Sauke Littafin Makauniyar Kaddara.

Sauke Littafin Makauniyar Kaddara.

 MAKAUNIYAR ƘADDARA😭

            Bilyn Abdukk ce🤙🏻

Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al'arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al'ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun.

Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare da ƴan uwana, yanda muka fara lafiya ALLAH ya sa mu gama lafiya, UBANGIJI ya bamu kariya yay riƙo da hannayenmu baki ɗaya.

Ya rabbi ka gafartama Mahaifina da sauran al'umma da suka rigamu gidan gaskiya. Idan tamu tazo ALLAH yasa mucika da imani. ALLAH ka wajabta mana tsoranka da soyayyar MANZON ALLAH😭🙏🏻.

Zafafa Next level

Page 1

“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.

      Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa. 

      A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu.

      Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.

    “Nagode”. 

Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun. 


     A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.

      Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak......”

“Ƙanwata ina zakije?”.

Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu'arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.

       “Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.

    Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.

       “Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.

     Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”.

     “......Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.

     “Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.


Download Now


Kuna iya tuntubarmu domin tambaya ko Neman wani littafin da babu a nan ta yanyar akiye tambayar a comment. Nagode

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post