfe shidda na yamma duk muna gida a lokacin har na bude dakin mami ina gyara don tun tafiyan ta dakin a rufe yake.

    Sai yau da muka dawone ta miko min key na bude duk da a gyare muka barshi da zamu tafi hakan bai hana yadan yi kuraba.

   Na gyara har bathroom na fito zuwa dakina shima na gyaro na shiga wanka dongon riga silk mai adon kamfala ne na dauko daga cikin kayab da anty Aisha ta bani na saka.

    Saida nayi sallah har isha,i na fito falon don yunwa da nake ji lokacin in samu abinda zanci a cikina.

  Suma mutanen gidan gaba daya a falo na same su saman dining suna cin abinci mami da yaranta maza su hudu sai  yan matan mami din gaba dayan su har anty Aisha.

    Simi simi na fito na zo diban abincin wasun su suka kuro min ido hannuna rawa na dibi abincin ina jin mami tana waya tana fadin muna kaduna yanzun haka.

  Insha Allahu da safe zamu shigo Igabin naji tana fadi haka yasa na san zasuyi tafiya washe gari saidai ban san ko dani bane.

    Diban abincin na juya zan wuce naji muryan yaya Jafar na fadin ke saida hanjin cikina ya kada don jin muryan shi saidai ban tabbatar ba ko dani yake don kaina na duke na basu baya.

   Na kara takawa gabana na mumunan faduwa da ban san dalilin haka ba duk lokacin danaji muryan yaya jafar din duk da ina tsron kowa a gidan saidai nashi yafi yawa a zuciyana.

  Ko dan ganin kowa ma yana shakarshi ne a gidan don tsare gida irin nasa .

   Haka naci gaba da takawa cikin karfin halin zan tafi dakina inda na saba zama inci abinci hankali kwance zuciyana cike da addua nake tafiya.

    Ya sake fadin come and join us ina zaki da abinci ga kowa nan a zaune hakan yasa nasan lalai dani yake magana na juyo a hankali.

   Yana rike da cibin abinci da yake ci a hannun shi ya rike baikai a baki ba gabana na faduwa yace.

   Daga yau a nan zaki rika cin abinci tare da kowa kinji abindana fada maki yana nuna min kujera da hannun shi .

  Kai na gyada mai, tare da nufar gurin kujeran dake saiti da inda yake zaune babu kowa saman kujeran na zauna.

   Idanuwan yan matan gidan duk a kaina bama su kadai ba har mami dake waya a lokacin idonta yana kaina.

  Ko ban daga kaiba nasan akwai idon dake kallona a lokacin don jikina ya bani hakan ba ido daya ba ba biyu ba kodana dago kai duk idanuwan su na a kaina suna kai cibin abinci a bakin su.

   Tundana zauna ya maida hankali gun abincin dake gaban shi hankali kwance yake kai cibi a bakin shi a hankali .

   Daga mami har ya  matan dama su jamal suka dago ido a sukwane suna kallon shi shiko ko a jikin shi.

   Sai juya cibin dake hannuna nakeyi na kasa sakin jiki inci abincin yadda ya kamata a wurin.

  Yadda kika san guba haka nake hadiyan abincin ba wai don baya da dadi ba don hadine na musanman akayi don zuwan su yau din su mama kande suka girka abincin mai rai da lafiya.

   Mikewa yayi tsam mami tace har ka gama cin abincin ke nan ko rabin plate fa baka ci ba ba tare daya juyo ba yace mami iam ok zanje na kwantane.

   Allah tashe mu lafiya mami tace yace amin yana tafiya sai jalal yace but yaya security dinka za a fada masu sutafi ke nan tunda ka shige ko ?

   Na sallamesu tunda muka fito massalaci dazun idan sun gama zasu tafi ya bashi amsa yana tafiya da dan sauri kamar mai uzuri.

   Mami ma bata dade ba wurin ta mike tabar falon sai mazan da suma suka mike lokaci daya falin ya rage mu kaida a ciki.

  Duk lokacin danayi yunkurin dago ido sai in samu ana aika min da wani irin mugun kallo da tsana dan dama salma da Aisha su ba kallon tsana bane saidai kallone mai kama dana mamaki lokacin.

    Amma dai yarinyar nan kina da sa, a yau kece yaya hero ke ba umurnin zama  a saman table kici abinci tare da kowa a gidan nan.

   Ke ko ba dole ba tunda ta iya makirci kamar ta mutu ta mairaraice ita gata Allah ba dole ta bashi tausayi ba Nazira ta fada

    To kodai kin zauna a cikin mu ba a dai taba canza maki suna daga zainab yar aikin mami zuwa diyar gidan nan kamar kowa Rufaida a fada .

    A, a,  za a yi kiranta ki da yar gida mana duba yarda yan kwanakin nan gaba daya tayi fresh da ita haka duk sai suka kalloni lokaci daya.

    Nagaji da cin fuska na mike don barin wurin, dama abincin ya fita min rai lokaci daya na dauki plate din zuwa kitchen.

   Ina ruwan ba saban ba yau har wanan ce zata bar abinci haka bataci don samun wuri.

   Ban kara fitowa dakin ba don na gamawa mami komai itama nasan ta gaji ta kwanta tunda akwai tafiya garesu washegari.

   Nasan da zancen tafiyan mami don naji tana waya kan tafiyan yasa na tashi da wuri na nufi dakin ta koda abinda zata sakani a lokacin.

   Aikuwa iba shiga dakin na samu ta fito daga wanka saida nayi mamakin hakan don bata ko tsaya jira inzo in wanke bandakin ba ta shiga.

  Gaisheta nayi na nufi bandakin har ta karasa shirinta na dawo na fara gyara don ko kadan ban kawo dani za a tafi tafiyan ba don banga alaman hakan ba.

    Hankali kwance nake aikina ina shiryawa maki kaya kamar yadda ta umurceni inyi mata anty Aisha ta shigo dakin tana gaida mahaifiyar nasu.

    Bayan dun gaisa mami ke fadin ina fatan kin shirya dai don banson bata lokaci ga tafiya kin sani dai.

   Mami wani shiri zanyi kauyefa zamu tafi banga abinda zan shirya bani ko haka zan iya tafiya ai ta fada cikin zolaya.

    Mami tace da ita ai kauye garine don akawai yan Adam a ciki na dauka dai daji zaki tafi ai ta kwashe da dariya don tasan ta tabo mami din .

    Gaba dayan mu zamu tafine mami ta tambaya tana kallon mahaiyar nata lokacin da ni kuma nake masu dan murshi don jin amsan da mami din ta bata.

   Naji mami tace eh dake da yan uwanki maza ba na fadawa kowa tunjiya don kada yau su kawo min wani zance na daban.

    Hae su Nazima ta sake tambayan mahaifiyar nata sai mami din tace haba dai Aisha ai ba zan sake zuwa dasu ba tunda da biyu suke zuwa 

    Tun wancan zuwan da sukai min tsiya nasha alwashin ba zasu sake zuwa garin nan da yawuna ba.

    Mami samu,naka ne fa ba wani gari ba can Aisha ki fice mun a ido tun raki bai kai ga baci ba a dakin nan.

    Zainab jeki ki shirya kada ku bata min lokaci ta juyo inda nake tana fadi hakan yasa na gunde dariyan da nake masu jin an abamci sunana ga tafiyan nasu da za,ayi wanda ni banso hakan ba don sati biyu da komawan school ke nan mu.

    Dole na mike ba yadda na iya na koma dakina na fara dan shiryawa yan kayana kala uku a dan karakin jakkar da Aisha taban da zamu tafi kaduna.

  Karfe goma safe mun karya sai kaya ake ta fita dashi ana sakawa a mota yan matan sunso subita amma mami tace ba zata dasu ba tunda suna raina mata gari idan sunje.

    Ga motocin da za ai tafiyan dasu sai wani sheki suke ga hasken ranan daya fara gama gari suna daukan ido a ranan.

    Suna falo zaune na fito da kayan mami zuwa wurin mota kamar yarda ta umurceni indauko zuwa bakin mota jamal yana gurin zai nuna min inda za,a saka jakkar kayan nata.

    Wanan wau da ita za,a tafi halan Nazifa ta fada sai Rufaida take fadin kema ai kin sani itace yar miko min kawo min dole a tafi da banza.

   Maganan yai min zafi sosai saida ai aikina ne din hakan don sun fadi hakan bakomai bane gareni tunda kowa yasan abinda ya kawo ni gidan ai shine aikatau.

   Mota guda muka shiga nida mami da Anty Aisha sai driver nice a gaba zaune tare da driver suna baya a zaune su.

    Tun kan a baro gida banyi magana da kowa ba har mukai nisa ga tafiya naji Aisha tana fadin waiko mami lafiya yarki take ?

  Kodai abinda su Rufaida suka fadane ya bata maki rai kikai shiru tun dazun ?

   Mami tace ai kinsan ita din ba gwana bace wurin surutu barta da saurin aiki kan kamar inji mema suka fada matane daya bata mata rai haka ?

    No ba wani abu bane serious maganan su necan suke fadin wai ita dni ai dole aje da ita don yimin miko min .

 Kai wa yan nan yaran akwai tsegumi garesu bari Allah ya dawo damu lafiya sai na masu tsiya dai a kan yarinyar nan .

  Don banga abinda ta tare masu a gidan nan ba   da suke matsa mata haka ko da yaushe.

  A raina nace kayya mami kullun haka dai kike fada kin kasa yin maganin su haryau su kuma basu barni ba da fitinan su.

    Wai mami yaya Jafar din ya yarda zai tafi gidan  kawar taki ya duba yarinyar Aisha ta fada don a kawar da zancen .

  Don tsuki mami tayi tana dauko abu a cikin jakarta tana fadin ai kin san hali  shi dai.

   Danayi mai magana dariya kawai yayi min ya mayar dani karamar yarinya sai na masa da gaske zai maida hankali wurin abinda nake son shi dashi ai.

   Mami da kin barshi ya zaba da kanshi nima ban goyi bayan wanan auren hadin ba kindai ga yadda na yaya mamud ya zama a karshe ai.

   Ni dai ina gaban mota ina faman tunane a raina har muka kai garin samu,naka din sai bin garin nake da kallon irin ni,imomin da Allah yai masu a garin.

    Wani gida motan mu ya tsaya duk da anyi gyaran gidan daga wajen shi amma mutum zai iya gane tshon ginane na mutanen da masu shi a lokacin akaiwa gyara.

  Tundai in ka shiga daga cikin gidan zaka samu part part gidane babba da ya kumshi jama, a masu yawa sosai a cikin sa.

   Sai tafiya muke ana faman yi muna sannu da zuwa har muka kai kofan wani part daya sha gyara sosai an masa irin ginan zamanin nan .

    Wasu mata biyu ne suka fito daga part din suna faman yi muna sannu da zuwa dukkan su na shedasu don sunje abuja na san su a lokacin.

    Da sallama muka shiga falin babba wanda yasha gyara da kujeru manya manya na zamani komai dai na bukata a kwashi a falon.

  Sai hoton wata dattijuwa dana gani tayi gwagoron irin daukan da akaiwa photon sai kuma photon mami da mijin ta duk da bantaba gani  wanan photo  ba amma na san fuskan marigayin mijin nata don akwai photunan manya a falin mami har gidan su na Abuja a saka a falon gidan.

    Mami bata zauna falon ba ta shiga daga cikin dakunan  a ca nake jiyo muryan ta ni da Anty Aisha ne a falon zaune muka gaisa da sisters din mami din suna tambayan mu yaya hanya ?

    Can murya mami ke fadin ina kuke ne ku shigo ga hjyn a daki zaune kuzo ku gaisa kafin wa yancan su shigo.

  Mikewa mukayi zuwa dakin wata tshuwace a zaune saman gadon alfarama kamar ba dakin tsofi ba duk da tsohuwace matar hakan bai hanata kwaliya ba tana cikin atamfar supar a jikin ta.

     Aisha kan muna shiga gadon da take zaune ta haye tana fadin wanan ce mara lafiyan da mami ta tayar muna da hankali ga mutum na gani garau haka ba alaman ciwo.

  Tsohuwa mai barkwanci tana fadin ke kuma wanan shiga haka kamar matar limami chochi fa ?

    Duke nayiwa shi dan Allah dai udan zaki tafine ki tafi kiba mutane wuri kina dagawa iyayyen mu hankali haka.

    Daga inda nake zaune kafin taba Aisha amsa nace ina wuni mama sai ta mayar da hankalin ta a gurina tana fafin kedai yar albarka kunzo lafiya ?

  Yaya hanya ya kuka barsu a can nace lafiya yaya jikin mama Allah sa kafara ne ?

  Da alama taji dadin yadda muke gaisawa da ita din sai wasan baki take tana fadin amin yar albarka.

    Niko ko yar taki da ake fadi kin samu ke nan yarinya haka mai hankali Allah yasa ku raka tare.

   To mu da ba, awa addu,an a hana mu raka din kaji min tsohuwa daga ma kin samu anzo gaidake har da zaben yiwa mutane addu,a.

    Muryan yaya mamud ke fadin ni ina matar take gani nazo kada ki tafi muna son ki a hakan ko dan kwanciyan hankalun uwayen mu.

    Kaji ja,iri kice dasu kike tafe ashe yau ina da babban bako a garin nan mamuda yaushe ranon ka da garin nan tana kokarin mikewa tsaye da kyar.

    Aisha ta mayar da ita ta zauna mami takai mata duka tana fadin Aisha yo ga tsiya karki balla muna tsohuwa garin shashancin ki.

    Barta ai gani take kamar ta fini kwari a hankan yanzu sai in lankada maki dukan tsiya a wurin nan.

  Duk aka sa dariya sai ga daya sister din mami ta shigo tana fadin hjy yau fa kinyi baki harda Jafar akazo gaida ke.

   Mami tace har kwana kuwa zasuyi maki a nan sai ki shirya ke nan kedasu yau a gidan nan.

   Tana tafin dadi da murna ta samu ta mike da kyar tana lale marhabi da manyan bakina yau kuce amarya nake sai na zaba ashe tana fita daga uwar dakin nata din zuwa wurin su ta taresu.

     Zeey jeki dauko mi kayana ki shigo dashi dskin nan mami ta fada na mike saida tsohuwar ta gama fita na dan bi gefen ta na fito daga dakin.

    Suna zaune dukkan su tana masu lale marhabin cikin jin dadi har na fito kayan da mukazo dashine aketa faman shigowa dashi gidan.

    Jakkar mami dana Anty Aisha na dauko na shiga dashi daga cikin daki  kafin i  koma in dauko nawa sai kuma na rasa yadda zanyi da jakkar nawa.

    Na dan tsaya daga kofa ni ban shiga ba sai da dayan sister din mami takece min dan Allah shiga da ruwan nan mikawa su anty in gama da wayan nan.

    A lokacin na samu komawa dakin na samu mami ta kewaya ban daki Aisha kuma tana rashe rashe saman gadin tsohuwar tana waya.

    Ruwan na aje masu kafin in dan samu sakon gado na aje dan jekar kayana a wurin na juyo ina fadin anty Aisha ga ruwan .

   Da hannu tayi min alaman a, a na dai samu wuri na tsugunna duk da kishin ruwan da nakeji ban yarda nasha ba tun kan mami ta fito tasha.

   Ta fito tana fadin an shigo da kayan nan duka zeey  don miyan nan kada a zubar dashi don Allah fadawa Ramatu ta kawar dashi kada a zubar.

   Don miyane mai yawa na zabbi dana kan saniya banda nama da mami ta saka a soya a zuba a babban ruba mai marfi kuma.

    Na mike da sauri duk da ban san wacece Ramatun ba a cikkn su sai dai nayi sa, a suna falon dukkan su nake fadin mama Ramatu mami tace akwai miya a waje akawar dashi kada a zubar.

   Ke wanan muryan wa zaisan kina magana a hanka yaya jalal ke fadi yana nunawa mama ramatun ni a lokacin.

    Na sake maimaita abindana fada da farko tana fadin aikuwa gara da aka fada muna bari yanzu a kawar dashi gurin.

   Umma ina key din dayan dakin yake akai kayan a ciki tana tambayan tsohuwar data mayar da hankalinta kan diyan mami da suka sakata tsakiya da hira.  ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣8️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


FATAN ALHERI GAREKU MASOYANA UBANGIJI YABA WUNI LAFIYA YA SADAMU DA RAHAMIMIN SA AMIN YA ALLAHU.

   

    KI BIYA HAKKIN MU KI KARANTA A CIKIN SALAM DA SAKEWA DARI UKUNE KACAL 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA NA DARI UKU.Ranan naga yadda ake nunawa jika so da kauna na gaskiya don tsohuwar kamar ta hade yaran su koma cikinta take ji basu kadai ba harni da nake bakuwa a cikin su bata nuna min bambancin hakan ba.

   Ga tawa kakar saboda wani dalilu nata na daban ta turoni bitnin yin aikatau badon Allah ya hadani da uwar daki ta Allah ba.

  Allah kadai yasan yadda rayuwata zata kasance a birni ba tare data damu da hakan ba ita nata butin dai shine ta samu kudi ta gareni kawai.

    Basu bar dakin ba nan kowa ke zuwa taron su suna gaisawa su yaya jamal ne suka mike don zaga gari zama wuri daya ya ishesu.

    Yaya mamud ya dade da fita daga dakin ya barsu yana fadin zai leka wani abokin shi ko yana nan suka bar yaya jafar dake faman aiki a cikin sytem din shi yamai da hankalin gaba daya ga abinda yakeyi din.

   Ina zaune takure wuri daya na kurawa tv dake aiki ido ana wani shiri a kscm kaduna hakab yasa hankalina ya dauku ga kallon.

    Ai bata jikaba tshohuwar ke fadi me take da suna tana murmushi take kallona nayi firgigit in dago kai sai naga ido shi a kaina.

    Bakiji me na fadaba yake tambayaba kai na girgiza mai ina tasowa daga inda nake ki dauke kayan nan da suka bari a nan ya kara fada.

   Sai lokacin nasan meya fada da farko na tashi da sauri na fara tattara kayan dake saman karamin table din.

   Waini kan dan gidan iyami yaushene zaka kawo muna sarakuwa tshohuwar ta fada tana kallon shi.

   Cikin basarwa da kalan maganan shi ba tare da ya dago kaiba yake fadin banga matar aure ba har yanzu.

   Allah na tuba duk matan daka baro kaduna har Abuja bakaga mata a cikin su ba don tsaban ruwan ido idan an fada uwarka ta tare maka.

  Ni yanzu nafi dason yaro yayi auren shi a cikin lokacin don wanan rayuwan baida tabbas dan rayuwan yanzu kadan ne.

   Ba sai ki nema min ba tunda ke kinga matan a ko ina birjit yo ko cikin yan uwanka ka nema mana ko wanan yar ta uwarku ai irice ta kwarai gata da hankali har naji dama ace ta shigo cikin zuria na.

    Ke kiji da kanki don Allah da wanan shirme da kikeyi an fada maki kowa irin kune halan ya fada yana zareww tshohuwar ido.

   Ta sake dariya tana fadin kaji min dan kawai ido ma zaka zare min don kawai na fadi gaskiya ko sai mun kaika mararaba mun ma wankane kafin a soka.

  Kinga idan kina matsa min da wanan magana idan na tashi na tafi ke nan ba zan dawowa ba ya fada kanshi duke.

    Nasan zaka iya dan nema mai zubin jan fata kai dama Allah yaga abinda ya gani ya kaika can cikin su da zama.

    Wanan karo  kan tare dake zamu koma ai don naga kema dasu kikafi kama ai barni na mutu musulma tsohuwar ta fada.

  Saiga mami ta shigo falin tana fadin hjy dake dawa kike magana sai ta ganshi a zaune take fadin a a aboki kai kana ciki ashe na dauka tare kuka fita ai.

  Ina nan mami idan wanan tsohuwar bata daina damuwana ba zan bar garin nan yanzu ba sai anjima ba.

   Zaka iya na sani damuwar dai nasan fadan so kankane takema da baka son ai maka ko ?

   Kamar kin sani yar albarka daga zancen aure yake wanan halakon haka kamar an mashi maganar mutuwa shi.

    Wai shi baiga mata ba duk garin nan nakece mai ga wannan yar taki tun ba a kai ko ina ba don ni na yaba da halaiyar wanan yar taki.

    Da sauri mami ta juya inda nake ina daukan gorunan drinks a kasa take fadin haba dai hjy har abin nasa yakai haka kuma ?

    Ai ba zan barshi ya tafi ba sai ya tsayar da matar da zai aura in yaso sai ya koma idan bukin ya karaso ya dawo ayi buki nima zaman shi haka a can shi kadai ya dameni yanzu.

    Kaji maganar gaskiya don wanan da kike gani idan bakiyi da gaske ba baida niyar aure yanzu gashi ya fara zama magidanci.

   Wani kallo yaiwa tshohuwar tare da mikewa lokaci daya sai kuma naji ta koma rarashin shi tana fadin ai kasan bama haka dakai.

  Kada kasa mamuda yai muna dariya tun ba,aje ko ina ba yanzun fa na gama mashi tsiya a kanka yai fushi ya fita don nace kai nake so.

    Yanzu ma zan fada mai ya dawo nabar masa  ke ya dauka bana so ni don kin faye jininini da yawa yanzu.

  Dawo dawo ka zauna na bar wanan jininin indai a kankane na isheka ni kadai ai dama ai baikai ciki ba zancen nawa ina ka taba ganin mutum ya dabawa cikin sa wuka ?

    Komawa yayi ya zauna  sai abin ya bani dariya har bansan lokacin da sautin dariyan ya fito min fili ba.

    A, a a takwarana dariya kike min kuma don ina neman shiri da maigida a gaban ki ?

    Hararana yayi yasa na bar falon na koma daga wajen dakin na zauna saman dan dakalin dake wajen ina kallon mutanen gidan dake gittaya tako ina.

   Sai da ta fito da niyar zuwa sallah mami ta biyo shi suna magana dashi mami ke fadin zeey a nan kuma kika zauna ne ?

    Na juyo ina dan gaida ita take fadin shiga mana ciki koda yake ma anyi sallah azahar yanzu sai ki shiga wancan dakin dake gefe akwai bandaki a cikin sa a gyare dakin yake ku zauna keda Aisha.

    Jin haka yasa na mike ina kokarin shiga dakin don kallon da yai min mai kama dana warning a lokacin.

      Dakin da mami tayi min kwatance na shiga dakine gyarare da katon gado hade da mirrow din shi sai kujera three seater dake dakin gadon yasha gyara dakin yana ta kakahin turaren wuta.

     Ban dakin na nufa na samu ruwa a manyan robobi aje dashi nayi amfani na dauro alwala nafito na tayar da sallah saman salyan dake dakin.

    Ko dana idar ban zauna ba falon na fito na gyarashi tsab har waje duk suna cikin daki basu sani ba sai da mama habiba tazo fitane ta ganni take fadin yar nan kina nan kina aiki baki huta ba.

   Hjyn su mami ke tambaya wace yace kuma sai kuma ta tuna dani take fadin au yar iyami ko ?

   Wani aiki take kuma yarnan ki huta hakana mana ina hankalce da ke baki da son kazanta ta juya inda mami take kwance tana fadin.

  Kin samu ya sai ki rike tada amana don Allah yarinyar tana da shiga rai lokaci guda gata da ladabi.

    Sai naji ina kwadayin hada iri da ita don irice mai amfani ita din ba abin yarwa bane haka.

   Hjy nima yarinyar ta kwanta min a rai sosai ina kulla da ita tankar yar cikina don bata da kyashi ga sanin ya kamata kamar wata babba can.

   Tarbiyane idan kinga haka ta samu tun daga gida uwarta ta tarbiyartar da abinda yadda akeson ko wani da ya kasance sai ki kara himma wurin riko Allah ya taya ki rikasu.

   Don tafi min wa yan nan marasa moriyan sau dubu a wurina sai hjyn tasu tace tafisu kan gaskiya yaron da ba sai kace ya tashi yayi ba yake abu ai yana da dadin zama.

    Hjy kin san wancan zuwan da nayi da yaran nan iskancin da sukai min saida muka koma gida nake ji nayi masu tas wallahi.

   Kiyi hakkuri dasu tunda su suka kawo kansu gare ki inma sunyi maki don kansu kowa ma zai girbi tsiyar shi ai.

   Ke dai ki rike wanan bisa ga amana da yarda idan dai bata kauce bane don mutum mugun icce ne sai yaga ya ginu yace kaine makiyin sa daga baya Allah ya kare mami ta amsa da amin.

     Sai dare mazan suka sake shigowa ina daki naji hayaniyan su ban daga daga inda nake zaune ba naji muryan mami ta fito daga uwar daka tana fadin.

   Garin yai maku dadi ke nan ko kun shige cikin gari tun dazun ina shi aboki yake ne banganshi tare daku ba.

    Wanan friend naki saike mami yana masallaci mun barshi wai yanzu yake son sallam guards din shi su koma kaduna su kwana.

   Da daren nan tau haka dai yace don wai baiga inda zakaisu ba nan suwa ke nan tsohuwar ta tambaya.

   Security din da mijin ki ke tafiya dashi don tsaro yaya jamal ya bata amsa a takaice take fadin.

  Ikon Allah tafiyan ma sai anyi shi da masu tsaro ko may sai yaya mamud yace kin san su can hakan ai wani abu ne tundaga can aka hadu shi dasu aikin su sukeyi su.

    Duniya inda ranka kasha kallo yanzu shi wanan dan figegen aron ne harda wasu masu tsaron shi.

  Hjy mu a nanne ba a dauki tsaro da mahinmanci ba amma su can idan har kai wani abune dole kana da masu binka a baya ai massanman shi da sukeji da shi a can.

   Waini na kasa gane aikin yaton nan sai jalal yace bako zaki gane ba don shi bros telent ne sosai ilimin shi yaja masa hakan.

    Yanzu zai iya kera maki wani abu a wurin nan wanda sai kinyi mamaki don har abin yai tafiya da kafansa su ake kira da sciencetics mana masu fasahan kwakwalwa ikon Allah tace.

  Tare da fadin gaskiya yaki aure haka har yana batun rufe arbain fa don in ba zan manta ba tun mulkin shagari na farko  aka haifeshi ai.

    Kai hjy wanan tashin tasgin haka kan friend dina yanzun dai ni abinda nake so kafin ya tura mutanen nan a cikin daren nan ai masu kokarin wurin kwana hjy.

    Tshohuwar ta tambaya su nawane akace hudu hudu ta fada da mamaki tana fadin har karte hudu ke yawo dashi wanan abindai da nake gani.

  Ikon Allah yafi gaban mamaki yau ace wai dannan ne Allah yaiwa bawa haka Allah ya ciyar daku baki daya suka amsa da amin.

    A daidai lokacin da dan bawan ke shigowa yana waya tsohuwar ke fadin gama yanan ya shigo dayani.

   Kai yanzu don baka da tausayi zaka tura yaran mutane da daren nan su koma kaduna don rashin imani.

   O lord wanan kuma wani zance take hakane da shigowan mutum ya fada yana kaiwa zaune yana aje wayan da yakeyi.

    Aboki wai yanzu da daren nan zaka tura security din nan su koma kaduna sai naga dare yayi ai.

    No sun fasa ai mami uncle bello ya sama masu wuri zama da zasu zauna suna can sun tafi suga wurin kafin su dawo su dauki abinci.

   Ko kaifa nace ko kai fa dan nan amma ka tura bayin Allah a cikin daren nan haka ai abin baiyi ba kamar dai ba mutane a nan.

   Enough dan Allah waiwa ya fadawa wanan mai wa,azin ta damu mutane da wa,azin nan nata a gurin nan.

    Kai rufamin baki aini yanzu nasan ba cikkaken namiji kake ba don a matsoraci nake kallon ka yanzu tunda sai an rakoka har karkaran mu matsoraci.

    Daidai lokacin nake fitowa daga dakin don kira da mami tayi na amsa daga ciki.

  Dariya ya bushe dashi bashi kadai ba duk wanda ke falon saida maganan ya bashi dariya yadda suke kwasa dashi din.

    Barin gani idan baki tsorona din da gaske ya fada yana mikewa ya harota ta juya tana neman abinda zata kare kanta kafin ya iso gareta .

   Tayi sa,a filo na kusa da ita ta dauka wai dashi zata kare kanta din tana kaimai duka yana dariya ya juyo a daidai lokacin na kawo wurin zan wuce sai ji nayi kumus nayi baya tangal tangal zan fadi.

   Mami tace zaka karya min da da wanan karfin naka haka kamar na doki shi kuma ya juyo yana fadin oh sorry .

   Tsohuwar nan kinga zaki saka in karyawa mami yarta don fitinan ki to yaushe rabo damuyi fitinan haka.

   Ai rabu a gana arzikine dan nan wata ran idan kunzo sai kun tunani da wanan wasan da mukeyi yau ina Alh ina mahaifin ku sun kare.

    Kowa yai wani iri a dakin don abinda tsohuwar ta fada wallahi hjy gashi yau muna kewan tsohon nan don da zaran zan shigo naga part din shi sai in tuna da lokacin da muke zuwa yana bamu mazzakwala muna sha yaya mamud ke fadi.

    Kai mukan bamu sanshi ba gaskiya sai dai a photo jalal ya fada  ai old man din nan ya kware mu daya tafi bamu sanshi ba.

    Waike zeey kin debi abincin nan kuwa na juyo ina fadin ban diba ba mami yanzu na idar da sallah dama.

   Jeki ki dibi abinci da wanan halin naki ga abincin mu can ankai mana daki tun dazu wanan nasu sai na mutane yayan ku  yacan sai a samu yaro yakai masu idan sun dawo.

     Juyawa nayi zan koma dakin don ban iya sake jiki suna wurin don haka na juya don na koma dakin hjyn su mami.

    Banji me yake fada ba yaya jamal yace ke wai kizo ki zuba mai abinci yar mami.

    Jin an ambaci sunana yasa na tsaya tare da juyowa na dawo zuwa inda abincin yake aje dan kallon yaya jamal nayi ina fadin wa zan zubawa.

    Yaya jackson ya fada hankalin shi naga wayan shi rasa abinda zan zuba mai nayi don kuloli ne gurin zasu kai biyar duk an cikasu da abincin alfarma har da fate da mami tace tana so yaji gyada a cikin sa.

   Fara bude masu kulan abincin nayi don ya zabi abinda ranshi ke so sai dai baya kallona hankalin shi naga waya yana rubutu.

     Yaya me zan zubama na tambaye shi ina dan gurfane a gaban shi don ba dining table falon tsohuwar kamar can gida kaduna.

    Ya dan dago kai yana fadin anything zaki iya zuba min Aisha ta fito daga dakin yaya mamud daya karbi plate din da mami ke shan fate yana dan sha yake fadin Essha kina gidan nan ashe tun zuwan mu ban ganki ba.

   Ina kwance ne yaya ta fada tare da ratsowa ta zauna a hannun kujera tsakiyan su shi da yaya Jafar din.

       Ke may kike a wurin nan ne haka ta tambayeni ya Jalal yace wai abinci akace ta zuba take tunane na dan kalleta ina fadi a hankali ban san may zan zubabane ai.

   Oh shine kike tsaye a gurin ya mamud yace ka duba ai tana da gaskiyar ta kada ta zubama abinda baka so ne.

    Wanan dai ina so inga matar shi kafin in mutu yaro da izza da isa kamar wani basarake dashi matar ka tana da hakkurin zama dakai haka.

   Hjy naga fa yau sai yar tsama kuke da yaya Jackson tunda muka zo Jalal ya fada don shi yafi yawan dan magana bisaga Jamal dake da zubin yanayi ya jafar din wasu halaiyan su suna da kama sosai.

   Aure nake son yayi hakana ya baku wuri kuma ku samu ku zaburo wanan gwauron ya tare maku wuri.

    Muka fada maki samarin suka fada tace to ai shike nan tunda baku son a matsa mai yayi aure.

   Wanan fa zata iya hada ma abincin nan duka tunda kace anything zata dauka kace tayima mix ne gaba daya Aisha ta fada tana kallona.

   Ke zuba min ki daga min nan don Allah ya fada tare dan dagowa yana kallona.

   Hasken kwan fitilan falon ya haskani gaba daya launina bada wani kala na daban ga mai kallona a lokacin.

    Na duka ina zuba mai kullan gabana wanda sakwara ne a ciki ashe sai na bude kulan miyan shi dake dauke da miyan ganye yaji egushi da manyan nama na zuba daida don nasan shi baya cin abinci da yawa.

  Mikewa nayi zan bar wurin ya kara fafin ruwan wanke hannu fa ba tare daya ko kallo inda nake bai yi ba yai magana.

   Har suka bar falon ban kara fitowa ba sai bayan danaji fitan su sunawa mami saida safe na dan kara mintina na fito.

   Kayan da sukaci abinci nake kwashewa yayin da nazo kan nasa naga spoon a ciki da alama dashi yaci.

   A raina nace bakin bature ke nan abincin ma da cibi zaici don sallo ai kakar nan tasuce maganin shi.

   Tas nayiwa falon kafin in shiga wurin mami ina tambayanta koda abinda zanyi mata kafin na kwanta.

  Zeey a kwashe kayan abincin nan da sukaci nace na kwashe mami ki duba min kayan barci na a cikin kayana ki ban shike nan sai kije ki kwanta.

     Har na kwanta a saman dogon kujera anty Aisha ta shigo tana fadin af namanta da charger na dakin tsohuwar nan dan Allah zeey dauko min.

     A kofa na tsaya nayi sallama kafin in shiga dakin yanayin dana samesu a ciki nagane wani magana sukeyi mai muhinmanci a tsakanin su su hudu.

  Tsohuwar da kuma kannen mami din duk suna zaune sunyi shiru da suka ganeni.

  Sai mami ke fadin bakiyi barci ba ashe zesy a, a nace nake fadi charger anty zan dauka ganin suna kallona duk sai na tsargu .

  Na dauka na fita da dan saurina daga dakin don ban son in dakatar masu da maganan da sukeyi din .

     Washe gari tunda safe  dana tashi nayi sallah na fara gyaran falon har zuwa waje ina jin hayaniyar su dakin har na gama wanka na shiga don  mami tana cikin dakin da yan uwanta.

    Sai kusan karfe goma suka fara shigowa falon ana gaisawa a tsakanin su babu muryan wanda nake jin tsoro don haka na fito na gaidasu da kwana ina jin mama Ramatu na fadin.

   Ga abinci nan tun safe aka aje masu shi basu shigo ba ina shi jafar din gana yan aikin shi nan suma .

  Bai fito ba jamal ya bata amsa tare da fadin mama kinsan shi baya fitowa da wuri haka ai sai idan ya gama abinda yake yi.ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅1️⃣9️⃣  ZAINAB IDRIS MAKAWA


YAN UWA  FATAN ALHERI  HAR KULLUN A GARE KU UBANGJI YA GAFARTAWA MAGABATAN MU DA DUKKAN MUSULMIN DUNIYA ALLAHUMA AMIN.

