Amaal Bugun Zuciya page 7&8

Amaal Bugun Zuciya page 7&8

 


*AMAAL*

*BUGUN ZUCIYATA💔*


*💫🌟 Labarin soyayyane mai ban tausayi, tsoratarwa, fadakarwa, tunatarwa da kuma nishadantarwa🌟💫**🦅🦅WRITTEN BY FANDI🦅🦅*


*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*


*FREE BOOK😻🔥*


*PAGE 7&8*

Intisar shikenan sun sace min 'ya waiyo AMAAL😭 Intisar da Ahmad suka rungume Ammi dake tsaye suka sa kuka gwanin tausayi... malam idi mai gadi ne yaji sautin kukan su hakan yasa yayi sauri yazo bakin kofan parlor yayi sallama... basu jisa ba saboda kukan da suke yi, shigowa parlorn yayi ya sake yin sallama Ammi ta amsa tana mai zubda kwallah tace baba sun sace ta yanzu suke kira... ka gani ko... gashinan sun sake kira... Malam idi yace ɗaga kiban ita nan... receiving Ammi tayi ta bashi yasa a kunne yana mai fadin Assalamu alaikum... daga dayan ɓangaren aka amsa da fadin wa'alaika salam dan Allah ko kasan wata mai suna AMAAL? baba mai gadi cikin sauri yace eh nasan ta dan Allah ko kinsan inda take? tana hannun kune? eh tun dazun yayanta ya kawo ta Asibiti da sukai accident yace min zaije ya sanar daku halinda take ciki... har ya bani contact dinsa yace in kirasa idan ana bukatar wani abu to amma inata kiran layin nasa baya ɗagawa ku... malam idi bai bari ta karasa maganar da takeyi ba yace innalillahi wa'inna ilaihirraji'un baiwar Allah wani asibiti ya kawo ta do Allah? Garkuwa hospital to insha Allah gamu nan zuwa... Tun sanda malam idi mai gadi yace nasanta kinsan inda take tana hannun kune?!  su  Ammi sukai shiru suka zuba masa ido... suna gama wayar da Nurse ya mikawa Ammi wayar ta amma bata amsa ba saima tambayar da ta jefo masa ta fadin ta mutu ko? a'a Hajiya ki kwantar da hankalinki tana nan a raye Sunyi accident ne dazun shine aka kaita Asibiti to amma wanda ya Kai... innalillahi wa'inna ilaihirraji'una! baba wani asibitin? asibitin Garkuwa... Ammi ta kwalawa Sani kira tace sani🗣️ sani🗣️... Hajiya sani ya fita nemo ta saidai ko in zaki kira Kabir... Ahmad jeka cewa Kabir ya fito da Mota zaikai mu garkuwa AMAAL tana can... to Ammi inji Ahmad cikin Muryar wanda ya gama kuka... Intisar ce tace Ya Rahman kasa ba wani ciwo babba bane ya samu yar'uwata ba... Ameen inji su Ammi... baba tare dakai zamu tafi dan kar mu Barka cikin tunanin halin da take ciki to Hajiya...


A bangaren SURAJ kuwa da yaga Abdussamad bayi da niyyan fada masa abinda ke faruwa a gidan Saiya kifa masa wata mahaukacin marin da tunda yake bai taba shan irin saba... shake masa wuya yayi yace nace maka meyake faruwa? Yaya HIBBA CE TA RASU😭💔 sakin sa yayi... a hankali yasa hannu ya rufe bakinsa hawaye Masu zafi suka zubo kuncinsa... ya kalli mutanen dake tsaye suna kallan su kowa yayi jugum jugum wasu suna mai jin tausayinsa wasu suna kuka! babban parlorn gidan ya nufa da gudu yana shiga yayi turus ganin gawa kwance a rufe! cikin hanzari ya yaye bargon da aka rufe ta dashi... yace a'a a'a hibbata kada kimin haka a'a baki mutu ba dan Allah ki tashi... hibbaaaa😭 waiyo wllhy ba ita bace😭 kuce min mafarki nake meyasa zaki tafi ki barni yar'uwata... mutuwa meyasa zaka dauki yar'uwata ka barni?!... bani da wani sauran amfani a duniya tunda ka ɗauke min yar'uwata nima kazo ka daukeni a'a bazan iya jurar rashin kiba yar'uwata a'aaaa😭 ya dauki kanta ya aje a cinyarsa ya rungume ya cigaba da fadin maganganu iri iri masu taba zuciya... duk  mutanen dake parlorn saida yasa su kuka... daddynsa yazo ya janye sa yace babana shin baka da takwakkaline? ko wani mai raida kake gani dole watarana ya mutu ya bar duniyar... idan lokacinsa yayi... babu abinda take bukata a gunka yanzu face addu'arka... da ace za'a tashe ta yanzu taga yanda kake mata kuka sai ta nuna rashin jin dadin kukan da kake mata... dad daddd... Faaɗi kasa yayi a sume... Mommy tace Suraj dan girman Allah kada ka tafi ka barni kamar yanda yar'uwar ka ta tafi ta barni suraj bazan taba jin dadin rayuwar nan ba idan kaima ka tafi ka barni ba... waiyo Allah na Allah na tuba Suraj ka tashi Suraj! suraj ta shiga kiran sunan sa abin tausayi😭💔 

da taimakon Abdullahi da Abdussamad da sauran mazan dake gidan suka dauke sa suka shashi cikin mota sukai asibiti dashi...✍️


Nurse bayan ta gama waya da baba mai gadi ta kalli AMAAL tace Gaskiya da baki farka da wuri ba wllhy ya'yan ki ya jamin babbar matsala... kilan ma a Kore ni daga aikina... ya kama bani numbern sa ya tafi ya barni dake... kuma nayi ta kiransa baya ɗagawa... fisabilillahi ya kyauta? AMAAL cikin Muryar marasa lfy tace kiyi hkr dan Allah kila wani babban uzuri ne ya kamashi... ba yanda za'ai ya tafi yaki dawowa ba tare da babban uzuri ba tafada kamar dagaske shidin ya yanta ne... ajiye papern da suraj ya rubuta numbern sa Nurse tayi akan durowar dake kusa da AMAAL ta fita... daukan Papern Amaal tayi ta kalli sunan dake jikin papern da numbern tace SURAJ... YAYA SURAJ ina matukar godiya da taimakon da kamin Allah Ubangiji ya saka maka da Aljannah... ya kuma sa ba katafi kenan ba zaka dawo in ganka na maka godiya da cetona dakai... kuma na baka hakuri game da rashin kunyar da nai maka dazun... koda yake ai kaine ka fara tsokana ta... Amma duk da... Assalamu alaikum AMAAL inji Ammi bude idanunta tayi cikin murna da kuka tace Ammieta... Ammi ta rungume ta tace AMAAL kina lfy? Meyasa meki? Garin yaya kukai accident... kinji ciwo sosai? ina yake miki ciwo yanzu?... Ammi ki natsu cewar Intisar... Uh Amaal? ba inda yake miki ciwo ko? eh Ammi ina lfy kaina ne ke min ciwo kuma shima yanzu nasha magani da sauki... Malam idi da Kabir driver Suka mata ya jiki... tace alhmdllh naji sauki... Ameen ngd... Ahmad ba magana ne? yaya ya jikin ki? naji sauki... intisar tace yaya ya kannaki baya dai miki ciwo sosai ko? eh inty ta... Wai garin yaya kikaji ciwon Amaal? Kuma wa ya kawo ki Asibitin cewar Ammi...✍️


TO BE CONTINUE...


*ALKALAMIN FANDI CE✍️*

07066554340

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post