AMAAL BUGUN ZUCIYATA💔 page 3

AMAAL BUGUN ZUCIYATA💔 page 3

Amal Bugun Zuciya


AMAAL BUGUN ZUCIYA

Larin soyayyane mai ban tausayi, tsoratarwa fadakarwa tunatarwa da kuma nishadantarwa


🦅🦅 WRITTEN BY FANDI🦅🦅


Bismillahir rahmanir rahim❤️

Page 3

After 7 months Ammi ta dawo daga kasar Germany aka sa musu rana da Alhaji Ishaq na 2 months bayan anyi shagulgula da kashe kudi suka tare a Kaduna unguwar malali G.R.A suna zaman lfy sosai da matarsa saide ya hana ta cigaba da karatunta.... shekaran su daya da aure Allah ya azurta suda yan biyu maza SHURAIM & ISHAM yanzu shekarun su 23... A Egypt suke karatu shuraem yana karantar medicine while isham kuma business yana san ya karanci business ne dan ya dinga taimakawa mahaifinsa a bangaren kasuwancinsa, bayan an haife suda 2yrs Allah ya sake azurta suda ya mace wato Amaal wacce take yar kimanin 21yrs tana karatu a Kaduna State University wanda aka fi sani da KASU itama medicine take karanta tana level 200 sai kuma intisar yar shekaru 16 da Auta Ahmad wanda yake j.s.s 1 yanzu... Wannan shine takaitacciyar tarihin su Amaal Ishaq Ali ✍️


Cigaban labarin...

Bayan Amaal ta shirya taje taiwa driver magana akan yakaita schl... suna hanyar tafiya motar su ta samu matsala, tace na shiga uku sani 11 nake da lectures Kuma ga motar ta samu matsala yanzu ya zanyi? Sani driver yace Amaal yanzu karfe 10:21 zan kira bakanike yazo insha Allah kafin shadayar zai gama gyarar sai in kaiki... Kai sani zanyi letti... bari na tari keke napep na wuce... Sani ne ya taran mata keke napep ta fada masa inda zai kaita... da bismillah ta shiga ta zauna ta gaida wani matashi dake zaune kusa da ita... Kallanta yayi dan ya amsa gaisuwar da tai masa amma sai ya kasa saboda wani irin faduwar gaban da yaji... Itama a bangaren ta hakane wani irin faduwar gaba taji tai saurin rintse kyawawan idanunta a zuciyarta tace bismillah... Kamar ance mata ta bude idanunta ta kalli madubin dake jikin keke napep din suka sake hada ido dashi... Ya kauda kai a ransa yace idan ma ke maiyace kuruwata kur namata da daci... Aiko sai ji yayi tace idan baka kalle niba taya kasan ina kallan ka? Kuma nidai ba maiya bace ta fada tana mai  murguɗa masa baki... Yace to ke waya ce ki kalleni? Dauke kanta tai... Tai kamar bataji abinda yace mata ba... Wayan sane yayi ringing picking yayi yace Assalamu alaikum Abdallah... SURAJ Ina kaje ne nazo office dinka ban ganka ba? Wllhy key dina na manta yanzu haka ina hanyar dawowa gida... Abdallah yayi dariya yace wannan saurin da naga kanayi ba dole ka manta abuba... Suraj yace kaide ka sani Sai na dawo... Bai saurari abinda zai ce masa ba ya kashe wayar... Ta madubi yaga tana hararar sa yace ke wa kike harara haka? Ta hade girar sama data kasa tace haka idona yake... Dan murmushi yayi baice mata komai ba... Wata yarinyar da baza ta wuce shekaru 11 ba ta shiga tsakiyar titi da zummar tsallakewa wani babban mota yayo kanta a guje ya bugeta Amaal da abin ya faru akan idanta ta kwala ihu cikin tsoro ta fita daga cikin keke napep din itama mota ya bige ta💔 suraj cikin daga murya yace wa mai keke napep dinda ke tukasu malam ka tsayaaa! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yace cikin tashin hankali yayi sauri yaje inda take zube kanta ya fashe ya dauke ta yasa ta cikin wannan keke napep dinda suka sauka... yace ka kaimu asibitin dake kusa da nan yi sauri✍🏼


07066554340

 

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post