    

    YAR UWA BA ZAN GAJI DA TUNATAR MAKU BIYA KAFIN KI KARANTA BA DON KAICEWA SHIGA HAKKI GA MASU IMANI ALLAH YASA MU DACE AMIN DARI UKU NE KACAL KI GUJI RAINA HAKKIN WANI A KANKI DON ALLAH.


Saida gabana ya fadi don jin muryan dodona da ya shigo gidan bani kadai na gane ina tsoron shi ba don har salma,  Rufaida da Nazifa.

     Idan ya shigo na kanga sun shiga taitayin su a gidan har jamal da jalal suna wanan rawan jikin da kama kai a gaban shi idan yana kusa .

  Nima hakan da nagani ya darsa min tsoron shi a lokaci guda duk da ban taba ganin wanda yaiwa cin fuska a gabana ba.

     Dagowa nayi a rikece ban ko debi abincin kwarai a platen din ba don in gudu in koma dakin mu.

    Na dai samu gaida shi da kwana na jakafata na shige dakin zama nayi don cin arish da kwai dana debo a falon .

   Nayi loma biyu ne naji mami na kwala min kira daga falon da sauri na mike na fito falon ina fadin mami gani.

   Tana can tana magana da mama Ramatu kanwarta a lokacin kafin ta juyo tana fadin .

    Yauwa zeey don Allah yi serving din yayan ku gashi nan ya shigo yanzu ni zan dan fitane yanzu zan dawo.

   Tana fadin haka ta mike sai naji yana fadin amma da mota zaku don akwai dan nisa daga nan gidan.

    Eh ai shine yasa nace Jalal ya sauke mu kada yaje nisa yana waje yana jiran fitowan mu ai.

   Amma mami jalal ne zai jaku ga driver suna waje sai shine zai jaku ban faye yarda da tukin yaran nan ba gaskiya yake fada da turanci.

    Sun saba jana a mota ko a kaduna don hakane ai na yarda da tukin motar nasu.

     Allah tsare yace yana mayar da kanshi ga wayan dake hannun shi aikin shi ke nan ko magana yake hankalin shi a kan waya ko sytem din shi shiya a raina nasa mashi mayen computer.

    Abincin na gama zubawa lokacin falon daga shi sai tsohuwar dake zaune itama kudi take kirgawa daga haban zanin ta nakai mai abincin gaban shi na aje.

  Ruwa na koma na dauko na aje mai cikin dan muryana nake fadin yaya ga abincin nan do  gudun kada inyi laifi kuma gare shi.

    Jin abinda nace yasa shi dan juyawa saman lafiyayyen kujeran falon tsohuwar da zaka iya da kira dakin wata amaryace can don haduwa.

   Wayan ya aje daga gefe kafin yakai kallon shi ga abincin ya dago kai yana kallon tsohuwar kuma.

   Kai kai kai wanan tsohuwar ko fashi kika farane haka ina kika samo wanan kudin haka masu yawa ?

   Yanzun kuma bakiki kariba don baki da tausayi sai kuma kin karbewa mami dan kudin ta maimakon ki kara mata.

  Kafin tsohuwar ta dago kai tana fadin ja,iri da hausan ka kamar na mai koyo uwar taka mai tausayina ita take aiko min da kudin ai.

     Yau kuwa zance ta daina don ba kashewa kike yi ba boyewa kike yi idan an baki ashe.

    Ina wurin fridge ina daukan ruwa insha suke wanan barkwamcin da kakar tasu na dauko ruwan na juya zan wuce daki don da farko tsoron shigowan shi ya hanani daukan ruwan .

    Naji yace ke wanan uban abincin da kika zuba ni dawa zanci shi haka ?

    Tsayawa nayi wuri daya da goran ruwan a hannu na ya sake fadin sai kizo ki dauka ki cinye shi tas.

   Cikin karfin hali nake fadin na debi abinci yanzu yana daki na aje zanci kai wanan yaron da fitina kake wallahi ina laifin yar nan tana iya kokarin ta da kai.

     An fada maki kowa irin kine dake loda abinci a cikin sa yana kiba kamar za,a tafi gasan gwaji dashi halan ?

    To ba zataci ba idan zakaci kaci da yawan fitina har yaushe zaka zauna kana matsawa yarinya mutane haka.

   Yar nan ko karyawa bata samu tayi ba yanzun taga ba yan uwanka abin kalaci suka fita kai kuma kazo da naka tsurkun yanzu.

  Idan kayi fushi sai kaje kayi aure kowa ma ya huta mitar ka na tsiya kaji min yaro da jarabar tsiya haka.

    Hjy dama naga kin gaji dani ai ki huta min gori yau kaduna zan kwana idan Allah ya yarda idan ka tashi ka wuce jos zaifi ma sauki ai.

     Ina tsaye wuri daya ni ban gusa ba ina sauraren  da bai karewa da tsohuwar ko da yaushe sai dai idan basu hadu ba idan kuma bata ganshi ba ta kafa mita ke nan ina ya shiga.

   Zo ki dauki abincin nan na fasa ci ya fada da dan  karfi simi simi na tako zuwa gaban shi ina zuwa nakai kasa tare da fadin.

   Don Allah yaya kayi hakkuri na fada ina kaiwa kasa kamar zanyi kuka a gaban shi bace min dagani a nan na firgita sosai tare da kai hannu ina daukan plate din abincin.

   Na juya ya sake fadin zo nan na dawo baya da sauri zuwa gareshi hjy ko sai faman yi mai masifan hakan takeyi bai kullata ba.

  Baki da wasu kayane sai wanin black dress din da kullun kike sakawa ba kyau gani ?

   Kallon kayan na jikina nayi ina fadin anty Aishace ta bani sune sabbin kayana yanzu dasu kawai nazo garin nan.

   Fadan da kakan nasu takeyine ya hana taji me yake fada min don babu yadda zata jishi a yadda yake maganan.

      Tafi don Allah ya fada in deep voice na juya da sauri don in bar wurin kafin yakai ga makeni yadda naga ya hasala din nan.

   Tunda na shige ban kara fitowa ba shi kuma bai fita daga falon ba don ina jin muryan shi jefi jefi da hjy tsohuwa a falon.

   Har su mami suka kai ga dawowa gidan hakan yasani kwantawa na kirkiri ciwon karya don da Anty Aisha ta ganin kwance take tambayana nace kaina ke ciwo.

   Data fitane mami ke tambayan ina inane tace tana daki wai kanta ke ciwo tace .

  Yo ai dole kai yayi ciwo ko don fitinan wanan masifafen dan naki da kika barta dashi ta bashi kalaci ya aza mata fitina.

    Aiko ya Jackson baida fada hjy kece dai baki fahince shi ba Aisha ta fada tana kallin dan uwan nata.

    Murya mami tasa ta kirani daga falon kamar ince wayo don wani irin faduwan gabane ya zuyarci zuciyana lokaci guda .

   Saboda tsoracewa gashi yai min fadan jallabiya baka dana saka a jikina wanda har yanzu shine dai din a jikin nawa.

   Don gigicewa ban ko tsaya daukan dan kwalina ba kaina dake da kitso tsoro hudu da nayiwa kaina a daren da zamuzo sun kwanta suyi lub dasu ga bakin gashi na sai sheki yakeyi.

    Na fito nazo na zube a gaban mami din dake maganata da mahaifiyar ta kan rashin sake jikina a cikin su.

   Ban iya dago kai na kalli kowa a falon ba kaina yana sade a kasa ina jiran inji abinda zatace dani.

   Shiko ko kallon inda nake baimayi ba tunda nazo gaban mami din gashi a kusa dashi mami take zaune a daya kujeran dake gefen shi.

   Meke damun kine zeey mami ta fada tana duban yanayina kai na dan girgiza tare da fadi cikin karfin hali mami kaina ke ciwo dama tun kan muzo nan na kuma sha magani ya fada min don kada tace a kaini asibiti.

  Haka baida wuya a gurin mami dan abu kadan gare su yanzu asibiti ne za a ce akai mutum.

  Mami tace dawo nan ki zauna ki daina wanan yawan zama ke kadai da kikeyi a daki ko yaushe koshi yana ja maki ciwo.

   Banda zabi sai yadda mami tace dani dole haka ja mataciyan kafata da yai sanyi na hau saman kujeran data nuna min din.

    Yaya jafar da ke rubutu a cikin sytem shi cikin kwanciyan hankali sai lokacin dana kai zaune ya dago kanshi yana fadin .

   Ke meke damun kine wani irin magani kika sha nayi tsuru tsuru da ido don ban san me zance ba sai da mami ta kara tambayana nace.

   Mami dama wanda aka ban asibiti ne a abuja sauran daya rage na sha dazun.

   Sai naji yaja uban tsuki ya mike yana gyara dan riganshi daya takure don zaman daya dade a zaune.

   Zaka fitane kafin ya ba mami data tambayeshi amsa sai hjy tace yo ina zai fita tunda tsoron mutane yake ji a waje.

  Wurin ta ya nufa direct yana fadin zo muje ki rakani kada kada a saceni garin naku.

    Wai wace ke zaune a kauye ke fadin wani na tsoron mutane ke idan ba tsoron kikeyi ba meya hanaki komawa kaduna ki zauna da mami.

  Ja,iri ba zan tafi ba a dakin mijina zan mutu inda ya barni ba dakin wani ba ya fice yana dariyan maganan ta.

    Ya dan jima a waje ina nan zaune falin tare dasu mami daketa baki suna fita don zuwa gaida mami din sai faman basu alheri mami keyi.

    Nasan dai da yawan masu zuwa gaida ita yan uwantane saura kuma abokan arzikine.

    Yayi sallama ya shigo falon suka amsa mai inda nake ya nufo yana mika min magani nasa hannu biyu na karba a cikin ladabi.

  Mami ke tambaya maganin meye wanan din yace stress don kila aikine yai mata yawa yana mika min ya juya ya fita daga dakin.

  Haka ya ban dama tashi  na hade maganin don dole duk da ban san maganin kome yake nufi ba aiko na fara jin jikina wasai.

   Ina sallah azahar sai barci ban tashi ba kuma ba wanda ya tayar dani din don sun dauka dai da gaske banda lafiya ne din sai bayan sallah la,asar na falka na tashi nayi sallah.

  Ina idar da sallah nayo falon part din tsit yake babu wani hayaniya acikin sa yasa na gane mami ta fitane a lokacin.

    Ko ina na gyara tunda aikinane nagama na hada kayan abincin da nagani ta nan na gane su yaya mamud sun dawo sunci abinci sun fita.

  Don da alama shi yasan garin sosai kilama yana da abokai a garin sabanin shi mai zaman gida ko yaushe.

     Salati naji a bayana mama Ramatu na fadin yanzu yarnan harda baki da lafiya baki kwanta kin huta ba ?

   Kina nan kina tikan aiki haka mama naji sauki na bata amsa  ina dauraye kwanoni dana tara wanda na wanke.

    Kinga idan baki da lafiya bar matsawa kanki haka ai kowa yasan ciwo ko a daga maki kafa dashi.

   Ni dai na gama ban ce uffan ba sai dan murmyshin da nakeyi kawai dakin na koma na shiga wanka kafin magariba yayi.

   Iya kacin ganina da yaya Jafar ke nan tunda ya ban magani saida darene nake jin su mami na magana wai ashe fitan da yayi tunda ya kawo min magani kaduna suka nufa.

  Yana zuwa kaduna gida ya nufa don yana son yayi wanka abinka da goggagen dan boko mai ilimi ashe duk zaman garin ya ishe shi .

  Dan daurewa yayi kawai don ya farautawa mahaifiyar shi da kakan shi raine.

   Sai dai ya kasa kanne zama har kwana biyu ko ukun da mami tace zatayi da mahaifiyarta a tare dasu don suga yan uwa yan uwa su gansu.

  Tun daga kofan shiga yake jiyo hayaniyar yan matan a gida yake mamakin me suka samu hakane suke wanan hayaniya haka ?

   Rawa suke tika ga kida yana tashi kamar gidan club Nazira da Ruby suna wani irin rawa wanda bai dace ace sunyi ba.

    Ba wanda yasan da shigowan shi har ya tsaya yana kare masu kallo a wurin kafin kamshin shi dakewa mutum sallama ya daki hancin su.

   Duk suka juya suna kallon kofan salma na zaune tana shan milk a cup tana dan kurba a hankali itama daga inda take din zaune tayi arba dashi.

   Rudewa ko wacen su tayi ya tako a hankali zuwa part din shi dake gidan don wanka yake son yi da sauran abubuwan daya bari a nan.

  Da sauri Nazira taje kashe kidan baiko juyo ya kara kallon inda suke ba ya shige part din bayan ya bude tare da gwauro kofan da karfi.

     Duk yadda yake jin shi a da sai yaji komai ya gushe mashi bacin ran yaran nan ya mamaye zuciyar shi.

  Yes yasan da yana wasu abubuwa da suka kaucewa addini da tarbiyan shi amma tsani yaga diya mace tana kauce hanya.

   Zama yayi sama  gado dakin tare da tokare hannaye shi ya kama haban shi yana tunanen zancen su da mami da take fadin.

  Ba zanso ka ketare gidan nan ba idan baka son yar hjy hindu sai ka zaba a cikin wa yan na yaran guda uku da ke gidan nan don nasan dukkan su babu wace ba zatayi makaba a cikin su.

   Tunda kai na fahinci baka da time din tsayawa dating da wata mace a yanzu tsuki yaja yana mikewa tsaye.

  Deep in  thought yaya za ayi ya auri daya daga cikin yaran nan da idon su ya gama budewa haka wai.

   Dadai yaso bin ra,yin mami don shi ba wata macen da ta tsaya mai arai yanzu don hakane zaibi zaben mami din gareshi.

    Wani tsuki ya kara ja ya fara cire aninin gaban rigan dake jikin shi fara longsilve yana maijin tarin haushin su a ranshi.

    Wanka ya fada ya dan dauki lokaci kafin ya fito ya samu waya  shi nata ringing ya nufi inda ya aje wayan yana dagawa.

   Yaya mamud ne a layin yai mai kira biyu bai daga ba gana ukune ya samu ya daga yake fadin ya jafar kana inane haka mami tana tambayan ka ta kira layin ka not reacheble.

    Ina gida yanzu haka ya bashi amsa kai tsaye gida yanzu na fito mami da hjy suna tambayan inda ka shiga yanzun hakan ina kofar gidan.

   Kaduna fa nake nufi ya bashi amsa kamar a hasale don har lokacin yana jin ranshi babu dadi ga abinda idon shi ya gane mashi din nasu Rufaida.

   Kokarin tayar da sallah dake kanshi yayi kafin ya gama ya shirya cikin wani jallabiya ya nufi gado ya fada.

  Saidai duk yadda yaso yayi barci hakan ya gagareshi don baison ya batawa mami rai ko kadan tunda yai mata alkawari ya zama dole ya cika mata burin ta..


    Mami tunda yaya mamud ke fada mata ai Jackson ya koma kaduna taji rayuwanta ya baci dashi sosai don me zai nuna bai iya zama a mahaifan ta.

    Ko kuma yayi hakane don gujewa zancen auren data tasa shi gaba dashi don ko a daren jiya saida sukai mai tas itada yan uwanta da mahaifiyar su.

   Wanan zance ne na sama sunayi da anth Aisha ta aikoni daukan mata charger ashe a dakin tsohuwar da dare.

   Mami uwar zamanice don haka ba tare data furtawa kowa bacin ran da take ji a ranta ba ta nasa zata kyaleshi taga iya gudun shi yanzu.

   Don haka ta daure taci gaba da tsabgoginta ba tare da nunawa kowa komai ba kamar ranta bai baci ba.

   Haka kuma tasa a ranta wanan karon ba zata kirashi taji dalilin yin hakan dayayi ya barsu can ba tare data sani ba.

   Karshe ma shigewa tayi da sunan zatayi wanka harta shiga dakin ta juyo ta fito zuwa dakin mu ta sameni kwance na rufe idanuwa na sai jin muryan ta nayi a kaina.

  Da sauri na bude idanuwana cikin laushin murya nake gaida ita take fadin ya jikin naki yanzu ?

     Naci sauki na fada a yar siririyar murya ina kokarin mikewa zaune ta sake fadin badai inda kike ji a jikin naki yanzu don in sani tun dare baiyi ba.

   Zama tayi a gefen gafon dakin tana dan kale kale a dakin kamar tana nazarin dakin ne ko kuma wani tunane.

   Na dago kai a hankali sai naga tana kallona can take ce min ko dai zancen karatun kine kika saka a rai haka zeey har yaja maki ciwon kai ?

   Nace lah mami wallahi bashi bane mami dazun daine kan nawa ya fara ciwo kuma ai nasha magani yanzu naji sauki.

   Tana mikewa take fadin to shike nan ina ganin zan karbar maki transfer tunda yanzu zaman mu zaifi yawa a can.

  Don ba zan barki ba inda bana don ke din kamar amana kike ga hannu na ai.

  Mami duk yadda kika zantar a kaina daidaine tunda kece uwana yanzu ai mami banda wata uwar dana sani kuma.

   Tace to babu laifi na gode ga yadda kike nuna min nima sai dai ina tsoron watarana kar asabe ta rabani dake.

    Asabe yamzu bata da iko kamar yadda kike dashi a wurina mami don ba tare nake zaune dasu ba kuma.

   Sai tayi murmushi tana fadin kafin dai ki kwanta ki kara shan maganin da aboki ya sayo maki dazun don ina ganin har da gajiyan aiki din a ciki.ZAINAN  IDRIS  MAKAWA


🦅   ABU CIKIN DUHU   🦅


2️⃣0️⃣


    ZAINAB IDRIS MAKAWA


  YAR UWA JUMMA,AT MUBARAK FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA UBANGIJI ALLAH YA KARBA IBADUN MU YA SADAMU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN RANAN YA GAFARTAWA MAGABATAN MUSULMI BAKI DAYA ALLAHUMA AMIN, , , , , , , 


   YAU MA DAI INA MAKI TUNI AKAN HAKKI DA KWABON KU MUKE SAMUN CIGABAN RUBUTUN MU A DAURE A  BADA HAKKI DON SAUKE NAYI A KAI, , , , 


Sai faman shiyawa muke tun dare ake shirin dawowan mu kaduna taaraba mai yawa aka hadawa mami irin abinda zata bukata a birni wanda babu shi sai a irin wanan gari.

    Gashi tare da wanan tsohuwar zamu koma don mami ta shawo kanta da kyar ta bari a kaita asibiti a dubata ta dan kwana mata biyu ta dawo koshi sai da wanan mami ya sa baki ta yarda da hakan.

   Tun a can mami ke fadin wanan bakuntar zeey ce da Aisha ce don dai nasan hjy ba shiryawa zatayi da sauran yaran nan ba cewa su anty salma dake gida.

     Bamu bar garin Samu,naka ba sai misalin sha dayan rana tafiyace maidan jayawa tsakanin kaduna da garin   sai dai a gurin su yake haka nikan a wurina kamar unguwane hakan ai.

    Don ko banza naga gari da kauyokan da nake jin sunan su a bakin mutane a da can da nake gida.

    Allah ya kawo mu lafiya don wanan karon  da motoci biyu muka juyo don mai tarin motocin ya juyo abinshi ya barmu can.

   Duk da nasan mami tana wayencewa kan barin ta can da yayi don kamar rashin da,a ya nuna mata ga hakan don naji suna magana da anty Aisha a dakin da muka sauka kan hakan.

   Aisha tana bata hakkuri da cewa mami ki dai bincika wata kila yana da wani uzurine yai haka don kinga ai daga baya jiya ya turo da sako a rabawa mutanen nan din.

   Mun samu su mama Kande sun gyara gida tsab suna koma kan aikin girkin da za a ci idan an iso,  da yake aikin nada yawa yasa basu kare ba kafin isowan mu garin.

     Sun fito sun tari kowa da murna da farin ciki ina tsaye wurin mota babu wanda ya kulani a wurin nikan driver na fara fitar da kaya na fara dauka na shiga dashi cikin gidan da nakw ji yanzu kamar gidan mune.

    Tsohuwarce tafe a hankali tana saye da glass din ido a fuskan ta sai farin gyale kwato dage yafe a jikinta dake saye da atamfan super mai ruwan haki da dorawa a jikin shi da manyan zane.

    Da sauri na karasa ina kokarin karban ledan maganin data rike a hannun ta zata shigo gidan ga su Rufaida suna gefe suna mata tsiya.

    A cikin ladabi na mika hannu ina karban ledan tace ba kaji ba yar albarka kedai kinfi wa yan nan kirki da hankali.

   Barshi kinji ba wani kayan nauyi bane a cikin sa ai, aiko sukayo min caaaa a kai Rufaida na fadin wanan ai bakin iya yi ne da ita ga kowa saita nuna ita yar munafukaine ai.

    Kai haba wanan zagin haka kuma fa ku daina wanan dabi,an bai da kyau ko kadan zagi harda iyayye.

    Rufaida ta hasala ta watsa min harara nidai duk da tace baida nauyi bai hana in karbi ledan a hannunta ba.

    Zama tayi a falo bayan ta iso da kyar don yanayin tafiyan nata yadda take yinshi a hankali ga tsufa ga ciwo dake damunta a jiki.

   Nan falo gaba daya suka zube sai nuna kauna ga juna sukeyi ni dai ina tsaye da ledan nama shagala ban sani ba.

    Banji fitowan shi ba sai kamshin shi daya doki hancina lokaci daya tare da muryan shi yana fadin watau nan ma kin biyoni ke nan ko ?

    Na gudo na barki can bai maki ba saida kika biyosu kuka dawo tare yana magana tare da daure fuskan shi kamar gaske .

    Ja,iri to baka tsira ba ai  don gani ko na biyo ka din don ba fasawa zanyi ba da magana ta sai kagaji kayi zuciya ka fito muna da mata mun gani idan shika guduwa dama.

    Mami yaya akayi kika zo muna da wanan yar matsalan tsohuwar gida yana magana yana kallon mami din data daure fuskanta tun fitowan shi kamar ba ita bace ke dariya yanzu .

    Saidai jin ya ambaci sunan ta fake fadin cikin daga mai hannu please live me alone don't metion my name again cikin kara daure fuskanta gare shi.

   Oh mami rely iam sorry for what i have done wanan tsohuwar ne ta dameni kuma nasan ba bari zakiyi in dawo ba idan na fada maki kai tsaye zanzo inyi wani abu a nan a ranan nima tafiyan ai da niyar in komane idan na gama sai gashi ban samu komawa ba.

   O hjy ce ma ta dameka har kana fadi a gabana forgive me mami iam sorry wlh wani abu nazo yi garin nan na lake a cikin sa.

  Alhalin tunda yazo yana gida bai fita ba yana daki yana ragewa kanshi zafi abindake tsunkularshi kwana da kwanaki.

   Is your on business koma meya baro ka da garin mu dai ai ba zaka hanamu yin kwanakin da mukai niyar yi ba a can.

   Ya dan laso bakinshi yana shafan kai don ya fahinci mami ta hau sosai dashi kan abinda yayi din na barin su can ya dawo nan shi kadai.

    Ke wai lafiya kin tsawa mutane saman kai haka kina bin mutane da kallo don rainin wayau Rufaida ke fadi a hasale.

  Keko gulma mana tana bin bakin kowa da kallon abinda ake fada kamar ba yar aiki ba ta dinga shiga cikin mutane tana kutsa kanta.

    Ikon Allah da alama yar nan dai bata jin dadi a wurin ku meye matsalanta don ta tsaya a cikin mu ita din ba mutum bace kamar ku ai dan mutum daraja gare shi tsohuwar ke fada tana kallo.

    Zo ki zauna a nan gaki tsaye kinyo tafiya baki zauna ba take fada tare da kallona tana nuna mi  wurin zama.

  Nace dama ledan nan ne ban san dakin da zan kai maki ba shine na tsaya na fada a dan marairaice.

    To kuma ji da abinda ya tsayar da ita a gurin ba tsayin banza tayi ba ta mika hannu in miko mata ledan dake hannuna.

   Mami tace na rasa me yarinyar nan ta tare masu a gidan nan da basu bata salama sai hattara da tsana.

   A,a in kinga hakan wata kila dai sun hango wani abune a gareta sukewa kyashin sa ko don yanzu ta karbe masu fada gurin ki.

  Su dai daina haka don ban so banyi sharawa da kowa ba da zan kawo ta gidan nan do haka ba zan dauki hakan ba gareta tunda ban bari uta ta raina ku ba.

   Gaban mami bazo na tsuguna ina fadin mami bani key in bude daki zan gyara ne kafin ki shigo.

    Ga dai key din gyara ki bari sai anjima yanzu dai ki kwashe kayan mu kikai min daki hjy kuma nata dakin ki kai mata sai ki koma dakin Aisha da zama ke .

   A, a barmu mu zauna  dakin ta a tare dama kawatace ki n ga ai ko tausa tayi min a dakin idan ina so naji kuma dumin mutum a kusa dani ai?

   Ko ba zaki zauna tare dani ba kawata tana tambayana cikin dan dariya tana kallon fuskana.

   Murmushi na sake wanda yasa fararen hakora dan baiya diple dina ya dan lutsa daga gefen fuskana ina fadin ina so sosai hjy .

   Ya daifi ni dama ba zan zauna da kowa a dakina ba Aisha ta fada tana mikewa tsaye  mami tace hakan baidai taso bane .

   A nan na barsu ashe baya  barina wurin Rufaida tayi fushi ta mike ta koma daki  su waya ta jawo tana fadawa uwarta wai mami tana disgata kan yar aiki ita gida zata dawo don hakan da ake mata yana ci mata rai.

   Duk da mami tace kada na gyara dakin ba yarda na barshi hakan ba don sai dana kara gyarashi tas na dawo dakina na gyarawa hjy yadda ya dace na dauko wani zanin gado dakin mami mai kyau na shimfida mata.

Falon na dawo inda na samu sun fara cin abinci har lokacin mami na zaune tare da yaran ta gaba dayan su a wurin sai salma da hjy ma kakarta ce don itace ta haifi uwarta a gurin tana nuna jin dadin ganinta.

   Yau zee kici abinci ki dauko zanin gado a daki ki shimfidawa hjycdakin ki .

   Nace na dauko na shimfida mami tun dazun ai tace kai zee na gode sa wanan karama hjy din da kike yi yamafi min ku zauna tare da zamanta da wanan mara moriya din tana nuna Aishan ta.

   Mami nice banda moriya bari ki gani har wanka zan dingawa hjy har ta bar gidan nan kuwa hannu mami ta watsowa Aisha tana fadin karbi naki nan ko uwarki Ramatu tayi kadan tayiwa hjy wanka yanzu ai.

    Abinci na diba na koma can gefe guda ina dan duban inda zan zauna mami ke fadin wanan abinci  zai ishe ki ke nan zeey ?

   Ya isa mami na fada ina nufar can nisa dasu don in zauna tsohuwar take fadin wanan ya da dadin zama take wallahi.

    Wanan ba irin yarwa bace a cikin ahali yarinyar ta samu tarbiya a gun uwarta kada ki bar wa yan nan marasa ta ido su kore maki ita gidan nan.

   Ai ba zan barsu ba mami ta fada duk wanda bai iya zama da abindanake so yayi gaba hanya a bude yake mai ai.

   Baidai kai can ba kowa ya tsaya a matsayin sa tsohuwar ta fada mami ta nuna salma tana fadin sune ai marasa hankalin yarinya ta girmamasu sai sun zubar da mutuncin su gareta zasuji dadi.

   No mami ba salma a ciki zancen nan don da kanta zeey ke fada min tana jin dadin zama da anty salma sosai idan muna hira da ita.

   Salma tace mami ni ina ruwana da harkanta gidan nan tunda bata tare min komai ba ga kowa.

   Shine daidai hakan ai kinji itama tana yabon ki a bayan ki gashi yanzu yar uwan ki tana fadi kuwa kafin ta juya wurin yaya jafar tana fadin.

   Kai gwauro ba zakaci abincin bane kai ko sai yayi sanyi ka tsikara ka tashi tunda baka aje ba balle a dumama shi.

    Zaki fara tsokanarshi ko hjy yaya mamud ya fada yana mikewa sai tsohuwar tace gashi ko yanzu ya iya yaji saboda korafina ba kuma zan fasa ba idan baiyi abinda nake son yayi ba.

   Ya dago kai yana fadin me kike ci na baka na zuba hjy kwana zan fitar da mata kowa ya huta ina shike nan.

    Shike nan kuwa kaga an wuce wurin haba ko kai fa mutum kamar me jin warin mata a tare dashi.

    Barshi hjy rainawa mutane yake son yi wanan karin ko ba zan saurara mashi ba don naga wasa ya dauki zancen nan.

   Mami ai na fada maki kwanan zan fitar kowama ya huta sai mami take fadin yar gidan wanene yarinyar da zaka fitar din ?

    Mami ai ko yar waye zaki gani idan Allah ya kaimu ranan dinan ki sai naba kowa mamaki a gidan nan sosai.

   Mami ai kin san sai yar gwauna ko wani seneter don irin su yaya Jackson sai diyan manya a kasan nan ai Aisha ta fada tana kallon shi tana dariya.

    Shima murmushi yayiwa zancen Aisha din yace kedai bari zan yi surprise din kowa idan na tashi sai hjy tace kada dai kaiwa mutane zaben tumun dare garin ruwa idon kan nan.

   Ni makoho ne aka fada maki ai kece mai bani shawara ki bari ki gani idan ban zabo da kyau ba sai ki fadi hakan.

   Wayan shi da yai kara ya dauka yana duba kafin ya mike ya bar wurin yana wani magana kamar yare sai hjy ke fadin.

   Itace ta kiraka kake gudu kar muji me kuke fada dama ka zauna da wanan yaren naku baji muke ba mu.

   Daga inda nake ina dan murmushi wani tunane yazo min nake fadin a raina zanso nima inga wanan zabin na yaya jafar yadda yarinyar zata kasance.

  Nasan badai kyau da kudi ba kan kamar yadda yake da kyau din nan ga ilimi ga wayewa dole wace zai aura din itama ta kasance kamar ai.

    Ni daya ke faman tunane har naji abincin ma ya fita a raina ina tuna sukan sunji dadin su uwa kudi uba kudi haka.

  Suma gasu kudi wai ina mutanen nan zasu da wanan dukiya hakane idan da nice su ai ba zan nemi wani kudi ba zan zauna in  hutane kwai inta jin dadi na a gida.

    Zeey zoki kwashe wanan kayan abincin nan wurin nan ki dawo ki kai hjy daki tayi sallah ta dan huta.

  Firgigit na dago kai tare da fadin to mami ina kokarin mikewa a inda nake zaune din.

  Sai dana gyara komai mami na zaune gurin tana waya da yayan ta da muka baro dazun garin su.

   Hjy muje in kaiki dakin azahar yayi tun dazun na fada a cikin ladabi ina kokarin daukan kayan ta gyale da ledan maganin ta dake gefenta aje.

   To yar nan har na fara gyangyadi ko a wurin ba tare dana sani ba tana mikewa tare da kokatin tattaro gyalen ta dake gefe.

   A hankali muke tafiya zuwa dakin har muka kai dakin yayi dan dumi sai kamshi ke tashi a cikin sa ledan na aje a gefen gadon kafin in nufi kofan ban dakin in bude mata shi.

  A, a kagani ba nan yayi min gara in zauna dake da in zauna da wanan mara moriyar Aisha wace ko kara ba zata iya kawar wa kanta ba balle wani.

    Bayan mun idar da sallah dukkan mu a nan kasan muka kwanta nabawa hjy filo tayi matashin kai dashi niko ko filon ban samu matashi dashi ba sai barci.

   Ban falka ba sai da hjy ta tashini don inyi sallah la,asar nasan yamma yayi saboda dadin barcin da nayi.

   Na idar na mike zuwa dakin mami bata dakin yasa na samu daman kara gyara dakin da yake ba wani datti a ciki dakin 

      A falo mamice da yaya mamud suke magana haka yasa na juyo zan koma dakin mu indan gyara don ko ba komai da zan wa dakin ban dakin yana bukatan wanki koda yaushe.

    Na wanke na fito ina daukan filon data kwanta a kasa take fadin yar nan idan kin rage sai ki kaini falo in zauna don yamma tayi yanzu.

   Na amsa da to hjy muje mami ma tana falon zaune tare da yaya mamud .

  Wai ni iyalin shi mamud din suna inane don banji duriyan su ba tun dazun ina a nan gidan suke zaune ne suma.

    Suna Abuja an barsu a can da zamu dawo kaduna yar ta kifen tana nan dai da halin ta har yanzu bata canza zani ba ko ?

    Dan dariya mai sauti nayi ba tare da nayi magana ba don ban san abinda zance da ita ba.

    Falin muka fito tafiyan minti daya daga dakin mu zuwa falin saida muka biyar muna lalabawa kafin mukai saman kujeran ta zauna a hankali.

  Mami na fadin kun lalabo kun fitone hjy take fadin yar nannta lalabo dani ina dan jin dadin hakan yarnan akwai kirki sosai.

   Allah yasa kiga aurenta hjy amin ta juya tana fadin kada ki tsaya dogon bokon nan na zamanun nan dake batawa mutum lokaci sai a dauki lokaci yaro na zubar da irin sa duk wata.

   Yaran nan da kun gane ai da ku aurar da su don har sun wuce munzali aure a yanzu .

  Hjy kin san ai aure dan lokaci idan lokacin sa yayi koda shiri ko ba shiri sai ayishi a lokacin.

     

  Zaune yake saman farar kujeran roba a gurden din gidan mai dauke da dogayen itatuwan da ba wani zugun ganye  suke dashi ba sai dai tarin tsayi a gasu.

  Babu wani abinda yakeyi duk da sytem din shi dake gaban shi a bude ya kasa aiwatar da komai sai faman tune a ranshi.

  Yakai hannu a hankali ya rufe sytem din ya dafe kan shi dashi yana ci gaba da tunanen shi ya rasa yaya zaiyi ne da wanan hukuncin da yake kokarin yakewa a ranshi.

   Allah ya gani bawai yana son yarinyar da mami ke son hadasu bane zai dai amincene don farin cikin mahaifiyar shi kawai.

   Don yadda mami dasu hjy suke nuna mai muhinmancin yin hakan gareshi saidai shi Allah ya gani bawai ya shiryawa aure a wanan shekarun nasa bane.

   Anya kuwa idan yayi gangancin yin aure a yanzu ba zai jawa kanshi matsala bane ga hakan.

     Kai ya girgiza shi kadai tare da fadin dole yai juriya da fin karfin zuciyar shi don ya samu su rabu lafiya da mahaifiyar su.

