Feenart Hausa Novel Page 4 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 4 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 4 | Novels Elite

Kokarin azawa akan tafarki, shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            FEENART

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

By

 Nusaiba Alkamawa

 Proficient Writers Association

🅿️4️⃣

Da mamaki naseeb ya kalleshi,wannan wane irin yayane da baya damuwa da lamarin yan uwanshi ,,,shi yanxuma har tsoro yake bashi, yafada acikin xuciyarshi ,Amman afili sai yace ameen ,tareda mikewa yafito domin yayan nashi yabata masa rai ,,direct part dinsu yanufa yana xuwa yawuce  bathroom ya sakarwa kanshi ruwa bayan yagama,   yafito ya shirya  ,ya kwanta yana tunanin halin yayan nasu 

 Anata bangaren kuwa

Bayan ya naseeb ya rakata yafita   ,,,toilet tashiga tayi wanka kota dan,ji kwarin jikin nata   ,,,,bayan tafito ,,bed tafada tana tunanin rayuwarta da Muhammad har barci yayi nasarar kwasheta . 

Haka rayuwa tayita tafiya inda naseeb da haleema suka kulla soyayya mai cikeda  tsafta ,inda nikuma bakuwar number nan kullum saita kirani tun INA dagawa INA tambayar waye ?saidai ace wani masoyinkine ,

.,nikuma hakan batamin rai yake saidai kawai nakashe wayar ,,yanxu hakama text ne yashigo wayata Wanda yasakani dubawa nafara karantawa, kamar haka !

"assalamu alaiki amincin Allah yatabbata agareki  ,yake ma' abociyar kyau da Kwarji ni 

idanuwa na suna sonjin xakakkiyar muryarki Dan Allah yau da misalin karfe shida kifito bakin gate dinku ,xanxo insha Allah ,,sako daga masoyinki mai kaunarki byee bye. 

 Bayan nagama karantawa mamakine ya kamani to wai waye wannan ?aikuwa ko wayema in anjima xan fita naje naga waye ,xan masa rashin mutumci kuwa ,,,,tunda anbi dashi ta lallami Amman bai hakuraba aikuwa xaiga abinda xan masa.

bayan yan awanni nafita parlour nan natarar da momy axaune tana kallon wani series film a Bollywood ,,,kwanciya nayi kan cinyarta nace ,momy kina xaune ke kadai ?

"momy tace ba dole naxauna nikadai ba ke kina daki narasa me kikeyi adakin idan kika shiga sai anganki ,,dariya nayi  nace momy xaman dakinne akwai dadi kuma kinga banason hayaniya. 

''gidanku mune masu hayaniyar ko kuma suwaye ?? "LA momy bafa dake nake ba ,,tafada cike da shagwaba tana duba agogon dake bangon parlour ,nan taga shida shaura  "

momy tace lpy daughter kike duba agogo ??? Eh momy bara natashi naje room dina .

"to tad'aka,cewar momy nikuwa murmushi nayi domin haka take tsokana ta 

________________Mikewa nayi naje daki nadauko shoe dina,  dama abayace ajikina saina warware mayafin Dana nade kaina dashi nayi rolling ,,ringtone wayata naji INA dubawa naga wannan number ce ,INA dagawa naji ance beb kifito ina jiranki batare da yajira abinda xanceba ya katse wayar 

fitowa nayi naga ma momy bata

 parlour   ,,harabar gate na nufa naga wata bakuwar mota hadaddiya agurin ,,nufar wajan nayi domin naga ko bakon da xanyine

 Amman ina isa naga yayan su halima "yacemin sannu yammata ,gaishe shi nayi nace yasu amme "yace 

suna lpy nace masa " haliman kake nema ko ?to bata xoba '"kallona yayi yace a'a ba halima nake nema ba ke nake nema ,

___________cikin xaro idanu nace masa nikuma ?to Allah yasadai lpy "eh lpy    agaskiya fenart baxan boye miki ba nafada cikin kogin soyayyarki ,tun lokacin Dana fara ganinki kuma nine Wanda nake kiranki kike kin dagawa . 

nikuwa cikin jin kunya nace masa au dama wai  Kaine  ?  


"ehm nine 

Acikin raina Dana sanin wulakantashi da nayi ,nake,SBD halima tamkar yar uwatace ta jini Amman maganar soyayya badaniba  Dan na rufe soyayya gabaki daya 

"kallona abrar yayi yace min INA fatan xaki amince da soyyayata. 

