AMAAL BUGUN ZUCIYATA💔 page 1

AMAAL BUGUN ZUCIYATA💔 page 1

Labarin soyayya ne mai ban tausayi, tsoratarwa, fadakarwa tunatarwa da kuma nishadantarwa


Labarin soyayya ne mai ban tausayi, tsoratarwa, fadakarwa tunatarwa da kuma nishadantarwa


*🦅🦅WRITTEN BY FANDI🦅🦅

FREE BOOK

Page 1


Wata yarinyar da bazata haura shekaru 21 ba ne  kwance akan wata hadaddiyar kujera 3 seater mai kalan dark purple da dark milk color, yarinyar ba lukuta bace haka zalika ba Siririya bace, ita din fara ce tana da gashin gira da matsakaitan idanu wanda suke farare tas kamar madara. Lips dinta dan karamine wanda yake pink color kamar na Francine diaz🥰 kanta da bata sa dankwali ba wanda yasha kalaba na kalla nace Masha Allah tana da gashi sosai kuma baki ne wuluk, reader's yarinyar ta hadu ba karya🤗 sanye take da riga da wando na bacci pink color da dan baki baki a jikin shi. Shuru nai ina sauraron cool voice dinta inda naji tana fadin insha Allah Zahra nima zan shigo schl din by 11:00am ta qara da fadin ohk sai mun hadun ta fada tana mai cire phone din daga kunnen ta. Muryar wata dattijuwa naji hakan yasani waigawa dan inga mai maganar da Muryar su take iri daya da yarinyar da ta gama waya yanzu, rike baki nai dana kalli kyakkyawar matar dake sanye da Black lace mai adon manyan duwatsu matar kama take da wannan yarinyar kamar yadda voice dinsu yaso yayi iri daya✍️ jinai tace Amaal bazaki tashi kiyi shirin zuwa schl ba ko yauma baku da lectures? Yarinyar dake kwance kan 3 seater ta tashi ta zauna tace good morning Ammi Matar da ta kira da Ammi tace morning how's your night Amaal tace it was fine Ammina, Masha Allah nace baki da lectures ne yau? Oh a'a Ammi muna dashi sai 11, to ai Amaal kafin kiyi breakfast ki shirya 11 din ma tayi kin ma yi wanka kuwa? A'a Ammi yanzu fa na tashi daga bacci nayo nan to ki zauna kar kije kiyi wankan kiyi breakfast din har 11 din tai kinji ko? Ammi ta karasa tana mai jifan tada hararan wasa, dan dariya tai wanda dimple da fararen hakoranta suka baiyana akan kyakkyawar fuskanta,tace Ammi insha Allahu 10 na fita daga gidan nan, To Allah yasa. Ameen Ammina✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post