   Muryan Rufaida dake fadin ki tabbatar da kin wanke kayan nan tas wallahi kada inga jirwaye a jikin su banza kawai mun zuba ke nan dake a gidan nan.

  Ke gaki kin samu wuri zaki mike kafan ki kiji dadi ko to wanki har na tufafina duk ke zaki dinga wankin su a gidan nan daga wanan ranan.

    Nima ga nawa Nazira ta fada shegiya munafuka mumuke zamuyi maki a gidan nan ba tare da mami ta san da hakan ba ta jefo min unders din ta a fuska.

   A daidai lokacin daya karaso wurin don jin zagin da suke min din yayi yawa a lokacin.

     Yana tsaye hannun shi duka biyu zube cikin aljihun wandon shi kallon kayan yayi yayi saurin kawar da idon shi ga kayan.

    Ya dago yana kallona su kuma sai dan kame kame sukeyi suna fadin sannu da hutawa yaya J ke daga daga nan ki shige ciki ya fada yana kallona.

    Da sauri na bar wiein kayan na koma ciki dama wurin su mama kande nake zaune suka sameni suka ban wanan sikin wankin.

   Nan nabar masu kayan nasu na shige ina share hawaye babu mami a falin sai hjy dake zaune ita kadai ta kurawa tv ido tana sauraren malam daurawa dake wa,azi a tashan sunna tv.

    Na zauna take fadin yar nan akwai kura kuren da mukasha tabkawa a rayuwa sosai a baya wanda sai yanzu kake jin bayanai akan abubuwan da bamu sani ba a can baya.

    Jin tana magana ban bata amsa ba yasata dago kai tana fadin kinga kamar da can baya ai bamu sancewa ga lokacin da mutum ya dace yayi , , , , 

    Ido ta kura mi  don hawayen data ga ina sharewa a lokacin salati ta saka hankali tashe tana fadin .

   Waya tabaki me akai maki yar nan ki fada min wanda ya musguna maki yanzu don nasan ranki aka bata haka.

    Muryan mami ne ke fadin hjy lafiya wa aka batawa rai zeey lafiya me ya faru yanzun fa kika bar falin nan da raha da hjy .

   Mami ba komai ba komai kamat yaya ta fada tana kallona tana zama saman kujera takon kafab shine yana shigowa daga kofan baya yake fadin.

  Mami kiwa yaran nan iyaka da yarinyar nan abin is too much sun mayar da ita boya a gidan nan .

   Mami idan baki iya masu magana su daina don Allah ki mayar da yarinyar nan gaban iyayyenta haka cin fuskan yayi yawa.

  Ya kwashe komai da yaji yana fadawa mami rai  bace yana gama fadi ya juya ya fita hjy ma tana masa magana bai tsaya sauraren ta ba ya fita don bai cikin dasin rai a lokacin.  ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅     ABU CIKIN DUHU     🦅 2️⃣1️⃣      ZAINAB IDRIS

 MAKAWAYAR UWA FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA TARE DA IMANI A ZUKATAN MU AMIN DON ALLAH KADA KI FITAR KARKI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA KI TUNA DA AKWAI RANAN HISSABI YANA NAN TAFE.


Ki biya ki karanta a cikin salama yar uwa kan dari uku kada a tsayar dake ranan da kowa tashi ke fitar dashi sai abinda ka shuka.

    Yau tun safe Lantana da haibaici ta tashi a gidan don kawai Abban mu ya kwana a dakin innar mu kuma taga Abba ya fito ban daki da asuban farko.

  Saboda ta hana idon ta barci duk ranan da Abba ya shiga wurin innan mu haka take kwana leken tagar dakin ta don ganin halin da suke ciki.

    Wanan dalili ke sa Abba ko zai shiga dakin sai yaji wa,azi da nasiha abokan shi ko wani na kusa dashi akan yadda yake wofintar da innan mu har yan waje suka gane hakan.

    Hakan ba abin mamaki bane sanin ko wacece uwar lantana a garin dan zaman kanta takeyi tana sana,ar tuwo tuwo.

    Haka kuma take mu,amula da maza bata boye halinta har mutanen gari suka ki auren yarta data taso shine Asabe kakar mu taje ta kwasowa Abban mu ita.

    Don kswai a lokacin suna dan dasawa da mahaifiyar ta har suka hada wanan alakan cewa idan Abban mu yana son lantana yazo ya nemeta da aure ko za,a dace ta haifa mai diya maza a gidan.

   Bayan auren yanzu kuma ya fita a tsakanin su suka koma kamar annabi da kafiri tun bayan dataga ta haifi namiji din duk da dan ba lafiyayye bane yazo.

    Innan mu tana bakin murhu tana hura wuta ta fito ta zauna a kofan dakin ta tana fadi a fakace.

    Yau kuma su oo me aka samu da farar safiyan nan ake wanan duke a gaban murhu ko anyo aikene daga bariki za a sha dadi haka ?

     Inna dai yi tayi kamar bata jita ba taci gaba da fadin muna nan dai idan tayi wari maji ai .

   Gashi dama ko a gida a shedesu da dan hannu balle anje birni anga banza aita wawurowa ana kawowa gida.

    Hakan bai mata ba ta sake fadin wasu dai sunji takaici ya ko auren fari babu har ta shiga duniya yawon banza .

   Har azo anawa mutane feleke a gari a saka a canza duk da kayan zina to ai haka  ba mamaki tunda tsohuwa ma ta tsufa bata san ta tsufa ba ka  jaraba kullun ana makale da naji ana abu daya diya tayi da kaitai a birni uwa tayi nan da tsoho.

    Allah sarki dadin abun dai da tsohon sunna tsohuwar ke makale ba mazan wasu take ci ba a titi kamar macijiyar da bata ramin kanta.

  Sai dai anyi rami tayi shige ko tabi darnin makwabta ana dannan ta    ana sukawa akanta saman titi da tsufanta diyata dana makwabta suna kallo.

 Innalillahi aikuwa dama inna takan tara mata na kwanaki kafin ta gaji ta bata amsa koshi sai idan taji ta tabo zancen diyan tane zata samu mai zafi daya ta fada mata taja bakinta tayi shiru ta barta tana haushi.

  Wani lokacin har makwabta sai sun shigo rabon ta akan tayi hakkuri ta daina idan kuma sun gaji sai tayi tayi sai ta gaji zata kyale don kanta.

   Wani lokaci kuma har uwarta takan tako gidan tazo taya ta fadan suyi harsu kare babu mai tankasu.

   Yau din ma da taga haka jin amsan da inna ta bata ta yafa gyalenta ta fita zuwa fadawa uwarta abinda ke faruwa harda karya da gaskiya ta kwasa ta fadamata.

   Sai gasu tare sun dawo ita haushi uwarta haushi Allah ya taimaka inna ta gama girka dan taliyan hausa da take dafawa yara su karya dashi din Abba yace kuntu billahi baida ko kwandala a hannun shi da zasu karya.

   Amma yana fita ya shiga dakin lantana data haushi da masifan ai ta ganshi ya shiga ban daki daga yau sai ka koma ka mannewa tsohuwar matar ka tunda duk kokarin da nake maka baka gani kai.

    Halin maza sai su nan Abba ya dan fara kame kame yana rarashinta har yakai ya dauko dan kudin daya kwana dashi hannun shi ya mika mata su gaba daya don kawai ya samu ya shawo kanta kada ta gujeshi kamar yadda ta fada din.

    Shine bayan fitan shi inna ta fito tana hura wuta ta ja inna da wanan masifan har yakai inna ta mayat mata da martanin da yai mata zafi shine uwarta ta shigo da masifa.

   Tana fadin sai tayi karan innan mu don kazafi wai inna tayi mata a cewan ta jin fitinan yayi yawa yasa Asabe fitowa don da farko batayi niyar fitowa ba.

  Ji datayi tace zata kai karan inna ga hukuma yasa ta fito tana fadin ke mai tuwo baki tunanen me yarki itama ta fada mata .

  Har ta bata wanan amsa itama don haka kawai ba zata fada mata ba ai don kawai an mayar da haulatu mai hakuri a gidan tana kawar da kai ga abinda yarki jeyi mata ko yaushe.

    To tsohuwar banza kin fito ki shigar matane ko me yanzy haulatun ce mutum a wurun ki tunda yarta na can birni tana bin maza tana zuwa maku nan da abin duniya yanzu sun koma abin son ki kuma ?

    Jin haka da innan mu tayi ta bude labulen kofan ta tana fadin saukin abindai kafin ta fara aikatau wasu sun tafi butnin sunyi har saudiya yin dandin kasa mai tsarki basu dawo da komai ba kasan nan sai tsaraban shegu.

   Idan kuma suna da uba yau a fito muna da uban su mu gani don haka kafin yata taje birni bin maza tsohuwar banza ta fara zuwa ta dawo muna garin nan da tsaraban annoba.

   Yau zaki san kin tabani garin nan yau zan nuna maki ko wacece ni a garin nan inna tace idan kin tashi kisa a rufeni dan makullin ya bace iyaka ke nan.

    Lokacin har yara da mata da muke makwabtaka dasu sun cika gidan suna kallo da saurare.

    In dai barikin ne ai iyawace don karshe sai an koro yar taki da ciki kowa ya gani a garin nan  lantana ta fada cikin jin kunya da nauyin yaran dake ihu bayan fitar uwarta don halin su ya ishe mutanen unguwa dama.

   Har wurin aikin Abban mu lantana da uwarta suka sameshi suna fadin  sai sunyi karan innar mu don tayi masu kazafi da cin mutuncin da ba a taba masu shiba yau.

  Abba ya shiga ba mahaifiyar lantana hakkuri yana fadin ta barshi da inna dama halin innan mu yakai mashi ko ina a gidan.

   Haka dai Abba ya samu ya lalaba su suka bar gidan bai dade ba shima a waje sai gashi ya shigo yana kwalawa inna dake bandaki kira .

  Bata amsa ba saida ta fito ta bayan shi take fadin gata ai tana sauraren shi.

    Ke don baki da mutunci yanzu har kika iya bude baki kika zagi uwar lantana a gaban ta karya suka fada wayasan inda yar taki take a birni dama.

   Allah sarki hakane dama ai na sani kaima yaran ba damuwan ka sukayi ba ai tunda tun lokacin daka mikata wurin yar uwarka har yau baka taba bin bayanta kaga inda take zaune ba don an hanaka zuwa gani don a samu abun fada min.

   To bari kaji malam idan ku dakai da uwar matan naka bakuyi karana ba yau ni zanyi naka a garin nan duk inda kakai min ya sai ka fito min da ita don wanan abin ya isheni.

   Ni ga Allah na dogara nasan irin tarbiyan dana ba diyana don bata gaji shashanci ba a gurina balle taje tayi shashanci a birni.

    Yanasu yau ke da bakin kike fadin zakiyi karana kan yar cikina a  mata ya baci inna tace kwarai kuwa bello ta fadi sunan Abba ba sakaye kamar yadda take kiranshi da malam.

   Mamaki ya kara kashe abba jin abindata fada sunan shi gatsau haka babu sakaye data sabayi mai don gabadaya ta birkice masu a gidan.

   Wani kalon kalo suka watsawa juna kafin Abba ya kuta yana fita daga gidan inda lanta taji haushi cikin daga murya take fadin tunda har kika zageni dani da iyayyena ke kuwa sai yar taki tayo abin kunya birni an korota ta dawo maki maga ta tsiya.

    

    Nikan unda na shige daki nabar mami na fada a falo ban fito ba sai bayan sallah isha,i koshi din abinci na fito.

   A falo gaba dayan su suke in ka debe mazan da basu rigada sun shigo gidan bako a lokacin don ko hjy a falon tayi sallah bata shigo dakin tayi ba nasan saboda tafiyan ne yasa ta zauna a nan bata dawo dakin tayi sallah ba.

    Banda hara ba abindaya shiga tsakanina dasu Rufaida duk da na gashesu a cikin jam,i saidai su basu  amsa min ba.

    Sai hjy ce ke fadin yarnan yanzu nake zancen ki a raina ina batun aje a dubo min ke a daki ko lafiya kika shige har wanan lokacin ?

  Ina zancen dai ai ya wuce tunda kinji uwar ku ta tsawata kan hakan suma kina ganin su da shegen son jiki suke ta yaya zaki dauki kayan kasan ki har kiba wata wanki can.

   Haba haba hjy a daina wanan zancen tunda mami tayi mana fada a kanshi dazu ba wanda zai kara bata irin wanan aikin acikkn mu ai tunda mami ta hana abata Aisha ke fadi.

    To uwata hanani in fadi tunda kun shuka rashin gaskiya wa yarinya baku son a fada kuma kai kuma dai kazamai ne wallahi.

   Ta fada rai a bace tana mai kawar da kanta ga kallon su sukai tsuru tsuru don mami na falon itama ta kafesu da idanu.

   Rufaida na shirin mikewa tabar falon don takai kololuwar cika tana batsewa wai akan yar aiki mami tana wullakantasu don kawai taga gidanta ne yanzu dan uwan mahaifin su ya rasu yasa ake masu hakan.

   Batakai ga tashi ba taji sallaman jalal yana washe baki ya shigo da ledoji niki niki a hannayen shi yakai gaban mami ya aje lodojin yana zama a kujera tare da fadin.

   Wassh Allah yau na gaji da yawa mami tace da kai me ke nan fa mami tunda aka fito daga sallah yaya jack , , , , 

   Bai karasa fadi ba saboda hararan da mami ta watsa mai yasan me take hararan shi dashi yace a wani yanayi i am sorry mami na mantane kin hana mu kirasa hakan ni kuma bakina ya saba da hakan tun a can.

    Rufamin baki ku kun fada inagana waje jalal ka fita min a ido duk kuka bari wanan sunan ya shigo kasan nan raku saiya baci sosai.

    Yana dariya yace yanzu dai mami ba wanan ba kinga ledan nan wai duk na tsohuwar nan ne yaya ya ban kudi a hado mata wai kada taci abinci da dare sai wanan din shi ya dauka nan irin can ne da tsofi sukecin wanan dadin yana magana yana zamowa daga saman kujeran yana kokarin budan ledan.

   Wanan ya hana rufaida dake cika tana batsewa tashi don tun shigowan shi falon ya dume da kamahin suya irin na yan gayu ba suya na gida ba wanda yasha kayan hadin sanadarin zamani.

   Hannun shi mami ta buge ya jaye yana fadin wassh Allah mami zan bude ku gani ne ai ko ya fada yana dariya.

  Mikawa hjy abinta babu maici a cikin ku wurin sai idan ta gama ta baku ragowa idan zaku ci.

    Haba mami ta bamu ragowan ta kuma bayan ta gama zuba mai miyau da goro zamuci salma ta fada tana kallon mami din.

    Hjy da sai yanzu ta fahinci me ake nufi lokacin da mami ke kallon jalal tana fadin ya mikamata take fadin au me muka samu ne wai.

   Bakiji bane hjy wai Jafar ne yasa a sayo maki wanan shine syke son su saka maki rani a ciki don suna yan kwadai.

    Ja,irin miskili ya gama babautan nasa yana neman shiri danine kuma yanzu dazun fa ya gama fadin me na biyo ku yi nan nazo in sakawa mutane nauyina sai gashi shiya fara daukan nauyin kuma ?

    Haka kika fada ko bari ya dawo saina fada mai wai badan Allah ya saya maki ba neman shiri dake yake ya sayo maki.

   Kaji ja,ira zaki hadani fada da wanan mai kama da yan ruwa yazo ya hanani shanruwa a gidan nan ke nan.

     Ya jalal yaga sun tsaya surutu mami bata sab sanda ya jawo ledan ba yana fadin bari nidai na bude don inyai sanyi bana iya cinsa kuma.

     Yana bude ledan farko wani kanshi ne duk ya game wurin leda daya ya tura a gaban yan mata yana fadin ku ku dau wanan wanan kuma hjy wanan nasu ne idan sun shigo.

   Ya mike ya isa gaban tsohuwar tare da ledojin a hannun shi yana fadin hjy mu muci wanan ko tace kaidawa ke nan miko min nan dagani sai yar nan da take dawainiya dani zancisa.

   Kaji hjy kuma ya wuce ki bata fifike ne a ciki kilama bata taba cin suya irin wanan ba ai Nazira ta fada a daidai lokacin da suke shigowa gidan shida Jamal.

   Yau kan ya wanke kanshi a wurin tsohuwar da murna da lale marhabin ta tare shi tana fadin kaga mijin arziki wanda yasan zafin iyalin shi.

   Mami na masu dariya yazo gaban mami ya dan dukar da kanshi wanda kamar hakan al,adan yayan mami ne don har ya mamud haka yake mata da girman sa in zai fita ko ya shigo zai duka mami ta ahafa kansu tana saka masu albarka tare da fatan alheri a garesu.

   Don tun ina mamakin hakan har nagaji don na saba da ganin hakan wurin yayan gidan maza ko Aisha da take mace kamar zata koma cikin uwar wani lokaci idan abin ya motsa mata ko yanzu tana zaune tunda tai magana da farko bata kara magana ba a wurin kowan su nakan waya suna abu daya charting ko dawa soke yi oho ?

   My friend an dawo ke nan mami ta fada tana shafa kanshi tare da fadin ubangiji yayi maku albarka ya kare mun ku a duk inda kuka saka kafanku.

    Tashi yayi ya nufi wurin hjy ya zauna a kasan carpet tare da riko hannun da ta dauki cinyar kaza tana ci yakai a bakin shi ya gutsura kadan kafin ya kai mata itama a bakinta .

   Ni dai ina gefe zaune a kasa daga gefen hjyn ina kallon ikon Allah tare da mamin wai yan gidan mami suke kwadayin nama haka ?

   Wanda nama sai an mayar da saura kitchen don sunci ya ishesu wanan wani irin nama ne hakan don idan kaga mami ta sayo nama a waje to kilishi ne zata shigo dashi mai yawa kowa yaci har a ture saura su mama kande su dauka..

     Dan albarka hjy ta fada tana hadiyan naman dayasa mata a bakinta ta gutsura kowa falon na busy suna cin naman suke gaidashi dashi.

    Dabi,an shine kyaluwa dan haka yi yayi kamar baiji su ba hjy ta juyo tana fadin taso mana yar nan ki diba kinyi zaune kina kallon kowa nacin abin arziki.

    Saiya dan juyo ya kalleni guri da nake zaune din ya kawar da kanshi kamar ba kowa a wurin .

   Na mike nazo gaban hjy din yana zaune har lokacin yayi rigingine a wurin kafanta idon shi a carpet nakai hannu zan diba Nazira tace

  Ke dakata don Allah menene haka zaki saka mata wanan hannun naki mai dauda a cikin abu haka kai tsaye ba tare da kin wanke hannu ba.

    Cak na tsaya daga daukan naman da nasoyi din ina kokarin mikewa a inda nake gurfane don barin wurin.

    Ke diba ki wuce ya fada batare daya dago kai ya kalli kowa a wurun ba ya fadi hakan sai jamal yake fadin haba Nazira ku daina irin hakan don Allah dai.

 Bazasu bari ba don da zasu bari ko ance suyi wani abu kan yarinyar nan ai basuyi ba kuma yadda nayi masu yau.

   Me ake mata idan ba iya yinta ba taga yan aiki a wurin nan ne ko taga su kande na zama a cikin mune haka su ?

   Nazira zan saba maki a gidan nan fiye da tsamanin ki to bari kiji zeey da kike gani daya kuke da ita a gidan nan yadda na daukeku dasu Aisha haka itama nake daukanta don ba wai aikin kudi aka kawota yiba yadda kuke tsammani.

  Rokota nayi gurin iyayyen ta suka taimaka min suka ban ita a cikin mutunci sau nawa wai kuke son in fada maku hakane wai ?

    Look akan yarinyar nan zan sabawa yarinya a cikin gidan nan ko wacece me yarinyar nan ta tsare makune wai haka kuke sakata a gaba ko yaushe ya fada a hasale cikin daga muryan shi dasai ranshi ya baci akejin shi irin hakan.

   May be don sunga ta fisu kyaune da tsari suke kyashin ta jalal sarkin barkwanci ya fada kai tsaye yana masu dariyan kyaita.

    Kai amma jalal din din don Allah kada tasa taji dadi har taji dadin raina mutane a gidan nan ta dauka wani kyaune da ita.

    Garin dauko naman saboda rawan da jikina keyi na dauko gefen fifiken kazan dayasha carbej da albasa dasu maggi curry da sauran hadi namike tsohuwar na fadin baki dauki abin kwarai ba nace wanan yayi min yanzu naci abinci na bar falon ga baki daya har lokacin jamal da jalal suna cacakan ya  matan a kaina.

    Jalal ke fadin wanan kina ganita idan tayi clean gidan nan ma baya daukanta ke zeey fa idan ta waye ba karamar classic lady bace wurin nan.

    Dakin na shiga na aje naman don naji ya fita min a rai don disganin da  nazira tayi wurin daukan naman a gaban kowa.

    Nima fa mutum ce kamar kowa da suke min haka don kawai ina yar kauye kuma diyar tallaka tallakama mai faci.

     Ina ban daki nake wanan fadan a raina na fito ban tsaya jiran komai ba na hau kujera na kwanta har barci ya daukeni ban sani ba don ban san lokacin da hjy ta shigo dakin ba bayan sun gama hiran su a falon don ko hidimar da nakewa mami ranan ban samu yimata shi ba.

   Koda mami ta rako hjy dakin ta samu ina barci bata tayar dani ba ta kyaleni hakana sai cikin dare dana falkone naga wutan dakin a kashe.

    Washe gari da safema motsin hjy ce ya falkar dani na tashi nima nayi sallah na idar na zauna a wurin hjy ta shafa tana fadin in koma in kwanta tunda ido akwai barci daga haka taci gaba dajan tasbahan ta.

    A daidai lokacin da nake shiga na gyarawa mami dakina falka kamar an tasheni har lokacin tsohuwar tana zaune a inda take.

    Mikewa nayi ba tare danayi magana ba na nufi dakin mami din ko a nan ma itama zaune take tana azzakar din safiya.

    Ban fito daga dakin ba saidana karasa komai na dawo na samu hjy ta dan kwanta a lokacin banyi dogon motsi ba wanka nayi tare da kara wanke ban dakin har na shirya a hankali duk tsohuwar tana barcin safe wanda nasan na gajiyane.

    Sai bayan goma da rabi ta falka lokacin mami tayi mayawa a dakin yakai sau uku tana duba mahaifiyar nata.

    Ruwan wanka na hada mata tayi wanka na taimaka mata data fito har ta shirya saiga abin karyawa an kawo mata har daki yaran gidan suna shigowa daya bayan daya suna gaida ita da kwana.

    Har suka dauke kafansu sai Aishace bata shigoba nasan bata tashi bane don ita sai wuraren sha biyun rana dama take tashi barcin safe ko ma zuwa dayan rana.

    Nan muka zauna muna hira da hjy don ban yarda na fita ba ko karyawa a cikin na tsohuwar na karya dashi take tambayana ni yar wani garine ?

  Nace ancau hjy tace ashema yar jaharnan ce ke na dauka ko yar shiyan jalingone ke ko bauchin don na ganki da zubin fulani.

    Nace innatace dai bafullata Abban kuma bazzagene shi  yar nan da asalin ki haka har yaran nan suke maki wanan tsiyar haka ?  ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅   ABU CIKIN DUHU   🦅


  2️⃣2️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


  FATAN ALHERI GAREKU MASOYA UBANGIJI YA DAUKAKA MUSULUNCI A DUNIYA AMIN, , , , 


Banyi zaton akwai macen da zata kai sha shidda a yanzu ba wace bata san zata mutu ta koma wurin ubangijin ta ba da har za a hada da Allah da annabi ta rufe kunne da ido don rashin tunawa da Allah dayai mata rai da numfashi da take takama dashi a duniya wanda ubangiji zai iya karban abinsa duk sanda yaso .

   Yan uwa mu kulla da daraja da nauyin wanan sunan biyu idan ance Allah da annabi a zatona angama da musulmi ashe abin ba haka yake ba a wurin wasu.

    Allah kasa mufi karfin zukatan mu ya Allah ka bamu cikawa da imani amin kada ki karanta idan baki biya ba mai turawa na barki ga Allah shi yasan tsakanin mu dake.

    Sallama akayi daga kofan dakin yayin da mu kuma dariya ya dauke muna hankali a cikin dakin don tsohuwar dariyan labarina dana fara batane ina fadin garin mu ai kauyene kuma yan garin muma kauyawane a cikin sa don kaka hajiya bata kaiki tsufa ba amma bata wanka daga jumma, a sai jumma, a take wanka tunda wai bata da miji da zataiwa wanka.

   Sallama ya kara yi nice na karba a cikin raha da walwala don dan zaman mu da tsohuwar yasa na mance da duk wani bacin rai dana kwana dashi a gidan.

    Dan miko min wanan kawar da wanan gurin nan sai duba can ki miko min abu kaza dauki wanan kici hakan yasa na manta da komai dake a raina a lokacin.

  Wa,alaikum sallam na fada don hjy ita dariya yaci karfin ta a lokacin itama dai cikin dariyan take amsa mai haka yasa ya turo kofan gaba daya ya shigo.

   Saye yake a cikin farar jallabiya mai laushi sai wani maiko takeyi ashe jallabiyar ma suna suka tara sabanin da danake masu bugu daya don duk jallabiya da farko daya nake daukan su sai zuwa gidan mami ne na fara bambanta jallabiya yanzu.

    Yakaraso yana tako kamar wani balarabe dashi har zuwa kujaran da hjy take zaune sama a cikin hausan shi mai kama dana dan koyon hausa din.

    Yana fadin wanan dariya haka hjy kamar an gafarta maki yau fa don nidai badon nasan iyayyen su ba sai ince su din jinin labawan asaline .

    Don hasken jikin su yafi kama dana larabawa a gidan ga tsayi duk dadai shi yaya jafar din ya fisu tsayi sosai a cikin su sai jamal da jalal saidai basu kaishi tsayi ba su zan iya cewa su din kamar mahaifin su suka kwaso don ko ban sanshi a fili ba na san shi a manyan photunan shi dake falon gidan.

  Don shi mutum ne fari dogo ga tsayi ga kyau kamar shi yayi kansa wurin halitta duk da ya manyata a photunan lokacin dayayi su hakan bai hana kyau shi fita ba a fili.

   Hakan yasa nake kasa bambanta tsakanin su da dan nasa ko a cikin su wayafi kyau haka.

   Shi yaya mamud duk da farine sol baikai yan uwanshi tsayi ba yana dai da nasa gwargwado sai Aisha da ta biyo mami sak wurin kama.

    Don ba inda ta rage mahaifiyar tasu sai dai idan halin mahaifin su ne ta kwaso na rashin hayaniya dason motsa jiki don mami kan ita da alama ba mai yawan son jikibane ita don wani lokaci zan samu tanayin abu da kanta sai nazo in karbe ta.

   A cikin dariya hjy ke labarta mashi hiran mu tana kwasan dariya fuska a daure ya dan dago ya kalleni tare da kawar da kanshi duk lokaci guda.

   Ina tsugune nake gaidashi da kwana tare da mikewa don barin dakin duk da ina tunane a raina ina zan dosa idan na fita don gudun haduwa da yan matsalan gidan mami din yan kafi mai abu iko.

   Don ni sai daga bayane ma nasan ba mami ta haifesu ba a wurin anty Aisha yadda nazo gidan na samu sunayin abu a gadarance da yadda mami ke nuna kamar itace ta haifi abinta.

    Ina kuma zaki muna hiran mu kin dauko ban labari ina sauraren ki indon wanan ne ai shi nasan yanzu fita zaiyi a dakin don ba zama zaiyi ba ko kunya fada a gaban shi kikeyi.

   Dawo ki zauna muyi hiran mu kinji jikata ta kaina aini kin ganni nan ina son jin irin labarin nan sosai wallahi don nima kinga daga karkara na fito ai.

    Idon shi a waya kamar mayen waya ko computer dana sa mai yake fadin wani No kuyi hiran ku ni nawa nakeyi nan .

     Tace dada Asabe kowa kikace sunan ta nace a sanyayye don kasancewan shi wurin nake fadin Asabe ne.

   Ta nuna min bakin gado tana fadin zauna mana a tsaye zamuyi hiran haka na kai zaune a dan takure.

   Yanzu mahaifiyar ki dai tana tare da Abban ki ko ta tambaya take yanayi na yacanza a hankali nace suna tare da Abbanmu har yanzu.

  Saidai ba a cikin dadin raiba don Asabe tasa Abban mu yai wani auren wai don innan mu diya mata take haihuwa ita kuma bataga amfanin diya mace ba.

  Shima dalilin turoni birni wurin mami da Asabe da lantana sukayi wai nazo inyi aikatau a nan don hakane kawai za a morewa diya mace na karasa ina share hawaye.

   Kai ya dago ya kalleni a cikin mamakin jin abindana fada din na zancen Asabe ga innan mu da muka bude ido dashi a gidan kullun sai tayiwa inna gorin shi.

   Haba haba yar nan kada ki kuka mana nasan  wanan zancen yana da ciwo sosai don baku ai kukayo kanku diya matan ba wasu ma nacan suna son diya matan kamar suyi hauka basu samu ba ita tasan baiwan da Allah yai maku dayayo ku diya mata a garesu.

   Abin mamaki sai naji ya saka muna baki a hiran mu yana tambayana ku nawane a wurin mahaifiyar ku da har take fadin hakan ?

    Mu bakwai ne nice babba a dakin mu sai kanne guda shidda dana bari tare da innar mu a gida.

    Babu ma wanda aka wanke a cikin ku ke nan tunda kece babba ashe kai wasu mutane da shishigin tsiya suke har da Allah sukewa izzigili.

   Shi mahaifin ki fa yaya ya tambaya sai na dago na kalleshi don ban fahinci mai tambayan shi ke nufi ba.

   Saidai na basu amsa da fadin yana nan kawai yace No ina nufin wani mataki ya dauka kan wanan zance 

   Da Abba baya daukan zancen Asabe amma yanzu tunda ya auro lanta kuma ta haifi na miji sai ya sauyawa innar mu damu ga baki daya a gida yanzu ba ruwan Abba damu kamar da can baya na fada idanuwana suna kawo ruwan da ban iya controling din su a lokacin.

    Haba yar nan ki daina kuka kada nima ki sakani kukan don wanan labari naki akwaicin zuciya gaskiya.

   Do me bataga laifin danta ba dashi yake ba uwarki diya matan sai uwarku kadai zataga laifin su ta fada a hasale.

   Muryan mami ne data dawo take kwala min kira daga waje yasa na mike tsab na fita dakin da sauri na barsu a zaune da hjy.

  Duban hjy yayi yana fadin hjy ashe har yanzu akwai itin mutanen nan masu halin dabba a kasan nan yadda yanzu addini ya zagaye kasan nan.

   Yo jafari mai za a fasa a wurin kishin muna mata wasu matan fa kishi suke da matan diyan su kila irin hakane ya ke faruwa a gidan har wanan tsana ya shiga.

  Amma idan bashi ba menene laifin haihuwan diya mace a duniyan nan ni ba gani ba kai bani kadai ba har kowa ai yanzu moriyan diya mace mukeci kaf zuriam mu ga baki daya.

  Don uwarkuce tsaye da gidan ni kaina da kaganni nan na fuskanci itin wanan matsalan lokacin dana jera haihuwan iyayyen ku mata har su hudu a lokaci guda ban haifi namiji ba.

  Sai dai ni kishiyace ta goranta min hakan bawai  uwar miji ko wani irun wanan zancen yana da shiga zuciyar bawa don yanzu Allah kadai yasan halin da uwar yarinyar nan take cikin dan bakin ciki kan tana ganin sa.

    Amma idan tayi hakkuri wataran sai labari yau ba gani danayi hakkuri na shanye hakan ba uwarku sai Allah ya daukaka muna ita ta zama muna zakara a cikin mazan.

    Yau zeey mami ta fada ki dauki wanan kikai dakin ku na hjy ne ki kula da bata tana ci lokaci lokaci kinji.

  Nace to mami ina daukan ledan da ban san ko na meye ba a cikin sa har na juya zan tafi take fadin zeey na juyo da na,am mami sai kuma ta kasa fadin abinda zata fada tana kallon fuskana da mamaki ta furta.

   Zeey kinyi kuka ko zancen jiyane har yanzu a ranki ko kuma wani ya kara tabaki gidan nan yanzu kuma ?

   Kai na girgiza da sauri alaman a, a tace to me akai maki fuskan a haka ko gida kika fara tunane kuma.

   Nace a a a sanyayye ina juyawa sai ta bini da kallo mikewa itama tayi ta biyoni baya ban san mami na bayana ba sai dana shiga dakin da sallama naji mami na fadin a a ashe kana nan tare da hjy ne yanzu fa nake shirin zeey ta kira min kai a waje na kira layin ka bakai picking ba.

   Yacs OK mami nabar wancan wayan daki da zan fito ai nazo gaida grany ce da kwana sai kuma na zauna muna hira.

    Wanan yarinyar na gani kamar tayi kuka ai shine na biyota in tambayeta ko wani abin kuma akai mata na ganta haka ?

    Ba wanda ya tabata tun safe muna dakin nan tare da ita nasan kukan da tayine kan labarin yan gidan su da take bani yanzu.

   Ta labarta maki jahilcin kakarta ke nan ko don shine damuwan ta a zuciya kullun Asabe ta tsani mahaifiyar su don kawai ta haifesu a diya mata.

  Shine fa yanzun nake mata musali dake kika kirata irin wanan mata da yawa suna haduwa dashi a rayuwan su in Allah ya hadasu zama da mace mara imani ga ubangiji har ma a cikin masu ilimin akwaisu sosai har gobe . 

    Na fada mata ta kwantar da hankalinta muddin ina raye a duniyan nan sai tayi ilimin data tallafi gidan su insha Allah .

   Asabe zata gane diya mata ma mutane ne kamar kowa ba abin wullakantawa bane a gida.

   Mikawa hjy ledan dake hannuna nayi ina fadin mami ne tace in shigo maki dashi nan nakine na fada ina ajewa gaban hjyn nata a cikin ladabi.

     Me muka samu kuma nan ta fada tana kokatin budan ledan dake gaban ta lokaci daya ba komai bane sai goron ki da sauran tarkace dazaku bukata a nan dana san kina amfani dashi mami ta fada.

   Mami goro kuma ya kamata ace ta bar cin goron nan a yanzu fa don jikin tsufa daya kamata zai iya mata illa wanan goron haka.

    Ungo naka da zai mun illa da tuni yayi min tun kan a haifeka nake cin goro na a duniyan nan gani ko garau kana ganina.

    Allah baki hakkuri ya fada tare da mikewa tsaye yana gyara rigar shi hjy tace tafiya zakayi kuma muna zaune muna hiran mu ?

