Budurwar Mijina page 13-17

Budurwar Mijina page 13-17

Budurwar Mijina page 13-15

*BM*


*Page 13*Mummy  da mmn Iman ne Suka bini aguje suka rikeni ta baya.


Na saka ihu Ina "ku cikani na kashe shi dan Allah ku cikani"


Mummy ta sakeni ta dawo ta gabana ta kwasheni da mari tana hucci


"Dama haka kike Lubna Ashe bakida hankali kishi hauka ne"?


"Aikuwa ga kishi nan ya sakata hauka ta zama Yar dabba kila har shaye shaye tanayi dan idan ba shaye shaye tayi ba,ba yanda zata zo ta samu Yar mutane ta kulle ta ringa dirmar ta Kai dalla shashasha lusari zoka wuce ka d'auko Yar mutane mu kaita asibiti Kuma wlh a yanzu zaka saketa ka gama aurenta"


Ammi tacewa mahfuz daya tsaya a bakin k'ofa Yana zare Ido,shi kawai na zubawa Ido Ina kallonsa,kallonsa da nake ya Kara tunamin Abubuwan da yamin, kirjina Kamar an dora bullo sabida nauyin daya min da azabar tsanarsa rad'ad'in da hannuna yake yasa na d'auke kaina daga kallonsa na kalli tsakiyar hannuna dana Sha Jan kunshi da baki duk a san na burge namijin daya kawomin budurwarsa har gida ya daidaita ni da ita ko nace ya fifita ni akanta,tunda Abubuwan da ya mata ko rabinsa bai min ba, itama har kunshi ta masa ta Sha kitso,na tuna yanda ta fito da Yan dari bibiyu sak irin Wanda mahfuz yabani nata ma yafi nawa yawa tamin karyar a banki ta ciro take na sake tuna wasu Abubuwan da ya Kamata na nasan gaskiya lamarin,hakane yasa na m'ike Sam bajin ma Mai mummy da Ammi ke cewa ba


"Ina zakije"?


Naji muryar mahaifiyata a bayana duk sun dauka kila dakina zanyi naga alamar tsorona ma mmn Iman da mijinta suke ji,akwai mutane a tsakar gida,Ammi har lokacin bata fasa masifa ba tana "Bari na duba Yar mutane naga ko ta jawo Mana balai tunda wancan shashashan ya kasa zuwa"?


Ta shige bandakin ta rafka uban sallati kafin su ankara nima na shige dakin da gudu na fada bandakin a bakin k'ofa take hakane yasa na bangajeta dan da balain gudu na Shiga dan nasan mummy zata iya rikeni.


Flat tayi a kasa ta saki ihu na danna k'ofar na saka mukulli najiyo takunsu da ihu dan Ammi itama ihu ta saka tana "Shikenan ta hadamu waje  daya zata kashemu Mahfuz"


Ta hau kwallawa mahfuz kira ko kallonta banyi ba na tsugunna a gaban Hadeeza dake kwance da alama ta fara fita a hayyacinta jini sai fita yake akanta


"tashi zaune"


"Bazan iya tashi ba Aunty kimin rai wlh jiri nakeji kaina kamar baa jikina ba Aunty kin karya min hannu Hajiya ki taimaka min ku kaini asibiti Zan mutu tace wa Ammi, Ammi kuwa mahfuz kawai take ihun Kira tana yazo ya cecesu a haukace nake.

Ban kalleta ba nacewa Hadeeza


"Kin dauka Wasa nake Miki ko"?


"Aaa Aunty"


Ta fara k'ok'arin mik'ewa zaune tana cije baki Ammi kuwa ihu kawai take tana Mahfuz yazo ya bude kofar zan kashe su sai k'ok'arin balla k'ofar suke, mahfuz na sallati mummy kuwa kuka ta fashe dashi,mmn Iman ma Ina Jin kukanta"


"Damka na kaiwa hannunta da yafi kumbura ta saka ihu"


Nace "Kudin kunshi da kitson nan mahfuz ne ya baki ko"?


"Ee Aunty shi yabani wlh shi yabani dubu Ashirin"


Na cije lebbena


A ranar daya baki kin bashi kanki kenan"?


"Eee Aunty shekaran jiya ne a ranar ya fara sanina"


Murmushin takaici nayi dan Ammi sakin baki tayi tana kallonta na watsa Mata harara 

Na Kara kallon Hadeeza dake sallati tana juya Kai dan jinin sosai yake fita a jikinta nasan dole ma a kwantar da ita a asibiti


A gaban ta na ringa hada kayan da nake so nayi amfani dasu dan na farantawa mahfuz kila tama sha wasu bansani ba tunda tana shiga kitchen din Kai tsaye Kuma a Fridge yake take na tuna tsumin dana Sha Mai daci


"Ke Kika zuba min abu

 Mai daci a tsumina ko"?


Na Kara matse hannun ta saka ihu tana "eee Aunty shanyewa nayi na musanya Miki da abu Mai daci,na Sha zumar ma dayawa dan Allah Aunty ki cika min hannu zan mutu"


Zanso ta mutun a lokacin data ce ita ta shanye min tsumin dana kashewa kudi,nida siya ita da amfani dashi dan ta jiyar da mahfuz dadi anya na tab'a ganin Mai karfin halin Hadeeza kuwa,sai a yanzu na tuno yanda take hararata a fakaice,har da shigowa dakina duk dan taga ya dakina yake.


Yanzu da ace ta zubamin  guba a abinci naci fa dan duk Wanda zai iya abinda ta yi zata iya kisan Kai har da fasa min bokiti dan tagani da mahfuz.


Idan har shekaranjiya ya fara kwanciya da ita hakan na nufin jiya ma wankan tsarki yayi ya nemeta,yaji dadinta kenan ya koma mata na saki murmushi takaici hawaye masu zafi suka hau kwaranyo min


Banida nauyin bacci banida Jin bacci da wuri tunda tazo gidanan na fara bacci da wuri mai nauyin gaske har ta Kai idan mimi ta farka sai nayi dagaske nake iya bud'e idona


"Mai kuke min keda mahfuz nake bacci da wuri"?


Na matse hannunta da k'arfi 


Wlh magani yake samiki dan kiyi bacci da wuri har yazo dakina ya tafi hannuna zai fita na Shiga uku 


Maganarta ta dakeni,Ashe Mahfuz ne yake samin magani a exotic din da yake min tayinsa idan muna cin abinci Na runtse idona jikina da kirjina wani irin rawa yake 


Na  sakar Mata hannu a daidai lokacin da  sukayi nassarar balla k'ofar, Mummy ta shigo da sauri tana shigowa ta rufeni da duka 


Tana "Lubna ko dai dagaske shaye shaye kike kanki daya kuwa wanan wane irin azababben kishi ne daga mijinki ya kawo kanwar abokinsa gida sai ki nemi kasheta.


