Budurwar Mijina page 1 - 12

Budurwar Mijina page 1 - 12

 

Budurwar Mijina

Budurwar Mijina

            *NA SADNAF

*E.W.F*


*Bismillahi Rahamanir Raheem*

Page 1


        Wai saurin me kake yi ne haka"?


Wayar sa ya Kara duba wa tare da Kara sauri Yana "Jirana ake fa karki damu yanzu zan dawo bazan dade ba yace tare da yin waje da sauri.


Da ido na bishi har ya fice daga gidan naji karar tashin lifan dinsa.


Tagumi nayi tare da bin kulolin da na ajiye a tsakiyar kafet din palon da  ido,abincin daren dana dau tsawon lokaci ina yinsa duk sabida na faranta Masa duk da cikin dake jikina ina jin yunwa haka na hakura da cin abincin sabida idan ya dawo muci tare kamar yanda Muka Saba sai gashi daga dawowar sa ya sake wanka ya fice daga gidan da Sunan kawunsa na neman sa.


Kwana biyu kenan Yana min haka.


Haka na zauna raina a b'ace Ina tsaki kasa kasa ganin idan na cigaba da zama a haka batare da naci abincin ba zan cutar da kaina da abinda ke cikina yasa na zuba abincin na fara ci.


Ban wani ci da yawa ba na rufe sauran na jawo wayata na fara chatting abinda kawai zai rage min kadaici da takaicin fitar da mahfuz yayi ya barni ni kadai a gida kamar Mayya.


Mahfuz bai dawo ba sai wajen goma na dare zuwa wanan lokacin Raina ya Kai kololuwa wajen b'aci kafa kawai nake girgiza wa Koda ya shigo da sallama ciki ciki na amsa mishi,ya saki murmushi Yana "Afuwan tawan wlh wani waje na raka kawu bansan zamu dade haka ba kiyi hakuri kinji matata"


Bansan Mai yasa bana iya dogon fushi da mahfuz ba Yana min murmushi da yar murya zanji na sauko.


Ledar daya shigo da ita ya bud'e Yana "Kinga kayan kwadayin dana taho Miki dashi


A binka da mai ciki da sauri na wafci ledar ganin alewar Madara da gulisuwa yasa na washe baki dan duk wani Abu Mai Madara da siga Ina so.


Sai da na fara Shan alewar Madarar na kalli mahfuz da ya zauna a kasan kafet Yana Danna wayarsa 


"Baza ka ci abincin bane?"


"Wlh kawu ya tilasta min cin abinci a gidansa sai dai gobe ki dumama min kafin na fita"


"Yanzu ko cokali daya bazaka yi ba sabida Kai na girka fa"


"Ai nace Miki gobe sai kimin dumame wlh yanzu a koshe nake"


Badan raina naso ba na cigaba da Shan alewar Madarata shi kuma ya mike kafarsa da hannu bibiyu Yana latsa wayarsa har da dan murmushinsa.


Ido na zuba Masa Ina tunanin canjawar da yayi  a kwanakin nan,Mahfuz mutum ne da bai wani damu da chatting ba dan sau tari ni nake tilasta Masa yin chatting sabida Ina tura Masa sakwanin ta watsapp,ada idan ya dawo gida ko waiwayar wayarsa baya Kara yi sai dai yayi ta jana da hira Yana bani labarai idan yaga na dauko wayata sai ya kwace yace a hakura da danna wayar nan azo a ji da ni amma a kwanakin nan har da asuba Zan ga Yana latsa wayarsa ban taba zarginsa ba bana Jin Zan Kuma zarge idan na tuna San da muke yiwa juna,ba Kuma mu dade da yin auren ba tunda yanzu shekara  biyu da auren mu a yanzu Allah ya azurtani da samun ciki


"Wai Mai kake yi a wayar kake ta murmushi haka"?


Dagowa yayi da sauri Yana "Da Abdul muke hira fa sai dariya yake bani kinsan halinsa da barkwanci"


Murmushi nayi nima Ina "Gwauro ba har yanzu sai ruwan ido yake ya kasa tsayar da budurwar balle mu sha biki"


Yana chatting muna hira har zuwa sha daya da rabi na dare kafin mu tafi daki mu kwanta.


Fitsarin da nake ji ne ya farkar dani sai da na wartsake na mike zaune ga mamakina mahfuz baya d'akin har Kara shafawa nayi Naga ko dai lumewa yayi a bargon da muka lulluba sai dai bargone kawai baya d'akin.


Kasa kunnena nayi naji ko dai Yana bandakin a daidai lokacin da na daga kaina Ina kallon agogo d'akin karfe biyu da minti goma Sha biyar na dare.


Mik'ewa nayi a hankali Ina mamakin Inda Mahmud yayi dan nasan baya bandaki tunda banji motsi ba.


Sai dana kunna fitilar d'akin na nufi wajen k'ofar dakin da aka dan bud'e idan har zan tab'a k'ofar ba abinda zai hana yayi Kara daga d'akin Ina Jin maganarsa hakane yasa nake so naji mai yake cewa zuciyata fal da mamaki da wa Mahfuz yake magana a tsakar daren nan ya baroni a daki ni kadai.


A hankali na samu na fito daga d'akin batare da na bari kofar tayi Kara ba, cikin sand'a na fito na nufi palon da yake akwai siririn corridor kafin a iso palon.


Hasken wayarsa kawai nake hango wa yayi rub da ciki fitilar palon a kashe.


"Nifa bana ganinki sosai wai me hakane"?


Abinda ya sauka a kunnena kenan daya bala'in fadar min da gaba har sai dana dafe cikin jikina sabida motsawar da yayi.


Ban motsa ba na tsaya Ina cigaba da Jin hirarsa da macen da nake Jin saukar muryarta a kunnena.


"Bana so na kunna haske na tashi Ameera fa Wai yanzu baka ganina"


"Rowa kawai zaki min Kisani mafarki a banza"


Dariya macen ta kyalkyale dashi Yana shirin magana bansan rike numfashina nayi ba Ina sakin numfashin yayi jifa da wayar da sauri Yana "Lubna"


Duk da jikina balain rawa yake Ina hada gumi bansan ya akayi nayi jarumtaka wajen daidaita kaina Ina "Farkawa nayi zanyi fitsari da ban ganka a d'aki ba shine na fito"


"Ooo e'e'e motsi naji a waje shine na fito naga waye har waje na fita ma"


Yace Yana in'ina ya sunkuya  dan ya dauki wayarsa na juya jikina na cigaba da rawa nabi bango na koma d'akin Yana daga bayana Yana fadin Yana tunanin barayi sun adabi unguwar bance Masa komai ba na kwanta tare da Jan bargo dan har wani zazzabi naji Yana neman rufeni.


Yana kwanciya a gefena ya fara k'ok'arin jawoni idan har na hana shi rungumeni zai zargi naji maganar da yake yi da mace.


Halin da nake ciki yasa ban iya jure rungumar da yamin ba dan gani nake kamar ya manna min garwashin wuta na janye jikina banaso nayi magana sabida Zan iya fallasa halin da nake ciki bana so nayi abinda zanzo Ina nadama inaso na samu nutsuwa nayi tunani Mai kyau.


Koda na janye jikina bai Kara jawo ni ba yace tom yau bbyn bayaso a tabaki kenan ya juyamin baya tare da Jan bargo saman kansa.


Ido na zubawa bayansa Ina Jin tashin maganarsa a kunnena nifa bana ganinki sosai wai me hakane 

Rowa kawai zakimin kisani mafarki a banza.


Da wa Mahfuz ke video call da tsakar daren nan har ya barni a daki ya tafi palo wacce ce ita,har yaushe Muka yi Aure da mahfuz zai fara kula Yan Mata,Anya ma mahfuz dina ne wanan ko dai mafarki nake yi na mitsini kaina wai dan na tabbatar da ba mafarki nake ba.


Zuciyata wani irin zafi yake min na tsananin kishi mahfuz dama Yana da budurwa duk soyayyar Nan da yake min dama zai iya kula wata, mahfuz makota ma sun shaida irin kaunar da yake min.


Soyayya mai tsafta muka yi a shekara uku da muka hadu dashi,naje banki zan bude acct shi kuma anan yake aiki,tun ban dauki soyayyarsa da wani mahimmanci ba har  sai da ya samu matsuguni a zuciyata,ba Wanda baisani dashi ba a cikin dangina haka ma danginsa,kawayena Kan roki Allah ya basu irin Mahfuz sabida yanda baya iya b'oye san da yake min a gaban kowa, nida kawayena mun Sha hada Kai mu siyi layi dan mu gwada shi,Yana Jin muryar mace zai kashe dan kafin muyi aure Ina balain saka kaina a matan da suka yi sa'a da dace samun nagartace kamar mahfuz ban fuskanci wani matsala ba har mukayi aure zan Kuma iya shaidarsa dan ba abinda yake boye min,a gurin mahaifiyarsa Hajiya Ammi kawai nake ganin ban wani samu karbuwa ba duk da da yawa ance haka take bata fiye sakarwa sirikanta fuska ba,da na auri Mahfuz sai na fuskanci idan kina so ta sakar Miki fuska ki bata abin duniya a ranar zata sakar Miki fuska na Kuma ji halayenta a wajen matar yayyen mahfuz Inda Suka ce Kar na sake duk wani abu da zai hadani da Mahfuz nace Zan Kai kararsa wajen mahaifiyarsa tsana zan janyowa kaina dan bata san laifin yayanta ko kad'an.


Daga aurena da mahfuz zuwa yanzu ban wani fuskanci matsala ba duk da kyautata min da yake Yi a waje da bambanci  a yanzu da muka yi aure, dama can ba soyayar kudi muka yi ba shiyasa Koda muka yi aure ba wani kudi yake bani ba nima ban damu ba bansani ba ko dan ban Dade bane Zan bukaci kudi a gaba kayan abinci dan abinda bazaa rasa ba ban Kuma damu ba.

Zuciyata suya kawai take bacci ya kauracewa idona zuciyata nata sak'a min na tashe shi na tambaye shi da wa yake waya,wata zuciya.kuma na hanani akan nabi komai a hankali.

Kiran sallah asuba a kunnena dama Ina rigashi tashi sallah ni nake tashinsa.Haushinsa da nakeji yasa ban tashe shi ba naje.na daura alwala inaga motsin rufe k'ofar bandakin ne ya tashe shi.Koda ya mike Yana Hamma yace "Da ban tashi ba,bazaki tasheni ba kenan"?Ban ma iya bashi amsa ba bama naso nayi magana dan wani abu ne ya tokareni a mak'oshi.

Banida burin daya wuce ya tafi massallaci na dan bincike wayarsa dan na tabbatar da zargina.Sai dai yana fitowa daga bandaki ya zura wayarsa a jallabiyarsa yayi ficewarsa.Zuwa yanzu zargin mahfuz nada budurwa ya tabbata dan a kwanakin nan yafara haka,amma baya  fita da wayarsa har password dinsa nasani dan sunana ne.Ina zaune ne kawai akan sallaya zuciyata fal da tunanin da mamakin mahfuz dana d'auko so da yarda na dora masa.

Mahfuz ba mutum bane da idan yaje massallaci Yake dadewa sai gashi har gari ya fara haske bai dawo gidan ba.Tuni wani irin kishi ya turnike ni jikina har rawa Yake.Har zan fita waje na koma dakina na dauki wayata tare da bin umarnin zuciya ta akan na gwada Kiran wayarsa naji ko dai wayar yake.Ina kuwa kira ya nuna call waiting Wanda hakan ya kara saka kirjina nauyi sabida kishi ban hakura ba na cigaba da kira dan idan har ya daukeni da mahimmaci ya Kamata ace ya dauki wayata tunda nasan dole zai ga kirana sai dai bai dauka ba nima ban fasa Kira ba nasan bazai wuce layin unguwar ba dan gida uku ne tsakanin mu da massallaci da hijabin jikina na fita waje wayata Kare a kunne na a dakalin gidan makociyata na hangoshi a zaune.Yana ganina ya katse wayar tare da mik'ewa tsananin bacin rai yasa tun kafin ya iso nace "Mahfuz da wa kake waya"?Murmushi ya sakar min Yana da Abdul nake waya ManaKatse shi nayi a dan tsawace Ina "Wlh karyane Mahfuz da mace kake waya bada Abdul kake waya ba""Ni nake miki karyar"?Yace Yana nuna kirjinsa fuskarsa ta sauya daga murmushi zuwa bacin rai"Ai nasan karyar ne mahfuz dan idan da Abdul zaka yi waya bazaka fito waje kayi wayar ba, jiya ai naji duk hirar da kake yi da budurwar ko zaka rantse ba da budurwa kake wayar ba,Mahfuz wacece ita?dudu yaushe muka yi aure da har wata zata fara d'auke maka hankali jiya har ka barni a daki ka fito Palo Kuna video call har kana ce wa zata saka kayi mafarki a banza"?Dogon tsaki yaja ya ratsa ta gefena ya Shige ciki na juya da sauri raina na balain suya daki ya nufa nabi bayansa Ina cigaba da tambayar sa da wa yake waya amma ko kallona baiyi.Takaici yasa na fashe da kuka Ina "Mahfuz wacece ita mai na maka da zaka sakamin da cin Amana"?Banza ya bawa ajiya ta abinda bai tab'a min ba ya d'auko wayarsa ya fara lalatsawa kamar ba dashi nake magana ba,tun auren mu bamu taba hayaniya dashi ba,bamu taba dogon fada dashi ba,Mahfuz da nasani Ina d'an b'ata rai zai hau rarrashina Yana bani hakuri sai gashi yanzu kuka nake a gabansa amma ko kulani baiyi baYanda ya watsar dani ya bawa banza ajiyata yasa na fusge wayar daga hannunsa a zuciye ya dago da idonsa da suka dan rine sabida b'acin rai ya mik'omin hannu Yana "Bani wayata Lubna kafin na sassab'a miki""Bazan bayar ba Mahfuz har sai ka Gaya min da wacce Yar iskar kake waya"Mik'ewa yayi Yana k'ok'arin Magana naji wayar sa na vibrating a hannuna da alama ya cire ringing tone din a vibrating yasa.Da sauri na juyo da wayar naga SR ke kira a waya a cikin Sakani na dauki wayar na Kara a kunnena yayo kaina da balain sauri a daidai lokacin dana ji muryar budurwar da bazan tab'a mantawa ba a rayuwata wacce ta watsa min farincikina ta kusa zautar dani."Sugar lafiya kuwa naji ka katse wayar"Maganar daya fito a bakinta kenan "Allah ya tsine Miki shegiya kwartuwa"

Ihu na saka sakamakon murd'emin hannu da yayi ya fusge wayar a hannuna Yana "Ke wacce irin wawiya ce mara hankali kinsan wacce kike zaginta"?"Nice wawiya mara hankali sabida na zagi budurwar ka mahfuz"?Nace Ina nuna kaina hawaye mai zafi ya hau zubomin yaja dogon tsaki ya nufi wajen wadrobe din kayansa ya fito da kanan kaya hawaye kawai nake Ina kallonsa har ya gama canza kayan jikinsa ko kallona baiyi ba ya fice daga d'akin.Rawar da jikina keyi yasa na zube akan gwiwa ta na cigaba da kuka Ina tunanin ko dai mahfuz ba'a hayyacinsa yake ba har wani dumm na ringa ji a kunnena dana tuna sunan da Yar iskar ta Kira mahfuz dashi Sugar....


*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻‍♀

Glow🧖‍♀️


💯 tested nd trusted🤝

GuaranteeSannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 2*Bansan tsawon lokacin dana d'auka a durk'ushe a kasa  ba,zuciyata Kamar an cinna Mata wuta ban tab'a sanin haka nake da tsananin kishi ba kawai Ina hararo irin so da kaunar da mahfuz yake gwadamin ya fara gwada wa wata,har ta d'auke Masa hankali a kaina akanta ya cemin wawiya Mara hankali waya sani ma ko zance yake zuwa wajen tsininiyar yarinya da ta Kira mahfuz da sugar,har san da yake Mata ya Kai Muna kwance ya baroni a daki ya fito Palo dan kawai yayi waya da ita.

Ko dan na samu ciki hallitar jikina ya canza yasa mahfuz ya fara ganin munina

Tunanin daya darsu a raina yasa na m'ike a hankali na nufi wajen da mudubi yake na fara karewa kaina kallo tunda ga saman goshina tare da shafa fuskata.

Tunda na samu ciki wani irin kananan pimples suka feso a fuska ta suka Sakani Muni,siririn lebbena yayi kauri.Haka hancina da bai fiye tsini ba ya doke nasan cikin nan yasani muni ba kadan ba fari dai na Kara tunda ni fara ce.Baza'a sakani a sahun masu tsayi da kyau sosai ba akan dai mahfuz za'a sakani a sahun masu kyau duk da mace sai ta dan yi kwalliya kyaunta ke Kara fitowa.Kwalliya da nake yi yasa ake ganin kyauna sosai. mutum tara yake bai cika goma ba abinda na rasa shine nono banida cikar kirji Sam idan na ga mace mai kirji sai naji Kamar na sace ko dan mahfuz da sai da muka yi aure na fahimci Yana balain san no-no,kafin na samu ciki indai Muna zaune hannunsa na saman kirjina Yana shafawa wai idan ana yawan shafa shi Yana fitowa.Bansan Yana san nono ba sai da naga ya fara siyomin duk wani cream ko supplement akan na ringa Sha zai taimaka wajen fitomin da nono.Ba abinda banyi amfani dashi dan nono ya girma ko dan na farantawa mahfuz rai amma abin ya gagara daya ga na fara matsawa kaina ya ce min na daina takura kaina duk da haka burina na samu nono na ya girma idan na d'auke nonon ba wani abu a jikina da baya burge mahfuz.Idan ya dawo bashida wajen kwanciya sai a jikina ya gwadamin kaunar daya narkar dani a kogin Sansa burina bai wuce nayi abinda zan faranta Masa ba Koda bana so har na samu ciki banga canji a wajensa ba duk da mitar da nake akan cikin ya sani muni hakan na iya sawa mahfuz ya rage ji dani.Idan na ce masa nayi muni dariya yakemin yace shi bai gani ba ai cikin nan yasa kirjina ya ciciko,bamu tab'a fushi da juna ba,bamu taba sa'insa ba,bai tab'a gaya min bak'ar magana ba sai gashi wata Yar iska tana neman juyar min da kwakwalwar miji bansan adadin tsinuwar da nayiwa macen da ta Kira shi ba.Gajiya nayi da tsayuwa agaban mudubin na koma Kan gado na kwanta Ina sak'e sak'en yanda zan biyowa mahfuz ni nasan idan ya dawo dole ya bani hakuri dan baya iya dogon fushi dani dole na nuna Masa bacin raina na Kuma jawo shi jikina na binciki wayarsa nayi blocking din Yar iskar yarinya da take kiransa,da Wanan tunanin na samu nayi wanka abincin ma da kyar naci sabida b'acin rai,sai duba wayata nake naga ko zai kirani ko zaimin text,har watsapp na hau naga ko ya ajiyemin sako duk shiru,hakan kuwa ya Kara saka min Jin haushinsa na tanadi masifar da zan Masa idan ya dawo.Kamar bazan yi girkin dare ba na daure na dafa jollof din shinkafa na hada Masa zobo.Nayi kwalliya kamar yanda na Saba na zauna zaman jiransa raina a had'e.Mahfuz bai dawo gidan ba sai goma da rabi na dare Ina Jin sa ya shigo da machine dinsa.Ciki ciki yayi sallamar ya hade rai da leda a hannunsa bai Kuma Kalli inda nake ba.Baki sake nabi shi da kallo har ya shige daki mamaki da bakin cikin halin ko inkular da ya nuna min ya rufeni,Mai mahfuz yake nufi dani yamin laifi ya nade tabarma da kunya a zuciye na tashi zan bishi har d'akin.

Kafin na isa d'akin na tsaya Ina bin umarnin zuciyata dana watsar dashi zai nemeni da kansa.

Da wanan tunanin na nufi daya d'akin da idan ba baki muka yi ba ba Mai kwana a ciki.Nan na shige zuciyata na balain tafasa 

Duk abinda nayi dan na samu zuciyata tayi sanyi duk a banza kofa kawai nake kallo ko zanga shigowarsa yazo bani hakuri ga yunwa da nakeji amma bana jin cin abincin.

Watsapp na hau sabida na samu nayi hira da Yan uwana da muke grp daya ko zan samu na rage bakin ciki dake Raina sai dai Ina hawa na duba mahfuz naga Yana online,wato ba abinda ya dame shi ni nasan da Yar iskar yarinya yake hira.Ban iya hakuri ba na rubuta "Mahfuz yanzu nice abar wulakantawa a wajenka ko,"?

Bai bud'e sakon da wuri ba na fara k'ok'arin Kara rubutu naga ya bude ya turo "hmmmmm" 

Bakin cikin bazai iya bani hakuri ko ya biyoni daki ba yasa na kashe data na wurgar da wayar,Idona akan agogo har karfe daya na dare sai juyi nake ba alamar bacci zai daukeni sai tunani daya cike min zuciya tunda mukayi Aure bamu taba raba shimfida da mahfuz ba sai gashi a sanadin haduwa da wata nayi fushi dashi bai ma kalleni ba.

Hawaye kawai ke zubomin Ina tsinewa macen da ke san Shiga tsakanina da mahfuz har ta samu matsayi haka a wajen mahfuz da zai k'i nemana a kanta sai da cikina ya tsufa mahfuz ya fara daga min kafa amma ko yayane sai ya nemeni ko period nake sai na Masa dabaru har hirar na tab'a yi da wata aminiyata take cemin namijin da baya iya daga ma kafa ba karamin gamsar dashi ake ba.Amma mahfuz yamin laifi akan Ina kishinsa bai iya bani hakuri ba,nifa yayi wa laifin nan amma shine ya kasa bani hakuri.Har tunani na Kara yi a tsanake dan naga ko dai zaginsa nayi cikin fushi batare da nasani ba sai dai banda karya tashi da nayi na zagi tsinaniyar da ta kira ban Masa komai ba.Zuciyata raya min kawai yake akan naje d'akin na sameshi wani b'ari na zuciyata na hanani akan shi yamin laifi shi ya Kamata ya nemeni.Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga dan bakin ciki sai biyu da wajen rabi na dare bacci yayi awon gaba dani. Ban tashi bude Idona ba sai wajen bakwai da minti goma Sha biyar.Na Mik'e da sauri Ina sallati na tsani naga sallah asuba ta kubcemin.Da balain sauri na fada bandakin na daura alwala na fito.Sai dai banida hijabi a dakin bana san zuwa dakina naga mahfuz sai dai ya zama dole tunda ba hijabi a d'akin.Fuskata a had'e na nufi dakina a hankali na tura k'ofar na shiga.Bangan shi a dakin ba na dai jiyo motsinsa a bandakin da alama wanka yake.