    Na gama hiran ai ku karasa hiran ku damani ai ba dani aka fara ba ya fada yana ficewa tace miskili kafi gaban gayya wanan wanan zan so naga macen da zata iya zama dashi haka.

  Mutum kuna zaune kalau ya birkice maka lokaci guda kuma ya hana ayi magana don tsaban miskilanci.

   Fita yayi daga dakin ba tare daya kara mata magana mami na gefe tana murmushi mama kande ne ta shigo dakin da sallamanta muka amsa take.

   Fadin mama ga abinci an gama na kawo maki da cewa hjy tana fadin sannu sanu yarnan sannu da kokari har kun kare na rana ban dade da cin na safeba ai.

    Ai kande akwai kokari shiyasa nake son daukesu mu koma Abuja don gwarawan nan sun isheni basu iya irin cimar muba nan sai kalar tasu abincin.

  Saidai kuma ina tunanen wanda zan bar yaran nan dasu a gidan nan don baka barin ya mace ita kadai a gida.

    Yo da kin fada tun bamu taso ba ai da anyiwa ladidi magana me take a gidan banda yawon bin makwata sai tazo ko ta zauna dasu nan kinga an rage mata ma wahala ai.

   Mami tace indai ya ladidin zata yarda hjy ai mata magana kafin mu wuce in sani don in tura su kande gida suyi sallama da mutanen su asan zasu tafi.

    Zan kira yayan ku in sheda mashi yai mata magana aji me zatace wanan ai ragewa ladidi nauyi ne babba.

    Kande ko baku zuwa mu koma Abuja mami ta tambaya sai kande din tace yo hjy ko ina kikace mu tafi aini mai bin umurnin ki ne.

  Yafi mun zama nan da yaran nan naki da basa jin magana na gara dai ina kusa dake yafi dadi ta fita tana murna tare da fatan Allah yasa a tafi da su din.

   Lokacin sallah yayi mami ta bar dakin aka barmu dagani sai hjy sai bayan mun idar ne muka zauna cin abincin rana lokacin ne kuma anty Aisha ta shigo gaida hjy da kwana.

  Tana wani daure fuska don tasan hjy zatai mata tsiya nan dai sukaita barkwancin su kafin Aishan ta juyo tana fadin .

    Zainab yanzu ba a ganin ki tunda hjy tazo na hadiye abincin dana saka a bakina ina fadin dazun na lekaki har sau biyu in gyara maki daki kina barci.

    To ai yanzu na tashi ta fada nace bari gama naje na gyara maki sai hjy tace ke arr ke kan anyi malalaciyar yarinya a nan sam baki biyo halin uwarki ba ke kan.

   Don Allah hjy ki rufa min asiri kafa mami ta shigo ta sakani gaba banda abinki don kawai ta gyara min daki shine wani abu.

    Yanzu ke haka za a kaiki aure ko gyaran daki baki iya ba kina haka tace wai hjy wa ya fada maki ban iya ba kawai dai ban samun lokacin hakane a tare dani.

   Haka rayuwan ke gudana yanzu zan iya cewa na samu sauki sosai iyakata in shiga dakin mami in gyara sai na anty Aisha sai bayan kwana biyu kuma a ce in gyarawa yaya dakin shi yayi datti.

   Su Rufaida iyaka ta dasu gaisuwa in suga dama su amsa in basuga dama ba su kyaleni sai ko idan na gilma idan ba mami kusa su sakar min magana mai zafi sai dai kawai in hadiye ban fadawa kowa kamar yadda mami tace in fada mata idan sun min wani abu.

   Ya safiya ma zuwanta biyu da muka zo tana wuni gidan a karshe kuma su kwasa da mami su fita don tunda mukazo da wuya mami ta zauna a gida.

   A bakin Aisha nake jin wai kafn mu tafi za a karrama mami nan jahar ta ita da wasu manyan jahar da suka samu mukamai shine dalilin ma da zamu kara sati daya nan gaba.

   Nikan naga sai manyan mutane ke shigowa suna fita gidan maza da mata suna ganawa da mami wani lokaci da yaya mamud don kome mami zatayi shine gaba wuri aiwatarwa a gidan sai dai shi baida daure fuska iri sauran fuskan shi a sake yake ko yaushe gayin ba,a da raha.

  Sai ince wanan shirin dinner kamar yafi wanda aka hada masu a abuja haduwa don irin shirin da naga anayi da kudin da ake fitarwa.

    Don kawai wana shagalin da za ai mata ake wanan barnar da kudin nake fadi a raina sai ga hjy itama tana fada kan hakan.

   Andace rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya har gashi ana gobe buki sai faman tanadar abinda zasu saka babba da yaro sukeyi a gidan.

   Ina kallo sai kiyasta abubuwa nake a raina idan naji suna ihun da shewa yasu yasun a falin har anty Aisha da yanzu kan wanan abin takan dan zauna tare dasu wani lokaci.

  Da farko hakan bai damuna abu ga mace kuma mai karancin shekaru irina a lokacin don haka na saka damuwa har na gaji na bakaina lafiya danayi wani tunanen cewa kilama badani za a tafi wurin dinner din ba kamar wancan na Abuja da yaya ya taimaka min ya tafi dani naga shagali kuma na samo abin bukin da har yau nake boyon su in kaiwa innar mu a gida idan zan tafi.

  Muna daki da hjy ta gama cewa in bata ledan goro taci na dauko mata na zauna ya shigo dakin suka fara gaisawa ni dai banyi gigin gaidashi ba don ko na gaidashi din ba amsawa yakeyi ba.

     Bai dade da zama ba sai ga Aisha dakin tana fadin hjy ni zan fita zuwa gyaran kai hjy tace shi jan ma har sai anje gun gyaran shi kamar wata kafira can dake ina dai irin gyaran kafirai din nan kike nufin zuwa.

  Kaji hjy kuma da wani zance bros ni zan tafi daga inda nake bansan lokacin danace anty Aisha nima zan tafi.

    Hjy ta jiyo inda nake tana fadin kema zaki tafi ai maki wanan banzan gyaran kanbna zamani yar nan a cikin mamaki take magana .

    Ballema ina zan tafi dake haka zainab don me ba zaki da ita ba ya fada fuska daure karbi nan kuje ai mata itama.

    Hjy tace balle yau daine da tayi sha,awan wanan abin ai, ina nan kuke ta sha,anin ku iyakarta ido ko dinkin nan bata samu albarkan ai mata shi ba gidan nan ina kallon hankalin iyami duk da aiyuka sun mata yawa.

   Har dai muka fita daga dakin bayan ya cikawa Aisha hannu da kudi masu yawa da suka sani mamaki a cikin raina.

   Aisha tayi mamaki kwarai lokacin da aka bude kaina da kullun yana cikin katon hulan da nake dunkule gashina a cikin sa ko kafi aula dubara baka taba ganin gashin kaina a gidan mami.

  Don haka ba wanda yasan wanan sirin dana barwa kaina sani ni kadai ba a gidan mami ba kwai ko a garin mu inna tace kan dunkula min a daki da dare.

    Aisha na kallon ikon Allah wayan ta yayi kara ta dauka ta kara a kunnen ta ni sai naji tana fadin to yaya daga nan din zamu wuce can insha Allah.

   Ashe ya Jafar ne ya kira ta ya umurce ta kaini wurun sayar da kaya a zaba min don hjy ta fada mashi ba a samu yu min dinkin fitar bukin bani don mami bata zauna ya kara da fasin kin san kuma tunda hjy ta fadi dole ayi basai mami ta sani ba tunda aiyuka sunyi mata yawa ranakun nan .

  Muna gamawa driver na waje na jiran mu don bata jan mota ita saboda mami bata yarda da hakan ba wai bata gama sanin garin ba.

   Ina mamaki idan ta dauko kayan yadda take gwadawa a jikinta kafin ta gwada a nawa jikin kayane masu kyau kala biyar babu na yarwa a cikin su.

   Ina kallo ta biya bayan ta hada da jakka da takalmi ko wani kayan muka dauki hanyan gida mami ko sai kira takeyi wai mun dade a waje ga hjy na fadan haka kuma.

   Dakin ta muka shiga da komai da muka sayo na wuce zuwa dakin mu ina shiga hjy fada sosai ta hau ni dashi wai na biyewa Aisha munyi dare a waje.

   Kala bance ba don ba dabi,a na bane babba na magana ina bashi amsa lokacin sai bayan mun idar da sallah magariba har isha i  har lokacin na kasa sakin jiki a dakin har hjy ta kare abinda takeyi ta juyo inda nake tana fadin

  Yi hakkuri yar nan kin san garin kaduna ba kamar sauran garuruwa bane girma ga kuma yan daukan amarya a sasssan shi.

   Shine yasa kukaga hankali bai kwanta ba don Allah ku daina fita kukai yamma garin nan.

  Hjy kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zamu karan hakan ba tace ya wuce a cikin wani sauti dake nuna bacin ranta har lokacin.

  Ni dai nayi shiru gefe daya nasha jinin jikina nasan tunda hjy ta hasala haka damu na mami sai yafi nata zafi.

  Aikuwa  ban gama tunane ba mami ta shigo dakin fada sosai mami tayi min a dakin kafin ta juya ta fita .

  Duk sai naji ba dadi a raina duk da nasan ba nice mai laifin ba amma kuma anga laifina a hakan ko sun mata da ni yar rakiyace kawai.

    Sai washe gari na samu hjy ta dan sake mun fuska muka koma daidai a dakin da ita har tana jana da hira tana fadin wanan gyaran kan danayi ya kara fitar min da suran fuskana a fili.

   Yar nan ashe haka kike da kyau kike munanta kanki baki gyara don Allah ki rika gyara kanki kina kwalliya kina fitar da suran ki waje.

    Ni dai sai dan murmushi nakeyi ina jin dadin yadda tsohuwar ke yabani koba komai dai na samu wace ta nuna min kauna nima kamar kowa.

    Hankalin kowa ya dauke gaba daya a gidan ma kuma cike yake da mutane don haka na makale daki tare da hjy sai jefi nake zuwa in leka dakin mami indanyi wani abin.

   Karfe bakwai kamar kowa jira yake yayi don dai shiga wanka akeyi ana shiryawa saiga anty Aisha ta shigo tana fadin   ke zainab na manta da kayan nan ai da sauri na dago ina kallon kayan da take magana akai.

   Kayan jiyane dana rakata ta sayo take miko min da sauri na karba ina fadin Anty nikika sayawa dama ?

    No bani ba ya J ne ya bada kudi a saya maki jiya bayan fitar mu ai mantawa nayi na baki tun jiya wanan tsohuwar tasa mami na muna fada kawai kamar yara kanana ne mu.

   Nikan banbi ta nasu ba hankalina yana gurin kayan duk na rikice don murna har ta gama ta fita ba,a jima ba ta aiko kirana nazo.

   Da sauri na mike nabar hjy da muke kallon kayan a dakin mu tare na nufi dakin Aisha watace ke mata kwalliy a fuska ina shiga taks ce min zauna a gyara maki fuska ba tare data dubo in danake ba.

   Wurin na samu na zauna saiga mami ta leko tana fadin kin san fa tare dake zan fita ki shirya ku fito mu tafi haka yasa akaiwa anty Aisha a gurguje ta shirya ta fita ta barni a dakin da mai kwalliyan.

  Ina mamain yadda mai kwalliyan ta zauna ta shiryani kafin in fito gidan har ya koma shiru duk an watse zuwa wurin buki.

   Raina naji ya baci ina raya ni yanzu wa zanbi kuma tunda wayanda na sani sun wuce sun barni a gida ba tare da kowa ya kulani ba.

   Rigar da mai kwalliyan ta shirya ni aciki nake faman tatarawa don kada in fadi kasa don yayi min dan tsawo saidai tace dana saka takalma zai zauna daidai a jikina .

  Har tafiyan da zanyi da yadda zan rike jakka ta nuna min ni dai sai dariya take bami a raina ina fadin wa zai tsaya kallona a wurin 

balle yaga tafiyana.

  Takon takalma da kamshin shi ya dawo da hankalin mu surin da muke jiyo takon ya fito naji matar na fadin sir mun gama you can go now.

   Thank you yace da ita nikan na nufi dakin mu tunda naji sun fara magana ban tsaya ta kansu ba tunda naga mai tafiya dani yau ko bai amsawa zanyi kundun bala in daure in tambayeshi ya tafi dani.

    Sai gashi dakin yana sallama hjy ke fadin a,a miskili kafi gaban gaiya ba,a fita ba ashe yace sai yanzu hjy ko munyi sauri  zuwa ba farawa zasuyi da wuri ba.

  Ke fito mu tafi ya fada fuska daure hjy tace dan albarka kamar ka sani yanzu ta shigo tana min korafin an tafi an barta har ina shirin kiran uwarku ta turo a dauke ta yanzu.

   Mun tafi sai mun dawo ya fada ba tare daya tsaya ya bata amsa ba don da alama sauri yake kada ya makara a wurin taron.  ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅   ABU CIKIN DUHU   🦅2️⃣3️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWAUBANGIJI ALLAH KA SADAMU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN RANAN KA KAREMU DAGA DUK WANI ABIN CUTARWA DUNIYA DA LAHIRA AMIN.


Ba a karanta min labari idan baki bani dan na saka data ba don posting idan kin karanta na biki bashi zaki biya.

 Gabana ya fadi don jin abinda ya fada ba shiri na mike nabi bayan shi saida hjy tace takalman fa na dawo na saka na dauki dan jakkar hannun na rike.

    Tsaye yake a falo na zata zan gansu da wanan mai kwalliyan sai naga babu ita babu labarinta wurin.

   Sai shi kadai yana kallon kofan fitowa jin takona tafe ya fara tafiya saida ya fita daga kofan falon yaja ya tsaya wuri daya.

  A nan na same shi ba tare daya kalleni ba ya fara magana kamar haka ki kama kanki ki natsu fiye da yadda kowa ya kama kanshi a wurin banda kauyanci da kalle kale duk abinda nayi maki ban son musu ko gardama so be cool kamar yadda na umurce ki.

   Duk da hausa yakeyi wai saidai kamal turanci yayi yawa ga maganan shi amma ba laifi ga dan turancin dana iya ina fahintar shi hakana.

   Ma,ana dai akwai abinda ke shirin faruwa a wurin yake min indirect akai wanda na kasa fahintar hakan a raina.

    Har ya fara tafiya naga yaja ya tsaya sai na tashi karo dashi wani wawan tsuki yaja yana fadin idan kikai min wanan wautar taki wurin nan tun acan zan balbalaki.

    Saboda haka kada ki bari in kara wuceki tunda ba dodo nake ba kuma ba sauri nakeyi ba.

   Ya takalman kafanane ban iya tafiya dashi don ban taba saka irin shi ba kallon kafan nawa yayi ya kawar da kai don gaba daya shigar tawa ya tsorata shi wurin sai take ganin bani bace a gaban shi.

    Kamar yadda yace hakan muka jero gabana sai faduwa yake min kamshin shi kamar a hancin na aka zuba turaren.

     Security din shi suna hango mu mun fito sukayo kan mu suna gaidashi tare dani tunda sun gani tare dashi.

     Umurni naji ya basu cikin turancin da baikai can ba suka amsa da yes boss da sauri wani daga ciki ke bude motar maimakon ya shiga sai kawai naji ya riko min hannu sai da gabana ya fadi uku uku don tsoro da bazatan da yai min lokacin .

    Kofan da zan zauna ya nufa ya bude min na shiga ya ya rufo a hankali sai ya juya ya nufi dayan bangaren da daya daga cikin security din ke rike da kofan yana shiga aka rufe motar suma suka shiga nasu.

   Mami dake zaune cikin taron duk rashin ganin shi hankalinta bai kwanta ba duk da ga sauran yan uwansa a gurin.

    Table daya aka ware mata daga ita sai diyan ta sai anty Nuriya da ban san da zuwan taba a gurin,  kujera biyu ya rage shine kujeran da Jafar zai zauna tare da matar dayace wa mami yau zai nunawa kowa a gurin wanda mami ta rigada ta gama sanarwa MC ya fada tun dazun kuma yake faman sanar da yau dan mami din nan matashi da duniya ke ji dashi saboda ilimi da nagartan iya sarrafa computer zai bayanawa kowa abin kaunar shi.

    Haka yasa mami zaran ido kadan kadan ta kalli hanyar shigowa don ganin bai karaso ba yau dai tana son ganin wanan yar mai sa, a haka a duniya da har ta iya sace zuciyar danta dake gudun mata.

    Wanda har ta fara zargin kodai aljannu ne suka aure shi bata farga ba don duk yar data nuna mai sai yace batai mashi ba shi.

    A lokacin kuma shima yana faman tunane a ranshi ne yadda mutane zasu dubi zabin nasa yadda aka kwallafa rai da cewa diyar wani kusa zai kawo ko diyar wani hamshakin mai kudi a kasan .

   Yes yasan ba mami ba kowa ma a wurin zai iya ganin rashin dacewan su to saboda me ita din ba mace bace kamar kowa tunda mami ita ta matsa mai sai yayi aure .

  Wanan itace kadai zai zaba ya zauna lafiya a rayuwan shi don zabin mami sam yasan ba zasuyi daidai.

    Lumshe ido yayi yana gyara zama kodai ya fasa wanan shirmen da yake shirin aikatawa ne idan hakan zai kawo masu matsala da mami.

  Shin meye laifin shi har in ya gabatar da wanan yarinyar a yau a matsayin macen da zai aura.

  Itace yaji rashin ya kwanta da ita a matsayin abokiyar rayuwa kamar yadda mami ke shan fada mashi kullun idan tana masa nasiha yayi aure.

   Shi gaba daya ya yarda da hakan har zuciyar shi da gangan jikin shi ya amince da wanan zabin nasa matukar zasu zauna lafiya.

   Yasan yarinyar is pretty shi ba wanan yabi ba nashi tsarin ne a hakan aure dai akace yayi kuma ita din zai aura yasan ta hanyan shi yarinyar itama zata zama wani abu a duniya muddin dai tana tare dashi.

    Ya dan muskuta kadan tare da gyara zaman shi yaci gaba da tunane yace a ransa yasan ko bai samu goyon nayan kowa ba zai samu na hjy matukar ba mamice ta zugata ba funda itace ta fara kawo mai wanan idea din a falonta.

   Yasan amsan da zai ba duk wanda ya tun kareshi da rashin yardan wanan zabin nasa duk na kowa bai damesa kamar na mami ba.

  Ko ita din a yanzu ya tanadi hujjojin da zai bata idan idan har ta nuna bata yarda ya auri yar nan nata ba.

   Ido ya kara lumshewa a hankali yasan dole akwai aiki ja a gaban shi ba shi kadai ba yanzu har wanan yarinyar ya jefata a cikin dabon tashin hankali don dole ta fuskaci kalubali daga mutane da dama daga yau .

   A yanzu kan yayi niyar hakan bayajin kiran kowa ko dakatarwan wani bai damu da duk abinda wani zai furta akan hakan da zaiyi ba.

  Ya shirya daukan duk wani rigiman da zai taso na barazana a kan mu duk yadda mutane zasu kalli abinda zai aikata din shi  a shirye yake .

     Wurin ya hadu da manya da yara da masu ruwa da tsaki a gwaunati tarone na yan boko da suka amsa sunan boko a wurin.

    Haka motar ta danno kai a cikin get din wurin inda hankalin yan sa ido ya dawo garta akwai daya a gaban mu sai wace muke ciki a tsakiya dayana bayan mu ma,ana dai sun saka mu a tsakiya ke nan.

  A daidai lokacin da motar ta tsayane driver ya fita da sauri sai ya rage dagani sai shi a motar .

  Ya dan ja lokaci ba tare da yai magana ba sai can ya danyi gyaran murya yana fadin ke ina son ki kara saurarena da kyau kiji me zan fada maki.

   Na dan daga kai a cikin tsoro kamar kadangaruwa ya furzu wani iska kamar abinda zai fada ansashi ya fada dole ne lokacin.

     Ya fara magana a cikin muryan nan nasa mai fidda wani irin amon sauti ya fara ratsa kunnuwana.

    Na fada maki tun gida wanan wuri akwai yan uwan mahaifina akwai na mahaifiyan mu kin sa wasu wasu baki sansu ba.

   Don haka duk abinda wani ko wata zasu fada maki iyakarsu dake murmushi kada ki yarda ki wani abinda zai ba dani a gurin duk yadda nace dake haka zakiyi.

   Zanso idan mun zauna zandan rika jan ki da hira ke kuma kina murmushi a cikin wayewa kada ki yarda ki nuna min kauyancin ki a nan.

  Idan kinyi abinda nake so kin taimaki rayuwan ki har na yan uwanki nan gaba sai duniya tasan da diya mace ma yace kamar kowa.

    Yana fadin haka ya dan yun kura kamar zai tashi daga wurin dai kuma ya dawo ya zauna tare da fadin nasan mami zata bincikeki idan mun dawo gida kice da ita ni kike so idan kuma kin ki ruwan ki wanan duk abinda mami zatayi ki nuna mata ni kike so.

   Yana fadin haka ya juya ya bude motar ya jefa kafanshi daya waje tare da juyowa hana fadin ki dakata an fito in bude maki motar aikin ki ya fara daga yanzu ke nan.

   A zuciya na amsa cikin damuwa da tsoron me haka ke nufi ke nan ga yanayi ya canza a lokaci guda duk murna da daukin da nakeyi in shiga wurin bukin inga irin kallon da su Rufaida zasu min sai naneme shi na rasa don yadda nake jina kamar wata mara lafiya dani.

   Daga haka ya fita a motar ya bani gabana na faduwa don har lokacin na kasa hada maganan shi wuri daya in gane me yake nufi da hakan.

   Kayan jikin shi kawai abin kallone don ina kulla yana sha,awan fararen kaya don duk kyau tufafi farin kala zai saka a jikin shi.

    Yau ma rigace da wando da ban san ko na wani yarene ba sai yar karamar hula fara mai zagaye a kanshi rigar tana da aninaiya a gaba manya dasu har uku sai wani adon zaiba na manyan zane da akaiwa jikin rigar.

   Idan nace wurin taron nan gaba daya ba wanda yakai haduwa banyi karya ba don yadda kyaushi da kayan jikin shi suka kara haska wurin.

    Don yayi matukar kyau yau fiye dama kullun ko dan yau adon buki yayi ya kara haskawa haka oho sai na nemi nawa kwalliyan na raina kaina a wurin.

  A hankali na fito daga motar tsikar jikina yana wani tashi yarrr daga kaina har zuwa kafana dole badan naso ba muka jera har muna hada kafada a yadda muke tafiyan.

   Da sauri na dan jada baya don yadda muka manne mind your self OK ya fada ba tare dako na bayan mu sunji yai magana ba.

    Buki bidiri birede wurin ya cika ya batse don tun daga ganin haraban kai ma kasan yau babu kama hannun yaro sai dai muce Allah sa a watse lafiya.

   Saida muka dan tsaya a wajen na yan mintina kafin a bude mu shiga kamar an bada sanarwa shigan mu don idanuwan da sukayo kan mu can.

    Masha Allah mai sanarwa ya fada kunsan kaduna da izala ko dan gala yana izala kaduna kowa sunna Allah yasa muga Annabi Allahuma amin.

   Kamar in shige kasa in nutse dan kunyan abinda mc din ke fada a kanmu da shigowan mu hakan ya kara jawo hankalin kowa gare mu.

    Tafiya muke guda guda wanda zai nuna muna inda zamu zauna yana gaba security din shi suna daga bayan mu.

    Kwalliyan da gyaran da mai kwalliyan tayi min yasa basuyi saurin gane nice ba kunsan yadda kwaliya yanzu ke canza siffan mutum lokaci daya tundai in an hadu da wace ta iya tsarawa.

    Haka muke ta tafiya kafada da kafada har zuwa wanan table da aka tana da don mami da iyalin ta a wurin.

    Tunda naga yan gidan na soma kokarin sunkuyar da kaina kasa don nauyi da kunyan su daya kamani lokaci daya saboda kallon mamakin da suke muna gaba dayan su.

   A, a, a ya J yau yar mami ne haka ka, , , ,  hannun daya daga mai yasa jalal ya kasa karasa abinda yai niyar fada sai ya zagaya ya ja min kujera tare da dan nuna min in zauna.

   Nakai zaune a hankali godiyana yau ga Allah da baiyini mai garaje ba sai sanyin jikin nawa a yau yaba da kala a wurin.

   Saidana zauna ya zagaya ya zauna a dayan kujeran a daidai lokacin da mc ke fadin yanzu dai kujeran hjy iyami ya gama haduwa tare da sanar da shigowa ya Jafar da bayanin ko waye shi da kuma inda yake aikin sa sai kuma ya kara da fadin.

    Sai bride to be insha Allah kamar yadda kuke ganin wa yan nan masoya sun shigo muna da haske mai haska gidan kowa a wurin nan.

    Ya jafar ya dan rankwafo inda nake yana fadin kinji me mc din nan ya fada game damu ko ?

   A dan razane na dan sake murmushi yake na bude bakina da mai kwaliyan nan ta fesa min wasu abubuwa tare da wani sweet na tsotse tun a gida sai hakan yasa bakina fitar da wani kamshi mai ma,ana har yana jin shi a hancin shi lokacin.

    Sai ka dauka kai dake kallon mu kaga masoya na asali a wurin yadda muke mami kan imani ya hanata magana da kawar da kai daga garemu.

   Ba mami ba har yaran ta da muke zaune gaba dayan su sun kasa boye mamakin su a wurin ;

   Hakama sauran kujerun dake kusa dana mami din inda yan uwane da abokan arziki suke zagaye damu a wurin kowa imanin ganin hakan.

    Rufaida tunda salma tace waike baki ganeta bane zee ce yar mami fa yarinyar mami dai da muka bari a gida.

   Ai bata san lokacin data mike tsaye ba tana fadin kutumar uban nan zeey zeey dai zeey yar aikin mami dai.

   Amma wai yaya hakan ya faru dama yarin yar nan haka take ashe ?

   Shike nan dama Ruby ta fadi hakan gashiko yanzu hakan ya tabbata muna nan shekara da shekaru muna dakon wahala ashe ?

   Yau ga wata yar kauye mara asali da tushe tazo ga banza ta sameshi a saukake a wanan lokacin muka danyi wanan magana Rubby tace ku duba ku gani wallahi soyayya sukeyi ki duba yadda suke nuna kauna a gaban mami.

    Kai haba ina wallahi sam sam wallahi ina hakan ba zai taba yuyuwa ba muna zaune wata banza kamar zee tazo ta kwace muna shi.

   Tunda kowa wurin nan cikin ku zaman jiran ya zabeta takeyi haka kawai zamu kyale muna kallo wanan yarinyar kauyen ta  rushe muna plain din mu.

    Humm yazu na yarda da zancen  ki Rufaida yarinyar nan matsafiya ce ta sace zuciyar mami yanzun kuma ga wanda ko a zato bamu taba kawo hakan ba a ran mu wai yaya J zai kali wanan banzan yarinyar yar aiki ya kyasa.

   Wallahi da sake sam hakan ba zai taba yuyuwa ba kan sai dai inda wata manufa yazo da ita wuri  nan wanan kan na yarda kai koma dashine wanan yarinyar ta gama shammatan mu yau.

    Da hannu aka kira Nazira daga table din da iyayyen su mata ke zaune ciki harda uwar nazira din dake zaune da matan yayyun ta a wurin.

     Tana zuwa ta dan duka dafata matar tayi tana fadin wai wanan yar yar gidan waye a garin ko kuma a kasan nan ?

    Wanan mama baki ganeta bane zeey ce yar mami mawa mami hidimar nan muma abinda mukewa magana yanzu ke nan a can.

    Mami tace Jafar wai me nake ganine nan haka meke shirin faruwa ne wai haka  ta tabaya tana tsure shi da idanu babu ko kakautawa a wurin.

   Please mami kada kiyi wani motsi a nan idan mutane yana a kan ku yanzu don Allah mami kibar komai har a koma gida.

   Jafar din baiyi magana ba sai murmushi yakeyi yana fadin surprise mami aina fada maki zan baki mamakine da zabina a yau ko ? 

    Please ya J gaji me ya mamud ya fada ai so a daina wana  maganan a nan please Aisha ta fada kanta na duke kamar ba itace ke magana ba.

   Daga inda Nuriya ke zaune kusa da mijin ta take fadin wai mamaki a nan kuma aka kare gun yar , , , , 

   Hannu mami ta daga mata yasa tayi shiru bata karasa maganan da zata fada ba lokacin taja bakinta tayi shiru.

    Koda aka kira mami tashi tayi friends din ta suka mara mata baya sai da ya bari an dan rage muka tashi zuwa wuri mami tayi niyar juyawa tabar wurin kafin mu iso saida wata kawarta ta dan rada mata kada tayi hakan don Allah.

    Kudin daya saka min a yar jakan hannuna nima na bude jakkan ina likawa mami din ya dan rada min zakace mudin wasu masoyane na gaske sai ji mami tayi mun rungumeta a lokaci guda.

   Masu photo suka shiga daukan mu a cikin karfin hali mami ta rungumomu a jikin ta don kawai ta kawar da hankalin kowa ga zargi komai a wurin kanmu baki daya.

    Saidai na ciki na ciki a zuciyar mami don in ma wasa jafar yai mata haka dani wasan yayi yawa haka don hankalinta ba karamin tashi yayi ba da ganin hakan.

    Tsoron ya Allah shine kada wanan abin ya zama gaskiya ga jafar don zuwa yazun bataga alaman wasa a idanun dan nata ba yau.

    Daga inda nake na dan dago ido na saci kallon mami din dake tsaye suna magana da wata kallon da taimin yasani jin wani irin ba dadi a raina.

   Haka yasa na fara shan jinin jikina gabana sai faduwa yake uku uku riko hannuna naji anyi daga bayana yasa na dago da sauri yayane dan rankwafo yana rada min zaki gaisa da abokainane gasu can .

   A haka muka bar wurin yana rike da hannu na har inda ya barsu kai maginet wanan irin zabin naka a ina kashiga kasan nan ka samon wanan pretty girl din.

   Suka shiga wasa shi duk su ukun yana tsaye kimkam ko murmushi baiyi kamar an tsayar dashi a wurin dole.

  Muryan wani daga cikin su ke fadin dole mc ya bamu fili mu gwadawa duniya farin cikin mu da zabin ka.

  Bai tsaya jirab komai ba ya nufi wurin mc tun kan ma ya dawo inda muke mc yasa muna wakan tare da sanarwa zamu fito fili abokan JM nason su nuna mai farin cikin su da wanan ranan.

  Ance ana buki da dollars ranan koda bansan darajan kudin ba nasan masu daraja ne wanan kudin yadda wurin ya dauki ihu ga baki daya ya jafar yana rike dani da hannu daya.

  Dayan hannun kuma yana cikin aljihun wandonshi muke takawa a hankali sai photuna ake zuba mana babu kama hannun yaro.

  Sai daya gaji yaja hannuna ko ya fahinci ina gab da bashi kunyane don kiris ya rage in duka in cire takalmin dake kafana kada in fadi.

   Daurewa kawai nakeyi a hakan sai gashi yaja hannuna mu fita daga hilin wasa bama nan ba kawai gaba daya dakin taron muka bari lokaci guda security dinshi na biye damu duk inda muka saka kafan mu a wurin.

   Maroka suka sakashi gaba yana rike da hannu na har muka fice daga dakin yayin da suka dan sarara muna ke nan.

  Wani iska mai sanyi naji ya dokeni sai da nayi wani irin ajiyan zuciya kamar an gafarta min a wurin.

   Mota muka shiga ba wanda yai magana a cikin to nima me zance nida nawa umurni kuma in aiwatar don dole na.

    Sai da muka shigo unguwar ne ko ina yayi tsit alaman dai dare yayi sosai a lokacin duk mutane sun shige gidajen su.

  Mota na tsaye kofan gidan mami din ana jiran maigadi da akewa horn ya bude get din gidan naji yana fadin kin taka matakin farko a cikin shirin mu.

   Yanzu saiki shirya mataki na gaba shine amsa tambayan mami a gareki kaina na fada maki abu daya nake so dake shine.

   Idan mami ta tambaye ki a kaina ki fada mata nine nace ina son ki nasan zata tambayeki ke kina sona ko bakya sona ?

   Kada ki manta da amsan dana fada maki dazun ki basu idan sun maki wanan tambayan.

  Kai na gyada don ba bakin bashi amsa don duk a cikkn fargaban abinda zai faru idan mami ta dawo nake yi.

    A kofan shiga gidan ma mun dan jima ana buga kofan kafin lami ta bude mana daga ciki don su aka bari jiran gida dakuma hjy dake dakina.

    Har dakin ya kaini tsohuwar na zaune saman sallaya taji shigowan mu take fadin a, a har kun dawo ke nan eeh gatanan na dawo maki da ita ya fada yana wucewa bai yarda ya tsaya a dakin ba.   ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅   ABU CIKIN DUHU    🦅2️⃣4️⃣  ZAINAB IDRIS MAKAWAUBANGIJI ALLAH KA KAREMU DAGA SABA MAKA TAKO WANI HANYA A RAYUWAN MU ALLAHUMA AMIN, , , , Gaba na faduwa ina tsaye ban iya gusawa a inda nake ba tunda ya bar dakin jin muryan hjy ce data juyo gareni tana fadin.

    Yar nan lafiya kuwa hawaye ne yazo min lokaci daya nayi karfin halin girgiza mata kai ina daga kafa da kyat nace ba komai hjy.

   A cikin karfin hali na karasa cikin dakin ina kokarin aje jakkar dake hannuna da naji ya kara min nauyi a wurin.

    Bandaki na nufa tukun na fara sake fitsarin tsoro daya taru mi a mara na dan dade tsugune ina sake shi kamar ba zai tsaya ba lokacin.

     Na dade a zaune ina tunane kafin in samu inyi tsarki in fito daga bandakin duk jikina a sabule har lokacin yau kan nasan na taro mach a gidan mami wanda mai fitar dani sai Allah.

  Ni da wani ido zan kalli mami dashi wai yau ni zainab yar aikin ta ke ikirarin zama sarakuwar mami a duniya.

    Ni zainabu wani hali da rikici na jefa kaina a ciki aikin dana sani daga baya ke nan yake zuwa don nayi dana sanin yarjewa yaya Jafar bukatan shi yafi sau dubu a wurin.

   A gurguje na shiga dakin mami a cikin daren nan don daya saura na dare a lokacin na gyara ko ina na dakin ban tsaya ba don kada mami ta riskeni a ciki na jawo kofan ina dawo na haye kujera dama na cire kayan jikina tun kan in shiga dakin mami din.

   Tundana kwanta ba dunkule a cikin hijabina ban yarda nayi ko motsiba wurin.