Ban bar zubar hawaye ba ina kallon mahaifiyata nace "Abinda yace miki kenan,Hadeeza ke kanwar abokin Mahfuz ce"?


Na jefawa Hadeeza tambaya da k'arfi ta bani amsa da sauri


"Aaa Aunty wlh ni budurwarsa ce"


Mahaifiyata wani irin dafe kirjinta tayi ta maimaita kalmar budurwa ban kalleta ba na fito daga bandakin mahfuz yayi sauri yayi baya,bana kaunar ganinsa a rayuwata na fito daga d'akin inajin mijin mmn Iman na "A gaskiya baka kyauta ba idan har hakane Mahfuz ya za'ayi ka kawo budurwar ka  har gida kaci mutuncin matarka wlh baka kyauta ba har gidan Aurenka fa mahfuz"


"Kanwar abokina ce Hamisu ba budurwata bace tsorata ta tayi shiyasa ta Fadi haka,zarginmu take na rasa Mai ya hau Kan lubna daga na fita massallaci na dawo ta kulle k'ofar zata kasheta ya fada cikin rawar murya


Naso na juya inda akwai tabarya a hannuna ko muciya na jefa masa sanin ba komai a hannuna mahaifiyata na biye dani yasa ban juya ba,Koda na fita palon jiki a sanyaye mahaifiyata ta biyo bayana mmn Iman kuwa sai jijjiga Mimi take tana kallona.


"Ammi ta fito tana dafe kwankwaso tana na karyata,har lokacin mahfuz bayani yakewa mijin mmn Iman dake ta Masa fada ce Masa yake yazo ya taimaka Masa ya Kai Hadeeza asibiti kar ta karasa mutuwa,mijin mmn Iman yace haram baa motarsa ba ya dauka mahfuz mutum ne mai hankali da sanin darajar Aure Ashe haka yake ya fito daga d'akin a fusace yacewa mmn Iman tazo su wuce su tafi ya kalleni cikin tausayawa Yana "Kiyi hakuri Lubna wlh bai kyauta ba bai kyauta ba koma waye dole ya dauki mataki yaci mutuncin Aure ya fita a fusace.


Sai a lokacin kukan da nake dannewa ya kufcemin na rufe fuskata na fara kuka mahaifiyata ta tsugunna a gabana itama idonta cike da kwalla mmn Iman itama ta tsugunna a gefena ta fara k'ok'arin rike hannuna dake ta zubar jini naga tsumma a hannunta kila so take ta dauremin itama sai hawaye take tana rike hannuna na fusge a fusace cikin kuka ina "kinsan komai mmn Iman,kinsan budurwar sa ya kawo min cikin gida Baki taba fadamin ba Kika sa na Zama shashasha na ringa hidima da ita,Mmn Iman idan nice bazan miki haka ba" 

Ban bari tayi magana ba na cigaba da rusa kuka itama kukan yaci karfinta dan har ga Allah taso ta fada mata a ranar da taga mahfuz ya tsaya nesa da gidan Hadeeza taje ta same shi ya dauketa suka tafi a ranar tsananin mamaki yasa ta kasa tabuka komai,anan ta Kara tabbatar da zargin da take akan Hadeeza ba dan Allah take zaune da lubna ba taso fada mata amma batasan ta hadata fada da mahfuz hakane yasa ta bata shawarar ta sakawa hadeezar ido ta daina sakar mata fuska.


Kasan makoshi mahaifiyata tace "Lubna bansan abinda ya faru ba kenan"


Na dago cikin ihun kuka na hau dukan kirjina Ina "Mummy har cikin gida ya kawo min budurwar sa yace min kanwar abokinsa ce wani abu tazo yi mummy na yarda dashi,ya kawo min budurwarsa har cikin gida nake bauta mata har daki nake Kai Mata abinci mummy abinci ma sai ta zabi Wanda take so zan girka mata mummy da zuciya daya,bai tab'a yimin shopping ba amma sabida zuwan budurwar sa gidanan yayo siyayya Mai yawa Ina murna nice har da Masa addua,sau tari inasan abu haka nake hakura duk a tunanina bashida kudi,bana ma iya tambayar sa komai mummy,iya k'ok'arina haka nake yi dan na kyautata Masa,wani zubin na samu canji da kudina nake siyan Naman Miya duk dan Miya tayi zaki yaji Dadi,ko yanka daya bana ci har sai ya dawo yaci san ransa kafin naci sauran mummy amma tunda ya kawo budurwa sa ya tsiri siyo nama balangu duk a tunanina budi ya samu,ya bani dubu biyar kudin kunshi da kitso ya bawa budurwarsa Dubu ashirin,mummy ya kawo budurwar sa gidana tazo ta gane min sirrina su ka maidani shashasha tunda tazo gidanan ya daina kwanciya da wuri,sai yacemin kallon ball zaiyi ya ringa sakamin magani a lemo duk dan nayi bacci da wuri ya tafi d'akin ta yaje ya kwanta da ita,duk hotel din garin nan bai gani ba,ya kawota gidana yasa na ringa hidima dasu mai na Masa dana cancanci haka daga wajensa mummy Mai na Masa"


Na Kara fashewa da kuka.


Naji muryar Ammi daga d'akin dan komawa d'akin tayi mahfuz ya kasa fitowa "kaje ka dauki yarinya nan ka kaita asibiti karta mutu fa kanta na ta zubar da jini dan ubanka na biku naga likita dan yarinya nan ta karyamin kwankwaso.


Ammi bari na Nemo abin hawa Kamar ta suma 


Duk Ina jinsu idona ma na kan k'ofar ya daga labule kad'an ya lek'o ya koma da sauri 

Ammi ta hankado shi waje  tana "dalla wuce muje ka Nemo abin hawa"

Bango ya fara bi Yana kallona cikin wani irin speed na daka tsalle na sha gabansa na cakumo kwalar jallabiyarsa cakuma bana wasa ba nace "Bani takardar sakina dan kutumar ubanka kafin ka Kai karuwarka asibiti tsinanne laanane Allah ya tsine maka albarka"


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Wai dama haka yarinya nan take dama Yar dabba ka aura wai"?


Ammi tace cikin masifa


Mummy tace "Yanzu abinda Zaki ce kenan Aseeya danki yayi wa yata irin wanan cin amanar bazaki Masa fada ba shine kike Kiran Lubna da Yar dabba"?


"Ina ganin ikon Allah fadan uban me zan Masa bayan urban dukan daya sha a hannunta har ni bata kyalle ba,ni ban yarda budurwarsa bace azaba ta sha shiyasa ta amsa laifin da ba nata ba dan Sam bata gane Hadeeza ba sabida kamaninta daya canja.


Hannuna a shake da wuyar mahfuz da hannu biyu Jin abinda Ammi tace yasa na kalleta cikin tsananin takaici Ina "Taya Zaki yarda budurwar sa ce bayan ta baki abin duniya kin Sha atamfa da mayafi da kudi,ta Ina Zaki yarda kin haifo asarare dan iska dan wuta,taya zaki taba yarda"


Lubna mahaifiyata kikewa magana haka"?