A madadin na d'auko hijabi na wajen da na hango wayar sa a saman bedside drawer na nufa da sauri na dauki wayarsa na fita daga dakin na koma daya d'akin na saka key na zauna a saman gado hannuna sai rawa yake.Ko da na bud'e wayar ajiyar zuciya na sauke da naga ba password.Message dinsa na fara shiga SR da na gani  ta turo message da bai bud'e ba yasa na bud'e message din jikina na balain rawa Message ta turo.masa wajen biyar na asuba da alama reply ta Masa "Kayi hakuri sugar banga kiranka ba sai yanzu kasan jiya ban kwanta da wuri ba how was your night my love zaka biyo d'in I missed you"Hannuna rawa kawai yake kirjina Kamar ya fado ji nake ma dakin na juya min"Lubna ki bud'e min k'ofar nan sabida Mai zaki zo ki dauki wayata?Wai me yake damunki ne"Najiyo mahfuz a bakin k'ofa Yana jijjiga k'ofar.Rawar da jikina keyi yasa ban ma iya mik'ewa ba na nemo lambar SR na fara kiranta a wayarsa bugu daya ta d'auka murya can kasa tace "Sugar ka iso ne"?"Kutumar bura ubanki tsinanniya ya iso wajen ubanki shegiya laananiya"Kit naji ta kashe wayar na Kara kiranta bata d'auka ba,ban hakura ba na cigaba da kiranta Mahfuz kuwa sai jijjiga kofa yake Yana kwalla min Kira akan nazo na bud'e k'ofar na bashi wayarsaGanin tak'i d'aukar wayata yasa na m'ike jikina na rawa naje na bud'e k'ofar mahfuz ya fado dakin da sauri ya fusge wayarsa daga hannuna idonsa ya Kada yayi jajjur cikin k'ak'ausar murya yace "Daga yau karki Kara tab'a min waya lubna wlh Kika Kara sai ranki ya b'aci kinji na fada miki"Ya fara k'ok'arin juyawa ya bar dakin na Sha gabansa da sauri hawaye na zubomin 


"mahfuz mai na maka da na cancanci haka daga wajen ?Mahfuz jiya baka san a ya na kwana ba amma ka kira wacce ba matarka ba dan kaji lafiyarta Kuma har zaka biya ka ganta kafin kaje wajen aiki, Mahfuz Kaine kamin laifi Ina gefenka ka fita Palo dan kayi waya da mace dan na tambayeka da wa kake waya ka rufeni da fada ka kirani wawiya mara hankali laifine dan nayi kishin ka har yaushe muka yi auren da zaka min haka?Ina duk alkawarikan da kayi min a baya Koda zaka kula mace mahfuz bazaka kwantar min da hankali ko dan cikin jikina ba? kayimin adalci kenan"?


Na karashe hawaye na zubomin


"Lubna kina da matsala shikenan dan kinji.ina waya da mace sai ta zama budurwa ta,kinsan ya muke da ita da zaki zageta ne?wajen aikinmu daya da ita kuma ba komai a tsakanina da ita sai Yar tsokana amma sabida balai kin dorawa kanki kishi,har kina Neman zagina,wane bayani kikeso na miki?


Mamakin maganar sa ya sa na kasa motsawa na zuba Masa Ido har ni zai cewa ba budurwarsa bace shi kuwa ganin ban magana ba yace "ba wani abu a tsakanina da ita ke kikesan ki dorawa kanki abinda ba haka ba,abinda yasa jiya ban waiwayeki ba naji Haushin karyatani da kikayi bai dace na miki magana ki karyatani ba har kina neman zagina kina nufin baki yarda dani ba kenan,nidai zanje wajen aikii dan na makara daga haka ya ratsa ta gefena nabishi da ido har ya shige ko minti biyar baiyi ba ya fito daga d'akin ganin Ina hawaye Ina Kuma tsaye ban motsa ba ya iso wajen da nake tsaye yana "Kina nan a matsayin da Kika sanki a zuciyata ba Wanda ya Isa ya kwaceni a wajenki gwara ki kwantar da hankalinki daga haka ya sunkuyo yamin kiss a kumatu ya juya Yana "Sai na dawo"


Lumshe idona nayi Dana shaki kamshin turarensa kukan da nake dannewa ya kwacemin har ga Allah ni nasan Mahfuz soyayya yake yi da wata amma yake San raina min hankali Ina balain San mijina dama yarinya nan ta barni da mijina ta nemo wani nayi nadama da ban dauki lambarta a wayarsa ba.


Ban tab'a tunanin mahfuz zaimin haka ba 


A daddafe nayi Sallah na dumama abincin da mahfuz baici ba naci dan yunwa nakeji.


Sai da na gyara ko'ina nayi wanka na zauna Ina tunanin hanyar da zan bi na raba mijina da SR dinan da take neman d'auke min hankalin Miji.


Kiran aminiyata farinciki rayuwata abokiyar sirrina ce ta katse min tunanin da nake mahaifiyata banida wacce tafita duk duniyar nan ba abinda nake boye mata a haka na taso sabida yanda take jana a jikinta ba Kuma Ni kadai ba haka duk kannena,koda na tashi aure ajiye kunya tayi a gefe ta karantar dani rayuwar aure da yanda zan kula da mijina.


Mahaifiyata a waye take dan nurse ce  bama na iya boye mata komai.


Ina sallama na hau gaisheta bata amsa ba tace "Mai yake damunki Lubna"?


Kamar Mai jiran kiris na fashe mata da kuka.


Sai da naci kuka na na koshi bata hanani ba ba ta kashe wayar ta ba Jin na tsagaita tace "Ina jinki lubna mai yake faruwa"


Tiryan tiryan na kwashe komai na gaya mata ba abinda na cire har yanda mukayi da Sr din da bansan sunanta ba sai da na gama tsaf ta sauke ajiyar zuciya tana "Wlh bansan bakida wayo da tunani ba sai yau,Lubna waye ya gaya miki ana yiwa namiji haka,waye ya gaya miki ana fada da budurwa Miji a waje,salon ki jawowa kanki raini,daga lokacin da Kika d'auko wanan hanyar kin kashe kanki da kanki ai komai dan wayo ne da dabara wlh na raina wa wayon ki Lubna,ai kiyi fushi da mijinki ko kiyi gaba dashi dan kin gano Yana da budurwa ba shine mafita ba dan kin nisanta kanki daga wajensa ne kin kusanta shi da budurwar tasa dan su maza haka suke Abu kad'an ka d'auke musu hankali,daga lokacin da Kika fara wanan haukar fita zaki nayi a zuciyarsa ya  fara ganin aibunki,waccen kuwa dama burinta ta samu ta kwace shi, karki sake wanan gangancin yanzu damara zaki daura ki jawo mijinki jikinki cikin kirsa ki rabashi da wancan yarinya cikin ruwan sanyi,ki rubanya kyautatawarki a gare shi.


Ai ke mijinki ma Yana shakarki tunda a boye yake Mata waya kinsan akwai mazan da agaban matansu zasu yi wayar sai dai ta hadiyi zuciya ta mutu.


Ki nesanta kanki da tab'a wayarsa ko da Kinga an turo masa text an Kira karki sake ki nuna Masa kingani cikin salo zaki rabashi da ita, kiringa kai zuciyarki nesa kishi hauka yake sawa da tarin nadama, kifita a zuciyarsa yaji ma gwara yayi auren kawai tunda kin k'i ki kwantar masa da hankali,ba dai text take tura masa ba kema sai ki dage wajen tura masa,Yana fita ki kirasa kiji lafiyarsa sau uku kafin ya dawo anan zaki ga hankalinsa ya fara rabuwa gida biyu har kiyi nasarar dauke masa hankali akan wacce yarinya ki fito da salo salo na soyayya da bai sanki dashi ba kiga ikon Allah"


Sai da muka shafe awa daya mahaifiyata na bani shawara na Kuma ji dadin shawarawarin da ta bani duk da ba k'aramin dauriya zanyi ba dan Ina da tsananin kishi bana iya controlling kaina idan ya motsa min.


Koda muka gama waya wacce take min lalle na Kira akan tazo tamin na Sha damara dawo da hankalin mahfuz kaina insha Allahu sai na raba shi da SR dinanMAHFUZ


Allah Allah yake ya isa gidansu Hadeeza dan ya bata hakuri tunda ya fito daga gida yake kiranta a waya taki d'aukar wayarsa.


Koda ya iso k'ofar gidansu ya cigaba da kiranta a waya bata dauka ba sai da ya mata text akan ya iso Yana waje ta fito Yana jiranta.


Sai da aka kwashi mintuna  wajen goma Kafin ya fara shako kamshin turarenta daya saka shi lumshe Ido ya bud'e Idonsa a hankali ya zuba Mata tana daga bakin k'ofa a tsaye ta harde hannayenta a kirjinta ta had'e Rai......
*

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 3*


Sauk'owa yayi daga Kan machine d'in fuskarsa d'auke da murmushi dan yasan fushin zagin da lubna ta mata take yi.

D'auke kanta tayi ta maida gefe Mahfuz ya sake sakin murmushi Yana "Kiyi hakuri wlh wanka na Shiga ta d'auki wayar bansani ba""Jiya ma haka kace wanka ka Shiga ta d'auki wayar ta zageni kaga ma d'aukar wayarka bashida amfani tunda ko na d'auka itace ta bugo dan ta zageni na rasa mai na tare mata inaga baka tab'a bata labarina ba in ba dan kaddara ba tasan bata Isa ta rigani samunka ba"Tace tana Jan siririn tsaki"Kiyi Hakuri hakan bazata sake faruwa ba ki dan saki fuskarki mana sweet dina"Sai a lokacin ta dan saki murmushi tana "Hmm Mahfuz ya zancen namu saura wata biyu naje gida fa"?"Karki damu insha Allahu madam na haihuwa zan yunkuro ki kwantar da hankalinki

Sai a lokacin Hadeeza ta saki murmushi tayi wal da Ido ta juya ta koma cikiBata fi minti biyar da Shiga ba ta fito da wani leda mai dan kyau ta mik'awa mahfuz daya washe baki Yana "Bakya gajiya sweetyna"

Ya bude ledar ya dauko dan karamin flasks din  potato balls ne a ciki ai sauce din albasa sai kamshi ke tashi  har dasu chocolate dasu  biscuit.

Yana Jin dadin yanda Hadeeza ke hada Masa break fast sabo da girkunanta yasa baya damuwa yaci na gida duk da yasan lubna itama ba a baya bace wajen iya girkin.Bai tab'a tunanin zai dawo da Hadeeza rayuwarsa har ta samu gurbi a zuciyarsa ba.Dan ta wulakanta shi a baya kafin ya had'u da Lubna yaso ya auri Hadeeza sai ta nuna Masa tafi karfinsa,dan zai iya cewa shine mai karamin karfi a manemanta.

Yana ji yana gani ya hakura da ita,Allah cikin ikonsa ya hadu da lubna da ta saka shi manta wata Hadeeza har yaji a yanzu yasan ya had'u da wacce take Sansa sabida Allah Tuni ya shafe babin Hadeeza ya manta da ita har Allah yayi aurensa da lubna wata hud'u da aurensa sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa koda ya daga a gigice ta jefa mishi tambayar "Mahfuz dagaske ne kayi aure"?Duk da yasan itace cewa yayi "Da wa nake magana"?

Kamar zatayi kuka tace "Haba Mahfuz Kamar ya da wa kake magana Hadeeza ce"

"Wacce Hadiza wai kimin bayani nagane"? yace Yana  hararar wayar dan karfin hali yake gani a wajenta""Mahfuz dan Allah ka bari nasan kasan wacce take magana so kake kawai ka wulakantani"Tsaki yayi ya kashe wayarsa ya danna lambarta a block dan kallon mai kwadayin abin duniya yake mata ko uban Mai yasa ta kirashi yanzu ko kunya bata ji ba.Kwana biyu a tsakani ta sake kiransa da wani lambar Yana Jin itace ya Kara kashe wayarsa Yana mamakin mai take nema a wajensa.

Bata hakura ba ta hau tura Masa message ta watsapp da  message ko karantawa baya yi sai ya goge.Bata tab'a fashin kiransa ba Kiran da take masa har da tsakar dare akan dole ya koma kashe wayarsa daddare ranar da abin ya ishe shi Yana d'aukar wayar yace "Wai Mai kikeso a wajena ne Hadeeza naga mun rabu nayi Aurena mai Kuma kike nema a wajen wanda ba ajinki ba"?Cikin muryar kuka tace "Mahfuz yanzu dagaske kayi aure kana nufin ka hakura dani ya kake so nayi da san da nake maka wlh ko a baya Ina kaunarka wlh gwadaka nake daga naje gida na dawo kawai naji labarin aurenka a wajen Abdul (A gidan kanin mahaifinta take a zaune tana karatu Iyayenta suna garin gombe)

Tsaki mahfuz yayi yace "Hadeeza ba gwadani kike ba a samarinki da kikeso ki aura aka yaudareki shine yanzu Kika nemoni nidai a yanzu nayi Aurena na auri matar da nake balain so da kauna muna zaune lafiya Dan Allah ki rabu dani ki daina kirana a waya"Daga haka ya kashe wayarsa ko minti biyar ba'ayi ba sai ga message kaca kaca daga wajenta na ban hakuri da irin san da take mishi ya  bata dama ta gwada mishi irin san da take masa,ta yarda zata je ata biyu za Kuma tayiwa matarsa biyayya.Ko ta kanta bai bi ba ya danna Mata blocking dan ko mai zata yi bayajin zai saurareta shi da Allah ya bashi finta ma Lubna Mai so da kaunarsa ba abinda ta rage shi dashi.Ga mamakinsa Hadeeza haka ta cigaba da canza lambobi tana kiransa ko da zai gaya mata bak'ar magana hakan bazai saka ta fasa kiransa ba har ta kai message din safe daban na rana daban na dare daban.Bai tab'a bari lubna tagani ba take yake gogewa dadin dayaji  lubna bata mai bincike bata damu da taba masa wayarsa ba.

A haka ya samu shekara da Aurensu da Lubna watarana yaje wajen aiki awa biyu a tsakani sai ga Hadeeza a office dinsa.Rabonsa da ita shekara biyar kenan taci kwaliyya ta Kuma yi kyau kamar ba ita ba ta canza akan sanin daya mata a baya ta Kara gogewa sai kamshin turare take. Ledar da ta shigo dashi ta ajiye masa agabansa ta langabar da kai ta hau matsawar kwalla.

Mahfuz kuwa kau da kansa yayi yana "Hadeeza dan Allah mai kike nema a wajena""Ba abinda nake nema a wajenka so nake kawai komai ya wuce mu cigaba da soyayyar mu""Shekara daya da Aurena Hadeeza idan ba yaudararki kikeso nayi ba banida ra'ayin yin soyayya ko na Kara aure matata ta isheni rayuwa Dan Allah kije ki nemi wani"Bai idda magana ba ta fara hawaye har da sheshek'a mahfuz ya shareta ya cigaba da danne danne a laptop din gabansa sunansa data Kira yasa ya dago ya kalleta"Allah ya jarrabceni da kaunarka mahfuz bansan ya akayi na wayi gari cikin tsananin sanka ba amma tunda kace haka dan Allah Ina neman alfarma mu cigaba da zumunci ka zama abokina""Ana abota tsakanin namiji da mace ne Hadeeza cigaba da muamalla dake kamar dai muna soyayyar kenan Mai amfanin haka""Dan Allah Mahfuz iya alfarmar da zaka min kenan ko ba kullum ba muringa waya ko chatt har Allah ya yaye min"Burinsa kawai ta tafi daga mata Kai kawai yayi yace jeki naji"Washe baki tayi ta mike tana "Nagode mahfuz ga wanan ba yawa sai na kiraka anjima"

"Hadeeza karki kirani kinsan inada mata kidaina kirana anyhow""Bakada matsala"

tace tare da sakar.masa murmushi ta juya tana wani irin takun daya sa Mahfuz kasa d'auke idonsa akanta har ta fice.Sai da ya gama abinda yake ya bude ledar da ta kawo turare ne.masu kamshi sai snacks da akayi wrapping a foil paper har zai mayar da snacks din ya gutsiri meatpie din yaji ya masa dadi a haka ya gyara Zama yaci iya Wanda zai iya ci dan ta hutashe shi siyan abincin Rana, lubna taso ta ringa aika Masa da abincin rana ya hanata dan baya san ya wahalar da ita.Tunda ga lokacin Hadeeza da zage wajen zuwa office d'insa tun bai wani bata fuska ba har ya fara bata fuska duk zuwan da zatayi da kalar abinda zata kawo Masa, text kuwa haka take tura masa.Bai tab'a d'aukar wayarsa ya kirata ba sai dai ita ta Kira shi.

Yau da gobe a hankali ya fara damuwa da lamuranta har idan bata zo wajen aikinsa ba bayajin dadi, yayi balain sabo da snacks masu Dadi da take kawo Masa.

A irin wanan yanayin ta daina aiko Masa da text din da ta sabar.masa dashi,ta bar zuwa office d'insa haka.kawai.yaji ya damu tun Yana ganin zai iya daurewa har yaga bazai iya ba aranar da aka samu sati daya baiji daga wajenta ba ya kirata a waya sai daya mata.miscall ya kusa goma Kafin ta daga murya can kasa da Sunan bata da lafiya shiyasa yaji shiru Nan kuwa karya takeyi so take ta gwada shi taga ko ya damu da ita.

Ana tashi daga wajen aikin ya kirata ta mishi kwatancen gidan da suka koma bai Sha wahala ba dan ba wani nisa tsakanin gidan nasu da wajen aikinsa.

Sai gashi har da kayan dubiya.

Har dan karamin palon gidan aka masa iso da alama ba kowa a gidan sai kannenta da suka kasance yaran kanin mahaifinta.


A kwance ya sameta a doguwar kujera ta Sha kitson attach da tayi parking,sai riga yar kanti armless da taje mata har kasa duk da batayi kwalliya ba bata yafa komai ba tayi wa mahfuz kyau.


Nanarkewa kawai take tana shagwaba Kamar bazai tafi ba lubna dake ta kiransa a waya yasa ya Mik'e ya Mata sallama ya ajiye Mata kayan dubiya ya fito.


Wani ikon Allah Koda ya dawo gida suna Hira da lubna Yana tuno Hadeeza da yanda ta ringa Masa shagwaba tunda ga wanan lokacin ya dawo da Hadeeza rayuwarsa ta samu matsayi a zuciyarsa dan ta Kai yanzu har breakfast take Masa idan zai wuce ya karba da Rana ma abincin take aika Masa.

Dak'yar yake yakice cin abincin dare a wajenta gudun kar Lubna ta zarge shi.

Zuwa yanzu baya iya kwana biyu bai ga Hadeeza ba duk da ba abinda Lubnarsa ta rage shi dashi wanan kenan.

LUBNA

Jan kunshi mai kunshina ta rangada min a hannu da kafa.

Tana ciremin na sallameta ta tafi na hada Abubuwan da nake dan gyaran jiki dashi na hada na mulka a jikina dashi sabida fatata ta Kara laushi.

Iya kokarina zanyi dan na dawo da hankalin Mahfuz kaina bazai yu wata Yar iska can ta kwace min shi ba,nima sai a yanzu naga wautata da na hau fushi da shi,waya sani ma ko kwana ma yayi jiya yana waya da yar iskar SR.

Sai da na goge ko'ina na  jikina na Shiga wanka har wani iska naji Yana Kara Shigana.

Mahfuz na san shinkafa da wake da salad hakane yasa na dafa shinkafa da wake na hada masa zobo sai da na gama na koma d'akina Ina duba kayan da Zan saka yau nayi Masa kwalliya yasan har yanzu da saurana ciki ne kawai yasa bana kwalliya duk kayana sun min kad'an dak'yar na samu wani kamfala da nayi wa dinkin bubu mai kalar dorawa da bak'i ya shigeni ya kuwa min kyau dan na cika kayan bansa breziya ba dan mahfuz bai fiye San na saka breziya ba, Hoda da Jan baki na shafa Nima kaina nasan nayi kyau na mulka jikina da turare na fito daga d'akin na koma Palo na zauna.

Wayata na dauko na kira shi a waya Yana fara ringing ya dauka na sauke ajiyar zuciya da naji muryarsa 

"Matata ta kaina kin sauko kenan"?

"Hmm dama ni ba fushi nayi ba kishin mijina kawai nake aka nuna nayi laifi"

"Mijinki nakine ke kadai bai Kamata ki dagawa kanki hankali ba"

"Tom mijina ya Kamata ka dawo yanzu matarka nasan ganinka"

"Mai Kika ajiyemin"?

"Kaima kasani"

nace Ina sakin murmushi kamar Ina gabansa

Murmushi yayi yace gashi nan ya kashe wayarsa yana kashe wayar Kiran Hadeeza na shigowa wayarsa.

Bayaso ya d'auka tace Masa yazo tunda har ya samu lubna ta sauko da kanta Kamata yayi shima ya faranta Mata.

Kashe wayarsa yayi gabad'aya dan yasan Kira zatayi tayi

Ana kiraye kirayen sallah magriba naji tsayuwar machine d'in mahfuz ido na zubawa kofar har ya shigo idonsa kyam a kaina Nima idon na zuba Masa ina dan sakin murmushi dan har dan sakin baki yayi nasan mai hakan ke nufi 

IIyye wai duk wanan kwalliyar ni akayiwa Kinga yanda kikayi kyau kuwa aikuwa ya Kamata na biya kudin kwalliyar nan daga haka ya nufo wajen da nake baiyi wata wata ba ya daukeni dak'yar Yana nishin nayi nauyi 

Nasan Mai yake nufi ce Masa nake ya bari muyi sallah fir yak'i har sai da muka samu nutsuwa da juna na gamsu da mahfuz nawane ni kadai ba wata Yar iska da ta Isa ta rabani dashi sannu a hankali zan rabashi da wata SR.

Tare muka yi wanka muka yi sallah mu kaci abinci tamkar lokacin da nake amarya.

A kan cinyarsa bacci ya d'aukeni Yana ta shafa min kaina Ina jinsa ya d'aukeni dak'yar ya je ya kwantar dani a d'aki bacci mai dadi da nutsuwa  yayi awon gaba dani.

MAHFUZ

Daga sakin munsharin da lubna keyi yasan bacci yayi awon gaba da ita,baisan Mai yasa hankalinsa ya rabu gida biyu ba so yake kawai ya Kira Hadeeza ya riga ya Saba sai sunyi waya ko video call yaji muryarta ta masa shagwaba a hankali ya zare jikinsa daga jikin lubna cikin sand'a ya fito daga d'akin  ya fito daga palon ya fita can waje gudun ma Kar lubna ta Kara kamashi.

Akan dakalin gidan ya zauna ya fara Kiran Hadeeza da tak'i daga wayarsa hankalinsa yayi balain tashi hakane yasa ya dage da kiranta.

LUBNA 

karar bud'e k'ofar palona yasa na bud'e idona dan banida nauyin bacci ko kad'an

Mikewa nayi a hankali na zauna da naga mahfuz baya d'akin.

Haka kawai gabana ya Yanke ya fadi Allah yasa ba Kara Kama mahfuz zanyi Yana waya ba.

Daga idona nayi na kalli agogon d'akin 12:20am.

Saukowa nayi daga Kan gadon haka kawai naji zuciyata na rayamin Mahfuz na palo Yana waya da Yar iskar yarinya Nan da bansan adadin tsinuwar da na mata ba.

Kishin daya rufe min ido yasa na fito daga d'akin da sauri sai dai Koda na fito baya palon hakane yasa nayi wajen tsakar gidan dan k'ofar palon a bud'e yake haka ma k'ofar gidan dagani sai sleeping dress na nufi wajen k'ofar a hankali kirjina na bugawa,zuciyata Raya min kawai take na koma Kar naji abinda zai daga min hankali daya zuciyar tawa da bakin kishi na ingizani da gwara na ganewa idona mai mahfuz keyi waje.

"Dan Allah kiyi hakuri haba mana na fada miki bada gangan na kashe wayar ba abinda ya sauka a kunne na kenan....


*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻‍♀

Glow🧖‍♀️


💯 tested nd trusted🤝

Guarantee

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 4*

          

                Runtse idona kawai nayi jikina na rawa badan nayi da gaske ba ba abinda zai hanani faduwa.


Tamkar a handsfree ya saka haka nake jiyo maganar ta Cikin shagwaba da kuka


"Dan kaga Ina sanka da kaunarka kake wulakantani mahfuz mai yasa kake min haka"?