 "kallonshi nayi nace masa sai nayi tunani. 

batare da najira mexaiceba nayi tafiyata

 Daga baya kuwa naji karar tashin motarshi ,,,,,,,,INA shiga dakina nahau gado na dafe kaina saboda tsananin ciwon dayakemin ,kallon photon dake bangon dakina  nayi nace muhd

 INA sonka baxan taba son wani idan ba kaiba ,,hawaye tafara

tana share

Haka kwanaki sukaita shudewa

A inda mahaifin abrar yaxo gurin mahaifinmu yana maii nemawa dansa  aurena. 

shikuwa mahaifina yace xai tambayeni haka kuwa akayi mahaifina yace a kirani ,,INA xaune yaya naseeb yaxo dakina yace fenart kixo inji dady ,,gabana ne yafadi saboda akwanakin nan  INA yawan mafarki da dady yana min maganar aure ,,,to nace masa INA kokarin tashi cikeda rashin kwarin jiki ,,, muka jera da ya naseeb

 "knocking mukayi dady yace mushigo ,,shiga mukayi bakinmu dauke da sallama ,,gabana ne ya bada daram -daram ganin yaya ansar dake gefe yana xaune ,,,gaishe su nayi naxauna kan Capet "amsawa sukayi 

"dady ya kalleni yace nafeesat,mahaifin kawarki halima wato alhaji khabeer yaxo yasameni da wata magana akan yana ne mawa dansa abrar aurenki ,shine nace masa sai na tambayeki Dan baxan miki auren dole ba Amman dai ashawarce INA miki sha'awar auren abrar saboda yarone mai hankali ga mahaifinshi mutumin kirkine ,kuma muntaso a unguwa daya ,,  kuma munbaki dama har shekara day

Batare da muntakura miki akan kiyi aure ba. 

 '"idan kikayi auren xaki fi mantawa da abinda yafaru abaya damuwarki xata ragu kuma muma hankalinmu xaifi kwanciya ,,,Amman dai duk yacce kikagani .

"nikuwa kaina akasa ga wata faduwar gaba Dana tsinci kaina aciki ,,duk iya xaman danayi  da dady baitaba cewa  nayi aureba  sai yau ,,gashi nikuma banason na hada soyayyar muhd data kowa idan ma nayi auren to mijina baxai taba samun kainaba,  saboda xuciyata da gangar jikina, tana dauke da son muhd .

Feenart kinyi shuru "

momy takatse mata tunanin datake ,kallon su dady  nayi nakara sunkuyar da kaina, nace dady na amince bisaga kyakkyawar shawarar da kuka bani ,nasan baxa kutaba xabarmin abinda xai cuceniba .

"Ahhh alhmdllh madallah da samun diya tagari Allah yayi muku albarka ,insha Allah baxa kitaba da nasani da auren nanba ,,,nasib yace insha Allah dady  

"dady da da aure a tsakaninmu Aida dani xa ayi auren nan yafada cikeda barkwanci ,,,xaro idanu momy da dady sukayi cikeda tsoro da fargaba Dan har saida cikin momy ya murda SBD tsoro 

''Dady ne yayi karfin halin cewa ,,innalillahi ,,nasib kada nakarajin irin  wannan Kalmar  abakinka koda kuwa da wasa kake . 

"To Dady insha Allah ,kallon momy dady yayi yaganta cikin wani yanayi yaga xata kwabsa musu ,,Jan hannunta yayi suka fita daga cikin dakin ,dakin momyn suka shiga"  yace fateema ki nutsu ko so kike sugane ne ?

shifa kawai fada yayi bada nufin wani abun ba Amman kikabi kika tsorata haka "aidole naji tsoro dadyn ansar kada sirrin da muka dade da boyewa ya bayyana  ,,,,,hakan baxai fa ruba  fateema cewar dady 

       Abangaren su fenart kuwa bayan fitarsu dady ,fenart na gefe tagagara tashi ,maganar ansar CE tadoki dodon kunnensu yace ,,,,,gaskiya xa'a cuce abrar yana saurayinsa dal Amman ahadashi da baxawara😳 ,nasib ne ya kalleshi da mamaki yace ya ansar feenart fa jinin kace Amman kake fadan wannan maganar kuma dakake fadan haka ai sunna xaiyi ,,kuma kaima baka saniba koda baxawarar xaka fara.

katse naseeb ansar yayi ta hanyar cewa ,,,,kaiiiiii yaushe raini yashiga tsakaninmu ne da INA fadan magana kana mayarmin kuma da kake fadan na auri baxawara to saidai din kagani akanka ,,yafada tareda mikewa cikin fushi yafita ,,,,,,,nikuwa banyi mamakin jin furucin shi ba idan da sabo yaci ace da nasaba Amman wannan Kalmar daya fadamin takona min raiii kuma insha Allah saiya auri baxawarar ,"fenart kiyahkuri da  abinda ya ansar yafada miki kada hakan yadameki ,,,,, "LA yaya naseeb babu komai , na kakalo da murmushi dabai kai xuciba ,,mikewa nayi nafita , shima tashi yayi yafita .

________________ Ina shiga dakina naga tarin missed called ,ciki kuwa harda na halima da kuma wannan bakuwar number ,


halima nafara kira  tacemin dama yaya ne yadameta data kirani waiya bugomin ban daukaba shiyasa takirani "ohk kawai nace mata don banajin xance yau ,haka mukayi sallama ,,bamufi 3minute ba saiga kiran shi ,,dagawa nayi bakina dauke da sallama amsawa yayi muka gaisa yacemin yaji sakona ya gode Dana amince da aurenshi .

nikuwa mamaki nayi nace kenan har dady yasanar musu ,haka dai nashare xancen ,,,shikuwa haka yayi tamin xance irin na masoya nikuwa saidai daga eh sai a'a har muka kammala wayar. 

Plx share and comment

Tnk

Our Facebook page

Telegram

Our Whatsapp Group

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post