"Gutsun uwarka da ita nake ka sakeni"


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Mahfuz agaban idonka take zagina tana gayamin magana dama Kai dan iskane yanzu kyautar da yarinyar nan tazo tamin zuwa kayi ka fada Mata"


"Wlh aa Ammi bansan yanda akayi tasani ba"


"Allah ya Isa tsakanina da Kai mahfuz Allah ya tsine maka albarka


"Wlh ka gama da Yar iskar yarinya nan a yau zaka saketa na rantse da Allah"


Sake shi Lubna kinji"


Mummy tace na girgiza kaina na Kara rik'e rigarsa Ina "wlh tallahi sai ya bani takarda ta"


"Mahfuz bata takardarta yanzu Nan kafin na tsine maka"


"Ammi bazan iya sakinta ba wlh inasan ta sharrin shaidan ne bansan Mai ya hau kaina ba nayi Mata ba daidai ba ki tayani bata hakuri Ammi ta cikani Kar Hadeeza ta mutu"


A wanan gabar na hau Kai masa duka a kirjinsa da karfi Yana k'ok'arin rike hannuna Ina "wlh sai ka sakeni na gama Zama dakai mahfuz ko a lahira bana fatan na ga Mai iirn fuskarka"


Lubna dan Allah kiyi hakuri


Mummy   ta janyeni dak'yar daga gabansa Ina rsntsuwa sai ya tsinemin


"Wlh indai ni na tsugunna na haifeka  sai ka saketa a yau dinan ba iya duka abin nata ya tsaya ba har da cin mutuncina da zagi tace Ina da kwadayi ni da nake mahaifiyarka ka saketa kafin na maka Baki"


"Wlh bazan iya sakinta ba Ammi ni na Mata laifi wa kikeso ya kular min da mimi ko wata daya batayi ba taya Zan rabu da ita"?


Hakan dayace ne yasa nace "idan mu hadu a kotu ka bani takarda ta"


Nayi daki a fusace banida lokacin d'aukar komai iya hijabina kawai na sako mahfuz a gigice ya hau bani hakuri Ammi na dura Masa zagi mummy kuwa ta karbe Mimi daga hannun mmn Iman dake sharar kwalla hakan da nagani ne yasa nace "mummy bashi yarsa bazan shayar da ita ba ya kaiwa budurwsa ta shayar da ita Mimi jinin mahfuz ce banasan naga wani abu daya danganci mahfuz"


Gwallo ido Mummy tayi tana mimin Zan ajiye Masa yarki ce fa"


"Yarsa mummy kaddara tasa ta tsago jikina ta fito ki basa yarsa mu tafi""Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun lubna ki rufamin asiri karki min haka"


Mahfuz yace hankalinsa a balain tashe "Mama ki tayani bata hakuri mmn Iman ku tayani bata hakuri"


Tsaki nayi na fice duk da zuciyata kuka nake na rabuwa da yata da nake satar kallonta zuciyata a bushe take bana jin komai.


Ina jinsa Yana bina ban kallesa ba Ammi kuwa sai masifa take tana a bata mimi ai tana da nonon zata nemi mai bawa Mimi nono.......Duk wacce tamin sharing Allah Yana kallonta

Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗


Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku  zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali 

Ina masu pimples 

Tabo(spot)

Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance 

Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba 


Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki 


Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu


Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself

100%tested nd trusted 


Soap price:3k

Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free


Maiso kindly message 08062991549

Call 08064532391


Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market  b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏


Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝


Mg's skincare*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 ZUWA 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaida biya zuwa ga lambar  08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel   Kika min sharing idan bansanki ba bana ganinki Allah Yana kallonki na barki dashi*


*Bm*


       *Na Sadnaf*


*Page 15*


                 Bugu daya ya d'auka Yana "Kasan kuwa yanzu nake Shirin kiranka inata Kiran Lubna dan na hadata da Aisha su gaisa bata d'auka ba halan bata kusane"?


"Hmmm Abdul Ina cikin matsala"


"Subhanallahi wani abune ya faru"?


"Abdul idan na fada ma nasan zaka ji haushina amma.kasa kanka a matsayina ko kaina zaka iya kwafsawa"


Mahfuz kasa ma bashi labarin yayi ya cigaba da kame kame sai daya ga Abdul zai kashe wayar ya bashi labarin abinda ya faru ya Kara da "Bansan Mai ya hau kaina ba banyi tunani ba Sam,wlh Hadeeza kanainayeni tayi,na kasa yakice mata gashi yanzu lubna tayi fushi tunda nake da ita wlh ban taba ganin ta yi irin Wanan fushin ba"


"Allah ya Isa tsakanina da Kai Mahfuz baka kyauta min ba yanzu dama yarinya nan budurwa ka ce Taya zaka aikata irin wanan danyen aikin,daka tashi abinka hada dani, wlh Azeem da nasan budurwarka ce ko kallonka bazanyi ba yanzu wane kallo kake San lubna ta ringa min kasa kanka.a matsayin ta yanzu ta kawo maka Saurayi gida ka ringa.kuma hidima da saurayin zaka ji Dadi,ka cutar da ita,wlh ka zalinceta"


"Wai dan Allah Abdul ka barni naji da daya Mana yanzu na kiraka dan.na samu kwanciya hankali da mafita Kai Kuma sai Kara maganganu kake"


"Toh Mai kakeso nace maka a lokacin da zaka yi abinka kayi shawara dani, wlh Ina Jin labarai naka ya banbanta idan ma holewar zakayi da ita ka kaita hotel mana why zaka kaita gidanka tsakani da Allah kace bazan maka.magana ba yanzu ka jawomin bakin jini a gurinta kenan,yanzu zata dauka da hadin bakina aka kaita gidanka a gaskiya banji dadin abinda kamin ba 


Yace cikin tsananin b'acin rai kafin mahfuz yayi magana ya kashe wayarsa


Mahfuz yabi wayar da kallo,shi kansa Abdul din bai tab'a jinsa cikin bacin rai kamar haka ba,sake kiransa yayi,bai d'auka ba.


Haka yayi ta  Kira a karshe yaji ya kashe wayar.


Mahfuz haka ya rike wayarsa Yana tunanin mafita Abdul kadai yake tunanin zai iya rokon lubna ta sauko sai gashi yak'i sauraransa.


Ammi Kuma  yasan ko zai mutu ya dawo bazata saurare shi ba,karshe dai sai yayyensa sun Shiga maganar nan dole su zasu shige Masa gaba wajen shawo Kan lubna.


Zurfin da yayi a tunani yasa Sam bai san dare yayi ba sai muryar Ammi yaji a kansa tana "Wai uban me kake a daki tundazu baka koma asibitin ba"?