"Wlh ba haka bane haba sweetyna ya za'ayi na wulakantaki ban isa ba cajina ne ya d'auke Kuma wani uzuri ya tasomin naje gidanmu ban baro can bama sai goma na dare wlh "


"Wlh ban yarda ba kace matarka dai ta kwace wayarka ta kashe ta hana ka zuwa wajena na dade da sanin tsoranta kakeji ka sa na sha wahalar dafa maka abinci har konewa nayi a hannu"


"Ya salam dan Allah kiyi hakuri wlh ba da gangan naki zuwa ba ki hakura Mana karki sa na kasa bacci"

"Um um bazan hakura ba sai ka goyani Kuma wlh sai ka biyo gobe kacinye abincin Nan shine kawai zan hakura" 


Dariya mahfuz ya kyalkyake dashi Yana "Angama sarauniyar mata idan na fara goyaki sai kin gaji gobe weekend bana fitowa da wuri wajen 10 zanzo a dumama min abincina,kinyi kitso da kunshin"?


"Emana har kwalliya nayi fa da sabon Kaya kak'i zuwa"


"Haha karki damu gobe idan nazo zan ma biya kudin kunshi da kitso amaryata kifita wajen haske na kiraki video call"Iya abinda na iya jure ji kenan zuciyata kamar ta fado sabida tsananin bakin ciki mutumin daya gama tumurmusheni san ransa da tsohon cikina shine yanzu ya baroni a daki yake zuba soyayya da wata.


Wutar kishi kawai ke ruruwa a raina Ina Jin kamar na rufe kofar na kulle ya kwana a waje ko yaje wajenta ya kwana da bakin ciki da takaici ace kina iya k'ok'arinki akan ki kyautatawa namiji amma shi ba take yake ba zuciyarsa na wani wajen.


So nake na bar gurin amma.kafafuna sunki bani hadin kai,haka na zubawa mijina Ido,dake ta  murmushi kamar an Masa bushara da gidan Aljanna har Mai nayi Masa haka,dame na rage shi da zai min irin wannan sakayyar bana ma iya gani sosai sabida hawayen daya cikemin idona.


Nasihar mahaifiyata kawai ke dawo min kaina da kyar na iya danne abinda nake ji da shaidan daya ke ingizani akan na kulle k'ofar ya kwana a waje ko naje na cakumu wuyan rigarsa na dadana Masa ashar.


Dak'yar na koma ciki Ina Shiga daki na kwanta naja bargo har saman kaina hawaye na cigaba da zubarmin zuciyata na suya,daga yanda Mahfuz ke magana da yarinya nan ba karamin so yake Mata ba har baya iya bacci idan baiji muryarta ba, wato shiyasa yanzu bai damu da yaci abincina ba? wacece yarinya nan,da take San kwace min miji,.har tana Masa shagwaba da sai ya goyata,tunani na tafi mai zurfi naga ko dai akwai ta inda na gaza har wnan yarinya ta dauke masa hankali Ina matarsa ta sunna ya baroni a daki ya fita waje dan kawai yayi waya da ita,tsafta, girki mai dadi, uwa uba iya gado,daga samun cikina na zama raguwa,Ina da kunya amma sabida kawai na faranta masa, duk da ni ba jarababiya bace har nemamsa nake da kaina,dan naji matan da  suke  neman miji da kansu  daban suke a wajen mazajensu.


Ganin ya dade bai shigo ba yasa na daga kaina na kalli agogo karfe biyu saura minti goma,wasu matan na can rungume a kirjin mazajensu ni gani a kwance nikadai mijina na waje Yana Shan soyayya.


Motsin rufe k'ofar Palo yasa na d'ad'a Jan bargon kaina.


Ina jinsa ya shigo cikin sand'a har da lekani kafin ya kwanta a gefena a hankali ko minti goma baiyi da kwanciya ba naji Yana sakin munshari.


Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga har aka Kira sallah na Mik'e naje na daura alwala na tada Sallah.


Har na iddar bai tashi daga bacci ba ta Ina zai tashi ya kwana Yana waya.


Ko ganinsa bana so nayi hakane yasa na koma Palo, so nake na taushi zuciyata na daure Kar na nuna Masa komai a fuska nabi shawarar mahaifiyata dan tunda na taso duk shawarar da ta bani idan har nabi Ina ganin haske.


Yanda nakejin jikina nasan ko tsinke bazan iya dagawa ba nama wahalar da kaina dafa Masa abinci shi da zaije wajen budurwarsa yaci dumame.


Haka nayi kwanciya ta a dogon kujera wajen tara sai gashi ya fito Palo Yana "Uwar biyu shine yau baki tasheni nayi Sallah ba ko wlh bansan ya akayi na makara haka ba,A'a lubna lafiya kuwa ya Naga idonki a kumbure ko bakida lafiya"?


Duk maganar da yake ban daga kaina na kalleshi ba,ban tabbatar idan na Budi baki dan na masa magana ba magana zan gaya Masa ba hakane yasa ban magana ba na ja bakina na tsuke Kai kawai na gyada masa da Sunan banida lafiyar"


Kamar gaske ya nufoni da sauri ya zauna tare da jawoni jikinsa Yana tattab'a jikina.


Na janye na koma na kwanta sam bana San ganinsa duk abinan da yake na munafircine Yana da wacce yake so da kauna.


"Jiya Kuma kalau kika kwanta fa,Allah dai ya saukemin ke lafiya sannu kinji"


Yace tare da manna min kiss a goshi,nidai lumshe idona nayi, ba'a zagin miji amma na danna masa Ashar a zuciyata.


"Bari na dan gyara gidan mai zakici na dafa miki"?


Ganin ban bashi amsa ba yasa ya kara yimin sannu   ya fita waje nabishi da mugun harara inajin Kamar na jawo shi na rufe shi da duka,sabida me zai nuna min kulawa alhalin Yana da wacce yake so da idan baiji muryarta ba baya iya bacci,a yanzu Kuma banida burin daya wuce na san wacce yarinya ce wanan da har ta d'auke masa hankali.


Bai dade ba ya dawo da leda a hannunsa daga kamshin nasan kosai ya siyo Ina balain san kosai da kunu,Yana cikin abincin dana fiso na karya dashi da safe kitchen ya wuce dama muna da garin kunu,da alama shi yake damawa.


Yanda yake nuna damuwarsa a kaina yasa wani bakin cikin Kara turnikeni duk abinan da yake min da wata a zuciyarsa.


Motsinsa da naji yasa nayi saurin maida idona na rufe Ina jinsa ya ajiye kofin daya damo kunun a ciki ya ajiye Yana "Lubna tashi ki karya kinji ga magungunan ki nan sai ki sha.


Ya jawo kafafuna kasa.


"Bana Jin cin komai"


"Ki daure mana kinsan baaso mace Mai ciki ta ringa wasa da abinci ko dan abin cikinta"


yace Yana kawo kosai bakina na d'auke kaina Ina "zanci anjima"


Tilasta min ya ringa yi naci nasan nacinsa akan dole nasaka hannu na fara cin kosai na karbe kofin a hannunsa dan bana San munafircin wani bani a baki.


Dadin daya min yasa na zage naci kosai baifi biyar ba na bari, na Sha maganguna na, ya dauki flasks din ya Kai kitchen,ya fito da tsintsiya ta share palon har da mopping mahfuz ba dai baya ba wajen aikin gida idan dai Yana nan, wanke wanke ne kawai bayamin.


Mai Mahfuz yake nema a wajen wata ya mace dan Allah mai na rage shi dashi daga kaina nayi na kalli agogo tara da rabi karfe goma sukayi da budurwarsa akan zaije wajenta bari naga ko zai hakura da fitar na ayyana a raina a daidai lokacin daya gama goge kayan kallon ya fara k'ok'arin nufar d'akin da a raina nasan wanka yakeso yayi ya fita.


"Kai mai zakaci"?


Na jefa mishi tambaya tare da zuba Masa Ido


"Ai zanje gida yanzu inaje can sai na karya na taho Miki da abincin rana ba sai kin wahalar da kanki wajen girki ba kiyi kwanciyarki ki huta kawai"


"Indai har dan abincin zaka fita yau weekends daya Kamata ka zauna a gida na samu kulawarka Zan daure na maka girkin ba sai kaje ko'ina ba""Ba iya dan na karya zan fita ba,Hajiya tace tana san ganina Yau bansan neman da take min ba"


Ko kunyar yanko karya baiyi ba na gyada kaina kawai ina Jin wani irin zafi a zuciyata bai kara cemin komai ba ya shige daki na fara tunanin.hanyar da zan bi na hana shi fita.


Tunanin daya darsu a raina yasa ni mikewa na nufi d'akin nawa Ina k'ok'arin.murda.kofar naji muryarsa Yana "Nan da minti goma Zaki gani wlh  na shirya"


Murda k'ofar nayi na Shiga yaya saurin sauke wayar daga kunnesa ya cigaba da goge jikinsa murmushin da bai Kai har zuci ba na sakar Masa Ina "bari na saka Kaya nabika dama na kwana biyu banje gidan ba""Keda bakida lafiya Lubna Kika je can ma hayaniya kawai ta isheki kiyi kwanciyarki ki huta kawai bazan dade ba Zan dawo"


"Aaa nima inaso na dan fita na Sha iska bana san na zauna Ni kadai a gida kamar mayya"


Take naga fuskarsa ta sauya ya Kuma kasa min magana na wuce shi na nufi wajen wadrobe na bud'e dan yau zanga iya gudun ruwansa.

 


Bakar doguwar Riga na jawo na fara k'ok'arin sakawa a daidai lokacin da wayarsa ta hau vibrating na juya na kalleshi Ina "Kila hajiyar ce ke kiranka ka fada Mata tare zamu Zo"


"Lubna ba dadewa zanyi ba wlh yanzu zan dawo bai dace ma ki hau machine da tsohon ciki ba"Ban ce masa komai ba na saka hijabina na fita Palo dan wlh yau kafata kafarsa inyasan wata bai San wata ba.Mahfuz kuwa rasa yanda zaiyi da lubna yayi,ga Hadeeza sai kiransa take,bazai so yau ma yayi wa Hadeeza laifi ba, dabarar da ta fado masa hakane yasa ya shirya tsaf ya fito Kamar waya yake Yana "Wai da da Lubna ma zamu zo ok to shikenan sai kun dawo"


Ya sauke wayar daga kunnesa ya nufi wajen lubna Yana "Kinga ma hajiyar ce ta kira Wai sunje gaisuwar mutuwa sai anjima zasu dawo idan sun dawo sai muje,tunda kin hanani fita bari na fita waje na siyo abu na dawo yace da sauri Yana k'ok'arin yin waje ga wayarsa na vibrating.


Yana faramin bayani nima na shirya karyar da zanyi Yana zuwa bakin k'ofa na kwalla ihu tare da dafe cikina Ina wayyo Allah cikina Zan mutu"


A guje yayo wajena ni kuwa na cigaba da zunduma ihu.


Mahfuz ba karamin rikicewa yayi ba hakane yasa ya ajiye wayarsa akan kujera duk ya dauka da gaske ne banida lafiya 


Yayi waje da gudu wai zai nemo.mana machine Mai kafa uku Yana fita tsinaniyar na kiransa a wayaAikuwa da sauri na dauki wayar Ina dauka tace cikin shagwaba "Nagaji da jiranka fa haba Mana Nima fa ban karya ba yunwa nakeji Kai nake jira ka karaso muci tare""Tunda nake ban taba ganin jaka balagaza irinki ba,tom jiya mahfuz ya bani labarin irin nacin da kike Masa yace kuma.ba kaunarki yake ba dan haka kije ki nemi wani, shegiya asarariya ko kunya bakiji ba mutum da matarsa kina wahalar da rayuwarki wajen.masa girki har da sai ya goyaki yazo yaci abinci da Kika girki kamar mijinki"


Kit naji ta kashe wayar nayi saurin ajiye wayar na cigaba da zunduma ihu danaji Mahfuz ya shigo.
HADEEZA


Hawaye ne ya hau wanke Mata fuska ta zubawa wayarta ido......

*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻‍♀

Glow🧖‍♀️


💯 tested nd trusted🤝

GuaranteeSannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 5*


HADIZA


Kukanta taci ta koshi,duk zagin da Lubna ta mata ya hau tafasa mata zuciya,ashe dai hasashen da takeyi akan Mahfuz tsoron matarsa yake ji da gaske ne,Karo na uku kenan da Lubna  ke zaginta, ta rasa ya ake yi wayar ke zuwa hannunta,duk uban wahalar nan da take sha duk dan ta samu Mahfuz ya aureta,bata San tana San shi ba sai da yayi Aure, duk da sai da Wanda ta kwalafa rai da auren wani saurayinta mustapha ya yaudareta,hakane yasa ta komawa Mahfuz,dak'yar dak'yar ta samu ya fara kulata, shine matarsa take neman hanata rawan gaban hansti, taga alamar  idan har batayi da gaske ba,bazata bari  Mahfuz ya aureta ba,aikuwa idan ta san wata bata san wata ba ba boka ba Mallam sai ta auri mahfuz ta wulakanta Yar iskar matarsa da sam bata ma san sunanta ba balle tasan kamaninta ta matukar tsanar matar mahfuz Kamar ta kasheta haka takeji,shi Kuma mahfuz bari taga karyar da zai Kara shara mata tun jiya yake raina Mata hankali har ace ya kasa tsawatar wa shegiyar matarsa da take zaginta idan ta kirashi.


Bakin ciki ne yasa ta kashe wayar gabad'aya dan tasan ta kafu a zuciyar mahfuz gwara ta Masa barazana akan zata hakura dashi idan yaga da gaske ne dole ya tura manya gidansu ta gaji  so take kawai ta samu ta Shiga daga ciki ta fitar da lubna ma daga gidan ta bar mata mahfuz dinta.Mahfuz 


Gigicewar da yayi yasa Sam bai bi takan wayarsa ba har suka isa asibiti da lubna dake ta zunduma ihun wayo cikinta sai kuka take.


Koda suka isa ihun da lubna ke zubawa taki bari ma likita ya dubata dak'yar dak'yar aka samu tayi shiru.


Likitan ya dudubata,yanda take ihun cikinta yasa likitan yi mata allura.Ba abinda yafi komai faranta min rai sama da zagin da nayiwa Yar iskar yarinya nan, yanda na zuba drama  ba mai yarda ba Ciwon marar nake ba,dan har da kukana awar mu daya a asibiti aka sallame mu ya kashe wajen Dubu biyar a siyan magani sai yaje ya biya kudin kunshi da kitso nagani.


Koda muka isa gida yanda nake langab'ewa Ina matsar kwalla yasa bai motsa daga kusa dani ba sai aikin yimin sannu da yake.


Abincin ma sai shi ya shiga kitchen ya dora da wanan na samu na goge Kiran da tayi dazu so nake nayi ta hadasu fada.


Sai da ya bani abinci naci na koshi Ina yamutsa fuska ya bani magunguna na Sha.


Sanan naga ya dauki wayarsa yayi hanyar palo 


Na riga nasan Kiranta zaiyi a waya.


Fitarsa da minti biyar sai gashi ya shigo bansani ba wayar yayi ko baiyi waya ba,Ya zauna a gefen gadon Yana matsamin kafa da hannu daya Yana latsa wayarsa da hannu daya,Sam fuskarsa ba walwala ba Kuma abinda ya shafeni addua ma nake Allah yasa ta sosoka masa Ashar wlh da wayar zai shigo hannuna text zan Mata na zazzageta.


A ranar ma ban bari ya fita waje waya ba dan kwanciya nayi a kirjinsa,ko da bacci ya fara daukana idan na tuna sai nayi sauri na kankame shi.


A ranar dai baiyi waya da ita ba duk da naga alamar idonsa biyu ba bacci yayi ba


MAHFUZ


Tunda suka dawo gida yake gwada lambar Hadeeza yake jinta a kashe,ya dubata ta WhatsApp nan ma Bata hau ba ya rasa duk Mai ke mai dadi,yasan fushi tayi sam bai so yau baije wajenta ba,dan shima ji yayi Kamar ya dade bai ganta ba,burinsa bacci ya dauki lubna ya fita waje ya kirata a waya idan yaji a kashe ya kira Ameera kanwarta,muryrta da zaiji kawai zai saka ya samu nutsuwa sai dai lubna kankame shi tayi taki barin jikinsa abu kadan sai yaga ta bud'e idonta a haka ya kwanta kamar yayi kuka baccin Kuma yak'i daukarsa.


Allah Allah yake gari ya waye idan ya fita massallaci ya kirata a waya.


Wajen tara yaje gidan nasu.


Kiran sallahr asuba a kunnensa hakane yasa ya mik'e da sauri ya fada bandaki ya daura alwala a daidai lokacin da Lubna ta mik'e zaune itama tana yamutsa fuska


"sannu ya jikin naki"?


"Wlh har yanzu ciwo yake min ga kaina Kamar ya rabe gida biyu dan Allah ka zauna kaja mu sallah ba sai kaje massallaci ba"


"Haba Lubna jiya ma fa banje massallaci ba ai ana iddar wa zan dawo bari naje"


Yace da sauri tare da yin waje ya jefa wayarsa a aljihunsa.


Na tabe baki dan nasan Kiranta zaiyi a waya,yau ma bazan bari yaje ko'ina ba


Sai dai mayyar taci kanta,na tsaya ma Ina neman dorawa kaina hawan jini bayan ga hanyoyi nan da Zan bi wajen rabasu,yanzu wayarsa ta kara zuwa hannuna lambarta zan d'auka


Bai dawo gidan ba sai wajen shidda da rabi.


Daga yanda naga fuskarsa ba walwala nasan ko bai samu yin waya da ita ba ko Kuma ta zazzage shi Kamar yanda nake fata da Addu'a.Ban koma bacci ba na dafe marata na fara wash wash,ya dafe kansa Yana "Lubna wanan wane irin ciwon Mara ne"


Ban bashi amsa ba na hau matsar kwalla.


Mahfuz kamar ya sa kuka dan bakin ciki,dan Yana ta Kiran Hadeeza a waya bata d'auka ba,karshe sai text tayi Masa da Allah ya hada kowa da rabonsa bazata iya ba tunda matarsa ke controlling dinsa.


Ya Kira dan ya bata hakuri Sam taki dagawa,bashida burin daya wuce tara yayi yaje gidan nasu.


Sam bazai iya hakura da Hadeeza ba Yana jinta a ransa ba abinda yake Balain so da ita sama da shagwabarta ko ba'a fada ba yasan idan ya mallaketa zai Sha soyayya sai gashi yau ma Lubna na neman hana shi fita.


 magungunan ta ya d'auko mata ya siyo kayan shayi ya hada mata.


Sai dai Koda ta Sha bata fasa ihun ciwo mara ba,Yana ji Yana gani Lubna ta dabaibaye shi bai samu ya fita ba a ranar.


Hadeeza kuwa ta Kara cika tayi fam tana ganin wulakanci mahfuz din ke san yi Mata ta dauka da ta Masa text din zai zo gidansu da sassafe sai dai ko keyarsa bata gani ba.


Sam ba walwala a fuskar mahfuz har wani tsawa tsawa yake min idan zaiyi magana hannunsa manne da wayarsa nima bakin cikin duk wanan abun akan wata can a waje ya keyi dan kawai bai samu fita wajenta ba,har mamaki yake bani wlh bantab'a zaton haka daga wajen sa ba,

banga ta Zama ba ko Ina so ko bana so dole gobe zai fita Kuma yaje gidan nasu sai dai Allah ya kawomin mafita.


Daddaren ma ban bashi space ba haka.na manne Masa banga Kuma alamar zai fita waje waya ba sai tsaki da nakeji yanayi akai akai.Washegari kuwa da sassafe ya fice daga gidan kamar akan Kaya yake mahfuz da ni nake tilasta.masa fita sabida kar ya makara sai gashi yau wata ta d'auke masa hankali koma wacce yarinya nan ban yafe mata ba na share hawayen daya zubomin na dauki wayata dan na Kira Mahaifiyata ita kawai zan Kira na samu kwanciyar hankali dan nasan zata bani shawarwari masu kyau.


Mahfuz 


Dak'yar ya samu Hadeeza ta fito dan sai da yayi ta turawa gidansu Tama k'i d'aukar wayarsa.


Koda ta fito shi kadai ya hau maganar sa Yana bata hakurin dalilin dayasa bata ganshi ba Lubna ce bata da lafiya kwanan su biyu a asibiti bada gangan yak'i zuwa ba 


Sai a lokacin Hadeeza ta kalleshi idonta cike da kwalla tana "Mahfuz Ina kaunarka amma ya zama dole na hakura da Kai dan na riga da nasan b'atamin lokaci kake,wlh bazaka iya Aurena ba,bazaka iya rik'e Mata biyu ba,dan kana balain tsoron matarka mahfuz zagi da cin mutunci haka ta zuba min sau uku kenan tana zagina da iyayena har karuwa tace min idan har bata da lafiya zata zageni ne"?


"Wlh da gaske Lubna bata da lafiya ko dai wata ce ta kiraki ta zageki matar da bata da lafiya taya har zata kiraki ta zageki"?


"Hmm Mahfuz kenan karya Zan Mata kenan wlh Azeem bamu dade da waya da kai ba na sake kiranka ta d'auka ta hau zazzagina har da cemin Kai ba sona kake ba,na like ma Ina ta dafa maka abinci Kamar wata matarka"


"Ikon Allah Mahfuz yace tare da d'auko wayarsa ta Shiga call log na ranar asabar din sai dai Sam bai ga Kiran Hadeeza ba dan suna waya yake goge lambar yanzu ya haddace lambar baiyi saving a wayarsa ba har wane lokaci Lubna ta daga wayar tayi zagin bayan yazo fita ta fara ciwon maran


"Wlh Kinga banga Kiran naki ba""To na mata karya Mahfuz"


"Ba haka bane bance kinyi karya ba amma kiyi hakuri dan Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu"Dak'yar dak'yar ya samu Hadeeza ta hakura Inda yace Mata ta daina kiransa ta bari ya ringa kiranta da kansa gudun sake faruwan hakan da haka Suka rabu akan zata aika Masa abincin Rana,dan ba karya Yana Jin dadin abincin ta sosai.Yana isa office Kiran lubna na shigo wa wayarsa sai daya zauna ya daga wayar yana tunanin ko wani matsalar ne ya taso,ga mamakinsa Yana dauka lubna tambayar sa tayi ko yaje office lafiya dalilin dayasa ta Kira kenan.


Murmushi ya saki Suka dan tab'a hira da ita kafin ta Masa sallama.


Yana kashewa ta turo Masa kalamai masu balain Dadi ya hau mamakin Kira da text din da ta masa bata Saba da Masa hakan ba.LUBNA


Shawarwarin mahaifiyata na dauka,na zage damara wajen San na dawo da hankalin mijina kaina,hakane yasa muna gama waya da ita na kirashi a waya naji ya Isa office d'insa kalau.na Kara da Masa text dan mahaifiyata tace na dage da haka,da rana ma sai da na kirashi na sake Masa text Inda ya hau tsokana ta Wai ko dai soyayayar ce yau ta motsa min.Murmushi kawai nayi nace Masa ee.


Tunda ga lokacin ban Kara ganin tsinaniyar na kiransa ba,har wayarsa na bincika daya shiga bandaki dan naga ko zan samu lambarta,sai dai na gama dube dubena banga lambarta ba.


Ba karamin danne zuciyata nake ba dan Yana yawan fita wayar daren Koda kuwa a kirjinsa nake zai kwantar dani ya fita.


Na rasa mai yake nema a wajen wata,nasan da kunya yanzu ya ce zai Aure ko shekara biyu ban rufa ba.


