*AMAAL*
*BUGUN ZUCIYATA💔*
*💫🌟 labarin soyayyane mai ban tausayi, tsoratarwa, fadakarwa tunatarwa da kuma nishadantarwa🌟💫*
*🦅🦅WRITTEN BY FANDI🦅🦅*
*Da sunan Allah mai eahama mai jin Kai*
*FREE BOOK😻🔥*
*PAGE 5&6*
*SURAJ* ɗane ga Muhammadu ministern man fetur, suna zaune a Abuja amma asalin su yan Jigawa ne... Mahaifinsa yana da mata biyu... Hajiya Aysha da Hajiya katum... Hajiya Aysha itace uwar gida yaran ta biyu suraj da hibba... Hajiya kaltum kuma yaran ta hudu, Abdussamad,safna,manal, sai kuma dan autar ta Mustapha... Hajiya Aysha da kaltum suna zaman lafiya kamar ba kishiyoyi ba komai nasu iri daya... duk abinda dayar su zatai sai ta nemi shawarar yar'uwar ta... kan yaran su a hade gwanin birgewa... Suraj farine Amma ba sosai ba... yana da tsawo da jiki daidai misali... yana da saje kwantacce wanda yake daidai da fuskar sa shekarunsa 30 a duniya... Pharmacy ya karanta... ba wanda yake bala'in so bayan iyayensa sama da kanwarsa hibba... Kasancewar Hibba tana da matsalar ƙwaƙwalwa... haka aka haifeta dashi duk da kafin su gane hakan saida suka kashe makudan kudi... Hibba bata cika lfy ba kwana kadan sai an kwantar dasu a asibiti hakan yasa idan ka ganta zaka ce yar 19yrs ce ba 26 ba... Bata cika san yin magana ba saida dan'uwanta wato suraj... bakomai ne idan ta fada ake ganewa ba amma shi suraj duk abinda ta fada sai ya gane saboda tsananin kaunar dake tsakanin su... Idan yana gida tare suke cin abinci... Ya goya ta ya zagaya cikin gidan da ita Sannan ya kawo ta dakin ta ya kwantar da ita... Duk abinda yasan idan yai zai sata farin ciki shi yakeyi baya san yaganta cikin damuwa ko wani hali... idan bata da lfy har kuka yake saboda tana shan wahala sai yaga kamar bazata tashi ba... Baisan ya rayuwarsa zata kasance ba idan ya wayi gari ba ita ba...
Dalilin da yasa yazo Kaduna shine mahaifin abokinsa Abdallah ne yaji labarin cewa ya gama karatunsa har za'a bude masa pharmacy shine ya kirasa yace kafin a bude masa nasa pharmacyn mai zai hana yazo nashi pharmacyn ya tayasu aiki... Bazai iya ce masa a'a ba hakan yasa ya sanarwa daddynsa tayin da mahaifin abokin sa ya masa sosai daddynsa yaji dadi har ya kira Abban Abdallah yayi masa godiya... Bayan Suraj ya sauka a garin kaduna ran Thursday yaje ya gaisa da mahaifiyar abokinsa Abdallah da mahaifinsa... Ya huta yaci abinci... Abdallah ya kaishi pharmacyn su ya nuna masa office dinsa da yanda tsari da dokokin su yake sannan suka dawo gida... Bayan kwana biyu Suraj ya gama shirinsa tsaf ya fita office... saidai yana zuwa ya manta ashe bai dauko key din office dinsa ba saboda saurin da yakeyi... juyawa yayi nufi inda motarsa yake har ya bude zai shiga sai ya fasa ya rufe ya tari mai keke napep ya fada masa sunan unguwar da zai kaisa... suna cikin tafiya sani driver ya tsayar dasu AMAAL ta sanarwa mai keke napep din inda zai kaita wato makaranta tana shig....