"Bana Jin dadi Ammi nima ban wuce a kwantar dani ba bazan iya komawa asibiti ba"


"Sabida ka rabu da Yar dabba Yar gwal ko"? shine zaka kwanta rashin lafiya,Kaine ka dauki yarinya Nan ka Kai gidanka matarka ta kusa kasheta badan Allah yasa tana da tsawon rayuwa ba,shine dan wulakanci zaka barta da shemau kawai a asibiti,idan ma dan ita lubna kake duk abinan toh kayi a banza dan ka gama Zama da ita dan yarinya nan Sam ba matuniyar arziki bace,Sam bansan tana da boyayyen Hali ba sai da abinan ya faru,har ni ta kalla ta zaga a gaban idonka ta ringa yiwa mutane hauka a gida,taya zaka dawo da ita ma Haram lubna ba matar da zaa zauna da ita bane"


"Ammi dan Allah dan annabi ya kike haka nifa na cutar da ita tsakani da Allah kema kinsani tunda Hadeeza ta dawo rayuwata ta kanainayeni ta hanani sukuni,bansan da manufa a ranta ba ashe so take ta tarwatsa min gida,Ammi Kamata yayi ki shige min gaba muje har gidansu mu basu hakuri bawai ki ringa ganin laifinta ba"


"Bakada hankali bazan tab'a taka kafata naje gidansu wata lubna ba Kai da kaga zaka iya da ita sai kaje tunda ka nace amma ka sa a ranka wlh tallahi sai ka Kara aure kurkusa ma kuwa bari yarinya nan ta warke"


"Wacce yarinya Ammi"?


"Wacce ka Kai gidanka Mana ko ka dauka ka samu abinda kakeso bazaka aureta ba,ai ka gama aurenta ka gama tunda har ka iya Kai ta gidan ka ta zauna kaga kuwa aurenta dole badani zaa cuci Yar mutane ba,wanan zalincin da lubna ta Mata ba abinda zaa saka Mata dashi sama da aurenta,dalla tashi kaje asibiti ka dubata."


"Bakin ciki ne ma ya hana shi ce Mata komai yaso ya kwana a gidan nasu,dan ji yayi Sam bazai iya kwanan gidansa ba lubna ba.


Amma da takurar Ammi gwara yaje gidan nasa ya kwana.


Koda ya bar gidansu gidansa ya nufa da isarsa d'akin lubna ya wuce,da wayarta ya fara cin Karo a side bed kafin ya bi koina da kallo Yana Jin inama mafarki yake ace duk abinda ya faru ba gaske bane yaso da wayarta ta tafi da yau bazai bacci ba text zai kwana Yana tura mata na ban hakuri,sai a yanzu ma yake dana sanin biyewa Hadeeza dan tunda ga lokacin daya Santa yaji kamar ba budurwa bace yaji zuciyarsa na Masa rawa akanta,ta Masa Abubuwan da dama daya sa yake zarginta  dan ko a ranar ma dayaje d'akin nata bada zumar wani abu ya Shiga tsakanin su ba yaje,yaje ne suyi hira su dan yi romance Kamar yanda ta fara sabar mai,sai dai Yana shiga yaga taci mahaukacin sleeping dress da babu marabarsa da tsirara a matsayinsa na namiji lafiyayye tuni yaji zuciyarsa ta harba ga wani irin fitinannen kamshin da take, gashi ya kwana biyu rabonsa da lubna hakane yasa Koda suka fara romance ya zarce Romance din ta Kuma bashi hadin kai dan kafin ma yayi wani abu da ita sai da ta kusa haukata shi dan da kanta ta zame wandonsa ta hau tandarsa Kamar ta samu alewa,Yana balain so ita Kuma lubna nada kyankyami ko zata Masa sai yaga tunda ranta bayaso shima ba wani Dadi zaiji ba,da hannu biyu ya damke bakinsa sabida Kar yayi ihu kasan zuciyarsa Kuma balain mamakinta yake taya.akayi ta iya ita da ba Aure ta tabayi ba ko aure kayi indai ba koya ma akayi ba taya ta kware haka,tuna wayayya ce kila bf ta kalla da wanan tunanin ya cire zargin ta a ransa har sai daya kusanceta Kuma yaji Kamar ba budurwa.bace dan lubna ya fara sani a rayuwarsa daga shi har ita ba karamar wahala Suka Sha ba,sai da lubna ta tafi wata uku ma kafin ta fara sabo dashi,Amma Hadeeza Kam Kamar kwararriya dan ta bashi hadin kai kwarai,dan gamsuwa Kuma ya gamsu dan kawai bayaso lubna ta tashi tazo ta Kama su.


Ya koma d'akin kamar bai komai ba.


Sai jiya da ya Kara komawa kafin su wayi gari yau da wanan tashin hankalin,Sam Hadeeza batazo masa da alheri ba,ba abinda yasa Hadeeza ta Kara fice Masa a rai sama da asirinsu duk da ta tona musu,har da alherin da tayiwa Ammi,yanzu lubna zatayi tunanin shi ya dauketa ya kaita gidansu Hadeeza ta Kara dagula Masa komai.


Juyi kawai ya ringayi ya rasa mai ke Masa dadi addua kawai yake Allah yasa Lubna ta sako da wuri.


Kowane gida ana shirye shiryen sallah gobe Banda shi da yake cikin tashin hankali da yanzu.Bacci rabi da rabi yayi washegari Koda ya fita.massallaci Suka hadu da Hamisu mijin mmn Iman bai wani sakar Masa fuska ba suna gaisawa ya wuce Kamar ba mutumin dake jansa da hira ba kila haka mutuncinsa ya zube a idon duk Wanda yasan ya kawo budurwar sa har gidansa.


Koda ya koma gida daga massallaci Kaya ya canza ya dauki wayar lubna yasa a  aljihunsa Yana so anjima kad'an yaje gidan yaga ko zai dace da ganinta.


Gidansu ya wuce acan ya hadu da yayyensa dan haka suke haduwa a gida su tafi sallah idi,daga nan su dawo suci tuwon sallah su Kuma bawa Ammi barka da Sallah dan idan har ka hanata haka zatayi ta mita tana bawa mutane labari wane bai bata barka da Sallah ba.


Yana k'ok'arin gaishe da Ya Ali da ya kasance shine baba sai Usman mai binsa sai Kuma Mahfuz.


Dukansu sunyi aure da matansu kannensu Mata uku suma sunyi Aure,Yar autarsu shemau kadai ce ta rage batayi Aure ba.


"Mahfuz ashe abinda ka aikata kenan kanka daya kuwa taya zaka dauki budurwarka ka kaita har gidanka"?