 A cikin wanan yanayin cikina ya Shiga wata na tara dama mun riga da munyi dashi Ina shiga watan haihuwa na zan koma gida har sai na haihu,dan sai na fi samun kulawa a wajen mahaifiyata tunda haihuwa farine,ji nayi Kamar na fasa tafiya gida dan nasan yanzu mahfuz zai baje kolinsa wajen waya da budurwarsa a baya yakan ce jina kawai yake bazan je gida wanka ba,sai gashi shine Kan gaba wajen hada min kayana.


Ko da nayiwa mahaifiyata magana fada ta rufeni dashi akan na fiye kishi na watsar da komai na ringa kyautata wa mijina zato.


Da haka na tattara na koma gidan mu amma hankalina na wajen mahfuz,haka zuciyata zata tayimin sake sake akan Yana can Yana waya ko ya tafi zance take Zan kirashi a waya tunda bana nan dani.ya Kamata ya ringa hirar.


Muna cikin wayar ba dadewa zaice min zai kwanta bacci yake ji.


Bayan Yan mintina idan na kirashi zanji alamar Yana waya haka.zan cika fam.idan ya biyo Kiran sai yacemin da Wani yake waya.


Mahfuz 


Tafiyar lubna gida haihuwa ba karamin Dadi yaji ba dan yanzu kullum Yana gidansu Hadeeza anan yake cin na safe rana da dare,haka ya bude Mata bakin Aljihu.


Waya kuwa idan suka fara kamar bazasu rabu ba.


Duk da yakan ware lokacin da zaiyi waya da lubna gudun zargi.


A haka lubna ta samu sati biyu da komawa gida.


A yau daya kasance weekend ya Yanke ya dan wanke kayansa,ya gyara gidan inyaso yau yaje wa lubnar da ta dage akan yau a gidansu take so ya wuni ta ajiye Mai abinci yau ma zizilewa Hadeeza yake dan baya so tace masa yazo.


Ya gama wanki kenan Yana cikin gyara gidan sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.


Abin mopping din ya ajiye ya daga wayar "lek'o waje"


Shine kawai abinda tace tare da kashe wayarWayar yabi da kallo cikin mamaki kafin yayi wajen Yana lekawa waje ya hango ta a machine mai kafa uku taci kwalliya tayi kyau 


Wajenta ya Karasa Yana "Kai Ina zakije haka wai dama kin san gidana"Murmushi ta sakar Masa tana "idan inasan abu dagaske nakesan abun ka gama wankin ne ga abinci na kawo ma kasan bazan bari ka zauna da yunwa ba"


Mahfuz kasa ma magana yayi ta sauko da basket din abincin tana "Wai ko dai bakaji dadin zuwana bane"


Mahfuz keya ya sosa ya hau dube dube dan bayaso Yan unguwar suyi Masa wani fassarar,


"Kinsan Yan unguwar tamu suna da sa Ido"


"Tab Kai kake tsoron Yan unguwa ma muje"


Tace a daidai lokacin da ta bawa Mai machine d'in kudinsa 


Mahfuz Kamar Wawa yayi gaba da sauri ya shige gidan.


Yana dan mamakin Hadeeza da tazo masa har gida.


Hadeeza kuwa ko a jikinta da biyu tazo gidan so take taga ya gidan ma mahfuz din yake ta dade tana Neman wanan damar daya ce Mata lubnar ta koma gida.Suna Shiga palon ta ajiye basket din ta hau kalle kalle tana "Masha Allah gidan namu yayi kyau sai dai ya Mana kad'an nida Auntyna"


Murmushi ya sakar mata Yana "ki zauna na d'auko Miki ruwa ya nufi wajen da fridge ke,Yana d'auko ruwan yaga ta cire mayafi ta d'auko mopstick ta hau mopping....


LUBNA...
*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻‍♀

Glow🧖‍♀️


💯 tested nd trusted🤝

GuaranteeSannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 6*


Mahfuz duk kasa sakin jikinsa yayi Kamar Mara gaskiya sai yake Jin Kamar Lubna zata iya fadowa gidan.


Hadeeza kuwa ko a jikinta ta zage ta gama mopping ta fara goge kayan kallon sai ce mata yake ta barshi amma fir tak'i har sai da ta gama tsaf ta koma ta zauna tana "da akwai wuta har guga zan maka"


Murmushi ya sakar mata Yana "haba dai wankin ma bayarwa nake Mai wankin ne baya gari"


Tana k'ok'arin Magana wayarsa ta fara ringing gabansa ne ya Yanke ya fadi daya ga Lubna ke kiransa.


Mikewa yayi da sauri yayi hanyar d'aki ya kalli Hadeeza data kura Masa Ido Yana "Ina zuwa"


Yana shiga d'akin tayi sauri ta mik'e ta leka k'ofar da ta gani,ganin kitchen ne yasa ta tab'e baki ta leka daya d'akin da ke bud'e ta daga labulen nan ma ta tab'e baki tana "ko kayan kirki.ma Babu a gidan da sannu Zan shigo kifita insha Allahu"


Tayi sauri ta koma ta zauna ta cigaba da karewa palon kallo,Sam palon lubnar bai wani burgeta ba kayan lubnar ma duk ba masu tsada bane da zasu daga mata hankali.


Rigar jikinta ta kara gyarawa na fulaninta ya fito ta saman riga sosai,dan so take ta rikita mahfuz yayi ya fito ya aureta.


Da zata samu yanda take so da lubna ma kafin ta dawo daga haihuwa zata zo ta tarar da sunyi aure da mahfuz har ta tare,sai dai ta rasa mai yasa mahfuz ya kasa motsawa duk gani take tsoron lubna yake,so take ma taga hoton lubnar amma babu ko daya data gani a palon,wayar mahfuz Kuma akwai password a wajen hotunan,da alama shegiyar matarsa ce ta kirashi ya wani shige daki,take taji ranta ya fara b'aci ta had'e rai.


LUBNA


Kwalliya nayi sosai na gyara d'akin kanina dan nayi kewar mijina duk da yana zuwa ganina so nake yau idan yazo mu dan keb'e dashi na faranta masa rai dan nasan halin kayana hakuri kawai yake.


Da taimakon kanwata zainab na tuka Masa tuwon semo da miyar wake na jera duk a d'akin kanina.


Karfe biyu muka yi dashi akan zaizo idan ya gama wankin da yake.


Ganin biyu da rabi tayi baizo ba yasa na fara k'ok'arin kiransa a daidai lokacin da kiran makociyata ya shigo Mmn Iman"


Ina dauka tace "Lubna kin dawone"?"Na dawo Ina"?


Shine tambayar da na mata cikin mamaki


"Ina nufin kin dawo gidanki ne"?


"Aaa Ina gidanmu mmn imam Mai zai dawo dani nida na zo gida haihuwa lafiya kuwa"


"Eee toh lafiya ba lafiya ba wata naga kamar ta Shiga gidanki sai na dauka ko kin dawone"Kirjina wani irin bugawa yayi nace "wata kika.ga ta Shiga gidana wacce"


"Nima bansani ba wlh ko bakuwa kikayi batasan bakya nan ba"? "Mmn Iman da idonki Kika ga mace ta shiga gidana Dan Allah jeki dubamin wacece"


Tana k'ok'arin Magana na  katse wayar da sauri ko dai budurwa Mahfuz ce taje har gidana dan taga bana nan,? Yanzu mahfuz zai iya cin amanata?Mikewa nayi da sauri hankalina ma na neman barin jikina sosai zuciyata ke sak'a min kila budurwar mijina ce taje har gidana,


Wayar Mahfuz na Kira jikina sai bari yake sai dube duben mayafi ko hijabi nake akwai tazara daga gidanmu zuwa gidana amma tabbas zanje gidana na indai har naga mace wlh tallahi sai na raba ta da numfashin ta,Yana daga wayar nace "Mahfuz kana Ina"?


"Gani a gida na shirya yanzu zan taho"


"mahfuz karya kakeyi wlh mace ka kawo min har cikin gida sabida kaga bana nan, yanzu cin fuska da cin amanar taka har ta Kai ka kawo min mace gidana Mahfuz innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"


"Kanki daya kuwa wacce mace na kawo gidan kin fara ko"


Mahfuz yace cikin dauriya numfashin sa na Neman daukewa


"Ai gani nan a waje wlh tallahi idona idonta.mahfuz sai na rabata da numfashinta.mahfuz"


Na katse wayar mahfuz yayi waje da sauri a daidai lokacin da ake buga kofar gidan


Hankali a tashe ya d'auka  da gaske Lubnar ce hakane yasa yayi Kan Hadeeza aguje baiyi wata wata ba ya rike hannunta ta ya fara janta ya kaita daya d'akin ya  tura ta bandakin daya d'akin nasu


"Mai haka mahfuz lafiya kuwa"?


"Shiii kiyi shiru Lubna ce ta dawo"


Cire hannunsa tayi daga bakinta tana "Toh sai me dan ta dawo ai ba wani Abu mukayi ba shine hankalinka ya tashi haka Mahfuz"


"Dan Allah kiyi shiru Hadeeza Ina zuwa karkiyi magana "


Yace tare da jawo kofar yayi waje da sauri


Lubna 


Ina katse wayata Kiran makociyata na Kara shigowa wayata a daidai lokacin da na samu na tare abin hawa Ina dauka tace "gani a k'ofar gidan Ina kwankwasa wa"


"Ki taimaka min mmn Iman Ina hanya yanzu dan Allah idan har Kinga mace a gidana ki rikemin ita har sai nazo Dan Allah dan annabi wata kwartuwa yarinya ce take bibiyar mijina""Nidai Naga shigar mace banga fitowarta ba,ba lallai Kuma budurwar tasa bace kila bakuwa kikayi amma dai Ina kwankwasa k'ofar ba'a bud'e ba"Katse wayar tayi adai dai lokacin da Mahfuz ya bud'e kofar ganin mmn Iman ce dan.ya Santa yasa shi sakin ajiyar zuciya take zuciyarsa ta bashi ita ta gayawa Lubna mace tazo gidan,kila taga shigar Hadeeza gidan.


Ko amsa gaisuwar da ta masa baiyi ba yace "Yanzu Mai amfanin abinda kika yi mace da cikinta kin daga mata hankali,daga gidan mu aka aiko min da abinci kanwata ce kuma tsabar munafirci shine Kika Kira lubna kika ce Mata mace tazo gidana dan Allah bakiji kunya ba da kika zo kina kwankwasa wa dan ki tabbatar toh kishigo kigani"


Yace mata a dan tsawace 


Ja da baya mmn Iman tayi sam bataji dadin abinda lubna tayi mata ba 


"Wlh ba ni nace Mata mace tazo ba ni muciya nazo ara ma wlh"


Tsaki Mahfuz yayi ya rufe k'ofar


Mmn Iman itama ta juya da sauri ta shige gidanta bakin ciki Kamar ya kasheta banda b'atar basira da rashin hankali irin na lubna name zata kira ma mahfuz da zuwan zatayi ai bai dace ta kira mahfuz ba.


Mahfuz kuwa Yana jikin kofa Yana ganin mmn Iman ta shige gida yayi sauri ya koma bandakin da Hadeeza take itama ta cika tayi fam,bata bari yayi magana ba ta fito daga bandakin ta fito palo ta d'auki Jakarta bata saurari mahfuz dake mata magana ba ta fice daga gidan tana zuba sauri mahfuz ya balain Kona Mata rai har mace yake tsoro haka Kamar wata uwarsa,har da kaita wani bandaki ya kulle wlh da ace ma tazo ba abinda zai hana ta fitowa ta ganta sai dai duk abinda zai faru ya faru,taya Mahfuz zai iya Kara aure Yana tsoron matarsa haka,yanzu Yana nufin ma yafi fifita matarsa akanta,duk wahalar nan da take sha akansa shine zai wani kaita bandaki ya b'oyeta sabida Yana tsoron kar matarsa ta ganta,shi daya Kamata ma ya fara gayawa matarsa tun yanzu akan aurenta zaiyi.


Da tsanin bakin ciki ta isa gida tana zuwa ta hau watsapp ta fara zanna Masa ta WhatsApp akan ta gaji da wanan kumbiya kumbiya idan har yasan ya isa da gidansa ba tsoron matarsa yake ba ya turo manya gidansu.Mahfuz 


Wani irin Ajiyar zuciya ya sauke daya ga Hadeeza ta bar gidan,shi baiga abin Jin haushi dan ya b'oyeta ba yanzu da lubna  tazo ta ritsa ta mai zai ce Mata har ga Allah bai tab'a tunanin zata zo Masa har gida batare da ko tsoro ba,har mamakin confidence dinta yake,Koda ba wani Abu suke yi ba ai bai dace lubna tazo ta ga ya kawota har gida ba, duk wanan munafikar makociyar tasu ce ta jaza Masa Kuma sai ya rabata da Lubnar baiji dadin fushin da Hadeeza tayi ba ya Kamata ta fahimce shi.


Mahaukacin bugun da aka yiwa k'ofar yasa shi mik'ewa yayi waje ya ma riga da yasan lubnar ce sai daya je bakin k'ofa ya tuna bai d'auke basket din abincin ba


Yana bud'ewa lubnar ta Fada gidan tana hucci Mahfuz kuwa ya hade rai Yana "Lubna daga yau karki sake ki Kara min wanan haukar ke yanzu ko tararki akayi akace miki na kawo mace gidanan sai ki yarda kina nufin zargina kike"?Ko ta kansa ban bi ba na ratsa gefensa nayi cikin gidan sai da na hau napep naji Kamar na rufe kaina da duka da nasani ban Kira shi a waya ba da tahowa kawai nayi da kila na ritsa Yar iskar yarinya,ai nasan dole ma kafin na dawo yasa ta gudu zuciyata ko gezau batayi ba na yarda dari bisa dari itace ta biyoshi har gida dan taga bana Nan,


Basket din abincin dana gani ya tsakiyar palon ya Kara tabbatar min da zargina abinci ta kawowa mahfuz har gidan Aurena,kila ma har iskanci sun yi,dandaga muryar ta da naji da goyata da tace ayi nasan yarinya Yar duniya ce Yar iska 


Basket din na d'auka a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo Yana cigaba da bambamin fadan zargin sa da nakeyi.


"Mahfuz yanzu dan bana Nan shine zata kawo maka abinci har gida"?


"Lubna Nagaji da wanan halin naki ni nace Miki macece ta kawo min abinci tunda kika tafi kabiru abokina yasa ake kawo min abinci wai wanan wane irin Hali Kika tsiro dashi ne?kishi hauka ne"?Ni kadai nasan halin da nake ciki jikina har rawa yake mahfuz na san sakamin hawan jini, palona na fara karewa kallo Ina ganin kamar Zan iya ganinta ma a cikin gidan, 


Ban bi ta kan masifar da yake ba na Mik'e da basket din a hannuna na Shiga dakina tamkar zan ganta a ciki Koda na Shiga ciki ma har karkashin gado na tsugunna na duba na kurawa gadona Ido naga ko an kwanta a akai shigowar mahfuz d'akin bai hanani cigaba da dube dubena ba Inda yaja wani dogon tsaki ya nufi wajen kayansa ya fara zurawa


Na zauna a gefen gadon na zuba Masa Ido hawaye na zubo min

"Mahfuz mai na maka dana cancanci haka daga wajenka, mahfuz ko aure zakayi bai Kamata ka kawo budurwar ka har cikin gidanan tazo ta gane min sirrina ba,mahfuz ni nasan ba rageka da komai ba Ina iya kokarina dan naga na faranta maka rai, a yanzu da nake d'auke da cikinka bai Kamata ka daga min hankali ba,wlh Tallahi budurwar ka tazo gidanan,mahfuz palona kamshin turare yake na daban da nida Kai mun San bamu irin wanan turaren har yanzu bamu yi shekara biyu da Aure ba,mahfuz mai kake nema a wajen wata da bani dashi,wlh tallahi yarinya da ta san Mai takeyi bazata ringa dafa maka abinci ba sabida tasan kana da aure, mahfuz bansan yarinya nan ba amma na mugun tsanarta mahfuz na yarda idan ma auren zaka Kara ka kara ka auri koma wacce Banda tsinanniyar yarinya nan da har dan bana nan zata biyoka har gida duk halin da kake ciki da ita nasani mahfuz magana ce kawai banayi,haka zamu kwanta dakai ka fita ka barni kaje kana waya da ita daddare wane irin kallo kake so tayimin shashasha ko wacce bata da matsayi a wajen mijinta?namiji shi yake fara siyawa matarsa mutunci da daraja a wajen budurwarsa,idan har kana min haka kana tunani ko Allah ya kaddara aurenka da ita bazata balain rainani ta ringa min gori ba,Kai kana tunanin idan ka auro mace irin wanan da bata damu da kana da Mata duk abinda ta ga dama shi zatayi da muyi fada da Kar muyi fada ba abinda ya dameta har kana tunanin zamu zauna lafiya idan ka aurota"."Hmm Ke dai kin d'auko wani banzan halin da bansanki dashi ba ni nace miki Ina neman aure ne,ai ko budurwa ma zan kula kinsan dai ba haramun bane Allah ya hallata Mana mu Kara auren ballantana ni bakiji a bakina nace Miki Zan Kara aure ba,amma tunda kin dorawa kanki balain kishi har dasu zargi ke Kika jiyo kizo muje na maidaki gida"Wani mugun kallo na watsa masa na kwanta akan gadon dan na dawo gida kenan,tunda abinda yakeso kenan na bar gidan


Ganin na share shi yasa ya fice daga d'akin a daidai lokacin da mahaifiyata ta kirani Ina dagawa na bata labarin duk abinda ya faru na kara da "tunda har dan.bana gidan take kawo Masa abinci har gida gwara na dawo gidana mummy Nagaji yarinya Nan so take ta zautar dani"


"Ke dai ba bazaki bi komai a hankali ba Zaki kuwa dorawa kanki hawan jini yanzu ke da kika je kinganta da idonki,a gaskiya kishin naki ya Miki yawa dole ki daura aure  da hawan jini kuwa, nace kiringa bin komai a hankali,idan har namiji ya fara kulle kullen nan, wlh baki Isa ki Hana shi ba ko dafa kanki Zaki ringayi kina bashi Yana ci,wanan haukar kishin da kike sai dai yasa ma kifita a ransa kuyita fada dashi,yaji ya daina ma Jin dadin Zama dake a karshe ma ya fara Shirin auren amma tunda kin k'i bin shawara ta shikenan Anjima zan turo miki zainab ta zauna dake har ki haihun Allah dai ya kyauta"


Daga haka ta kashe wayar 


Mahaifiyata bazata Gane halin da nake ciki ba ni nasan wanan yarinya da ta likewa mahfuz idan har banyi dagaske ba idan ni ban hanata shigowa ba fitar dani zatayi.


Badan babu kyau zubar da abinci ba naso na zubar da abincin a karshe na bawa almajirai narasa Ina Iyayenta suke suka barta take aikin dafawa saurayi lafiyayyen abinci haka,waya sani ma ko zaman kanta take Yar iskar.


Idan ferfesun mahfuz keso nima ya ringa  siyowa yaga idan ban masa ba,duk bakin ciki da takaici ya cikani.


Koda na Shiga gidan mmn Iman masifa ta hau yi tana "da nasan Zaki Kira mijinki wlh Tallahi da ban kiraki ba,Haka kawai kin zubar min da mutuncina yanzu zai ringa mun kallon munafika,ke sam baki iya ba da so kike ki tabbatar ko ki kamashi,ai da baki kirashi a waya ba da muka gama waya dake sai kizo ki ritsa shi gajen hakurinki ya Miki yawa""Hmm mm Iman bazaki gane ba,kisa kaina a matsayin kece na kiraki nace ga budurwa ta shigar Miki gida baban iman na Nan wlh abinda nayi zakiyi"


"Hmmm ai shikenan Allah dai ya kyauta"


"Dan Allah baki ga fitowarta daga gidana ba Naga dai kayan abinci bansameta ba"


"Ya zaayi ma kisameta kiringa da kin kirashi tab a gaisheki ni banga kowa ba dan gida nayi shigowa ta da mijinki ya rufeni da masifa na hada Masa munafirci"

"Na Shiga uku mmn Iman ki kawomin agaji wlh yarinya Nan so take ta kwacemin miji ta k'arfi da yaji"


Shawarwari mmn Iman ta hau bani akan na ringa daurewa Ina danne kishina zuwan zainab kanwata yasa nayi Mata sallama muka koma gida ta dora Mana abincin dare Ina ta tunanin Inda mahfuz yayi.


Mahfuz kuwa Yana barin gidan, gidansu Hadeeza yaje.


Da isar sa ta fito fuskarta a hade


Mahfuz kuwa Sam bai lura da fuskarta ba shigar da tayi ne ya d'auke masa hankali dan indai lafiyayen namiji yaga a yanda yaga Hadeeza dole yaji ya harba


Farar doguwar riga ta sa dayaje mata har kasa kana iya hango duk undies dinta har kalarsu.


Yawu ya hadiye ya daure ya d'auke idonsa daga kirjinta Yana k'ok'arin Magana tace "Mahfuz idan har kasan kana Sona ka tura manya gidan mu ka daina b'ata mun lokaci a gaskiya Nagaji dan bazan zauna na ringa wahalar da kaina akanka alhalin ba Aurena zakayi ba,dan a yau na Kara tabbatar wa da cewar tsoron matarka kake ji bazaka ma iya Kara auren ba Ina kuwa dalili wlh indai dagaske kake.kana sona kazo ka samu babanmu idan Kuma kasan matarka tsoron ta kakeji bazata barka ka Kara aure ba tom sai mu hakura da juna dan a yau ka tsoratani"....... *mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻‍♀

Glow🧖‍♀️


💯 tested nd trusted🤝

GuaranteeSannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 7*


          Wlh idan Kika ce Ina tsoron matata mamaki kike bani,haba Hadeeza karki manta fa gidan ta kikaje Taya zan bari tazo ta Sameki ai sai tayi mana wani fassarar,kamar ace ke yanzu muyi aure bakya nan kizo ki tarar na kawo mace gidan ya zakiji?ai ba batun tsoro bane,sanan zancen na turo  mubi komai a hankali na samu na shirya a tsanake ,tunda kinsan ba yaudararki zanyi ba, idan har gurin manyan naki kikeso naje zanje na same su su san kina da tsayayye Nan da shekara mai zuwa sai a saka mana rana"
"Tabdijam Nan da wani shekarar fa kace wane shiri zakayi haka,haba Mahfuz ka duba maganar nan taka,har sai wata shekara zamuyi aure,a gaskiya yayi nisa ni kaga idan har tunanin kashe kudi zakayi wajen yimin lefe ni na yafe lefen kayimin daga baya,wlh mahaifina kullum sai ya bugowa Abba waya akan na fito da mijin Aure,ni banga dalilin da baza muyi auren ba yanzu,dalili daya kawai zaka cemin zai saka kace min bazaka iya Kara aure ba tsoron matarka  kakeji mahfuz a gaskiya lokaci yayi da zaka daina mata b'oye boye ka fito ka fada mata matsayina a wajenka,ni ka fara so kafin ka sota,ni ka fara sani kafin ka santa banda dai kaddara wlh da bata Isa ta sameka ba"


"Ban da dai san zuciya irin naki Zaki ce koma Mai yafaru ai ke Kika jawo Hadeeza Kinga koma mene bai dace kiringa ganin laifina ba,a lokacin da na so aurenki ai k'i kikayi Kika ringa wulakantani wlh ba dan Ina kaunarki ba kinsan ko saurararki bazanyi ba a lokacin da naso muyi aure k'i kikayi sai yanzu ni Kuma da na riga da nayi auren zaki sakoni a gaba""Kayi min gori mahfuz kayimin gori dan nace kazo muyi Aure"


Hadeeza tace idonta cike da kwalla


"Nifa ba gori nayi miki ba Wai inaso ki daina ganin Kamar k'in fitowa nayi na aureki zan aureki idan Allah ya yarda ki dan bani lokacin yanzu dududu shekara daya da wata takwas Aurena Kinga ya Kamata ace na bari na shekara biyu kafin na koma musu da zancen Karin aure""Hmm"


Kawai Hadeeza tace tana share hawayen daya  zubo Mata


"Haba Sweetyna kiyi hakuri dan Allah nifa bana san haka"


"Yanzu dai yaushe zaka zo ka samu Abban mu yasan da maganar taka,zaka iya turowa fa inya so sai a saka shekara guda Kamar yanda ka bukatan""Ki bari next week zanzo na same shi amma batun turowa ki dan bani lokaci Hadeeza wai ko dai yarinya auren take so hakane"


Yace yana kanne mata Ido daya


Ta sunkuyar da Kai tana "toh laifi ne dan naso auren masoyina"


Murmushi Mahfuz yayi suka cigaba da hira a bai bar gidan ba sai da ya take cikinsa da tuwon shinkafa miyan kuka dayaji nama.