Cigaban labari🔥
Suraj ne ke fadin Abdallah ka rage gudu mana nifa ban shirya mutuwa yanzu ba... Hawaye ne ya taru a idan Abdallah jin kalmar da ya ambata wato mutuwa... a ransa yace abokina ka yafe min amma bazan iya sanar dakai wannan mummunar labarin ba! Mtsw wai tunanin me kake haka ka barni ina ta magana ni kadai... Na'am me kace? Banza dashi yayi Abdallah yace kayi hkr abokina hankalina ne ya tafi wani guri me kace? A jiyar zuciya ya sauke yace wllhy tun dazun nake jin gabana nata faduwa... Ya fada yana mai lumshe idanunsa... Abdallah yace karinga fadin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allahumma Ajirni fi musibati wa'aklufli khairan minha... Suraj yace insha Allah ngd... Bayan mintuna kadan suka isa gidansu Abdallah... Wanka Suraj yayi ya canza kaya ya dauki abincin da yaga an aje masa... Har zai kai baki yace bari in kira hibbata inji ko ita taci abinci? Allah yasa ma batai fushi dani ba yau ban kirata ba... Kiran wayan yayi sai ya jita a kashe ya kira na mommynsa yana ringing Amma ba'a daga ba yace bari zuwa magriba zan kara kira... Abdallah ne ya shigo yace ya naga baka ci abincin ba? Eh mtsw barshi ma dai bana jin yunwa... Abdallah faduwar gaban nan sai gaba yakeyi... Gyaran murya Abdallah yayi yace may be saboda zamuje Abuja da yamman nan shiyasa kake jin faduwar gaba... Abuja Hmm da yammar nan kaiko Abdallah me zai kaimu Abuja da yamman nan... Toh nima dai daddy ne ya kirani yace muje... Kuma su umma ma sun tafi... Su umma ma sun tafi? Eh Abdallah ya basa amsa to ne hakan ke nufi? Toh nima dai bansani ba... Ko shiyasa naga miscalls din daddy dazun kusan 10 Abdallah lfy daiko? Share hawayen da suka zubo masa yayi ya rungume suraj ya fashe da kuka dan ya kasa dannewa... Saida yayi mai isarsa sannan yace kana da passport? Ba tambayar da suraj baima Abdallah ba akan ya fada masa abinda ke faruwa amma Abdallah yaki fada masa... Wanda har Fushi suraj yayi dashi....
Bayan awanni su suraj ne nagani a wani tangamemen gida mai Black gate mai gadi ya bude musu suka shiga koda suraj yaga mutane a gidan saida gabansa ya fadi... Abdussamad ne yazo da gudu ya rungume ya fashe da kuka harda shessheka... Yace Abdul me ya faru? Dan girman Allah ka sanar dani kada ka barni cikin duhu kamar yanda Abdallah ya barni cikin duhun... Abdussamad zama yayi a kasa ya cigaba da kuka... Suraj cikin daga murya yace Abdul tambayar ka nake meye ke faruwa ka fada min nace ka fada min kafin jikin ka ya fada maka... Ya fada cikin tsananin bacin rai....
Ammice hankalinta yayi natukar tashi ganin har 8 AMAAL bata dawo gidaba kuma driver yaje daukota amma bai ganta a inda ya saba daukanta ba... duk inda tasan AMAAL na zuwa saida ta kira ta tambaya amma amsar daya ce bata nan bata zoba... Tsakar gidan ta fita ta kira sani da malam idi mai gadi tace AMAAL har yanzu shiru kodai kidnapping dinta akai bamu sani ba... Nashi ga ukuna sani bayan makarantar ba inda kake kaita? Wllhy Hajiya daga makaranta sai makaranta ba inda nake kaita... Malam idi mai gadi yace ki kwantar da hankalin ki insha Allah tana nan cikin koshin lafiya kowa yaje yayi alwala yayi Sallah Allah ya baiyana ta... To baba nagode mu shiga intisar Ahmad jeka dauko min wayana a daki in kira Abban ku ina sanar dashi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga ukuna ta fada tana mai zubda hawaye abin tausayi... Dauko mata wayar yayi tana amsa wata bakuwar number ta kirata tace intisar shikenan sune wllhy sune suka sace min 'ya
*ALKALAMIN FANDI CE✍🏼🦅*
07066554340