Mahfuz najin haka yasan Ammi ce ta fada musu,fada Suka rufe shi dashi Kamar zasu dake shi sai Ammi ce ta tsawatar musu tana "kuka san dalilin dayasa ya kaita gidansa ni abinda yasa na fada muku sabida kuji irin dibar albarkar da yarinya nan tayi mana idan haka ta kasance sau tari mace tagari rufawa mijinta asiri take,amma.yarinya nan haka ta Tara Mana jamaa  a yanzu nasan kowa yasan mai ya faru yarinya nan Sam ba matar rufin asiri bace sai kunga yanda ta canzawa yarinyar kamani"


"Haba Ammi ya zakice haka wlh duk Wanda akayi wa haka dole ya dau matakin da ta d'auka har gida fa ya Kai budurwarsa dan bashida mutunci ,a madadin ki Masa fada shine kike k'ok'arin fito da laifinta bansan Mai yasa bakya san laifin yayanki ba  yanzu da shemau ko Amina akayi wa haka wlh nasan kece gaba wajen cewa Baki yarda ba"


"Fito kawai fili ka dura min ashar Aliyu Kai dama ai bakada mutunci tunda kayi aure kunnuwaka Suka Kara fadi kamar na matarka,nama manta Kai waye na tsaya Ina fada muku na manta bazaku bi bayan dan uwanku ba ai bance muku yayi daidai ba abinda yayi Amma abinda ita lubnar tayi yayi yawa yanzu da auren sukayi da yarinya nan halan haka kishi zai saka ta zuba Mana hauka"?


Duk sun Riga da sun San halin Ammi dan yanzu nan ma sai laifiin Kuma ya koma Kan matansu da suka San hakuri suke da ita hakane yasa Suka ja bakinsu suka tsuke har ta gama ta fice kafin suma suyi waje gabad'aya dan su tafi massallaci mahfuz na dab da fita Ammi ta tsayar dashi tana "Ka tabbata daga massallaci ka jeka ka gano yar mutane idan an sallameta a yau ta dawo nan din ta zauna kafin Iyayenta su dawo"


"Aaa Ammi dan Allah idan an sallameta na bata kudin mota ta tafi wajen danginta ba dai a gidan nan ba yanzu dan Allah idan lubna taji labarin tana gidanmu wlh bazata ji dadi ba zan Kara jawowa kaina matsala ne a wajenta.


Mahfuz Anya haka.yarinyar nan ta barka kuwa"?


"Mun tafi massallaci Kar mu makara yafice daga gidan da sauri yabi bayan yayyensa.Suna fitowa daga massallaci,Mahfuz cikin kwantar da murya da biyyaya ya hau neman taimakon su ya Alin akan su shige Masa gaba wajen zuwa bawa lubna hakuri,Ya Ali tsaki yaja yayi tafiyarsa Yana ba inda zaije.


Sai Ya Usman ne yayi ta Masa fadan abinda yayi a karshe yace "yarinya nan daka Kai gidanka Sam Bata da tarbiyya karka soma aurenta domin ka aureta wlh sai kayi matukar nadama Taya mace zata biyo namiji har gidan aurensa wanan yarinya sam bata da kamun kai, idan ma so kake ka aureta ka gaggauta fasawa Ina laifin matarka yarinya Mai hankali dududu yaushe ma kayi auren dan masifa.


Sharrin shaidan ne Yaya tsaki Ya Usman din yayi Yana "Ka fara zuwa asibitin ka dubota karfe uku kazo ka sameni a gida sai mu tafi Allah ya kyauta"Mahfuz machine dinsa ya hau  ya nufi asibitin Ya Usman Kuma yaje ya hau motar ya Aliyu suka tafi.


Hadeeza.


    Bakin ciki kamar ya kasheta data ga mahfuz baizo ba,Koda ta ce shemau ta Kira mahfuz taji Yana Ina ce mata tayi ta kirasa bai d'auka ba.


Ko baccin bata koma ba har gari ya waye tunani kawai take Yana can kila ma Yana rarrashin Lubnar da ta kusa kasheta ko'ina na jikinta kuwa ciwo yake mata, idan kanin mahaifinta ya dawo sai dai tace Masa hatsari tayi,lubna bata daki banza ba insha Allahu sai ta rama dukan da ta Mata idan ta auri mahfuz sai ta fitar da ita daga gidan,cikin kirsa zata saka Mahfuz ya saketa,dan ta gano logon Mahfuz.


Wajen sha daya taga mahfuz ya shigo fuskarsa a daure.


Shemau na gaishe shi ta mik'e tana "Wlh dama na gaji Yaya ko sallah idi  yau bansamu zuwa ba bari naje gida"


Yana Jin idon Hadeeza daya balain kankancewa sabida kumburin da yayi a kansa,ko kallonta baiyi ba dan haushinta Yake ji bashida burin daya wuce ya yakice ta ta barshi ya sarara "Nima ai ba dadewa zanyi ba ai inaga ba wani matsala sallamarta kawai za'ayi yanzu dan na biya ta wajen likita yace ba wani matsala"


"Toh nidai na tafi Yaya sai kun fito"


Tayi waje da sauri sai a lokacin ya kalli ya Hadeeza da take zubar hawaye fuska a had'e yace "Ya jikin naki"?


"Mahfuz sai a yanzu zaka zo wajena"?tun jiya da kuka kawoni mahfuz baka Kara waiwayata ba, kaga yanda matarka ta min lahani kaga fuskata mahfuz duk halin nan da nake ciki matarka ce jefani a ciki amma shine baka zauna dani a asibiti ba sai a yanzu kazo"


"Kinsan halin da Kika jefani a ciki ko Hadeeza kin zubar min da mutunci Hadeeza wanan wane irin rashin hankaline   taya zaki saki baki  ki fadawa lubna komai har dasu Ina zuba mata magani a lemo dan nazo dakinki Kika ce mata kin bawa Ammi atamfa wane irin rashin hankaline wanan"?


"Mahfuz mutuwa na gani Kai yanzu damuwarka abinda na fada ba lafiya ta ba haba mahfuz matarka kiris ya rage ta kasheni da ban fada mata ba ba abinda zai hana ta kasheni fada ya Kamata kazo kana min Ina cikin wanan halin tsakani da Allah Mahfuz"


"Komai zata miki bai Kamata ki fada mata komai ba kinzo kinsani nayi Abu mutuncina ya zube lubna tayi fushi ta koma gidansu,kin jefani cikin tashin hankali Hadeeza nifa Ina kaunar matata bance Miki bana Santa ba,badan kin dawo rayuwata ba ni ta isheni rayuwa bana bukatar wani Karin Aure Kuma na fada Miki"


"A yanzu Kuma fa"?