Ba laifi kanin mahaifin  Hadeeza nada rufin asiri Yan boko ne shiyasa basu damu da yanda Hadeeza ke aikin girki ba akwai komai a gidan enough,shi kansa mahfuz din da kwadayin yanda take zuba girki da namomi kaza kifi da sauransu yake, har ya Kai ma ko Lubnar tayi abinci sai yaji Kamar girkin nata bai Kai na Hadeeza dadi ba,bai sani ba ko dan ba kasafai yake Kai naman ayi girki dashi bane, Lubna ce ma ke dan k'ok'arin dafa abinci da Naman.


Wajen karfe goma ya iso gida tun kan ya shiga gidan ya had'e rai dan Yana so ya nuna wa Lubna yaji Haushin zargin da ta masa dazu ya hada Mata da borin kunya,har ga Allah ya kanji Kamar baya kyauta Mata toh ya zaiyi shima zuciyarsa batayi shawara dashi ba ya fara san Hadeeza duka su biyun gani yake bazai iya rayuwa batare dasu ba.


A Palo ya tarar da Lubnar da tsinin ciki ta baje a kasan kafet Zainab kanwarta na dadana mata kafa da ya kumbura,take yaji tausayin ta ya Kuma ji dagaske bai kyauta mata ba ko Yaya dai cikinsa take dauke dashi kulawarsa tafi bukata yanzu.


Gaisuwar zainab din da ta mik'e da sauri ya amsa,ta nufi d'akin bakin


Ya zauna shima a tsakiyar kafet Yana neman kwayar idon lubnar da ta sunkuyar  dakai tunda ya shigo bata daga kanta ta kallesa ba.


"Uwar biyu fushin kike dani kenan"?


Ko kallonsa banyi ba na janye kafata daya fara k'ok'arin d'anna min, ko ganinsa bana san yi dan na riga da nasan wajen dai budurwarsa yaje da ta fini mahimmanci,a yau ma da na dawo gidana sati biyu rabona dashi,ba dokin zuwana yake ba,ba nice a gabansa ba budurwarsa ce a gabansa,wlh a baya ko fita nayi haka zai ta jera min Kira Yana tambayar na dawo,bazai daina kirana ba har sai na dawo gida hankalinsa zai kwanta,ni nake tilasta masa ya fita ma,yayi ta mitar korarsa nake, soyayya muke yiwa juna mai wahalar fassaruwa,mahfuz yaji dani ya soni,sai gashi lokaci guda ya canza min duk wanan soyayyar Yana neman rushewa a gaban idona, tunanin da nayi yasa hawaye zubomin na share hawayen naji saukar hannunsa a kumatuna ya dago fuskata 


"Lubna dan Allah ki daina sawa kanki damuwa wlh tallahi Ina kaunarki kina nan da matsayin ki a zuciyata,ki cire komai a ranki ni mahfuz nakine ke kadai"


"Mahfuz wlh idan har kana kaunata Kamar yanda kace bazaka so bacin raina ba mai na rage ka dashi dan Allah,dududu yaushe mukayi Aure da zaka fara kula wata mahfuz Ina alkawarikan da kayi min,ko shekara biyu mahfuz har yanzu bamu yi da Aure ba har wata ta d'auke maka hankali akaina baka iya bacci  idan baka ji muryarta daddare ba,har abincinta yafi maka nawa dadi, haba Mahfuz a haka kace kana kaunata,sati biyu rabona dakai amma na dawo ko a jikinka ka fice sai yanzu zaka dawo?Mai na maka dana cancanci haka daga wajenka dan Allah"?


Na karashe tare da fashewa da kuka ya jawoni da sauri ya rungumeni tunda na fara magana Naga ya kyab'e fuska da alama maganganu na sun shige shi sai bubuga bayana yake Yana bani hakuri na janye jikina daga nasa Ina"Mahfuz Dan Allah wacce ita?


"Dan Allah kibar zancen nan"


"Dan Allah ka fadamin wacce ita yaushe kuka hadu"?


"Tsohuwar budurwa ta ce lubna mun dade da haduwa da ita,Allah ne yayi bantab'a baki labarinta ba dan har ga Allah a lokacin da na had'u dake na shafe babinta  a rayuwata"


"Mai yasa baka aureta ba Mai ya rabaku"?


"Wai Dan Allah Mai ya kawo tambayoyin Nan lubna"?


"So nake na san matsayinta a wajenka Mahfuz"


"Allah baiyi munyi Aure ba lubna sai a yanzu kaddara ta sake hada mu"


Shiru nayi ina jin wani irin abu ya tokare min makoshi bana jin ma zan iya maganar so nake na auna maganganun sa


"Wlh Lubna ita ta dawo rayuwata ta nace min na rasa yanda Zan yakice ta"


"Kana santa Mahfuz ni ba mahaukaciya bace wlh nacewa juna kukayi,ba itace ta nace maka ba,yanzu aurenta zakayi kenan"?


Na zuba masa Ido gabana na faduwa


"Lubna mu bar zancen nan kema ko yanzu aka ce miki zanyi Aure ai zaki karyata kin isheni rayuwa"


"Na isheka rayuwa kake kula wata yaudarar ta kake ko watsewa kuke idan har ba aurenta zakayi ba Mai amfanin kulata ka b'ata mata lokaci mahfuz"?


Lubna dan Allah ki bar zancen nan haba kiji da cikin Nan dake jikinki muyi addua Allah ya saukeki lafiya haba Ina ta kwantar Miki da hankali kin kara dagawa kanki hankali"


Yace a d'an tsawace tare da mik'ewa tsaye


"Ga abincin ka nan ko kaje wajenta kaci"?


"Lubna dan Allah kidaina min maganar wata idan har kina san mu daidaita dake wai wane irin dabia Kika samo haka mara kyau ni nace miki naci abinci"


'toh zauna kaci abincin"


Tsaki yayi ya zauna duk da a koshe yake ya bude flasks din ganin faten doya ne yasa ya zuba kad'an ya fara ci yanda ya had'e rai yasa ban sake magana ba har ya gama cin abincin ya kwashe komai ya Kai kitchen.


Ya dawo ya taimaka min na Mik'e muka Shige d'akin mu.


Koda ba kallonsa nake ba idona na kansa Yana fitowa daga wanka ya kashe wayarsa ya jefa a side drawer ya Kwanta.


Nima nayi Shirin kwanciya da maganganu a bakina amma akan dole na hakura na kwanta a gefensa.


Ya mirgino kusa dani,muka faranta wa juna bana iya kwanciya ba tare da nayi wanka ba a dadafe nayi wanka sabida baccin daya cika idona Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani.


A zababben ciwon Mara ne ya tasheni daga baccin daya daukeni


Damko mahfuz nayi Ina sallati

Dan ciwon maran haihu daban yake kamar yanda ake bamu labari nasan haihuwa zanyi


A gigice ya mik'e Yana tambaya ta lafiya


Dak'yar na hada Masa kalmar haihuwa zanyi.


Wani irin dirowa yyi daga Kan gado ya kunna fitilar d'akin ya kalli agogo karfe uku da minti ashirin"Bari na leka gidan Hamisu ya taimaka min da aron motarsa Ina kayan naki yake"


"Mummy ta riga da hade min shi waje daya kayiwa Zainab magana na karashe Ina Kara sallati dan ciwon gadan gadan ba kaukautawa ga wani abu Mai dumi danaji Yana bin kafata.


Mahfuz shi ya taimaka min na saka Riga da zani hannunsa sakale a kuguna kamar Mai koyan tafiya mukayi wajen da Hamisu mijin mmn iman ke jiranmu dan cewa yayi shi zai kaimu daga shi har matarsa suna da balain kirki sun san Kuma darajar makota.


Bansan sanda ma aka iso asibiti ba ban iya tafiya ba sai gado suka kawo da taimakon mahfuz suka dorani sukayi d'akin haihuwa dani zainab na biye dani Mahfuz sai sannu yake min hankalinsa duk a tashe.


Da shigar mu d'akin da haihuwata baifi minti ashirin ba.


Duk Wanda bai haihu ba ba lailai yasan darajar mahaifiyarsa ba Allah ya saka wa iyayenmu da Aljannatul firdausi banyi doguwar nakuda ba amma naci ubana bayana Kamar baa jikina yake ba.


Sai da suka gyarani Suka gyara yarinya da ta d'auko kamani na ba Inda ta baroni amma bata kaini haske ba da alama hasken babanta ta d'auko ido kawai na zuba Mata Ina Jin kaunarta har a cikin raina.

Muryar mahfuz danaji akaina yasa na d'auke idona daga kanta 


"Sannu Lubna sannu da k'ok'ari wanan diyar tawa ta baki wahala"


Yace tare da daukarta yana murmushi.


Nima murmushin na sakar masa.


Bakinsa ya kafa a kunnenta Ina kallonsa ya gama ya kwantar da ita a gefena Yana "Sunanki na saka mata Allah ya Raya mana ita sai ki zab'a mata sunan da zamu ringa kiranta dashi"


Har ga Allah naji dadi a raina ban manta da Addu'a mai nakuda karbabiya ce hakane yasa na zage nayi addua Allah ya raba mahfuz da tsinaniyar budurwar sa dana tsana tamkar mutuwata.Karfe bakwai na safe aka sallamo mu.


Da taimakon kanwar mahaifiyata nayi wanka tayi wa mimi wanka sunan da za'a ringa kiranta dashi,baccin gajiya yayi awon gaba dani duk da ana ta tururwa shigowa yimin barka.


Kukan da Mimi keyi yasa na bud'e idona babu ma ruwan nono haka Aunty Sa'a tace na bata no-no tana fita sai ga mahfuz ya shigo sai da ya gama tsokanata yake tambayar Koda wani abu da muke bukata,


Girgiza masa Kai nayi dan bana Jin akwai abunda muke bukatan dan yayi Mana siyayya daidai karfinsa nama Mai yawa ya siyo aka saka min a fridge.


Bakin da ake tayi yasa ya mik'e dan mahaifiyarsa ma tazo "Nidai bari na fita waje idan ana bukatar wani abu ki kirani na manta ma Abdul yace na gaisheki zai shigo Nan da jibi"


Murmushi na saki dan muna shiri da abokinsa Abdul sosai Yana da matukar kirki Yana Kuma sona da Mahfuz aikine ya mayar dashi garin inyamurai.


Har yaje bakin k'ofa nace "kaci abinci kuwa"?


Gyada min kai yayi Yana "Na Sha kunu ama koshe nake ke kuwa na zama uba wa yake ta wani abinci.


Murmushi na sakar Masa ya fice daga d'akin budurwar sa da ta fadomin yasa naji farinciki da nake ciki Yana neman gushewa,tun jiya dai banga alamar waya a hannunsa ba Addu'a nake Allah yasa maganganun da mukayi dashi jiya yasa ya canza alhamdulillah na haihu lafiya yanzu zan daura damarar kwato mijina na dawo da hankalinsa kaina da izinin Allah


Mahfuz


Yana fitowa daga d'akin ya Shiga daya d'akin da yawancin Yan barkan anan Suka zauna wasu Kuma a Palo,ba laifi lubna Yar dangi ce shima haka,


Wajen Mahaifiyarsa Hajiya Ammi yayi dan so yake yace Mata fita zaiyi.


Sai dai Yana gaya mata ta mik'e tana itama tafiyar zatayi ya sauketa a gida.


Tare Suka fito daga gidan Bayan ta Kara yiwa Lubna barka.


Har gida yaje ya sauketa baiyi niyyar shiga gidan ba tace ya shigo magana zasuyi.


Yasan halin mahaifiyarsa da mita da kin d'auke Ido akan Abu duk kankantarsa duk tunani yake kila wani abun tagani a gidan nasa.


Sai dai Yana zama tace 


"Dazu nan wata yar albarka tazo har gidanan ta gaisheni tace min ita budurwa ka ce yama take da suna yauwa Hadeeza yarinya tana kyau da hankali ga tarbiya wlh kaga ma abin arzikin da ta kawomin da ta tashi tafiya har dasu kyautar kudi da dukan alamu Yar baban gida ce"?


Tace tana zaro turmin zani daga ledarsa har da mayafi da turare


Tsananin mamaki ya hana mahfuz magana


"Ammi Hadeeza ce tazo har gidanan"?


"Eee fa wlh har gidanan tazo yarinya ta matukar burgeni a gaskiya Ina kaunarta kaga tsalallen atamfar da ta kawomin har da mayafinsa kaga na samu na sawa ma ranar suna"Tace tana washe baki


Mahfuz kasa magana yayi dan har lokacin mamakin yanda Hadeeza tasan gidansu yake.har gidansa ma ta sani,haka kawai yaji baiji dadin zuwanta gidan su har tazo wajen Mahaifiyarsa ba wani zubin Yana ganin rawar kanta ba kad'an ba 


"Baka ce komai ba ka tsaya kana wani zare Ido ko bakaji dadin kyautar da ta kawomin bane ta girmamani a matsayina na mahaifiyarka yau naga yaro da yiwa uwarsa bakin ciki"


"Wlh ba Haka bane Ammi ni mamakin yanda tasan gidanan nake""Mai wani abun mamaki yarinya Yar arziki a Ina kuka hadu da ita ne"?


"Ammi tsohuwar budurwa ta ce fa ita na fara nema kafin lubna Allah baiyi ita zan aura ba na auri lubna sai kuma yanzu ta dawo rayuwata,k'arfi da yaji so take muyi aure Bayan ban dade da auren ba,har ga Allah banida niyyar Kara aure yanzu amma ta dage min"


"Aikuwa gwara ka daura damaran auren dan nikam tayi min haka nake san mutum mai mutunci da sanin ya Kamata,matarka tunda ka aureta sau daya ta taba bani turmin zani wanan kuwa bama ka aureta ba ta gwangwaje ni da irin zanin nan har dasu mayafi ga kudi Kuma habawa ai ka shirya Kara Aure insha Allahu"


Yasan halin mahaifiyarsa Sarai wajen san abun duniya yasan kila ma ta zubar Masa da mutunci a wajen Hadeeza Sam baiji dadin zuwan da tayi gidansu ba."Kayi mata godiya idan kaje"


"Zan mata insha Allahu bari naje"


Yace tare da mik'ewa yayi waje Yana k'ok'arin tayar da machine dinsa kiranta ya shigo wayarsa tun da ya baro gidansu jiya basuyi waya da ita ba dan wayarsa a kashe take bai ma kunna ba sai dazu da text dinta ya shigo bai Kirata ba dan so yake yaje inyaso ya fada mata haihuwar Lubnar daga wayar yayi Yana "Gani Nan zuwa yanzu"Ya katse wayar......


Kunsan yawancin novel dina true life ne na baya na canza na Kara daga wanan shafin zuwa na gama ya faru a gaskeKAYAN MATA


Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?


Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?


Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?


Shin minene matsalar?

Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?


Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,


Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,


Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 🥰 kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,


Munada tsumi nau'i nau'i

Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu

Akway ruwan jaraba

Ruwan Dadi

Hadin minannas

Hadin dafa kaza(manta uwa)

Hadin yar gaban goshi,

Turarukan mallaka.


Duk a farashi mesauqi.


Serious buyers call, WhatsApp 07046881166


Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagodeSannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 8*


Koda isarsa a karamin palon gidan da suke zance yayi zamansa Yana jiranta,tun kafin ta iso palon ya fara jiyo kamshin turaren ta, Hadeeza ba baya ba wajen saka turare a ransa Yana so ya nuna mata rashin Jin dadinsa da zuwa gidansu da tayi baya san garajen nan da takeyi yafisan su bi komai a hankali yasan Yana santa amma har ga Allah da san zuciyarsa ne babu bukatar wani Karin Aure,Sam baiji dadin yanda lubna duk ta dago halin da yake ciki da Hadeeza ba tun a jiyan ya daura damarar canzawa wajen iya takunsa sam bayaso ta ringa Jin kamar ya daina santa,yasan tana iya k'ok'arin ta wajen faranta Masa


Sallamar da Hadeeza tayi cikin takunta najan hankali ya katse masa tunanin da yake ya dago idonsa Yana kallonta har ta samu waje ta zauna ta sakar Masa murmushi,dayasa ta kashe Masa jiki kwana biyun nan tana shigar dake dan bayyana surarta.


"Sai yanzu ka tuna dani,jiya ko bacci banyi ba dan banji muryarka ba""Lubna ta haihu fa an samu bby girl shiyasa Sam jiya ban bi ta Kan waya ba"Sai da ta dau tsawon lokaci kafin ta daure ta saki murmushi dan Addu'a tayi a ranta dama mutuwa lubnar tayi da tazo haihuwar


"Masha Allah Allah ya Raya mana ita kace na samu takwara""Sunan lubna na saka Mata zaa ringa kiranta Mimi ashe kinje gidanmu dazu"?


Kamar ya watsa Mata ruwan zafi dayace sunan lubna ya sawa yarsa dan taji labarin idan har miji yasa wa yarsa sunan matarsa ba karamin kaunarta yake ba,bata so ta nuna Masa rashin Jin dadinta yak'e tayi tana "Eee dazu naje na gaida mama tunda baka tab'a cewa muje na gaisheta ba"


"Dama kinsan gidanmu ne"?"Tunda har nasan gidanka sanin gidanku bazai min wahala ba Mama nada kirki wlh tayi min tarb'a Mai kyau da dukan alamu na samu karbuwa a wajenta ba nida wani fargaba""Hmmm ai da kinn fada  min zakije kila akwai shirin da zanyi kafin kije din amma tunda kin riga da kinje shikenan tace na miki godiya"


"Ba wani damuwa ai nima mahaifiyata ce"


"Hadeeza"


"Naam"


"Magana nakeso muyi mai mahimmanci Ina fatan Kuma Zaki fahimceni"


Gaban Hadeeza yanke wa yayi ya fadi duk tunani take mahfuz cewa zaiyi tayi hakuri bazai iya aurenta ba bata iya cewa komai ba ta zuba Masa Ido


"Kinsan dai Ina sanki Ina Kuma kaunarki,fatana Allah ya mallaka min ke Babu yaudara a tsakanina dake,da ace bana kaunarki bana Jin zan tsaya na ringa b'ata Miki lokaci ina b'atawa kaina,saura wata hud'u na samu shekara biyu da aurena,kafin ki dawo rayuwata wlh banida wani plan din auren Mata biyu a nawa tsarin mace daya ta isheni rayuwa sai dai idan Yana cikin kaddara ta sai na Kara Aure,Hadeeza Kamar yanda Kika sani a baya ni ba wani shahararren Mai kudi bane da na tada kai,rufin asiri gareni rayuwa ta a saukake nake yinta,kina kallo ko mota har yanzu bani dashi,dama burina bai wuce idan lubna ta haihu na fara tunanin yanda Zan samu motar ba,banida wani gida daya wuce Wanda Lubna ke ciki sai wani fili da na siya nida wani abokina Abdul komai a rayuwa sai kana tsarawa yanda bazaka yi abinda zai takura ka a yanzu nauyi ya Kara hawa kaina.tunda na fara tara  iyali,Hadeeza abinda yasa nake Miki wanan maganar naga kin matsu kina so ko  a yayane na turo muyi aure, inaso kisan komai sai da plan bana so muyi gaggawa ko garaje,inaso mubi komai a hankali a yanzu da Allah ya kaddara Zan aureki Zan fara shirye shiryen yanda Zan zauna da Mata biyu,dan haka zanzo na samu Abban naku yasan da maganar auren a bani lokaci na samu mu tsara komai,na biyu ba zancen Ina tsoron matata bane ko wani abu,inaso mu canza taku yanda ba zaa ringa saurin dago mu ba,wayar daren nan da mukeyi inaso mu hakura da wanan wayar,

Idan na fito daga gida Zan Kira ki da kaina.


kema kinsan Ina samun sarari Ina baki lokaci sosai a wajen chatting wanan shine maganar kawai dafatan Kuma zaki fahimceni"


Ba karamin dauriya tayi ba wajen danne zuciyarta   cikin yak'e tace "Na fahimceka wlh ba wani damuwa zan daina kiranka idan kana gidan kamar yanda ka bukata amma inaso kasan cewa wlh ba sharri a zuciyata bansani ba ko matarka wani abu tace maka kazo kake min maganganun nan"


"Aaa wlh ba abinda tace min kawia naga ya dace yanda nake baki lokaci itama na ringa bata lokacinta Kinga bai dace na ringa shiga hakkinta ba ko""Eee hakane kuma"


Tace cikin yak'e tana "yaushe zanzo barka ne kaga ya Kamata naje naga 'yata"


"Kai aaa Zan kawo Miki ita idan ta fara wayo"


"Kasan kuwa next week su Abba zasu tafi umara wlh dukansu har da yaran ni Kuma wai na koma gida idan sun dawo sai na  dawo"


"Allah sarki kice zanyi missing dinki"


"Tab ai ba Inda zani bazan iya kwana biyu banganka ba  wlh"Dariya mahfuz yasa Yana "toh ya zaayi kenan"?


"A jaka zan saka ka mu tafi can"Hira kawai suke mahfuz Sam baima San lokaci ya ja ba sai da aka fara Kiran sallah magriba yaso daga massallaci ya wuce gida Hadeeza ta hana shi har sai daya ci abincin dare a gidan.A lokacin daya isa gida har Lubna tayi bacci.


Zainab da Aunty Sa'a kanwar mahaifiyar lubna kuwa Suna daya d'akin Yana jiyo hirarsu.


Wanka kawai yayi yazo ya kwanta ganin Lubna na bacci yasa ya kunna data Suka hau chatting da Hadeeza da ta ajiye masa message rututu na irin kaunar da take Masa ta hada da ya turo mata hotunan baby.


Sai da ya fara Jin bacci yayi Mata sallama ya kashe wayarsa.LUBNA


Ba laifi naga canji daga wajen mahfuz tunda na haihu,ban sake ganin yayi wayar dare ba,idan ya dawo gida baya sake fita har a raina naji dadi Inda na ringa addua Allah yasa ya dore a haka Allah yasa ya rabu da wanan tsinaniyar budurwar tasa,har bincike nayi a wayarsa na shiga message dinsa da watsapp banga alamar lambarta ba a wayanda yake Hira dasu yafi hira da Abdul na Kuma ji dadi sosai.


Ba laifi ya min dinki masu dan kyau da tsada daidai karfinsa duk da mummy ta riga da tamin dinkin fitar suna haka ma ta kusa cikowa mimi akwati da kaya.