   Ina jin hjy na magana tana fadin su a can zasu kwanane har wanan lokacin basu dawo ba haka.

    Shiru nayi kamar ina barci haka yasa ta kyaleni sai can na fara jin hayaniyan mutane a gidan alaman an fara dawowa ke nan daga dinner din.

     Can aka turo kofan dakin da karfi ana kiran sunana muryan Aisha ce sai naji hjy na fadin yau naga sha shanci a gidan nan.

  Zaki turo kofa haka babu sallama to boyar taku tayi barci tunda yaron nan ya dawo da ita don da alaman a gajiye takema ko da ta shigo.

   Mami ke kiran ta yanzun nan a dakin ta ta fada a cikin wani murya da ban santa dashi ba sai ranan.

     Kada ki soma ki tada yar nan daga barcin nan kije ki fadawa uwar taku tayi barci tun dazun inji ni   haba kowa fa rai gare shi kamar kowa ace mutum ba zai huta ba haka dare ai mahutane ta fada cikin bacin rai.

    Ina jin lokacin data rufo kofan hakan yasa nasan ta tafi na sauke wani iri ajiyan zuciya daga kwancen hjy taci gaba da fada ita kadai a dakin.

   Sai muryan sallaman mami tana fadin hjy ashe baki barci ba ina zanyi barci kuna waje har wanan lokacin iyami.

     Ki duba lokaci fa karfe nawa yanzu zaku biyewa shedanu kukai lokacin nan a waje dare fa mahutun muminine don a daren yake raya rayuwan shi walau ta hanyar barci ko na samun ganawa da ubangijin shi a natse.

  Wallahi hjy taron ne ba, a fara da wuri ba tana magana hankalinta na inda nake kwance zata tayar dani .

   Yar nan tayi barci tun dazun haba ku rika sauwaka mata hakana tana iya kokarin ta gidan nan yanzu sha shan yarki ta shigo tayar da ita.

  Koma me zatayi ita Aishan tai maki mana baku bari yaron ya samu albarka a wurin ku saboda karyan zamani har yaushe kamar Aisha za ace ba zata iya aikin da wanan yar zata iya maki ba.

  Ba aiki zatai min ba hjy dama dai tambayan ta nake son yi kawai mami ta fada sai hjyn tace.

  Koma menene tunda tayi barci ai sai a kyaleta har safe a tambaye ta itama fa mutum ce kamar kowa a cikin ku.

  Hjyce ta ceceni a ranan don mami fita tayi a dakin ba tare data tasheni ba kamar yadda mahaifiyar ta ta hana.

    Ranan idan nayi barci barawo ne ya sace ni don haka na kwana ina sake sake bani kadai ba har wanda duk abin ya shafa banda ya jafar dashi ko a jikin shima hakan.

    Aiko gari na wayewa sai ga sakon mami inzo gabana na duka uku uku na mike daga inda nake zaune a takure na nufi dakin mami din.

    Addu,a kan nasha shi yafi cikkn kwando ranan da sallama na shigo dakin daga ita sai Aisha da mama Ramatu.

   Mami tayi tagumi tana zaune kasa a inda ta idarda sallah asuba ta rasa abinda ke mata dadi a rai so kawai take taji na bakina abindake wakana a tsakanina da danta.

   Nayi sallama na shiga sai mama Ramatu ne ta amsa min a lalace koshi Aisha ko tana bina da wani irin kallon mai kama da mamakina a fuskanta.

   Kasa nakai cikin karfin hali ina fadin ina kwana mami ban jira amsawan ta ba na juya airin mama ramatu itama na gaida ita na juya gun anty Aisha itama hakan ne.

    Shiru dakin yayi na dan lokaci ina tsugune kafin inyi yunkurin mikewa don shiga ban daki in wako yaddana saba yi.

    Dakata zainab komaki zauna mami tace dani na koma da sauri inda na tashi ta dan dago kai ta kalleni kafin tace zeey ban saki da karya ba ko wani abu makamancin hakan.

   Balle boye magana don baki taba min shi ba tun zuwan ki gidan nan wurina.

    Kaina dan gyada a hankali yayin da gabana yaci gaba da faduwa sosai jiya tare da wa na ganki zeey ?

    Kai na dan dago da sauri na dan saci satan kallon mami na samu ta kafeni da ido tana son amsa daga gareni.

   Shiru na danyi tare da dukar da kaina kasa ina kallon carpet din da nake saman shi.

   Bakiji me aka tambaye ki bane mama Ramatu ta fada daga inda take zaune din da dan karfi hakan yasa na dan zabura tare da dago kaina ina fadin babu komai mami.

  Babu komai kuke haka jiya tare dashi a gaban kowa Aisha ta fada a dan hasale tana watso min harara.

   Ni ban san komai ba tun bayan da kikace mai kwaliya ta shiryani yadda ya kama kika fita kika barni da ita mun gama na fito na samu duk kun tafi babu kowa da zanbi sai gashi shi yace nazo mu tafi.

    Wani ajiya zuciya mami ta sauke har ina jinta daga inda nake Aisha ko na kokarin fadin  wai kina nufin ni No wallahi mami ban san komai ba a kai kawai dai ya ban kudi a gyara mata kai daga can kuma ya kara turo kudi waina saya mata kaya expensive one don kin manta ki saya maya yanzu hjy ke fada mai.

   Jeki zan kara nema ki mami ta fada tana kallon mama Ramatu da itama din ita take kallo don jin abinda ta fada.

    Kai mami ta gyada mata alaman ta bari in fita daga dakin tukun suci gaba da magana zan shiga ban daki tace barshi anjima ki dawo idan mun fita.

   Na juya na fita nan na barsu a dakin sai da na fita ta juya tana kallon Aisha dake zaune tana fadin duk abinda aka kitsa tare dake aka shirya hakan ashe kika boye muna.

   Wani mami wallahi ban san komai a kai nima iya abindana sani ke nan na ta fada yanzu dana sani ai dana fada maki komai tuni.

    Daki na koma na takure a wuri daya ina faman funane a raina don na kara daure kaina again ban san da wani ido zai kalleni ba kuma nasa bangare ga mami bawai ta yarda dani bane tunda har tayi mi  abinda bata taba min ba yau shine.

  Wai in fita idan sun gama na dawo in gyara dakin kenan da sauran maganan da zasuyi a kaina ke nan a dakin.

   Shirun da nayi yasa hjy dake magana still kan daren dasu mami sukayi jiya a waje taji nayi shiru hakan yasata jutowa gareni.

   Hawayen da ban san yana zubane daga fuskana ta ganin haka ta fara sake salati tana tafa hannu tare da fadin yarnan an maki wani abi ne ko kiranda iyami ke maki jiya na hana a tasheki tai maki fada a kansa yanzu don naga bata so hakan ba dama.

    Saboda shine ta bata maki tunda farar safiyan nan ko da sauri na girgiza kai don nasan baida wuya yanzu ta sauke wa mami bala,i akai ta kara jamin wani tsana.

    Kofan dakin aka turo Aisha ce tsaye a kofan tana fadin zainab mami na kira daidai lokacin da hjy ke fadin.

  Ke kan yar nan arr da halin nan naki ace dan musulmi bai iya sallama idan zai shiga guri gara dai da uwarku ta raboku da kasan kafiran nan tun kan kufi haka ai.

  Sai kuma jin abinda ta fada ta sake fadin wai wani laifi tayi maku haka baku bari yarnan ta hutane wai ?

    Ba laifi tayi ba naji Aishan ta fada a daidai lokacin da zan fita daga dakin bayan fitana asheta fada mata komai dake faru tun daren jiya din a bayana.

   Sai da tsohuwar ta gama ji take fadin meye laifi a cikin zancen nan idan shi jafarin yace itace zabin sa ai baiyi zabin banza ba nake gani ko ?

    Haba hjy yar aiki ce fa wanan yarinyar da bata waye bane zai dauka a matsayin matarshi yadda ya J yake wayayye dan boko mai ilimi din nan dashi.

  Yo wani waye akwai wanda yafi wani a gurin Allah ne idan ba Annabin rahama ba shi kadai zai fadi haka sai ko wa yanda sukai zamani dashi aka tabbatar masu da aljanna . 

   Kai don Allah hjy ki daina danganta wanan da yayan mu please ai abin kunyane ace wai wanan ce zabinsa haba dai.

   Kaji min ya da wani maganan banza meye laifin zabin nasa har idan da gaske yakeyi ba wasa ba uwarku da ubanku ya aureta takai wanan din wayewa ne a lokacin.

  Aida ba yanzu bane Aisha ta bata amsa tana fita tace kinci gidan ku nace kinci gidan ku yarnan da wanan maganan banza kece zaki zauna mashi da ita koshi zai zauna da abinsa.

   Fita tayi ta kyale tsohuwar tana jin zancen ta na kara mata takaici a ranta sai ta dauki zancen tsohuwar ga tsufane kawai ke damun ta ba wani abuba don da tasan abinda takeyi da bata fadi hakan ba ai.

   Ina shiga dakin mami ba tare data kalleni ba tana jin sallamana take fadin jeki ki wanke muna bandakin nan idan kin gama ki daukowa hjy abin karyawanta a kitchen.

   Don mami ta dauki zugin mama Ramatu da wata kawarta da tun jiya ta zugeta a kaina baki daya don haka ta kudurta canza min daga wanan lokacin tun ban dauko mata magana ba a cikin diyan ta.

   Wanan zugin kan mami ta haushi ta zauna akai sosai har yakai ta fara ganin aibuna a gareta yanzu.

   Kafin in fito har ta shirya zata fita ta gaisa da mutane take fadin yi ki karasa ki fufo min dakina na amsa da toh kawai a cikin sanyin jiki ga canjin da nagani gareta.

   Dakin mu tashiga gaida mahaifiyar ta inda ta samu hjy har lokacin tana mitan zancen ita kadai a dakin.

   Koda mami ta shiga amsa sallama dai tsohuwar tai mata babu sakin fuska suka gaisa tayi mata ya jiki ?

    Mami bata tsaya ba ta juya tana fadin bari ta leka yan uwa a dakin in dawo tana fadar haka ta fice daga dakin.

   Har na gama gyaran dakin na jawa kamar yadda ta umurceni in mata da dakin na wuce kitchen na karbowa hjy abincin.

   Ban daki na shiga nayi wanka na fito na shirya a cikin wani atamfa da Aisha ta bani dinkin buje da riga bujen dai bai matseni sosai ba yadda ita yakan matse jikinta idan ta saka a jikinta kafinta bani .

   Ban zauna a dakin ba na nufi kofan fita daga dakin ina zuwa kawata hjy ta fada zan je in karbo abincine a kitchen na bata amsa.

   Yau kuma ba a nan mukeci tare ba dake mazaki dawo ki dibi abincin nan kici karna saba maki.

    Ko ta fahinci tsoron mami nake sai tace kowa yasan tare dake nake cin abinci sai yaune zasu kawo min wani zance.

   Dole na dawo na rakube a gefe ba tare dana yi yadda na saba muna wasa da dariya a gurin ci ba haka hjy ta sakani gaba dole na debe abinci mai yawa tana kara ina ya isheni haka ta kyaleni.

  Na fara ci ke nan mami ta shigo dakin tana magana sai ta dagata da maganan tana fadin ke kuma meye haka ?

   Me tayi hjy ta tambaya tana kallonta da mamaki hjy don me zata zo ta zauna tare dake a nan tana cin maki abinci ?

   Yau din kuma iyami ina har ke muna zama da ita ana aci abinci baki taba fadan wani magana sai yau ?

    Daga yau din ban son in kara ganin hakan ta koma can wurun yan aiki ta dinga ci tare dasu kande da lami.

   A, a iyami bana son irin haka wanan ba halinki bane hakan ban san kuma yaushe kika fara hakan ba.

   Hjy na canza tsarinane yanzu a gidan nan don a fara bambamta yan aiki da yan gidan nan iyami dakata hakana hjy ta fada tare da juyawa inda nake tana kallona kafin tace dani kinga kawata.

  Jeki falo kici abincin ki ki bamu wuri zamuyi magana da uwar ki ina jin hakan na mike da sauri don barin dakin.

  A daidai lokacin mami ta kai zaune a kusa da mahaifiyar ta saidai ita saman kujeran ta zauna ba a kasa ba inda hjy take zaune.

    Ko dana fita ban nufi cikin falon inda nake jin dan dararakun mutane na zauna dan filin da zai sadaka da falon da gefen dakunan mu din.

    Ina kallon abincin ba tare danayi ko yunkurin cin cibi daya daga abincin ba sai idon dana zuba mai kawai.

    Iyami kada ki bari shedan ya rudeki kiyi yunkurin yaki da ubangijin ki kan abinda Allah shida kanshi ya halasta hakan.

    Yarki dazun ta fada min komai dake faruwa daku tun jiya wanda na hango kina kokarin fita daga ilimin ki da irin tarbiyan ki dana sanki na girmama dan adam a duk yadda yake.

    Hjy ba hakana bane ni yaran nan zasu kunyata a cikin taron jama, an arzikina wai yaron nan ya nemi ya raina min wayau ya hada baki da yar nan a kunyatani hjy ?

   Akunyataki kamar yaya hjy ta tambaya shi auren ne kunya ko yarinyar ce kunya a gareki yau kuma kina kunyan a santa da ahakin ki kika ajeta a gidan ki har kika jata a jikin ki kamar kece kika haifi abinki.

    Wani irin shedani ne yayi saurin tasiri haka a jikin ki har kika manta da bayan ki ke ?

   Da sauri ta dago kai ta kalli tsohuwar hjy tace eh kin manta da naki bayan kina son ki maimaita tarihi a kanki yau.

  Hjy bawai hakana bane ni abinne yai bala,in bata min rai kawaion su wullakantani har jafa, , , , , 

   Hannun da tsohuwar ta daga matane ya dakatar daga karasa maganan ta datayi niyar fadi a kanmu.

   Iyami na haneki tun wuri da wanan halin abinda zai kawo dana sani daga baya wanda zai zama keya gareki.

  Yaya zaki idan Allah ya nufa wanan abin mai yuyuwane garesu ko kina son in kin matsa da jayayya da ubangiji ya dauki ranki ayi a bayan ki.

   To ina baki shawara ki natsu ki shiga hankalinki tun wanan abin bai fita waje an dawo ana maki dariya ba daga bayan ki.

   Ina yar nan ke kika kawota gidan nan har danki ya ganta ya nuna sha, awan shi gareta duk ko da yadda take ba yar kowa ba kamar yadda ku kuke gani.

    Shin iyami kin manta da yadda akayi lokacin auren ki da mahaifin yaran nan sam ban taba zaton zaki manta da hakan ba har ace yau ke da kanki kike kokarin yin wanan halin da ba, a san musulmin kwarai dashi ba.

    Ina wanan abin ke kanki kamar darasine a gareki ban taba zaton har zaki yada kiyi ko maka mancin hakaba a yanzu.

    Daga inda nake zaune naji takon tafiya haka yasa na dago kai da sauri ina kallon mai zuwa a lokacin ya Jafar ne da yaya mamud suna tafe suna magana a tsakanin su.

   Saidai ganina a wurin yasa sukaja suka tsaya suna kallona da sauri na gyara zaman da nayi da farko ina gaidasu.

   Duk kallon mamakin ganina a wurin sukeyi sai ya mamud ke fadin lafiya kanwata kika zauna a nan haka a kasa baki je dinning kin zauna ba.

    Wani kallo ya Jafar ke min ba tare dayayi magana ba sai hannayen shi daya zuba a cikin aljihun wandon shi bakin wandon jeans dake ciki ya dan fito waje ya wani kara haske ko kallon tsoro nayi masa oho.

   Badake ake magana ba ya jafar din ya fada na dan dago kai na kallesu sai nayi saurin dukar da kaina don duk idon su yana a kaina.

  Ganin ina kokarin mikewa yasa ya mamud ya fara tafiya shima ya mara masa baya zuwa dakin dana baro su mami din da hjy.

   Da sallama suka shiga dakin saidai ganin yadda daga hjyn har mami suke sai yasa suka dan tsaya daga kofa basu karaso ba sai ya mamud ke tambaya lafiya dai mami ko wani abinne ya faru ?

   Shike nan ma hjy ta fada ga magani ga ciwo Allah ya kawo ki tambayi dan ki a gaban mu yanzu aji idan da gaske yakeyi ko wasan da kike tsamani kika tsani yar mutane haka ba gaira ba dalili lokaci guda .

  Kin hana yar mutane tun jiya kwanciyan hankali duk kunbi kun rikita yarinya ga baki daya ni bani son irin haka wallahi abu baikai abin daga hankali ba zaku sakawa mutane rigima a gida.

   Kallon mami yayi ya karaso inda take yana kaiwa zaune ta gefen gujeran tare da kamo hannun mami din yana fadin wani abu ya farune mami ?

    Bai faru ba zai dai faru ka gaya muna meke tsakanin ka da Abu dana ganku jiya a gurin taro har kana nuna muna wai surprise din ka ke nan garemu ta fada rai a bace.

    Abu mami ?

Waye hakana mami ban gane wa kike nufi ba hannun ta dake rike a nashi ta fisge tana fadin zeey yar aikina nake nufi ba wani ba.

   Kai ya girgiza tare da dukar da kanshi kasa can ya dago yana fadin mami ba ke kikace na fito da yarinyar data kwanta min a kasan nan ko diyar waye ba ?  ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅     ABU CIKIN DUKU     🦅


2️⃣5️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWAYA ALLAH MUNA ROKON RAHAMANKA DA KARIYAN DAGA DUK WANI ABIN CUTARWA A GAREMU ALLAHUMA AMIN, , , , , To ka samo din ta tambaye shi a cikin gatse ?

   Eh na soma mana mami kuma ai a karkashin ikon ki take itama yarkice kamar su Aisha.

    Wa ke nan ya mamuda ya tambaya wanan yatinyar taki da kika dauko a kauye mana ga zahiri kun gani jiya tunda kun gamu tare.

  Mami kan yake tayi wanda yafi kuka ciwo kafin ta tattaro natsuwa don hjy dake wurin a zaune bata da halin furta mai wani abu a lokacin.

   Saidai duk da hakan sai da mami tayi bajintar fadin wai zeey dai kake nufi ai zee din kasan a matsayin dana daukota kuma bayan haka karatu take a yanzu.

    Mami nasan da hakan saidai ai takai munzalin aure a yanzu don haka aurena da ita ba zai hanata karatun ta ba.

   Ko kin manta kin fada muna kema kina karatun secondry daddy ya ganki ya aure ki lokacin.

   Look jafar bana son shirmen banza mata nace ka fito da ita in maka aure at dis stage bawai ka tsaya kana min wanan shirmen ba haka.

   Zainab na fadama karatu take kuma bata cikin zabin matan da nake son ka aura don tayi kankanta gare ka yanzu.

    Hjy dai da yaya mamud na gefe zaune suna sauraren draman uwa da danta sai murmushi suke masu kawai.

  Mami to aini ita din ce chooice dina sai ta karasa girman ta a gurina don ni a hakan da take yayi min daidai.

   Jafar kada ka mayar dani abokiyar wasan ka idan kai tayi mani ba, , , ya mamud ne yace mami please.

    Ki barshi ya zabi abinda yake so a rayuwan shi tunda shine zai zauna da ita bake ba kada a tillasta mai yayi abinda baiso a dawo ana dana sani daga baya kuma.

   Hjy tacs fada mata dai dan nan ko kai zataji maganan ka tunda ni ban kai matsayin da zan tsawata mata ta saurare ni ba 

   Hjy bawai haka bane na lura yaron nan rainawa mutane wayau yake son yiwa mutane tunda mun tursasashi yayi aure bari ya zabo wace bata yuyuwa a gareshi yanzu ya rama abinda mukai masa ko ?

   Wallahi mami tunane baikai ga hankan ba itace dai din naga tana daidai da rayuwana ita kuma din nake so a matsayin a bokiyar rayuwana.

  To ban yarda bami ta fada a hasale tana mikewa hjy tace iyami dawo ki zauna mu kai karshen wanan maganan a nan tun wani bai kaiga ji ba.   

   Shiko jafar jikin shi ne yayi sanyi lakwas don bai taba tunanen mami zata dauki abin da zafi haka ba.

    Ya mamud ne ya kawar da duk wata magana ta hanyar fadin tunda ita ka zaba din ba laifi ga hakan saidai yana da kyau itama muji ta bakinta ai idan tana son ka shike nan aurene mami ba wani abuba ai.

  Mai yuyuwa kai itace zabinka ka ganta kana sonta a haka karamar ta ita kuma yarinyar ba kai mata ba a ranta .

  Kaga ba zamuyi mata dole ba a kanka a matsayin na yar amana a wurin mami din don haka  sai muji ta bakin ita yarinyat kuma.

  Ban gane abinda kake nufi ba mamud mami ta fada tana kallon yaya mamud din taci gaba da fadin kaima kasan tunda ya tursasa mata ai bazatace batayi ba tunda duk mace ko banza neman irinsa takeyi.

    Mata ma masu aji da ilimi da wayewa suna binsa su sameshi yana gudu sai akan wanan yar kauyen yarinyar idon ka zai sauka sai dai idan kana da wani manufane a kan hakan dai.

   Banda manufar kome mami ita din ce nagani nake kuma so a hankan don banga wani matsalan da zaisa a hanani aurenta ba a tare da ita.

  Mtss mami taja wani matsiyacin tsuki tana fadin Jafar kana son bacin raina da jefa yarinyar nan ga fushi wallahi.

   Mami kiyi hakkuri yanzun nan zan kira ita yarinyar a gaban sa muji ta bakinta idan tace ta yarda dashi shike nan mami sai ki masu fatan alheri a rayuwan su.

    Me zata fada tunda tana son shi mamud karka mata fa yar kauyece dama nema tafito yi a birni kuma ta samu a yanzu.

  Gashi ta samu wanda darajan ta da kimarta baikai ta samu ba a yanzu,  abinda bata taba tsamanin samun shi ba sai tace maka a a kuma ?

  Mami please ayi hakkuri aji ta bakin ta idan ta amince ai masu fatan alheri shiyafi yanzu.

    Mamud na fada maku yarinyarce bana son ya aura gaba daya don haka abar wanan na zancen tambayan ta please mamud.

   But mami ni kuma ita din nake don banga wata da hankalina ya kwanta da ita ba bayan wanan din.

    Jafar idan ma tausayinta ne yakaika fadin kana son ta ai ba sai ka furta kalman aure a tsakanin ku ba kana iya taimaka mata ta hanya da dama basai wanan hanyar ba daka fito dashi wai auren ta zakayi.

    Jafar dake ta faman latsan wayan hannun shi tankar ba da shi ake zancen ba sai lokacin ya dago kai yana fadin.

     Mami bawai taimakonta kawai nakeson yi ba ni kawai dai auren ta nakeso nayi dan tayi min a raina yana magana a cikin daure fuskan shi.

   Daga inda hjy take zaune tace da kyau na mijin duniya kai mamuda kira muna yarinyar muji na bakinta yanzu.

  Na bar gurin da suka sameni zaune don abincin ya gagara ci gareni don haka na dauka na kai kitchen.

   Daga nan ne na tsaya don yin wanke wanken kayan da akaci abincin safe gasu nan an tara birjit don bakin da akayi gidan.

    Maganan da mami tayi nake son in fara kiyayyewa da tace in dinga zama a cikin su lami da kande sune yan aiki irina.

    Ina tsaye na fara tara kayan ne lami na faman sakamin albarka don haka suke min duk lokacin da nashigo zan tayasu wani aiki daya shafesu.

   Muryan yaya mamud ne a kofan kitchen din yake fadin ke zainab zo mami na magana dake a dakin hjy.

  Yana tsaye ya tokare hannayen shi a kofan shigowa kitchen din yayin daya zubamin idanuwan shi sai tausayin yadda ya sameni ya kamshi.

    Juyawa yayi ya fara tafiya haka yasa na dauraye hannaye da sauri nabi bayan yaya mamud din ina jin wa yanda ke falo zaune na fadin.

   Yar iska yarinya yau zakici uban ki gidan nan don yarinya kin tarowa kanki bala,i da hannun ki.

     Idona ne ya kawo kwalla don ban kaunan abinda zakai a zagi iyayyena ko kadan saboda sanin daranjan su da nakeyi suko yan gida mami zagi a wurin su ba bakin komai bane a wurin su.

   Zaune suke su hudu a dakin mami hjy ya mamud dashi gabana ne ya fadi don ganin su har lokacin a dakin .

    Sallama nayi cikin yar siririyar murya hjy da ya mamud suka amsa min mami kan kai ta dago ta dan kalleni tare da kawar da kanta ga kallona.

   Zauna a nan ya mamud yace dani yana nuna min wuri daga gefen kofa da nake tsaye saina kai rusunne da sauri ba tare dana zauna ba kamar yadda ya bukaci inyi din ba.

   Kaina kasa ya mamud naji ya kira suna sai na dago kai a hankali na kalleshi yace mun kirakine muji ta bakin ki a kan wani maganan daba musan dashi ba tsakanin ki da jafar gashi zaune.

    Ya nuna min shi da hannu sai lokacin na dan saci kallon Jafar din da idonshi sun kada a lokacin da gani shima yana cikin bacin rai ke nan.

   Jafar ga yanan ya gabatar muna dake a matsayin wace zai aura kamar yadda mami ta bukaci da yakawo mata,  matar da zai aura a yanzu.

  Da sauri na sake dago kai nakai kallona ga Jafar din da shima a yanzu nice yake kallo da idanuwan da suka kade mai lokaci guda.

  Don haka muke son jin ko kin amince da wanan ra,ayin nasa kema kin shirya da zaki aure shi kamar yadda ya bukata dake.

    Dukar da kaina nayi kasa don ban san amsan daya dace in bada ba a wurin ga gardadin dayai min tun daren jiyan a mota ina tunane.

   Ga mami dana hango tsanata saboda wanan zancen daya taso tsakanina dashi mami ta canza min gaba daya daga dare zuwa wanan lokacin kamar ba mami bace a gabana.

  Don ba wanan yanayin na tausayina data min yau a gare ta ko kadan illa tsana karara da take nuna min a fuskanta.

   Kiyi magana ke muke saurare ya mamud ya fada yana kallona don jin amsan da zan basu a lokacin.

  Kai na fara girgizawa a hankali na samu na bude baki da kyat ina fadin ban san da maganan bani koma na sani ya jafar ba sa, an aurena bans shi don matsayina dana iyayyena baikai ko na yaron shi ba yaya.

    Tunda na fara magana ido kowa ya zuba min sai mami dake fadin nikan nayi mamaki ina hankalin zeey da yatafi har take shirin tafkamin wanan kuskuren duk, , , , 

   Dakata iyami ke a matsayin ki na uwa kin taba ganin inda aka tsiye yarinya haka wai ana tambayanta zabinta kai tsaye.

   Kiwa Allah kiwa yaran nan adalci iyami tunda ni yanzu ba magana ta kike ji ba ban isa ba ko dan nima din banda mutuncine tunda nima daga kauyen nake ko ?

   Yarasulu hjy me ya kawo wanan zance kuma har kina danganta kanki da hakan Allah ya gani ni ba manufa ke nan ba ta fada tana kallona az cikin yanayin daba zan iya fassarashi ba a lokacin.

    Ke tashi ki tafi ya jafar ya fada a tsawace kuma ranshi bace ga wasu jijiyoyin kai da suka mai jasur a goshi abu fa farar fata sai suka mike sukai wani layi layi a saman goshin shi kamar mai tsananin ciwon kai a lokacin.

     Da gani hankalin shi gaba daya a tashe yake mai a lokacin zainab jeki abinki ya mamud ya sake fada da sauri na mike nabar dakin.

    Don dama a kage nake dana bar aurin saboda rikicin da nake hangowa a idanuwan su wurin.

    Ina barin dakin kitchen na nufa har ina hadawa da tuntube don sauri saboda gaba daya na gama tsoracewa da lamarin nasu ga baki dayan su.

   A daki kan hjy ta tubure tana fadin ya mamud yazo ya mayar da ita dakin ta ba zata zauna inda ba,a san darajan ta ba.

  Hankalin mami ya tashi tsohuwar taci gaba da fadin yaron nan yace ga zabin shi ta yaya bayan kun gama tsorata yarjnya tun safe yanzu za a kirata ace ta fadi ra, ayinta a gaban kowa ?

   Ke lokacin da akai maki aure haka mukai maki mami tace hjy kina dai son ganin laifina ne yanzu.

    Wanan shawaran yaran nan sukazo da shirmen su a gaban kifa akai komai yanzu don Allah hjy kada kija zancen nan inda bai kai ba.

  Yarinya dai tace ba zatayi dashi ba final Allahu akabar don kuma hankalin ki ya bata yanzu sai kikaji dadin hakan ke.

   Allah na tuba ashe gaskiyane mace komai tsufanta wayau ta ragagge ne.

   Ke yanzu har kina murna yar da kika raina kike gani ba a bakin komai ba ta iya budan baki a gaban idon ki yau tace maki batayi da dan naki da kike dauka wani kayan gabas a wurin ki.

   Niyi tir da wanan hukuncin da kika bari yaron nan ya yanke a gaba me zan zauna inyi tunda banda sauran kima a idon ki.

   Gidan ki nazo zaki iya min duk wani rashin da, a don yanzu kina ganin ke kin isarwa kanki a komai sai dai da badon jafari ba da sai ince yarinyar nan zainabu ta burgeni sosai .

   To jinin ka jinin kane banji dadin yadda ta watsawa jafarin kasa a ido ba a gaban kowa don  kawai tsoron idon ki data gani a daure kin sakar mata na mujiya .

    Wanan maganan kuma sai yasa mami ta ji daci a zuciyar ta da kyat dai ta samu ta shawo kan yar tsohuwar ta fasa tafiya saidai mami bataji dadin yadda tsohuwar ta dauki zafi da ita ba haka.

   Ya jafarko tunda ya fita ya bar mami da su ya mamud a dakin ya bar gidan tun mami bata damu da rashin ganin shi ba har dare yasa ta tambaya ko ina ya shiga haka bai dawo gida ba don hakan ba dabi a shi bane yin dare a waje .

      Har yakai ta fara tambayan duk wanda ya shigo gidan a cikin mazan dake gidan amsa dayane dai daga shi har security din shi fun safe basa gidan.

   Ta kira wayan shi yafi a kirga wayan ba ya shiga kwata kwata ba, a samun shi gaba gaba daya  ranan.

  Tunane kala kala mami tayishi ga zafin yarinyar daya mamaye mata rai gaba daya taji ta tsani yarinyar tana dana sanin daukoni dayi ta jefa a cikkn iyalin ta.

  Gashi kuma hjy ma a nata ban garen haka ya jawo masu matsala da ita don tana matukar son mahaifiyar nata sosai.

   Gaba daya gidan sai yai min zafi a yan kwanaki biyun nan babu wurin wanda nake dafawa inji sanyi kowa tsanata yake a gidan ga baki daya.

   Sai gurin hjy kawai ita kuma yanzu ba zama muke sosai ba idan na shiga dakin sai zanyi wani abu don ina gudun mami tashigo ta sameni a ciki zaune yasa na koma kitchen wurin yan aikin da dukkan mu kawomu akayi gidan don aiki.

    Hjy tayi fadan hakan har ta gaji ta saka min ido ta kyale ga yadda lamarin ya juye muna.

   Ga zagi da nake sha a gun yan matan gidan a yanzu yayi yawa har takai ranan Rufaida tayi min mari biyu masu kyau.

   Saida anty Aisha tayi mata fadan hakan kan su dan sasautamin don Allah tunda ba laifina bane shine ya ganni yace yana sona ai.

   Ba nice na leke mashi ba kuma yanzu ba wanan zancen budan bakin Rufaida sai cewa tayi Aisha kece baki san halin yan kauyen nan ba.

  Mudake tare dasu muka san halin su basu shigowa gari sai sun shirya an asirce su yadda duk namijin daya gansu ba zai iya kawar da idon shi a kansu ba meye ba a yi yanzu halan.

  Gasu da sihiri mai dafi da kaifi wanda in basu ba kainan dan birni kace ai maka saidai aci kudin mu ga banza.

  Tace au hakane nima fa abin yaban mamaki ace wai duk wanan baiwa da jin kan na ya jafar ga ilimi da wayewa amma ace wai zee yake so shi .

    Wanan to zarcin da suke min ne yasa hankalina ya kara dagawa sosai a gidan naji ina son komawa kauyen mu baki alaikum ba tare dana fadawa kowa ba.

  Sai dai kuma ina jin tsoro don ban san kan garin ba kada in fita ni kadai a ganni ba kauya a saceni.

    Tunda na fara jin ana fadin jibine tafiya Abuja na fara funane a raina don nagama yankewa kaina hukunci .

  Gara kawai in gudu in koma gida ko ta kan anty safiya data kawoni da itama tazo tayi min tas kan wanan zancen a gaban mami ta wanke tas wanda nasan hakan tayi shine don kawai ta wanke kanta a wurin mami din.

     Saida na bari hjy tayi barci na mike na fara hada kayana a cikin jakkata inayi ina juyowa ina kallon ta kada ta tashi ta ganni.

 Aiko ban tsira ba don ashe idon ta biyu tun dana fara take kallon abinda nakeyi.

  Juyowan da zanyi sai ganin ta nayi zaund ta kura min ido kaduwa nayi don ban zaci hakan ba na dauka tayi nisan barci a lokacin.

   Ikon Allah yar nan me kike kokarin yine karda ace guduwa kike son yi daga gidan nan sai kawai na durkushe a wurin ina kuka ina fadin hjy gida zan tafi.

   Babu mai sona a gidan nan mami ma fushi take dani har su anty Aisha da nake dan dafawa naji sanyi yanzu itama bata sona suncewa asiri nakeyiwa mutane suke sona.

  Sai naga tsohuwar ta danyi murmushi can kuma tace kai yaro dai yarone ke in banda abinki dama ai duk wanda Allah ya mayar sani abu a duniya saiya fuskaci kalubali mai tsanani kafin ya taka nasaran shi.

    Ba wanda ya tsamaci haka gareki sai gashi kwatsam Allah ya doraki a kan kowa dake gaban ki ga yanzu sun san da sani ke din yar bawaice kinga dole ko su nuna hassadan hakan gareki

   Yanzu kinga mayar da kayan nan kafin gari ya waye wani ya shigo dakin nan yasan abinda kikai kokarin aikatawa har makiyan naki suji suyi maki dariya.

    Hjy Abujan ne da za a koma ban son zuwa gara dai in tafi tun muna nan kusa da gida.

   Yar nan ashe haka kike da gardaman banza ko dai kin san inda Jafarin din yake ne ?

  Hakan data fada yasani fadi wallahi hjy babu komai a tsakanin mu ban san komai ba game dashi.