Tace tana zubar da hawaye


Mahfuz ya d'auke kansa Yana Hadeeza bari na karbo takardar sallamarki idan an sallameki sai na raka ki tasha na biya Miki kudin mota zan nemeki idan komai ya daidaita"


"Taya zanje gida a haka bayan na fada maka ba kowa,can gombe ma ba kowa sai dai naje gidanku"


"Hadeeza baza kije gidanmu ba wanan wane irin masifa ne Taya zakije gidanmu da wane Ido kikeso dangina su kalleki a kin gama zuwa gidan aurena kin zauna kin zauna Kuma a gidanmu Zan aureki,sai kace a kudu,a kudu nasan ake haka,mace zata je ta zauna a gidansu saurayi,wannan ba al'adar bahaushe bane Sam,dan haka bazaki zauna a gidanmu ba gidanku Zaki tafi"


Yayi waje a fusace Hadeeza tabi shi da kallo baki a sake,sam bata tab'a tunanin zai Mata haka ba,lailai idan batayi dagaske ba Mahfuz bazai aureta ba,da alama duk Haushin tona musu asiri da tayi yake ji anya Haka  lubna ta barsa ba asirice shi tayi ba.


Mintuna da fitarsa sai gashi ya dawo da likita.


Likitan ya duduba ta ya tambayeta inda ke Mata ciwo ta fada Masa kanta ne har yanzu yake balain ciwo.

Yayi rubuce rubuce a takarda ya bawa mahfuz akan a siya Mata magunguna Yana karba yace tazo su wuce su tafi


A wajen tashin haka tayi ta cicije lebbe tana faduwa da gangan taga ko zai taimaka Mata amma ko kallonta baiyi ba har ta saka takalminta  ta fara tafiya a hankali tana binsa a baya.


Ta d'auka gidansa zai kaita ta kwaso kayanta tana so taje taga ko Lubnar na nan, sai dai suna zuwa ya tsayar da abin hawa akan ya kaita gidansu zai aiko Mata da kayanta yaki bari ma ya kalleta ganin Yana k'ok'arin tafiya yasa ta ruko hannunsa tana "Ya zancen Aurenmu mahfuz"?


"Allah ya Mana zabin daya fi alheri"


Yace tare da fusge hannunsa daga nata......Kuringa hakuri dani wajen posting din Daren da nake a lokacin nake da time 


Don't share my novels plc

Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗

Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm 

Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉

Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅

Mg's will gv you the best out of all 

With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃

We have herbal whitening black soap now nd beauty set available

Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗

Just gv it a try now nd see wonders✅

Chat:08062991549

07046881166

Call:08064532391

Soap price:3k

 set:11k


Follow us on 

Instagram@glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare


what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️

Pamper ur skin🦵

Shine like a bride 👰

 be part of the glow team karkubari abaku lbr

Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆

Like nd comment pls dearies😘

Patronize us🙏

mg's always serve you the best✅❤️


*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min sharing idan bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi**Bm*


     *Na Sadnaf*


*Page 16*Hadeeza ji tayi wani zazzabi na Neman rufeta dama da zazzabin ma, matsawar mahfuz bai aureta ba taga ta kanta dan shi kadai ne option dinta yanzu bata da  wani na aure dukan samarinta Yan bariki ne, lubna kuwa Dole ne ma ta rama abinda ta mata ko yan dabba sai ta haya sun rama mata.


Sai da taje gidansu ta tuna mukullin na cikin akwatinta wayarta ma na gidan,sai makota ta Shiga dan ta Kira mahfuz ta gaya masa ya kawo Mata akwatinta da mukullinta a ciki da ace tasan Lubna zata mata irin wanan dukan da bata soma zuwa gidan ba,bata san Mai ya hana ta rama dukan da ta mata ba har ta bari ta Mata irin wanan dukan,Koda ta Shiga gidan makotan mamn khairat sallati tayi ta sanar da ubangiji tana tambayarta hatsari tayi, gyada Mata Kai kawai tayi akan hatsarin tayi dan shine karyar kawai da zatayi,dan ba mai yarda dukan ta Sha haka a wajen siririya da bata kai.ta kauri ba,wayar mmn khairat ta karba ta saka lambar mahfuz sai da ta Masa miscal uku kafin ya d'auka Yana Jin muryarta ya kashe wayar,take ta sake kiransa amma haka yayi ta ringing bai dauka ba sai text ta masa akan kayanta da mukuli.


Bata san Mai yasa mahfuz yake neman wulakanta ta ba,bayan uban dukan da ta sha awajen lubna a yanzu ya Kamata yafi kula da ita ya turo kudin aurenta gidansu,sai gashi  a madadin kulawar nema yake ya juya Mata baya,haka ta rike wayar tana tunanin zai Kira,bayan minti goma sai ga sallamar almajiri da akwatin ta tayi sauri ta mik'e ta leka waje ko zata ganshi dan tasan dole shine ya kawo Mata kayanta.


Sai dai babu shi babu dalilinsa jiki a sanyaye ta ja akwatin ta bayan ta bawa mmn khairat wayarta ta bude gidansu ta shige dole ta zauna a gidan ita kadai har sai sun dawo daga aikin Hajjin.Mahfuz 


Ji yayi Kamar ya rabu da K'aya a lokacin da Hadeeza ta ta tafi,a lokacin da ta kirashi dama Yana gida sabida ya kwashe kayanta ya Kai Mata sai gashi ta kirashi duk abinan da ya faru gani yake ita ta jawo Masa,balain haushinta Yake ji,duk kayanta ya tattara mata nesa da gidan ya tsaya ya samu almajiri ya bashi akan ya Kai  gidan dake jikin gidansu dan  yasan Dole tana can, bashida burin daya wuce ya samu  ya shawo Kan lubna,indai Lubnar daya sani ne yasan wuyanta su keb'e ya marairaice Mata,da kwarin gwiwarsa ya Kara wanka ya saka sabon kayan daya dinka na sallah,ya nufi gidan ya Usman ya riga da yasan Mai ya kawo shi hakane yasa basu wani b'ata lokaci ba suka nufi gidansu Lubna,a k'ofar gida Suka tarar da zainab na zance kanwar lubna,bata ko kalli mahfuz ba iya ya Usman din ta gaisar yace mata ta musu iso wajen mahaifiyar su Suka zo dan mahaifinsu ya dade da rasuwa,kuma bata sake aure ba.


Mahfuz kuwa ganinsa a k'ofar gidansu lubna Kuma sai duk yaji hankalinsa ya tashi dan baisan Mai zai tarar ba.


Gabansa ne ya hau faduwa a lokacin da suka shiga gidan har palon mahaifiyar lubna da aka fi Kira da Aunty nurse ita  kadai  suka samu a palon da alama da baki a gidan sabida ranar take sallah suna Kuma jiyo hirar mutane a dakunan palon.


Mahfuz sai wurga Ido yake yaga ko zai ga lubna daga yanda Aunty nurse ta amsa gaisuwar shi sai yaji jikinsa ya Kara sanyi ya sunkuyar da kansa Yana Jan ya Usman na mata bayanin basu dadin abinda ya faru ba,ya  hau bada hakuri yana a dubi zuriar dake tsakani.