Hankalina kwance muka Sha Suna a ranar sunar ba inda Mahfuz yaje Yana nanike dani,Muna ta hotuna.


Ko kunyar mutane bayaji da suka cika gidan,har anko mukayi dashi na wani blue shadda munyi kyau sosai Koda ba'a fada ba.


Zuwan mahaifiyarsa Hajiya Ammi da ta had'e rai tana dan harararsa yasa ya bar wajena yayi waje.


Koda na gaisheta Mimi kawai ta karba daga hannuna ta amsa gaisuwar ciki ciki nakan yi mamakin yanda take min,Banda matan yayyen mahfuz nace min haka halinta yake da nace sona ne batayi.Yan uwana sai da suka tayani kintsa koina Kamar ba'ayi taro  a gidan ba kafin suka tafi Aunty Sa'a Dai sai ta Kara kwana biyu kafin ta tafi.


Mahfuz


Yaji dadin hadin Kan da Hadeeza ta bashi wajen daina damunsa a waya suna gama chatting yake gogewa gudun kar Lubna ta masa bincike a waya ta gani yafiso ta dauka sun rabu da Hadeeza Sam bayasan ta ringa zarginsa tana dagawa kanta hankali.Ranar suna da Mai kwalliya tazo ta rangada wa Lubnarsa kwalliya ba karamin kyau ta masa ba hakane yasa yayi ta zuba musu hotuna a wayarsa da mimi.


Hotunan dayafi kyau ya zab'a ya Dora akan status da rubutun "Allah ya Raya mana Mimi ya baki lafiyar shayarwa Rabin Raina


Ko minti biyar baiyi da sawa ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.


Bai kawo komai ba ya daga wayar 


Kukanta ne ya karade wayar 


Sam baisan Mai yasa ta kuka.ba hakane yasa a rude ya hau tambayarta lafiya mai ya faru bata ce masa komai ba ta cigaba da rusa kuka.


Katse wayar yayi ya haye machine dinsa yayi gidansu dan bata tab'a kiransa tana rusa uban kuka haka ba.


A lokacin daya iso gidansu sai daya dade Yana jiranta kafin ta fito idonta ya kada yayi jajjur.


Mik'ewa yayi da sauri dan ya d'auka ko wani ne ya mutu da sallati yace "Lafiya kuwa Hadeeza Mai faru


A wajen kafarsa ta zauna ta Kara fashewa da kukan


Ya zauna da sauri.yana "Hadeeza wai Mai yake faruwane"


Dagowa tayi kafin ya ankara ta jawo hannunsa ta manna a kirjinta "kaji zuciyata Mahfuz kaji yanda yake bugawa,Ina da kishi mahfuz hotunan nan daka dora ya daga min hankali mahfuz anya kana Sona kuwa"?

Tunda muke da Kai baka tab'a dora hotona ba""Wai wane hotone ya daga Miki hankali hoton nida Lubna ko me"?


"Gyada Masa Kai tayi har lokacin Tana kankame da hannunsa ba hotunan da sukayi tare da mahfuz ne ya daga Mata hankali ba bata kawo Lubnar ta kai haka kyau da haduwa ba,bata ga abinda zata Gaya wa Lubnar ba,sai taga ma kamar ta girmi Lubnar Sam ta kasa danne kishinta har sai data Kira mahfuz din,gani take mahfuz na iya kubce Mata kowane lokaci,tundaga lokacin daya kafa mata sharadin kiransa a waya,ta tsorata dashi,dan taga dagaske Lubna nada wani irin matsayi a wajensa abu.kadan na iya sawa mahfuz yace ya fasa aurenta.


Tsananin mamakin Hadeeza yasa ya saki baki Yana kallonta kallon Anya ma tana da hankali kuwa hoton lubna ne bataso ya dora ko me


"Yanzu ke kishin lubna kikeyi har dasu kukan ki yanzu laifi ne dan nayi hoto da matata matata ce fa ba wata ba"?


"Mahfuz bazaka gane ba nidai dan Allah kayimin alkawari bazaka rabu dani ba duk runtsi duk wuya"


"Wai duk hoton namune ya rudaki haka,lailai kinma fi lubna kishi to bakya so muyi hoton ne ko me"


"Ni ba haka nake nufi ba"


"Toh Mai kike nufi"


"Nidai kayimin alkawari bazaka rabu dani ba"


Girgiza Kai mahfuz yayi Ya hau dariya dan dariyar ma ta bashi biye mata yayi yace yayi alkawari kafin ta yarda ta cika Masa hannu tace Masa tana zuwa.


Bayan minti goma sai gata ta dawo cikin kwalliya ta Sha shadda pink mai duhu  ta kashe dauri,


Da ido yake binta har ta zauna a gefensa kafadarta na guga  nashi ga kamshin turarenta nan ya bade ko'ina.


Bai san mai  take nufi ba sai da ta d'auki wayar ta tana "nima hotunan zamuyi naji dadi dama bamu tab'a hoto ba tace tare da daga wayar murmushi kawai yayi ta hau yi musu hotuna har tana dadafa shi kamar irin couples dinan da basu Dade da Aure ba.


Shi dai biye mata yayi sukayi tayi har da su videos sai daya gaji ya kwace wayar daga hannunta yana ya isa haka.


Jera hotunan ta hau yi status sai duk yaji hankalinsa bai kwanta da dorawa da tayi ba duk da yasan Lubna ba saninta tayi ba yanzu idan ya ce ta cire sai ta masa wani fassarar.


Yanda take wani nanarke Masa tana neman daga Masa hankali a banza yasa ya mik'e yace Mata zai tafi.


Sai da ta raka shi har waje ta Kara komawa ciki ta d'auko leda mai dan girma ta bashi tana ya kaiwa yarta.


Yakan yi.mamakin Inda take yawan samun kudin da take kashewa haka,duk da yasan shima Yana tura Mata kudi Dan Yana da acct number dinta sai dai kudin daya ke tura Mata bai Kai yawan hidimar da take dashi ba har dinkin shadda ta Masa da agogo da turare mai tsada lubna duk ta d'auka shi ya siyo da kudinsa.


Godiya yayi Mata bayan ya roketa da daina dorawa kanta wahala haka.


Koda ya isa gida a zaune ya tarar da Lubna tana shayar da Mimi yanda ta zubo Masa Ido yasa yaji duk ya tsargu sai yake ganin kamar zata gane  wajen Hadeeza yaje.


"Ina ta gwada wayarka tundazu Ina ka shiga ne"?


Nace Ina Kare Masa kallo nidai duk da ban Kara Kama shi Yana waya ba idan har ya dan Dade a waje sai naji kamar zance yaje."Ina can gida mun hadu da Yaya Mustapha"


Ya mik'o min ledar hannunsa "ga Kaya nan  inji wani abokina"


Karba nayi na bud'e na fara fito da kayan ciki,kayane masu kyau da tsada wajen kala biyar sun balain yimin kyau


"Wane abokin naka ne ya Mana abin arziki haka"?


"Baki San shi ba a wajen aikinmu yake"


"Aikuwa ya kyauta sosai kayi Mana godiya"


Kai kawai ya gyada min ya hau Wasa da mimi.


A yanzu dai Zan iya cewa banida wani matsala Ina samun kulawa sosai a wajen mahfuz, tuni hankalina ya fara kwanciya dan da alama yanzu baya tare da yarinya data so saka min hawan jini sau tari na Sha Masa bincike ban ga alamar bakon lambar da bansani ba.


A yau da nasamu sati biyu da haihuwa baifi saura kwana shidda ayi babbar sallah ba bayan fitar mahfuz wajen aiki ya kirani a waya akan Abdul Yana hanya zai zo ya shigo garin na tanade shi.


Nasan yanda Abdul yake a wajen Mahfuz aminan juna ne Yana da balain kirki Nima Ina matukar ganin mutuncinsa,baya Wasa da duk wani abu daya shafi Mahfuz duk da baya garin na haihu sai da ya hada kayan barka ya aiko Mana dashi.


Kitchen na Shiga da kaina na fara k'ok'arin dafa fried rice a cikin awa daya na kamalla komai na gyara gidan zainab bata Nan taje gida ta dawo.


Wajen karfe biyu naji sallamarsa tare da bugun k'ofar gidan.Hijabina na saka har kasa,naje na bud'e k'ofar fuskata d'auke da murmushi.


Tsokanata ya fara yi Yana "Uwargida sarautar mata"


"Dagani ba kari insha Allahu na karashe Ina "toh ashe da amaryarka kake tafe aa lalle marhaban shigo shigo.


Nace Ina  bawa macen dake biye dashi a baya fuskata washe ita kuwa sai wani sunkuyar da Kai take hannunta janye da dan madaidaicin trolley.


Suna Zama na dauko musu ruwa da lemo Ina satar kallon budurwar Abdul din bana iya ganin komai na jikinta dan hijabi tasa har kasa fuskarta ce kawai a waje kyakyawa ce ba laifi.


Mimi kuwa na hannun Abdul Yana ta mata Wasa "wato ka gaji da gorin auren da muke ma kenan"


Nace ina tsokanar Abdul daya gyarawa Mimi Zama a jikinsa Yana "Tukunna dai wlh har yanzu ban samu wacce ta kwanta min ba wanan ai 'yar babar yayar mu ce da suke zaune a Lagos inaga mahfuz ya tab'a baki labarinta lokacin dayaje can Lagos din ko"?"Kwarai kuwa ya tab'a bani labarin yayarka ta Lagos"


"Toh wanan yarta ce ta fari.


Ta shigo garin nan ne zatayi wani training na kwana goma,shine nace bari na kawota nan ta zauna idan ba damuwa"


"Haba haba ba wani damuwa wlh ai an Zama daya fatana dai ta saki jikinta Nan ma gidane ai"


Muka hada ido da ita ta sakar min murmushi tare da sake sunkuyar da Kai,nikam yanayin ta ya burgeni da alama tana da nutsuwa da kamun Kai.


Sai da suka ci abinci na Kai mata akwatin ta daya dakin.


Muka dan tab'a hira da Abdul kafin yamin sallama.akan goben nan zai koma ya ajiye min kudi Mai yawa na hau yi mishi godiya har bakin k'ofa muka raka shi nida ummi bakuwar da mukayi sabida tsiya irin na Abdul Ashe bai fadawa mahfuz zai kawota ba Wai Idan ya dawo na fada Masa.....Wanan novel din na kudine a page 10 zamu gama free pages biya 500 dan ki samu kicigaba da karatunki cikin sallama tura 500 ta 2029764071 first bank  nafisa Nuhu ko ta wanan 0000551222 Taj bank nafisa Nuhu turo da shaidar ta wanan lambar 08033719070 ko katin mtn ta wanan layin 08033719070 karku bari a barku abaya. KAYAN MATA


Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?


Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?


Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?


Shin minene matsalar?

Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?


Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,


Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,


Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 🥰 kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,


Munada tsumi nau'i nau'i

Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu

Akway ruwan jaraba

Ruwan Dadi

Hadin minannas

Hadin dafa kaza(manta uwa)

Hadin yar gaban goshi,

Turarukan mallaka.


Duk a farashi mesauqi.


Serious buyers call, WhatsApp 07046881166


Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagode

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*PAGE 9*Koda muka koma ciki,a kasan kafet ta zauna ta miko min hannu tana na bata mimi.


Mik'a mata Mimi nayi Ina "Mai Kika zauna a kasa ki koma ki zauna mana akan kujerar"


"Nan ma yyi Aunty ngd"


"Kai Kai sunana Lubna  ba Aunty ba"


Murmushi kawai tayi ta cigaba da Wasa da mimi tana ta zuba mata kiss a fuska ni.kuwa take ta sake burgeni ni nasan Zainab gajiya tayi ta gudu toh tayi a banza tunda na samu Yar tayin hira.


Hira na fara janta dashi Ina dan jefa Mata tambayoyi duk dan ta saki jikinta,anan take fadamin ta kamalla degree dinta tana neman aiki, shine kafin su dauketa suka turota nan ta danyi wani programme a shiyarsu ta nan.


Ina da saurin sabo da mutum kamar na dade da saninta haka na hau janta da hira bamu tashi ba sai da aka Kira sallahr laasar.


Na nuna Mata d'akin bakin akan ta Shiga ciki tayi sallarta.


Nima na shige d'akina dan na canzawa Mimi Pampers dan bansamu tsarki ba tukunna Ina cikin sawa Mimi Pampers Kiran Mahfuz ya shigo wayata Ina dagawa yace "Ashe har Abdul ya tafi yanzu nan ya kirani Kuma kinsan dan wulakanci bai biyo ta office dina ba wlh sai na Masa rashin mutunci"


Murmushi na saki Ina "kunfi kusa kaima kasan bazai tafi batare da ya ganka ba kila anjima kaga ya dawo,tare yazo da wata bakuwa Wai zata yi wani program Yar yayarsa ta Lagos bansan bai fada ma ba sai daya zo tafiya Wai Idan ka dawo na fada maka"


"Wlh Abdul ya Raina ni yanzu nida gidana zai kawo min wata bai nemi izini a wajena ba"


"Kai Kam da rigima kake wlh yanzu dan Yar yayarsa zata zo tayi kwana biyu a gidanan shine sai ya nemi izininka"?Tsaki yayi Yana "Zan Masa rashin mutunci ai sai mun hadu dashi tukunna"


Murmushi na sake yi nace "ba ruwana Ina daga gefe"


"Ina Mimi"?


Gata nan yanzu nan na canza Mata Pampers goyata zanyi na Shiga kitchen


Hira Muka dan Kara tabawa kad'an kafin ya kashe wayar na goya mimi na fito nayi kitchen banga ummi a palon ba nasan tana cikin d'akin kila hutawa take tunda Lagos ba nan ba duk da banga alamar gajiya a tare da ita ba kila jirgi suka hau dan su Abdul din nada rufin asiri.


Ina cikin kitchen din na jiyo muryar Mmn iman tana kwankwasa k'ofa.


Ajiye muciyar hannuna nayi naje na bud'e Mata k'ofar ta shigo da ledoji a hannunta ko bata fadamin ba nasan na menene kayan gyara ta kawo min dana bata sautinsa dan so nake na tsantsame kafin na samu tsarki.


"Ke Kaya masu zafi ta kawo wlh sai kinyo ciko"


Gefenta na zauna na fara duba kayan a daidai lokacin da ummi ta fito daga d'akin motsinta yasa muka dago muna kallonta nace "kinfito kenan da zan shigo nace ban sani ba ko baccin gajiya kike"


Murmushi tayi a daidai lokacin da ta karaso wajenmu ta zauna a kasan kafet tana "Aa idona biyu ai ba wani gajiya da nayi tunda jirgi muka biyo Ina wuni"


Ta gaida mmn iman ta amsa cikin sakin fuska tana "kice bakuwa kikayi"?


"Eee wlh tun daga Lagos tazo"


Na bawa mmn Iman amsa na cigaba da duba jarkokin tsumin data shigo dasu  da dan bokitin da aka dafa min ciccibi a ciki.


Kice Abban Mimi zai Sha Dadi na kashewa mmn Iman Ido data dafe baki tana "lah bakida kunya fa agaban bakuwar kike badala ko dai matar aure ce"?


Sunkuyar da kai tayi da muka hada ido da ita dan ni banma San kallona take ba


Murmushi nayi Ina "ba matar Aure bace wlh Mai dan nayi wanan hirar a gabanta ai Yan matan suma yanzu sun San komai"Na karashe Ina dariya a daidai lokacin da nake dandana wani zuma Nan ma na sake hada Ido da ita ta sunkuyar da Kai da sauri


Mmn Iman tace "nidai mallama ki bani cikon kudin dana ranta Miki"


"Har nawa Kika ranta min"?


"Dubu bakwai na cika Miki wlh"


"Kai dubu ashirin na baki fa"


"Kwarai kuwa ai kayanta masu kyau ne da tsada wlh tamkar budurwa Zaki koma duk Inda Kika saka kafarki bbn mimi na biye dake"


Washe baki nayi Ina "Zan  baki kudinki idan na Kai shi duniyar can kila na baki fiye da Dubu bakwai din"Tafawa muka yi da ita ta mik'e tana "naji ma kamar abincin da kika Dora na kauri bari naje Nima na dora nawa girkin na biye miki ba abinda zan zanyi.


Tayi hanyar waje nayi mata godiya tare da kwashe kayan da dan bokitin cicicibin nayi hanyar kitchen dan a kitchen nake ajiyar irin kayan nan sabida wani zubin mahfuz akwai dube dube,Ina zuwa bakin k'ofa naji muryar ummi tana "Aunty ba abinda zan kama miki a kitchen din"?


"Lah tuwone kawai zanyi ba abu Mai yawa ba inada Miya dama ngd ki saki jikinki dan Allah Nan ma gidane ki kunna tv kiyi kallo"


Ina daga kitchen din nake Mata maganar na fara k'ok'arin tuka tuwon.


Muryarta da naji a bakin k'ofa yasa  na juya


"Bari na Kama miki wani Abu aunty ki kawo na tuka miki"


"Kai haba wlh ki barshi"


Dak'yar.na samu ta koma Palon na tuke tuwon na kwashe.


Na Kara gyara ciccibin da aka kawomin na dumama na juyo a plate na dauki tsumi daya da na zuba a fridge din kitchen na nufi palon.Tana zaune wanan Karin a saman kujera tana latsa wayarta har yanzu da hijabinta a jikinta har kasa.


"Wai bakya Jin zafine ki cire hijabin naki ki Sha iska Mana dagani sai ke a gidan fa kin k'i sakin jikinki"


Murmushi tayi bata ce komai ba na kwantar da mimi akan kujera na  zauna a kasan kafet na mik'ar da kafafuna sabida naji dadin cin  cicibin.


Ban taba ci ba na dauka dadi ne dashi ai Ina kaiwa bakina naji daci daci na kwabe fuska Muka hada Ido da ita dama tunda zu Ina Jin idonta a kaina


Dak'yar na hadiye Ina "Kai kinji daci kuwa da kina da Aure da kinci kinji"


Murmushi ta sake yi wani zubin Ina da surutu na hau zuba "Kinsan mace sai da gyara idan baka dage kayi gyaran nan ba sai namiji ya fara k'ok'arin hango ta waje kuma idan mace ta haihu Salam take komawa dole sai ta zuba gyara sosai zata koma yanda take sai kinyi Aure zaki gane haka,Amma dai kin kusa shiga daga ciki ko"?


"Eee"


Washe baki nayi Ina "Masha Allah ansa Rana.kenan kice Muna da zuwa Lagos Shan biki dama ban taba zuwa ba Kinga ta silarki sai naje"


"Insha Allahu"


"Saura wata nawa"?


"Saura wata uku"


Masha Allah Allah ya nuna mana shima acan Lagos din yake"?


"Eee acan yake"


"Saurayine ko Mai Mata,kiyi hakuri Kinga Ina ta zuba miki tambayoyi"


"Lah ba komai wlh Mai Mata ne"


"Kash amma banji Miki Dadi ba auren mijin wata ai bashida wani dadi,ki more aure shine ki samu santalellen saurayi ki aura ku Sha soyayyar ku,kai amma na tausayawa wacce zakije ki tarar nasan tana nan zuciyarta kamar tayi bindiga kishiya ba dadi sam Allahu ya tsare mu da ita ya nisanci mazajen mu da tsinannun Yan matan Nan dake makale wa mazajen mutane,kiyi hakuri fa karki ce da ke nake wlh nima Ina da wata shegiya da ta makalewa mijina sai da nayi da gaske suka rabu matar saurayinki Allah ya bata hakuri da juriya kema dan Allah karki cutar da ita"


"Aunty ai har yan matan baa san ransu suke auren mai Mata ba sai dan kawai ya tsago a kaddararsu nima saurayi naso aura Allah baiyi ba toh ya zakayi da kaddara"


"Hakane Kam mudai Allah ya rabamu da mumunan kaddara"


Ji nayi nama kasa cin ciccibin hararowa nake ni zaa kawo yarinya irin ummi,satar kallonta nayi Muka hada Ido,ta sakar min murmushi ta sunkuyar da Kai Ni kuwa ban d'auke idona ba na zuba Mata Ido,doguwa ce mai zagayyen fuskan hancinta nada tsayi gashin girarta yakusa hadewa waje daya,tana da dan.manyan ido,da karamin baki,bata fiye duhu ba bata fiye haske ba,duk da banga kalar jikin nata ba,daga zaunen da take Ina iya hango tudun kirjinta indai ba ciko tayi ba tana da na fulani manya kiris ya rage ta shiga sahun masu kib'a indai kishiyar tata ba mai balain zafi bace lailai wanan zatayi saurin kwace shi,badan tace an sa Mata rana ba da gidanmu Zan kaita wlh bazan bari ma mahfuz ya ganta ba na ayyana a raina.


Kiraye kirayen sallah magriba yayi daidai da tsayuwar machine d'in mahfuz a k'ofar gida.


"Aikuwa ga maigidan ya dawo"


Mik'ewa tayi da sauri nace "A Ina zakije ki koma ki zauna idan ya shigo ku gaisa"Komawa tayi ta zauna a kasan kafet ta sunkuyar da kanta sai Wasa take da zoben hannunta inasan yanda take da dan kunya.


Shigowar mahfuz da sallama yasa na m'ike Ina "oyoyo Abban Mimi"


Na karbe ledojin daya shigo dasu Ina ta mamakin ko dai kudi ya samu haka da yawa wanan uban leda haka.


Wajen da Mimi ke kwance ya nufa bai ko kalli b'arin da ummi take ba ya d'auki mimi a daidai lokacin da ummi ta Masa sannu da zuwa sai a lokacin ya kalleta ya amsa ya d'auke idonsa daga kallonta a daidai lokacin da ta mik'e ta nufi daya d'akin sai dana tabbatar da ta shige ciki nace "itace wacce Abdul ya kawo bakuwar tamu"


"Naganta takura Mana kawai yakeso yazo yayi dan rainin hankali"


Kasa yayi da murya ya matso kusa dani yana "Wai kina nufin a wancan d'akin zata zauna"?


"Emana da a Ina kakeso ta zauna"?


"Lallai bakida hankali,ga dakinmu ga d'akin da take ciki kinsan kuwa duk motsin da akayi a daki ana jiyowa"


"Kai jamaa toh Ina kakeso na kaita"?


"D'akin tsakar gida amma zamanta anan ai da takura gaskiya"


"Haba Mahfuz d'akin tsakar gida sai kace namiji taya zan sauketa a tsakar gida sai nake ganin kamar hakan bai dace ba ko Abdul ne yazo gidanan yaga na ajiyeta a tsakar gida zaiji ba dadi wlh"


"Wlh ba abinda ya shafeni nida gidana baza'a a zo a takura  min ba a d'akin tsakar gida zata zauna na gama magana"


Ya fara k'ok'arin mik'ewa yanda ya had'e rai.yasa ban Kara magana ba na fara bude ledojin daya shigo dasu,gwanwanin Madara ne dasu bournvita har dasu cornflakes, siyayya sosai har dasu kifin gwangwani  da balangu bredi mai yanka yanka mamaki yasa nace "A ina ka samo kudi haka mahfuz"


"Wlh wani kudi yau aka raba Mana shine nayo Mana siyayya"


Tunda na aure shi bai tab'a yo Mana irin wanan siyayyan ba, shiyasa mamaki rufeni farinciki Kuma ya gaza b'oyuwa a fuskata,dan dama ni mayyar cornflakes ce dan sacet nake siyowa

"Yeee nima na faso gari mun zama yan gayu Kai wanan bakuwar ta zo da goshi"


Bai kulani ba ya nufi daki Yana bari yaje yayi alwala


Cikin farinciki na kwashi kayan na Kai kitchen na hau jerawa a dan glass din dake kitchen din har dasu bama ya siyo Mana na kuwa ji dadi sosai.


