ASUU: Dalibai su gaggauta komawa ajin karatu ranar Litinin, 26 ga Satumba

ASUU: Dalibai su gaggauta komawa ajin karatu ranar Litinin, 26 ga Satumba

ASUU: Dalibai su gaggauta komawa ajin karatu ranar Litinin, 26 ga Satumba

Dalibai su gaggauta komawa ajin karatu ranar Litinin, 26 ga Satumba – Hukumar jami'a sun yi watsi da yajin aikin ASUU

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, ta umurci kafatanin dalibai na kowane fanni da su koma makaranta don ci gaba da daukar karatu ranar Litinin 26 ga watan Satumba.


Hukumar ta bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da magatakardar Jami’ar, Malam Bala Ahmed ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.


Mista Ahmed ya ce matakin ci gaban tare da komawa ajin karatu wani bangare ne na kudurin taron gudanarwa na musamman da aka gudanar a ranar Juma’a.


Sanarwar ta kara da cewa: “Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi, a taronta na musamman da aka gudanar a ranar Juma’a, 23 ga Satumba, 2022, ta sanar da bude jami’ar a ranar Juma’a, inda za a fara karatu ranar 26 ga Satumba, 2022.


Dangane da kalandar ilimi da ke makale da sanarwar, rajistar semester ta biyu za ta fara ne a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, yayin da za a fara laccoci a ranar 3 ga Oktoba, 2022.


Saidai a bangare guda, da yake mayar da martani, shugaban jami’ar na kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, Samuel Alu, ya ce ba a dakatar da yajin aikin ba, kuma malaman ba za su koma ba.


Sai dai ya bayyana cewa majalisar ta yanke shawarar neman a janye daga hedkwatar kungiyar ta kasa don dakatar da yajin aikin na tsawon watanni bakwai saboda jajircewar da gwamnatin jihar ta yi da kuma tsoma bakin masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da majalisar dokokin jihar da sarakunan gargajiya.


“Mun yaba da kokarin gwamnan jihar da yadda ‘yan majalisar dokoki da sarakunan gargajiya suka shiga tsakani, amma wannan yajin aiki ne na kasa baki daya. Ba za mu iya dakatar da shi hakanan kawai ba.


“Amma mun yi taron Majalisarmu a yau, kuma na gabatar da bukatar masu ruwa da tsaki daban-daban ga majalisar, amma suka ki.


“Duk da haka, mun yanke shawarar rubutawa hedkwatar kasa da neman a janye yajin aikin. Mista Alu ya jaddada.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post