   To wanan tafiyan da zakiyi ne zai sa a kara zargin ki a dauka kun hada baki dashine kan ki gudu hakan kuma na iya jefa iyayyen ki dake a cikin wani mawuyaci  hali.

   Kallon ta nayi da mamaki tace kwarai kin dai san iyami na da halin da zata sa a daure kowa naki a kasan nan ko.

  Tsoron maganan da hjy ta fada ya kamani sai na kara fashewa da wani irin kuka tace kinga ki shiru kin san yanzu darene kada wani yajiyo mu a waje.

  Na maki alkawari muddin ina raye zan tsaya maku har burin ku yaci ka duk da naga kin sare kin ji tsoron barazanan uwar taku har kina fadin shine ya tsara hakan.

  Da sauri nace wallahi hjy ban san komai ba a kan zancen nan ni dai kawai komai da yace nayi a wurin nayi.

    Da haka har ta shawo kaina muna dan hira kafin ta mike ta shiga ban daki ta dauro alwala tana fitowa nima na shiga don cewa da tayi min in yawaita yawan ibada in roki ubangiji sauki.

  Naji dadin wanan shawaran da tsohuwar ta bani sosai don  duk kunci dake zuciyana sai na nemeshi na rasa washe gari naji na tashi raina ya sake duk da mutanen gidan basu daina halin da suke min sai dai ko dunyima hakan bai damuwa na yanzu don shawaran dana samu daga tsohuwar.

  Ga kuma iyayyena da nakejin tsoron lefin da basuji ba basu gani ba yazo ya shafesu ya zama dole a gareni in daure ga duk abinda zan gani don yakin nawa ni kadai kamar yadda hjy din ta fada min kar in yarda in kada iyayyena ga tashin hankali.


  ZAINAB IDRIS MAKAWA

🦅    ABU CIKIN DUHU    🦅  ZAINAB IDRIS MAKAWA    JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI FATAN ALHERI GA MUSUMAI DUNIYA BAKI DAYA AMIN, , , , , 


    

  Yar uwa ban son ki da shiga hakkin wani ko wata don Allah kiyi kokari ki biya kafin ki karanta kada ki raina hakkin wani a kanki gara ace kece mai bi da abiki.

  Allah ubangiji ya bamu ikon aikata alheri da fin karfin zukatan mu Allah ka sadamu da rahamomin sa amin.

    Mami ta shigo dakin wurin hjy a lokacin ina zaune ina gyarawa hjy kayan ta da aka wanke don da ta cire kaya zan dauka in hada danawa in wanke tas.

    Shine hjy ta tsayar dani in gyara mata jakkar kayanta muna dan hira ina dariya don gareta kadai nake jin dadi a gidan bayan ita sai dan dama anty Aisha duk da yanzu itama akwai sauyi sosai a fuskanta gareni.

    Mami na shigowa dakin saidana kadu dan fargaban daya ziyarci zuciyana lokaci guda don yanzu ina tsoron ta sameni a dakin tare da hjy saboda kada ta yi min cin mutunci.

   Don haka nake iya kokarina wajen kaskantar da kaina a garesu kamar yadda suke nufi da zancen su gareni.

  Ba wai suna takuramin ga hakan bane saidai ko sakin fuska ance rahamane to babu wanan yanzu tsakani da kowa a gidan sai hjy sai ko yan samarin mami jalal da jamal da basu taba nuna min wani canji ba a fuskokin su.

   Kamar yadda muka saba hakan ne har yanzu a wurin su do shi jalal sarkin wasa har yakan min ba, a da fadin amaryan mu.

    A cikin wasa hakan yasa yanzuma dana fito daga dakin hjy na sameshi zaune tare da yan matan gidan yana cin abinci suna hira nazo zan wuce zuwa kitchen wurin su mama kande.

   Muryan shi naji yana fadin a, a ke kuma armaryan mu yau ko dan gaisuwan ban samu ko dai har kin fara amarcin ne mu fara kawo gaisuwa don yanzu ke dan kin zama key a gurin mu sai an murdaki za a bude, 

   Kai kai haba jalal wanan irin maganan kesa kuna kara hurawa yarinyar nan kai amaryan wa kuma wanan yar kauyen yar aikin kakewa irin wanan maganan.

    Sai ta dauka kamar daidai take da kowa a gidan nan yanzu don dan kauye bai iya samun wuri ba.

    Wuce daidai yanzu tunda har ta iya halbo zuciyar ya J aiko tafi kowa ke nan dai a yanzu tunda ta doke duk yan matan dake garin nan kai bama garin nan kadai ba duk kasan nan zance.

    Ya jamal naci karo dashi da sauri na dan duka ina gaidashi da kwana yadda na saba na shige kitchen haka yasa ban ji sauran maganganun su ba a wurin.

   Ashe a bayana har zancen yaso koma masu fada don Rufaida ta dauki zancen da zafi har gaban mami saida maganan ya kaisu.

    Mami kan jalal taiwa fada sosai a wurin jamal yace haba mami kina wanan maganan haka gaban kowa bayan yarinyar nan kin sanda cewa itace dai ya jafar ya tsayar zai aure kice kika sanda wanan zancen a yanzu.

    Amma shi ya J din ai ya dade da nuna yana kaunar zeey din ki tun muna abuja da kika fara ganin su wurin dinner rantsar daku .

   Dalilin kine fa har ya J ya fara kula yarinyar nan yanzu kuma kina fadan wanan irin maganan a kanshi idan bakya son wanan abin ki mayar da yarinyar hannun iyayyenta kowa ya huta idan yana so sai yaje can gurin iyayyenta ya nemeta.

   Kai jamal ka rufa min baki da wanan bakar maganan da kake fadi duk yan matan dake garin nan ace baiga wace tayi mashi sai wanan zeey din da bata da asali yar kauye.

    Meye to aciki mami ya tambaya da mamaki yana kallon ta tare da fadin itace fa zabinsa mami don me kike kokarin kawo matsala a cikin zancen nan yanzu ?

  Jamal ta fada a cikin tsawa tare da fadin ka fita a idona tun kan ranka yakai ga baci dama halin ku daya da Jafar ai don baku san ciwon kanku ba.

   Mami don kawai na fadi gaskiya ki barshi mana yayi abinda yake so zaifi ace kin takura kanki akan wanan magana.

   Yana fadin hakan ban tsaya sauraren me zata fadaba ya juya wurin jalal yana fadin kai ya mutafi ko ?

   Jalal din dakewa mamin su kallon mamakine ya mike yana fadin mami zamu tafi wurin ticket din don a samu da wuri sai dai bamu san na mutum nawa za,a saya ba idan munje.

   Ajiyan zuciya mami ta sauke don yanda ranta ya baci da zancen yaran da safen nan tana fadin naku sainawa da hajiya da Aisha Nuriya da yaran tunda shi mamud din ya tafi tun jiya.

   Mami zeey din bada ita za, a tafi bane wanan karon ko a nan za a barta ne wanan karon kinsan fa basu haduwa dasu Rufaida a wuri daya ko banza.

    Ya za a barta a nan jamal ya fada dole ai da ita za a tafi ko dan taimakawa hjy wa zai iya da lalurar ta idan ba ita ba.

   Jin wanan zancen yasa mami ta danyi tunane kafin tace da ita zamu tafi amma mota zatabi wanan karin ita dasu kande da lami da drivobi.

    Haba mami ai hakan ba girman ki bane yarinyar nan meye laifin ta dankine fa duk yaja mata koma meye a wurin ku zeey din nan tana da halin kirki gun kowa.

   Kallon data watsa masune yasa su fita daga dakin da sauri har suka kai wurin sayar da ticket din suka sayo jamal yace su hada da nawa su saya koma me mami zatace dai sun saya ai.

  Hjy kawai zamu fadawa da mun koma gidan zai fi  suna wanan maganan ne wayan ya jamal yayi kara ya dauka da mamaki yake kallon wayan daya nuna lamban kasar South Africa.

    Waye kuma ya kirani daga south africa ya fada yana nunawa dan uwan nasa dayake tuki a lokacin.

   May be wani friend din kane ko ya fada shima yana kallon lamban kafin ya mayar da hankalin shi ga tukin da yakeyi din.

   Jamal kuma ya dauki wayan da hello muryan dan uwan shi jafar yaji yana fadin kai jamal ya kuna lafiya ya mami.

    Ya Jackson kaine kayi nisa fa ka daga hankalin mami sosai don har yanzu bata koma daidai ba rashin jin inda ka shiga.

    No ball kawai nazo kallo don in samu natsuwa a tare dani ya kana gidane ko waje ya tambayi dan uwan nasa.

    Wallahi ya gamu nan munzo yankar ticket gobe zamu koma Abuja mami zasu fara aiki monday din nan mai zuwa.

   Wanan yarinyar fa ya tambaya sai jamal din yace yanzun haka zancen ta muke a mota don mami tace wai kada mu yanki ticket da ita a mota zasu tafi ita da sauran yan aiki kamar ta.

    Yanzun fa ya tambaya No mun yanko da ita zamu hada da hjy saitawa mami magana fine idan ka koma gida kayi flashing layin nan zan yi magana da ita ok ya nagode take care.

    Sun dan biya wani guri kafin su dawo sai bayan sallah azahar suka dawo gidan a dakin hjy suka sameta ita kadai a dakin sun gaisa take fadin yau bata  gansu ba tun safe.

   Jalal yace dazun na shigo da niyar idan nagama karyawa in shigo mu gaisa sai wa yanan yan rainin hankalin suka so raina min wayau suka ja har mami tayi min fada kan yarinyar nan zainab.

  Nan dai yake fada mata komai har zancen sayo ticket din da sukayi dani take fadin sun mata daidai don daba haka ba ko ita ba zata tafi ba idan ba wanan yarinyar cikin su don ko taje wa zai kula da ita a can kamarta.

   Karbi waya wani ke son magana dake ya fada a dake sai ta watso mai wani irin kallo tana fadin wani wa ka samomin da yake son magana dani.

   Wayan ya kara mata a kunne jafar din yana jin rikicin da sukeyi a dakin yana murmushi kafin yace ke tsohuwa kanki nake so nawa zaki sayar min a turo maki kudi gobe nazo na sare.

  Dan nema mai muryan turawa ka dauka ba zan sheda muryan ka bane halan ?

    Jafari ina ka shige kabar mutane a cikin damuaa haka kan dan magana kankani ka yankewa kanka wanan hukucin.

   Ashe kai baka cika jarumi ba kaja fadan da baka iyawa da uwarka na dauka kai cikkaken jarumi ne ashe ba haka ba.

   Matsoraci kawai yace lailai tsohuwar nan kin gama sani yau zan ko gwada maku ni jadumine da bai magana biyu.

    Ni baka da bakin fadar komai yanzu a gabana tunda kaja fada kabar yar mutane nan da yaki ita kadai.

   Hjy wa ya isa ya yakar min mata ban gama dashi ba ai ita mami ta sani tasan bana magana biyu yasa na bata wuri ta sauko daga fushin data dauka.

   Yanzun dai ba wanan ba wallahi tafiya ne ya kamani gani nan a kasan africa ta kudu nazo wani abu zan dawo da yardan Allah nan zuwa jibi idan Allah ya kaimu.

   Nikan daka ban mamaki sai ince wanan jarumin nawa bai cika jarumin maza ba ashe a duniya.

   Yanzu dai hjy ina yarinyar take don nasan nabar sarkin yaki a gida yasa ban daga hankaliba ga zancen.

    Yarinya kan na nan tana fuskantar matsi da tsangwama don har tayi niyar guduwa wallahi na dakatar da ita daga hakan.

   Kallon juna jamal da dan uwanshi sukayi shikuma yana fadin hjy don Allah kada ki bari ta gudu daga gidan nan idan na dawo zan sake zama na karshe da mami akan zancen.

  Bazata ko ina ba a yanzu kan sai dai ban sanarwa gaba ba idan ka kasa shawo kan uwartaka kan zancen.

    Ba jamal waya yace jamal din ya karba yake fadin idan mami ta tambaya ka fada mata nine nace a saya da ita.

   An gama yaya ya fada yana dariya suka danyi maganan su kafin yace jamal din ya ban wayan.

   Ina kitchen abinci lami ke kwasa ina mika mata ledan da take saka tuwon data tuke a cikin sa naji muryan ya jalal na fadin ke zeey karbi waya ana magana dake a bayana..

   Sai da gabana ya fadi kanfin in juyo ina fuskanta shi bai tsaya jiran komai ba kawai ya ban wayan na karba.

    Tare da karawa a kunnena gami da sallama duk da bansan mai magana ba a lokacin amma sai da nayi sallaman dan koyi da sunan ma,aiki S A W .

    Ajiyan zuciya naji an sauke wanda hakan ya tabbatar min dashi ne a layin duk da ban tabbatar da hakan ba lokacin.

    Ido lumshi yana maijin wani iri a zuciyar shi ya amsa sallaman tare da fadin ya kike kina lafiya ko kina nan kina aikin kuka da tunane ?

   Ko baki maganane ya fada kamar bashine jafar din mami mai yawan daure fuska ga kowa na gidan ba in badon ina yawan zama da hjy ba ina ganin yadda yake sakin jiki a gaban tsohuwar zan iya rantsaewa da baya dariya tunda yake don yawan daure fuskanshi koda yan uwan shi maza.

    Sai yau gashi shike min magana mai kama da ba,a a kunnena haka ina jin shi.

    Sake maimaita abinda ya fada yayi yana fadin ko bakiji mena fada ba kina nan kin saka kanki a damuwa ko ?

   Aa,a na samu kaina da fadi a cikin sanyin murya ina mai girgiza kai kamar yana gabana a lokacin.

   To ki daina damuwa don banga laifin ki ba ko kadan a ranan don na gama fahintar dama ke matsoraciyace sosai.

   Ko kin fasa taimakawa yan uwar ki da innan kine in sani don in kyaleki in neme wata.

    Daga inda nake na dan runtse idanuwa don da ace shidin sa,a nace da zan so haka ya kasance ko dan kyaushi da wayewan shi saidai nasan shirme nakeyi don  wutsiyan rakumi yayi nisa da kasa.

    Shi din ba ajin irin mu bane yayan talakawa kamar yadda mami ta fada muryan shine ya katse min tunane yana fadin.

   Da kun koma abuja zakici gaba da karatun ki don nayiwa mamud magana yanzu ma abinda ya kaishi Abuja ke nan zancen karatun ki don zanfi son sai kin kamala secondary kafin in aure ki mu tafi.

    Nagode yaya na fada a dan kunyace danaji zancen karatu Allah yasa dai kina da kokaerin karatun kamar yadda nake zafo ya fada.

    Gane bazanyi magana kamar yadda yakeso ba yasa shi fadin ni zan kashe tunda har da magana a  hanaki yi dani yanzu.

   Sai an jima nace a kage don na matsu ya kashe wayan in huta da wanan bugun zuciyar danake ji a lokacin.

    Maimakon naji ya kashe din sai ji nayi yana fadin kingaji dajin muryana ne to idan kin gaji ni ban gaji ba zan iya barin wayan a haka har lokacin dana gama sauran bugun zuciyarki da numfashin ki tunda naga a tsorace kike.

   Ban kaiga sani anmsar da zan bashi ba sai muryan Nazira ke fadin ji min yar iska ana aiki kinzo nan kin labe kina waya da maza ko ?

    Uban wama ya baki wanan wayan dake hannun ki haka ko sato wayan mutane kikayi kina waya dashi yar iska muga wayan har sata kika fara a gidan nan ashe yau Allah ya tona maki asiri magen banza mai kwanciyar kwanto ayi sake tayi wuf da abin mutum.

   Duk abinda take fada a cikin kunnen ya Jafar yana ji bata farga ba don bata kai ga karban wayan ba tana shirin tara min mutane a wurin.

    Shigeya yar kauye mara gata da asali watau ke kinzo birni kinsha jan miya har kina kokarin sace zuciyar dan masu gida da kissan ki na yan kauye ko ?

    Ki rasa wanda zaki likewa kamar chewing gun sai ya J da kowan mu a nan take zaman jiran shi mutumin da ko ganin shi tsadane a wurin mu.

  Ke amma dan bakin tsafin ki da maitar ki har kika iya sanin yadda kika ja hankalinki gareshi yasan da zaman ki gidan nan maza ban wayan naga ko wayan waye kika sace.

    Idona ya riga daya ciko da ruwan hawaye a cikin karfin hali nake fadin ni ba barauniya bace kuma bana maita waya kuma ba satan shi nayi ba ya jalal ne ya kawo min shi yanzu da kansa.

    Lami daga gefena take fadin haba Naziran hjy yanzu fa jalal ya kawo mata wayan nan muna tsaka da aiki ya miko mata shi.

   Karyane wallahi satoshi tayi yar iska watau ke zaki goya mata baya ta dinga muna barna a gidan nan wallahi yau sai kowa yaji sata ta fara muna don kowa ya kankanta kayan shi tunda muna tare da barauniya.

   Wallahi ni ba sata nayi ba na fada don ni ko tsinken wani ban taba tabawa a gidan nan na samu kaina da fada cikin sheshekar kuka sai ga Rufaida da salma dake falo sun shigo suna tambaya take fada masu.

   Wallahi yarinyar nan na kama ta sato waya tana magana dashi a nan Allah ya kawoni da maishi yau yayi hasara iphone ce kamar ta jamal salma ke fada.

   Ba sata nayi ba anty salma yanzu ya jalal ya kawo min wayan inyi magana karya take Nazifa da Rufaida suka hada baki wurin fada.

    Satan shi kikayi ke har kina da darajan da zasu baki wayan su shegiya yau Allah ya tona maki asiri don dole sai kin bar gidan nan yau.

    Hasken da wayan yayi daga hannuna yasa salma fadin dawa kike waya yar mami a hankali na dago kai na kalleta kafin in mayar da kaina a kasa ba tare dana bata amsa ba.

   Dawa ko zatai waya banda munafukan iyayyen tan nan dake mata tsafi a gida.

    Nazifa kin san koda ya J take waya kike fadan wanan maganan haka don duk abinda kike fada yana jin ki tun dazun don wayan sai yanzu aka kashe ta.

    Sai jikin ta yai sanyi ta juya tana fadin ke ki bari don Allah dama wayan a kunne take ashe salma tace wallahi shi yasa nake fada maki ku fita harkan yarinyar nan ku kyaleta ba kuji.

    Zeey yar mami kin gama wayan ki miko min muryan ya jalal ne daya dawo yake fadan haka daga kofa sai kuma yai shiru yana binsu da kallo lokaci guda.

   Ina sharan hawaye nake miko mai wayan tare da fadin nagode duk suna tsaye suna kallon mu a wajen lami tace haka kawai kinzo kin dafawa yar mutane sata ba gaira ba dalili kina neman tara mata mutane ki kunyata ta.

    Na fada maki shi ya kawo mata wayan yanzu muna aiki a wurin nan  amma bakiji ba.

   Ba dole in zargeta ba ta fada tana watso min wani kallon tsana daga inda take tsaye Rufaida kuma wani irin kallo mai nuna matukar tsana gareni take jifana dashi kafin tace.

    Ya J din kike waya dashi a boye ashe shigiya mai bakin sihiri kin rantse sai kin sace mai zuciya a gidan nan ko to tsaya kiji .

  Ya J ba sa, an yin ki bane gaja irin ki yar kauye idan ko ba aikin asiriba me ya gani a jikin ki yake wanan haukan haka akanki .

    Jeki ki tambaye sa ai dan uwan ki ne don me zaku ga laifin yar mutane a banza ga mailefin daya nace mata hjy tsohuwa ta fada daga bayan su don layin jalal daya kira yake fada masu hankali tashe abinda suke min a kitchen din.

    Hjy bashi keda laifi ba wanan dince mai laifin ita da batar aika mai da asiri ba ke rufaida ki shiga hankalin ki dani kada ki kawo min diban albarka a gaba wurin nan.

    Ba kunya har kike maganan asiri haka a gabana yaushe kika san wani aikin asiri can idan ma shi kuke tunane ai da asiri tai masa daba hakan ba.

    Da sauri ta dago ido tana kallon hjy din tace eh da idan ya zare a gidan nan baijin assh a kanta wanan ake kira da asiri.

  Wanan ko kauna zallasa so da kaunane nata yaja hankalin shi har don sa ya rufe ya gama mutuwa a kanta ta yadda bai iya jin kiran kowa a yanzu.

     Mami dake kwance salma ta kirata ta fito da dan saurin ta zuwa kitchen din ta samu hjy na yanka sababi a kofan shiga kitchen din.

     Tsaye take bata san abinda ke mata dadi a wurin ba sai faman tunane take a ranta ita kan ta daukowa kanta jidali da hannun ta.

    Ita kan dame wanan abin yai kama me jafar dinta ya gani gun wanan yar haka ya mace a kanta  ya hanata sakat a zuciyar ta yan kwanakin nan kan wanan magana.

   Wai me ya kawo wanan zace mami ta fada daga bayan mahaifiyar nata inda take tsaye.

   Mami wanan munafukan ne na kama a kitchen yanzu da wayan su jalal a hannun ta shine na zata satowa tayi take waya dashi nake mata magana hjy ta taso.

   Dawa kike waya zeey ya akayi wayan su ma yazo hannun ki har kike waya dashi.

    Diyan ki zaki tambaya wanan don su suka bata wayam ba sata tayi ba a gurin su hjy ta fada a hasale ta juya wurina tana fadin fito mu tafi daki ba zan barki a nan ba tunda basu da imani.

  Daga mami har yan matan dake tsaye su biyu suka dago ido suka kalli junan su .

  Ina tsaye rakube a jikin bango ban ko motsaba don tsoro naji mami tace ba dake ake magana bane kinyiwa mutane tsaye haka.

  Na dago matacciyar kafata daya gama sanyi da sarewa na fara dan tafiya nazo na ratsa tsakiyan su na fice daga kitchen din ina jin wani iri a zuciyata sosai.

   Nazo wucewa gaban mami dake tsaye a kofan naji tana fadin ku fito daga kitchen din nan kuma da tada zaune tsaye kuke wallahi ina ruwan ku tunda ba wayan ku ta dauka ba.

    Da kyat naga dakin don nisan da yai min lokacin ina shiga na zauna daga kofa na fara rera kuka a fili hjy na shigowa dakin tana mitan zancen.

   Nace hjy don Allah don so  da kikewa Annabi ki roki mami ta mayar dani gidan mu hannun iyayyena .

   Ba sai ta rokeni ba ma zeey nima wanan abjn ya fara isata hakana don haka ki shirya gobe a mayar dake gida.

  Mudai shirya a maidamu gida zaki fada don ba yar nan kadai zata tafi a gobe har dani yar kauyen uwar yan kauye zamu tafi kafanta kafana a gidan nan goben,  har gaban iyayyen ta zan kaita in yaso dan naki yaje gurin iyayyen ta ya nemeta idan yafi maki sauki.  ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅     ABU CIKIN DUHU     🦅2️⃣7️⃣  ZAINAB IDRIS MAKAWAFATAN ALHERI GARE KU YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA BAMU WUNI LAFIYA AMIN, , , , , Jin abinda hjy ke fadi yasa dole na daina kuka don ba zanso nayi sanadin mami da mahaifiyar ta arayuwana ba don na samesu cikin so da kauna iri ta da mahaifi a tsakanin su.

   Ni na bar shiri sai ga tsohuwar ita tana hada kayan ta wai ita gida zata bata kara kwana gidan mami.

   Hakan ya tayar da hankalin kowa a gidan don mami har kasa take tana ba hjy hakkuri hjy ko sai fada take tana fadin.

    Sam bazan zauna inga wanan cin fuskan da yaran ki kewa yar mutane ba haka idan ke kin kasa da ita ni zan tafi da ita can kauyen mu in yaso shi Jafari yazo gurina ya nemi auren ta.

   Kin dauko amana dadi dadi kina riko tsakani da Allah ashe rikon naki ga yar baikai ciki ba da har dan ki zaiji shawan hada iri da ita ki fito kina fadin baki yarda ba don ita din ba diyar kowa bane a kasan nan.

    Gasu nan birjit a gari dan naki yaje ya zabi daidai dashi a kadarta yau Aisha ce dan tallakawa ya fito nema ashe ba zaki iya bada aurenta ba ga wanda take so ?

   Don kawai yanzu kudi ya bude maki ido kowa kuna kallon shi a mutumin banza koko samun abokai yan duniya dakikayi ne yanzu ya sauya maki yanayi.

    Idan ma hakan ne sai kije ki aura mashi wacce duk kike son aure mai din ita kuma wanan din zan tafi da ita gurina in sakata karatu idan ina raye wata ran sai kince ba ita bace a gidan nan.

   Kuma ki sani koda danki zai mutu ne idan yazo ba zan bashi yar nan ba muddin na bar gidan nan da ita.

     Inda nake ta kalla tana fadin tashi muje yar nan nasan dai ko ban san kowa a garin nan bazan kwana a waje ba yau zan samu na Allah da zasu duba tsufana su tausaya min.

    Tana kokarin sungumar jakkan kayan ta daga saman gado inda yake ajiye mami tayi saurin dafe jakkar tana fadin hjy don Allah ki rufa min asiri a garin nan kada kije ko ina gwiwa biyu nakai kasa tare da daga hannaye biyu sama ina fadin.

  Hjy don girman Allah kiwa mami hakkuri karki fushi da mami ba laifin ta bane laifin zuciyane.

   Da yau danta bai bijiro da wanan zancen ba da mami batai fushi dani ba har gobe mami uwace a gareni mai mutunci da kima a idona.

    Bazan taba mance mutuncinta a gareni ba don Allah kiyi hakkuri ni in tafi ko mami da yaran ta zasu zauna lafiya.

    Hjy ba zan biki ba zan koma gidan ubana in zauna duk abinda Allah yayi min mai kyaune a rayuwata Allah ne shedata wani kalami na soyayya bai taba hadani dasu yaya ba a gidan nan wanan yana daga cikin kaddaran rayuwata.

  Don Allah hjy kiyi hakkuri ki zauna a cikin gatan ki kada ki fushi da mami sabodani kada laifin hakan nima yazo ya shafeni watarana.

  Ina fadin hakan na fashe da wani irin kuka mai tsanani na mike tare da nufar wardrobe inda kayana yake cikin jakka a jere ina kokarin daukan jakkar.

    Takwara ina yanzun kika gama bani hakkuri akan uwarki idan nayi hakkuri ke kuma ina zaki a cikin daren nan .

   Ko so kike in fasa hakkuri da uwar taku mu tafi tare kafata kafarki mubar gidan nan a yau din nan basai gobe ba.

    Hjy ba Anchau zan tafi yau din ba zanyi kokari in kai kaina gidan anty safiya har kashe gari ta sakani mota in koma gida nufina ke nan muddin barina gidan mami zaisa ta samu sallama tsakanin ta daku.

    Ba zaki bar gidan nan ba koda bana raye sai idan aure ya rabaku da uwarki kamar yadda aure zai rabata da yarta Indo.

    Muryan mami ke fadin ke zeey mayar da kayan nan ki fice daga nan ki ban wuri da hjy kije gun su kande ko dakin Aisha ki jirani.

   Mami ta bani umurni da   hakan da sauri na juya na bar dakin nan na barsu tare da mahaifiyar ta na nufi gurin su mama kande na zauna.

    Sun dade da mami da hjy a dakin har bayan magariba san nan salma tace dani hjy tana kirana a daki.

    Na mike na tafi ina addu,a a raina Allah yasa sun yake hukuncin in koma gidane gaban iyayyena zaifi min wanan zaman rashin yancin kai da banda shi a gidan mami yau har ni zainab Nazifa ta dafawa satan waya.

    Hajiya ta idar da sallah har isha,i ina shiga da sallama fuskan tar a kaina tana son ta fahinci halinda nake ciki take tambayana da nayi sallah na bata amsa da nayi tun dazun hjy.

   Zauna ki zuba muna abinci ta fada kai tsaye dai umurni ta bani babu daman yin mussu gareta ke nan.

   Itama ba wani cika mata nayi sosai ba na dai zuba kadan kadan sai dai nawa din yafi zama kadan don nasan ba zan iya cinye wanda ma na zuba din ba.

    Sai faman cakulan abincin nakeyi cikin sanyin jiki itama dai hjyn haka dai take kokari  tura abincin a bakin ta can naji tace kada ki yarda in hada nawa baki karasa cinye wanan dan abincin da kika zuba ba kamar za,abawa yaron goye.

   Dole na fara tura abincin da sauri ds kyat nake hadeshi gaba daya raina babu dadi a lokacin har na samu na gama kamar yadda ta umurceni dayi.

   Ba zancen hira garemu sai kowa yayi shiru a dakin dan dama hjy ma takan dan jefo min magana jefi jefi.

   Washegari aka tashi da shirin tafiya kamar in dora hannu akai ince wayo ni Allah don banson inyi nisa da gida kuma.

   Dan dama nan na rike sunan unguwar da muke dana su anty safiya don bam manta da sunan unguwar ba har yanzu a raina.

   Ina ji ina gani har aka fara fadin a fito da kayan da za a wuce dashi a mota don masu mota zasu rigamu tafiya nake gani.

    Jakkunan kayan mu gaba daya an labta su a mota hakan yasa naji raina ya kara baki nasan yanzu kan zuwa ba fashi gareni.

    Hjy ta aikeni dakin mami don in tuna mata zancen maganin ta da za a saya mata nan kaduna.

   Ina gab da shiga dakin nake jin muryan mami na fadin saida nace kada ku sayo ticket da zeey mota zatabi ita dasu kande baku maganata ba sai da kuka sayo.

   Ba laifin mu bane mami ya J yasa mu saya mata kinga ko ba zamu ce masa a a ba tunda kudin sane.

    Gulman ku zai ciku daku har jafar din in dai akan wanan yarinyar ne ido na zuba dani da jafar din a gidan nan za,aga waye zai sare a karshe.

    Jikina ya sake yaraf kamar kayan wanki inaji kamar in juya kada in shiga dakin a lokacin sai dai na ba zuciyata sanyi na fada dakin da sallama.

   Duk suka juyo suna amsa min shigowana ya basu daman sulalewa daga dakin suka bar mami tare dani ina fada mata sakon da hjy ta aikoni.

   Naji ki fada mata za a saye na daga don barin dakin sai naji ta dakatar dani ta hanyar kiran sunana.

  Da sauri na koma na tsuguna a inda nake tare da dukar da kaina kasa ina sauraren abinda zata fada min a lokacin.

    Mami ta dan dade tana kallona na dan wani lokaci kafin ta bude baki ta soma magana dani.

   Zeey ina son ki saurareni dakyau kiji abinda zan fada maki kaina gyada ina wasa da yan yatsun hannuna dana hade a wuri daya ina saurenta.

    Ba zan taba bari ki bar gidan nan ba koda hjy bata nuna hakan ba don in taimakeki ki taimakeni na raboki da iyayyen ki zuwa nan.

    Saidai zanso kiyi nisa da duk wani dana bawai jafar ba kwai a a ina nufin gaba dayan su muddin kina son mu zauna lafiya dake a zaman mu.

    Zancen karatu kuma da mun koma abuja zan sa a nema maki wani makaranta gwaunati ki karasa karafun naki a nan.

    Saboda haka in kinyi abinda na fada maki kiji dadina idan kuma kinki to ina mai fada maki zeey zaki kwammace dama baki sanni ba a duniyan nan.

  Na riga nagiwa jafar mata amma saboda ke yana kokarin ya bijire min kan umurni na don kawai ya nuna min shi dan zamani ne.

    Mami kiyi hakkuri in Allah ya yarda zan kiye ni ban taba magana dashi ba kuma bazan taba ko a bayan ki mami.

    Shike nan zeey zaki iya tafiya mami ta fada ba sakin fuska a tare da ita zuwa gareni a yanzu haka na mike na fita daga dakin.

    Karfe biyun rana muka fito mami tana makale da yan matan ta dake mata sallama mu kuma muna guri daya dasu ya jalal da hjy sai Aisha dake daga gefen mu tsaye tana sana,an ta da waya.

   Ba wanda ya kula da yai min sallama kamar yadda suke sallaman su hjy da su jalal dan dama salma dace zeey za a tafi ke nan na danyi dariyan yake ina fadin sai mun dawo anty salma tace ko sai munzo ba.

     Haka motar mu ya daga kamar su jawoni su fidani daga cikin motar yadda suke watsa min harara daga sama har kasa kuma kowa ya kula da hakan.

    Karfe hudu duk muna cikin gidan mami na Abuja da farko mami taso raba muna daki ni da hjy don tace naje daki daya zamu zauna dasu kande a nan.

  Sai hjy tace ni kuma na zauna dawa idan kin kaita can kinsan ko a gida da yaran yayan ki nake zama ai.

 Don haka barmin ita mu zauna tare kawatace ko banza tare muke kashewa mu bisa a dakin mu daga ni sai ita.

  Haka yasa na koma da zama a dakina dana bari da farko kafin mu wuce kaduna don yanzun ma a nan zamu zauna da hjy din.

   Mami bata da lokacin zama gida tare da mu karfe taran safe baya mata a gida don hakane nake tashi da sassafe nai mata aiyukan dana saba mata a dakin ta harta shirya ta tafi.

  Kamar yadda mami ta canza min hakan nima nake canza don a gurguje zan karasa aikina  kafin ta fita na bar mata dakin sai idan ta gama zata rufo dakin ta kawo makulli gurin hjyn ta ta fice.

   Satin mu daya da zuwa wani yammaci muna zaune da dare a falon dukan mu ya mamud ya shigo muka shiga gaida shi da dawo yana amsa muna.

    Ina zaune kusa da kafan hjy naji yana fadin mami monday fa yarki zata fara shiga school don na samo mata makaranta a nan garin.

    Da bakin wa kayin wanan mami ta fada a daidai lokacin da nake murnan hakan ina kuma gode masu a raina sai naji wanan furcin nata a bazata.

   Gabana ya yanke ya fadi lokaci guda naji taci gaba da fadin ko akwai wanda ya kawo min ita gidan nan ne a cikin ku da kuke nuna min gaba gadi game da yarinyar nan.

  Meye gaba gadi cikin wana zancen iyami ina taimaka maki yayi kan abinda baki samu lokacin yin sa ba kuma nautin kine kiyi hakan.

   Ko haka yar taki zata zauna a gida ita bata karatu ta taimaki rayuwan ta nan gaba tunda a zamanin nan kome ka zama idan ba wanan karatun baka cika cikkaken mutum ba a idon jama,a..

    Hjy kikan so tarewa yaran nan fada a kan gaskiyata da zai tafi nema mata ai sai ya nemi shawarata yaji abinda na yanke a kanta.

   Fada muna yanzu ai gashi zaune me kika yanke a kan yar nan a yanzu tunda an hutar dake baki ga hakan ba.