Sai da na gama jerawa na dauki balangun na juye a plate na dibar wa ummi na saka mata tuwo mulmule biyu da Miya na dauki karamin exotic na hada a faranti gabad'aya na Kai Mata har daki a kwance na tarar da ita da alama daga wanka ta fito dan jikinta da lema ta saka karamin t shirt da bakin dogon skirt,sai da gabana ya Fadi dana ga surarta take na karbi shawarar mahfuz na in maidata d'akin tsakar gida tab.


Tana ganina ta rarumo hijabi tasa ta tareni tare da karbar farantin hannuna tana "Sannu Aunty"


"Yauwa nace Mata cikin murmushi Ina ga abincin ki nan idan kin gama ci zanzo na Kai ki d'akin can Kamar sai kinfi sakewa acan"


"Toh Aunty ngd da dawainiya"


"Lah ba komai na sakar mata murmushi na fito daga d'akin.


Na Shiga nawa mimi ce kawai a kwance da alama mahfuz ya fita massallaci.


Wanka na Shiga dan tuni na watsar da wankan jego na koma normal wanka.


Ina fitowa daga bandaki yayi daidai da shigowar mahfuz bai d'auke idonsa akaina ba ya zuba min Ido 


Nida kayana nasan hali, ya matsu yaga Ina sallah


"Mallama Wai har yanzu shiru nafara gajiya fa"


"Tab kwana ashirin kawai da haihuwa sai nayi arbain fa"


"Wlh baki isa ba tab so kike na mutu kenan ya zauna a gefen gado,na gama shafe shafena na saka kayan shan iska.


Ina sai kayi sallah zamuci abinci ko na zubo yanzu"?


Bari ayi sallah Isha Kar nazo na kasa tafiya massallaci.


"Tom mu tafi Palo mu zauna"


Na dauki Mimi nayi gaba ya biyoni a baya.


A Palo muka zauna Muna kallo muna tab'a hira Yana latsa wayarsa hankalinsa dai Yana Kan wayar gabad'aya.


Sai ni kedai ke zuba surutuna har aka Kira sallah Isha ya fita massallaci bai dawo gidan ba sai wajen tara daga zuwa massallaci abincin ma da na jera Mana ya hucce tuni na cika nayi fam zuciyata ta fara rayamin kodai zance yaje take naji hankalina ya tashi,Ina tsoron tsinaniyar yarinya nan Mai nacin tsiya ce ta dawo rayuwar mijina wayata na d'auko dan na kirashi sai gashi ya shigo,da carbinsa a hannu da jalabiyar sa.


"Daga zuwa massallaci abban Mimi"?


Ina k'ofar gida wlh da Hamisu muke ta hira da kin leko zaki ganmu ai


Sai a lokacin hankalina ya kwanta


Muna cikin cin abincin Muka ji motsin bud'e k'ofar d'akin sai ga ummi ta fito da dogon hijabinta har kasa mahfuz ko kad'an bai dago ba Ina k'ok'arin Magana tace "Aunty dama bacci nakeji shine nace ko Zaki nunamin d'akin"?


Mik'ewa nayi Ina sude hannuna nace "eee zomuje nama dauka kinyi baccin ne wlh'


Nayi gaba tana bina a baya har muka fice daga palon,dama d'akin duk da baa kwana a ciki Ina yawan gyarawa Ina Kuma turarawa sai dai ba  bandaki a ciki, bandakin a tsakar gida yake idan nayi baki da bandakin tsakar gidan suke amfani ,Yan uwa ke Shiga bandakin cikin daki.


Muna Shiga d'akin nace "dafatan d'akin ya Miki"?


Kai sosai ma wlh yayi aunty ngd Allah yasaka da alheri"


"Lah ba komai ai an Zama daya sai dai nace sai dasafe kenan"


"Toh aunty sai da safe a shafa min Kan Mimi"


Da murmushi na amsa Mata na fito daga d'akin.


Sai da muka gama cin abincin na kwashe komai na Kai kitchen na dawo na tarar da mahfuz na latse latse a wayarsa.


Nima wayata na d'auko na hau latsawa Ina chatting Ina kallo kafin goma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana.

Hakane yasa na kashe data na kalli mahfuz daya danke wayar sa da hannu biyu nace "Tom nidai bacci nakeji zanje na kwanta"


"Kije kiyi kwanciyar ki dan ni ba bacci nake ji ba ko na biki daki ciwon maran zaki sani a banza nidai na fara gajiya fa tam"


"Kazo muje mu kwanta na maka tausa wlh Zan maka dabaru"


"Naki fa kibar ni na cigaba da hira da abokina"


Ya hasko min fuskar wayarsa Inda naga sunan Abdul din da Abokina 


"Ai shikenan sai ka shigo"


Bai bani amsa ba Ina shiga ciki na canza kayan jikina zuwa na bacci Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani bansan lokacin da ya shigo ba.


Washegari da wuri na tashi dan na hada breakfast dan mahfuz da wuri yake fita.


Ina cikin soya dankali naji sallamar ummi.


Na amsa Mata daga kitchen ina mamakin me ya sa ta tashi da wuri haka.


Har kitchen tazo ta sameni muka gaisa da ita Ina satar kallonta Ina San yanda take shigar hijabi har kasa da alama tana da kamun Kai


"Aunty Ina tsintsiya nayi shara"?


"Ummi dan Allah koma kiyi kwanciyarki dan kawai ki tayani aiki Kika taso"


"Dan Allah karki hanani tun jiya nakeso na tayaki kina hanani" karfe Tara zanje wajen da zamuyi program din shiyasa na tashi da wuri"


Duk yanda naso hanata ki tayi akan dole na nuna Mata wajen da tsintsiya yake ta d'auko ta fara share palon.


Har tsakar gidan naji tana sharewa.


Sai da ta gama ta Kara shigowa da bokitin mopping da abin mopping din tana cikin mopping mahfuz ya fito daga d'aki cikin shigar suit sai kamshin turare yake.


Adaidai lokacin da Nima na fito da farantin abincin karyawarsa.


Gaisuwar ummi ya amsa ba yabo ba fallasa ya tambayeta ya bakunta ta sunkuyar da Kai tana murmushi nidai idona nakanta atoh karta sake ta kallarmin miji ganin na ajiye farantin a gabansa yasa ta ajiye abin mopping din tana "idan ya gama na dawo na karasa"


Hankalinta na Kara gani,dan naga tana nesa nesa da mijina haka nakeso shima mijina ya iya tsare gida.


"Mai kike murmushi ke kadai"?


Tambayar da mahfuz ya jefomun kenan


"Wlh yarinya nan nada hankali mahfuz da gani ta samu tarbiyya sosai duk da a Lagos take zaune"


Tab'e baki yayi bai ce min komai ba Nima ban Kara magana ba har ya gama  cin abincinsa 

Ya Mike zai tafi na tafi dan na raka shi munje bakin k'ofa ya juyo Yana "Na manta ban fada Miki ba Abdul jiya yace na fada Miki wanan yarinyar ba komai ta iya ci ba ya roki arzikin a ringa tambayarta abinda zata ci ko a barta ta dafa abinda takeso dakanta wlh badan kin dage ba da sai na Masa rashin mutunci nida gidana azo ana min iko"


"Allah sarki wlh ba damuwa ai kana ganinta kasan Yar hutu ce ba irinmu da duk abinda muka samu ci zamuyi ba Tom ba damuwa ai tunda ba laifi muna da Abubuwan Yan gayu yanzu a gidan idan ma cornflask take so ta ringa Sha gashi nan"


"Ku kuka sani"


Yace a daidai lokacin da ya ida fitar da machine dinsa ya tayar ya tafi Ina daga masa hannu.


Ina komawa ciki na karasa mopping din na turara koina kafin na koma d'akin Ummi dan na tambayeta mai zata ci.


Kwalliya na tarar tanayi a lokacin da na Shiga tana ganina ta saki murmushi tana "so nake na shirya kar nayi latti"


"Kina nufin bazaki karya ba Zaki tafi nidai na soya dankali da kwai sai kayan shayi bansani ba kinaci ko bakya ci idan bakya ci sai a sama Miki wani abu dan Abdul yace Wai ba komai kike ci ba"


"Eee wlh aunty duk wani abu Mai maiko ban fiye ci ba da safe nafiso nasha corn flask haka ko bakin tea"


"Toh shikenan ki gama shiryawan akwai cornflask sai ki hada ki Sha"


Godiya tamin na sakar mata murmushi na fito.


Ban Dade da fitowa ba sai gata ta shigo da dogon hijabinta har kasa da farin glass.


Tana Zama na dauko mata kofi da cokali da tuni na ajiye Mata Madara da cornflask din


Cikin nutsuwa ta hada ta Sha sai satar kallona take narasa Mai yasa take San satar kallona.


Tana gama Sha ta mik'e da Yar Jakarta tana "Bari naje kar makara sai na dawo"


A dawo lafiya" ta fice daga gidan ni Kuma na koma daki.


Ina kwanciya mamn Iman ta hau bugun kofa tana kwallamin Kira


Ko mai take nema a wajena da sassafe haka oho na mike nayi hanyar waje........
Karku manta a gobe zamu gama free pages insha Allahu ku biya 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko ta Nan 0000551222 taj bank nafisa Nuhu ko katin mtn a turo da shaidar biya ta layin nan 08033719070 yanzu zamu shiga cikin labarin budurwar mijina karki sake a barki a bayaKAYAN MATA


Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?


Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?


Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?


Shin minene matsalar?

Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?


Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,


Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,


Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 🥰 kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,


Munada tsumi nau'i nau'i

Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu

Akway ruwan jaraba

Ruwan Dadi

Hadin minannas

Hadin dafa kaza(manta uwa)

Hadin yar gaban goshi,

Turarukan mallaka.


Duk a farashi mesauqi.


Serious buyers call, WhatsApp 07046881166


Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagode

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


*LAST FREE PAGE*


*PAGE 10*


Ina bud'e kofa na yamutsa fuska Ina "Shi bawa bazaa barsa ya huta ba"


"Eee baza'a barki ki huta ba wuce muje"


Dariya nasa dan muna Yar Wasa da mmn Iman sosai muna Shiga ciki ta zauna a dogon kujera tana kalle kalle nima na zauna a kujera mai kallonta Ina "kefa wani zubin kanki ba dadi Mai kike dubawa ne"


"Mai nake dubawa kuwa so nake na tabbatar da ba kowa a gidan kafin nayi magana duk da Naga fitar mahfuz da bakuwarki"


" Ba kowa dagani sai Mimi kin samo mai zafi kenan"?


Nace Ina maida hankalina gabadaya kanta dan Naga alamar da magana tazo Mai mahimmanci


"Eee da magana nazo Kam amma nariga da nasan halinki gajen hakuri baki iya bin komai a hankali ba"


Mik'ewa nayi da sauri na koma gefenta na zauna Ina "Mai ya faru mmn Iman bani labari"


"Wai ya kuke da bakuwar nan da tazo jiya"?Yamutsa fuska nayi Ina "Wai Ummi"?


"Eee"


"Ba dangi iya babu na baba Ina Abokin Mahfuz Abdul da nake dan baki labarinsa Yana yawan yi Mana aike har kike cewa idan kina da kanwa da kin bashi"


"Eee na tuna shi""Toh yarinyar yayarsa ce suna zaune a Lagos tazo nan wani program ne na sati daya ko kwana goma yace ne jiya dai da kansa ya kawota,lafiya kuwa kike tambayeni"?


Ajiyar zuciya ta sauke tana "Ni yarinya Sam ban yarda da ita bane naga tana ta Abu kamar mara gaskiya,kinsan jiya nan Ina zaune wlh satar kallonta kawai nake ni a idona ma sai naga kamar kallon banza take miki kasa kasa"


Dariya na kwashe dashi Ina "Kai mmn Iman abin naki har da sharri yarinya da ko kallona bata iya yi ga kunya"


"Kefa dadina dake hauka wlh Ina miki maganar serious shi Abdul din duk wayanda ya sani anan ga gidansu mahfuz Mai yasa bazai kaita can ba sai nan, Taya zaa kawo Miki tsalleliyar budurwa irin wanan haba mana"


"Wani kusancin ai yafi wani mmn Iman shiyasa ya kawota nan Allah sarki kawata tsoro kike zaa kwace mun miji ko"


Na kyalkyale da dariya mmn Iman ta zuba tagumi tana kallona 


"Kwantar da hankalinki ba Mai kwace min miji mahfuz Zan iya rantse Miki ba lailai yasan kamaninta ba dan ko kallonta bayayi,itama ba lailai tasan kamaninsa ba dan tana ganinsa take sunkuyar da Kai"


"Tom ai shikenan amma nidai ban yarda da ita ba wlh masu shiru shiru da saka hijabin nan wlh munafikai ne,a idona jiya ta Miki kallon banza ke Kuma ga saurin sakin jikin balai name kike wani janta da hira"


"Kai mmn Iman bakonka annabinka so kike na hade rai,nifa kinsan ban iya wulakanci ba"


Mmn Iman shiru tayi dan ba iya maganar da ya shigo da ita kenan ba,jiya taji mahfuz nata waya a k'ofar gidan ta har makalewa tayi a jikin kofa dan taji Mai yake cewa soyayya yake zubawa a waya da wata taso ta fadawa lubna ta saka mishi ido amma tuna haukar data Mata kwanaki yasa ta hakura"


Maganar lubna ya katse Mata tunanin da take


"Mmn Iman mun zama yan gayu fa jiya Kinga siyayyar da Mahfuz yayo Mana kuwa zomuje kitchen kigani"


Na jawo hannunta mukayi kitchen din Ina bata labarin abubuwan da mahfuz ya siyo Mana jiya.


A bakin kitchen ta tsaya na hau nuna Mata ta ringa gyada Kai dan ita dama mijinta na siyo mata nice dai bakuwa da aka siyomin  a Karon farko.


"Aaa lailai kam kun zama Yan gayu kin huta da siyan kanana Yan sachet nidai ko dan bakuwar aka muku siyayya haka sabida Kar ta Raina ku"?


"Ko daya fa tazo dai a daidai ne wani kudi suka samu yayi Mana siyayyan,dazun Nan yake cemin ya bada kudin ragon layya,yau saura kwana biyar fa Mai da me ya Kamata muyi?


"Mai kuwa zamuyi daya wuce ayi yanka mu soya ban karya ba mallama zubo Mana dankalin muci"


Ta koma Palon na juyo dankalin a plate da kwai flask din tea din na Palo da bredi Muka fara ci


"Kiringa Jan class dinki lubna ki daina sakar wa wanan bakuwar taki fuska kina zuba a gabanta haba jiya kin bani haushi wlh banda kin dage da a shawarce kin yiwa mahfuz magana ta koma gidansu wlh tunda akwai Yan mata acan itama sai tafi sakewa"


Mmn Iman nifa haka nake wlh ba sakin baki ne dani ba,ni ban iya wulakanci ba Sam,idan taga bana Mata magana ko bana Mata hira ai sai taga dan tazo gidana cin arzikine kinsan Kuma haka ba dadi""Hakane Kuma toh ki ringa ragewa"


Insha Allahu Koda muka ci abinci hirar muka cigaba da yi ta tayani yiwa Mimi wanka kafin ta tafi.


Tana tafiya Nima nayi wanka Yau kwalliya da soyaya nake ji dan dazu mahfuz yamin kyau.


Kwalliya naci da sabuwar atamfa a irin dinkin da mummy tamin dark purple ce da zanen yellow ta balain yimin kyau,ni kaina na kasa d'auke idona daga Kan mudubin. 


Shayar wa da nake yasa kirjina ya ciciko ya fito har ta saman rigar dinkin yamun das a ciki,banida burin daya wuce mahfuz yaga kwalliyar nan.


Mimi itama purple din kayan kanti na saka Mata wayata na dauko na kira mahfuz a waya bugu daya ya d'auka


Yana "Madam yanzu nake Shirin kiranki naji lafiyarku"


Wal nayi ido kamar yana gabana nace "idan ba abinda kake yi ka kunna data muyi video call"


"Angama"


Ya katse wayar Ina kunna data kiransa na shigowa


Ina dagawa na sakar Masa murmushi tare da bankaro kirjina 


Ido ya zuba min sai daya dade baiyi magana ba kafin yace "hmm kin kirani ne dan kawai ki tsokane ni ko?, zan kamaki ne ai"


Yace Yana tauna lebbe na Masa gwallo "Ina bakace nayi kyau ba"?


"Sai na dawo zakisan kinyi kyau ko bakiyi kyau ba ke kadai ce a gidan"?"Eee wlh ni kadai ce ummi bata dawo ba so nake ma yanzu na tashi na dora abincin rana sabida ita amma idan tani ne cornflaskes Zan Sha"


Tab'e baki yayi bai ce komai ba nace "Ko na dafa har da Kai na Aiko maka dashi"?


"No ba sai kinyi dani ba karki wahalar da kanki abincin ranar ma karki wahalar da kanki wani dafa Mata idan ta dawo kice ta Shiga kitchen din ta dafa abinda take so da kanta ba yanda zaayi wata gardiya tazo ta samin mata wahala"


Abu kad'an ke Sakani dariya gardiyar da yace yasa nayi ta dariya har cikina na neman kullewa ganin zai kashe wayar nace "bakuwa ce fa bai dace nasa ta aiki ba"


"Kika dafa Mata Abu ban yafe ba kibari ta dawo tayi kayanta ke ai Yar aiki ma aka kawo miki har girkin Daren ma ki bata tayi"


"Lalalala Haram wata tayiwa mijina girki ni zan ma girki da kaina"


"Dariya yasa Yana to ayi mana mai dadi Zan aiko da kayan ciki anjima a dan yi Mana ferfesu"


"Waw abban Mahfuz kudi Wai ka samu haka kasan kuwa inata shaawar ferfesun kayan cikin nan bana so na maka maganar ne bansani ba ko bakada kudi"


"Da kin gayamin ai tunda na Sunan soyewa akayi karki damu Zan aiko anjima bari nayi wani aiki ya sakar min kiss ta wayar nima na mayar Masa ya katse wayar.


Bai sabar mun da haka ba hakane yasa na kasance cikin tsananin farinciki Ina adduar Allah ya Kara buda Masa inasan irin rayuwar nan dama ne bansamu ba.


Naso nayi girkin amma sabida mahfuz ya hana ni na hakura idan ta dawo nace ta girka abinda take so din.


Bacci bacci na fara ji na kwanta a doguwar kujera Mimi bata da rigima ko kad'an ba karamin abu ke sata kuka ba.


Baccina ya fara nisa naji an kwankwasa k'ofa na Mike na kalli agogo karfe daya da rabi.


Ina bud'ewa naga Ummi ce da fuskarta ke  d'auke da murmushi nan da nan ya dishe ta daskare waje daya tana kallona ni na dauka ma wani abin ne na juya dama da haguna na dawo da kallona kanta Ina "Ummi lafiya kuwa"?


Nidai a idona sai naga kamar murmushin yake tayi idonta har ya canza kala


"Sannu da gida Aunty kinyi kyau"


"Anya kalau kike kuwa ummi na ganki wani iri ko duk gajiyar ce"?


Gyada min kai tayi a daidai lokacin da ta shigo tana "bana dan Jin dadi ne wlh"


"Allah sarki sannu inaga gajiya ce ki watsa ruwa ko zakiji dadin jikinki Kinga ma ban yi girki ba dan bansani ba ko Zan girka abinda bakya so nace bari ki dawo ki dafa abinda kikeso da kanki"


"Toh Aunty ngd bari na watsa ruwan"


Ta bude d'akin tsakar gidan ta shige.


Na koma Palo na zauna na kunna tv na kai tashar Bollywood Ina cikin kallon aka Kara buga kofa naje na bud'e almajirin mmn Iman ne da kula a hannunsa.


Karbe kular nayi nace ya mata godiya na koma ciki.


Ina bud'ewa naga danwake ne ya sha hadi har da dafaffen kwai gashi da manja tuni yawuna ya tsinke na je kitchen na wanko hannuna har Zan fara ci na ga dacewar yiwa ummi tayi kila tana cin Dan wake.


Labulen d'akin na daga da sallama tana waya kasa kasa shigowata yasa ta katse wayar da sauri,nidai a idona Kamar akwai abinda ke damunta duk sai naji ba dadi a yanda na ganta.


"Ummi dan wake aka aikomin dashi bansani ba ko kinaci nace bari na miki tayi"


"Wlh aunty ban fiye san dan wake ba ngd sosai


"Ummi kodai na kawo miki Panadol ki Sha ne"?


"Aaa wlh aunty gajiya ce kawai da yunwa yanzu zan fito na dafa ko indomie ne"


"Toh sai kin fito"


Na juya na koma palo na zauna na fara cin danwake Ina korawa da exotic din mahfuz ya siyo mana jiya saura kiris na cinye duka sabida dadin daya min.


Da sallama ta shigo palon na amsa Ina kallon doguwar rigar da ta saka Mai balain kyau yellow ta yafa mayafinsa.


"Bari na dafa indomie Aunty"


"Akwai komai mai kike bukata a kitchen din"


Ta amsa da toh ta shige na cigaba da kallona Ina hararo doguwar rigarta a jikina yamin kyau inama Ina da kudi na siyi irinsa Ina Kuma mamakin Inda ta ajiye hijabin nata,ko saka hijabin dama na bakunta ne.


Ta dan jima a Kitchen din kafin ta fito da plate a hannunta sai pure water da ta d'auko da daya hannun har zata wuce nace "kiyi zamanki anan Mana kici kya  shige daki ke kadai ki zauna"


Murmushi tayi ta dawo ta zauna a kasan kafet ta tankwashe kafafunta ta dago tana "Aunty kizo muci"


"Kai cikina a cike yake wlh"


Na saci kallon indomie da ke ta zuba  kamshin sardine lailai da alama ummi Yar hutu ce da mahfuz bai siyo kifin ba da kila sai dai ta siyo kifin da kudinta,a Raina na ayyana kila ta d'auka haka muke da kayan a ajiye.


Tana cin abinci lokaci lokaci muna hada Ido sai muyi wa juna murmushi,bakina ma nauyi yamin a San na dau shawarar mmn Iman Kar na ringa zuba kamar yanda tace amma so nake kawai muyi Hirar.


Sai data gama cinye indomie ta kai plate din kitchen ta dawo ta zauna.


A daidai lokacin da wayata ta fara ringing ganin mahfuz ne yasa na d'auka cikin murmushi Ina "Abban mimina"


"Madam na aiko yanzu zaa kawo kayan cikin"


"Tom sai an kawo ya aikin"


"Alhamdulillah Ina mimina"?


"gata idonta biyu kaci abinci"?


"Aa banci ba sai na dawo zanci abincin Mai numfashi da Mara numfashi tunda har Kika tsokano ni"


"Lalala badani ba ban shirya yiwa Mimi kanwa ba"


"Zaki shiryeni ki tanadeni mallama"


Ya katse wayar na sauke wayar Ina dariya na kallo wajen da ummi ke zaune naga ta zuba min Ido muna hada Ido ta d'auke da sauri.


Bance Mata komai ba na ajiye wayar nima Ina satar kallonta tana ta cizar yatsarta.Tuna ban gama Shan tsumin da mmn Iman ta kawomin ba yasa na m'ike naje kitchen na d'auko na dawo na zauna na bud'e ta dago ta kalleni ta sakar min murmushi Nima na sakar Mata na Kai gorar bakina.


Wani daci naji ya gauraye min baki na furzar da tsumin da sauri Ina "Subhanallahi"


"Lafiya kuwa Aunty"?


Ban iya bata amsa ba na cigaba da goge bakina dan daci sosai.