Aunty nurse bata katse shi ba har ya gama kafin itama tayi gyaran murya tana "Abinda Mahfuz yayi  ya munana,ba uwar da zaa yiwa yarta haka bata ji zafin abinda aka mata ba,kafin ya Kai budurwarsa gidan ta sha dan min korafin wayar da yake yi da budurwa a cikin gidanta,har barota yake yi a daki ya fita dan kawai yaji muryar budurwarsa wlh idan ta fadamin hakuri nake bata, tana ta Kai zuciyarta nesa,a iya sanina  basu wani Dade da Aure ba da har ta cancanci haka daga wajensa iya nan bai ishe shi ba sai gashi ya dauko budurwar ya kawota har cikin gidansa ya zuba karyar Yar uwar abokinsa ce tsakani da Allah yayiwa yarinya nan adalci duk macen da mijinta zai iya Mata haka wlh ba kaunarta yake ba,dan haka a ganina kuyi hakuri yaje ya auri wancan din dan yafi kaunarta,ita Kuma Lubna Allah ya mata zabin daya fi alheri"


Mahfuz nasan baiyi daidai ba,abinda yayi ba abinda zaa yi saurin mantawa bane ko a yafe,amma idan kuka tuna Allah ma muna mishi laifi ya yafe Mana Ina ga mu Yan Adam,dan Allah dan annabi kuyi hakuri"


Mahfuz baki ya sa ya hau bada hakuri shima 


Aunty nurse ajiyar zuciya ta sauke tana "ba fa nice lubna ba idan lubna taga zata koma bazan hanata ba dan haka bari na turo muku ita"


Ta mik'e ta bar palon ta shige daya daga dakunan dake cikin palon.Lubna 


       Nayi kukan fili nayi na zuciya har na gaji,nasan daga jiya zuwa yau sai da jinina ya hau, duk abinda ya faru dawo min yake kawai a kaina daga lokacin da Hadeeza ta taka kafarta zuwa gidana har jiya da ya kasance min bak'ar Rana, mahfuz yaci mutuncina ya wulakanta ni da yanzu asirinsu bai tonu ba har ta samu ta tafi,da ahaka Zan saki baki ya aurota bayan ta gama sanin komai nawa sai a yanzu na tsani halina na saurin sabo da mutum Koda a ranar na fara haduwa da mutum,Banda mmn Iman ta kwabeni da komai nawa Zan kwasa na fadawa Hadeeza,Ina Jin Haushin mamn Iman har a cikin zuciyata da ace ta fadamin tun wuri da Hadeeza bata Dade a gidanan haka ba,tsabar munafirci mahfuz ko kallonta baya yi Ina murna ba ruwansa ashe yaudarata suke har abin ya Kai ya sakamin magani a lemo,a yanda nakejin zuciyata bana Jin akwai Wanda na tsana kamar mahfuz domin ya ci amanata,Ina matarsa ya hadani da dubu biyar ya bawa budurwarsa Dubu ashirin,wlh ko zaa na rantse min mahfuz zai iya kusanta kansa ga zina karyatawa zanyi,sai gashi a cikin gidana yaje ya kwanta da Hadeeza Ina can dakina ya bugar dani Ina bacci.


Mummy gajiya tayi da rarrashina ta hau ni da fada akan Kar naja wa kaina wani matsalar akan abinda ya riga da ya faru ya Kuma wuce dan kuka da saka damuwa a zuciya bashi zai canza komai ba.


Hakane yasa na koma kukan zuci,da ciwo Wanda ka aminta dashi ka bashi Amana ya maka irin Wanan cin amanar.


Shigowar Mummy data zauna a gefena da Sam bansan da shigowar ta ba sai da ta zauna a gefena na dawo daga tunanin dana tafi.


Ido ta zubamin har sai da na sunkuyar da kaina 

"Haba Lubna wai bazaki sasautawa kanki bane Kinga yanda Kika rame daga jiya zuwa yau haba dan Allah dan annabi so kike ki mutu da bakin ciki  ko abinda ya faru ya Riga da ya faru ba abinda zai iya canza hakan nasan da ciwo amma haka zakiyi hakuri ki fuskanci kuma gaba Aure gabad'ayansa dan hakuri ne,duk wata macen da Zaki gani a gidan mijinta da nata kalar jarrabawa da take fuskanta ke naki jarrabawar kenan,dan haka kiyi addua Allah ya baki ikon cinye wanan jarrabawa"


Jinta kawai nake dan gani nake ba Wanda ya Kai nawa zafi 


"Kije Palo yayan mahfuz na kiranki""Mummy wlh bazan koma wa mahfuz ba na gama Zama dashi idan ma hakuri yazo bani gwara kar ya wahalar da kansa dan na Gama auren mahfuz yaje can ya karata da Hadeeza data fiye Masa ni ya Aiko min da takadar da ta cikin ruwan sanyi idan ba haka ba wlh hisba Zan Kai shi Kuma na Kai shi Kara kowa sai yasan mai ya aikata"


"Ki tashi ki saka hijabinki duk sai ki fada masa nidai bazan miki dole ba amma inaso kisan indan Zama bai Kare a tsakanin ku ba haka Zaki hakura ki koma ana abinda yafi wanan ma a koma a cigaba da Zama"


Zuciyata tafasa take har nasa ka hijabina bana san ganin Wanda ya danganci mahfuz amma gwara naje idan Yana tunanin dan ya turo yayansa zan hakura toh yayi a banza ba abinda zai taba mayar dani gidansa.Sai dai ga mamakina Ina fita naga ashe har da mahfuz yazo,hada idon da mukayi dashi yasa na watsa mishi wani mugun kallo Ina Munafiki kawai ni nasan yajini haka ma yayansa da isana wajensu na samu waje na zauna banso ma gaida yayansa ba amma sam sai naji bazan iya k'in  gaishe shi ba,


Ciki ciki na gaida shi ya amsa da murmushi a fuskar sa Mahfuz kuwa yayi rau rau da fuska Kamar zaiyi kuka 


"Lubna kiyi hakuri Mahfuz bai kyauta ba duk Wanda aka bashi hakuri ansan an cutar dashi,ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki yafe Masa wlh yayi nadama ya Kuma gane kuransa ko dan yarinyar dake tsakanin ku kiyi hakuri ba Wanda baya kuskure tunda baki tab'a kamashi da irin wanan laifin ba insha Allahu wanan shine Karo na farko Kuma shine na karshe da Zaki Kama shi da laifi irin wanan"A dake na dago na fara magana ba tare da naji wani nauyinsa ba 


"Ya Usman wlh ko mahfuz shine autan maza na gama aurensa bazan tab'a komawa gidansa ba inaga karyar da ya Saba yi mutane ya ma shiyasa baka san ainihin abinda ya faru ba bari na baka labarin abinda ya aikata kasa kanka a matsayin yayana idan kanwarka ce ni wane mataki zaka ce na d'auka.