  Iyami bansan yaushe hali  ki ya sauya ya zama na mutanen  zamanin nan wajen , , , 

   Hjy ba nufina ke nan ba bandai jin dadin yadda yaran nan suke min abu gaba gadi haka kamar banda daraja a gunsu kamata yayi yazo ya fada min kafin ya samo mata din.

   Sai kawai yazo yanzu yana fada min magana haka kai tsaye wai mondaya zata fara tafiya wani makarantar ma ka samo mata din.

   Mami inda yaran nan suke zuwa a nan na sama mata itama sai su dinga zuwa tare duk da ita a secondary section zata zauna.

     What har nawa za a dinga kashewa a kanta ke nan ina kosu yaran nan kana min korafin yayi yawa da farko saidana haneka.

   Mami indai zatayi kararun ai karuwan kowa ne nan gaba don haka kiyi hakkuri nayi kuskure ya fada yana dukkar da kanshi kasa alaman ban hakkuri a gareta.

    Allah ya kyau hjy ta fada tare da dafani tana fadin yar nan nayi maki murna ubangiji yasa a shiga da kafan dama nace.

   Yaya na gode Allah ya karawa arziki albarka yace ba komai ki dai dage da karatu sunce idan sun gwada ki kinyi nasara zasu iya barin ki inda kike a can kaduna.

   Allah yasa hjy ta fada tana tattara takardun dake gaban ta alaman zata bar falon ke nan nayi saurin mikewa ina karban kayan daga hannun ta.

   Sai naji tana fadin wa zai dinga sauke su a school din kai ko driver zai kaiku ya amsa da fadin.

  Dama ai nike saukesu kafin in shiga office yanzun ma nidin dai ne zan dinga sauke su idan zan fita .

  Ka nema masu driver daga yanzu da zai dinga sauke su kai ka wuce office din ka kaji abindana fada ta juya wurin hjy tana fadin hjy zan shiga in karasa aiki a daki.

    Ni dai na aje kayan na fito daga dakin don babu wani abinda zan mata a lokacin don haka na dawo falon na samu hjy da yaya mamud suna hira Aisha ta shige dakinta ko lokacin.

   Har kasa nakai na kara mai godiya yacs Jafar ne ya saka in sama maki nan don haka shi zaki godewa idan ya dawo.

   Sai ki mai da hankali ki samu abinda kikaje mema banda wasa ko wani hali na banza don Allah.

    Nagode yaya na kara fada kaina yana kasa nake fadin hakan don gabana na faduwa tun lkkacin daya ambaci sunan ya Jafar din.

   Suna ta hiran su da hjy ni kuma ina faman tunanen gargadin hjy a raina a wani bangare kuma ina Allah Allah in ga na fara zuwa makaranta ranan monday din.

  Rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya hausa suka fada don yau gani a class tare da diya manyan mutane don an gwadani na ketare da kyat don su ba wani gata da zaka nuna masu su yarda su kaika gaba saidai idan kokarin kane ya kaika.

   Na mayar da hankalina sosai ga karatuna banyi kawa ko aboki ba kamar yadda naga wasu sunayi a school din koda yaushe ni kadai zaka sama a class din ina bitar takarduna da akai mana darasi.

   Ranan kwatsan mun dawo daga school tun a haraban gidan idona yayi tozali da bodyguard din shi suna tsatsaye waje suna mazurai da idanu don motan mu daya danno kai gidan.

   Gabana ya shiga faduwa haka na daure na shiga cikin part din mu da sanda nayi arziki babu kowa a falon sai tv dake aiki a falon shi kadai babu mai kallo.

    Da sauri na shige dakin mu inda na samu hjy zaune ta idar da sallah la,asar a gurin tana zaune.

    A gurguje na tube uniform din jikina na fada bandaki ban fito ba saidana shirya a cikin wani dogon riga duk kayan da Aisha ta ban ne nake sakawa a jikinao.

   Na fito na o da sallah nacewa hjy zan leka kitchen in fito daga can na zauna abina ina taya su mama kande aiki har muka karasa na dawo don yin sallah lokacin har mami ta dawo tana dakin ta .

    Tunda na tun karo wuein kamshin turaren shi ya daki hancina na tsaya na dan saurara ko yana dakin in koma kitchen in zauna har ya fita.

  Naji banji wani hayaniya a dakin ba na shiga hjy ne zaune ita kade tana ganina take fadin wai ina kika shiga haka daga barin je in dawo naji shiru sai yanzu.

   Har yaron nan ya dawo daga balaguron da yayi yana tambayan ki bai dade da fita daga dakin nan ba.

   Wa ke nan na tambaya kamar ban fahince ta ba tace wanan bayahuden mana jafari ai ya dawo tun dazun da ranan nan wai wata kasa yaje kallon ball kawai don barnan kudi.

  Shiru nayi don ban san me zan fada ba sai kuma hakan yaiwa hjy zafi take fadin anya yar nan kinko damu da yaron nan kamar yadda ya damu dake.

   Don shi da zuwan shi ke ya fara tambayana na fada mai kindan fita sai gashi shiru shiru baki leko ba dakin nan sai yanzu daya fita.

   Ko uwar taku tayi nasara a kanki ne tun yanzu nace hjy dan Allah ki daina zancen shi dani kada mami taji ta riga da tayi min kashedi a kanshi tun a kaduna hjy.

    Ita iyami din hjy ta fada nace hjy kada kiyi mata magana ko dan karatun nan da yanzu nakeyi kada in rasa sa,ata ta wanan dalilin.

   Wai maryama kanta daya kuwa gaba daya yarinyar nan ta rikice min lokaci guda na kasa gane inda ta dosa kan zancen nan.

   Haka mukai ta shan bambam dashi ban yarda mun hadu ko sau daya ba a gidan tundaya dawo garin.

   Ran ba makaranta ina zaune inawa kaina kitso muna hira da hjy ya fado dakin namu daga sallaman shi ya kutso kai ciki.

   Ba daman in gudu in shige koda bathroom ns don ya riga daya ganni ko dole na daure na gaida shi tare damai an dawo lafiya.

  Shima yadda ya amsa min naji dadin hakan don ba yabo ba fallasa gareni sai na mike zan bar masu dakin don dai kawai in kaucewa warning din mami gareni.

    Ki zauna fita zanyi na leko hjy ya fada daga inda yake tsaye yana magana da hjy gashi ya kara haske sosao yayi wani kyau dashi bakin gashin kanshi yayi lub kwace a kanshi sai sheki yakeyi ga wani saje daya bari a fuska  tasa wanda bai saba bari shi a fuska ba.

    Yana gama magana ya sa kai ya fita ya bar dakin gabana sai faduwa yakeyi min don abinda idona ya gane min din duk da ban kalleshi sosai ba ma ke nan.

  Tun daga wanan rana  ban yarda mun kara haduwa dashi ba a gidan don ina ganin shima bai faye zama a gidan ba sosai sai jefi jefi.

   Ranan zan fito daki ke nan don hjy na falo mami tafita gurin aiki bata dawo ba ina ganin shi na ruga da gudu na koma daki a zatona ko bai ganni ba ne.

  Saida ya dan dade a zaune kafin ya mike ya nufi dakin namu hjy dai tana zaune tana kallon shi tare da tausayi  mu a ranta.

   Ya tsaya daga bakin kofa dakin bai karasa shigowa dakin ba sai hannun daman shi dayayi amfani dashi wurin rike labulen dakin dashi.

  Wa kike gudu haka ya fada a cikin muryan nan nasa mai fida sauti mai dadin saurara kunnuwa suka jiyo min hakan.

   A razane na juyo ina kallon shi yana tsaye a kofan yadda yake a wurin wani irin tsoro da damuwane suka ziyarci zuciya sosai take jikina ya fara kyarna ta yadda har ya fahinci hakan.

  Hannun ya sauke daya tokare kofa dashi yana gyara suit din dayake sagale a hannun nasa karya fadi.

   Takowa naga ya fara yi zuwa inda nake 

haka yasa gana ya tsananta da faduwa sosai a haka ya iso inda nake rakube ga bango ginan dakin.

  Wani abu naji yana taso min wanda yasa na duntse idona a hankali kafin ya kara tako ya cin min a gurin.

  Jin kamshin turaren jikin shi gab dani  yasa na bude idona na dube shi kadan babu sauran tako a tsakanin mu ko daya a yadda muke tsaye a dakin.

   Kokarin ja nayi baya sai dai babu inda zan daga don gaba daya ya tare wurin ya tokare hannayen shi a ginan dakin.

  Shiru ya ratsa dakin ba wanda yai magana a cikkn mu kamar babu kowa a dakin lokacin.

  Inan tsakiyan hannayen shi har lokacin idanuwa na a rutse kamar naga dodo a gabana.

  Ga ba hanyar da zanbi in gudu daga wajen don ya hana hakan gareni ya kankame ko wane gefe da zan iya guduwa mashi.  ZAINAB IDRIS MAKAWA


🦅     ABU CIKIN DUHU     🦅2️⃣8️⃣


  ZAINAB IDRIS MAKAWA


  LITTAFIN KUDINE DON TURA KUDI ZAKI TURO GA WANAN LAYIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK DARI UKU NE KACAL KATIN WAYA KI TURA GA WANAN LAYIN 08036959257 

  

   YAR UWA DON ALLAH KI DAURE KINA BIYAN HAKKIN MUTANE DON ABIN BAN YAFE BA KALMACE MAI NAUYI GA MUSULMI NAGODE.Har lokacin idanuwana suna a rufe ga numfashinsa ina jin saukan su a kunnuwana idon na kara budewa don jin shirun da yai yawa na dauka nike haukana a lokacin shi baya ko wurin.

    Yana nan tsaye a yadda yaken haka yasa na soma kokarin sunkuyawa ta kasan hannun shi in samu in wuce don tserar da rayuwata ga mami dashi.

    Ji nayi ya kamoni ya kankame ni a jikin shi tare da mamaye ni cikin wasu irin abubuwan da ban taba tsintar kaina a cikin ba ko a mafalki ban san da wanan nau,in abinba.

   Haka kuma ban taba sanin ana wanan abin ba na dauka sai kafiran turawa da nake ganin haka a film danazo gidan mami.

  Suma din kuma idan sunayi kawar da ido nakeyi koma na tashi na bar wurin ga baki daya.

  Can kasan makogorna na iya furta innalillahi don Allah ya jafar ka bari kada kayi min sanadin da mami zata koreni gidan nan.

    Bai kula da abinda nake fadi din ba yaci gaba da abinda yake min kamar ma zancena ya kara mashi kaimi ne .

  Babu inda baya karkarawa a jikinsa don abinda yake min din nikan na sadakar sai hawayen da ke zubomin kamar an sake famfo na barwa Allah lamarin sa duk abinda Allah ya kaddara min mai kyaune.

    Muryan shi naji a kunne kamar mai rada yana fadin mami kike tsoro yasa har kika fara guduna kina boyewa ?

   Idan mami din ta sakaki ki min hakan ko ta hana ki aure ni kamar yadda na bukata ai ba zata hanani wanan bako ?

   Abinda mami taji ke nan a karshe wurin da take tsaye ta mutu a tsaye don mamakin ganin halin data same mu a ciki a dakin.

   Da sauri mami ta juya kafin ko wanin mu ya ankara mu farga tana gidan a lokacin ta nufi dakin ta da sauri duk maganan da hajiya ke mata a falon bata jita ba.

   Karan sakin kofan da mami tayi ne ya farga damu don dai kawai tsoron  dake yawa a zuciyana ne daya rufemin ido ban farga da ita ba tun shigowan ta dakin.

   Yanzu kan sheshekan kuka na fara mai don na kula in dai ba mami ba hjy tsohuwa ce ta rutsamu a halin da muke ciki.

   Ya jafar don girman Allah don ya rasulillahi ka, , , , , shhh yace tare da fufe min baki da hannun sa na kasa karasa abinda nake nufin fadi karshe.

   I boldly care da duk wanda zai shigo ya same mu a haka dake dakin nan idan su basu san soyayya yada yake ba wanan ni bai taba damuna tunda sun hana min abinda nake so.

   Naji yaya ba zaka taba damuwa ba don kai nan gidan kune bayan hakan kuma kai na miji ne dama mace itace da kunya ai.

   Idan mami ne ta bar wurin nan na tabar da yau ban kwana a gidan nan don ta riga da tayi warning dina tun kan muzo garin nan a kanka.

   Babu inda zaki tafi matukar ina raye a gidan nan doIn ko kin tafi dawowa zakiyi ita mami tasan halina idan ke baki sani ba.

  Ban taba cewa ina son abu har in sashi a raina ban in rasa samu wanan abin don haka ba zan soma shi a kanki ba.

  Naji amma don Allah ka barni in bar gidan nan yanzu tun mami bataji wanan maganan ba yau ta kasheni gidan nan.

   Don girman Allah ka daga,  daga nan in fice na fada cikin wani irin kuka daya zo min mai karfi.

   Maimakon ya daga daga wurin saima naji yana kokarin kara matseni a jikin shi.

   Kayi ma Allah kaimun alfama na hadaka da girman iyayyen ka ka daina rike ni haka kana hadani da fushin ubangijin mu.

   Ka rabu dani ya jafar ka kyale rayuwana hakana ya huta da wanan ukuban daka sakani a cikin sa yanzu.

  Ka taimakeni ka taimaki rayuwana da kake shirin rusa min yau karatuna shike nan na rasa shi tunda mami kauye zata mayat dani ina gap da gamawa.

   Nima ki taimake ni zainab don ke kadai zan aura a kasan nan in zauna lafiya dake bani na sawa kaina son ki ba Allah ne ya zaba min ke don hakkurin ki da tarbiyan ki.

   Abu daya nake so dake shine ki daina cewa zaki bar gidan nan ko karatun ki zai tsaya ba wanda zai faru daga insha Allahu.

    A razane na dago kai na kalle shi kafin in mayar da kan kasa don kwarji da nauyin da yai min ga kallon shi.

   Ya daga min gira yana fadin nasan mami zata yarda da bukata na idan na kafe a kanki a cikin sauki.

   Don farin cikin ta shine nawa itama nawa shine nata bata taba hanani abu nayi shi ba a duniyan sai wanan karon kinga ko zatayi min adalci a nan.

   So da sannu mami zata fahinta ta yarde mana muyi aure in dauki mu tafi can inda zaki karatu sai kince kin gaji da karatu a rayuwan ki.

    Wani irin takaicin sa da tsanar sa yake tokare min zuciya ga tausayin kaina danakeji nida kaina  kamar in dora hannu aka in ta kurma mai ihun a dakin sai anzo an ceceni.

    Sai da ya fahinci ya gama hada min zafi akaina don kansa ya janye min daga banga bangan dayi da farko ya tare ko ina da zan iya sulalewa in gudu daga tsayin dayayi a gaba.

  Kamar jira nake ya nuna min kofa in gudu aiko yana nunawa na sheka da gudu ina kuka mukai karo da hjy a kofa da tazo shiga kamar.

    Duk da nayi murnan ganin ta amma naji haushin da sai yanzu ta zo dakin duk dadewa da mukayi a tsaye tare dashi zuwan ta yai min kama da zuwan yan sandan indiya da sai an gama cin gari suke isowa.

  Fadawa nayi a jikin ta ina kuka take ta rude a wurin tana fadin a rikice maikai mata jafari na fadama kabi yarinyar nan a sannu akwai kurciya a tare da ita yanzu sai ka lalabata tukunna.

   Ask her idan nai mata wani abin just magana nayi mata kan guduna da takeyi kawai.

   Ba dole ta gujeka ba kaida uwar ka kun saka yar mutane a gaba haka wanan hattaran yai wa yar nan yawa a gidan nan.

   Ai saika tashi kaje don uwar taku ta dawo har ta leko nan baka sani ba kana nan kana gyara kanka a wurin mace.

  Hjy kefa kikace sai na jata a hankali zata fahinceni na fara hakan kuma laifine yanzu hjy ?

   Laifine kan indai zaka dinga sakata kuka haka ko wani lokaci murmushi ya sake mai laushi yana kada kai tare da fadin well i know what to do next barin leka mami ya fada yana mikewa har lokacin ina a jikin hjy ina dan sheshekan kuka.

   Yana fita daga dakin na dago kai ina fadin shike nan hjy yau zamana ya kare karatun da nakewa murna ya tafi daga gareno don mami korata zatayi yau gidan nan.

   Saboda kawai kun kebe dashi a nan zata kore ki hauka tayi kome daga haka sai kora kawai.

  Hjy mami tayi warning dina tun a kaduna kada in yarda in tsaya da danta don ta riga da tayi mai mata ko.

    Ita iyamin ta fada maki hakan na gyada mata kai kawai ba baki idan ma har ta fadin hakan ai yanzu bake kika bishi ba shi ya biyo ki ko sai tayiwa danta fada shida ke binki.

   Dakin mami ya nufa direct ba tare da jin komai a zuciyar shi ba duk da hjy ta fada mai mami ta leko dakin mu yana ciki yasan kuma ta ga halin da muke ciki a lokacin.

    Da sallama ya leka dakin ba,a ansa ba haka yasa kai ya shiga dakin mami ya hango a zaune gefeb gado tayi tagumi da hannayen ta dukka biyu kamar wacce ke cikin tsananin damuwa.

    Ta rasa abinda ke mata dadi a duniya yaron nan wani abin kunya haka yake son jawo mata ne duk ita a zaton ta ya bar wanan zance ashe shi yanzu yakema ga zancen wata namiji dai sai a barshi ga abinda yake so ya kwallafa rai kuma.

    Kallon mamaki yake mata har ya karasa bakin gadon da take zaune a kai yace mami lafiya kuwa na ganki a haka ?

    Wani abu ya faru ne ko wani abin kike tunane haka ke kadai a daki kinyi tagumi.

   Ido mami ta dago ta gallamai harara da idanuwan ta da suka kade sukai ja tankar zasu fado.

   Ji take kamar ta wanka mai mari da tana iyawa a yanzu so yake ya tozarta ta ya kunyata ta a idon kawayen ta tozarta.

    Maganan hjy da take tunawa guda biyu shike taka mata burki ga koran yarinyar nan ta koma kauye.

   Saidai idan ta tuna da kalamin hjy da take fadin idan ta kori yarnan a gidan ta sai danta yaje gun iyayyen ta a bashi ita ya aure muddin yaje da waliyan shi makusanta ita kuma a barta tana hargowa a gida. 

    Ga kuma barazan hjy data ita kuma idan ta matsa sai ta dauke yar ta koma da ita wurinta ta inganta rayuwan ta fiye da tsamanin ta to me hjyn ke nufi da hakan.

   Hannun ta ya riko don yaga ko a yanzu da take kallon shi hankalinta na ga tunanen da takeyi a lokacin.

   Riko hannunta yayi yana fadin haba mami meye zai sakaki irin wanan damuwan haka kinsan fa yanzu aiki na maki ya, , , , 

     Baiyi aune ba yaji saukan mari a lafiyayyen  fuskan shi lokaci guda ya dago kai da mamaki yana kallonta da kyar ya iya furta mami you slap me ?

   Ko zaka ramane tunda yanzu ka girma har bakajin umurnina kake ganin kaika isa har yanzu kake mamakin na mareka ko ?

  Allah yasa yanzu da idona na gama ganin ku da kazaman yarinyar nan a dakin hjy ba wani ya tsegunta min hakan ba.

  Yanzun kai bakaji kunya ba ace kamarka jafar kamar kafa kamar kake rugumar wanan kazaman yarinyar zainab yarinyar da wani lokaci ma tsami takeyi da wari.

    Da sauri ya dago kai a karo na farko tun bayan marin data kwasheshi dashi ya dukar da kanshi bai daga ba yana dafe da wurin cikin mamaki.

   Wari mami wari fa kikace yarinyar nan tanayi ban taba jin haka ba a tare da ita asalima ni yau wani kamshin ma naji a wurin ta.

  Mami nifa kome takeyi ina sonta hakana da don itace zabina a duk yadda take ya fada yana kokarin mikewa tsaye.

  Jikin mami ya sake yaraf kaman ruwan sanyi  a gabanta yau jafar ke wanan magana kan mace macen ma wai yar aikin gidan ta wanan wani irin lalacewa ne ya kama dan nata haka?

   Ganin ya soma batrin dakin don tafiya don marin ma datayi mai shiko a jikinshi ya yadda nunata take ta soma magana tana fadin.

   Yau da uban ka yana raye jafar zakai min haka ince ga wace nake son ka aura kace kai ba hakan ba yaushe ka fara wanan halin banzan na kafi ban sani ba ?

   Mami daddy , aiko daddy yana raye ba zai hanani zaban abinda hankalina ya kwanta gareshi don dama daddy yana raye aida yanzun akaiga matsaya ga zancen nan don shi daddy ban taba ganin ya kyamaci wani a rayuwan shi ba

  And mami kin san koda daddy yake da rai mun fi shakuwa dake fiye da daddyn mu

   Mami kin kasa fahintana ne kin kasa tausa zuciyar ki akan yarinyar nan why mami zaki hanani abinda nake so.

   Ba zaka aure ta ba nace bazaka aureta ba ko dole zakai matane mu gani idan zaka iya No mami ba dole amma nasan itama tana sona don naga alaman hakan tare da ita.

   Tsoron warning dinki gareta ne take amma ba matsala zan gwada sa, a ta tunda kinban dama a yanzu.

   JAFAR mami ta fada da karfi ya fice dakin ba tare daya juyo ya kalleta ba tunda mami take da danta haka bai taba faruwa a tsakanin su ba sai akan wanan dalili.

   Me yaron nan yake nufi dani da wanan kalamin nasa tursasa yarinyar nan zaiyi taso shi tunda a yadda ta samemu a dakin da alaman tsoro shi a fuskana don kuka ta samu ina masa.

  Ma,ana dai shi jafar din ne ke bibiyan ta a dole meya gani ajikina har ya mace ga son yar nan haka.

    Yarinyar da saida tazo nan ma tadan yi wanan clean din da yake rudin shi ta runtse idanunta tana mai fadin kada Allah yasa so ya rudi yaron na  ya aikata wani abinda zaija mata kunya ga idon mutane.

   Ya zama dole ta jashi a jiki tasan hanyar data bi ta lalashi da lalama ya janye kudirin shi akan yarinyar na don koranta gidanta baida wani fa,ida a yanzu idan tayi amfani da maganan hjy.

   Zeey bata da laifi ta sani amma wanan dalilin ya jawo mata tsanar yarinyar ba gara ba dalili taji yarinyar ta fita mata rai ga baki daya ta wanan dalilin.

   A dakin mu hjy ta samu ta lalabe ina kwance lamo sai faman ajiyan zuciya nakeyi ga tunanen abinda ya faru tsakanin mu yaki fita a rai.

    Duk motsi nayi sai inga kamar a lokacin abin ke faruwa dani uwa uba ga kamshin turaren jikin shi daya dameni a hancina yana kokarin saukar min da kasala a jikina.

    Mikewa nayi zubur hjy dake zaune ta kalloni tare da fadin ina zaki ban daki zan shiga inyi fitsari na fada.

   Na shiga ta bini da kallon tausayi tana gyada kai Allah kadai yasan yadda take ji a zuciyar ta kan yaranan a yanzu.

    Na dan jima a ciki kafin in fito rike da digana dana cire ina daure da tawul a jikina wanda nake kewayawa dashi don a dakin muka same shi wani babba haka dashi fari mai kyau da yan flawer a jikin shi kanana a gefe.

    Dogon rigar yar katin da anty safiya ta saya min da zanzo gidan mami na jawo na zauna saman kujera ina dan shafawa jikina mai don kada in bushe.

   Au yar nan wanka kikayi gabanin magariban nan kudai yaran yanzu baku da tadan lokacin yin abu.

   Hjy na magana tana kallon gashina da har lokacin yana tuke babu kitso a kaina sai fibon dana daure gashin dashi ta bayan kaina.

    Kafin ta mayar da kallonta da kyau a inda nake tanaci gaba da fadin yadda kike nan da tsari irin hakane mutanen boye ke so su shige jikin mutum a sauke.

  Mutanen boye kuma hjy na fada ina juyowa gareta tace kwarai kuwa yar nan ai su abinda sukw so ke nan urin wanan sakacin da kukeyi a yanzu take sun shigeka suyi maka illa.

   Kinga mu a zamanin mu duk irin wa yan nan abubuwan musanshi iyayyen mu na fada muna mukiyaye don tsaron lafiyan mu.

  Hjy daga yau na daina ba zan sake kewaya a wanan lokacin ba in Allah ya yarda tace dadai yafi maki kam.

   Waini meya hadaki da mutumin naki ne dazun kike ta wanan kuka ina saka riga a jikina da sauri don maganan da tayi naji wanan maganan.

    Juyowa nayi da a daidai ina karasa saka rigan na dauki hulan dana dora saman gado na dawo kusa da ita na zauna tare da dan marairaicewa nace hjy ki taimake ni ya jafar yafita daga tsabgata a gidan nan don Allah idan ba haka ba mami zata koreni ta fada.

   Kin taba ganin inda aka cirewa mutum rai ga abinda yake so farat daya wanab sai uwarku da take ganin tana iya hakan.

    Wai yau dai ki fada min yar nan shin kina son jafarin nan ko bakya son shi inji da sauri na dago kai na kalli tsohuwar sai kuma na dukar da kaina kasa don bansan amsan da zan bata ba.

  Ince ina son sa in kaishi ina ko ince banson jinin ta kiri kiri haka a gabanta anya zataci gaba da sona nima duk da nasan tun kan haduwan mu da jafar din tsohuwar take nuna min kauna sahihi.

  Sai kuma yanzu da take nuna min kauna tankar itace ta haifi iyayyena ta san zafina fiye da kowa ta yaya zan iya bude baki ince banson jikanta mafi soyuwa a gareta ido da ido haka.

  Nasan wani abu yanzu ma saboda shine ta tsaya min take tsare min komai a gidan yadda ya dace.

  Murmushi naji tayi tana fadin to ai abu yayi kyau takwara shiya nake kara sonki saboda halin nan naki na alkunya ga kuma girmama mutum saidai iyami taki gane hakan .

    Ke din wani baiwace a garesu takwara naso iyami ta gane hakan amma idonta ya rufe ta kasa hangon hakan da kanta.

  Nidai har ta gama maganan daidai ana kiran magariba ga agogon dake dakin namu ta mike da sauri zuwa bandaki do  bata wasa da ibanda ta kiran sallah kawai ta kan jira ta mike ko wani lokaci.

   Bayan kowa ya kammala komai aka fito cin abincin dare kamar yadda aka saba da kyat hjy ta shawo kaina na yarda na fito daga dakin.

     Mun samu mami a falon har ta fito tana zaune tunda muka tun karo wurin ta dago kallo daya tayi min ta kawar da idon ta gareni tana fadin hjy kin fito yanzu nake zancen ko lafiya yau baki fito da wuri ba haka.

    Muna daki nida mutumiyar ina bata labari  mutanen da can yadda suke rayuwan su ga wuri hjy ki zauna tana fadawa mahaifiyar nata cikin girmamawa gareta.

   Kafin ta dago kai inda nake tana fadin cikin bada umurni ke jeki aka hijabi a jikin ki baki ganin gidan nan akwai samari ne kike fitow haka dake.

    Ya ilahi nikan ko me zanyi mami a yanzu bata ganin haske na na juya naji hjy na fadin zancen banza ke nan yo ai shigarta yafi naki dana yarki mutuntuwa bakiwa wanan mai zama kamar arniya a gida ba haka kai babu hula ko dan kwali sai wanan da jikkn ta yake a suturce.

   Hjy mu muharamin si ne ita fa irin shigar da ta dauko yi ke nan har yaro  nan ya jefa kanshi a tarkon ta.    Ita yar nan din tasan ta danawa wani tarko da ace hakan take da baki fada ba da bakinki yanzu don da kin gane kabewa ruwane.

    Tsohuwar ta juyo gareni tana fadi  jeki ki saka hijabin ki dawo muci abinci nikan ina shiga dakin ban kara fitowa ba na neme wuri na kwanta ina sharan kwalla.

   Abuja ba kaduna bane don ko sunan uguwanin su ban gama sani ba sabanin kaduna da tun ban shigo shi ba nake jin sunaye unguwanin cikin shi a bakunan mutanen kauyen mu.

    Ina barin wurin mami ta mike ta nufi dakin dan lelen ta a karo na farko tun dawowa shi Nigeria don ba dabi,an ta bane zagaya dakin samari  nata.

   Kofan dakin yana rufe ta murda taji shi a ruwa saidai karan tv dake aiki ana wasan kwallo tana dan iya jiyo hayaniya daga inda take tsaye.  ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅  ABU CIKIN DUHU  🦅2️⃣9️⃣  ZAINAB IDRIS MAKAWA


LITTAFIN KUDINE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON TURA KUDINSA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL A WANAN LAYIN  08036959257 NAGODE GA WANDA YASAN ZAFIN ABINDA NA FADA.Da mamaki ta juya don a zaton ta yana cikin dakin sai dai bataji alaman mutum a part din ba haka ta dawo dakin ta ta nufa direct .

    Har ta zauna ta bude system dinta da niyar tayi aiki a cikin sa sai zuciyar ta ba zai barta tayi abinda take so ba a lokacin.

   Har dare duk wanda ya shigo gaida ita tana tambaya idan ya dawo sai suce basuga shigowan shi ba kuma security din shi basa nan saidai ga wayan shi na shiga kuma karshe taji wayan a kashe.

   Washegari wanan dalilin ya hana mami fita aiki da wuri ni dai nagama mata komai tana bandaki kafin ta fito na karasa na fita daga dakin shiryawa nayi a gurguje kar driver dake kaimu school ya jirani.

   Mami ta gane me nake nufi don ta fahinci tun jiyan ina gudinta don ban fito ba ita kuma bata tambaya ba duk ta san banda laifin kan hakan amma zuciyar ta ya kasa daina jin haushina.

   Zazzabi mai karfe gaske yake ji a jikin shi tunda ya falka da safe da kyat ya iya shiga bandaki yai wanka ya fito yayi sallah asuba ya koma ya kwanta.

  Mami ta fito daga dakinta ta samu hjy zaune a falo ita kadai tana kallo wa,azi da takance kafin mu kai mata kafin mu fita da safe.

   Mami ke fadin hjy tun jiya banga shigowan jafar ba ko kinga fitan shi da safen nan da mamaki hjy ke fadin yanzun nake maganan shi a raina ni kadai.

   Ko tafiyan yayi babu salma kuma wanan karo  ma mami ta dan yi tunanw tare da fadin anya don bai dade da dawowa ba da wuya ya sake fita.

   Part din shi ta nufa tana fadin bari in dubashi ko yana ciki har yanzu idan ba fita yayi ba.

   Murda kofan tayi taji kofan a bude yake haka ya bata daman shiga dakin kai tsaye tsab falon yake kamar kullun sai kamshin dake tashi a cikin sa.

    Cups har biyu ta gani aje saman dan table din glass din dake gaban kujera sai fararen takardu dasu laptop a gefen kujera aje.

  Kai tsaye ta nufi dakin kwanan shi ta fara kwankwasa kofan ta fara kwankwasawa sai gana ukune ya amsa da kyar ya iya yin magana ya tambaya da waye ?

    Nice ta bashi amsa a gadarance ba tare da ta kara furta wani abuba a kai.

   Kofan a bude yake ya fada yana kokarin cire bargon dake jikin shi rufe mami ta tura kofan ta shiga daga cikin dakin.

   Ta hango shi yadda yake kwance saman gado ya dan rufe rabin jikin shi da bargon.

  Lafiya kake kwance haka a rufe tun dare baka leko muba baka kuma shigo da safen nan ba mami ta fada tana karasawa bakin gadon nasa tana zama.

    Sai daya dan dago daga kwancen cikin yanayin yamutsa fuskan shi yace yau bana jin dadi ne amma yanzun nake son in shiga.

    Baka jin dadi shine zaka kwanta a daki kai kadai haka ba wanda ya sani kamar karamin yaro mami ta karasa fadan nata da tambayan wai meke damuwan kane.

   Cikin dauriya yai magana da kyat yana dafe kirjin shi mami ina jin kirjina na ciwo da zazzabi.

   Wani kallo tayi mashi kafin tace dashi ai saika tashi kaje likita ya dubaka ko ?

    Mami ba sai naje asibiti ba nasha magani dazun da zan kwanta tace ka karya ne da kasha maganin ?

   Baida matsala mami yanzun zan fito ya fada yana maida kanshi ga filon da ya dago akai.

   Ido mami ta dan kura mai kafin tace zaka jawa kanka matsala akan wanan yarinyar har da kwanciya ciwo don kawai na fadama gaskiya.

   Murmushi kawai ya danyi tare da lumshe idanun shi ba tare daya iya mata magana ba ta mike tana fadin idan ba zaka iya fitowa insa lami ta kawo ma abin karyawan ka nan ka tashi ka karya ko zakaji saukin jikin.

   Sai lokacin ya iya magana yace ba sai ta kawo min ba mami zan fito da kaina ai ya sake lumshe idon shi a hankali.

    Mami a cikin dakewa take da karfin hali a lokacin don gaba daya hankalinta ya tashi ga halin data samu dan nata a ciki wanda take tunanen maganan su najiyane yaja masa wanan kwanciyar haka.

   Hjy na zaune falo tana dakon fitowan hjy sai gata tun kan ta karaso take tambaya kin same shi a ciki ?

   Yana nan hjy wai ashe baya jin dadin jikin sane yakw kwance daki shi kadai bai fadawa kowa ba.

  Subbahanallahi me ya sameshi haka har yaron nan yake kwance bamu sani a cikin gidan nan.

   Ciwo yake son jawa kanshi kawai hjy don nayi masa fada jiya shine yake wanan ciwon don batacin zaijawa kanshi ciwo ya halaka kansa akan abinda baikai ya kawo ba.

   Hjy bata ba mami amsa ba sai mikewan da tayi tana fadin bari na leka shi inga halinda yake ciki tabar mami na kiran lami daga falon.

   Dakin shi hjy ta nufa daga kofa ta tsaya tana kwala sallama daga can ya jiyo muryanta ya yunkura da kyar ya taso zuwa falon.

    Da kyat ya iso yana kokarin zama saman dogon kujeran tare da fadin hjy kin tasone yanzun nake son tashi in shiga mu gaisa dake ai.

   Kai da baka da lafiya aikai ya kamata azo a duba koda yake uwarka tace kaine kajawa kanka ciwon bansan dalilin ta na fadin hakan ba.

    Hankalinshi yaji ya kara tashi lokaci guda idon shi suka kada sukai jawur gashi abinda yake ji a zuciyar shi kamar ya fita a lokacin ya aikata saidai baison ya biyowa mami ta wanan hanyan da yake ganin ranta zai mugun baci a karshe.

   Gashi hundred pacent ya amin a zuciyar shi da zabinshi yasan da farko ba son yarinyar yakeyi har cikin ranshi ba.