Sai da na gama nace "wlh daci ne da tsumin nan sosai ke kinji dacinsa"


Bata ce komai ba tamin murmushi na fara mita Ina bari na gama aikina na Shiga gidan mmn Iman na fada Mata.


Ba'a fi minti goma ba sai ga Wanda mahfuz ya aiko ya kawo kayan cikin.


Ummi ce ta bud'e masa kofa ta Kuma karbo ta kawomin nace ta Kai kitchen karfe hudu zan shiga kitchen,Koda ta Kai banga ta fito ba sai buruntun ta kawai na ringaji a kitchen banaso nabi bayanta ta d'auka ko yarda ne banyi da ita ba hakane yasa na cigaba da Zama amma hankalina na kanta.


Bayan Yan mintina sai gashi ta fito tana "tayaki dorawa nayi Aunty na dauraya kwanun da naci abinci dashi


"Allah sarki na kuwa gode ummi"


Har a raina naji dadi bata da san jiki Sam.


Koda na Mik'e dan na Shiga kitchen din tashi tayi ta bini Ina tayi zamanta ba sai ta tayani ba amma ta dage sai ta tayani a dole na kyalleta muka yi fried rice na hada coslow.


Ga ferfesun kayan cikin shima yayi dadi sosai.


Sai da muka gyara kitchen din.


Muka fito tayi tsakar gidan ni Kuma na fara hada ruwan da zanyi wa mimi wankan yamma.


Tun jiya kamar jinin ya d'auke duk da Wasa yake min inaga anjima nayi wankan tsarkin amma ban shirya daukan wani cikin ba banaso mahfuz ya  tabani har sai nayi tsarin iyali.


Ban Kara Jin motsinta ba har nima nayi wankar yau shigar kananan Kaya nake ji.


Hakane yasa nasaka Riga da wando maroun yayi balain min kyau banida wani tsayin gashi sai cika na gyara gashin nayi parking na Kara gyara ko'ina  na turara jikina da turare na kame a Palo.


Kamar zan leka ummin Kuma na fasa dan bana so na Kuma ringa shige Mata tunda nice matar gidan.


Gab da magriba mahfuz ya dawo.


Sai daya shigo har palon naje na rungume shi dak'yar na kwace bakina daga nasa nayi baya yayo kaina Yana "Baki Isa bafa Ina zaune Kika tsokano ni"


Dariya na ringa yi sabida zagaye kujerun Palon mukayi tayi,dana ga ya kusa kamani na fita waje da gudu a daidai lokacin daya damkoni jikinsa Yana "Wa na Kama"


Karar faduwar bokitin da muka ji yasa mukayi firgigit muka kallo wajen da muka ji karar Ummi ce a tsaye ta sunkuyar da Kai jikinta na dan rawa da alama ruwa zata Kai bandakin rigar dazu ce dai a jikinta bata cire ba.


Mahfuz cikani yayi da sauri ya koma ciki.

Na nufi wajen ummi Ina "garin yaya bokitin ya Fadi"


Bata dago ba tace "wlh subuce min yayi"


"Gashi rigar taki kuwa ta jike"


"Ee dama wanka zanyi Bari na canzo ta dago ta kalleni.


Yanda take kallona daga sama har kasa yasa nace "Yadai"


"Kinyi kyau sosai Aunty"

Cikin murmushi nace "Kina san fasa min Kai ummi jeki yi wankanki bari nayi sallah Nima.


Na juya na shige palon na barta a tsaye tana kallona


Nima ko bata fadamin ba nasan nayi kyau inaso ace min nayi kyau Dadi nakeji, idan har mace Yar uwata zata ce nayi kyau inaga mijina.


Ina shiga d'akin mahfuz ya fito daga bandaki ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya ruwan kasa Mai zip a gaba.


Ya dau carbinsa yayi waje.


Bai dawo cikin gidan ba sai da aka iddar da Sallah Isha


Yana shigowa na jera Mana abinci a tsakiyar kafet na zubawa ummi na dora Mata akan karamin farantin na d'auka na Kai Mata har daki.


Koda na Shiga akan katifa na ganta a zaune ta saka wani vest ja Rabin na fulaninta a waje sai dogon wando.


Da murmushi na ajiye abincin Ina "gashi nan"


"Tace ngd Aunty"


Nayi waje Ina fatan ba abinda zai sake fito da ita,dan sam.bangane Mata ba jiya wuni tayi tana saka hijabi yau Kuma ba hijabin dan ma naga.mahfuz ko kallonta bayayi abinda ya kwantar min da hankali kenan"


Koda na koma Palo hankali kwance muka ci abincin mu muna tab'a hira Inda nake ce Masa jibi zanje kitson sallah da kunshi sabida bazan iya bin layi ba,yace Allah ya kaimu ya bani kudin.


 Karfe goma naji na fara Jin bacci nikam bansan Mai yasa yanzu nake da saurin Jin bacci ba.


Ina mik'ewa shima ya mik'e ya d'aukar min Mimi muka Shige daki.


Ban bari yayi komai ba sai dabaru da na Masa Nima yamin muka samu nutsuwa dan ce Masa nayi ya bari nayi allura tukunna.


A tare mukayi wanka na dauka zai kwanta ne yacemin Palo zaije yayi kallon ball baya Jin bacci.


Sama sama ma naji shi dan baccin ne a kaina sosai.


Bansan lokacin daya shigo ba.


Washegari ma ummi ce ta tayani sharan tayi mopping Ni Kuma na hada mana breakfast mahfuz yaci ya tafi.


Itama Tara nayi ta fice na shiga gidan mmn Iman muka yi ta hira anan nake fada mata a cikin tsumin da ta kawomin akwai mai balain daci,tace tana ganin ba tsumin na Sha ba dan duk tsumin ba mai daci ko kad'an nayita mamaki tace na gwada sauran ragowar naji ko da daci sai da na koma gida na dauko mata ta dandana tayi ta mamaki tana ta sha irinsa ba daci ko daya,ban bar gidanta ba sai karfe biyu na koma gida a daidai lokacin. Da ummi ta dawo wanan karon ma ita ta Shiga kitchen ta samawa kanta abu taci.


Ta tayani wanke wanke,girkin yau ma ta dage min ita zatayi yanda ta dage yasa na kyalleta tayi girkin.


Yau dai ita take Jin hirar hakane yasa nima na biyeta dan nikam inaso naga muna Hira.


Yau ma bata saka hijabin ba Kamar na tambayeta na Kuma share.


Sai cewa take na iya wanka zata Zo wajena d'aukar course idan auren ya kusa muna burgeta nida mahfuz


Tuni na washe baki nace insha Allahu duk zan bata sirrin zamantakewa na aure,na bata labarin irin soyayya da muka zuba da mahfuz kafin muyi aure,kamar zan bata.labarin tsinaniyar yarinya nan data makalewa mijina da irin hawan jinin da ta so doramin na Kuma fasa.


Itama ta bani labarin yanda saurayinta ke Santa akanta har fada yake da matarsa.


Anan na nuna mata rashin Jin dadina akan bai dace saurayinta yayi haka ba dan itama zai iya mata haka idan ya aureta idan giyar so na kwasar sa yanzu ta ringa Dora shi akan hanya.


Godiya tamin wajen shidda ta mike ta tafi d'akin nima na dau mimi dan yau bamuyi wanka da wuri ba.


Haka kawai sai na fara gaskata mmn Iman akan bata yarda da ummi ba,dan sau biyu Ina Kamata kamar hararata take idan taga na ganta sai ta wayance da sosa Ido,yau bansan inda mahfuz ya tsaya ba,bai dawo kafin magriba kamar yanda ya Saba ba.


Koda na iddar da magriba ban fito daga d'aki ba dan so nake idan akayi isha sai na fito gabad'aya kafin dai ayi sallah Isha na tashi Ina dan gyara kayana dana hargitso.


Sallamar ummi da shigowarta har tsakiyar dakina yasa nayi saurin juyawa Ina kallonta.


"Tun dazu ake ta kiranki aunty ganin baki fito ba yasa nace bari na kawo miki"


Sam banji dadin shigo min d'akin da tayi tana kalle kalle ba hakane yasa na karbe wayar a hannunta fuskata a had'e nace Mata na gode ta juya ta fice tana karewa dakina kallo kamar na bita na gaura  mata mari wlh na tsani a shigo min dakina 


Da alama fuska biyu ne da yarinya nan,dole kuwa na taka Mata birki bana san iskanci dan ko a yanzu ma ba hijabi a jikinta riga da skirt tasa taci kwalliya kenan ma a palona ta zauna da Mahfuz ya shigo ya ganta faTake naji raina ya b'aci na  dauki Mimi nayi hanyar palo.


A kasan kafet naganta a zaune tana kallo mugun hade rai nayi dan naga alamar na sake Mata da yawa.


Sau daya ta dago ta kalleni tana "kinfito ne Aunty"


"Um"kawai nace mata 

Karar machine d'in mahfuz da naji a waje yasa na kalleta naga ko zata tashi amma Ina zamanta tayi ba alamar zata tashi.


"Ko zaki koma ciki ga Abban Mimi ya dawo"


Nace fuskata a had'e.


Mik'ewa tayi bata ce min komai ba ta fita waje naja tsaki ta juyo ta kalleni ta Kara d'auke kanta ta fice a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo na mike da sauri dan nasan ma ya ganta shegiya kawai naji na auna Mata zagiDaga labule Ina kallonsa bai kalleta ba har ya shigo 


Yanda yaga raina a had'e yasa murmushi daya shigo dashi ya kau Yana "Lubna lafiya kuwa"?


"Ba komai"


Kawai nace Masa na samu waje na zauna Ina Masa sannu da zuwa ya amsa Yana "Lubna ban Saba ganinki a haka ba lafiya kuwa"?


"Wlh wanan yarinya ce ta bata min Rai kasan na tsani naga an shigar min daki kwatsam sai gata ta shigo min daki ni naga alamar tana da rawar Kai a gaskiya in zata cigaba da min haka bazamu shirya ba"


"Oo keda kanki yau Kuma kika cewa ta bata miki rai, da da Kika kawota wancan d'akin fa"


"Gaskiya badan kusancinka da Abdul ba wlh gobe zata barmin gidanan bana San munafirci kaga kwalliyar da tayi sai kace wata matar gidan"


Daga hannuwansa sama yayi Yana "Ni ba abinda nagani mallama muje ki hada.min ruwan wanka tunda zu ma nake kiranki baki dauka ba"


Mik'ewa nayi na nufi d'akin ya biyoni a baya.


Koda na zuba Mata abincin a bakin k'ofa na ajiye Mata "Ina ummi ga abincin ki ban tsaya jiran ta fito ba na koma Palo mukaci abinci da mahfuz .


Muka tab'a hira lokacin baccina nayi na mike dan nasan sai yayi kallonsa na masifa daya tsiro dashi.


Washegari ban bari ta wani tayani aiki ba kafin ta fito na gama komai yau Kam bata Isa na Mata wani abin karyawar va abinda nayi zata ci.


Doya da kwai da tea.


Har mahfuz ya fita bata fito ba.


Ban Kuma damu na dubata ba bansani ba yau ko ba inda zataje,nidai yau fita zanyi zanje kunshi da kitso.


Mmn Iman tun jiya tana unguwarsu.


Idan ba inda zataje sai ta zauna tayi gadin gida na kulle palona.


Na shirya kenan,na fito Palo sai gata ta shigo palon sanye da hijabinta har kasa a Raina nace munafika


Gaisheni tayi.murya na rawa na amsa Mata Ina k'ok'arin goya mimi tace " Aunty ko dai akwai abinda na miki ne bansani ba"?


"Mai zakimin kuwa ummi"?


"Wlh sai Naga kamar na Bata Miki Rai bansani ba Dan Allah kiyi hakuri"


Tuni naji ta bani tausayi nace "ba komai wlh ummi jiyan ne raina a bace,ga abincin ki nan fita zanyi kinsan saura kwana biyu sallah zanje kitso da kunshi"


"A koshe nake Aunty bana Jin yunwa yau nima ba inda zanje Dan Allah ko zan iya binki kunshi bana so na zauna ni.kadai"


"Ba damuwa ki zo mu tafi.


Mik'ewa tayi da sauri ta fita waje ba dadewa sai gata ta fito da hijabinta har kasa.


Na kulle ko'ina muka nufi gidan kunshin.....

*BUDURWAR MIJINA*


             *NA SADNAF*


*E.W.F.*


*PAID BOOK*


Last free page 


Anan na kawo karshen free pages tighten your belt dan labari rikita rikita  karamin yak'i a cigaban budurwar mijina biya 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko 0000551222 Taj bank nafisa Nuhu idan katine turo Mtn ko Airtel ta layin nan 08033719070  ku turo da shaidar biya ta nan layin 08033719070 mutanen Niger Kuma katin Airtel zaku turo na dari biyar ta layin mtn din,daa baki labari gwara ki bayar da ki tsaya a sato Wanda ya hucce gwara ki kasance cikin grp ki karanta da duminsa,Yan albarka shekarar Nan hajji nakeso naje maza a harhado na samu na calle😀😀😀Last free page


Ba mu dade sosai a gidan kunshin ba dan dama Mai kunshin tasan da zuwana na Kuma dade da Kama layi.


Ni aka fara yiwa hannu da kafa ja da baki.


Ita Kuma ummi tace ayi Mata a iya hannu 


Sai amsa waya take kamar wata Yar kasuwa waya biyune da ita babba da Karama,anfi kiranta a karamar wayar.


Na riga ta cire kunshin hannuna,zaman da nayi bana komai yasa nace "Ummi dan bani wayarki na kalli hotuna"


zaro Ido tayi tana "Kai Aunty sai dai na baki karamar dan akwa sirrikana  a wayar nan kiyi hakuri"


Dariya ma ta bani na Kai hannu zan d'auka dan Yana cinyarta tayi saurin daukewa wayarta ya kawo haske.


Kamar dai hotonta ne da wani.


Girgiza kai nayi Ina "Ai shikenan"


A Raina na fara gasgata zargin da nake Mata da kila Yar duniya ce daga yanda maza rututu ke kiranta Anya ma ba karya tamin akan an sa mata Rana ba kuwa".


A haka na zauna itama ta cire nata.


Hannu na saka ajaka dan na dauko kudin kunshin tunda iya hannu aka Mata Dubu daya dai zan iya biya Mata Dan Dubu biyar mahfuz ya bani sababin dari bibbiyu.


Kafin na ciro kudin itama ta ciro sababin dari biyun ta kalli hannuna na kalli nata,ta saki murmushi tana "kema ashe dari bibiyun ne dake,jiya na tsaya a banki na cira"


Ta kirga Dubu uku ta bawa Mai kunshin dan nawa Dubu biyune.

Na maida kudina jaka Ina ngd.


Daga nan Muka wuce saloon,Ashe ba karamin gashine dani akanta ba.


Kitso aka fara Mata na kari shuku,ni Kuma aka fara yarfa min kananan kitso da iya gashina dan idan akwai abinda na tsana bai wuce Karin gashi ba banayi Sam duk da kitson Karin na balain saka mace kyau ni iya gashina ake kitsemin Kuma Ina kyau a haka.


Ummi kuwa ta balain yin kyau dan kitson nata har gadon baya aka Mata.


Bamu koma gida ba sai wajen shidda 


Da sauri sauri nayi wanka na fito na Dora Mana jollof din taliya da kifin gwangwani ummi Kuma tunda muka dawo data shige daki bata sake fitowa ba.


Mahfuz Bayan magriba ya dawo gida.


Kamar yanda muka Saba bayan sallah Isha na zuba mana abinci na zuba wa ummi nata daban.


Na Kai Mata har daki,sakin baki nayi Ina kallonta dan sleeping dress ta saka fara iya cinya shara shara Ina iya hango komai na jikinta ta saki gashin dokinta har baya, konida nake matar Aure bana fesa uban turaren da ta fesa yanda nake kallonta tasa ta jawo hijabi ta saka tana "Aunty wlh yau zafi nakeji"Gyada Mata Kai kawai nayi na ajiye Mata farantin na fito kaina na Kara daurewa da lamuranta.


"Kisa Ido sosai akan yarinya Nan lubna wlh ban yarda da ita ba bansan Mai yasa nakejin kamar ba alherine ya kawota gidanki ba"


Na tuna chatt din da nayi da mmn iman dazu


Duk sai naji jikina yayi sanyi har muka gama cin abincin abin na damuna a Raina sai matsawa kaina nake da tunani ko dai akwai abinda mmn Iman ta Sani akanta Wanda ni bansani ba,Ni mahfuz ba wani kallonta yake ba ballantana ince zata kwace min miji.


Haka dai na zauna mahfuz na latse latse a wayarsa.


Lokacin baccinmu nayi nace ya tashi muje mu kwanta sai yace min bayajin bacci


Ido na zuba Masa dan a da ba haka yakemin ba ko lokacin da yake ganiyar soyayya da wanan tsinaniyar Yana kwanciya sai dai ya saci jiki ya sake fitowa,Sam bana so Kuma na zarge shi muna zaman lafiya a yanzu.


D'akin nawa na shige na bar shi a palon Ina kwanciya bacci  ba dadewa bacci yayi awon gaba dani.


Mugun kishirwar da nakeji ne yasani tashi daga baccin daya d'aukeni.


Idona ya sauka akan agogon daki karfe biyu na dare,ba abinda ke tashi a palon sai karar Tv.


Mik'ewa nayi dan naje kitchen na d'auko ruwa kila ma bacci ya d'auke mahfuz akan kujera.


Ina zuwa palon na ga ba kowa bansan Mai yasa kirjina bugawa da balain k'arfi ba nayi sauri na Shiga kitchen nan ma mahfuz baya ciki.


Na fito da sauri,kwakwalta ta kasa bani wani tunani abinda kawai na iya ayyanawa a zuciyata shine Kar nayi kwakwaran motsin da zaa jini.


Hanyar wajen na nufa Ina tafiya cikin sand'a kirjina Kamar ya fado, Hoton ummi kawai nake hangowa a idona data Sha sleeping dress da mijina a d'akin.


Tunanin nan ya Sakani tsayawa Dan ji nayi Kamar an caka min wuka a kahon zuciya na Dade a tsaye dan kasa motsa kafata nayi Ido kawai na zubawa d'akin da ummi take dan Ina tsaye a tsakiyar tsakar gidan ba abinda nakeji sai karar fankar dakinta sai gani da adduar Allah yasa mahfuz na waje Yana Hira a waya da budurwarsa ba a d'akin Ummi zan gan shi ba na kara taku biyu zuwa k'ofar dakinta na manne a jikin k'ofar da aka turo ban Bari k'ofar tayi Kara ba.


"Dan Allah har ki bar gidanan karki yi abinda zata gane mu pls"


Shine abinda ya sauka a kunnena muryar mijina uban yata.


Wani Duhu ya giftamin ta Ido naji dum akaina.


Nidai bansani ba ko Nike da iko da jikina barin bakin k'ofar nayi na zagaya ta bayan d'akin da window yake burina na leka mijina na tabbatar da shi naji muryarsa


A tangal tangal din da hawan jinin a wacce ta samu karamin tabin hankali na leka ta window.


A kwance take a kirjin mijina ya cusa fuskarsa a tsakiyar kirjinta ta kankame shi tana shashafa shi sai sauke ajiyar zuciya take.


Wani duhu ya kara giftamin sai da na dau tsawon lokaci na fara ganin haske 


"Jeki kitchen ki d'auko ashana ga jarkar fetur can ki cilla musu ki Konasu Lubna"


"D'auko wuka ki Shiga har d'akin ki cakawa Ummi shima ki caka Masa"


"Jeki kwanta ki dauki mataki Mai kyau"


Duk zuciyata ke sakamin har na koma Palo cikin sand'a. 


Tamkar wacce aka bawa umarni na shige d'akina na kwanta nayi rub da ciki,abubuwa da yawa na dawo min kaina,fuskar Abdul abokin mijina kawai nake gani,Ummi Mahfuz,waye ya Kamata nafi Jin zafinsa.


Ina Jin labaran cin Amana Amma nawa yayi Muni budurwar miji har gidana har dakina"

Na kasa furta innalillahi wa Inna ilaihi rajiun idona dai kawai a rufe yake.


Anya a duniyar cin Amana akwai irin nawa kuwa"?


Dole akwai abinda mmn Iman ta Sani bata gayamin ba ta munafirceni,na Zama shashasha Ina bautawa budurwa mijina a gidan Aurena.


Ba digon hawaye a idona zuciyata kawai nasan ke zubar jini.


Ina kwance a rub da cikin naji shigowarsa a lokacin da ya kashe tv ya shigo d'akin.


Ya kwanta a gefena bayan ya Kara gudun fanka.


Tamkar huramin wuta ake a jikina haka naji na kasa tunanin mai ya dace nayi,


Ki tashi ki d'auko wuka kizo ki caka Masa Lubna


Allah sarki Mata da yawa da suke kashe mazajen su waya sani ko cin amanar da aka musu kenan"Tsawon awa uku akwance rabi mutum rabi Mai tabin hankali zuciya da gangan jiki azabar k'una aka Kira sallah asuba alarm ya tashe shi ya mike ya bar gefena kafin naji Ina shakar iska Mai kyau.


Idona rufe sai da yayi wanka ya fito ya zura jallabiya ya girgiza kafata Yana tashi kiyi sallah karki makara yayi waje.


Karar rufe k'ofar gidan da yayi yasani na mike tsaye.


Na nufi kitchen na d'auko katon muciyata Ina fita tsakar gida na kulle k'ofar da mukulli na Kara komawa na dauko wuka Mai kaifi.


Wandone dama a jikina. Tura k'ofar dakin nayi tana kwance da santala santalan cinyarta a waje.


Sai zuba minshari take.


Take yanda na ganta da mahfuz ya fadomin.

Jikina rawa yake hannuna damke da muciya.


Wani mugun bugu na Mata da muciyar  akanta  ta kwalla Kara a gigice ta mik'e zaune


Kallonta kawai nake Ina wani iirn hucci dama kece BUDURWAR MIJINA,?

girgiza min kai ta fara yi da sauri ta gwallo idonta tana kallona 


Tunda na gansu sai a yanzu hawaye ya zubomin "DAMA KECE BUDURWAR MIJINA KIKA ZO MIN HAR CIKIN GIDA DAN KI GANE MIN SIRRINA ?UMMI DAMA KECE BUDURWAR MIJINA KIKA BIYO MIJINA HAR GIDA,KARUWANCI HAR GIDAN AURENA UMMI"?


"AUNTY DAN ALLAH KI RUFAMIN ASIRI KI TSAYA NA MIKI BAYANI"


Wani irin ihu nasa kamar sabon kamu nayi kanta na hau hada kanta da bango na damke gashin dokinta da k'arfi Ina ja 


Ni nasan daga farko layi har zuwa kasan layi ana jiyo muryarta ban damu da jinin dake zuba a kanta ba Kamar wata doki sabida karfin da nake ji a jikina na cigaba hada kanta da bango Ina bugu.


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun lubna karki kashe yar mutane ki budemin k'ofar Nan naji muryar mahfuz da karfi"......

Dandandan akwai show a gaba akwai Abubuwan daya Kamata a warware Taya Hadeeza ta samu ta rinjayi Mahfuz ya kaita har gidansa?Taya akayi Abdul shima ya yarda ya Kai Hadeeza gidan Lubna?


Kallon da Mahfuz yake yawan cewa lubna zaiyi dama d'akin Hadeeza yake tafiya"?


Ya kuke ganin zata Kaya tana bude k'ofar?ko ta karfi ake shiga gidan?


Mahfuz na auren Hadeeza kuwa?


Hmmm kubiyo sadnaf ta Baku labari da dari biyar dinku kacal,

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post