Tiryan tiryan na kwashe komai na fada masa game da duk abinda Hadeeza ta fada min har yanda ta shawo kansa kafin ya kawota gidan da duk abinda sukayi na zayyane masa


"Idan har Mahfuz zai min haka ya zuba min magani a lemo na Sha dan yaje d'akin budurwarsa karshen cin mutunci yamin wlh Mai kaunarka bazai tab'a maka haka ba tsananin Santa da yake yasa ya kawota gidansa dan ya ringa ganinta bama zai iya Hakuri har sai an daura musu aure ba taya zan komawa Mahfuz da idona nagansa kwance a jikin ta da wane idon zai kalleni na kalleshi har ya samu matsayi a zuciyata da Sunan mijina wane irin Zama zanyi dashi, mutuncinsa ya Riga da ya zube a idona,bazan tab'a girmama shi har na iya Masa biyayyan Aure ba har yaji dadin Zama dani dan haka yaje ya auri hadeezar sa ya kawomin takarda sakina idan na yaye mimi yazo ya d'auketa"


Daga yanda Ya Usman ya kasa motsi nasan ya rasa Mai zai cemin ne hakane yasa na fara k'ok'arin mik'ewa mahfuz yayi sauri ya Sha gabana ya zube akan gwiwar sa idonsa ya Kada yayi jajjur kiriss yake jira ya saka kuka"Lubna dan Allah badan halina ba kiyi hakuri,wlh tallahi sharrin shaidan ne kema kinsan Ina balain kaunarki wlh na hadu da shaidaniyar mace ne,banyi niyyar kaita gida ba wlh Allah haka ta dagemin har ta shawo kaina"


Bayan ta maka kiss kaji tudun kirjinta a bayanka sabida kwarto ne Kai dole ta shawo kanka nifa Mahfuz da kasan irin tsanar da na maka wlh Tallahi da baka tsaya a gabana da Sunan bani hakuri ba idan har baka San tonan asirinka ka aikomin da takardata ko ka bani yanzu idan ba haka ba wlh tallahi hisba Zan Kai ka Kuma kasan naje can dole na fada musu abinda kamin dayasa nake neman takardar saki,wlh bama kada kunya mahfuz,har gidanku ka Kai Hadeeza da baka Santa zaka kaita gidanku dan ta gaida Ammi ne,duk siyayyan nan da ka ringayi Ashe duk sabida ita ne Allah ya Isa tsakanina da Kai mahfuz ka rubutamin takarda sakina idan ba Haka ba wlh jibin nan Zan Kai ka hisba suma Dole ka bani takarda ta domin bazan Kara Zama da mazinaci ba"


Na fara k'ok'arin kewaye shi na wuce dan yayansa har ya fice daga palon 


Mahfuz ya rike kafata gam dan duk abinan da ake Yana tsugunne akan gwiwarsa


"Wlh bani na Kai Hadeeza gidanmu ba,ita ta Kai kanta ki yarda dani,Wlh wasu Abubuwan da ta fada Miki karyane so take ta rabamu lubna ki dubi soyayyar dake tsakanina dake ki yafemin"


Ba abinda nake sai k'ok'arin fusge kafata amma ya rik'e gam har sai da na hada Masa da duka Ina ya sakeni.


Karar bugun da nake Masa ne ya fito da mummy daga d'aki da sauri tayo wajena tana ke Mai haka ka cika ta mahfuz.


Sai a lokacin ya cika ni na kewaye shi na shige dakinmu ya hau rokon mummy akan ta bani hakuri yayi nadamar abinda yayi na Masa kowane irin hukuncine,mummy ce masa tayi yaje gida zata min magana godiya ha hau yi Mata yace mata Yana San ganin Mimi,Mummy tace Masa bacci take.


Ina Jin Yana Mata sallama akan zai dawo daddare,mummy tace ba sai yazo ba ya bari a kwana biyu har yanzu Ina Kan zuciya ne.


Koda na Shiga d'akin Ina Kara tuna abinda mahfuz yamin ne ina Kara Jin zafi a zuciyata.


Mummy kuwa data shigo rarrashina ta hau yi tana nayi hakuri,mijina na sona kila ma asiri Hadeeza ta Masa baa hayyacinsa ya kaita gida ba"


Murmushin takaici nayi dan nasan an Sha rainawa Mata wayo da Sunan asiri aka yiwa mazajensu bayan karyane ba wani asiri zalar iskanci ne ko asirine ma asiri na tada hali.


Wayata ta mikomin akan shi ya kawomin


Na kuwa karba nayi blocking lambarsa.


Miscall din Abdul nagani rututu har dasu text Koda na bud'e text dinsa hakuri yaringa bani da rantsuwar baisan abinda Mahfuz yayi ba kenan da bai kawota ba.


Ban Masa reply ba dan ba amfanin hakan ban Kuma wani ji haushinsa ba dan ada na dauka da hadin bakinsa amma tunda ga lokacin da nasan ba ruwansa naji ban rik'e sa a raina ba.Har a raina so nake bayan sallah idan har Mahfuz bai kawomin takarda ta ba hisba Zan Kai sa.


Wasa Wasa sai gashi kullum mahfuz sai yazo gidanmu duk da bana fita,haka ya ringa kawomin mutane iri iri akan su bani hakuri ciki kuwa har da mijin mmn Iman da yace mahfuz Yana neman zarewa na yafe Masa yayi nadama.


Sam bana Jin mahfuz a Raina dan Mummy ma yanzu tausayinsa takeji,ita ta ringa hanani zuwa hisba.


Daidai da zainab kanwata sai da ta fara tausayinsa amma niko Ina nan Ina Jin haushinsa har yanzu Ina kwanta bacci Ina tuno yanda na gansa da Hadeeza.


A irin wanan lokacin Ina da wata daya da sati daya a gida Abdul yazo bayan dogon nasihar da yamin da waazi da roko akan na komawa Mahfuz na dage Masa na gama auren mahfuz,dan ko na koma wlh bazai ji dadin Zama dani ba dan mutuncinsa ya zube a idona na har abada ba Kuma na jinsa a zuciyata balle har na iya kyautata Masa.


A takaice dak'yar da nasiha da rarrashi dan mahaifiyata da ta sakoni agaba da mmn Iman na yarda Zan koma baa san Raina ba Ina jimanta irin zaman da zamuyi da mahfuz da ko kad'an bana kaunarsa, indai Zan gansa sai na tuna abinda yamin zuciyata tayi ciwon abinda yamin,sabida na bashi wahala nace Masa bazan zauna a gidanmu ba dan indai Zan kalli d'akin da Hadeeza ta zauna sai na tuna ta.


Take ya nemo gidan haya ya Kama mana sai rawar jiki yake yabi ya rame Kamar bashi ba,bana ma jinsa a Raina nasan bazaiji dadin Zama dani ba,dan.bazan tab'a yarda ya kusanceni ba dan bazai zo ya shafamin cuta ba......
Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post