ZAMANTAKEWA: Wasu halayen Mata guda 15 da Maza suka fi tsana

ZAMANTAKEWA: Wasu halayen Mata guda 15 da Maza suka fi tsana

Wasu halayen Mata guda 15 da Maza suka fi tsana

Daga Taskar Fatima Zamsarf Katsina

Ko da bai damu da dole sai tayi ba. amma tasirin akan ganshi cikin zaman su ne

1.Mace mai son kanta da yawa: Itace wacce bata duba maslahar kowa a gida sai tata, sai anyi da kyar take iya sauya ra'ayi saboda yaranta, irin wannan matan sune wa'yannan basa damuwa da samu ko rashi a cikin bukatunsu, kawai kowane lokaci sukace kaza to ayi musu

2. Macen da bata iya godiya ba. Itace wacce ko duniya mijinta ya kawo mata baza tace ta fode ba, ya dawo daga aiki, ya siyo cefane amma ko Allah ya kara budi baza tace ba bare yasa ran zatayi godiya da yanda yake kokarin sauke hakkokinsu.

3.Macen da bata da tsafta. Gidanta martabarsa da bola ( shara) kadan ne, itace wacce mijinta bayada damar zama kusa da ita saboda warin rashin tsafta, shine zaya kawo cefane amma saidai yaje waje yaci abinci, irin wa'yannan matan ko yaransu basu damu da su gyara ba, to bata gyara kanta ba Ina maganar gyara wani. Sune majority na maza ke hakura da aurensu, ko kuma su karo musu abokiyar zama.

4. Macen da bata wa miji labari ko magana mai dadi sai idan gaban abokan sa ne. Irin wannan sune wa'yanda idan abokan miji suka zo kamar wurinsu suka zo, zata iya kai 4 na yamma bata gama girkin rana ba, amma idan yace mata wane zaya zo tun 12 zata kammala, idan yazo kuwa tafi mijin zakewa a labari. Idan har yaga farin cikin ta da walwala to tare yake da abokansa. Irin wa'yannan matan sune suke saukin kashewa kansu aure, saboda ga wanda ya ijeki a gida ke kuma ga wanda kikewa hidima.

5.Macen da bata tausayawa miji/mai yawan bani-bani. Bata da wani fata illa taji tana tambayar mijinta kudi ko tana fada masa babu kaza babu kaza. Bata tausaya masa ko kadan duk karancin bukata koda zata iya yinta ba sai ta tambaya ba ( misali kamar siyen gishiri ko ashana), to tana kyashin tayi din tadaifi gane ta loda masa ayyuka.

6.Macen da bata san mutuncin kanta ba bare na mijin. Irinsu ne wa'yannan ko Ina wurin magana ne a gunsu, ko ina wurin washe Baki ayi magana ko dariya ne, batada kamun kai, batasan mutuncin kanta ba bare ta kare mutuncin mijinta. Da yawansu mazajensu basa son shiga dasu taro saboda bayar da kunya suke.

7.Mace mai banbanta tsakanin danginta da naka. Idan ka siyo atamfar dubu biyar kace ta kaiwa mamanta zata ji dadi sosai, amma idan ka siya ta dubu hudu zaka kaiwa mamanka saita bata rai ko ta nuna cewan yayi tsada, ko dai ta kawo wani abu da zata numa ita fah nata kadai takeso kayiwa. Idan yan uwanta suka zo fara'a da sakin fuska kamar tana gidansu, amma idan nake ne sai idan taga ka bata rai sannan ta fito ta zauna cikin su.

8.Macen da bata iya bada hakuri ba. Idan zatayi laifin duniyar nan to girman kai bazaya bari ta baka hakuri ba, koda taga ka kai karshe a fushi da bacin rai, ita bazata ji cewan ya kamata na bada hakurin abinda nayi ba. Irin su kowane lokaci gani suke su akayiwa laifi koda su sukayi laifin kuwa.

9.Macen da bata iya tafiyar da miji ba. Wacce idan yana cikin damuwa zata iya karantarsa ba tare daya fada ba, wacce idan yana bukatar kasancewa shi kadai take girmama ra'ayinsa, wacce tasan lokacin da yake bukatar wasa da dariya, da sanda ya kamata a tattaunawa matsalolin cikin gida ko na yara ba. Ita ce wacce duk motsin mijinta akan idonta yake, takan gane ta fahinci hatta kallonsa zata fahinci abinda yake nufi. Macen da ta kasa fahintar mijinta irin haka, wahalan zama ne da ita, saboda ita komi sai ya fada mata sannan ta gane.

10.Mace almubazzara. Itace wacce idan tasan taliya daya ta ishesu a gida, saita dafa daya da rabi, Maggie a miya saita saka yayi yawa, idan ta lalace a zubar, itace wacce hatta sabulun wanka ko na wanki sai mijin ya rika kula dasu idan ba haka ba komi kafin wata ya kare. Batada tattali, komi na gidanta abin banzatarwa ne. Da yawan mata masu wannan halin suke talauta mazajensu idan baiyi hankali ba. Basuda dadin zama saboda sukan saka kayi aiki biyu ne, ka fita ka nemo kuma ka dawo ka kula da abinda ka kawo a gida.

11.Mace mai saurin fushi. Da yawansu basu san wasa ba, ba damar yadan ja ta ayi raha saita hade rai, suma irin su wahalar sha'ani garesu.

12.Mace mara kwalliya da gayu. Wacce idan kaga kwalliyar ta to waje zata, amma a gida ita da mahaukaciyar anguwarku banbancinsu kadan ne, idan ka siya mata duniya dan tayi ado bazaka ganshi ba sai idan kace zaku fita.

13 Mace mai dagawa miji murya. Itace tayi laifin amma idan kaji tana bala'i saika dauka almajirinta ne takewa fada, irinsu basuda kara ko gaban waye masifa zasuyi maka, sannan ba suda bako danginka ko nata kowa ya taba ta sai ya jita. Suma irinsu shakkar fita dasu miji keyi.

14.Macen da bata iya girki ba. Idan ka kawo shinkafa ka ije, to insha Allah har watan ya kare kuna cin shinkafa da miya, da mai da yaji, da kuma dafa duka, su kadai ta iya ai, wacce ko indomie ta dafa sai ya cabe, bata iya komi ba.

15.Mace jahila. Idan har Namiji yasan kansa, to ko saboda yaransa zaya nemi mai ilimi da tarbiyya, wacce ko bata zurfafa ba to tana aiki da wanda take dashi, kuma tana kiyaye dokokin Allah dai-dai gwargwado. Hakama tarbiyyar yaranta. 


Suma wa'yannan abubuwa ne da yawan gaske, idan akace za'a fadesu duka lallai za ayita read more ne, Fatanmu dai dan karanbanin da mukayi adan anfana dashi, samun sauyi a al'umma shine gurinmu, fatan Allah ya anfanar damu gaba daya.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post