  Illa tausayinta da taimakon kanshi ya zauna lafiya a rayuwan shi don itace kawai fufin asirin shi a rayuwan shi.

  Zai iya samunta da sauki fiye da wace mami ke shirin aura mai yasan ko wacece indai yaran ire iren kawayen mamine dole idanun yarinyar a bude yake itama.

   Sai dai kuma daga jiyan da mami ke kara ikirari akan ya janyewa yarinyar nan zeey abinda ya faru tsakanin su yasa yana jin wani irin feeling yana matukar jin yarinyar a ranshi.

   Fiye da yadda bai taba tsanmanin faruwan haka ba a tsakanin su  tunda yake mu,amulan shi da mata a rayuwan shi badai wani abune ke shiga tsakani su ba sai dai hugging da dan kiss a tsakanin su kawai.

  Hannun shi yakai a kai yana dan shafan kanshi tare da jin wani wutan son yarinyar na kara ruwa akansa.

  Tankar yadda wutan kara yake kamawa gadan gadan yana saurin yaduwa a duk lokacin daya kama a cikin jeji.

  Jafari ka sassauta zuciyar ka kabi lamarin nan a sannu kamar yadda na fada ma da farko kada kajawa kanka ciwo idan har iyami bata yarda da bukatan ka a cikin lalama ai tana da magabata ko, wa yanda zaka iya gani bayan ita.

   Saida ya sanye harshen shi ya lashi labbansa da suka bushe masa yana cike da takaici da kunan ran wanan lamarin da mami ta bijiro masa.

   Kafin yace hjy mami bata sani ba idan har tace a yanzu ba zata yarda da zabina ba sai dai in fasa auren duk wata yarinya da take fadin zata hadani da ita a kasan nan.

  Ni namiji ne fa ina da daman da zan zabawa kaina abinda nake son rayuwana dashi don ba wani ne zai zauna da ita ba saini.

   Ta bangarena ranan dai naje school ne amma babu abindana iya tsinta a cikin abinda akai muna don tune biyu daya tsaya min a rai.

   Na farko shine mami yadda take min din nan abin ya fara tsoratani sosai duk a kan danta take nuna min wanan kyamar dana kasa gane dalilin ta nayin hakan gareni idan nayi dubaiya ga yadda muke da, da ita.

    Amma sanadiyar bullowan wanan maganan gaba daya mami ta sauya min ga sabon halin disgani ko agaban waye data dauko yi min yanzu wanda hakan ya fara taba min zuciya duk da ina yarinya.

   Sai nabiyu abinda ya jafar yai min a jiyan ya tsoratani matuka gaba daya ya dasa min tsoron shi a zuciyana.

    Haka muka dawo gida ina a cikin damu tun daga ranan na daina fitowa falo idan ina gidan har ma in na fito sai idan zan shiga kitchen dauko abinci ko wurin su mama kande mudan taba hira.

   Gashi tun ranan ban kara saka yaya a idona ba saidai nasan yana gidan ba tafiya yayi ba don ina ganin security din shi da safe idan zamu tafi makaranta.

  Ta hakan na gane yana gidan bamu dai haduwane dashi ko kuma mami ta shawo kanshine ya yarda zabinta gareshi.

  Yanzu ya gane niba ajin sa bace ya wuce ajina ga aure saidai diyan manya irin su can irin wanda mami keson ya aure har hakan ya jawo matsaloli a tsakanin mu.

    Na fito ina tafiya kamar yadda na saba zakace ko ina tsoron kasa ne yadda nake takona,  ga uniform din jikina sun karbeni sosai.

   Kamar ance in daga kai in kalle saitin dakin ya jafar daga inda nake tsaye jikin mota ina jiran fitowan yaran yaya mamud mu kama hanya.

   Caraf idona ya hadu da nasa daga inda yake tsaye jikin aindon shi yana sanye da bathrobe a jikin shi ya bude gaban rigar yadda zaka iya hango six pack din shi na kiran maza a waje.

   Yana rike da cup din farin glass a hannun shi idanun shi a kaina da sauri na juya na bashi baya daga kallon shi da gujewa nashi ganin kuma.

    Kai ya girgiza cikin dan murmushi yana mai jin dadin yanayin danayi din don shi abin nawa ma dariya yake basa ko yaushe a yadda nake nuna tsoro idan na ganshi.

    Yasan bayin kaina bane hakan mami ce ta riga da ta dasa min tsoronta a raina akan shi don hakan dole inyi hakan don tserar da mutuncina a furin mami din.

   Har muka shiga mota yana tsaye a gurin yana dan kurban abinda yake sha a hankali a cikin cup din.

   Sai da motar mu ta daga na sauke wani irin nauyayyan ajiyan zuciya a fili tare da lumshe idona a hankali ina mai jin wani iri a raina.

    Haka shima ya jafar din bai daga, daga wurin ba saida yaga motar tamu ta bace ga ganin shi ya sauke wani irin ajiyan zuciya lokaci guda tare da juyawa yabar wurin da sauri.

    Mami na zaune dakin ta tana shiryawa adaidai lokacin yayi sallama ya shigo dakin direct inda take ya nufa ya danyi hugging din ta.

   Tare da fadin morning mami kanshi ta shafa tare da fadin dan albarka ka tashi lafiya lafiya kalau mami ya fada ya koma bakin gadon ya dan kidinshida tare da daga kafan shi daya yana duban wayan shi.

   Friend wai gaba daya ka sauya dabi,un ka yanzu har abincin dare ka daina zama dani muci ka kuma san wanan time din ne kawai nake dashi danake dan kebewa daku.

   Tunda ba fitowa kake da safe ba kafin in wuce wurin aiki balle in ganka shiru yayi bai bata amsa ba sai ta dauka hankalin shi yaga wayan hannun shine hakan yasa ta juyo tana kallon shi.

   Saidai ganin sabanin hakan garshi lokacin data juyo din yana kallon wani wurin na daban tare da yanayin tunane a fuskan shi.

   Friend wai me yake damun kane haka ina magana ka lula wani duniyan tunane me kake tunane hakane wanan kwailar yarinyar zeey ka saka a zuciyar ka ko ?

   Kan shi ya dago a hankali ya dubi mami tare da fadin babu komai mami me kika gani halan.

   Kai ta girgiza tare da juyowa gareshi gaba daya tana fadin babu yadda za ayi kace babu komai duk mutum mai hankali da zarar ya dubeka yasan kana cikin yanayi na damuwa.

   Amma dai tunda ba zaka fada kuma ni nasan zancen yarinyar nan ne har yanzu ka saka a ranka kamar yar wani da wata.

  Kai yanzu kana ganin kafanka ya kama kasa ban isa kai min abinda nake so kayi a matsayina na mahaifiyar ka  balle har kace ba zaka fada min abinda ke tsoce ka ba sai dan dogon wuya kake ajewa kanka.

   Mami na fada maki bani tare da wata matsala kirjinane kawai har yanzu bana jin dadin sa zancen zeey kuma aini na fita wanan zancen yanzu, don shirin komawama nakeyi tunda an fasa zancen auren kince bakyayi da zabina sai a fasa auren a yanzu sai na laluba wata kuma.

  Mikewa mami tayi tana fadin kaima kasan hakan ai ba zai yuyu ba ka koma ba tare da aje iyali ba .

  To mami ki bari in auri zabina don shine rufin asirin daki dani daku ga baki daya ba ko wace mace bane zabin namiji ko wani namiji da kalar macen da yake so a rayuwan shi.

    Haka kace ke nan ni bansan abinda zuciyar ka keso ba ke nan na zaba maka nawa ra,yin ko to tashi ka ban wuri .

  Ga mamakin mami sai taga ya mike don barin dakin kamar yadda ta umurceshi ya bari din.

   Har ya fice daga dakin mami tana binshi da kallon mamaki da tsoron abindaya fada yanzu a gabanta wanda ta kasa gane me hakan da yaron nn ke fadi yake nufi ne ?

   Ya dan jima tare da hjy a falo suna fira inda yake fada mata zai koma bakin aikin shi bada dadewan nan ba.

   Hjy ta dago kai tana fadin har tafiyan ya karaso ke nan yaya zancen auren naka don idan ka koma a yanzu wayasan ran dawowan ka wanan kasar jafari ?

   Hjy zan dawo a daidai lokacin daya dace sai dai wanan sirine tsakanina dake ki kula min da yarinyar nan yadda ya dace zan dan barta ta kara wayau da sanin kanta.

   Yanzu zan nunawa mami ni yarinyar bata gaba sai daidai da lokacin daya dace in dawo gareku da wanan zancen zan dawo da nuna mata gaskiyata.

  Ban fahinci maganar kaba jafari tsohuwar ta fada yacs zaki fahinta hjy don koma  a bayane zaizo maku hjy.

    Mikewa tsaye yayi yana kallon agogon hannun shi tare da fadin zai soma tafiya a rude tsohuwar ke fadin don Allah dan son manzon tsira ka saurareni kada ka je ka dan dakata mu kara fuskantar iyami na dan lokaci.

    Shu,umin murmushi shi kawai ya sakar ma tsohuwar ba tare da ya tsaya ya furta wani abuba akai yai mata Allah bamu wuni lafiya yasa kai ya fita daga gidan.

  Ashe hjy ta samu mami ta yi mata tas akan ya jafar tare da lurar da ita halinda take son jefa danta a ciki takare da fadin idan kin kashe shi ko kika bari ya tafi yabar kasan nan kan wani dalili naki can baku fuskanci juna ba kanki zaki tarawa bakin ciki.

   Shi auren gatan da kike fada bashi bane kukaiwa mamud yanzu ki fada min dadin da kukaji a cikin wanan hadin na mamuda din.

    Ke kanki ba dadin yarinyar nan kike ji ba ina gani sai taga dama take shigowa nan koshi sai da wani dalili mai kwari shi mamudan basai ya fada ba da ganin sa kasan a tauye yake da ita duk dai saboda ku a gidan nan.

    Iyami da zaki gane abinda nake nufi a nan da sai ince ki kyale yaron nan ya auri zabinsa tunda dai hakan ba haramun bane.

  In kin hanashi auren wacce kika san halinta ai zai kwaso maki fitsarariya da zata zo ta wargaza maki gidan ki.

   Kindai ji ikirarin da yaron nan keyi a gaban ki  ko yaushe da yarinyar nan itace daidai dashi kinsan abinda hakan ke nufi a zuciyar shi ke baki kwantawa ki auna me hakan da yake fada ko yaushene yake nufi.

    Maza fa ba ayi masu dole ba kamar mata suke ba su ki barshi da zabin sa abinda yagani da idon sa yace yana so.

   Ai gara wanan din ma daya zaba kinsanta kinsan ta kinsan halinta ciki da bai kina yi tankwasa ta aduk yadda kike son ta ba kamar wanan ta wurin mamudan ba.

   Sannan har idan itama yarinyar nan ta kamu da son yaron fa kinga kin zalunce su tunda itama a karkashin ki take.

   Har in kina gudun tayar da alkawari ne ga iyayyen wacan da kika nema masa ki barsu dashi shida kanshi zai nuna masu halinshi ita din ba zabinsa bane amma ina amfanin ayi abu adawo ana danasani akansa haka.

    Iyami ki rabu da dan yau idan ya furta baison abu to ki kyaleshi yai wanda yake so matukar ba abinda zai sabawa mahaliccin shi bane abin.

  Gaba daya jikin mami yayi sanyi lokaci guda hankalinta da natsuwa suka zo mat lokaci guda ta bude baki tace hjy ni kaina kalamin yaron nan yana sakani a duhu ko yaushe idan na zauna nayi tunane mai kalman nan da yake yawan fada min haka yake nufine gareni .

   To kin gani ABU A CIKIN DUHU SIRINE  shi yasan me hakan ke nufi ya kuma barwa kanshi sirin abin a zuciyar shi maza ba kamar mu mata suke ba yaron nan shi yasan me yagani gun yarinyat nan ya dahe mata har baijin kwabon ki a yanzu.

  Hjy zan ga iyayyen yarinyar mu zanta zancen dasu in Allah ya yarda hjy tace ba sai na shiga zancen ba ke nan yanzu.

    Hjy basai kin kara magana ba in Allah ya yarda zan zauna da yan uwana muyi duba dakyau  ki barmu da kaina zan gyara kurakurena zan shirya komai.

    Hjy tace koke fa Iyami Allah yayi maki albarka ya daukaka maki zurian ki ya kare ku daga sherin makiya da mahassada.

  Naji dadi kwarai da kika fahinci mai nake nufi kafin wani abinda ba a so yazo ya faru kan maganan nan yanzu.

   Duniya yanzu idan zaka biyewa mutanen cikin ta ba zaka taba aikata daidai ba a rayuwan ka sai a baka gurguwan shawara idan ta kwabe adawo ana zunden ka a baya.

   Sai yarinyar nan ya zama dole yanzu ki gyara mu,amulan ku da ita tunda kin riga da kin bata komai a tsakanin ku don dai yarinyar ma mai hakkurice da sanin yakamata.

   Ba kowa bane za a nunawa hakan ya iya shanyeshi a zuciyar shi ki gyara tsakanin ku kada yazo ta rike abin a ranta ki nuna mata mu ba butulai bane kuskure aka samu a baya hakan ya faru.

   Nayi mamaki sanin kankine aurene fa yarin ga yace yana so da yar nan taki don yarinyar ta zama yarki halal malal  sanan aure sunnan ma,akin Allah ne.

   Bai kamata kiyi shishigi da nuna iko a cikin lamarin aure ba hakan nan kizo ki mutu akuma yi wanan auren idan da rabo a tsakanin su azo ana fadan da baki mutu ba ba za,ayi wanan auren ba.

  Idan ma baki mutum ba ayi ba acikin yardan ki ba kikuma gansu a tare da babu yadda zakiyi da hukuncin ubangijin ki a kansu.

  Wani hawayen bakin cikine ya zubu a idon mami lokaci guda tace wallahi nima hjy na rasa me yasa bana son wanan auren ko nayi niyar barin shi yayi abinsa.

   Don zeey har ga Allah abin asone a gida dubaga irin hakkurin yarinyar da sanin yakamatan ta kamar ba karamar yarinya ba da ita.

   Gata abin tausayi to hjy na rigada nayiwa hjy saude alkawari akan yar ta duba da yadda muka dade da ita muna amintaka yau ace naki hadin da take so a tsakanin mu.

   Hjy tace ai itama ta haifa tana dasu ba zataki abinda danta zaiso ba har in son gaskiya take maki bazata taba ganin laifin ki kan zancen nan ba.

  Tunda ba kece maiyin auren ba wanda zaiyi yace yarta batai mashi ba sai dai tayi hakkuri yanzu kan.

   Tana fadan haka ta mike tana fadin ni zanje inyi alwala inyi nafila lokaci na kure min.

  Nan tabar mami zaune da dinbin tunane a ranta na yadda zata bullowa wanan al,amarin da yaronta ya bijiro mata dashi a yanzu.

   Don ko ita dadin tane ta sani nan gaba don samun yarinyar garesu ba karamin alheri ba wurin jafar sai dai kawai ace babu good backgraund gareta ne na iyayyen da suka isa gare ta shine kawai abin duba.  ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅   ABU CIKIN DUHU   🦅3️⃣0️⃣  

ZAINAB IDRIS MAKAWAYAR UWA BARKA DA WARHAKA SHI KO KINSAN LITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH DON KAUNAN ANNABI IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KASADAN KARANTA SHI DON KINSAN BAKI BAN HAKKINA BA UBANGIJI ALLAH YASA TUNANEN KI NA ALHERI YA RINJAYI SHEDANI DAKE TARE DAKE KODA YAUSHE ALLAHUMA AMIN ALLAH 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA 08036959257 ALLAH YA BADA IKON BIYA ALLAHUMA AMIN, , , , , , Tiryan tiryan hjy ke mayar mai da yadda sukayi da mami zaune yake kawai yana sauraren hjy din ba tare da yai magana idon shi na kan wayan hannun shi.

   Sai idan ta fadi wani abin tambaya ta dago kao tayi magana ya danyi murmushi kawai ta gefen fuska.

   Bai bari ta gama fadin labarin duka ba ya mike yana fadin hjy zan dan fita akwai ida nake son zuwa kafin rana yayi sosai don gobe kaduna zamu akwai abinda nake sonyi a can.

    Kace gobe gida kayi ke nan ni likitan bai gama dubana ba ai da nabika mun tafi tare zaman garin nan wuri daya ya fara isata yanzu.

     Wa zai tafi dake ya fada yana kallon fuskanta tace bandai tashi ba yaro idan na tashi ai dole kaje dani.

    Hannun rigan shi yake gyarawa tare da fadin wa ni in jera dake ki zama min matsala sai wurin fita jirgi kice min naki san hakan ba.

   Dakuwa tayi mai da hannu tana fadin wani munafukin ne ya fada ma  dama yaran nan biyu akwai bakin gulma ko kuma Indo ce don dai takwarana ba zata taba fadin wanan labarin ba.   

   Kinyi ke nan ya fada yana fita daga dakin tace miskilin banza nagama ma yaki a wurin uwarka,  yanzu ka dawo zakai min sheri kuma.

    Yana fita ya daga wayan shi dake ringing da security din shi yai magana na minti daya bai karasa fitowa ba har sun kawo mai mota bakin kofan shiga gidan.

   Ya fito kamar mai kare rana fatar jikin shi yayi sumul dashi kamar jikin larabawa don farin shi na daban ne .

  Bai tsaya jiran komai ba ya fada mota suka rufe a hankalin motar tafita daga tangamemen get din gidan mami din a hankali ya lumshe idanun shi yana tuna kalaman hjy data gama rabtabo mashi yanzu.

   Wani shu,umin dariya ya sauke yasan waye mami don mahaifiyarshi ce ya kuma san halinta don ita hjy sanin da can baya tana karama taiwa mami din.

   Lalai da akwai wani plan da mami ke kullawa tayiwa hjy wanan dadin bakin har yar tsohuwar tayi saurin yarda da maganan ta.

   Gyara zaman shi yayi yana gyara lumshe idanuwan shi tare da fadin mami sai dai kiyi hakkuri dani don tun ranan dana fara dora idona kan yarinyar nan tausayinta ya rikede ya zama soyayya a zuciyar danki.

    Shi kanshi yasan akwai kyawan mata dasukafi wanan yarinyar da idan yau yace a aura mai aure dasu zai yuyu.

  Sai dai shikan ubangiji ya dagwara mai tausayin ta da sonta a yanzu don bai taba fadawa tarkon son wata mace ba irin wanan yar abin da mami ke rainawa.

  Shiya idan mami na korafinta a kaina bai iya furta komai a yanzu don son da yakewa yarinyar baki ba zai iya furta shi ba har abin yakan bashi mamaki.

  A wani babban shago motar ta tsaya ya dan dade kafin ya fito motae ya shiga shagon biyu daga cikin security din shi na bayan shi duk inda ya bi sai binshi ake da kallo.

    Sayayya yayi sosai a shagon saga turare sabulun wanka manshafi  da sauran kayan gyaran jikin mata ya biya suka fito daga shagon daga nan ya shiga wani shago na sayar da redmed nan ma ya duba ya zabo ya fito.

     Bai dawo gida ba don ya wuce kallon ball sai bayan sallah isha,i ya shigo gidan ga security din shi har biyu da kaya niki niki a bayan shi suna biye dashi.

   Daga mami Aisha da hjy duk suna falon sai ya jalal suna zaune a dining suna cin abinci suma.

  Welcome ya J suke fada yana amsawa a cikin basar ya nufi kujera ya zauna security din suka shiga gaida mami da hjy.

  Suna tsaye saitin inda yake zaune a bayan kujeran tsaye da ledojin da suka shigo dashi a hannun su.

  Ya kalli Aisha yana fadin a cikin turanci karbi kayan nan ki shigawa yarinyar nan dasu dakin su.

   Ba Aisha ba har mami saida ta dago kai a cikin mamaki tana kallon shi,  shiko fuska a daure ya kara bata umurni yana fadin ki karbi kayan nan ki kaiwa zainab daki nace.

    Ta mike simi simi don bata hango sassauci a fuskan shi ba lokacin idan taki tasan kwanan wasan a wurin shi.

    Meye a cikin mami ta tambaya a hasale ba wani abu bane ya fada yana mayar da kanshi saman kujera tare da fadin john kuna iya tafiya yanzu and make sure by six kun fito don bakwai jirgin mu zai tashi zuwa kaduna.

    Aisha dawo da kayan nan,  nan mugani mami na fada maki ba wani abu bane a ciki perfume ne da kayan  body odor da kikace tana wari na saya mata .

    Ido waje mami ke kallon shi waje don jin abunda ya fada don ita har ta manta da tayi wanan maganan a cikin fada ashe shi yana rike da zancen a ranshi.

    Wari kuma wake wari a gidan nan hjy ta tambaya a cikin mamaki saida ya mike tsaye bayan ya tabatar da shigan Aisha dakin namu yake fadin.

  Tare da duban hjy har lokacin fuska a daure yace wai yarinyar nan zainab shine na sayo mata kayan kamshi.

    Jafar zaka fice min a ido tun kan na feto ka ko sai kayi min rashin kunya a nan na fada bata warin ne ko wani oud take shafawa daba za aji warinta ba.

  Ok fine mami shine ai na saya mata yanzu don ta dinga kamshi kamar kowa ya dan juyo ya kalli hjy yana fadin ya kike hope ba wani matsala dai ko ?

  Ba matsala dan duniya hjy ta fada tana dariyan draman shi da mami din don ita abin ma dariya ya bata kuma.

    Mami kan binshi tayi da kallon mamaki har ya bacewa gani ta ta juyo da kallonta wurin hjyn ta .

   Iyami na fada maki kibi zancen yaron nan a sannu yanzu ina dadin wanan zancen da yaron nan ya fada koda yarinyar na wurin shi fada zaiyi abinsa namijine bai damu ba.

    Hjy gaba daya yaron nan ya sauya akan yarnan don wanan ba halin shi bane musaya min magana ta.

  Amma yanzu kan zeey yake kokarin saba min tun kan aje ko ina inaga ya riketa ta zama tasa ke nan.

    Don nace zeey din tana da body odor shine ya nuna min shi yasan hanyar gyaranta ko ?

    Wanda yaki jin bari ai bayaki gani ba dan zamani ne fa kike jayayya dashi iyami tunda baki jin zance ai yanzu sai ku zuba dashi namu ido.

  A karshe idan an zugaki kin ma dan naki baki ya lalace sai ki dawo ku zauna a gidan ina shike nan dai tunda haka kike so.

    Daga haka ta juya ta mayar da hankalinta gun tv dake aiki duk daba fahintar abinda ake ciki takeyi ba.

   Daga hakan kowa yayi shiru a falon ba wanda ya kara magana sai Aisha data dawo tana zuburan baki take fadin gaskiya ya J ya jamin raini mami nice zankaiwa zeey sayayyan daya yo mata daki.

   Ni wallahi dana sani da  ban zauna falon nan ba yanzu ke enough kada ki cikamu da surutun banza a nan dan Allah mami ta fada a hasale.

   Kafanta ta dauka ta dora saman dan karamin table din dake gaban ta tana karkadawa a hankali kafin ta juyo wurin zeey din tana fadin.

   Jeki kira min zeey din tazo nan da kayan da kika kai mata dakin mu gani ikon Allah iyami yaushe kika zama haka.

    Ashe bawa yakan canza rayuwan sa yanzu wani zubar da mutunci zai sa ki karbi kayan toshin yarinyar nan  don baki data ido.

    Daga yau ba zan kara saka maku baki a cikin zancen nan ba na fada tundazun karki dauka wasa nakeyi a zancen nan .

    Hjy kiyi hakkuri yaran nan ne da abin bacin rai bawai karban kayab zanyi ba ai dubawa kawai zanyi idan babu na assha a cikin sa.

    Barwa yar nan kayan ta a hannun ta koma meye a ciki ina kinfi karfin shi a yanzu hakan kamar zubar da kimar kine a idon ta ai.

   Koda Aisha tazo daki ina zaune ina assgment na baje saman gado hakalina ya dauku ga abinda nakeyi.

  Naji shigowan mutum dakin haka yasa na dago da sauri don jin karan ledan dake motsi a hannun ta don nasan ba hjy bace wanan mai karfine ya shigo.

    Anty Aisha na fada ina niyar gayar da ita take fadin ke dan raini nine zan kawo maki kaya kallonta nake da mamaki don jin abinda take fada daga kofa ta dangwara min kayan tana fadin you will pay for this.

    Kiyi hakkuri Anty na fada tare da fadin ba kayana bane don a zatona bata tayi dasu.

   Ke dan Allah ja can ya J yace a kawo maki wai kazama kawai ta fada tana juyawa don barin dakin.

    In kalli inda kayan suke aje a kasa in kalli bayan anty Aisha dake fita daga dakin ina mamakin kalaminta a fili.

     Ni zainab na fada na tare da sake biron dake hannuna na kurawa ledan kayan idanu kamar mai nazari.

    Da kyar na iya furta na shiga uku ni zainab me wanan bawan Allah yakeso danine a duniyan nan koso yake sai rayuwana ya salwantane ?

   Shiru nayi cikin dakin na kasa cigaba da assigment din da nakeyi sai tunane da nakeyi barkatai a dakin.

    Nasan sai tara hjy zata bar falon mikewa nayi na dauki kayan na nufi dakin mami dasu a hannuna bata dakin yasa na aje nafito ba tare dana bude ledan don ganin abinda ke ciki ba.

    Gaba na faduwa na fito sai muka hade da mami saidana kadu don tsoron mami da nakeji yanzu a raina .

  Gaida ita nayi ta amsa min da kyat na zata zatayi min magana me na tafi nema a dakin nata sai naga ta wuce ta shiga dakin.

   Hjy na hango a falo na nufi wurin ta don tsoron zama dakin ma nake ni kadai don ban san abinda mami zata fada idan taga kayan dana kai mata dakin.

    Yauwa yar albarka kin zo a lokacin daya dace yanzun nake shirin tashi yau sun watse sun barmu ki kama min kofin nan zuwa daki na amsa da to hjy na dauki kofin da sauri muka jera zuwa dakin.

  Ina tsaye saidata zauna na aje mata kofi a gefenta na nufi bandaki don a tsure nake lokacin ina sauraren kiran mami a lokacin duk cikin tsoro nake don bansan abinda zata fadamin ba kan kayan da bansan dalilin su ba.

    Na fito na dauke littafina dana bari saman gadon na koma sama kujera na zauna hjy na dan dube dube a cikin aljihu bujen yadi dake jikinta.

  Don ko yaushe a cikin kidayan kudi take kamar wani na taba maga gashi idan ina kusa nice mai lissafa mata su kullun.

   Duk da babu abinda take saye da kudin ta a gidan komai takeso saidai mami ta sayo mata ko daya daga cikin yaran mami din.

    Yauma lissafin muka fara don anyi baki sun bawa hjy kudi da bana nan shi take son mu lissafa da ita.

   Mamine ta tsaya daga kofa tana kwala min kira ke zeey na amsa da sauri ina fadin na,am mami tare da mikewa lokaci guda.

   Nasamu tako daki ko duk saurin danayi na amsa kiran don naso kada mu kauce a gaban hjy lokacin.

   Ina shiga ta zauna a bakin gadon ta  kafunta a harde mami gani na fada bayan na shiga dakin da sallamana.

   Wanan kayan fa da kika kawo min nan tana nuna kayan take tambayana ba tare data dago kai ta kalli inda nake ba.

   Shiru nayi saidata sake fadin kayan nan fa me sukeyi a nan tafada a cikin dan tsawa.

   Mami nima yanzu anty Aisha ta shigo dashi dakin mu wai ya J ne ya ce ta kawo nan .

   Zeey ta fada tana dago kai ni sa,arki ce ita Aisha data kawo maki bata fada maki naki bane dauke min kayan nan a na tun kan ranki yabaci.

   Da sauri na duka na dauki kayan ina kiciniya da ledojin saboda nauyin ledan su yi yawa sosai bazan iya dauka ba .

  Hakana ja su zuwa dakin mu na ajesu da kyat ina nishi hjy dake zaune har lokacin tana lissafi ta dago tana kallona tare da fadin.

  Ina kayan nan suka fito kuma a cikin mamaki take tambayana na aje a gabanta na koma na zauna tare da tin tagumi don fargaban abinda zaije ya dawo gareni kan kayan nan yadda naga mami ta dau zafi a lokacin.

   Yaushe aka kai kayan nan can ko can dakin Indo takai maki don bakin ciki yaron nan fa ya yo maki toshi dazun a gabab kowa ya bada kayan a kawo maki nan dakin.

    Hjy don Allah kice ya daina min hakan kada mami tayi min fadan haka sai ta dauko koni ke rokon su abu.

    Ina roko anan takwara kayan nan fa keya sayowa su don kansa kuma a gaban uwar taku ya bayar a kawo maki ai.

    Maza tashi ki bude muga abinda ya sayo a cikin ledan mai nacin tsiya shine ai daidai da uwar taku .

    Kamar ba zan tashi ba ta kara fadi na mike badon nasoba na fara fitar da kayan ledan da man shafa suke su turare da kayan shafe shafen jiki dana wankin kai wasu ban san su ba.

   Ja,iri hjy ta fada so yake yakai uwar taku kul idan tace katobara ta iya a gaban yara dayan na jawo na fara budewa dogayen rugana ne masu kyau da daukan ido.

    Sai kamahin sabontaka suke duk wanda na daga ko anty Aisha ban taba gani da irin su ba dukda ko irin su take sakawa.

    Dayan ledan kuma karami ina dagashi saida nakai zaune don photon waya danagani a jikin kwalin haka ya tabbatar min da cewa wayane a cikin kwalin ko ledan shi ba a cire ba saidai andan yaga gefe da alama a dan budeshine an duba.

   Komawa nayi na kai zaune tare da kurawa kayan ido ina tunane kala kala a raina karshe dai tasa na tattara kayan zuwa drower kayana naje.

    Har hjy taga ba anta ban samu bakin magana ba don tsoron da fargaban ganin ran mami yana a bace sai na dauka akan yaya jafar din take cikin yanayin dana sameta din.

   Washe gari ana public holiday don haka kowa na gida bamu fita zuwa school ba ina idar da sallah na koma na kwanta saman gado don hjy tana zaune a gurin sallah har lokacin.

    Muryan shine a kofan yana sallama ta amsa mai daga inda take zaune din saiya shigo daga cikin dakin .

   Kafito ke nan hjy ta fada a daidai lokacin daya karasa shigowa dakin idon shi na akaina yadda nake kwamce nayi tub da ciki saman gadon.

   Wanan barci takeyi ne ya fada daidai yana zama saman kujeran dakin inda nakan kwana wani lokaci.

    Yanzu dai ta idar da sallah ta kara kwanci kafin gari ya waye tafi aikinta.

   Wai hjy aikin nan ba a neman wata ta dinga yinsane a barta haka da aikin nan don Allah.

   Fadawa uwarku nima na dade ina shawaran hakan a raina duba ga irin sakkon da takeyi na zuwa makaranta tunda safe.

    Amma hjy yakamata iyanzu ace ta daina hakana kuna, , , , ,  ina kwana yaya na fada a daidai lokacin dana dan mike zaune saman gadon.

    Lafiya ya fada tare da kawar da kanshi daga kallona ko ya fahinci fita nake sonyi daga dakin ne oho ?

   Zauna abinki yanzun fita zanyi ni hjy nazo sallama dama ana jirana a waje ya fada.

    Dan satan kallon shi nayi yayi wanka fes yana saye cikin suit baka ga farar riganshi ta ciki ta dan fito waje don aninaiyan su a bude yabarshi.

    Zan tafi hjy sai na dawo ya fada tare da mikewa zuwa inda take zaune ya aje mata kudi a gabanta ta shiga jero mai adduan kariya a gareshi kwando kwando.

    Har yakai kofa nace da sauri nagode yaya naga sako jiya Allah ya karawa dukiya albarka.

   Kisa wayan a caji ya fada daga haka yasa kai ya tafi hjy da har lokacin sai albarka take zuka mai  tace tashi ki saka wayan caji yadda yace.

   Hjy mami batace min komai akan kayan ba kuma ni naga kamar ranta a bace yake dani .

    Yaushe zaki tsaya jiran cewar ta ki saka waya a caji kada kija hasara kuma kudi daine ya riga ya kashesu sai dai tayi hakkuri.


    KADUNA


Gidab ya nufa kai tsaye saida yadda ya samu gidane ransa bai masa dadi ba sai sha biyu yake da meeting din dayazo yi anan kaduna.

    Yadda ya samu falon kamar ba mutane a gidan musanman ma mata ko ina ga kayanan ajiye sun baza.

    Part din shi ya nufa ya bude da niyar ya dan huta a ciki saidai yaga kuran dakin da kyankyami kasancewar shi mai tsabta sosai.

  Fitowa yayi don ya duba mai aiki sukai kicibis da Nazifa ta fito falin sannu da zuwa ya J ta fada cikin nuna kulawa ba taee daya amsa ba yace ke dauko tsintsiya ki share part din nan.

    Wa ni ya jafar ta fada tana wani turo baki gaba bake ba wancan zaki bace min kiyi abinda nace tunkan ranki ya baci wurin nan.

   Ta juya tana gunguni zuwa kitchen yana tsaye har ta fito abinka da wanda bai saba aiki ba ji rakeyi kamar ta kurma hannu akai tayi ihu a lokacin.

     Wajen gidan ya koma ya tsaya harta karasa can ya dawo ya samu wai ta gama kamar bata taba komai ba a dakin dakin na nan yadda yake.

    Fita yayi da sauri yana kiran sunan ta da dan karfi ta fito ya balla mata harara yace common shara ma ba zaki iya ba.

   Yayani fa bana shara wanan ma ai nayi kokarin yin sa yanzu kawai ba a sa yan aiki irin su , , , 

  Ji kake fauuu ya wanke mata fuskan ta da mari  da sauri ta kurma wani uban ihu daya fito da sauran daga daki.

      Ta durkushe a wurin tare da dafe kuncinta da dukka hanayen ta biyu ta durkushe a wurin.

     Saiga salma da Rufaida sun fito daga dakin da sauri suna ganin shi suka rikice  sai sannu da zuwa suke mashi.

    Kai ku fito ku gyara ko ina na gidan nan yanzu kafin indawo ko kuma ku samu naku hukuncin zaku zauna kubar gida haka a kazance kamar babu mutane a gidan.

   Ya J mai sharan ne bata zo ba wai danta baida lafiya ku ba mata bane aikin me kukeyi a gidan ku ?

    Ya j ba aikin mu bane shara fa yace oho relly ku din ba mata bane oya ban son in dawo gidan nan in sameshi a haka ya juya fita ya barsu nan tsaye nazifa na dafe da kumatunta tana hawaye.


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post