Amaal Bugun Zuciya page 2

Amaal Bugun Zuciya page 2

 

Amaal Bugun Zuciya pahe 2

*AMAAL BUGUN ZUCIYATA* ๐Ÿ’”


*๐Ÿ’ซ๐ŸŒŸ labarin soyayya ne mai ban tausayi, tsoratarwa fadakarwa tunatarwa da kuma nishadantarwa ๐ŸŒŸ๐Ÿ’ซ*


*_๐Ÿฆ…๐Ÿฆ… WRITTEN BY FANDI_*


*FREE BOOK*


*Page 2*


Su wanene Amaal? 


Alhaji Ishaq Ali shine sunan mahaifin Amaal... babban dan kasuwane... yana da manya manyan Company's a Nigeria dama wasu ฦ™asashen duniya... Alhaji Ishaq bafulatani ne, shi kadai iyayensa suka haifa, mahaifinsa soja ne, mahaifin Alhaji Ishaq mutum ne mai tsananin tausayin talakawa kuma ya kasance yana taimaka masu. Yana sa masu girkin gidan shi ko wacce ranar jummu'ah suyi girki su rabawa marasa karfi... hakan yasa wasu masu kudin unguwar suka fara koyi da wannan halin nasa na rabawa talakawa abinci, talakawa na matuฦ™ar jin dadin wannan taimakon da yake musu hakan yasa suka sa masa suna DAN ALJANNAH. Dan aljannah yana da mata guda daya Hajiya saudat... Hajiya saudat itama kusan halinsu yazo daya da mijin nata nason taimakon na kasa dasu hakan yasa suke zaman lfy tare da mijinta, dan aljannah da saudat saida sukai shekaru 5 da aure tukun Allah ya azurta suda Alhaji Ishaq wato Daddyn Amaal.. a inda garin haihuwar Alhaji Ishaq Allah ya karbi ran saudat a hospital๐Ÿ’” ana sanarwa dan aljannah ya yanke jiki ya fadi ashe shima raine yayi halinsa! Alhaji Ishaq kamar yasan ya rasa iyayensa ya callara ihu ya dinga kuka๐Ÿ’”... Mutanen garin Yobe sunji rasuwar su matuka, marasa karfin da suke taimakawa suka ce ai ba familyn sukai rashi ba su sukai rashi... to anan sai muce Allah yaji kan musulmi ya gafarta musu idan tamu tazo yasa muci kada imani allahumma Ameen✍️


Bayan anyi arba'in mahaifiyar dan aljannah wato kakar baban Amaal ta dauke shi tai Kaduna da shi dan anan suke zama da mijinta saboda mijinta anan yake aiki.... baban Amaal anan kaduna ya girma ya kammala karatunsa na secondary, sannan ya tafi Germany yin degree dinsa a fannin business... a kasar Germany Allah ya haษ—a sada matar sa Ammi yar garin Bauchi karatu ya Kaita Germany inda take karantar law yar kimanin 19 yrs ce, bayan ya gama karatunsa ya fara business dinsa gadan gadan Allah ya sawa business din nasa albarka✍️

 watarana Kakan ninsa suka zaunar dashi sukai masa maganar aure ya sosa kai yace yan tsofaffi na ai ina da wanda nake so kuma nake san na aura... nan da 6 months zata gama karatun ta ta dawo nan gida Nigeria... kakarshi tace maigidana nan gida Nigeria? kishiyar tawa ba anan take karatu ba kenan? oh Allah matarnan kinjini fa amma da yake kishi ya rufe miki idanu shine kike sake tambaya ta to eh... ya fada yana mai dan girgiza ta๐Ÿ˜… kakansa yace ka kiyayeni wllhy idan ka karya min matata nima sai na karya ka ya fada cikin zolaya... tace yanzu in ba fada kai cewa mu din kakan ninka bane wa zai sani? Ishaqu ina muke da tsufarda har kake tsokanar mu kake kiran muda tsofaffi eh? Eh hakane ba wanda zaisan cewa kudin baku kuka haifeni ba in ba fada naiba... ya kwanta akan cinyar kakansa yace Allah ya barmun ku iyayena kuma kakanni na. suka amsa da Amin suna mai sa masa albarka.✍️


07066554340

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post